President Bola Ahmed Tinubu

Welcome you to Jagaban official website

02/01/2024
Photos from President Bola Ahmed Tinubu's post 19/12/2023

Had a fruitful bilateral meeting with the President of the UAE, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan, reinforcing the strong Nigeria-UAE partnership and our shared commitment to expanding ties between both countries.

01/10/2023

Fellow Nigerians,

Nigeria is remarkable in its formation and essential character. We are a broad and dynamic blend of ethnic groups, religions, traditions and cultures. Yet, our bonds are intangible yet strong, invisible yet universal. We are joined by a common thirst for peace and progress, by the common dream of prosperity and harmony and by the unifying ideals of tolerance and justice.

The journey ahead will not be navigated by fear or hatred. We can only achieve our better Nigeria through courage, compassion and commitment as one indivisible unit.

I promise that I shall remain committed and serve faithfully. I also invite all to join this enterprise to remake our beloved nation into its better self. We can do it, We must do it. We shall do it.!!!

I wish you all a happy 63rd Independence Anniversary.

01/10/2023

JAWABIN MAI GIRMA, SHUGABA BOLA AHMED TINUBU, GCRFR, SHUGABAN KASA KUMA BABBAN KWAMANDAN ASKARAWAN NAJERIYA A CIKAR JAMHURIYAR TARAYYAR NAJERIYA SHEKARU 63 DA SAMUN ‘YANCIN KAI, RANAR LAHADI 1 GA OKTOBA, 2023

‘Yan uwana ‘yan Najeriya,
Ina farin cikin yi muku jawabi a yau, ranar cikar kasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban kasarmu mai albarka, kuma zallar dan uwanku dan Najeriya.

2. A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, muna jinjina ga iyayenmu da s**a kafa Najeriya, mazansu da matansu. Ba don su ba, da ba a samu kasar Najeriya ba. Gwagwarmayarsu, sadaukarwarsu, da jagorancinsu ne s**a haifar da ‘yantacciyar kasar Najeriya mai mulkin kanta.

3. A wannan lokacin, muna karfafa wa juna gwiwar cewa a matsayinmu na ‘yan Najeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunkule da kuma a daidaikunmu. Babu wanda ya fi wani a cikinmu. Nasarorin da Najeriya ta cimma su ne abin alfaharinmu. Kalubalen da muka jure wa su ne ke karfafar mu. Kuma babu wata kasa ko wani iko a duniya da zai iya dankwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan kasar taku ce, ‘yan uwana. Ku so ta, ku karrama ta a matsayinta ta kasarku ta kanku.

4. Najeriya ta isa kasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarinta. Allah ya azurta mu da kabilu, addinai, da al’adu dabam-dabam. Sai dai dankon zumuncin dake tsakaninmu ya na da matukar karfi ko da yake ba ganin sa ake ba. Mun hadu kan buri guda daya na samar da zaman lafiya da cigaban al’umma, da fata guda na bunkasar arziki da hadin kai, da kuma manufofin hadaka na juriya da adalci.

5. Samar da kasa da aka dora bisa harsashin aiwatar da wadannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabanbata ya zamo aiki mai matukar albarka da yake fama da kalubale. Wadansu mutanen sun ce bai k**ata a samu ‘yantacciyar kasar Najeriya ba. Wasu sun ce kasarmu za ta rushe. Har abada su na bisa kuskure. A nan, kasarmu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.

6. A bana, mun tsallake wani siradi mai muhimmanci a tafarkinmu na tabbatar da cigaban Najeriya. Zaben da muka yi wa gwamnatin dimokradiyya ta bakwai a jere, na nuna cewa kasarmu ta yi riko da tsarin dimokradiyya da aiki da doka.

7. Ranar da na k**a mulki, na dauki alkawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar kasa ta mu. Daga cikin alkawurran har da yi wa tattalin arzikinmu garanmbawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.
8. Na ce daukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin dora kasarmu kan tafarkin walwala da bunkasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo karshen tallafin man fetur.

9. Ina sane da wahalhalun da s**a biyo baya. Idanuna suna gani kuma zuciyata ta na kunci. Ina son in bayyana muku dalilin da ya sa wajibi mu cigaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Wadanda ke son a cigaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kudaden waje, mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje a cikin fadama. Ni ba haka nake ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan muna son gidanmu ya yi kwari, ya dade dole ne mu gina shi kan tsandauri.

10. Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da ci gabanmu da daukakarmu ke bukata. A yanzu muna dauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin kasarmu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurinsu. Zamu samar da Najeriyar da za a mayar da yunwa, fatara, da wahala su zama tsohon labari.

