Babban Malami DR BUK

Babban Malami DR BUK

Karatuttukan Malam da Nasihohin Shi Arubuce Insha Allah

24/05/2022

Fassarar Ayar Qur'an.

Surah An-nisa'i/سورة النساء
Chapter: 4 Verse 136.

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا آمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ وَالْكِتَابِ الَّذِي نَزَّلَ عَلَى رَسُولِهِ وَالْكِتَابِ الَّذِي أَنْزَلَ مِنْ قَبْلُ وَمَنْ يَكْفُرْ بِاللَّهِ وَمَلَائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا بَعِيدًا
MA'ANA:
Ya ku waɗanda s**a yi imani Ku yi Imani da Allah da Manzonsa, da Littafin da (Allah) Ya sassaukar ga ManzonSa (Muhammad SAW, shine Al-qur'ani) da (Kuma) Littafin nan wanda Ya saukar daga gabanin (sa, wato sune dukkan littafen allah Wanda ya saukar wa annabawa kafin zuwan Annabi Muhammad SAW, misali attaura,linjila,zabura.) To, wanda (Kuma) ya kafirta (ai, yaqi bada Gaskiya) da Allah da mala'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Ranar Lahira, to, lalle ne (wannan bawan) ya ɓace, ɓata mai nisa (ma'ana ai ya nisantar da kanshi daga Allah mahaliccin Shi, amma Kuma ya saurayi zuwan al-amarin Allah agareshi, a Domin kuwa yanada wata irin rayuwa mai kunci a anan duniya da baqin ciki na har abada a lahira)

SHARHINTA ATAQAICE...
shine Bawa ya sani cewa idan ya kuskura yabi wani a anan duniya dasunan wai bauta ko biyayya a gareshi, matuqarde ba Allah ne ba Ubangijin sammai da Qassai to, yayi hasara.

Haka Nan Kuma idan bawa ya bi wani mutum ko ya kwaikayi wani mutum, ba daya daga cikin Annabawan Allah ba Kuma ba Annabin Qarshen zamani ba(wato Annabi Muhammad SAW) to haƙiƙa yayi asarar ayyukan shi tin anan duniya.

Kuma kowa ya k**a ya k**a iska, a domin baze amfaneshi da komaiba aranar tashin Al-qiyama.

Ya Allah ka tsaremana imanin mu ka shiryar damu ka dawwamar damu akan hanyar ka madedeciya, ka Al-qur'ani ya zamo hujja agaremu ba akan muba.
AMINN.

+2348168311092
tambayoyi akan darasi.

18/05/2022

GA WANI HADISI.

Tunatarwa ne...

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

An rawaito daga Abi Muhammadu Abdullahi dan Amru, dan Asi (RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: imanin dayanku ba ya cika har sai abin da ya ke so ya zama mai bi ga abin da na zo da shi (Al-qur'ani).

Allah ka Bamu ikon sanin Al-qur'ani da Kuma aiki dashi.
Amin.

15/05/2022

WANNAN BAITI NE A GARE KA YA RASULULLAHI S.A.W.

Muhammadur Rasulullahi S.A.W, Dan Gatan Allah ne.
Kuma masoyin Allah ne.
Babu k**ar shi a duk yare.
Kyawun fuska da ta zuciya ai, Kai karshen Shi ne, Qamshi jikin ki ka yakeyi ko Babu turare, fuskar haske takeyi ko Babu koyaye.

Uwata Ubana fansa ne a gare ka ya Rasulullahi.
Wallahi Annabi Muhammad Kai ne Kuma kai ne, wallahi Annabi muhammadu Kaine Kuma kai kadai ne, wallahi Annabi Muhammad Kai ne Wanda zakayi ceto a ranar da Babu wani me ikon ceto a ranar da Babu wani Mai dama, Kai ne kadai ubangin ka ya baka dama, Nide roko na ga Allah a wannar Rana in dace da ceton ka ya Mahmudu masoyina, wallahi da badan Kai ba da bansan Allah ba, da badankai ba da bansan addini ba, wallahi nikam Kai ne gata na, wallahi soyayyar zata kasheni sauqinka ya tunasardani, aikin ka Yana nitsar dani, wallahi nide a barni dakai, nide na zabeka akan rayuwata hadama dukiyata hada 'ya'ya na da matana harda iyayenama.

Nide buri na shine insadu dakai aran Qiya musha ruwan alkausara, wanda Ubangiji ya zurtaka da ita, manzannin ma zasu nemi temakon duk ma.

Al-qur'ani ma Kai kazo dashi wallahi da ba dan kai ba da bansan harafin Shi ko guda ba, godiya ga Allah da wannar Ni'imar dayi akan Al-ummar ka S.A.W.
Da kyautar dayi mana da Aiko ka.

Kafurai Arna Mushrikai basu san ko waye kai ba, basun girman darajar ka ba, sun Qulla makirci kan makirci a Domin su kashe, se Ubangijin ka ya kare ka, wallahi Annabi Muhammad da badan kai ba haƙiƙa da ankifar damu, da Yanzu wata magar ake ta dabam, amma se gashi Addu'ar ka Tai mana Rana, se gashi Kai kayi mana Rana, kuma arnan ma albarkacinka suke ci.
to me Karatu a Yanzu fa zanyi wata tambaya, dakai nake Kai maqiyin Allah maqiyin Manzon Allah me kasamu A wanga rayuwa, banda kunci da baqin ciki na zunubinka, ga baqar zuciya data fuska wai, ga warin jiki seka ce mushen jaki, ga doyin baki k**ar warin shadda, ahakan ne zaka zo wai ka zagi Manzon mu Kuma Annabin mu, Kuma wai ace mukyale ka, ai wallahi Bamu kyaliya, ai wallahi bamu kyaliya, ai wallahi Bamu kyaliya a Domin Annabin mu, a domin Annabin mu, a domin Annabin mu.

