Ummu Ahmad
Am nothing am Zero behind decimal point
*ADDINI NASIHA NE*
Mutane suna so su yi arziki amma suna manta zunubai suna hana arziki.
Manzon Allah, sallallahu alaihi wa sallama, ya ce: *"Lallai ana haramta ma bawa arziki saboda wani zunubi da yake aikatawa"*.
"Abinda yafi komai takaici a Alkiyama shine, ga ladanka baka iya bawa iyayenka da 'ya'yanka da masoyanka ba amma kana kallo za'a dauka a ba makiyanka don kaci namansu ko ka zalunce su wajan yin munarfurcinsu ko cin dukiyarsu bada izni bah".
*Ya Allah ka tsaremu da fadawa tarkon Shedan
HANYOYI DA ZASU AMFANEMU DON CIN MORIYAR SAURAN KWANAKIN DA S**A RAGEMANA MASU MATUKAR TSADA:
1. Yawaita Istighifari
2. Yawaita Karatun AlQur'ani Ladan bai misaltuwa.
3. Yawaita Sadaka - Hanyar samun tsira ce.
4. Dauki Waya ka Kira 'Yan uwa - Sadar da zumunci ne.
5. Kame bakin ka - Zaka kubuta daga gulma ko alfasha.
6. Yi Addu'a wa danuwa - Malaa'iku za su maka.
7. Taimaka Wa mabuqaci - Allaah zai baka mafita.
8.Ciyar da mai Azumi - Zaka samu ladar Azumi a sauqaqe.
9. Kwanta da wuri - Hakan zai baka daman tashi da dare.
10. Yawaita yin zikiri - Wannan zai baka daman kusantar mahaliccin ka.
11. Rage Shiga Social Media - Hakan zai Baka damar Ibadah.
12. Yafe ma Wanda Ya Maka Laifi, Hakan zai Sa Allaah Ya Yafe Maka.
13. Tura Wannan Saqon Wa Wani - Hakan Zai Sa Ka Samu Ladan Wanda Yayi Aiki Da Shi.
✍🏼✍🏼Ummu Ahmad
Da GASKE Ka KE KO YAUDARAR KANKA Ka KE??
Imam Ibnul Jauzi Allah ya masa rahama yana cewa, "Sau tari akan samu mutum yana ikrarin yana da tauhidi alhali mushrikine wa Ubangijinsa, dayawa akan samu mai cewa shi bawan Allah ne alhali kuma bawan cikinsa ne, yana saɓawa Ubangijinsa wurin yiwa kansa biyayya, ya sayar da yardar Allah dan neman yardar abun halitta irinsa.
Sau nawa aka samu mai bin son zuciyarsa wanda ya riki zuciyarsa a matsayin abun bautarsa, sau nawa kuma aka samu wanda yayi riko da umarnin Ubangijinsa wanda yake sayar da kansa wurin neman yardar Ubangijinsa".
Mace ta gari ita ce wadda ta san Abinda ya dace ta yi idan mijinta yana cikin fushi ko yunwa ko gajiya. Sakarai ita ce wadda ake jin sirrin mijinta daga wurin ta.
Namiji sadauki shine idan ya samu alheri sai ya nufo gida wurin iyalansa. Sakarai
shi ne mai dukan matarsa.
A lahira Munafukai sune a ƙasan wuta. Amma a duniya sunayensu ne a saman Jarida.
Mutum biyu ba a gaskata maganarsu: Mai neman aure da mai neman aure
Mutum uku kana iya biyan su: Wanda ya fara yi maka sallama, da wanda ya ba ka wurin zama, da wanda ya yo tafiyayya zuwa wurin ka. Na huɗu sai dai ka roƙi Allah ya biya shi: Shine, wanda yake da buƙata bai ga inda ya dace ya nemi taimako ba sai a
wurinka.
