Hadimin Dan Modi

Hadimin Dan Modi

computer software professional

25/08/2024

Kainuwa

05/08/2024

Game da Addu'ar Ƙasa (National Prayer):

1. Ba za mu je Abuja ba saboda dalilan tsaro. Jama'ar kowace jaha za su haɗu a wani babban masallaci, ko gurin haɗuwa na mutanen jahar, su ɗebi wani adadi na saukar karatun da za su iya yi a ranar, sannan addu'a ta biyo baya. Buƙatarmu shine mu haɗa sauka MILIYAN ƊAYA zuwa faɗuwar ranar Asabar.

2. Za a fara da salatin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ranar Juma'a, wato ranar 9 ga wata. Ba mu ɗaukewa kowa ba a wannan. Muna fatan kowa ya yi salati dubu (1000) zuwa sama a wannan ranar. Don Allah kowa ya ware wata awa, ko awanni, don yin salati a wannan ranar, kaɗai don neman taimakon Allah Subhanahu wata'ala a kan sha'anin ƙasarnan!

3. Ranar 10 ga watan ita ce ranar Asabar kuma, wato ranar Al-Ƙur'ani. Don haka za mu yi saukokin karatu a ranar ne kawai, sannan mu yi Azumi a ranar Litinin, 12 ga Agusta kenan, duka don neman taimakon Allah Subhanahu wata'ala.

4. Muna kira ga ƴan'uwa Gwanayen Alƙur'ani na wannan dandali da su isar da wannan saƙo ga dukkanin ƴan uwa makaranta Al-Ƙur'ani da ke kowane lungu da saƙo, Islamiyyu da makarantun Al-Ƙur'ani a duk inda su ke.

5. Za mu sanar da gurin haɗuwarmu a nan Kano, tare da adadin saukar da za mu yi a nan Kano, da kuma jagororin taron addu'ar in Sha Allahu, zuwa gobe.

6. Muna jiran saƙonnin ragowar jahohi.

7. Za mu buɗe ƙofa ga duk wanda ya ke da ikon kawo ruwa, lemo ko abinci ga masu karatu a ranar Asabar, musamman saboda masu tahowa daga nesa, da kuma dalilin shigar da ladan ciyarwa cikin ibadun da za mu yi tawassuli da su!

Allah ya karɓi addu'o'inmu, Ya kawar mana da dukkanin azzaluman da s**a matsa mana, albarkacin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da Al-Ƙur'ani! Amin!
Kayi sharing dan mu hadu a ladan gaba daya
Mubarak Ibrahim Lawan

27/07/2024

Gwamnatin Jigawa za ta haɗa hannu da Saudiyya don inganta makarantun allo

Hadimin Dan modi

Photos from NTA Network News's post 27/07/2024
Photos from Hadimin Dan Modi's post 24/07/2024

Malaman addini, gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago, ƙungiyoyin ɗalibai, lauyoyi, 'yan kasuwa, bakanikai, mahauta, ƙungiyoyin matasa, direbobi, ƙungiyoyin kiristoci daƙi mazauna jihar Jigawa, sun nesanta kansu da duk wani yunƙuri ko fitina da sunan zanga-zanga wadda ka iya shafar zaman lafiyar da mu ke da shi a jihar Jigawa.

Sannan sun yi ƙira ga al'umma musamman matasa da su guji shiga duk wata harka da za kawo fitina ko hatsaniya a cikin al'umma. Domin duk abin da zaman lafiya bai kawo shi ba, hayaniya ko tashin hankali ba zai samar da shi ba. Don haka sun yi ƙira da a ci gaba da yiwa ƙasa addu'a, da yin duk wani abu da zai wanzar da zaman lafiya, har zuwa lokacin da Allah zai warware wannan hali da ake ciki.

Daga karshe, sun yi ƙira ga gwmnatin jihar Jigawa da ta ci gaba da yin ayyukan alkhair da ci gaban al'umma da ake, wadda hakan shi zai ci gaba da wanzar da zaman lafiya da rusa duk wani yunƙuri da tayar da tarzoma.

©Jigawa New Media Office.

Hadimin Dan modi

Photos from Hadimin Dan Modi's post 24/07/2024

Flags Off Training 1000 Youth on Artificial Intelligence and Block Chain Technology.

Vice President Shettima also inaugurated the 4th Expanded National Micro Small & Medium Enterprises Clinic in Dutsen, the State Capital.