S.A.W SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW SAW

15/05/2022

TA'ADDANCI NE BABBA a ce wai a ringa samun Wassu Ko wani a bayan Qasa Wanda suke Zagin Annabawan Allah da Manzannin Allah ma'abota daraja. Wanda
Su fa wadannan bayi ne na Allah Kuma Suma mutane ne amma ba k**ar kowaba, su ba komai bane face Bayin Allah Na gari masu nagarta a gareshi Kuma Masu girman daraja Kuma 'yan aiken Allah, Kuma sune wakilan Allah a bayan Qasa, toh su anan dan Allah me nene laifinsu. Gyara fa sukeyi ba Barna ba mu duba tundaga kan annabi ADAMU,NUHU,IBRAHIM,MUSA,ISAH,DAWUD,MUHAMMAD S.A.W. Dukkan su amincin Allah ya tabbata agaresu su din fa Annabawa ne Kuma duk Wanda ya bi su, bi na Gaskiya, bi na tsakani da Allah a Dukkan zamunan su ko a bayan su, to shi din fa ba a bun zargi bane a wajen Allah Duniyar shi da Lahiran Shi.

Mu sani Sufa 'yan aikene kawai basuda wuta ko aljanna ahannun su, ashe yanzu Bai k**ata ace munyi musu kara ba inde munada tunani.

Kuma wallahi Allah da kanshi ya fada cewa lalle ze tambayi Bayi akan cewa shin manzannin Nan sunzo muku da sako na, se Bayi s**e Eh. haka Kuma Allah ze tambayi su manzannin cewa shin Kun isar da sako na zuwa ga Bayi se Suma s**e Eh. Toh shikenan daga Nan Kuma se hukunci duk abinda bawa ya gani marar kyau a rannan To kada ya zarge kowa sede kanshi.

Shi yasa Dukkan wani littafi da manzannin s**a zuwa mutanen su dashi Gaskiya ne Kuma daga ne Allah, a saboda haka nema suke zuwa da hujjoji bayyanannu da mu'ujizozi na wuce duk wani tunani da hankalin Dan Adam ko aljanu, a domin meya, a domin al-umma su fahimci Qarfin abinda s**a zo dashi, a saboda su gane cewa daga Allah ne s**a zo dashi ba wai wani halitta ba.

Idan aka samu wassu daga cikin Kafirai ko mushrikai suna zagi da cin mutunci Annabi ko manzo toh hukunci Kisa ne akan su, Kuma anan hukuma ce kadai takeda haqqin yin hukunci, ba wai wassu tsiraru ba daga cikin talakawa ko mabiya, Domin aikata hakan Kuskure babba Wanda ka iya haifarda tashin hankali, shi Kuma addini Inde addinin Allah ne to babu koyarwar tashin hankali ko cin zarafi ko zagi ko zalunci a ciki, haka Babu kashe juna ba tareda haqqi ba, babu hayaniya ko tada hankalin sauran Al-ummar Duniya.

Sede wajibi ne akan musulmi da ya kauracwa wannan me zagi ko zarafin Annabin Allah, ya yanke duk wata mu'amala dashi.

Mu sani duk Wanda yayi daya daga cikin wadannan abubuwa na tada hankali ko zakuntar wani, to tabbas ba addini yake yi ba, ya sane cewa duk abinda yaje ya dawo to bashi da wani lada a wajen Allah sede zunubi me girma daze dauka akan shi, a saboda haka Dan Allah mu kula mu ringa aikata abu da ilimi, idan ko bamu da sani akan abu to muyi tambaya kafin mu aikata, Domin jahillci ba uzuri bane Awajen Allah.

Mu sani fa Ita wannar rayuwar jarrabawa ce, haka Allah yaso ya gammu daban daban launin fata daban da banbancin addini da banbancin kabila da banbancin harshe, duka wannan ajiyar Allah ne, Kuma mu sani Dukkan mu daga Annabi Adam (A.s) muke mu 'ya'yan shine, a bin sani de kawai shine Mafi daraja a cikin mu a wajen ubangijin mu Allah Shine Mai tsoron Allah a cikin mu.

Wallahi Allah da kanshi ya Haramta yin zalunci a karan kanshi, sa'annan Kuma ya Haramta ta a tsakanin bayin shi, koda ko akan Wanda ba musulmi bane haramun ne ka zalince Shi, a Saboda haka mu kula sosai.

A kullum adalci shike wanzar da zaman lafiya, zalunci kuwa shike kawo fitina da Rudani da asara.
Don Allah kowa yayi wa kanshi adalci Arayuwar Nan, yayi abunda ya dace. Insha Allahu Allah zeyi mana mafita Kuma haqiqa se ansamu sauyi da ci gaba.
WALLAHU A'ALAM.

Allah yasa mudace AMIN.

14/05/2022

Alal Haqiqa Duk Wanda yazo da wannan irin Littafi Mai Girma wanda babu irin shi a duniya wato , to wallahi yafi Qarfin Zagi.
Dukkan Wanda ko ya zageshi to fa haqiqa Rayuwar sai ta tabe.
Annabi Muhammad SAW Manzon Rahama ne Kuma Shi Rahama ne Ga Al-ummar Duniya, Kuma shi fitilla ne Ga Al-ummar Duniya, haka Nan Kuma Shi madubi ne ga Rayuwar Al-umma.

Shine Al-aminu hatta Kafurai Arna Mushrikai maqiya Allah maqiya Manzon Allah sun tabbatar da Gaskiyar Shi da amanar Shi.

