Kiñg_Bashø

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kiñg_Bashø, Electronics Store, Tripoli.

22/01/2022

HUKUNCIN AURE:

SHARE 🔔

A jumlace malamai sun kasu kashi uku dagane da hukuncin aure :

1- Su ne waɗanda s**a tafi akan wajabcin yin aure sau ɗaya a rayuwa.

A ra'ayin waɗannan malamai Idan mutum ya yi aure sau ɗaya to ya sauke nauyin dake kansa. Ya yi aiki da da hadisan da s**a ce ayi aure.

2- Malamai na biyu su masu ra'ayin cewa shi aure mustahabbi ne, wato ba wajibi ba ne. In ka yi aure za ka samu lada. Idan baka yi ba kuma ba ka da alhak i- amma da sharaɗin mutum zai iya tsare mutuncin kansa.

Ba zai zamo mai kalle kallen matan mutane ba har ya kai ka ga sha’awarsu ba,.

Ba kuma zai aikata zina ba ko danginta ko ya dinga bin wasu hanyoyin da s**a saɓawa shari'a wajen biyan buƙatarsa ba. Kamar wasa dabal'urarsa ko maɗigo ko nau'rorin zamani na biyan buƙata ba. Wato "Baby ko Boy doll "
Yin hakan , alama ce dake nuna yana buƙatar aure , don haka wajibi ne ya yi don ya kare kansa daga tafarkin halaka .

Amma ga wanda zai iya mallakar kansa kuma ba ya ƙyamar auren ya zaɓi ya zauna haka ba aure to ba wajibi ne ya yi ba. Musamman idan ya shagala da aiwatar da wasu abubuwa na taimakon addini kamar ianyatrwa da makamantansu.

Shehin Malami Abu Gudda ya wallafa littafi guda na manyan Malamai da s**a fifita ilmi akan aure. Ya kawo malamai kusan talatin da y’an kai, maza da mata, mashahurai, sanannu, gogaggu masu tsoron Allah, waliyan Allah, waɗanda har s**a koma ga Allah ba wanda ya yi aure a cikinsu.

Ba don suna ƙyama , ko suna gudun auren ba, sai don rayuwarsu ta shagaltu da wani aiki wanda ba su gama shi ba s**a koma ga Allah.
3- Malamai na uku su ne waɗanda suke da ra'ayin cewa shi aure ba wajibi ba ne ba kuma mustshabbi ba kai tsaye.

Suna ganin shi hukuncinsa yana sassaɓawa ne da saɓanin mutane s**a sassaɓa.

Don haka ba za a iya cewa wajibi ne ga kowa ba. Kuma ba za a ce mustahhabi akan kowa ba. Ya danganta da mai yin auren.

Don haka ba wajibi ne akan kowa ba. Kuma ba mustahabbi ne akan kowa ba Ya danganta da mai yin aure.

Akwai mutumin da aure yake wajibi akansa, shi ne mai ikon da ba zai iya kamewa ba.
Akwai wanda aure yake mustahabbi a kansa , shi ne mai ikon da zai iya kamewa.

Akwai wanda aure yake haramun a kansa, shi ne wanda aure zai kai shi ga sarayar da haƙkin Allah ko zai kai shi ga zaluntar iyalinsa ta hanyar hana su haƙkoƙinsu koda kuwa yana da iko.

Akwai wanda aure yake makaruhi akansa, shi ne wanda aure zai kai shi aikata abubuwan ƙyama da zubar da ƙima. Ko ya kaishi da shagaltuwa ga barin wasu ayyuka muhimmai da suke taimakawa al'umma kamar karantarwa kuma shi ga shi ba mai ƙarfin sha'awa ba.

