Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform

Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform

The Jigawa Future Group (JFG) is a registered non-governmental,non-partisan and not for a profit org

23/08/2023

Kawo karshen nemawa Hajara Muhammad Taimako a wurin Al'umma.

Cikin hukuncin Allah da rahmar sa, a yau Laraba 23rd August, 2023. Muna masu farin-cikin sanar da dukkanin al'umma cewa anyi wa Hajara Muhammad aiki na EX-LAP kuma cikin rahmar Allah anyi nasarar yin aikin, a yanzu haka an sallamaita daga Asibitin Fmc Birnin kudu ta koma gida, Gidan na nan a Audu Bako Road, Birnin kudu, gida mai Number 63, gidan Marigayi Malam Dan-azumi.
Adadin kudaden da aka samu daga wurin Al'umma ta sanadiyar wannan gidauniya ya kasance nera 63,000 daga baya kuma aka kara samun tallafin nera 12,000 daga wurin wasu mutane wanda muma bamu su waye ba, jimlar kudaden da aka samu ya k**a 75,000 chip da chip dama kuma shine adadin kudaden da hukumar Asibiti s**a bukata, kuma cikin ikon Allah anbiya har ma anyi sallama.

Muna rokon Allah ya sakawa dukkanin mutanan da s**ayi taraiya wurin ceto rayuwar wannan baiwar Allah tunda masu yadawa, masu turo sadaqa da sauran al'ummar annabi. Allah ya amsa daga garemu baki daya a matsayin ibadah ita kuma Allah kaffara ne.

Sako daga:
Jigawa Future Group For Leadership and Social Reform.

13/08/2023

Tunasarwa Gamai da Taimakon da mu ke Nemawa Hajara Muhammad.

Cikin ikon Allah da rahmar sa, Hajara Muhammad ta samu taimako daga wurin mutane da dama, ciki akwai wani bawan Allah wanda ya bukaci a boye sunan sa, ya tallafa mata da Nera Dubu Arba'in(40,000). Baccin haka an kara samun wata Mata wacce ita ma ba'a bada damar bayyana sunan ta ba ta bada tallafin Nera Dubu Goma(10,000). Muna rokon Allah ya saka musu da gidan Aljannah.

Jimlar kudaden da aka samu domin yi mata Aiki ya kasance k**ar haka: 40,000+10,000+11,500(wanda aka tura acikin asusuwan gidauniya) ya k**a = 61,500.

Hakikanin abunda ake nema domin biya mata kudin Aiki shine: 75,000. Wanda ayanzu haka muna neman cikwaton kudi nera 13,500.

Dan Allah ku taimaka domin asamu abiya kudin.

05/08/2023

Cikin ikon Allah da rahmarsa a kokarin ceto rayuwar Hajara Muhammad daga halin rashin lafiya da ta fada na fashewar hanji. Kawo yanzu munyi nasarar tara kudi nera 10,500 acikin asusun da ake nema mata taimako. Wanda ayanzu haka muna neman cikwaton nera 64,500 daga wurin al'ummar annabi domin asamu abiya mata kudi aiki nera 75,000.
Dan Allah ku taimaka wurin sanya sadakar ku komai kankantarta tare da tura wannan sako zuwa wurin al'ummar annabi.

02/08/2023

CETON RAI.

Dan Allah Yan-uwa ku tallafa da abunda Allah ya h**e mu ku komai kankantarsa domin ceto rayin Yar -uwar mu a musulunci mai suna Hajara Muhammad.

Hajara Muhammad, mazauniyar ƙaramar hukumar Birnin kudu, Titin Audu Bako, gida mai number 64. Hajara Muhammad na fama da matsananciyar rashin lafiya wanda aka kwantar da ita a dakin A&E na Federal Medical Centre Birnin Kudu, a binciken da likitoci su kayi sun gano cewa HANJINTA ne ya ɓule sakamon tsananin ciwon typoid, dalilin haka yasa dole sai anyi mata aiki wanda ake kira da EX-LAP domin ceton rayuwarta.