A Saboda haka ta'addanci ne babba abayan Qasa a ringa zagin Annabawan Allah, a domin mu musulmai bama banbanta daya daga cikin su, Dukkan annabawa da manzannin Allah mun yarda dasu, a Saboda haka mu musulmai mude kawai munji ne Kuma munyi biyayya a Saboda Allah shi kadai a Saboda kwadayin rahamar shi da tsoron azabar shi.

Abinda ya shafi Kisa kuwa ko kuma Hukunta wani me lefi, Gaskiya wannan haqqin Shugabanni ne, a Saboda haka Kuma duk abinda ya faru akwai lefin iyaye da Shugabanni da malami da fastoci, harda ma sauran talakawa mabiya, a Saboda kuwa mu mutane bil-adam munada yawan shagala ga yawan son zuciya ga yawan jahillci da zalunci arayuwar mu.

Abu mafi muhimmanci shine Addu'a da aiki tukuru, da kuma yawaita neman gafarar Allah da yafiyar shi, to a hakane fa zamu iya dacewa a rayuwar mu ta Duniya da Lahira.

Ya Allah ka tausaya Mana, ya Allah Bamu da wayo ko dubara sai a gare ya Allah, ya Allah kaine kadai ke da iko mu bamu da iko, ka temakemu da aikata Dede, ka karemu daga fizga irin na shedan. AMIN

Allahumma Salli wa sallim ala Muhammad wa alihi wa sahbihi wasallam.

29/04/2022

ZAKKAR FIDDA-KAI DA KUMA LADDUBA NA RANAR IDI.

Tunatarwa ne...

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

Allah (SWT) ya tsaramana wata ibada A Karshen Azumi, wato ya tsara mana mu ciyar da junanmu abinci (Shine yin Zakkar Fidda-kai).

Zakkar fidda-kai.
Ma’anarta: Ita ce Zakkar da ake kira Zakkar buda-baki ko zakkar jukkuna. Ita ce kuma har yau ake kira Zakkar kono.
Hukuncinta: ita Zakkar fidda-kai ko zakkar kono, wajibi ce a kan kowane Musulmi, namiji da mace, yaro da babba, d'a ne shi kode bawa. A domin kuwa malamai sunce fassarar ayar nan ta cikin Suratul a'ala wato" قَدْ أَفْلَحَ مَنْ تَزَكَّى"
A nan a nufin Zakkar fidda-kai ce.
Wallahu a'alam.

Toh, Me ake bayarwa idan za'a fidda Zakkar?: Ana bayar da sa'i guda, watau muddun Nabi hudu, a kowane mutum, daga abincin da mutanen gari s**a fi amfani da shi. Kuma Mai gida ne yake fitar wa da iyalinsa wadanda yake ciyarwa, bayan ya fitar wa kansa.

Toh, Yaushe ake fitar da ita?: Ana fitar da ita a Ranar safiyar sallah, kafin a tafi sallar Idi. Idan kuwa aka bari har sai bayan sallar Idi, to ba Zakkar fidda-kai ba sunanta. Ta koma daidai da kowace sadaka. Duk da cewa yana da kyau a bayar da ita tun kwana daya ko biyu kafin Idi. Domin Sahabban Annabi (SAW) haka suke yi.

Toh, Su wa ake bai wa ita Zakkar?: Ana bayar da ita ne ga faKirai da miskinai, Amma fa wannan ba ya na nufin idan kai faKiri ne ko miskini shi ke nan ba za ka fitar ba, a’a, lallai ne ka bayar ga wanda ya fi ka talauci. Domin ba ta sauka daga kan mutum sai idan ya zama a safiyar Idi ba shi da abin da zai fitar bayan ya ciyar da iyalinsa.

Toh, Ina za a kai ita Wannar Zakkar?: Idan akwai wurin da hukuma ta ware, to yana da kyau a kai can. Amma lallai a kai a Kalla, kwana biyu kafin ranar Sallar. Idan kuwa ba haka ba, to sai mutum ya raba ta wa faKiran da suke kusa dashi. Babu laifi a ba wa limami ko malamin unguwa idan faKiri ne shi.

Ko za a iya bayar da Zakkar da Kima na kudi ko kayan kudi ?:
A'a Lallai ne a bayar da abinci. Sai idan babu abincin ko kuna abincin ba zai yi amfani ba awannan Lokacin ga Wanda za'a baiwa ita.

Babbar Hikimar fidda Zakkar, ita ce ciyar da miskinai da Kuma kar abar wani musulmi da kunci da tunanin ci da sha aranar farin ciki Ranar Sallah. Hikima ta biyu kuma ita ce, cike kura-kuran da mai azumi ya yi da ladanta.

Kuma mu akula 'yan uwa cewa ita fa sadaka tana tunkude fushin Allah, sa'annan Kuma tana janyowa bawa yardan Allah.
Hakanan ita sadaka tana tunkude kofofin sharri ga bawa, Kuma tana sanyawa baya rigar Qima da Girmamawa tun agidan Duniya.

Haƙiƙa Allah baya son rowa kuma baya son mai rowa, saboda haka rashin yin sadaka yakan jawowawa bawa taulauci da kunci, yin sadaka Kuwa ya kan janyowa bawa arziki, Saboda haka karmuyi rowa ga junanmu.
Dafatan Allah ya bamu ikon aikat Dede.

LADDUBAN RANAR SALLAH, WATO LADDUBAN IDI.
Anaso aranar Sallah wato Ranar daya ga watan shawwal, mutum da yayi wanka ya sanya tufafi mai kyau me stafta, son samu sabon kaya, ayi ado harda fesa turare.

