Ehp Yazid Ahmed

Ehp Yazid Ahmed

Serving Humanity

12/11/2023
18/06/2023

YANZU-YANZU: Shugaban kasa Bola Tinubu ya bawa sakataren Gwamnati umurnin ya ruguje dukkannin daraktotin hukumomin Gwamnatin Tarayya baki daya, domin su nada sabbi.

Hukumomin sun da NCC, FIRS, NITDA, NIMS, CBN, NNPC, NBS, NPA, NIMS da sauran manyan hukumomin Tarayya baki daya.

Photos from Ehp Yazid Ahmed's post 14/06/2023

BINCIKE YA BIYO TA KAN EFCC

Maigirma Shugaban Nigeria Tinubu ya dakatar da Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Nigeria (EFCC) Abdulrashid Bawa
An kuma nada Muhammad Umar Abba a matsayin shugaban riko

Allah Ya kyauta

09/05/2023

KADA KA ZAMA KAMAR MACIJI DA BAKIN SA BAYA FITAR DA ALHERI GA MUTANE.
Min shiga wani zamani da wasu mutane sika maida kafafan sada zumunta k**ar filin yaki sun maida su wurin habaici cin mutunci da walakanta mutane da domin Neman suna da burge iyayin gidan su , kuma hakan kuskure ne , babu daraja kuma ba kima ace sai kaci mutunci wani zakaji dadi kuma yin hakan walakanta Kaine da tozarta kyakyawar tarbiyya gidan da kafito domin na tabbata babu wani Uba da yake koyawa yayansa cin mutuncin wasu da kuma walakantawa. Sannan kuma ya k**ata mu rika tunawa duk abun da muka rubuta mu rike fijja akai domin zami bayani akansa a ranar jumuar da bata da asabar . Allah ya karemu yasa kar soyyayar wasu ta kaimu ga halaka
A wannan gabar nake Jan hankali matasa damu tashi mu koyi Sana'a domin itace kimarmu da mutunci .
Allah yasa mudace .

17/04/2023

A karshe dai hukumar bayar da lamuni ta Duniya IMF ta kaddamar da COIN dinta mai suna Unicoin Wanda take fatan zai kasance kishiya ga BTC ta fuskancin tsaro da decentralization Wanda Kuma zai kasance kudin da zata dinga bayarwa aro ga kasashe domin saukaka HARAJI da kudin ruwa da sauran wahalhalun da tsabar TAKARDU na DALA suke kawowa | Gonar Bitcoin

09/04/2023

Kada a manta da wanannan adduar ya ubangiji Allah ka dawo mana da zama lafiya mai dorewa a kasar nan
~Ehp

Send a message to learn more

09/04/2023

Barka da shan ruwa , Allah ya karbi ibadinmu.

09/04/2023

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah
Allah ka karawa rayuwarmu Albarka kaji kanmu ka tsaremu daga sharri ma sharranta
~Ehp

09/04/2023

Akwai wata rana da Allah Zai tara
yan aljanna ayi wata gagarumar
walima sai Allah Ya tara Annabawa
gaba dayansu sai yace za ayi
karatu. Wanda za a fara tasa shine kakan
Annabi Muhammad (S A w) Annabi
Ibrahim (AS) ya fara karatu
daganan sai a baiwa Annabi isah
(AS)ana nan har akai ga Annabi
dawud (AS) daga nan sai Allah yace kuna son ku ji muryar da tafi
wannan dadi? Sai muce eh sai a ba Annabi
Muhammad (sallallahu alaihi
wasallam ) idan ya fara karatu sai
mu manta da duk na sauran
Annabawa. Daga nan sai Allah Ya ce kuna son
ku ji wanda ya fi wannan? Sai muce eh sai Allah Ya ce to Ni
Zan yi da Kaina sai Allah Ya fara. An ce Surat da Zai karanta ita ce
Suratul Ar-Rahman. Bayan Ya gama sai Ya ce to Zan
gwada muku abinda Annabi musa
(AS) ya so a janye yau Zan janye
muku shi sai mu ce to menene Ya
Ubangiji? Sai Ya ce wani hijabi ne wanda ba
wani wanda ya ganshi.
Sai mu ce to menene? Sai Ya ce yarda Ta mana. A nan ne Allah Zai bayyana KanSa
kowa ya ganShi. Allah Ka yi mana hanyar shiga.