Akwai wanda aure yake halal a gurinsa shi ne wanda aure ba zai canja masa wani yanayi ba.
Wannan shi ne abin da mazhabarmu ta Malikiyya da wani ɓangare na malaman Shafi’iyya da na Hanabila s**a tafi akai. S**a ce na farko aure ya kan zama wajibi akan wani mutum. To waye wannan wanda wajibi ne ya yi aure? S**a ce mutumin da yake da sha’awa mai qarfi kuma yana da buqata zuwa ga saduwa da mace. Wanda idan bai yi aure ba, ko idan ba ta yi aure ba akwai tsoron suna iya faɗawa zina. To wannan tsoron za a faɗa zina ɗin, ko ganin alamun haka, to wajibi ne ya yi aure domin ya kare kansa; itama mace wajibi ne ta yi aure domin ta kare mutuncin ta.

Abinda wajibi ba ya cika sai da shi to ya zama wajibi. Ma’ana tsare kai wajibi ne, to amma sai ya zama hakan nan ba zai yiwu ba sai an yi aure, ka ga aure ya zama wajibi kenan domin a tsare mutuncin kai. Sai malaman s**a ce matar da ta samu kanta a irin wannan yanayi, da namijin da ya samu kansa a irin wannan yanayi, wanda in bai yi aure ba zai iya faxawa halaka, to ko da ya tsare kansa daga halaka ɗin, wajibi ne yayi aure. Wannan shine kaso na farko da s**a ce maganar aure.

Abubuwa dai da ake awo da su , su ne yanayin kula da haƙƙin Allah da haƙƙin iyali da kuma buƙatar shi kansa mai auren. Sawa'un namiji ne ko mace. Ɗaya zai aura ko fiye da ɗaya.
Abin da ake cewa wajibi shi ne abin da ya zama dole ta yadda idan mutum bai aikata ba ya yi laifi.

Mustahabbi kuwa shi ne abin da idan mutum ya aikata zai samu lada. Amma idan bai aikata bai yi laifi ba.

Shi kuwa haram shi ne abin da idan ka aikata shi kana da zunubi. Amma idan baka aikata ba zaka samu lada.

Mai biye masa shi ne makaruhi wanda cikin aikata shi babu laifi. Amma akwai lada cikin barinsa
Na ƙarshe shi ne Mubahi. Wato abin da yinsa da barinsa duk ɗaya ne.

Babu laifi ma'aurata ko wani daga cikinsu ya sarayar da wani haƙƙi nasa, don a samu daidaito da kyautata zamantakewa. Matsawar dai hakan ba zai kai ga shiga halin ƙaƙa na kanyi ba.

Kamar yadda ba a yarda da sarayar da wani hakƙi na Allah ba.

Malamai sun yi saɓani dangane da waɗannan hukunce hukunce na aure guda biyar.
Shin sun taƙaita akan namiji ne kawai ko kuwa hukuncin ya haɗa har da mata ?
Wasu malaman sun tafi akan cewa wannan hukuncin bai shafi mace ba. Su a gurinsu mata dole ne su yi aure. Ba ya halatta ga wata mace ta zauna babu aure kodan kare kanta daga zargi.

Amma wasu malaman suna da ra'ayin cewa , kamar yadda hukuncin auran maza ya kasu kashi biyar.
To su ma mata hukuncin aurensu kashi biyar ne kamar na maza.

Masu wannan ra'ayin suna kafa hujja da hadisin Abu Sa’idul Khudri cewa: Wani mutum ya kawo ƙarar ƴarsa wajen Manzon Allah (SAW) Ya ce ya rasulallah wannan ‘yar tawa ta ƙi ta yi aure.