Sa'annan kuma anaso mutum yaci abinci kafin ya tafi filin sallar idi.

Sa'annan Kuma ana son mutum ya tafi da Qafa ne (sede idan akwai laluri na nisa ko tsaro) Kuma yana tafiya Yana mai yin kabbarori ALLAHU AKBAR,ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA'ILAHA I'LLALLAHU ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR,WALILLAHIL HAMDU. Kuma ana so mutum ya tayin wannan kabbarorin har izuwa sanda za'a tada Sallar idi.

Ana so mutum ya canza hanyar Shi awajen dawowa gida, ma'ana ya bi wata hanyar wacce ba ita ya biyoba azuwa.

Kuma a Wannar ranar ana so mutum ya ringa yada sallama a tsakanin yan uwa musulmai wato ya ringa cewa TAQABBALALLAHU MINNA WAMINKUM.

Ana so mutum ya saki fuskar shi, ya ringa farin ciki dashi da iyalan shi dama sauran 'yan uwa na jini da kuma na addini, ana so a yafewa juna, kuma ayi raha ga juna, a Kuma yalwata abinci me kyau ga iyalai da 'yan uwa dama sauran Al-ummar Annabi SAW.

Ba'a son ayi almubazzaranci awannar Rana da abinci ko dukiya, haka Kuma ba'a son yin ayyuka na alfasha, k**ar zagi jin kide-kide, aikata zunubi, gulma, yin Qarya, kauda hankali ta hanya buguwa, da Kuma shiga hakkin wani wai duk a soboda murnar ranar Sallah.

Ana so da a yawaita yiwa Allah godiya da girmama Allah mahalicci, da kuma sauran ayyukan alheri kmar sada zuminci a wannar Rana ta Sallah.
To idan mutum yaganshi cikin masu aikata haka tabbas alamace ta cewa ibadar shi Allah ya karba.

Muna ronkon Ubangiji Allah da ya karbi ibadunmu duka, tundaga farkon wannar wata har izuwa Qarshen ta, Allah ya yafemana kurakuranmu na cikin watar dama wajen watar, Allah ya hada fuskokin mu da manzon Allah Annabi Muhammad SAW acikin gidan aljannah.
Amin

WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

+2348168311092.
Tambayoyi akan darasi

27/04/2022

Mabudin Jin Dadin Rayuwar Duniya Yana A cikin Abu Uku ne (3).
AL-MIFTAHUS SA'ADA ATH-THALATHA.

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

Alalhaqiqa, Kamar yadda babbam malami ibinul Qayyimul jauziyya yake fadi cewa" lalle lalle ita Wannar rayuwar Tana da wani mabudai guda uku, wanda wadannan sune mabudi na dukkan jin wani dadin Rayuwar duniya.

Duk wani abu daze biyo baya to zai kasance jin dadi ne dan kadan kuma na Dan wani Lokaci, Amma ba wai asalin jin dadi ba Mai karawa bawa nitsuwa Duniyar shi da lahiran Shi.

Abu na farko shine:

1- YIN GODIYA GA ALLAH.
Lalle ana son bawa ya ringa yiwa Allah godiya akan dukkan ni'imomin shi.
Kamar yadda Allah yake fadi acikin Al-qur'ani cewa" wallahi idan kuka godemini (akan ni'imomin da namuku) zan kara muku (wata Ni'imar) idan Kuma kuka kafirce mini (kuka qi godemini) toh ku sani fa lalle azabata Mai tsanani ce (ai, tabbas zaku hadu da azabata a gaba gareku)"

Anan malamai s**a ce ita Dogiya ta kasu izuwa kaso uku (3) ne:
A-akwai GODIYA ta zuciya (misalin yin Imani da miqa wuya ga Allah).

B-akwai godiya ta kan harshe (misalin zikiri,tasbihi,hamdala,hailala,salati,Karatun Qur'an,umarni da abu me kyau da Hani da aikita abu mara kyau, dade Sauran su).

C-akwai godiya ta aiki da gabbai (misalin Sallah, Azumi,hajji, dade saura ibada da akeyi da jiki a Domin Allah).

Abu na biyu shine:

2- HAKURI.
lalle ana son bawa ya lizimci yin hakuri. k**ar yadda Allah yake fadi a cikin Al-qur'ani cewa" lalle ne haƙiƙa Ubangiji Allah yana tare da masu hakuri"

Toh, anan ma malamai sun kasa hakuri shima izuwa kaso uku (3).

A-Hakuri akan bala'in rayuwa, da hakuri akan jarrabawan rayuwa.

B-Hakuri akan yiwa Allah da'a, (wato duk wahala da bawa ka iya gani ko ji akan ibadar Allah to yayi hakuri akai).

C-Hakuri akan aikata sabo (wato bawa yayi hakuri ya kauda kai akan dukkan wani aikin sabawa Allah aikinda Allah bai yarda dashi ba, komin dadi da ribar wanann aiki).

3- YIN ISTIGFARI, WATO TUBA ZUWA GA ALLAH, DA KUMA NEMAN AFUWAN WATO YAFIYAR ALLAH.

wato anan shi istigfari shine, misali Allah ya hana bawa aikata wani abu se kuma bawan ya aikata, to idan ya tuba tuba na gari se Allah ya gafartamishi zunubin abinda ya aikata.
Ita kuma afuwa da yafiyar Allah shine, misali Allah ya sa bawa ya aitaka wani aiki to se ya aikata shi ba yadda akeso ba, wato ya kuskure toh idan ya nemi afuwar Allah to se Allah ya yafemishi.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

Muna Rokon Ubangiji Allah da ya gafartamana lefuffukan mu, ya Kuma yafemana kura kuran mu wanda muka sani dama wanda bamu sani ba, ya Kuma karemu daga fizga da huduba irin na shedan la'ananne.
Amin.

