Kabiru Gombe Tafsir 2023
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kabiru Gombe Tafsir 2023, Grocers, 21 Etsu Close Kaduna, Gombe.
MU KULA DA DUKIYAR MARAYU!!
✉️✉️✉️✉️✉️✉️✉️✉️✉️✉️✉️✉️
Tare da: Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah)
Zaku Iya Samun Cikakken Wannan Video ta wannan Link dake Ƙasa:👇
https://youtu.be/diwYmjtvrlM
Karku manta ku danna mana a Subscribe domin samun short videos na Malam da zaran an ɗaura.
22/04/1445 A.H
Wasu Idan S**a Mutu Sun HUTA, Wasu Kuma Idan S**a Mutu ANHUTA Dasu
Allah Kasa Munacikin Wadanda Idan S**a Mutu Sun HUTA
🤲
Labarin Haɗuwar Annabi da Aljanu Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum
Yau ne Insha Allahu
Mafi albarkan lokaci shine goman farko na watan zulhijja saboda matsayi da suke dashi mai girma a wajen Allah madaukakin sarki,wanda hakan ke nuna soyuwar su a wajen sa, da basu fifiko da yaye.wadannan ranaku masu matukar albarka ne, masu yawan lada ne, masu karancin lefuka ne, masu matsayi ne me girma, masu nauoi daban-daban ne ne lada, Allah yayi rantsuwa dasu, kuma baya rantsuwa saida abu mai girma, sannan ya sanya su mafifitan ranakun duniya gaba-daya.
huduba ta
Manufofin hudubar
Bayanin cewa Allah yana halittar abin da ya so kuma yana zava
Tunatar da mutane da lokuta na alheri, da cin moriyarsu cikin aiyuka na kwarai
Bayanin falalar wayannan kwanaki goma
Bayanin yalwar rahamar Allah, da falalarsa a kan bayinsa
Huduba Ta Farko
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma mua neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan aiyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar dashi, wanda kuma ya atar babu mai shiryar da shi, kuma ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi kaxai ne bashi da abokin taraiya, kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawansane manzonsane, (Yaku waxanda kuka bada gaskiya kuji tsoron Allah yadda ya cancanta aji tsoronsa, kada ku mutu face kuna Musulmi). (Yaku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicce ku daga rai guda xaya kuma ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga gare su (su biyu) kuji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya dashi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Ya ku waxanda s**a yi imani kuji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku aiyukanku, kuma ya gafarta muku zunubanku. Wanda ya bi Allah da manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawun shiriya shiriyar Annabi Muhammadu (ﷺ) kuma mafi sharrin al’amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wata bidi’a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta.
Bayan haka: Ya ku
WAYAR ZAMANI ALKAIRI DA SHARRI DUK SUNA CIKI YARAGE NAMU KUMA👌
Matsalar dayawa mutane s**a samu kansu aciki yanzu shine wayar hannu (phone)
Akwai mutane dayawa waďanda da kamammune amma yanzu har blue film suna kallo a wayarsu wannan jarrabawace ko ba jarrabawa bace?
Jarrabawa ce👌
Abinda zakayi nasiha akansa kace babu kyau,Idan kaga wata da wani suna hira kace ai hirar no gab kai kuma kaje ka buďe wayarka kana kallon blue film a waya,kaima ai no gab
Har akwai ustazan da wannan jarrabawar s**a gagara tsallake ta
mutum ne mutumin kirki mai addini amma zai kulle kansa a daki ya kalli batsa yadda yakeso
Yanzu Dan ALLAH da wanda zai buďe wayarsa ya kalli blue film da wanda zaije bayan gari menene banbancinsu?
Duk ýan iska ne👌
To Yanzu ga wayar nan idan kashiga ďakinka kai daya agun ne za'a tabbatar da ustazancinka na gaske ne ko bana gaske bane
Gaka ga wayarka babu kowa sai ubangijinka shine kadai mai kallonka idan zakaci jarrabawar a wannan lokacin zaka ci
idan bakaciba a wannan lokacin zakasan bazaka ciki ba
ALLAH kabamu ikon cinye wannan Jarrabawa ta wayar zamani
MALAM AHMAD TIJJANI YUSUF GURUNTUM🎤
ILoLin zina da kuma Hukuncinta
Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi
(ﷺ) a kan wane zunubi ne ya fi girma, sai
Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Shirka da Allah
alhali Shi ne Ya halicce ka.” Sai aka ce ‘sai
wane?’ Sai ya ce, “Sannan kashe ɗanka don
kada ya ci tare da kai.” Sai aka ce “sannan
sai wane?” Sai ya ce, “Ka yi zina da matar
makwabcinka.” (Bukhari). yadda ruwaito
Allah Maɗaukakin sarki Ya sanya hukuncin
wanda duk ya yi zina kuma ya taɓa aure, a
jefe shi, namiji ko mace; idan kuwa bai taɓa
aure ba, sai a yi masa bulala ɗari, sannan a
baquntar da shi a wani gari daban tsawon
shekara guda.
Duk wanda ya kalli hukuncin zina, zai ga
Allah Ya keɓance shi da wasu abubuwa masu
yawa, saboda munin zina. Ga kadan daga
cikin abubuwan da hukuncin ya kunsa:
1. Kausasawa wajen ukubar mazinaci, ta
hanyar jefewa. Ko kuma bulala da
bakuntarwa shekara guda.
2. Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya
yayin da ake musu ukuba. Allah Ya ce :
ٱلزَّانِيَةُ وَٱلزَّانِى فَٱجْلِدُوا۟ كُلَّ وَٰحِدٍ مِّنْهُمَا مِا۟ئَةَ جَلْدَةٍ ۖ وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِى دِينِ ٱللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِٱللَّهِ وَٱلْيَوْمِ ٱلْءَاخِرِ ۖ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَآئِفَةٌ مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِين
“Mazinãciya da mazinãci, to, ku yi bũlãla ga kõwane ɗaya daga gare su, bũlãla ɗari. Kuma kada tausayi ya kãma ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kunã yin ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Kuma wani yankin jama, a daga mũminai, su halarci azãbarsu.” . (Annur : 2). .
Yi musu ukuba a gaban mutane, ba a
yarda a yi musu a boye ba, Allah Ya ce :
Duk waɗannan abubuwa suna nuna mana
munin zina da rashin kyanta a Musulunci.
Imamul Bukhari ya kawo, a cikin ingantaccen
littafinsa, daga Maimun Al-audiy ya ce,
“A lokacin jahiliyya na taɓa ganin wani biri da
ya yi zina da wata biranya, sai sauran biran s**a taru s**a jefe su”.
Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar makwabcinsa. Allah Ya kare mu.
ILLoLin Zina: ,,,
Assalamu Alaikum muna
Muku barka da sallah
Amma malam yazo ya karbi
Barka da sallah
Gobe Dai Sallah
See 🙊
006 Ramadan Tafseer 2023 Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum Malam Ahmad Tijjani Yusuf Gurumtum Tafseer 2023
FINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS).
Idan ka Karanta ka Turawa Sauran Ƴan Uwa Domin Su Amfana.
BLue FiLms Fina-finai ne da Wasu Tsageru Daga Cikin Yahudawa Suke Shiryarwa Wanda Yana da ILLa Sosai.
Domin Yanzu Anyi IttiQakin Cewa Ba Abin da Yake Saurin Rufta Mutum Zuwa Zinace-zinace Kamar Shi KaLLon BLue FiLms Ɗin Wanda Zamani Yazo da shi, Ba Ga Namiji ba, Ba Kuma Ga Mace ba.
Babban Abin Takaici Yanzu Yan Mata Sunfi Kowa Qwarewa Wajen Iya KaLLon Wnnn LaLaci na BLue FiLms.
HUKUNCIN SA:
KaLLon Tsaraici Haramun Neh a Shari'ar MusuLunci in Banda Na Matarka Ko Na Mijin ki, BaLLantana Kuma KaLLon Saduwa Tsakanin Mazinata, Wnnn Abune Mai MatuQar Muni Sosai.
Allah Yana Cewa:
"Ka Gayawa Muminai Maza su Rintse Idanuwansu Daga KaLLon Haram Kuma Su Kiyaye Daga Yin Zina".
'Yan Uwa Mu Kiyaye, Duk Wanda Yake KaLLon Irin Waɗannan Abubuwan to LaLLai Yayiwa ALLAH Tawaye.
A Wani Gurin ALLAH Yana Cewa:
"Kada Ku Kusanci Zina hakika ita Zina ALfasha Ce Kuma Mummunar Hanya ce".
Kunga Saboda HaLakan da Take Cikin Zina, Sai ALLAH Yace Kada Mu Kusanceta, shi Kuwa Irin Wnnn KaLLon Yakan Sanya Masu Yinsa su Afka Cikin Zina Kai Tsaye.
Manzon Allah (S.A.W) Yana Cewa:
" ALLAH ka Tsinewa Mai kallon Tsaraici da Kuma Wanda Ake KaLLon Tsaraicin nasa".
Daga Qarshe Ina Qara Jawo HankaLin Masu Yi su Tuba su Daina.....!!!
Don ALLAH Daure ka Rubuta Ameen Bamusan tawa Za'a Karɓa Ba...
Sannan KaLLon Fina-finan Batsa Yana Kai Mutum Zuwa ga Aikata Mummunar Ɗabi'ar Nan ta Istim'na'i Wacce Itama Tana da iLLoLi Ga Lafiya.
Ya ALLAH Ka Tsarkake Mana Zukatan Mu, Ka Kare Zuri'ar Mu Daga Afkawa Cikin Mummunar BaLa'in Dake Tattare Da KaLLon BLue FiLms.🙏🙏🙏
ALLAH Ya Qara Shiryar da Mu da ƴan Uwan mu Masu Aikatawa 🤲.🤲🏿🤲🏿🤲🤲
Assalamu Alaikum warahmatullah.
Insha Allahu Gobe Alhamis Malam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum zai cigaba da Tafsirin Azumin watan Ramadan kamar yadda Aka saba, Wanda Zai gudana kamar Haka:
👉🏽. Wuri: Masallacin S.19 Dutsen Tanshi Bauchi.
👉🏽. Lokaci: 4:30 - 5:30 na Yamma
Allah Ya bada ikon Halarta da amfanuwa da abinda zamu saurara.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Gombe