_Akwai wata rana da zantafi💔_
_Kuma bazan sake dawowa ba💔_
_Akwai wata rana da zanyi bacci💔_
_Kuma bazan sake tashi ba💔_
_Akwai wata rana da zan rufe idona har abada💔_
_Akwai wata rana da zata zama babu ni💔_
_Akwai wata rana da zakuyi message a contacts dina amman babu reply zakuyi ta tunanin k**ar zanmuku reply amman na tafi forever and I will never come back a haka har kowa zai manta da ni💔_
_Akwai wata rana da zaku yi kuka shi kenan babu ni💔_
_Akwai wata rana da zaku so ganina amma babu ni💔_
_To kunsan yaushe ne wannan ranar💔_
_Wata kila yau ne !💔_
_Wata kila kuma bayan sati Daya ne !💔_
_Wata kila kuma bayan wa ta daya ne !💔_
_Wata kila kuma bayan shekara daya ne !💔_
_Wata kila kuma bayan lokaci me tsaho ne !💔_
_Wata kila kuma kana gama chat da ni ! 💔_
_Sai mutuwa ta dauki rayuwata !💔_
*Sabo da haka !💔*
*Ina me neman afuwa akan duk wani laipi dana muku yan uwa kuma ni nayafewa dukkan masoyana Allah ya yafe mana baki daya😭*
✍🏼✍🏼Ummu Ahmad
*RAYUWA TAYI TSADA*
Naje sayen *GASKIYA* aka cemin *WALLAHI* tayi wuya sai mai rabo ne yake mallakar ta
Nace to *AMANA* fa akace min tab wannan ai sai wane da wane
Nace ko zan samu *AMINCI* da abota saboda *ALLAH?* aka ce min su wadannan akwai su amma sai kana da abin duniya zaka samu
Nace to *SOYAYYA* fa? Aka ce eh muna dasu amma kadan ne na gaskiya in kana bukata sai kayi hakuri
Nace to ina zan samu *HAKURI DA JURIYA?* Aka ce min a'a gaskiya anfi siyan gaggawa don haka bama kawo ta
Nace Ina zan samu *TARBIYYA* farashin sari?
Aka ce min akwai amma tana tsada don tayi karanci wahala take.
Nace *LADABI* fa? Aka ce min ai tuni aka daina maganar sa, tun yan shekarun baya sai tarihi
Nace *ADALCI* fa? sai naje masarauta, ko gidan gwamnati ko kotu ko tsakanin ma'aurata? Aka ce min tab ai suma tasu ta kare tun lokacin iyaye da kakanni
Nace da can wajen manya ake samun *DATTAKU* da *ALKAWARI,* Ko Zansamu? Aka ce min ai yanzu karyace tafi komai yawa acan gurinsu
Nace to menene mafita da zata kai ni ga samun *JINDADI* da kwanciyar *HANKALI* a yanzu???
Sai yace ga *WASIYYA* zan baka: Kaji tsoron *ALLAH,* kayi amfani da naka lokacin wajen *Ibada* da *Addu'a.*
Kar ka sake lokaci ya kure maka, kuma ka kusanci mutanen kirki don zama da "madaukin kanwa".......!
*Allah Ya sa mudace!*
✍🏼✍🏼Ummu Ahmad
*Ya ALLAHU YA HAYYU YA* *QAYYUM* Ka Karbi Ibadunmu, Ka Tsarkake Mana Niyyar Mu, Kai Mana Maganin Abunda Ke Damunmu, Kayi Mana Mafita, Ka Kyautata Karshenmu, Kajiqan Dukkan Magabatanmu. *Alfarmar Annabin Rahma* *Sallallahu Alaihi* *Wasallam*
Barka da asuba
*Ya ALLAHU YA HAYYU YA* *QAYYUM* Ka Karbi Ibadunmu, Ka Tsarkake Mana Niyyar Mu, Kai Mana Maganin Abunda Ke Damunmu, Kayi Mana Mafita, Ka Kyautata Karshenmu, Kajiqan Dukkan Magabatanmu. *Alfarmar Annabin Rahma* *Sallallahu Alaihi* *Wasallam*
Barka da asuba
Rukayyah Muhammad Abdallah
Ummu Ahmad
,: https://chat.whatsapp.com/E5PWVZPx4uqG9cFblttrIT
🌷ALLAH YASAKAWA MALUMANMU DA ALKHAYRI🌷
🌷Bazan manta da jan hankalin da malamata take mana Ba kullum.🤍
🌷A kullum tana fadi mamu cewa Duk Diyar da ta bautu A Gidan mahaifanta, Tazamo mai yimusu biyayya da kyautata musu sunajin dadinta,
🌷Babu shakka zatayi mamakin mijin da Allah zai bata,Nagartacce wanda bata taba tsammani ba a rayuwarta😢
🌷Yak**ata `yan uwana `yan mata Mu rage son jiki da biyewa wayoyin hannunmu Dan wallahi matuqar zamu biyewa waya taw Bazamuyi abunda yak**acemu ba na rayuwa,
🌷Abin takaici da bakin ciki wata tana kwance tana dannar waya tabar mahaifiyarta da wanke-wanke,shara,Kai dan rashin kunya harma da girki a gaskiya wannan babban abin kunya ne🤦♀️
🌷Shin na tambayeki mana🤔Shin zakiso `yar ki da kika haifa tamaki kalan wannan?