Sai Manzon Allah ya ce da yarinyar, ke ki je ki yiwa baban ki biyayya ki yi aure.
Sai yarinyar ta ce a’a ya rasulallah ba zan yi ba har sai ka bani labarin haƙƙin da miji yake da shi a kan matarsa. Idan na ji zan iya sai na yi.
Ta sake maimaitawa Annabi. Shi ma ya sake maimaita mata. Da ta sake maimaitawa.
Sai ya ce, to hakkin da miji yake da shi akan matarsa shi ne, da za a ce miji yana da gulando, ko maruru, ko kaluluwa, a ce ciwon ya fashe yana fitar da mugunya, ko yana zubar da jini. Ko kuma a ce hancinsa ya fashe yana zubar da mugunya ko yana zubar da jini, mace ta zo ta sa harshenta tana lashe wannan jinin, ko wannan mugunya da ke fita daga wannan ciwo ko gyambo, ko gulando, ko maruru ko, kaluluwa, to ba za ta iya biyan haƙƙin mijinta ba.

Sai wannan yarinyar ta ce “wai wai wai, na rantse da Allah da ya aiko ka, bazan yi aure ba har abada. Ba zan iya wannan ba.”
Sai Manzon Allah (SAW) ya ce " kada ku aurar da su sai da izinin waliyan su ".

Abin lura anan wannan yarinyar Manzon Allah ya ƙyale ta da ta ji cewa ita ba za ta iya sauke haƙkin miji ba tunda dai ba za ta yi zina ba. Saboda haka aka ƙyale ta da ta ce ba zata yi aure ba.

Da wannan wannan hadisin malamai suke ganin cewa akwai uzurin ƙin yin aure ga wacce ba za ta iya kula da auren ba, sannan ba za ta iya biyan haƙƙin mijin ba matuƙar ba za ta yi zina ko ta jawo wa babanta zagi ba.
Idan za ta jawowa babanta zagi ko abin faɗe kuwa to dole ta yi aure tunda za a iya cewa ya bar ‘yarsa ta gandame a gida.
A al'adance ma mata basa jin daɗin rayuwar idan s**a girma s**a gansamewa a gaban iyayensu, musamman su da ba zasu fita shagunan waje ko soron gida kamar namiji ba.
A irin wannan yanayi ta hanyar aure ne kawai za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali.
Don haka zai fiye mata ta yi aure koda kuwa ba zata ji daɗin auren sosai ba. Fiye da zama a yananin da zata damu kanta ta damu wani.
Zaɓar ƙaramar matsala akan babba yana daga ginsheƙai na koyarwar musulunci.
Allah masani.

22/01/2022

Wasu Mata Guda 5 Da Basu Cika Zaman Aure Ba:



A lokacin da wasu matan burinsu suyi aure sai mutuwa zai rabosu da gidan mazansu. A hakan kuma akwai matan da basu ma damu da auren ba, wasu kuwa idan ma sunyi aure basu ciki zama a gidan auren nasu ba. Ga irin matan nan guda 5 domin kaucewa maza asaran kudi da lokaci.


1⃣ Mata Kyawawa:

Su mata Kyawawa a kullum cikin yaudaran kansu suke yi da wannan kyau da Allah Ya musu.

Ganin yadda maza suke musu chaaaaa, na bukatar aurensu, hakan yasa koda sunyi aure abu kadan zai hadasu da mazan nasu sai su nemi saki.

Idan ka samu mata masu kyau halitta guda 10, sai ka samu 6 daga cikinsu sun taba yin aure fiye da sau daya.

2⃣ Mata Masu Illimi Mai Zurfi:

Su rukunin irin wadannan matan ba wai auren ne basa son zaman ba, babban matsalarsu shine basa son namijin da zai sa su ko ya hanasu. Wannan yasa koda sunyi aure suke kasa zama da mazan sai su fito.

Sai dai ga namijin da bazai takurasu ba zai sakar musu mara suyi abunda suke ganin shine dai-dai, to anan suna iya zama.

Domin akasarin irin wadannan matan za a samesu suna rike da wani matsayi na mukami a rayuwarsu. Ko kuma suna harkar kansu da basa son matsi ko takura.

3⃣ Mace Mai Tsananin Kishi:

Duk wata mace mai tsananin kishi bata iya zaman aure. Saboda a kullum tana son ta rika bibiyan abunda mijinta yake yi a gida da wajen gida.

