Ri ga Kafi Yafi Magani
Rɪ Gᴀ KᴀFɪ YᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ
Shan Taba Sigari Nada illa ga Lafiya.
Tsakanin Mace da Namiji wa Yafi Jin Daɗi Lokacin Jima'i, Kuma wa Yafi son Jima'i ?.
A kimiyyance, masana sun bayyana cewa Namiji ya fi Mace abin da ake kira (s*x drive) wato jin son yin jima'i. Hasalima abin da bincike ya nuna shi ne Namiji yana ninka Mace yawan tunanin jima'i a kowace rana a yanayi iri ɗaya.
To amma idan an yi jima'i wa ya fi jin daɗi tsakanin Mace da Namiji ?.
Binciken kimiyya ya nuna cewa Mace ta fi namiji jin daɗi idan har ta gamsu (or**sm). Amma kuma idan shima Namiji ya gamsu kuma ita ma Mace ta gamsu to Macen ta fi Namiji jin daɗi.
To amma matsalar ita ce, a kaso 100, sama da kaso 90 na Mata basa samun gamsuwa a yayin jima'in, amma Maza a kaso 100 sama da kaso 95 suna samun gamsuwa saboda gamsuwarsu ta fi sauƙin samu fiye da Mata.
Kenan hakan yana nuna Maza sun fi jin daɗi a mafi yawan lokaci fiye da Mata saboda suna iya gamawa a daidai lokacin da su Matan suke shirin farawa. Kuma da sun gama ba sa iya ci gaba sai bayan an ɗauki lokacin da ita Macen wataƙila ma ya fita daga ranta.
Kusan Mata da yawa suna nuna k**ar sun gamsu a zahiri amma a zuciyarsu sam ba su gamsu ba (faking or**sm). Suna yin hakan ne saboda sun san a halayyar Namiji yana so ya ga ya gamsar da Mace saboda hakan yana sa ya ji daɗi a ransa. To suna yin hakan ne don kawai ya ji daɗi ba don wai a ƙarƙashin ransu sun ji daɗin ba.
Ri ga Kafi Yafi Magani
Sunday 25th August,2023.
Mene banbancin Maniyyi, Waziyyi da kuma Wadiyyi ?.
Assalamualaikum.
A Yau a wannan Rana zamuyi ɗan taƙaitaccen bayani akan banbancin dake akwai tsakanin Mayiyyi, Maziyyi da kuma Wadiyyi. Da farko dai ya k**ata mu sani babu kunya a cikin neman ilimi, domin Nana Aisha (R.T.A) tana cewa "Allah ya jiƙan matan Madina saboda ko kaɗan kunya bata hana su neman ilimi game da addini".
1A.Maniyyin Namiji :- Maniyyin Namiji Ruwa ne mai kauri fari wanda yake fito wa ya yin babbar sha'awa ko wasa da al'aura, sannan yana tunkuɗo juna lokacin da yake fitowa kuma warin sa yana k**a da warin hudar Dabino ko damamman Gari sannan idan ya bushe yana ƙamshin kwai.
1B.Maniyyin Mace:- Maniyyin Mace shi kuma ruwa ne tsinkakke mai fatsi-fatsi fari wanda yake fitowa ya yin babbar sha'awa k**ar saduwa ko wasa da al'aura, sannan yana tunkuɗo juna lokacin dayake fitowa kuma zataji tsananin sha'awa da daɗi lokacin da yake fitowa kuma warinsa yana k**a da warin hudar Dabino ko damamman Gari, sannan yana ƙamshin kwai idan yabushe kuma sha'awa tana Yankewa bayan fitowarsa.
Hukuncin fitar da Maniyyi shi ne Yana Wajabta Wanka.
2.Maziyyi shi kuma ruwa ne tsinkakke da ya ke fotowa yayin ƙaramar sha'awa k**ar tunanin Aure da sauransu ko mace ko Namiji duk Maziyyi yana fito musu ya yin irin wannan tunani, amma mafi yawan lokacin ba'a sanin fitowarsa kuma yafi fitowa Mata diye da Maza.