🌷Taw matuqar kuwa bakyaso yazama wajibi Yanzu ki farka daga barcin da k**eyi, Ki tashi kiyi wa mahaifiyarki hidima,tin kina da Sauran dama Dan wallahi yanzu ne k**e da dama daga sanda kika rasata zakiyi kuka zakiyi nadama, nadamar da bata da amfani,Saidai kita neman gafarar ubangiji
😭Dan ALLAH ´´yan uwana mata Kumu zamo masu tausayawa mahaifanmu,domin duk duniyar nan wallahi bamu da k**arsu.
🌷kumu musu abinda zasuyi dariya suyi Alfahari damu,Ko da bayan sunmana aure Su dinga tina Alkhairanmu a garesu,
🌷Har suna cewa Allah Sarki wance da tana nan Da yanzu duka aikin nan itace zatayishi😊ALLAH yamata Albarka, Yaqaro musu zaman lafiya da mijinta, taw kinga baki san anayi ba amma Albarkar mahaifiyarki tana ta bibiyarki, Kullum kina kara shiga ran mijinki da mahaifiyarshi,da danginshi,
🧏♀️Yanzu wannan bazai zamo abin alfahari a gareki ba, Ga yaranki Suma suntaso da jin kan mahaifiyarsu da Kyautata mata, kisani duk abinda kikai shi za´a maki, Ki aikata Alkhairi Sai ki girbi Alkhairi , Allah yasa mudace Aameen
Kowa yaji dadin wannan Tinatarwa yamin Addu`an Alkhayri, Da ni da mahaifiyata☺️
JAZAKUMULLAHU KHAIYRAN🙏
🇵🇰 بلغوا عني ولو آية 🇵🇰3 WhatsApp Group Invite
☸☸☸☸☸☸☸☸☸☸☸☸
*🌐DUNIYA MAKARANTA KASHI NA BIYU (2)🌐*
*Rubutawa: Prof. Muhammad Mansur Sokoto*
👉351.Wayar Salula da intanet suna kusanto maka wanda yake nesa. Amma idan ba ka yi hankali ba sai su nesanta ka da wanda ya fi kowa kusa da kai, shi ne Allah
mahaliccinka.
👉352.An tambayi wani mai hikima, me ya sa muke ganin sama fara tas? Sai ya ce, don ba mu rayuwa a cikin ta. Ido na raina wanda yake gani kullum.
👉353.Abu biyu ne suke sa ka ci riba a rayuwarka: Sanin girman kai da barin girmankai.
👉354.Mutane da yawa da ka san abin da suke fadi a bayan idonka, da ka yanke hulda da su. Wani rashin sani ma yana da amfani.
👉355.Duk abin da ka yi masoyanka ne kawai kake burgewa. Masu hassada sai dai su yi
murmushi don su batar da hankalinka. Amma fa hasada ga mai rabo taki ce.
*Ga masu bukatar shiga group*
⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇⬇
Email: [email protected]
Facebook: Jibwis Katsina L.G
WhatsApp: 07062584992, 08038977817, 0703074 7392, 07036879671, 08036958490
As Copied.
*I find this Message Very interesting and meaningful to pass it on*:-
```IF:
A = 1
B = 2
C = 3
D = 4;
E = 5
F = 6;
G = 7
H = 8;
I = 9
J = 10
K = 11
L = 12
M = 13
N = 14
O = 15
P = 16
Q = 17
R = 18
S = 19
T = 20
U = 21
V = 22
W = 23
X =24
Y = 25
Z = 26.```
*THEN,*
```H+A+R+D+W+O+R+K
=8+1+18+4+23+15+18+11
= 98%
K+N+O+W+L+E+D+G+E
=11+14+15+23+12+5+4+7+5
=96%
L+O+V+E
= 12+15+22+5
= 54%
L+U+C+K ;
=12+21+3+
11
= 47%
A+N+O+I+N+T+I+N+G;
1+14+15+9+14+20+9+ 14+7 = 94%
None of them makes 100%.
Then what makes 100%?
Is it Money?
NO!
M+O+N+E+Y
= 13+15+14+5+25```
*=72%*
Leadership?
NO!