Kuɗin da aikin EX-LAP ya k**a ₦75,000. Banda kuɗin gado da magunguna wanda su ma suna buƙatar kuɗi na mussaman, kuma a halinta basu da ƙarfin da zasu iya biyan kuɗin aikin. Dan haka muke roƙon al'umma da su saka hannu wajen ceton ran baiwar Allah nan wadda ayanzu haka take neman agajin al'umma.

Duk wanda yatemaki wani domin ceton rayuwarsa haƙiƙa ya zuba dukiyarsa awajen da zai girbeta aranar sak**ako.

Domin bada taimako:
ACC: 2244635464
ACC NAME: Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform.
BANK NAME: UBA BANK

KO a tuntube mu a number waya k**ar haka:07042434683, 08112880947.

Allah yabada ikon taimakawa.

03/04/2023

Assalam, ina mai farin cikin sanar da ku cewa mun kammala Project din mu, na nemawa yan-uwan mu musulmi Marayu, Nakasassu da Mabukata taimakon a wurin al'umma domin raje musu radadin rashin abun da zas**ai bakin su a lokutan sahur da buda baki. Insha Allahu daga Gobe zuwa Jibi zamu kai kayayyakin abuncin ga mutanan da s**a chanchanta. Muna godiya ga dinbum al'umma da s**a tayamu da kuma wanda s**a turo tasu sadaqar, Allah ya saka da gidan Aljannah.

26/03/2023

Cikin ikon Allah da rahmar sa, a yanzu haka mun tara kudi kimanin nera 25,800 a asusun ciyar da Marayu, Mabukata da marasa galibu a cikin wannan wata mai rahma. Muna kara rokon Al'ummar annabi da ku sanya naku tallafin domin sanya yan-uwan farin-ciki da yaye musu damuwar abun da zasu kai bakin su yayin sahoor ko buda baki.

25/03/2023

We appeal more donation to reach our target. In this Ramadhan our target is to distribute 200 food packs to 200 fasting muslim households in jigawa state. Please we appeal your donation no matter how small it is.

09/03/2023

Shin yan'uwa muna tuna halin da yan'uwanmu marayu, gajiyayyu da nakasassu su ke ciki???, Muna tuna halin dazasu shiga acikin Watan azumin Ramadan mai zuwa duba da yanayin tsadar rayuwa da aka shiga?? Yan-uwa tayaya zamu iya yin sahur da buda baki da abinci mai dadi da gamsarwa alhalin wasu suna fadi tashin neman abin da za s**ai bakin su, shin ya zakaji Idan kaine a wannan yanayin? Dan Allah yan'uwa mutaimaki bayin Allah nan suna neman agazawar mu. Mu so wa yan-uwan mu abunda muka so wa kan mu.

06/03/2023

Mu na roka wa Yan-uwa musulmi Nakasassu,Marayu da Mabukata sadaqar kayan abinci wanda za su kai bakin su a lokacin azumi.

28/02/2023

Kulawa ta kwarai da za mu iya nuna wa junan mu ita ce; mu so wa yan-uwan mu abun da muka so wa kan mu. Dan Allah ya ya kace ji idan ka rasa abun zaka yi sahur da shi??? Wanne irin yanayi kace shiga idan ka rasa abunda zakayi buda baki da shi???. Ko wanne daya(1) daga cikin ya na so idan ya kai azumi ya samu abinci mai gamsar wa domin ya kai bakin sa, Dan Allah kayi tunani gamai da halin da yan-uwan mu musulmi Marayu, Nakasassu da Mabukata suke shiga a lokacin azumi.
Insha Allah, Ba za mu gajiya ba wurin nema wa yan-uwan mu sadaqa domin sanya su farin-ciki da yaye mu su damuwar abun da zasuci a lokacin watan azumi.

28/02/2023

Ba da gudunmawar ka domin ciyar da marayu,nakasassu,gajiyayyu da marasa galibu a watan azumi mai zuwa. Allah ya bada iko.