Hukuncin fitowar Mazoyyi shi ne wanke Al'aura baki ɗaya.
3.Wadiyyi :- Shi kuma wani farin Ruwa ne dayake fitowa bayan an gama fitsari, kokuma lokacin da aka ɗauki kaya masu nauyi sannan yafi fitowa Marasa Aure Mace ko Namiji.
Hukuncin fitowar Wadiyyi ahi ne a wanke Wajem.
Wallahu Ta'ala A'alam.
Idan Akwai tambaya za'a iya Tambayar Malamai.
SʜᴀFᴜᴋᴀɴᴍᴜ Nᴀ Sᴀᴅᴀ Zᴜᴍᴜɴᴛᴀ.
ᴇ-ᴍᴀɪʟ :- RɪGᴀᴋᴀFɪʏᴀFɪᴍᴀGᴀɴɪ@Gᴍᴀɪʟ.ᴄᴏᴍ.
WʜᴀᴛsAᴘᴘ :-
+2348146236510.
FᴀᴄᴇBᴏᴏᴋ :-
www.facebook.com/rigakafiyafimagani.com
Yᴏᴜᴛᴜʙᴇ :- www.rigakafiyafimagani.youtube.com.
"Rɪ Gᴀ ᴋᴀFɪ ʏᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ"
Kaɗan daga cikin Alamomin Mace Ƴar Maɗigo (Le***an).
1.Macen da take rungumar ƴar uwarta Mace ko sumbatarta da nufin wasa.
2.Macen da take bayyanawa Ƴar uwarta Mace tsiraicinta.
3.Macen da ke yaba kyawun Ƴar uwarta Mace ta fuskar sha'awa.
4.Macen da take nunawa ƙawarta bidiyon ƴan Madigo.
5.Macen da za ta k**a hannun mace Ƴar uwarta ta dinga shafawa babu wani dalili.
6.Macen da za ta dinga shafa gashin kan ƙawarta.
7.Mace mai lazimtar kwanciya akan cinyar Mace ƴar uwarta ba tare da dalili ba.
8.Macen da a kodayaushe take son ganin surar jikin Mace ƴar uwarta.
9.Ƴar maɗigo tana da yawan son yin kyauta ta bajinta da ban mamaki ga wadda ta gani tana so.
10.Yana daga cikin alamomin ƴan maɗigo keɓancewa a ƙuryar ɗaki su kaɗai.
11.Ƴar maɗigo ba ta da wata hira sai ta mace ƴar uwarta.
12.Suna ƙyamatar yin mu'amala da Namiji, ba su damu da yin saurayi ba.
13.Suna da sha'awar kallon fina-finan batsa, musamman na ƴan maɗigo.
14.Suna matuƙar zama a gidan da mata ne zalla, k**ar zawarawa da ƴan mata.
15.Macen da ke tuɓe rigarta a gaban mata ƴan uwanta ba tare da jin kunya ba.
16.Mace mai yawan son shafa Nono ko taɓa mazaunan ƙawarta maimakon musabaha.
17.Suna yawan kiran junansu da "Sweety" ko ''Darling'' ko ''Dear'' ko kuma ''My Love''.
18.Suna da son yin ɗinki matsattse mai bayyana dukkan surar jikinsu.
19.Sun iya yin fari da idanu don janyo hankalin macen da suke so.
20.Sunfi koɗa kyawun mace fiye da Namiji.
21.Suna da baƙin kishi
22.Suna da son yin tsabta ta kece raini.
23.Suna amfani da turare masu tsadar gaske.
24.Suna son saka sarƙa a ƙafarsu da zobe a yatsan ƙafa (Duk da an mayar da shi ado yanzu)
25.Suna son saka zobe a babban ɗan yatsansu na hannu.