+2348168311092
Tambayoyi akan darasi.

22/04/2022

LADDUBAN YIN ADDU'A.

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

Alhamdullih muna kara yiwa Allah godiya bisa ni'imomin da yayi agaremu maras adadi.
Haƙiƙa shi yin Addu'a yanada wassu ladduba Wanda idan mutum yabi wadannan ladduba to da yardan Allah addu'ar da yayi Karbabbeya ce, matuqar de babu nufi na mugunta ko cutarwa ga wani mutum na dabam a cikin addu'ar tashi.

Da farko Ana so mutum idn zeyi Addu'a to ya fara da yiwa Allah yabo da kirari, wato dukkanin wata kalma da kasan ma'anar ta Shine yabon Allah ko kirari ne ga Allah to ita zaka fara ambato aciki Addu'ar ka.

Ladabi Na biyu Shine mutum ya yiwa Annabi Muhammad SAW Salati.

Na uku shine kayiwa iyayenka Addu'a da sauran muminai Duniya.

Na hudu ana so ka daga hannayenka sama kana mai Qasqantar da kanka ga Allah mahaliccin bayi.

Na biyar ana so mutum ya dage da kuma sa naci da jajircewa a wajen yin Addu'a, wato a kullum ko yauce Kayi Addu'a.

Na shida sharadine Abincinka da kaci da wanda zaka ci agaba ya zamo halak ne, hakan abin shanka ya zamo halak ne, haka tufafinka ma ya zamo halak ne, haka guzurinka ya zamo shima halak ne, babu Haram a ciki ko kadan.

Sharadi Na Bakwai shine, ya zamo mutum ya sakankance jiki cewa Addu'ar shi Allah yaji kuma ya amsa mishi ita.

Mu sani cewa idan kayiwa dan uwanka Addu'a a bayan idon shi, to kai kuma Allah zesa mala'iku su maka Addu'a.

Kuma Ana son mutum ya fara da ronkon buqatun kanshi da kanshi ne kafun wani.

Ana so mutum ya roki Alkairan Duniya da na lahira, kada mutum rokonshi ya tsaya a iya Duniya ne kawai, a Domin kuwa iya abunda ze samu kenan Awajen Allah, shikenan Kuma bashida wani Rabo alahira.

Yana daga like yin Addu'a mutum ya ringa kiran Ubangiji, yace Rabbi, ya Rabbi, ya Allah kai ne kai wanda zaka share mini kuka, ya Rabbi na rokeka da ka sharemini kuka na, ya Ubangiji Allah na rokeka daka amsa mini Addu'a ta.

Haka Nan Matuqar mutum de Shi musulmi ne kuma yayi Addu'a, to haƙiƙa wannar addu'a bata faduwa a banza, a domin kuwa kode Allah ya jinkirta amsa mishi, kode Allah ya tunkude mishi wata bala'in ta dalilin Addu'ar, kode Allah ya ajiye mishi ladanta aranar alqiyama ta amfaneshi.

Daga Qarshen Addu'ar kuma ana son ka rufe ta da kamun kafa da sunayen Allah ma'abota Dara.

Wajajen amsa Addu'a, akwai Lokacin da mutum yayi sujjada, ana amsa Addu'a agun.

Lokacinda akeyin ruwan sama, ana amsa Addu'a agun.

Lokacinda mutum yake halin tafiya, ana amsa Addu'a agun.

Akwai wani Lokaci aranar juma'a, da ake amsa Addu'a.

Ranar arfa, ana amsa Addu'a aranar.

Sa'annan Kuma A kula ba'a yiwa Allah dole wajen amsa Addu'a, wai kace Allah dole ka amshi Addu'a ta, a'a ba'a haka, ko Kuma kace Allah ka amsa mini alokaci kaza ko Allah ni yanzu Yanzu nake so ka amsa mini, duka ba'a son haka, kaide kawai Kayi hakuri ka jira hukuncin Allah kuma kaji aranka Addu'ar ta karbu, to se Allah ya tausaya maka.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

Dafatan Allah ya tausaya Mana, Allah ya amshi Addu'o'inmu na Alkairi duka, Allah ya gafartawa iyayen mu, malumanmu, Allah ya temakemu mudace dayin ibada a cikin wannan dare mai albarka Lailatul Qadri.
Allah mun tuba izuwa gareka, Allah ka amshi tubanmu, ya Allah ka Mana afuwa, ya Hayyu ya Qayyum Bi rahamtika Astagisu.

+2348168311092
Tambayoyi akan darasi

21/04/2022

DAREN Lailatul Qadri Mai Albarka.

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

Allah da kanshi yana cewa"
إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ
MA'ANA:
Lalle ne Mu, Mun saukar da shi (Alƙur'ani) a cikin Lailatul ƙadari (wato daren daraja)

وَمَا أَدْرَاكَ مَا لَيْلَةُ الْقَدْرِ
MA'ANA
To (kai mai karatu) me ya sanar da kai abin da ake cewa Lailatul Qadari?

لَيْلَةُ الْقَدْرِ خَيْرٌ مِنْ أَلْفِ شَهْرٍ
MA'ANA:
Lailatul Qadari (wani darene wadda ya zamo Shi kadan Shi) mafi alheri ne daga wasu watanni dubu.

تَنَزَّلُ الْمَلَائِكَةُ وَالرُّوحُ فِيهَا بِإِذْنِ رَبِّهِمْ مِنْ كُلِّ أَمْرٍ
MA'ANA:
(Kuma) Mala'iku da Ruhi(wato Mala'ika jibril) suna sauka a cikinsa da iznin Ubangijinsu sabada kowane umurni.

