JABBI TV

JABBI TV

Shi Adalci
Sunansa Adalci, bashi da alaqa da waza kaiwa adalci Allah karamana haquri

20/12/2022

Waken dan ance 🥰

13/12/2022

Shi Adalci
Sunansa Adalci, bashi da alaqa da waza kaiwa adalci Allah karamana haquri

Photos from JABBI TV's post 20/12/2020

ALLAHU AKBAR

Malamin mu Sheikh Dr Bashir Ahmad Sani Sokoto Malamin Allah tarnakin yahudawan duniya, har yanzu dai yana kwance a asibiti yana fama da matsanancin rashin lafiya

Allahu Akbar ga Malam daga kan kujerar wa'azi inda yake baje kolin makircin yahudawa da 'yan Masoniyyah yau ya dawo ana tureshi akan keken marassa lafiya

Yaa Allah Ka tashi kafadun Malam
Yaa Allah Ka yaye masa cutar dake damunsa
Yaa Allah Ka dawo dashi kan kujerar wa'azi lafiya Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

30/11/2020

A R E W A

A Sannu a hankali dai sha’anin tsaro kai tsaye Alama ce ta ruguza duk wani Tattalin arziki na Arewa.

Mutanen da suke safara an bi hanyar su an tare, ba iya kudin hannunsu ake karba ba, su din ake daukewa sukutum a nemi su kawo abin da s**a tara a gida.

A bangaren noma kuwa a yankunan da abin ya ke faruwa tuni da yawa sun daina noma.
Ko da kayi noman ma ba ka isa ka kwashe ba Sai ka biya kudin masu daji. Kuma a hakan ma baka da tabbas na rayuwarka ko na abincin da ka noma. Abin dai Sai kace a tsofaffin fina-finan india na Daku.

Daga lokacin aka ce noma ya gagara a kauyuka, sannan safara da kasuwanci sun gagara a tsakanin birane. To fa tattalin Arziki zai tsaya ne cak. Kudade zasu daina motsi, Masana’antu zasu daina samin ababan sarfawa.

Daga nan Sai karuwar talauci da yawaitar laifuka. Babu birni babu kauye. Rana zafi inuwa kuna.

Zuwa yanzu duk wani mutum da yake daukar wannan masifar ta tsaya ne a kan Mutanen kauye ko na wajen gari to ya shirya.

In dai idon zamu cigaba da zubawa k**ar mujiya. To mu shirya
“abin da yaci doma bazai bar Awe ba.”

Allah ya kawo mana karshen wannan masifar.

30/11/2020

JABBI TV
DIREBA YA GANE WANDA YATAƁA GARKUWA DA SHI A CIKIN FASINJOJIN DA S**A SHIGA MOTARSA A JAHAR SOKOTO
-Direban ya gane wanda ya taba garkuwa da shi daga cikin fasinjojin sa a tashar Kwannawa da ke jihar Sokoto - Direban wanda aka yi garkuwa da shi watanni biyu da s**a gabata a Kankara da ke jihar Katsina ya yi saurin gane mutumin kuma ya sanarwa da shugabbanin tashar - Yan sanda sun k**a wanda ake zargin kuma tuni aka maida al'amarin zuwa hedikwatar yan sanda ta Sokoto don fadada bincike Wata dambarwa ta faru a tashar mota ta Kwannawa da ke Karamar Hukumar Dange-Shuni a jihar Sokoto bayan da wani direba ya shaida wanda ya yi garkuwa da shi a cikin fasinjojinsa.
Direban wanda ba'a bayyana sunan shi ba, an yi garkuwa da shi a Kankara da ke jihar Katsina watanni biyu da s**a gabata.Direba ya gane wanda ya taba garkuwa da shi cikin fasinjojinsa. direban ya shafe kimanin sati uku a tsare bayan biyan kudin fansar da ba'a bayyana adadin su ba.
Daga dan uwanku.
Bashiru Bello Jabbi

Photos from JABBI TV's post 23/11/2020

INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJ'UN 😭😭

Ministan sadawar Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya rasa 'yar sa, 'yar sa mai suna Aisha Isa Ali Pantami ta rasu yau Litinin bayan sallar Magriba nan.

Za'a yi mata sallah gobe Talata da misalin 'karfe 1:15 na rana, a masallacin Annur dake birnin Abuja.

Allah ya gafarta mata, yai mata rahama.

Daga Ustaz jamilu bello jabbi

Photos from JABBI TV's post 18/11/2020

Allah yakarawa wa malam Dr Isa Ali Pantami lafiya da Nisan kwana, ya albarkaci rayuwar shi, ya kareshi da dukkan sharrin mai masharri .

18/11/2020

INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI'UNN

Allah Ya karbi rayuwar Mahaifin marigayi Sheikh Albaniy Zaria wato Malam Adam wanda ake yiwa lakabi da Baba Danjuma Dattijon albarka wanda ya haifowa duniyar Musulunci gwarzon Malami shahidi Insha Allah Sheikh Albaniy Zaria

Malam Adam Ya rasu dab da asuba bayan yayi fama da rashin lafiya, zuwa an jima kadan da misalin karfe 9 na safe za'a yi masa jana'iza a gidansa dake 'Yan Awaki Muchiya Sabon Garin Zaria

Muna rokon Allah Ya gafarta masa
Allah Ya kyautata makwancinsa
Allah Ya hadashi da 'dansa Malam Albaniy Zaria a gidan Aljannah tare damu gaba daya
daga Jamilu Bello jabbi

15/11/2020
12/11/2020

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'ON
Allah yayi ma alh sani fodio shugaban kungiyar Y.S.O rasuwa yau dina za'a gudanar da sallar shi k**ar yadda musulunci ya tanada da misalin karfe5:30pm a masalacin umar kanoma dake bypess Allah ya jikanshi da rahama
Naku a ko yaushe.
Bashiru Bello Jabbi

10/11/2020

Mutuwa tana kan kowa

10/11/2020
09/11/2020

A YAU NE AKE BUKIN MIKA SANDAR GIRMA GA SABON SARKIN ZAZZAU.

A yau ranar litinin 9 ga watan nuwamba ne ake bikin bayar da sandar girma ga alh.Ahmad nuhu bamalli sabon sarkin zazzau.
Gwamna nasir el-rufa'i ne ya mika wa sabon sarki sandar girma.
A watan jiya ne gwamnatin kaduna ta nada ambasada Ahmad nuhu bamalli a matsayin sarkin zazzau na 19 bayan rasuwar sarki alh. Shehu idris wanda ya kwashe fiye da shekaru 40 a gadon sarautar zazzau.
Dubban mutane ne s**a halar ci wajen bikin. Ciki har da sarkin musulumi mai alfarma Alh. Muhammad abubakar na III da shehun borno Alh. Abubakar ibn umar garbai.
Da fatan Allah ya bashi ikon gudanar da sarautar kan adalci.
Naku a ko yaushe.
Bashiru Bello Jabbi

07/11/2020

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN
Allah yayi ma Dr Aliyu malami yan doto rasuwa yau a jahar sokoto za'a gudanar da sallar jina'izarshi k**ar yadda musulunci ya tana da a garin tsafe a gobe karfe 10:00am Allah ya jikanshi da rahama.
Daga Bashiru Bello Jabbi

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Gusau?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

@jabbitv
Waken dan ance 🥰
Mutuwa tana kan kowa

Category

Website

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00