Mata ne da suna iya yiwa mazajensu rashin mutunci a kowani lokaci a kuma ko ina.

Duk irin kauna da soyayyar da namiji yake yiwa mace mai zafin kishi dole ya hakura da ita muddin yana son yayi tsawon rai a duniya. Wannan yasa idan aka auresu dole ake rabuwa dasu.

4⃣ Matan Da S**a Saba Da Zina:

Duk macen data saba da zina yana da wahakar gaske ta iya zaman aure.

Kamar namijin daya saba da zina ne, da zai ajiye mata 12 idan anayi dole sai ya fita yayi wannan zinar, haka ita ma mace mazinaciya take. Hakurin saduwa dana miji guda ba sauyi bata saba da shi ba. Ita burinta duk namijin da yayi mata kawai ta nemeshi. Don haka aure zai iya takura mata a rayuwarta.

5⃣ Mata Masu Buri Na Musamman:

Akwai matan da suke da burin da suke fatan ganin sun cika a rayuwarsu. Irin wadannan matan burin nasu yana biyowa ne da wasu abubuwan da ba duk maza bane suke iya hakuri da basu hadin kai domin cimma su ba. Hakan yake sawa koda bayan auren idan miji ya nuna bayason abunda take so, sai ta gwammace rabuwa da shi maimakon jinginar da wannan burin nata data saka a gaba.

Akwai mata 'yan kasuwa da suke da burin ganin sunfi Dangote kudi, irin wadannan matan a kullum suna cikin tafiye tafiye ko rashin zama ko kula da iyalansu. Mata masu irin wannan burin sun gwammace hakura da aure da a rusa musu shirinsu.

Haka nan akwai matan da suke da buri na siyasa. Suma mata ne da basu cika zaman aure ba ganin ba duk maza bane suke basu damar da zasu cimma wannan burin nasu.


Sai dai ba ana nufin cewa kwatakwata mata masu irin wadannan siffofin basa zaman aure ba. Tabbas akwai da yawansu masu zaman aure kuma lafiya da mazajensu. Don haka idan akace wasu, ba ana nufin duka ba.

Da fatan za a mana kyankyawan fahimta.

22/01/2022

*YADDA ZAKA KULA DA MATARKA*

*1-Idan tayi fushi jawota jikinka ka rarrasheta,mata suna son rarrashi*.Hatta Manzon Allah SAW ya kasance yana rarrashin iyalinsa, kuma shi ne babban abin koyi ga kowa.*

*2-Idan kaga tayi shiru tambayeta meye matsalarta cikin murya mai sanyi da tausasawa da tausayi da jin kai*

*bawai da fada ba,al'adan mace ne ko anyi mata abu sai tace ba komai saboda ita komai sai tasa shagwaba kuma tana son mai rarrashinta.*

*3-Idan tayi kwalliya ka yabawa kwalliyarta,idan tayi girki kaci kana santi koda dadinsa baikai ayi santi ba.*

*domin idan baka ya A ba zata ga tayi kwalliyar a banza nan gaba baza kuma ba,ko kuma idan tayi ta dora a social media Nan zata samu masu yabawa.*

*4-Idan kukayi kwanciyar aure da ita ka nuna mata kololuwar jindadinka da ita, haka kuma da rana ka dauko zance kana zuzuta ta kana yabawa da irin ni'imarta wannan shi zaisa ta kara kaimi wurin kula da kanta*

*sannan ka fifita bukatar ta akan nata idan ka biya naka bukatar ka jira sai itama ta samu gamsuwa,inda baka da lafiya ka nemi magani idan baka iya ba ka koya.*

*5-Kana yabon kyawawan halinta kuma kana tausayawa mata da yimata uzuri idan tayi ba daidai ba*.

*6-Duk sanda ka samu lokaci kana shiga kitchen kana tayata ayyukan gida ko ba yawa ne, mata suna son su gansu tareda mazajensu suna tayasu aiki kai koda zuwa kawai kayi ka zauna bakayi komai ba zataji dadi a ranta*.