Hadimin Dan modi

Photos from Hadimin Dan Modi's post 24/07/2024

VICE PRESIDENT KASHIM SHETTIMA’S HISTORIC VISIT TO JIGAWA STATE

In a landmark visit to Jigawa State, Vice President Senator Kashim Shettima, GCON, arrived in Dutse on Tuesday, where he spearheaded the commissioning and launch of various developmental projects executed in the state.

Governor Malam Umar Namadi and the people of Jigawa warmly welcomed the VP, with large crowds lining the streets and attending various events. The Vice President's one-day visit underscored significant strides in economic growth, job creation, and technological advancement, marking a new era for the state.

The day started with Governor Namadi, along with other top government functionaries, welcoming the Vice President at the Dutse International Airport. From there, he directly proceeded to Madobi village in the outskirts of Dutse, where he commissioned a 20,000-hectare sprinkler-based solar-powered irrigation scheme.

The VP also commissioned a 100 KVA solar-energy power supply for Dutse Markets.

At the Aminu Kano Triangle, the Vice President launched the 4th Expanded National MSME Clinics, a pivotal initiative aimed at promoting entrepreneurship and the development of small and medium-scale enterprises. This program aligns with President Bola Ahmed Tinubu’s Renewed Hope Agenda, which focuses on creating an environment for inclusive and sustainable economic growth in Nigeria.

"We are delighted that this also aligns with our agenda for Greater Jigawa," stated Governor Namadi. "We have mobilized over 100 MSMEs, including startups and home-based entrepreneurs, to participate in today's clinic. This is a rare opportunity for MSMEs to access a wide range of business development services."

Vice President Shettima revealed that the Federal Government under President Bola Tinubu has created over 300,000 businesses through various small and medium-sized enterprises (SMEs) interventions, aiming to create over one million job opportunities, especially for youth and women across the country.

21/07/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Yaqub Abdallah, Abbas A Muhammd

21/07/2024

An yi musayar yawu tsakanin fitacciyar jarumar Kannywoo, Nafisa Abdullahi da masoyanta a soshiyal midiya - Duba maganganun jarumar a sashen sharhi.

Hoto: (X)

12/07/2024

Hadimin Dauda Kahuta Rarara ya fayyace bidiyon wakar Atiku dauke da muryar mai gidansa.

Hoto: Dauda Kahuta Rarara (Facebook).

Ba gaskiya bane

11/07/2024

"Zan mayar da kudaden."

Tsohon Akanta janar zai mayar da kudin kasa.

Ana zargin Anamekwe Nwabuoku da wawashe N1.6bn.

11/07/2024

Sanatoci sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta magance matsalar tsadar abinci tun kafin hakurin 'yan Najeriya ya kare - Duba cikakken rahoton a sashen sharhi.

Hoto: (X)

Photos from Hadimin Dan Modi's post 11/07/2024

Da safiyar wannan rana, mai girma gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar A. Namadi FCA ya ƙarɓi baƙuncin tsoffin shugabannin ƙananan hukumomin jihar Jigawa, wadda wa'adin mulkinsu ya ƙare a watan da ya gabata.

11/07/2024

11/07/2024

Kotun Koli ta umarci Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ƙananan hukumomi daga asusunta. Karin bayani a sashen sharhi.

Hoto: Asiwaju Bola Tinubu/Facebook.

11/07/2024

Ga Jerin Takunkumi Guda Biyar da Kotun Koli Ta sanyawa Gwamnoni Dangane Da Cin Gashin kan Kananan Hukumomi

1- Gwamnonin Jihohi ba za su sake samun ikon rusa zababbun kananan Hukumomin da aka zaba ba

2-Za a soke kwamitin riko a fadin kasar nan

3- Za a aika da kason tarayya kai tsaye zuwa ga Kananan Hukumomi, a ketare Gwamnonin Jihohi.

4- Jihohi ba za su sake samun kudaden da aka tanadar wa ƙananan hukumomi ba.

5- Ikon Gudanar da zabe yana ƙarƙashin Gwamnatin tarayya ba Gwamantin jihohi ba.

Jama'a hakan ya yi kyau?

Photos from Hadimin Dan Modi's post 08/07/2024

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!

A jiya Lahdi Allah ya yiwa al'ummar garin Kalgwai ta ƙaramar hukumar Auyo a jihar Jigawa rasuwa su 30 bayan da Kwale - Kwale ya kife dasu a daren jiya akan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Gujungu.