Photos from Ehp Yazid Ahmed's post 28/03/2023

RAYUWA KENAN

Wannan baiwar Allah marainiya ce, iyayenta duk basa raye, mijinta ya gujeta ya bar mata yara

An koreta daga gidan haya saboda ba kudin da zata biya, shine take buga bulo na laka domin ta gina matsugunin da zata zauna ita da yaranta a filin da ta gada a gurin mahaifinta

Tana zama a hayin Rigasa a garin Kaduna, wanda yake son ya je ya ga halin da matar take ciki musamman mazauna Kaduna ya kira wadannan layukan waya
O7084113798
07037128035

Wanda zai taimaka da kudi ga account number:
1638117283
Access Bank
Khanasar Abubakar Abdullahi

Wannan hotunan an dauka ne a yau Litinin, kuma da azumi a bakin matar take aikin buga bulo domin ta gina daki

'Yan uwa Musulmi mu taimaki rayuwar wannan baiwar Allah da abinda ya sauwaka albarkacin watan Ramadan mai tarin falala

Muna rokon Allah Ya rufa mana asirin duniya da na lahira

18/03/2023

AL-HASSAN BN ALIYU
Mahaifiyar sa itace Fadimatu 'yar Annabi [SAW]. Yayi k**a da Annabi [SAW].
Haka kuma shi da dan uwansa Hussain Annabi [SAW] yafiso cikin jikokin sa.
An ruwaito daga Usamatu dan Zaid yace: Annabi [SAW] yana cewa,
"Alhassan da Hussain jikoki nane ya Ubangiji ni ina sonsu, kaima kaso su, kaso dukkan mai sonsu".
Alhassan ya kasance kyakkyawa ne kuma mai kyawun hali.
Yayi kyakkyawar rayuwa yana tare da Annabi [SAW] har yayi wafati, bayan wafati ya kasance tare da khalifofi.
Yana cikin wadanda s**a kawo dauki domin kare Khalifa Usman lokacin da makiya suke kokarin kashe shi.
Haka kuma ya kasance tare da Baban sa a matsayin mashawarci.
Anyi masa mubayi'a a matsayin Sarkin Muminai, amma bayan kankanin lokaci sai ya kirawo Mu'awiyya Bn Abu sufyan yabashi jagorancin musulmi.
Wannan kuwa gaskata fadin Annabi [SAW] ne da yake cewa
"Lalle wannan jika nawa shugaba ne kuma ina fatan ta dalilin sa Allah zai sulhunta wasu bangarorin musulmai masu girma".
Allah ka kara masa yarda.

13/03/2023

Idan kaji labarin rayuwar wasu sai ka zidda hawaye saboda tausayi
Ya Allah wadda aka cucesu ka karba musu hakkin su

13/03/2023

Ya Allah ka ciremana kunci da talauci da damuwa ka iya mana cikin nemanmu, ka tsare Imaninmu da Mutuncinmu

10/03/2023

NASIHA
Kar ka sake Kayi rigima da Wanda zai halarci jana'izar ka bayan ka rasu, akan Wanda ba zai San ma ka rasu ba.

01/03/2023

Koma waye yaci zabe Idan baka da Sanaa babu wani chanji da zaka gani
Matasa ku tashi ku nemi Sanaa shine mafita

Photos from Ehp Yazid Ahmed's post 28/02/2023

Nifa gaskiya yanzu bana goyon bayan dokar da ta bawa kowa damar yin zabe

Ya k**ata ayi mata kwaskwarima a kalla a samar da wani tsari na a kalla ace sai mutum yana da wani qualification both karatun addini ko na boko ko wani experience kafin mutum ya chanchanchi kada kuri'a

Saboda har ga Allah wasu kauyawan da wasu jahilan su ne suke dawo da kasar mu baya
Ta yaya me hankali zai karbi ledar taliya yayi zabe?

24/02/2023

Bamu da k**ar ka duniya da lahira Fiyayyen Hallita Muhammad Rasulillahi
Allah kasa mu gama da duniya lafiya

24/02/2023

Duk wadda Ya baku kudi ranar zabe ku Karba amma ku zabi nagartattun mutanan da s**a chanchanta
~Ehp

23/02/2023

Bawa {mutum} ba ze
suturta bawa ba har sai Allah ya suturtashi a
ranar lahira”

23/02/2023

NASIHA✅| Duk yawan zunubin ka, kada kayi kokonton komawa Neman afuwar Allah madaukakin sarki, don kuwa shi ya rufa maka asiri lokacin da kake saba masa, to kaga kuwa ba zai kunyata ka ba yayin da ka koma gareshi da nufin tuba. Dafatan Kun wayi gari lafiya.