26.Yawancinsu suna son ƙara tsawon gashin idonsu ko shafa masa kala.
27.Suna auren junansu k**ar yadda Namiji ke auren ƴa mace.
28.Shakuwa mai tsanani tsakanin mace da mace, barci kawai ke raba su.
Allah Ya sa mu Dace Amin.
Har kullum dai muna cewa "RɪGᴀ KᴀFɪ YᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ"
Dᴀʀᴀsɪɴᴍᴜ ɴᴀ Yᴀᴜ Dᴏᴍɪɴ ɪʏᴀʏᴇɴᴍᴜ ᴍᴀᴛᴀ.
Da yawa daga cikin uwayenmu Mata musamman Hausawa sun ɗauki sha da ta'ammuli da wasu magungunan gargajiya wajen gyara kansu ko kuma don ƙara wa ƴaƴansu ƴan Mata ni'ima wajen gamsar da mazajensu.
Ko kaɗan ba zai zama laifi idan an yi ba, sai dai matsaloli da illa da yake haifarwa bayan an yi amfani da shi ya fi muhimmancinsa yawa musamman ga mace budurwa da ba ta taɓa aure ba.
Wasu Mazan suna ƙyara da tsangwama ga irin Matan da suke seda waɗannan magunguna, domin wasu matan sun ma ɗauki wannan hanyar a matsayin sana'a. Sukan kai tallar irin waɗannan magunguna gidajen mata musamman inda ake biki don tallata hajarsu.
Da zarar an ce mace an sa ranar aurenta, to iyaye da kuma ƴan matan kansu za su fara zuwa neman taimakon irin waɗancan magungunan dana faɗa a farko.
Akan ɗauki tsawon lokaci ana haɗa mace, ana yamutsata kuma ana rikita sha'awarta ta hanyar bata maganin sha da Madara ko Kazar magani da dai sauransu, maimakon a barta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata na sha'awa, amma sai ayi amfani da irin waɗancan magungunan wanda zasu janyo ma ta rikicewar sha'awa.
Dan Allah uwayenmu Mata, ku dena ɗurawa ƴa ƴanku waɗannan magungunan, wallahi ko kaɗan basu da wani amfani, ku bar yaranku da sha'awarsu k**ar yadda Allah ya haliccesu, babu laifi idan kuka basu maganin Sanyi dana Basir, amma gaskiya ku ƙauracewa basu waɗancan magungunan domin gujewa janyo musu illa ga rayuwar zaman aurensu.
Allah ya ƙara Mana Lafiya Amin.
Kada a manta kullum dai muna cewa "Rɪ Gᴀ ᴋᴀFɪ ʏᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ"
•••
SʜᴀFᴜᴋᴀɴᴍᴜ Nᴀ Sᴀᴅᴀ Zᴜᴍᴜɴᴛᴀ.
ᴇ-ᴍᴀɪʟ :- RɪGᴀᴋᴀFɪʏᴀFɪᴍᴀGᴀɴɪ@Gᴍᴀɪʟ.ᴄᴏᴍ.
WʜᴀᴛsAᴘᴘ :-
+2348146236510.
FᴀᴄᴇBᴏᴏᴋ :-
www.facebook.com/rigakafiyafimagani.com
Yᴏᴜᴛᴜʙᴇ :- www.rigakafiyafimagani.youtube.com.
"Rɪ Gᴀ ᴋᴀFɪ ʏᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ"
Dᴀʀᴀsɪɴᴍᴜ ɴᴀ Yᴀᴜ Dᴏᴍɪɴ ɪʏᴀʏᴇɴᴍᴜ ᴍᴀᴛᴀ.
A shekara muna da kwanaki 365.
1.Mace mai lafiya a fiɗrance tana al'ada a duk wata, idan kwana 7 ta ke yi sai mu ce 7×12 = 84, kenan a shekara tana al'ada na kwana 84.