سَلَامٌ هِيَ حَتَّى مَطْلَعِ الْفَجْرِ
MA'ANA:
Sallama ne shi daren(ai, aminci ne shi daren daga farkon Shi) har (Izuwa) fitar alfijiri.

To wanna kenan, yadda Allah SWT ya bamu labarin Irin girman Daren da alherin dake acikin shi.

Kuma Ya zo a cikin Hadisin Annabi Muhammad SAW cewa" Ana samun Daren Lailatul Kadari a kwanaki na goman karshe na watan Azumi a daren ashirin da daya (21) ko ashirin da uku (23) ko ashirin da biyar (25) ko ashirin da bakwai (27) ko ashirin da tara (29) da dare na karshen watan Ramadan.
Nana Aisha (R.A) ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku nemi Daren Lailatul Kadari a goman karshe.

Kuma Ana so a yawaita addu’a Da neman gafarar Allah a Daren Lailatul Kadari. Nana Aisha (R.A) ta ce, na tambayi Manzon Allah (S.A.W)a ce, ya Rasulullahi, idan na ga Daren Lailatul Kadari me zan fada a cikinsa? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ki ce:
"اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى.
Wato mutum yace:
Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa'afu anni.
Ma’ana:
Ya Ubangiji, hakika, Kai mai afuwa ne, kuma kana kaunar yin afuwa, ya Allah ka yi min afuwa.
Kuma ana so a karanta wadannan ayoyi masu yawan lada.
1- آيَةُ الْكُرْسِيُّ 2- آمَنَ الرَّسُولُ 3- إِذَا ذُلْزِلَتِ اْلأَرْضُ 4- قُلْ يَأَيُّهَا الْكَافِرُونَ 5- قُلْ هُوَ الله أَحَدٌ 6- سُورَةُ يَاسِين.
Wato a karanata
1. Ayatal Kursiyyu 2. Amanar-Rasulu 3. Izazul zilatul ardu 4. Kulya ayyuhal kafiruna 5. Kul huwallahu ahad 6. Suratu Yasin.

Amma wannan ga Wanda yasamu iko ne, kuma ana son a yawaita yin istigfari, tasbihi, tahmidi, salati ga Annabi, sannan Babu lefi mutum ya roki alhairan duniya da Kuma na lahira.

Idan da Hali ma ana son mutum ya shiga i'tikafi, wato yayi niyyar lizimtar yin ibada kawai na wassu kwanani.

Shi i'itikafi Shima ibadane mai zaman kanta a wasu kwanakin watan Ramadan wato goman Qarshe.

Kuma shi li’itikafi yana da sharadan inganci guda bakwai:

1-Musulunci: Li’itikafi ba ya inganta ga kafiri.

2-Balaga: Ba ya inganta ga yaron da bai balaga ba, ko mahaukaci.

3-Tsarki: Ba ya ingantaga mai janaba ko haila ko nifasi.

4-Masallaci: Li’itikafi ba ya inganta a cikin gida ko daki ko Masallacin da ba a sallar jam’i a cikinsa.

5-Azumi: Li’itikafi ba ya inganta ba tare da Azumi ba.

6-Barin runguma ko sunbatar mace da daddare ko da rana.
وَلاَ تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنْتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ.
Ma'ana:
Kar ku rungume su (matayen ku), lokacin da kuke li’itikafi a cikin Masallaci.
Acikin Suratul Bakara: aya ta 178.

7-Neman iznin miji: Li’itikafin mace ba ya inganta idan mijinta bai yi mata izini ba.

Sa'annan Li’itikafi yana baci don aikata babban laifi k**ar:
Zina da shan giya da karya da kazafi. Haka nan yana baci don yin jima’i da sumba da daddare ko da rana bisa sha’awa. Haka nan yana baci da zuwan haila, haka nan yana baci da cin abinci ko shan ruwa da rana, haka yana baci in an fita daga Masallaci ba don neman abinci ko wata bukatar dan’adam ba.
Wallahu a'alam.

SHARHI ATAQAICE.
To alalhaqiqa gafa dama ta samu Wanda wallahi sau daya take zuwa ashekara a Saboda haka ya k**a fa ace mundawo cikin hayyacin mu na Dukkanin wani kyal-kyal da rudani na Duniya.

Mu tsaya da addu'a na neman kariyar Allah daga shedan la'ananne kada ya ci riba akan mu yahanamu samun wannar dama, domin kuwa wallahi bamuda tabbacin rayuwar zata kai wata shekaran, shine yasa shedan la'ananne zeta rudar mu a Domin yaga mun rasa wannar damar.
Don Allah mu yaqi shedan mu wajabtawa kanmu lalle ne se munyi wannar ibadar da Addu'o'in ko ta halin qaqa.

Allah yasa mudace, kuma muna fatan Allah ya karemu daga fizga na shedan.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

+2348168311092.
Tambayoyi akan darasi.

19/04/2022

HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR (25).