21/02/2023

An karbo daga Abdullahi dan Umar (rta) yace,
Manzon Allah (saww) ya dafa kafadata yace; ka
kasance a duniya tamkar kai bako ne ko kuma
wanda yake kan hanya dan Umar (rta) yana
cewa; idan kai kai yamma kar kayi jiran safiya
idan kuma wayi gari to kar ka jira yamma, ka riki
aiki alheri lokacin rayuwarka, saboda lokacin
rashin lafiyarka, ka riki aiki alheri lokacin
rayuwarka, saboda ka amfana lokacin
mutuwarka, (Bukhari ne ya rawaitoshi a hadisi
mai lamba 6416).
ABIN NUFI;
Abin Nufi da ka zama Bako, duk yanda bako yaje
wani gari komai dadewar sa dolene sai Ya bar
garin Ya koma garinsu, abin nufi anan komai
dadewar ka a duniya dole ne ka koma gidab
gaskiya wato Lahira.
Abin Nufi da Idan ka wayi Safiya kar ka jira kace
sai An juna zan yi aikin Lada kaza, ko kace ai
jiya na sabawa Allah (swt), amma ba zan rokeshi
gafara yanzu ba sai An jima ko sai gobe, sam
karkayi haka kayi amfani da lokacinka.
Abin Nufi da kayi Amfani da ka rika aikin Alheri
lokacin Lafiyar ka saboda Duk aikin Ladar da
kake yi lokacin da kana da Lafiya to, ko ka
kwanta baka da lafiya za'a rubuta ma ladar
yinsa.
Abin Nufi da ka Rika aikin Alkheri lokacin
Rayuwarka Shine, idan ka Mutu lada zata rika
jema ko a makwancinka.
Yaa Allah Kasa mu dace duniya da Lahira.

21/02/2023

https://vrlps.co/u2ktqj0/cp
CryptoGPT layer 2 blockchain project ne da aka kirkireshi musamman domin Artificial Intelligence (AI), a yanzu sun bada damar yin rijista dasu domin samun airdrop idan sunyi launching coin dinsu $GPT. Abubuwan da akeso mutum yayi sune 👇

1. Yayi rijista
2. Ya tabbatar ya shiga telegram group dinsu
3. Ya tabbatar yayi following dinsu a twitter.
4. DOLENE yayi referring mutane akalla bakwai (7).

Nan gaba kadan zasu saki application dinsu, sannan a karshen shekarar 2023 akesa ran zasu saki mainnet dinsu, k**ar yanda yake a road map dinsu. Ga link nan a kasa/sama kuyi rijista dasu, sannan ku tabbatar kun chika ka'idojinsu.
https://vrlps.co/u2ktqj0/cp

21/02/2023

Zaɓaɓɓe Daga Zaɓaɓɓu,
Mai Girma Ɗan Masu Girma, Mai Daraja Ɗan Masu Daraja, Shugaba "Muhammadu" Rasulillah ( ﷺ).. * 🥀 💔

21/02/2023

Lallai duk wadda Allah ya shiryar shine shiryayye , wadda kuma Allah ya batar dashi babu Mai iya shiryar dashi. Alhamdulillah

20/02/2023

Yara manya gobe a kyautata musu kada a koya musu abin daba daidai ba
~Ehp

20/02/2023

Yawaita murmushi Yana kawo zaman lafiya da ƙaunar juna a cikin Al'umma, Dafatan Kun wayi gari lafiya.

17/02/2023

" Jahilci ba uzuri ba ne a wurin Ubangaji
don haka dole mutum ya tashi tsaye wajen
neman ilimin sanin addininsa"

02/02/2023

1.Annabi S.A.W. yace: "Wanda ya karanta
Qulhuwallahu
Ahad sau 10 a jere, Allah zai Gina masa
katafaren
gida
achikin Aljanna". [SahihulJami'i. 6348]
2. Manzon Allah S.A.W. yace: "Wanda yakaranta
Ayatul
Khursiyyu bayan kowace Sallah ta farilla, babu
abunda
zai hanashi shiga aljanna sai mutuwa. [Sahihul
Jami'i]
3. Manzon Allah S.A.W. yache: "Idan mutum
yazo
kwanchiya bacci a kan shimfidarsa to ya karanta
Qulya
ayyuhal kafirun, Idan mutum ya mutu acikin
daren
bazai mutu mushiriki ba" [Sahihul Jami'i]
4. Manzon Allah S.A.W. Yace: "Wanda yakaranta
suratul khahfi ranar juma'a Allah zai haskaka
masa da
haske harzuwa wata juma'ar yana cikin farin ciki
yana
chikin jindadi" [Sahihul jami'i]
5. Manzon Allah S.A.W. yace: "Wanda
yahaddace
ayoyi
goma na farkon suratul khahfi,Allah zai tsareshi
daga
fitinar dujal"!!!Allah kabamu iko