11. Ba na farin cikin ganin al’ummar kasar nan na fama da wahalar da ya k**ata a ce an sauke ta a shekarun da s**a wuce. Zan so a ce babu wadannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari.

12. Gwamnatina na yin bakin kokarinta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana muku matakan da muke dauka domin rage wannan radadin da magidanta da iyalai ke fama da su.

13. Mun fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.

14. Bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.

15. Domin kawo ci gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunkasa bangarorin dake da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi s**a karbi kudi domin ba da tallafin sassauta radadin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da gobe.

16. Bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matukar muhimmanci. Dangane da haka ne muka bude wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar Gas a fadin kasar nan. Wadannan motoci za su caji kudi mai sauki da bai k**a kafar yadda ake biya yanzu ba.

17. Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa kasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bada horo a fadin kasa domin koyarwa da bada sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da kasarmu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samarwa tattalin arzikinmu mak**ashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.

18. Na dauki alkawarin tsaftace barnar da ta yi wa Babban Bankin Kasa dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na nada na gab da gabatar da rahotonsa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance afkuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokinmu na tasarrufi da kudi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kudi kadai.

19. Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da adalci. Na kaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a kasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaki ga ci gaban kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.

20. Domin bunkasa samar da aikin yi da kudin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da s**a nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun kara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.

21. Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan wadanda ake bai wa tallafin kudi kai tsaye domin rage masu radadi.

22. Gwamnatina a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunkasa hadin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An dora wa manyan hafsoshin sojin muhimmin aikin farfado da karsashin rundunonimu.

23. A nan, nake jinjina da yabo ga dakarun tsaronmu, da suke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron kasarmu. Da yawansu sun riga mu gidan gaskiya. Muna tuna su a yau tare da iyalansu. Za mu bai wa dakarunmu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kansu a madadin al’ummarmu.

24. Zamu ci gaba da nada mutane bisa muhimman muk**ai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a cigaba da kulawa da mata, matasa da masu bukatu na musamman a wadannan nade-naden.

25. Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Kasa murna kan rawar da s**a taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da bata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya dora musu na tantance wadanda za a nada da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

26. Haka kuma ina taya bangaren Shari’a murna a matsayinsu na ginshikin dimokradiyya da adalci.

27. Ina kuma taya murna ga kungiyoyinmu na ci gaban al’umma da kungiyoyin kwadago bisa sadaukarwarsu ga dimokradiyyar Najeriya. Ba ko da yaushe ra’ayinmu kan zama daya ba amma ina mutunta shawarwarinku. Ku ‘yan uwana ne kuma ina girmama ku.

28. ‘Yan uwana ‘yan Najeriya, tsoro ko kiyayya ba za su kawo mana ci gaba ba. Za mu iya samun ingatacciyar Najeriya ne kadai ta hanyar kwarin gwiwa, tausayi da kuma sadaukar da kai a matsayin dunkulalliyar kasa guda.

29. Na yi alkawari zan ci gaba da mayar da hankali tare da bauta muku cikin amana. Ina kuma gayyatar kowa ya bada gudunmawa wurin ci gaban kasarmu abar kaunarmu. Za mu iya. Ba makawa za mu yi. Kuma tabbas za mu yi nasara!!!
30. Baki dayanku ina taya ku murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

31. Nagode da sauraro.
32. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.

27/09/2023

I congratulate Muslims in Nigeria, and beyond on this year’s Eid-el-Maulud, marking the birth of Prophet Muhammad.

In Prophet Muhammad’s teachings and life, there are great lessons of devotion, perseverance, tolerance, humility and selflessness that we can all learn from.

I therefore urge all Muslims celebrating the Maulud festival to extend their hand of fellowship to the needy and vulnerable in the spirit of the season while praying for the country and her leaders at all levels.

Photos from President Bola Ahmed Tinubu's post 17/02/2023

Alh. Bola Ahmed Tinubu For President APC 2023
BAT/SHET

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Bauchi

Other Government Officials in Bauchi (show all)
Masarautar Bauchin Yakubu Masarautar Bauchin Yakubu
Bauchi Emir Palace
Bauchi

Sadiq, Saeed fans Sadiq, Saeed fans
Gumau
Bauchi

Sen. Bala Muh'd Kauran Bauchi 2023 Sen. Bala Muh'd Kauran Bauchi 2023
G. R. A Chamber
Bauchi

Gov. Senator bala muhammad kauran bauchi official page

Oyma ganda family Oyma ganda family
Inkil Off Gombe Road
Bauchi

To promote the image and interest of Oymagandans

Bauchi emirate Council Online Bauchi emirate Council Online
Emir Drive Bauchi
Bauchi

traditional tittle