Muna Addu'ar Allah ya musu rahama. Amin.

Photos from Hadimin Dan Modi's post 07/07/2024

HOTUNA;.Gwamna Namadi ya halarci taron aza harsashin gini domin sake tsugunnar da waɗanda iftila'in rikici ya baza su (RSPIC) a Kauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

Idan ba a manta ba, ƙungiyar gwamnonin Arewa, a zamanta da ta gabatar a watannin da su ka gabata ta zartas da ƙudurin yadda za a tallafawa al'ummar da iftila'in fadawar bam ya shafa a kauyen na Tudun Biri da ke Jihar Kaduna. Wadda a lokacin ƙungiyar ta haɗa kuɗade tare da gudunmawa da aka samu daga manyan yan kasuwa, jami'an gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin tallafawa waɗanda iftila'in ya shafa.

A jiya juma'a ne, mai girma gwamnan Jihar Jigawa, Mallam Umar A. Namadi FCA tare da sauran gwamnoni da kuma mai girma mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima , wanda shi ne babban baƙo na musamman a taron, manyan jami'an gwamnatin tarayya, sarakunan gargajiya da sauran manyan baƙi sun halarci wannan gagarumin taro.

Taron kafa Harsashin ginin, kamar yadda mai girma gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Uba Sani, ya bayyana a jawabinsa, ya shafi gina gidaje ga waɗanda iftila'in ya afka wa, gina asibitoci, gina t**i, samar da cibiyar koyon sana'a da sauran abubuwan more rayuwa ga al'ummar Tudun Biri da sauran yankunan da ke fama da rikicin ta'addanci a yankunan Jihar Kaduna.

-Government House Media Office
06/07/2024

Photos from Hadimin Dan Modi's post 06/07/2024

Bikin ba da tallafin kayayyakin Sanaa da Mai girma gwamna yayi

05/07/2024
Photos from Hadimin Dan Modi's post 05/07/2024

YA ALLAH KA'IYA MUSU, KA KUMA DAFA MUSU A WANNAN RANA TA JUMA'A.

Ya Allah muna tawassali da sunayinka dari ba ɗaya, ya Allah albarkachin wannan rana ta juma'a, kuma wannan wata da muke ciki, ya Allah ka'iyawa gwamnatin mai girma gwamna Mal. Umar A Namadi Fca tare da mataimakin sa Engineer Aminu Usman Roller.

Ya Allah duk abinda yake alkhairi ne a wannan gwamnatin tasu, Allah ka sada su dashi, Allah duk abinda ba alkhairi bane a wannan gwamnatin tasu Allah ka nisan ta waɗannan bayin naka a jihar Jigawa Alfarmar wannan rana da muke ciki ta juma'a.

Ya Allah kabawa gwamnatin mai girma gwamna tare da mataimakin sa ikon sauƙe nauyin da ya rataya a kansu, Allah karka basu da iyawarsu, Allah ka'iyamusu Alfarmar Annabi Muhammad s a w.

Ya Allah ka zaunar mana da jihar Jigawa ta jigawa lafiya, Allah kahaɗa kan shuwagabannin mu na Jigawa, ka kuma basu ikon kawowa jihar Jigawa ci-gaban da bamu taɓa tunani ba, Allah karka kawo abinda zai raba kawunan shuwagabannin mu na jihar Jigawa albarkachin wannan rana ta juma'a.

Ya Allah muna sake roƙonka Allah ka zaunar mana da nigeriyar mu lafiya, Allah ka kawo mana sauƙin duk wani ƙunchi da wahalhalu da muke fama dasu, Allah kai kasan yanayin da bayinka suke fama, Allah ka kawo mana sauƙi a nigeriyar mu baƙi ɗaya.

Ya Allah yadda kanuna mana wannan rana mai falala ta juma'a da ranmu da lafiyar mu, Allah kasa muyi sallah cikin nutsuwa da annushuwa, Allah ka karɓi ibadun mu baki ɗaya, Allah ka yafe mana kura-kuremu alfarmar Annabi Muhammad s a w.