2.Idan mace ta haihu tana buƙatar kwanakin biƙi kwana 40, ta shirya kanta ta kuma yi tsarki daga jinin biƙin.
3.Duk tsananin Miji a ƙalla matarshi za ta yi tafiya zuwa gurin ƴan uwanta, ko ɗaurin aure ko suna ko gaisuwar rashin lafiya na kwanaki 15 aƙalla a shekara.
4.A ƙalla mace a shekara ta samu kwanaki 30 da za ta kwana ba ta yi bacci ba ko dai jariri ya yi ta kuka ba gaira ba dalili, ko kuma jaririn ba lafiya. In kuma yaran na da yawa kwanakin za su fi haka.
5.A ƙalla Mace a shekara a kwanaki 30 za ta iya tsintan kanta a halin fushi, rashin lafiya ko kuma ta ji kawai ba ta cikin nishaɗi.
6.A ƙalla Mace a shekara ta tsinci kanta a kwanaki 10 tana asibiti, an kwantar da ɗaya daga cikin yaranta a asibiti musamman idan yaran suna da yawa.
Adadin kwanakin sun zama 84 + 40 + 15 + 30 + 30 + 10 = 209
Kenan adadin kwanakin da mijinta zai iya moranta kai tsaye su ne 365 - 209 = 156
Kenan lokacin da mace take free shi ne (156 ÷ 365) × 100 = 42.7. Kunga percentage ɗin ko 50 bai kai ba.
Wannan lissafin na matar da bata aiki kenan, ita tana gida ne ko yaushe, to b***e kuma ma'aikaciyar gwamnati ko shaharrriyar ƴar kasuwa, ko uwa uba ɗalibar Jami'a.
Kunga kenan duk Namiji mai Mata ɗaya yana k**a da gwauro a cikin kwanaki 209 a shekara.
Allah ya sakawa Matanmu da alheri.
Allah ya ƙara musu Lafiya.
Allah ya bamu abinda zamu basu na Halak. Amin.
Kada a manta kullum dai muna cewa "Rɪ Gᴀ KᴀFɪ YᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ"
SʜᴀFɪɴ "Rɪ Gᴀ KᴀFɪ YᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ"
Sʜᴀ Fɪ ɴᴇ ᴅᴀ Zᴀɪ ᴅᴜᴋᴜFᴀ ᴅᴀʀᴇ ᴅᴀ ʀᴀɴᴀ ᴡᴀJᴇɴ ɪʟᴍᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ ᴅᴀ Fᴀᴅᴀᴋᴀʀ ᴅᴀ Aʟ-ᴜᴍᴍᴀ Kᴀɴ ʟᴀFɪYᴀʀᴍᴜ ᴀ Sᴀᴜᴋᴀᴋᴇ ᴄɪᴋɪɴ Hᴀʀsʜᴇɴ Hᴀᴜsᴀ.
Dᴀʀᴀsɪɴᴍᴜ ɴᴀ Yᴀᴜ Kᴀɴsᴀʀ ᴍᴀᴍᴀ
Kansar Mama ba ƙwayoyin cuta ke haddasa ta ba kuma ba cuta ce mai yaɗuwa ba, kansar Mama na faruwa ne sak**akon rikiɗewar ƙwayoyin halittar Mama. Duk da cewa kansar Mama ba ta yaɗuwa daga wani zuwa wani, amma tana iya bazuwa zuwa sassan jiki.
Alamomin Kansar Mama.
1.Fitowar ƙari a kowane sashi na Jikin Mama.
2.Sauyawar girma, sifa ko k**annin Mama.
3.Bayyanar lotsawa ko kwarmi a Jikin Mama.
4.Sauyawar launin fatar Mama.
5.Sauyawar sifar kan Mama ko kuma launin fatar kewayensa.
6.Fitar baƙon ruwa daga kan Mama.
Wacce Hanya zaki bi domin ganin kin tseratar da Kanki daga Kansar Mama.