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

An rawaito daga Abi Zarrin (RA) cewa: wadansu mutane daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) sun ce da Annabi ya Rasulullahi, ma'abota dukiya sun tafi da lada mai yawa, suna yin sallah k**ar yadda muke yi, kuma suna yin azumi k**ar yadda muke yi, kuma suna sadaka da mafificyar dukiyar su, sai Annabi (SAW) ya ce: HaKiKa ai ku ma Allah ya ajiye muku abin da za ku yi sadaka da shi, haKiKa kowani yin tasbihi(Subhanallahi) sadaka ne, kuma kowa ce kabbara (Allahu Akbar) sadaka ce, kuma kowa ce hailala (la'ilaha I'llallahu) sadaka ce, kuma horo da aikin alheri (ma'ana umarni da aikin alheri) sadaka ne, haka kuma hani daga aikata haramci ma sadaka ne, kuma gaban dayanku (wato) yin jima'in dayanku (ga iyalinsa) shi ma sadaka ne. (Sai sahabbai) s**a ce: Ya Manzon Allah, yanzu dayanmu ya zo wa sha'awarsa kuma ya sami lada! Sai Annabi ya ce: Shin ba kwa ganin da zai je ya sanya ta (ita gabar) cikin haram, zai sami zunubi? To (ku sani) haka ma in ya sanya ta a halal yana da lada.

SHARHI ATAQAICE.
shi wannan Hadisi ne da yake karantardamu tarun falala na yin tasbihi zikiri salati, dama sauran ayyukan alheri.
Matuqar de bawa zaiyi riko da Irin wadannan halayya to haqiqa koda bashida dukiya a Domin yin ayyukan alheri to de shima ba'abarshi abaya ba ta wajen samun ladan me yin sadaka da Kuma ladan yin biyayya ga Allah madaukakin sarki.

Haƙiƙa yin murmushi ga Dan uwanka Shima sadaka ne, haka magana Mai dadi itama sadaka ne, mutum ya kauda abin zecurtawa akan hanya Shima sadaka ne.

Wato dukkanin wadannan abubuwa ne masu saukin gaske,kusan de za'a ce babu Wanda baze iya aikatasu ba ako wani Hali ya kasance, riko da Irin wannan halayya musamman acikin Irin wannan wata na Ramadan wanda Allah yake rubanya lada,to alalhaqiqa Gaskiya dacene wanda duk ya Sami kanshi aciki to wallahi ya godewa Allah, a Domin wasu shedan baya bari su ringa furtawa duk da irin sauki da kalkomin suke dashi wajen furtawa. .

Wato gaskiya musulmi ya godewa Allah a domin kuwa Ubangiji Allah ya Riga da yayi komai akanshi, Shi yasa Annabi Muhammad SAW yake cewa" kowa zai shiga aljanna sede Wanda yaqi" sahabbai s**a ce ya Rasulullah wazeqi shiga aljanna Kuma? Annabi SAW yace duk Wanda ya bini ze shiga aljanna Wanda duk yaqi bina kuwa Tamkar yaqi shiga aljanna ne.
Allah kasa mubi annabinka sauda Qafa, ka Bamu dacewa da sunnar shi, ka shiryarda hanya madedeciya, Kaji kanmu, ka gafartamana, ka yafemana kurakuranmu Duniya da lahira.
Amin ya Hayyu ya Qayyum.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

+2348168311092
Tambayoyi akan darasi

18/04/2022

FASSARAR AL-QUR'ANI ME GIRMA.

Surah An-nur/سورة النور
Chapter: 24 Verse 24-26.

بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.

Ubangiji Subhanahu wata'ala Yana cewa"
يَوْمَ تَشْهَدُ عَلَيْهِمْ أَلْسِنَتُهُمْ وَأَيْدِيهِمْ وَأَرْجُلُهُمْ بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ
MA'ANA:
A ranar da harsunansu da hannayensu, da ƙafafunsu suke bayar da shaida a kansu, game da abin da s**a kasance suna aikatawa.(su mushrikai, ko Kuma su kafirai, kode su masu aikata sabo)

Allahu SWT yace"
يَوْمَئِذٍ يُوَفِّيهِمُ اللَّهُ دِينَهُمُ الْحَقَّ وَيَعْلَمُونَ أَنَّ اللَّهَ هُوَ الْحَقُّ الْمُبِينُ
MA'ANA:
A (Wannar) ranar (ne ta Al-qiyama wad) da Allah Yake cika musu sak**akonsu (ai, yake musu hisabin ayyukan su) tabbatacce (da s**a aikata marasa kyau, ya kuma sakankamusu da maras kyau wato shine ya sasu a Wuta) kuma (hakika) suna sanin (cewa) lalle Allah, Shine Gaskiya bayyananna (ai, tabbas suna sanin cewa lalle ne wannan hukuncinda Allah yayi akan su shine dede a Domin sun cancanci ayi musu hakan a Saboda kafircewar su ga Allah da ayoyin shi da manzannin shi da Sukayi a gidan Duniya).

Shine Sai gaba Allah yake cewa"
الْخَبِيثَاتُ لِلْخَبِيثِينَ وَالْخَبِيثُونَ لِلْخَبِيثَاتِ وَالطَّيِّبَاتُ لِلطَّيِّبِينَ وَالطَّيِّبُونَ لِلطَّيِّبَاتِ أُولَئِكَ مُبَرَّءُونَ مِمَّا يَقُولُونَ لَهُمْ مَغْفِرَةٌ وَرِزْقٌ كَرِيمٌ
MA'ANA:
(Sanide kawai su) Miyagun mata domin miyagun maza suke, kuma (su) miyagun maza domin miyagun mata suke (hakanan) kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke. waɗancan su ne waɗanda ake barrantawa daga abin da (masu ƙazafin nan) suke faɗa (akan matar Annabi SAW Wato syydn Aisha) kuma suna da gafara da arziki na karimci (ma'ana ai su wa 'yanda akayi ƙazafin akan sunada gafara agun Allah kuma da arziqi wato Shi aljanna, ko Kuma su wassu dag sahaban nan wanda s**a rinjaya akan kazafin nan, amma Kuma se daga baya s**a kafimci Gaskiyar magana cewa lalle sayyidina Aisha (Ra) bata aikata wannan abinda ake Fadi ba akanta ba a sak**akon Allah ya saukar da aya ya wanke ta, to su wadannan Suna da gafara ma'ana ai Allah ya gafarta musu sa'annan Kuma sunada wani arziqi ai gidan aljannah)
Wallahu a'alam.