24/02/2023

Sadaqah tana kankare zunubai k**ar yadda ruwa ke kashe wuta. Ku taimaka da abunda Allah ya h**e mu ku domin ciyar da Nakasassu,Marayu, da Mabukata a wannan wata mai zuwa wato Ramadhan.
A wancan azumin da ya gabata, a madadin dukkanin wanda s**a bada taimako munyi nasarar raba kayan abinci ga mutane 42, wanda a wannan shekara kuma a madadin ku mu ke addu'ar mu raba kayan da kimanin mutane 200 zasu amfana.
Future Group
Alkhairi

03/10/2022

Alhamdullahi, lafiya na kara samuwa!

Photos from Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform's post 20/09/2022

Allah mai rahama mai jin kai.

Bayan tsawon watanni da muka dauka muna kai kawo da wannan yaro mai suna Surajo Yusuf a Asibitin Malam Aminu Kano, cikin yardar Allah da hukuncin sa, anyi Aiki (Surgery) kuma aiki yayi kyau, Surajo Yusuf ya samu lafiya alhamdullah. Muna kara rokon Allah Almaliku, Assalamu, Alkhaliqu, Alwududu ya sakawa dukkanin wanda s**a taimaka ta bangaran bada tallafin kudi, yadawa, da kuma addu'a. Allah yasa wannan yaro ya zamanto haske kuma abun alfahari ga al'umma.

Future Group For Leadership and Social Reform.

12/09/2022

Innah lillahi wa'innah ilaihi raji'uun.

Muna jajantawa al'ummar Garin Gabari dake jihar Jigawa bisa ambaliyar ruwa da ta yi sanadiyyar rushewar gidaje, asarar dukiya da asarar rayuka. Ya Allahu ya Alraheem ka kawo musu agajin gaggawa, Ubangiji Allah ka biya musu bukatunsu na samun matsuguni, sutura da abinci.

Ameeen ya hayyu ya qayyum.

05/08/2022

Kimanin Naira 213,126.00 (Dubu dari biyu da sha-uku da dari da ashirin da shida) aka kashe a kwana ki 35 da Surajo Yusuf ya dauka a asibitin Malam Aminu Kano.

Amadadin wanda s**a ba da sadaka domin ceton rayuwar Surajo Yusuf, mun biya kudin abubuwa k**ar haka;
-Munbiya kudin kwanaki 35 a gado (Total bill) Nera 112,645.00
-Munbiya kudin Aiki (Surgery) Nera 40,268.00
-Munbiya kudin Allurar bacci (Anesthesia) Nera 30,213.00
-Abunci (Nutritional meal) Nera 20,000.00
Banda sauran kananun kudade da s**a tafi ta hanyoyi da dama, wanda bamu isa mun kidajesu ba.

Abaya kudin da muka tara 167,000.00 ya kare kwata-kwata. Amma cikin ikon Allah wani mutum da makwabcin s**a turo sadakar Nera 80,000.00 domin cigaba da kula da Surajo Yusuf.

Likitoci na cigaba da kula dashi har zuwa lokacin da Allah zaisa ayimasa aiki. Muna barar Addu'ar ku, Allah ya tashi kafadun wannan yaro.

04/08/2022

We prayed for Allah to please protect the lives of all victims of this flood. Provide safe passage out of danger. Guide them to a place of dry and comfortable lodging. Provide them with clean drinking water and nutritious food.

18/07/2022

Hukumar Asibiti ta bukaci a kara biyan kudin gado da magani nera Dubu-talatin 30,000 a karo na uku (3).

Hukumar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, ta bukaci a kara biyan kudin gado nera 30,000 domin cigaba da kula da lafiyar Surajo Yusuf, Cikin hanzari kungiyar Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform ta biya nera 15,000 a madadin nera 30,000 domin kaucewa taba kudin aiki nera 80,000

Kamar yarda muka baiyana abaya cewa kudin da hukumar asibiti ta nema kafin yiwa Surajo Yusuf aiki (Surgery) shine nera 167,000 wanda za'a kashe su ta hanya k**ar haka;
• Kudin kwanciya (Admission)= N50,000
• Kudin gwaji (Ct-scan)= 17,000
• Kudin aiki da allurar bacci (Surgery & Anesthesia)= 80,000
• Kudin magani (Drugs)=20,000
Wanda jimlar su ya tashi 167,000

Kana akwai nau'in maganunuwa (drugs) da allurai (injection) da lokaci-lokaci ake bukata, wanda hukumar asibiti bata rubuta su a acikin lissafin kudin da aka bawa kungiya ba tun farko sai daga baya.

