Jibwis Media Yandoto

لا طاعة لمن لم يطع الله عز وجل

26/03/2024

ya Allah ka kawo mana dauki a jihar mu ta Zamfara da sauran jihohin musulmi baki daya!

AudioCutter_AudioCutter_AudioCutter_هدم الحديث(2) - تحميل 26/03/2024

DAGA CIKIN MIYAGUN HANYOYIN Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi WURIN RUSHE HADISAN ANNABI :
Daga cikin ababen da Dr. Gumi yake fa'da domin rushe hadisan Annabi , da gabatar da ra'ayi akansa ; akwai cewarsa :
" Hadisan Annabi sun zo ne bayan fiqhu ya tabbata , kuma fiqhun shine ya rubucesu , don haka shine asalinsu , saboda haka idan hadisi ya ci karo da fiqhun malami to za a yi jifa da hadisinne , saboda fiqhun shine ke gaba da shi , domin shine ya samar da Hadisin !
Ga sautinsa anan :
https://www.raed.net/file?id=707238
Abun lura daga maganganunsa :
1. Dr. Gumi ya na ganin asali Annabi ya hana rubuta Hadisi , amma sai Umar bin Abdil Aziz ya yi amfani da Fiqhu ( ra'ayi ) sai ya rushe wannan Hadisi na hani , don haka sai ya yi umarni da rubuce Hadisi . Don haka su Hadisai fiqhune ya samar da su , don haka fiqhunne hujja akansu .
Amsa :
Amsoshi akan wannan magana ta hanyoyi kamar haka :
1. Asali Annabi bai hana rubuta hadisi ba kai tsaye , abun da aka sani ma ya yi umarni da rubuce Hadisan , kuma ya sani cewa wasu daga cikin Sahabbai suna rubutawa kuma bai hanasu ba .
Hadisin da Dr. Gumi yake rarumowa akan wannan batu wasu hadisan masu yawa wa'danda s**a fishi 'karfi suke nuni akan halascin rubutawan sun ci karo da shi , kamar hadisin Abu Harairah cikin Sahihul Bukhari , wanda Abu Huraira yake cewa Abdullahi bin Amru ya na rubuta hadisi amma shi ba ya rubutawa , da Hadisin da Annabi ya yi umarni da a rubutawa wani mutum daga mutanen Yaman ( Abu Shah) Hadisansa , da Hadisin Aliyyu bin Abi Dalib da yake bayanin abunda ke cikin littafinsa na Hadisan Annabi da ya rubucesu , duka wa'dannan suna cikin Sahihul Bukhari , da ma wasu hadisan daban .
Malamai sun samu sa'bani wurin ha'dawa tsakanin Hadisin Abu Sa'id na Muslim wanda yake hani akan rubutawa da kuma wasu Hadisai masu yawa da suke halattawa , sun fa'di maganganu kamar haka :
1. Wasu sun ce : Hadisin Muslim (من كتب عني غير القرآن فاليمحه) ya na da illa ; mafi inganci Hadisine MAUQUF ; bai isa zuwa ga Annabi ba , maganar Abu Sai'd ce , don haka ba zai ci karo da maganar Annabi ba na halascin haka . Daga cikin masu wannan fahimta akwai Al Imamul Bukhari .
2. Wasu kuma su ka ce an hanane saboda tsoron caku'dewarsa da Al'qur'ani , don haka bayan yankewar Al'qur'ani rubutawan halalne , don haka an share hukuncin Hadisin Abu Sai'd na hani akan rubutawan .
3. Wasu kuma su ka ce hanin ya shafi wanda ya tara hadisai da Qur'ani ne acikin littafi 'daya , amma wanda ya warewa kowannensu littafinsa to shi rubutun halalne gareshi .
4. Wasu kuma su ka ce an hana wanda ya aminta da rashin mantuwane , amma wanda bai haddace ba , ko ya haddace amma ya na tsoron mantuwa to ya halatta ya rubuta .
Wa'dannan sune zantukan malamai wurin ha'dawa tsakanin Hadisin hani da Hadisan halascin rubutawan . Sannan ijma'i ya tabbata akan halascin rubuta hadisan . Don haka rubuta hadisai ya tabbatane da nassin Hadisan Annabi da Ijma'in musulmi da ya dogara akan nassoshin Shari'a, ba a rubuta hadisai ba da ra'ayin wani mutum _wai_ bayan Annabi ya yi hani akan haka ( kamar yanda Dr. Gumi yake fa'di ) .