SHARHI ATAQAICE.
wato su wadannan ayoyin Suna fadakarwa gare mu mu Al-ummar Annabi Muhammad SAW, musamman ita wannar aya ta Qarshen inda Allah yake buga mana misali cewa" mu sani Kuma lalle mu hankalta fa mu fahimci su matan kirki fa suna dacene da mazan kirki, Kuma bai yi yuwa ace matar Annabi Muhammad SAW ace anzargeta da aikata fasikanci.

Wato a qarkashin wannar maganar abaya akwai wani abunda ya faru ne awani lokaci sanda Annabi Muhammad SAW ya na tafiya da rundunar shi a domin zuwa daga kalmar Allah, to acikin wannan rundina akwai mata harda matarshi Nana Aisha (RA) se s**a yada zango awani waje a domin hutawa, to shikenan bayan sun huta se akata tashi domin anausa gaba, to ita Nana Aisha adede wannan Lokacin se wani uzuri ya k**ata akace ko zobenta ne ta yasar kode wani abun na lalura, ma'ana de kawai akwai wani uzuri da yasa har akabar Nana Aisha abaya, to dama kuma Idan aka fito da tawaga irin wannar tawaga akan bar wani mutum kuma abaya Wanda aikin shi shine ze ringa kula da abinda ka iya faduwa na jama'ar wannar rundina, to shikenan se shi wannan irin Mutumin da ake Bari abayan sai s**a hadu da ita sayyidina Aisha (Ra) a Sak**ako anbarta abaya.

To shine fa Bayanda s**a taho dashi wannan wanda ake Bari abayan a tare, To dagan shikenan shine fa se kawai munafukai s**a ringa yada jita jita akan cewa ai fasikanci Sukayi dashi wannan Mutumin da ake Bari abayan, daganan har maganar ta isa ga Annabi SAW wadda har shubuha ta sameshi a cikin lamarin, har seda aya ta sauko akayiwa Annabi Muhammad SAW wahayi aka wanke Aisha daga dukkan wani zargi ko shubuha.
Ataqaice taqaitawa de wannan shine abinda ya faru.
Har Allah yace an barranta nana Aisha daga maganar masu ƙazafin nan.

Wato Abin lura anan gabar shine ma'anar Da ita ayar take koyarwa ga Al-ummar Annabi Muhammad SAW, farko de Idan aka samu jarrabawa ta munafikai ko makaryata s**ayi magana akan wani bawa wanda shi bawan mai nagarta ne ansanshi, to tunanin farkode da Ya k**ata ayi akanshi shine k**ar yadda Allah ya buga mana misali acikin ayar, wato mazan kirki Allah yana basu matan kirkine, haka nan mutanen kirki Allah yana hadasu da na kirkine, haka nan idan ko na banza ne Allah yana hadasu dana banzane.

Ma'ana de kawai anasun mu musulmi muminai kasance masu kyautata zato ga junanmu da kyaky-kyawan fata tsakani.
Harsede Idan wani abi ya bayyane a garemu na zargi, to anan Kuma anaso muyi wa junanmu addu'a ta shiriya ba aikatawa ba.

Sai Kuma bayani akan Aya ta farko Wanda ayace da take yi mana Gargadi da Kuma tsorataswa akan cewa lalle Mu sani da akwai wata Rana da hannuwanmu da kafafunmu da harsunan mu zasu bada sheda akanmu a gaban Allah, matuqar de bamu sarrafasu ba ta Yadda Allah yace.

Kuma hakika musani cewa Lalle alkawarin Allah gaskiya ne hakanan azaban Allah Gaskiya ne Kuma tabbas gaske ne babu ko kwanto a ciki.

Saide kawai mafita guda shine imani da tsayuwa akan imanin, da neman temakon Allah acikin lamuran mu , kana mu ringa yawan tuba da neman gafarar Allah tin kafin lokaci ya kure, wato tin kafin wata Rana tazo Mana wadda zamu koma ga mahaliccin mu shine Allah.
WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

Ya Allah Kai ne mai afuwa Kuma kana son Afuwa, ya Allah ka mana afuwa. Ba dan halayyarmu ba, Allah ka tausayamana albarkacin Ramadan.
Amin.

+2348168311092
Tambayoyi akan darasi.

Want your business to be the top-listed Food & Beverage Service in Gombe?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Gombe
Other Food & Grocery in Gombe (show all)
Saidu Bello adamu Saidu Bello adamu
Jekadafari Jankai Gombe
Gombe, SAIDUBELLOADAMU

Twins multi purpose homeshope Twins multi purpose homeshope
Bypass Gombe
Gombe

Nigerian Navy Nigerian Navy
Gombe
Gombe

I love how I do my things

Bash Shoe's Bash Shoe's
State Lowcost
Gombe

Ken provision shop opposite Gsu Ken provision shop opposite Gsu
Opposite Gombe State University
Gombe

Gombe rice Gombe rice
Federal Low-cost
Gombe

Dan bakoo Dan bakoo
Gombe State Dukku Lga
Gombe

Ashaka Muslim Ummah Ashaka Muslim Ummah
Gombe
Gombe, 762102

Education

Ameer celebrity Ameer celebrity
Bolari Gombe
Gombe

Gaskiya Dokin Qarfe MAI Lantarkin Kawai Gaskiya Dokin Qarfe MAI Lantarkin Kawai
Herwagana NNPC MEGA
Gombe

Musa kj Musa kj
Bolari
Gombe