Hadimin Dan modi

04/07/2024

Majalissar zartarwa ta jahar jigawa ta kaddamar fara daukar ma'akatan hisbah kimanin 1950 domin fara aiki gadan gadan bi'izinillahi ta'ala

04/07/2024

Kwamatin kar ta kwana (Task Force Committee on Loan Recovery) da Majalissar zartarwa ta jihar Jigawa ta kafa kan yadda za a dawo da bas**an da aka bayar a ƙarƙashin hukumar samar da ayyukan yi da dogaro da kai ta jiha (Jigawa state Agency for Youth Empowerment and Employment ) zai fara aiki. Kwamitin zai bibiyi waɗanda su ka karɓi bas**an wadda ya ɗauki tsawon lokaci ba a biya ba, domin dawo da su don hukumar ta samu damar sake bayar da shi ga ɗumbin al'umma da ke buƙatar bashin domin haɓaka manya da ƙananan masana'antu da ke jihar Jigawa.

'Yan kwamatin sun haɗa da:

-Chairman Jigawa Public Complaint and Anti-Corruption Agency

-Special Adviser on Security Matters

-Attorney General/Commissioner of Justice
-Commissioner of Special Duties

-Commissioner of Women Affairs

-Director General Jigawa Agency for Youth Empowerment and Employment

Photos from Hadimin Dan Modi's post 04/07/2024

HUKUMAR GANDUN DAJI TA ƘASA TA ZIYARCI GWAMNA NAMADI A SHIRYE-SHIRYEN MIƘA DAJIN BATURIYA GA GWAMNATIN TARAYYA

A safiyar wannan rana, mai girma gwamnan Jihar Jigawa Mallam Umar A. Namadi FCA, ya ƙarbi tawaga daga hukumar kula da gandun daji ta ƙasa (National Park Service) ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban hukumar ta ƙasa Dr. Muhammad Kabir, a cikin shirye-shiryen da ake yi mayar da ikon gudanar da dajin jiha na Baturiya "Baturiya Wetland and Game Reserve" ga hukumar.

Shirin miƙa dajin ya faro ne tun shekarar 2011 a lokacin taron inganta muhalli da gandun daji na ƙasa da aka yi a Kaduna. Duk da ƙoƙarin da aka yi a wancan lokacin, shirin bai kammala ba sai a shekarar 2022, lokacin da gwamnatin tarayya ta sanya hannu a takardar amincewa da mayar da dajin Baturiya da ke jihar Jigawa tare da sauran dazukan da aka amince da mayar da su a sauran sassa na faɗin ƙasa.

A jawabinsa, mai girma Gwamna ya jaddada aniyar Gwamnatin jihar Jigawa kan shirin miƙa gandun dajin ga gwamantin tarayya, ta yadda hakan zai kawo bunƙasar tattalin arziki ga al'ummar yankin da ma jihar Jigawa baki ɗaya.

Ya kuma yi nuni da muhimmancin kyautata wa tare da bawa al'ummar da ke yankin gandun dajin damar yin sana'arsu ta kamun kifi, kiwo da sauransu bayan an miƙa gandun dajin.

Da yake jawabi tun da farko, wakilin shugaban hukumar kula da gandun dajin, ya nuna godiyarsa ga gwamantin jihar Jigawa bisa ƙoƙarin da ta ke yi na ganin wannan al'amari ya tabbata da kuma inda ya naɗa wakilai a ƙarƙashin hukumar kula da muhalli ta jihar jihar Jigawa, wajen jagorantar zama da rukunin al'ummar da ke zaune a kewayen gandun dajin, zaman tattaunawa da wakilan hukumar kula da gandun dajin ta ƙasa.

Government House Press
4/7/24
Hadimin Dan modi

02/07/2024

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TA ƘULLA YARJEJENIYA DA BANKIN BUNKASA MASANA'ANTU NA KASA.

Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Mallam Umar Namadi ta sanya hannu a yarjejeniyar bunkasa masana'antu da bankin bunkasa masana'antu na kasa (Bank of Industry).

Yarjejeniyar za ta samar da gidauniyar hadaka (Matching fund) ta naira Biliyan 4, wadda a karkashinta gwamnatin jiha za ta saka naira biliyan 2 yayin da shi ma bankin zai zuba biliyan 2.

Sannan akwai gidauniyar gudanarwa (Managed fund) wanda gwamnati za ta zuba kudi naira Biliyan 2 a cikin ta.

Wadannan kudade masu kanana da matsakaitan masana'antu a jihar Jigawa ne za su iya karba bashi domin bunkasa sana'o'in su.

Jihar Jigawa ita ce jiha ta farko a fadin Najeriya da ta shiga irin wannan yarjejeniya da kudin da yakai har naira Biliyan 6.