*7-Idan tace zata matsa daga kusa da kai riketa kace baka yarda ba, Idan kaga tana kuka sa bakinka ka tsotse hawayenta*.

*Idan kaga tana kishinka kyaleta kar ka kyareta,so kesa ayi kishi wanda baya sonka bazaiyi kishinki ba.*

*8-Idan bata da lafiya ka fita damuwa da halin da take ciki*.

*Idan kayimata laifi ka nuna rashin jin dadinka da hakan kuma ka bata hakuri.*

*9-Duk sanda zaka fita ka sumbace ta a goshinta.
Kana kasuwa ko office kirata ta waya kace kana kewarta*

*10-Kada kalmar (ina sonki ta dinga yiwa harshenka nisa) Maza ku gane wani abu ba ci da sha da sutura ne kawai zakayi ka burge mace ba. Wata zakaga ba abinda ta rasa na nau'in jin dadi amma tana cike da damuwa me yasa? Saboda ta rasa abubuwanda na lissafo a sama.*

*Wallahi akwai wanda sunfi shekara nawa suna samun matsala da iyalinsa sai kaji yana tutiyar bai rageta da ci ko sha ba sutura ma yanayi kawai halinta ne. Ba halinta bane ta rasa muhimman abubuwane a rayuwarta.*

*Sau da yawa anbar mazan hausawa a baya wurin kula da matansu kuma sune mafi dacewa da su kula da matansu idan mukayi duba da yanda Manzo S.A.W yakeyi da matansa.*

*Allah ya bamu nagari Wanda xamu kula da dukkan hakkinsu*

☏+2348037538596 or ☏+2348066627317
Sɪʀʀɪɴ ʀɪᴋᴇ ᴍɪᴊɪ
Sirrin Rike Miji

05/01/2022
21/12/2021

🧢
👔
👖
🧦

Want your business to be the top-listed Computer & Electronics Service in Tripoli?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Tripoli
122345
Other Electronics Stores in Tripoli (show all)
Mokab مكعب Mokab مكعب
Zaweit AL Dihmani
Tripoli

يفخر مكعب بأنه علامة تجارية ليبية متخصصة في بيع كل ما هو جديد في عالم انظمة الحماية وملحقاتها

تقنية لخدمات الانترنت تقنية لخدمات الانترنت
طريق المواشي
Tripoli

خدمات انترنت شبكات كروت انترنت

Spider Libya Spider Libya
Tripoli

Spider Libya for Satellite Receivers

Brandz store-متجر براندز Brandz store-متجر براندز
Tripoli

ارقى المنتجات النادرة في العالم بين يديك✨

Lenovo online libya Lenovo online libya
Tripoli

متجر الكتروني متخصص بمنتجات شركة لينوفو العنوان طرابلس

Al-sarh electronic الصرح للكهرومنزلية Al-sarh electronic الصرح للكهرومنزلية
Tripoli

الصرح للكهرومنزلية

مزايا موبايل مزايا موبايل
Tripoli, 218

بيع وشراء واستبدال الموبايل صيانة سوفتوير تنزيل برامج فتح ايكلود وجميل وتخطي شحن us للعاب زيارتكم تسعدنا

ليبيا تكنولوجي _libya technology ليبيا تكنولوجي _libya technology
Tripoli

عالم التقنية بين يديك ليبيا تكنولوجي إمتلك عالمك الذي تُحب

متجر اللؤلؤة -  alluwlua Store متجر اللؤلؤة - alluwlua Store
Tripoli

متجر الكتروني

BlueTech_بلو تيك BlueTech_بلو تيك
حي دمشق
Tripoli

متجر بلو تيك يقدم لكم أجود المنتجات بأفضل الأسعار في ليبيا

Mohsen phone Mohsen phone
Tripoli

خدمات صيانة هواتف � اكسسوارات