A cewar likita mai kula da Surajo Yusuf ya baiyana wa kungiya cewa acikin satinan za'a iya yiwa Surajo Yusuf aiki (Surgery) sbd haka yana bawa kungiya shawara ta tanadi kudin aiki a hannu, wannan dalili yasa kungiya ta futar da nera 80,000 cif-cif daga cikin asusun da aka yiwa Surajo Yusuf domin biyan Kudin aiki kana daga baya a nemi sauran kudadan jinya da magani.

Allah ya sakawa al'umma da alkeri, Allah kuma ya tashi kafadin Surajo Yusuf.

09/07/2022

Barka da Sallah!

07/07/2022

Karin haske akan halin da Surajo Yusuf ya ke ciki a asibiti!

Barkan mu da wannan lokaci.

Kamar yarda bayanai s**a gabata a baya, wanda yayi dai-dai da 30th June,2022. Kungiya ta sheda wa al'umma cewa an kwantar da Surajo Yusuf a asibiti koyarwa na Aminu Kano, wanda hukumar asibitin s**a nemi a biya kudin gado nera Dubu-goma (10,000) na tsawon kwana ki bakwai (7) a karo na farko (i).

Jiya laraba 6th July,2022. Hukumar asibiti na Aminu Kano sun bada takardar tunasarwa cewa kudin da aka biya na kwana ki bakwai (7) ya kare kat, sabida haka su sanarwa masu daukar nauyin kwanciyar yaron a asibiti cewa a hanzarta kara biyan kudin gado a karo na biyu (ii) domin cigaba da bawa yaron kulawa a gadon asibiti. Kungiyar Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform ta yi azama wurin biyan kudin da hukumar asibiti s**a bukata nera Dubu-goma (10,000) daga cikin asusun da akayiwa yaron.

Jama'a musani cewa;
Wannan abubuwa da akeyi yanzu sune wanda aka kasa yin su a baya, tun daga ranar da aka haifi yaron zuwa lokacin da kungiyar Jigawa Future Group ta sa hanu, kimanin wata goma (10) da sati daya (1), hakan ya faru sanadiyar rashin kudin da iyayen yaron zasu bayar, wanda hakan yayi sanadiyar sa wurin cutar (meningocele) zubar da ruwa har takai da kwakwalwar yaron ta fara tabuwa. Likita da ke kula da Surajo Yusuf ya baiyana cewa idan ana so a ceton rayin wannan yaron dole sai an yi hakuri da juriya kana a bi matakan da hukumar asibiti s**a gindaya domin samun waraka da zarar wurin ya warke toh babu shakka a ranar za'ayi aiki kuma ya samu lafiya insha Allah.

Akarshe, muna rokon Allah ya saka wa al'umma da alkerin sa, Allah ya kara bude mana kofofin rahma, Allah ya tashi kafadin wannan yaro.

Sai kun kara jin mu...

Photos from Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform's post 06/07/2022

Heartfelt Congratulations.

Congratulations on passing this significant milestone Parade Passing Out. Nice work you have done all of you, and now you see how essential is to have determination, optimism and patience. Sincerely the uniform have suited and will gives you chance to prove yourself as Social Reformers And Humanitarians.

This is a day of great happiness for everyone in Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform. Actually You’ve made us all proud, this magnificent triumph is the result of your continuous efforts, resolve and determination.

We wish all of you a successful life ahead. Congratulations our own officers Khalifa Ringim and Sani Umar Sara.