L+E+A+D+E+R+S+H+I+P
=12+5+1+4+5+18+19+8+9+16
=97%
Every problem has a solution, only if we perhaps change our```
*ATTITUDE*...
```A+T+T+I+T+U+D+E = 1+20+20+9+20+21+4+5 = 100%
It is therefore OUR ATTITUDE towards Life and Work that makes
OUR Life 100% Successful.```
*This Mathematics is Amazingly Instructive*As Copied.
*I find this Message Very interesting and meaningful to pass it on*:-
```IF:
A = 1
B = 2
C = 3
D = 4;
E = 5
F = 6;
G = 7
H = 8;
I = 9
J = 10
K = 11
L = 12
M = 13
N = 14
O = 15
P = 16
Q = 17
R = 18
S = 19
T = 20
U = 21
V = 22
W = 23
X =24
Y = 25
Z = 26.```
*THEN,*
```H+A+R+D+W+O+R+K
=8+1+18+4+23+15+18+11
= 98%
K+N+O+W+L+E+D+G+E
=11+14+15+23+12+5+4+7+5
=96%
L+O+V+E
= 12+15+22+5
= 54%
L+U+C+K ;
=12+21+3+
11
= 47%
A+N+O+I+N+T+I+N+G;
1+14+15+9+14+20+9+ 14+7 = 94%
None of them makes 100%.
Then what makes 100%?
Is it Money?
NO!
M+O+N+E+Y
= 13+15+14+5+25```
*=72%*
Leadership?
NO!
L+E+A+D+E+R+S+H+I+P
=12+5+1+4+5+18+19+8+9+16
=97%
Every problem has a solution, only if we perhaps change our```
*ATTITUDE*...
```A+T+T+I+T+U+D+E = 1+20+20+9+20+21+4+5 = 100%
It is therefore OUR ATTITUDE towards Life and Work that makes
OUR Life 100% Successful.```
*This Mathematics is Amazingly Instructive*
Umar Bn Khattab radiyallahu anhu yace:
"MATA IRI UKU NE:
1. Mace ta farko dai ita ce Musulma mai sauƙin kai, mai tausasawa, kuma k**ammiya, abar ƙauna kuma mai haihuwa, ta na taimakon iyalinta a game da zamani amma ba ta taimakon zamani a kan iyalinta (wato ta na taka-tsantsan da zamani game da iyalinta), ba kuma za ka same ta ta gaza a kan haka ba.
2. Mace ta biyu ita ce Musulma k**ammiya wadda ɗanta shi ne damuwarta kuma ba za ka samu wani abu ƙasa da haka a gareta ba.
3. Mace ta uku: gul (k**ar sarƙa) ko ka ce kwarkwata wadda Allah ya ke rataya wa a wuyan wanda ya so, ba kuma mai iya cire ta face Shi (Allah, ɗin).
MAZA IRI UKU NE:
1. Namiji na ɗaya mutum ne Musulmi, k**amme mai hankali, ya na tintintuni a kan abubuwan da su ka bijiro kuma su ka yi k**a da juna, idan hakan ta faru sai ya fice daga cikin lamuran domin tsira da ra'ayinsa.
2. Namiji na biyu mutum ne Musulmi k**amme wanda ba shi da ra'ayi, idan wani abu ya faru sai ya je wajen ma'abota ra'ayi masu bada shawara domin tuntuɓar su, su kuma sai su ba shi umarni kafin ya yanke hukunci a kan al'amarinsa.
3. Namiji na uku mutum ne fitinanne, fusatacce, ba ya maraftar shiriya kuma ba ya yi wa duk wani mai shiryarwa biyayya."
📙(مصنف ابن أبي شيبة 126)📙
Khalīfah Sulaymān bn AbdulMalik ya taba tambayar Abū Hazim ﺭﺣﻤﻬﻤﺎ ﺍﻟﻠﻪ :
"Ya Abū Hazim! Me yasa muke ƙin mutuwa?"
Abū Ḥāzim ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ ya amsa:
"Saboda kun gina rayuwar duniyarku amma kun yi watsi gami da lalata lahirarku, don haka kuna jin tsoron barin abin da kuka gina don komawa zuwa ga abinda kuka lalata."