A jawabin mai girma gwamna a wajen sa-hannu a yarjejeniyar ya ce bikin sanya hannun wani ci gaba ne da aka samu domin tunkararar yaki da fatara da talauci, da kuma samar da aikin yi ga dimbin mutane a wannan jiha. Taimaka wa mutane wajen bunkasa sana'oin su wani tsari ne na musamman da gwamnati ta dauka domin bunkasa tattalin arzikin jihar Jigawa, kuma hadin gwiwa da bankin bunkasa masana'antu zai taimaka wa gwamnati wajen cikar burin ta.

Gwamnan ya kara da fadin cewa da wannan sa-hannu da aka yi, gwamnati ta dauki kudurin hada kai da bankin domin samar da bashi ga kanana da matsakaitun da kuma manyan masana'antu a jihar Jigawa.

Bayan sa-hannu a yarjejeniyar, mai girma gwamna ya jagoranci jami'an gwamnati da shugabannin bankin wajen bude sabon ofishin bankin da ke kusa da unguwar makanikai (Mechanic Village) a birnin Dutse.

Babban daraktan bankin maikula da kanana da matsakaitun masana'antu Alhaji Shekarau D. Umar a jawabin sa wajen bude ofishin bankin ya ce sun shafe sama da shekaru 13 suna fafutikar ganin an bude ofishin bankin a Dutse, amma ba su sami sahalewa ba sai a wannan lokacin karkashin Gwamna Umar Namadi.

Ana sa ran yarjejeniyar za ta yi dalilin yad

02/07/2024

Yau ma muna nan tafe da wani abun alkhairi a jihar Jigawa. Ɗan-modi zai sake kafa wani tarishin.

02/07/2024

Idan kamfaninka ya cancanta abaka aikin ƙwangila a jihar Jigawa, basai kayi kamun kafa agun kowa ba, basai wani yasanka ba, ita gwamnatin Baba Ɗan-moɗi alheriche ga duk "ɗan jihar Jigawa.

Ita gwamnatin Baba Ɗan-moɗi dan tabaka aikin ƙwangila a jihar Jigawa ba ruwanta da karɓar percentage daga gunka illa abinda tafi so shine katsaya kayi aiki tsakani da Allah, saboda gaba.

Mai girma gwamna Allah yayiwa gwamnatin ka albarka, Allah ya cigaba da kawowa gwamnatinka alkhairi akodayaushe a jihar Jigawa. Amin

No collecting 10% percentage from any Dan kwangila.

MALLAM FA YANA KAN DAI-DAI



Hadimin Dan modi

02/07/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! Abdulsalam Idris, Ibraheem Abdulmumini, Odesey Ringim, Abubakar Sama'ila, Ahmad Abdussalam Nadankoli, Salisu Umar

Want your business to be the top-listed Grocery Store in Jigawa?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Kainuwa
#nigeriantiktok #Danmodi #jigawastate #meditation
#danmodi # @followers
@
#JigawaNewMediaOffice
#JigawaNewMediaOffice Hadimin Dan Modi

Category

Telephone

Website

Address

Jigawa Khs
Jigawa
Other Food & Grocery in Jigawa (show all)
Risilan Abdullahi ondemand Risilan Abdullahi ondemand
Katanga. Kiyawa Local Government
Jigawa

Mai kayan miya Mai kayan miya
Ramadan
Jigawa

Muhd Auwal khamisu Muhd Auwal khamisu
Gombe Steta
Jigawa

Hussaini Wuriwa Hussaini Wuriwa
No. 4 Unguwar Wuriwa Hadejia
Jigawa

Ksp Nasari Ksp Nasari
Malam-Maduri
Jigawa

Najib Aujara Najib Aujara
Aujara, Aujara
Jigawa

It's thë Rëãl Amînü Müñîr Rîñgm It's thë Rëãl Amînü Müñîr Rîñgm
Ringim Ktt
Jigawa

The firstly i have the name by Aminu Munir but some people call me with A Muneer and I'm living in Ringim local government

Kairulla Muhammad kazaure Kairulla Muhammad kazaure
1234
Jigawa, KAZAURE

Kairulla Muhammad

Triumph praise Triumph praise
JIGAWA
Jigawa

Umar Muhammad Umar Muhammad
Maigatari
Jigawa

Makomar gobanmu Makomar gobanmu
Kanya Babba Babura Local Government
Jigawa, KANYABABBA

Yahaya Ali Usman Yahaya Ali Usman
Y D
Jigawa