05/07/2022

Today’s headline ought to read: “Offer of Provisional Appointment given to the most qualified, deserving person,” with a adamantine humanitarian heart in person of Aliyu Adamu Dutse, Secretary General Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform.

Despite our best intentions in reducing the rate of poverty in Jigawa State and building the leaders of tomorrow, we never know exactly where our paths will take us. That yours has led you to this offer of provisional appointment is simply sensational. You are more than ready for it, and we know you’ll rise to the occasion insha Allah.
Congratulations on your provisional appointment as Assistant Lecturer, Jigawa State Polytechnic Dutse.

30/06/2022

Halin da ake ciki gamai da rashin lafiyar Surajo Yusuf.

Barkan mu da wannan lokaci, Kamar yadda mu ka alkawaranta cewa lokaci-lokaci zamu ringa sanar mu ku halin da Surajo Yusuf ya ke ciki.

Kamar yadda mu ka sheda mu ku wancan Satin ranar laraba 22 June,2022. Wakilan wannan Kungiya sun kai Surajo Yusuf Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin ayi masa aiki, kuma an sheda mu ku Bayanai dalla -dalla da yasa ba'ayi aikin ba.

Ranar lahadi 26th June,2022. Wakilan wannan kungiya sun ziyar ci Surajo Yusuf a gida domin duba lafiyar sa, cikin ikon Allah su ka tarar jikin sa yayi tsamari harma hakan ya sa iyayen sa zubar da hawaye, ganin matsanan cin halin da Surajo ke ciki, yasa a ranar lahadin walikan kungiya su ka Kai shi asibitin karamar hukumar Birnin kudu domin abashi agajin gaggawa. Likita ya duba shi kana ya rubuta magani da allurai da za'a siyo an kashe kudi nera 2300 wurin siyo magagun guna da allure, kana aka biya nera 500 na Gwaji (test). Ranar Litinin 27th june, 2022. Likita ya kara bata takarda dauke da sunayen alurai da magani, an kashe kudi nera 440 wajen siyowa. Haka zalika ranar talata 28th june,2022. Likita ya rubuta magani da allurai wanda aka kashe nera 2250 wurin siya.

Ganin yarda jikin Surajo Yusuf ya kara tsanan ta duk da cewa yana asibin karamar hukuma, kungiya da iyayen Surajo Yusuf da taimakon wasu malaman lafiya s**a yanke shawarin kaishi asibitin kudi, duk dai domin ceton rayuwar Surajo Yusuf. Cikin ikon Allah jiya laraba 29th June,2022. Kungiya da iyayen Surajo su ka tafi zuwa PRIME SPECIAL CLINIC kano, zuwa wannan asibiti, aka bukaci nera 7000 domin bude file, kana aka tura su zuwa wurin likita da zai dubashi, likita ya bukaci ayiwa wurin Meningocele din dressing akan nera 2000. Bacin haka likita ya fadi cewa kudin aikin meningocele a asibitin yana kaiwa 2.5 million. Kungiya da iyayen yaro s**a nuna basu da karfin haka, cikin ikon Allah sai likitan ya bada shawarin a kara mai da Surajo asibitin koyarwa na Aminu Kano aka karo na biy

Photos from Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform's post 22/06/2022

.

Assalam alaikum, barkan mu da dare, sak**akon gwaje-gwaje da aka yi wa Surajo Yusuf ya nuna cewa baza'a iya yi masa aiki ba yanzu, domin kuwa wa'adin da aka debar masa a kan su koma asibiti basu samu damar ko mawaba a kankari, wanda hakan ya haifar masa da taruwar ruwa, hakan ya faru sanadiyar rashin samun kudin da za'ayi masa aiki akan kari.

A sanadiyar haka likitoci da suke lura da Surajo Yusuf sun bukaci a mai dashi gida, kana kuma sun gindaya matakai wanda za'abi domin a samu wurin ya kame da wuri domin ayi masa aiki, sun rubuta wasu kayayyaki da za'a siya domin a ringa wanke masa wurin, kana sun bada sunan magunguna wanda yaron zai ringa sha da kalar abincin da za'a ringa bashi wanda cikin ikon Allah da kudin da aka tara an saya, sannan an ajiye kudin aiki acikin asusun kungiya sai ranar da Allah ya kaddara kamewar wurin.