Ibnus Salah ya ce bayan ya ambato sa'banin magabata a karon farko game da rubuta hadisai :
" ثم إنه زال ذلك الخلاف ، وأجمع المسلمون على تسويغ ذلك وإباحته ،ولولا تدوينه في الكتب لدرس في الأعصر الآخرة "
( معرفة علوم الحديث )
Suyu'dy ya wa'ke wa'dannan zantuka na malamai duka acikin Alfiyyarsa , inda yake cewa :
كتابة الحديث فيه اختلفا...... ثم الجواز بعد إجماعا وفا
مستند المنع حديث مسلم ...... [ لا تكتبوا عني ] فالخلف نمي
فبعضهم أعله بالوقف ......وآخرون عللوا بالخوف
من اختلاط بالقران فانتسخ.......لأمنه، وقيل ذا لمن نسخ
الكل في صحيفة ، وقيل بل ...... لأمن نسيانه ، لا ذي خلل
2. Rubutawan da Umar Bin Abdil Aziz ya yi umarnine na rubutu a 'kar'kashin kulawar Gwamnati , ba wai dama can malamai da 'dalibai ba sa yin rubutun bane , sai kuma daga baya Umar ya ce to yanzu ya bada dama a yi rubutun ( kamar yanda Dr. Gumi yake fa'di ) , a a , dama can mabu'kata suna rubuce hadisansu , saboda Annabi ya badu dama , sai kuma Umar ya yi umarni da a rubuce Hadisan a 'kar'kashin kulawar gwamnatinsa , kamar yanda Usman ya yi umarni a rubuce Qur'ani bisa kulawar gwamnatinsa , wanda dama can musulmi suna rubuce Qur'aninsu , saboda Annabi ya basu daman yin hakan .
Shaikh Muhammad bin Aliy Al'atyuby ya na cewa game da umarnin Umar bin Abdil Aziz na rubuce hadisai :
"والمراد بالتدوين المذكور هو التدوين الرسمي ، بحيث يكون مجموعا مرتبا، وإلا فقد كان يكتب في الرقاع والعظام من لدن رسول الله صلى الله عليه وسلم وهلم جرا "
( إسعاف ذوي الوطر، ١/٣٧)
Saboda haka , indai umarnin Umar bin Abdil Aziz na rubuce Hadisi a gwamnatance shine dalilin da zai sa a ce ra'ayi shike gaba da Hadisi , to kuwa a fa'di hakan akan Al'qur'ani ; a ce fiqhu shi ke gaban Qur'ani , saboda fiqihunne ya ce a rubuta Qur'ani a gwamnatance a zamanin kilafar Usman bin Affan !
3. Wannan magana ta Dr. Gumi cewa : fiqhu ( ra'ayi ) shine ke gaba da Hadisan Annabi ( wahayi ) wai saboda shine ya samar da su ; wannan maganar asalinta qa'ida ce wurin 'yan bidi'ar ilmul kalam ( Jahmiyyah , Mu'utazila Rafidha , Murji'ah dss) , sune suke cewa : hankali shike gaba da wahayi , wai saboda hankalin shine ya gano ingancin musulunci daga sauran addinai , don haka dole a gabatar da shi akan wahayin da musulunci ya zo da shi , idan ba a yi hakan ba to hakan zai bayu ga rusheshi , rusheshi kuma rusa asalin musuluncine , don haka ingancin musulunci ba zai tabbataba har sai an yarda da gabatuwan hankali akan wahayi !
To shima Dr. Gumi akan wannan mummunan muqaddima ya gina wannan 'batar ta shi , shi ya sa yake cewa matu'kar ba a yarda da gabatuwan fiqhu ( ra'ayi ) akan hadisai ba , to hakan zai bayu ga rushe Hadisan daga tushensu !
4. Abun da aka sani a wurin malamai shine : asali malamai suna himmantuwane da rubuce Alqur'ani da Hadisan Annabi ba tare da ha'dasu da wasu maganganu daban ba , daga baya ne aka fara samun wasu malamai s**a fara ha'dawa da fassaran wasu 'dai'daikun kalmomi na Qur'anin ko Hadisi , kamar Ma'amar Ibnul Musannah acikin Majaazul Qur'an , duk da cewa wasu malaman sun 'kyamaci hakan , kamar Imamu Ahmad ; su suna gani a bar maganar Allah da Annabi zallansu kamar yanda suke , kar a gwamasu da fahimtar wani tare da su , hakanan aka samu wa'danda s**a gwama Hadisan Annabi da fahimtar wasu Sahabbai da Tabi'ai , kamar Imamu Malik , anan ma wasu malaman s**a 'kyamaci wannan salo nashi , kamar Imamu Ahmad da wasunsa .