•Na farko Akwai abinda ake kira da (Breasts Examination) wato gwajin Mama wanda Mace zata tsaya a gaban Babban Mudubi, ta kalli Mamanta da kyau duka biyun, idan suna da banbanci ko na girma ko na launi ko kuma na shape ko Kan Maman daya yafi daya girma, ko dai duk wata alama da zaki gani da idonki wacce Mamarki daya ta banbanta da Daya ta bangaren girma launi ko shape to kada ki ɓoye.
•Na biyu ki hanzarta sanar da Mahaifiyarki ko wani makusancinki matsalar da kika gani Lokacin da k**e Breasts Examination.
•Na Uku kada a bata lokaci a tafi Asibiti akwai kwararrun likitoci a Wannan fannin, in sha Allah zasu taimaka Miki Sosai.
•Na Hudu idan kika ɓoye Wannan matsala ko dan jin kunya ko wani abu to ki sani fa babu wanda zai cutu sai ke, dan idan abin ya gagara za'a iya cewa sai an yanke ko wani abu mak**ancin haka, to kinda ina Amfani, shi yasa dama kullum muke cewa "Ri ga Ka fi Yafi Magani".
Hanyoyin da za su taimaka wajen rage haɗarin kamuwa da kansar Mama.
1.Shayarwa.
2.Motsa jiki ko atisaye akai-akai.
3.Daƙile ƙiba/teɓa.
4.Ƙauracewa shan taba, shaƙar hayaƙin taba da dangoginta.
7.Ƙauracewa radiyeshin k**ar hasken 'x-ray' da sauran jinsinsa.
Da Sauran su.
Kada a Manta kullum muna cewa "Rɪ Gᴀ KᴀFɪ YᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ".
The food you eat can be either the safest and most powerful form of medicine or the slowest form of poison.
Ri ga Ka Fi Ya Fi Magani.
✅💉💊✅
Ri ga Ka fi Ya fi Magani
✅💊💉✅
Rɪ Gᴀ KᴀFɪ YᴀFɪ ᴍᴀGᴀɴɪ.
💉💊💉
••• Jan Hankali •••
Da zarar munji zazzaɓi ko ciwon kai mu dena ɗaukar Maganin Malaria muna sha barkatai, saboda ba ko wane zazzabi da ciwon kai bane Malaria, haka kuma ba ko wane ciwon Ciki bane Olsa, sannan ba ko wane ciwon Dubura bane Basir, kuma ba ko wane tari bane Mura.
Mu fara zuwa asibiti a aunamu sannan likita ya bamu maganin da ya dace da matsalar mu.
Kada mu Manta har kullum dai Riga kafi yafi Magani".
.
Mu dinga kwana a Cikin Gidan Maganin Sauro, Mosquito Net domin kare kanmu daga zazzabin Malaria.
Duk Lokacin da Zaku yi buɗa baki kada ku manta da kayan Marmari.
🍋🍊🍉🍎🍌
Ku kasance da Wannan Shafi domin samun bayanan kiwon lafiya a Cikin Harshen Hausa.
Muna Fatan Duk Lokacin da kuka yi Buda Baki kuna hadawa da kayan Marmari.
🍍🍌🍍🍎🍒🍐🍉
Kayan Marmari suna da Amfani ga Lafiyar mu.
🍉🍐🍌🍋🍊🍎
Fadada Lafiyar Al'umma Ita ce Aikinmu.
✅💉💊💉✅
I have chosen to be happy because it is good for my health.
✅💊💉💊✅
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Telephone
Website
Address
10, SANNI ABACHA Road
Gusau, 860211
We are no 1 in Health Services Management in Zamfara State
Janyau Ta Gabas Along Gidan Dawa
Gusau
To improve health care delivery system
Samaru Area Gusau
Gusau
This page is created to disseminate all activities of Zamfara State Drugs and Medical Consumables Management Agency . It is managed on behalf of the Agenc