Muna yiwa al'umma godiya bisa jajircewa da nuna kwazo wurin taimakon wannan yaro ta hanyar bada tallafin kudi, da tayamu neman agajin al'umma wanda hakikanin gaskiya bamu da kalaman da zamuyi amfani wurin nuna farin cikin mu agare ku, amma muna kara rokon Allah ya saka mu ku da mafificin alkerin sa.

Sai kun kara ji daga garemu insha Allah.

22/06/2022

To the greatness of almighty Allah and through your kindness,dedication and donations, today being Wednesday 22 June, 2022. We've been able to raised the sum of 162,000.00 naira and our target is to reach 147,000.00 naira and we're now having an extra amount of 15,000 naira.

We truly can't thank you enough for the generous donation you made toward saving the life of Surajo Yusuf. Your donation will allow us to pay for his admission, surgery and anesthesia, Ct scan and drugs and the remaining 15,000 naira we'll make use of it for Transport from Birnin kudu local government to Aminu Kano teaching hospital. We feel so blessed that so many people came together to support us when we need it most.

The representatives of Jigawa future group for leadership and social reform are presently now at Aminu kano teaching hospital together with the patient at the paediatric clinic waiting for the result and outcomes.

We'll further inform you about the outcomes insha Allah .

following our update!

21/06/2022

Assalam barkan mu da safiya.
Muna samun ci gaba sosai, Yanzu haka kudin da ake hadawa domin yiwa Surajo Yusuf aiki ya kai 54,800 muna rokon Allah ya sakawa al'umma da alkeri, Allah ya bashi lafiya. Dan Allah mu ci gaba da kokari har sai mun hada kudin aikin nera 147000. Allah yasa mudace, Allah ya bashi lafiya.

20/06/2022

See how this lad is suffering a lot! Please donate with the little you have perhaps he might be the one to help you tomorrow.

20/06/2022

See how this lad is suffering a lot! Please donate toward saving his life, perhaps he might be the one to help you tomorrow.

19/06/2022

We genuinely appreciate your donation toward saving the life of Surajo Yusuf, a 9 months old boy who hails from Birnin Kudu local government. Through your kindness and donations, today we raised 40,600 naira for this cause. There's a hope insha Allah and the hope is you (the one who donate and ask for, the one who share and pray). Thank you again for your generosity.

18/06/2022

Assalam Alaikum.
Thank you for your continues support and donations, we raised 24,000 naira as per day. Please lets keep sharing and mobilizing tl we reach the target.

18/06/2022

Dan Allah, idan ka san wani mutum wanda idan aka sameshi da matsalar wannan yaro zaiyi kokari matuka. Dan Allah kayi mana kokari zuwa gareshi ko abamu bayanan sa domin muje mu sameshi akan matsalar wannan yaro, wanda kullin acikin fargaba iyayen sa suke sabida tsabar tsananin zafin ciwo dake damunsa, Sun kai wata daya da rabi, suna ta jele domin ceton rayuwar sa, Amma sabida rashin dama haryanzu yaron yananan kullin matsalar sai habaka takeyi...Allah ya sa adace.

18/06/2022
17/06/2022

To the glory of almighty Allah, we raised the sum of 11,000 naira as of today Friday. One person can stop a great injustice, one person can be the voice of the voiceless and the voice of truth, one person's donations can save the life of Surajo Yusuf.
Whoever saves one life, saves the world entire. Thank you for your great generosity, we at Jigawa future group for leadership and social reform, greatly appreciated your donation and sacrifice.
Donation continue.... The target amount is 147,000 naira.

17/06/2022

Ceton Rai.