[ ﺻﻔﺔ ﺍﻟﺼﻔﻮﺓ ﻹﺑﻦ ﺍﻟﺠﻮﺯﻱ ]
*“”MAI SAƁON ALLAH!“”*
_“Kaiconka, kuma dai Kaiconka, me ke gareka da har kake jin daɗin saɓawa ubangijinka Allah alhalin kuma shi ne wanda ya halicce ka?”_
*“Da wacce fuska kake shirin tunkarar mahaliccinka Allah a ranar lahira idan ka kasance mai yawan saɓa masa a wannan duniyar?”*
_“Za ka sami mutane da yawa shaiɗan ya gama yin tasiri a jikinsu, yabi jini yabi tsokar da take cikin jikinsu, dukkanin wata mu'amalarsu cikin saɓon Allah suke yinta!”_
*“Abin da zai baka haushi ma, wani a daidai lokacin da zai saɓawa Allah ɗin sai kaji ma ya kira sunan Allah ɗin, sannan sai ya saɓa masa, kai in banda Allah madaukakin sarki mai rahama da jin ƙai ne, da tuni bai juya wannan duniyar da mutanen cikinta sun kife ƙasa ba.”*
_“”Allah Ta'ala Kayi Mana Rahama Baki ɗaya.“”_
*Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!!!*
Ana gayyatar yan uwa Musulmi zuwa wurin gagarumin wa'azin da aka shirya za'a gabatar k**ar haka:
*Rana: Asabar 23 ga watan October, 2021*
*Lokaci: Bayan sallar Isha'i*
*Wuri: Masallachin Mua'z bin Jabal, kwabren dorowa, Katsina*
*Malamai masu wa'azi:*
Malam Abdullahi Ayyub. Malam Abubakar mai kano. Malam Abdurrahim sabi'u Rafin Dadi
Malam Munir isa kerau
Dr. Muhammad Usamatu Abbas
Malam Aminu Usman (Abu Ammar)
Malam Shamsudden Abdulkarim
Malam Bunyamin Muhammad Balarabe
Malam safiyyu Alkasim Saulawa
Malam Haruna Muhammad sani. Malam Zakariyya Aliyu sandamu
Allah ya bada ikon zuwa Amen.
📢Sanarwa daga kwamitin shirye shirye
بلغوا عني ولو آية 2 WhatsApp Group Invite
NASIHA CE
Mai Rike Addini Ba Jin Dadi Ne Bai Iyaba, Macce Mai Hijabi Ba Adone Bata Iyaba, Mai Kyauta Ba Kudi Ne Baya So Ba.
Kowannen Su Ya Kware Ne Wajan Sanin Abinda Ke Amfanin Sa, Sai Ya Rinjayi Son Zuciyar Sa.
*“”Kalmar Shahada: LAA ILAHA ILLALLAH“”*
●Dalilinta:
_Allah Madaukaki yace:_
*"فاعلم أنه لا إله إلا الله".*
"Ka sani cewa, babu abin bautawa face Allah" [Muhammad-19].
●Ma'anarta:
*Babu abin bautawa bisa chanchanta face Allah Madaukakin Sarki.*
●Ta na da rukunai guda biyu(2):
_(1)Korewa(Nafyu)_
Allah Madaukaki yace:
*"فمن يكفر يالطاغوت..."*
"Wanda ya kafurcewa dagutu".(Bak'ara:256)
"Dagutu: Shine dukkan abin da a ke bautawa koma bayan Allah.
(2)Tabbatarwa(Ithbaat)
Allah Madaukaki yace:
"ويؤمن بالله..."
"Kuma yayi imani da Allah".
*●Fadinta ba zai amfanar da mutum ba har sai:-*
1-Ya san ma'anarta.
2-Ya yi aiki da abin da ma'anarta ke nuni.
_“Allah Yasa Mudace
NASIHA CE:
"Kada ku gaji dayin addu'a
babu wanda zai halaka
mutukar yana yin addu'a
Cewa ma'aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam)
ALLAH ya kara mana himma wurin cigaba da gabatar da addu'o'i.
Barkamu da war haka yan uwa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Contact the university
Telephone
Website
Address
Abuja
NO
Lincoln Building Along Jikwoyi/Karshi Road, Jikwoyi
Abuja, 900110
We are now in Nigeria to offer purely practical courses to train you with the needed skills to earn money and get employed before you graduate. Installmental payment options and sc...
Dutsinma Street
Abuja
This is a good page if you can join it you will be a smiler
No 42 Sule Mai Ganga Street Un/sule Romi, Kaduna
Abuja, CHOICEBRIGGS
De YOUNG Brakers group is all about the youth, entertainment, awareness, informations, empowerment and culture. Young breakers we break through the challenges.
Abuja
Vote vote Sputnik ultimate search contestants number 075 by Monday adams,stage name Rayms