Don haka abun da yake asali wurin malamai shine : rubuce Alqur'ani da Hadisan Annabi tsuransu , daga baya ne a ka fara ha'da hadisan da fahimtar wasu Sahabbai da Tabi'ai saboda bu'katuwa zuwa ga hakan .
Don haka jahilcine mutum ya zo ya ce wai Hadisai sun samune bayan Fiqhu !
Sannan kuma shi wannan ra'ayi na mazahaba da Dr. Gumi yake ihu akansa har yake gabatar da shi akan Hadisan Annabi , shi fa wani abune sabo fil a musulunci , su magabata Sahabbai da Tabi'ai basu sanshi ba , suma jagororin mazhabar basu sanshi ba , su addini a wurinsu shine Al'qur'ani da Hadisi da abun da Sahabbai s**a rayu akansa , daga bayane da ilimi ya yi rauni aka bu'katu zuwa ga mazhabobi domin sau'ka'kawa ga gama_gari da mai koyon ilimi wurin fahimtar addini , amma babu wani mai hankali da yake 'daukan ra'ayoyin mazhabobin amatsayin hujja akan halittu , abun da yake hujja akan halittu kawai sune Qur'ani da Hadisi da Ijma'in Sahabbai.
Da tafiya ta 'kara nisa kuma sai a ka samu wasu kasalallu marasa tsoron Allah , sai s**a mayar da mazhabobin a matsayin Shari'ar Allah saukakkiya , s**a mayar da shuwagabannin mazhabobin tamkar allola masu shar'antawa , s**a lalata addini , s**a zare kwarjini na maganar Allah da Annabi daga zuciyar gama_garin musulmi .
To in ba hauka ba ta yaya za a ce abun da ya faru daga baya saboda raunin musulmi kuma ace shine ke gaba da asalin tushen musuluncin ?!
Abu Zaid Ubaidullah Addabbusy Alhanafy ya na cewa :
" وكان الناس في الصدر الأول أعني الصحابة والتابعين والصالحين رضوان الله عليهم أجمعين يبنون أمورهم على الحجة ، فكانوا يأخذون بالكتاب ، ثم بالسنة ، ثم من أقوال من بعد رسول الله صلى الله عليه وسلم ما يصح بالحجة ، فكان الرجل يأخذ بقول عمر رضي الله عنه في مسألة ، ثم يخالفه بقول علي في مسألة أخرى ، وقد ظهر من أصحاب أبي حنيفة رضي الله عنه أنهم وافقوه مرة وخالفوه أخرى على حسب ما يتضح لهم بالحجة .
ولم يكن المذهب في الشريعة عمريا ولا علويا، بل النسبة إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم، فكانوا قرونا أثنى عليهم النبي صلى الله عليه وسلم بالخير ، فكانوا يرون الحجة لا علمائهم ولا نفوسهم ، فلما ذهبت التقوى من عامة القرن الرابع ، وكسلوا عن طلب الحجج ، جعلوا علمائهم حجة واتبعوهم ، فصار بعضهم حنفيا، وبعضهم مالكيا ، وبعضهم شافعيا، ينصرون الحجة بالرجال ، ويعتقدون الصحة بالميلاد على ذلك المذهب ، ثم كل قرن بعدهم اتبع عالمه كيف ما أصابه بلا تمييز ، حتى تبدلت السنن بالبدع، وضل الحق بين الهوى "
( تقويم الأدلة ، ٤١٥)
5. Matu'kar Dr. Gumi ya nace akan gabatar da ra'ayi akan Hadisi bisa umarni da Umar bin Abdil aziz na rubuce hadisan a gwamnatance , to za a yi masa ilzami da rubuta Alqur'ani a gwamnatance a zamanin Usman bin Affan ; sai a ce da shi : to shima Qur'ani ka gabatar da ra'ayi akansa , tunda shima ra'ayine ya samar da rubuceshi a gwamnatance .
A taqaice , maganar Dr. Gumi cewa wai fiqihune( ra'ayi ) ya samar da Hadisi ; wannan maganar ba gaskiya bace , Annabine ya ce a rubuta Hadisi , sannan kuma ijma'in musulmi ya tabbata akan haka . Sannan kuma gininsa akan haka da cewa : Fiqhun ( ra'ayi) shike gaba da Hadisi ; wannan kuma 'batace mabayyaniya , wacce aka assasata akan mugun son zuciya da jahilci .
Mallam Ateeq Sulaiman