Kungiyar goben jigawa domin jagoranci da gyara zaman takewa. Amadadin iyayen Surajo, muna rokon al'umma da su taimaka da abinda Allah ya h**e musu, Surajo yaro ne dan wata 9 da haihuwa, wanda iyayen sa suke zaune dashi a unguwar Kurima da ke garin Birnin kudu a jahar jigawa. Sarajo yana fama da wata nau'in matsala/cuta dake sa kashin baya da jijiyoyi su habaka ta waje, wanda idan ba'ayi da gaske ba hakan ka'iya janyo shanyewar jiki. likitan da ke kula da marar lafiyan ya tabbatar da cewa ana da bukatar naira 167,000 kachall domin yi masa aiki, k**ar yarda yake a lissafe:
• Gado. 50,000
• Aiki (tiyata). 80,000
• Sikanin. 17,000
• maganunuwa. 20,000
Jimla= 167,000

Ku sa ni cewa;
Kafin wannan rana, iyayen Surajo sun futa neman taimako daga hannun al'umma harma s**a sami 76,000 sunyi amfani da 56000 wurin zirga-zirga, gwaje-gwaje, magunguna da sauran su wanda yanzu haka kudin daya raje shine 20,000 kachall. A dalilin haka ne muka ga ya dace mu sanar wa al'umma halin da wannan yaro ya ke ciki domin bashi taimako, sabida iyayen sa basu da karfi. Ya na da matukar amfani domin kaji daga bakin iyayen marar lafiyan ko kuma domin bada gudun mawa, 08067680557.

Haka zalika zaka iya bada taka gudun mawar ta lambar asusun ajiya k**ar haka;
•2244635464
•Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform
•UBA

Allah yabada iko.

rai
taimako
# ka/ki turawa wanda sakon baije gareshi ba.

16/06/2022

Save the life of Surajo Yusuf.

Jigawa future group for leadership and social reform wish on behalf of Surajo to solicit your generous donations, surajo is 9 months old boy, who hails from kurima birnin kudu local government, jigawa state. surajo is being managed with lumber myelomeningocele who's being worked up for excisional and repair. according to his consultant he will require the sum of 167,000 naira only as per breakdown;
1- Admission. N50,000
2-Surgery and Anesthesia. N80,000
3-Ct Scan. N17,000
4-Drugs. N20,000
Total: N167,000naira only.

Note that, Initially the parents of the patient sought for donations and raised the sum of 76,000naira, they spent 56,000 naira for necessary drugs, transport,scanning and transport the remaining amount now is 20,000 naira only. It's in view of the above that we found it essential to inform the general public and ask for generous donation of 147,000 naira as his parents are less privilege.

You may find it essential to contact his Father for further information or assistance as the case may be, phone number 08067680557.

More ever you can send your donations through;
Account number: 2244635464,
Account name: Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform.
Bank name: UBA

life of Surajo
Appeal

Photos from Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform's post 09/04/2022

Seasons Greeting!
It came to our notice that a chap from chamo dutse local government, Haruna Yahuza Chamo by name, is using our flayer background in a wrong way, just for himself interest. Moreover we contacted and warned him against the acts, he promised to not do it again and asked for forgiveness. With that we're pleasing you to disregard the fake flayers and clear your mind that Jigawa Future Group has no any relation with any politician rather then advice where necessary or as the case may be.
Attached are the differences the fake flayer and original.

Photos from Jigawa Future Group for Leadership and Social Reform's post 07/04/2022

Season Greeting!!!
Today being 7th April, 2022. Jigawa Future Group For Leadership And Social Reform managed to distribute *32* Ramadan Food Packs to most vulnerable families in Kaugama Local Government, therefore we're using this medium to thanks our esteem donors for this noble cause. To be frank with you, your whole hearted donation is what actually make us to moved the mountain and the mountain appeal with your donations, we can't do any things as an organization with out your supports and encouragement.
May Allah grant you Jannah

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Jigawa?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

See how this lad is suffering a lot! Please donate with the little you have perhaps he might be the one to help you tomo...
See how this lad is suffering a lot! Please donate toward saving his life, perhaps he might be the one to help you tomor...
Just listen to it
Please  grace our program by Attending and supporting.
please Donate

Telephone

Website

Address

Jigawa