AudioCutter_AudioCutter_AudioCutter_هدم الحديث(2) - تحميل AudioCutter_AudioCutter_AudioCutter_هدم الحديث(2) - تحميل

08/03/2024

Tasting

08/03/2024
15/10/2023

Wannan shine son Manzon Allah?

15/10/2023

Allah ka taimaki Falasɗinawa

Vous voulez que votre personnage public soit Personnage Public la plus cotée à Niamey ?
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.

Vidéos (voir toutes)

Tasting
Wannan shine son Manzon Allah?

Téléphone

Adresse

Niamey
Autres Personnage public à Niamey (voir toutes)
Que pensez vous sur les prédilections du 21/12/12 Que pensez vous sur les prédilections du 21/12/12
Niamey
Niamey, 00227

scientifique, superstitieux, fanatique et tous ce que vous pouviez etre, vos commentaire sont trés

Mar çien Mar çien
Niamey

L'aigle ne fuit jamais la tempête.par contre,il s'en sert pour prendre de la hauteur 🦅🦅🦅🦅✅✅

NASTY NASTY
Rn1
Niamey, 8001

[email protected]

Collège et lycée cours de soutien Collège et lycée cours de soutien
Hachimouhachimou42@gmail. Com
Niamey

Enseignant de formation، Enseignant particulier, tout est mathématiques. Merci de vous abonner

Leader Raoul Officiel Leader Raoul Officiel
Niamey

Entrepreneur - Formateur - Motivateur - Conférencier

POOJA POOJA
Niamey

Welcome to the new page of entertainment and publication of the stories of lovers who were once called the chronicles of Malachi. We created this new page with the aim of finding ...

Cesfap-Mahkmon Cesfap-Mahkmon
Yantala-Gadafawa, En Direction De L'Ambassade De France
Niamey

Collège d'Economie Sociale Familiale et des Apprentissages Privé-MAHKMON