12/01/2023

CBN GOVERNOR
Kazaure
Reveal something Important

12/01/2023

Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace:
"Ban ta'ba ganin wani abu mai kyawu
k**ar Manzon Allah (saww) ba. Sai kace
rana ce take gudana akan fuskarsa.
Kuma ban ta'ba ganin wani mai Sauri wajen
tafiya k**ar Manzon Allah (saww) ba. (idan
yana tafiya) Sai kace na'de masa Qasar akeyi.
"Mun kasance muna wahalar da kanmu
(wajen binsa aguje) alhali shi kuwa ba ma
sauri yakeyi ba".
HADISI NE SAHIHI ADUBA :
- Sahihu Ibn Hibban hadisi na 6309.
- Sunanut Tirmidhiy Hadisi na 3648.
- Musnadu Ahmad Hadisi na 8588.
:- Wannan wani bangare ne
daga Jarumtakar Manzon Allah (saww)
domin shi ba mai sakin jikinsa bane k**ar
yadda Shugabannin duniya sukeyi.
Shi mai Qarfin jiki ne, Mai kyawu ne kuma ga
kwarjini ga Jarumtaka iron wacce babu
irinta.
Ya Allah ka Qara salati da girma da aminci da
albarka gareshi da iyalan gidansa da
Sahabbansa da masu Qaunarsa da dukkan
mabiyansa har zuwa ranar taruwa.

Photos from Ehp Yazid Ahmed's post 09/01/2023

JARRABAWAR RAYUWA

Wata baiwar Allah a jihar Katsina ta jefar da jaririn da ta haifa bayan masu garkuwa da mutane sun k**ata sun kashe iyayenta da kowa nata, ita kuma s**a mata ciki ta hanyar fyade

Bayan ta jefar da jaririn, ta rubuta wasika ta ajiye, ga abinda ta rubuta:
Assalamu Alaikum
'Yan uwana Musulmai, ga kaddara nan ta sameni wadda zata iya samun kowace irin mace
Ga dan nan (jariri) banda wanda zai iya rikeni da shi, na barshi ba don ban sonshi ba
Fyade ne barayi s**a min, sun kashe mini kowa
Twa zai rike wannan? Shiyasa ma har na yanke wannan (shawaran jefar da jaririn) dan ban oya kashe shi, idan kungaa laifi na to ku yafeni
Ina rokon Allah Ya sa ya fada hannun nagari
Na haife karfe 3 na daren Litinin (Yau 9-1-2023)

Idan da gaske ne abinda ya faru da ita ta hanyar barayi da s**a mata fyade, to ina ganin bai dace ta jefar da jaririn ba, na tabbata ko gurin limamin garinsu ta je zai Jagoranci isar da ita zuwa ga Gwamnati, kuma zata samu tallafi ko da a gurin jama'ar Musulmi ne

Wannan k**ar misalin 'yan matan Chibok ne wadanda Boko Haram s**a k**asu s**a auresu s**a haifa musu 'ya'ya, wasu sun dawo da yara uku da s**a haifa, duka 'ya'yan fyade ne, kuma sun samu tallafi daga Gwamnati

Sai dai watakila ita wannan baiwar Allah tsoron kallon da mutanen mu zasu mata shiyasa taki bayyana kanta, saboda mutanen mu akwai wuyar sha'ani

Muna fatan Allah Ya karemu daga mummunan kaddara

31/12/2022

Bankwana da 2022
Alhamdulillah, Alhamdulillah Alhamdulillah
Na roki Allah abubuwa da yawa a shekarar 2022 ya bani , ya kuma bani abubuwa da yawa wadda ban rokaba cikin ikonsa da yardar sa , Tabbas Allah shine abin godiya gagara misali bisa wadan nan nasarori.
Alhamdulillah Tabbas na cimma nasarori masu tarin yawa cikin ikon Allah da yardar sa a cikin shekarar 2022 mai Albarka.
Ina kuma sake rokon Allah a shekarar 2023 munga arzikin da wadatar da ban taba gani ko tsammani ba a cikin wannan shekarar.
31st_Dec_2022
ALHAMDULILLAH

Photos from Ehp Yazid Ahmed's post 29/12/2022

PI NETWORK

A kalla kasuwannin Crypto wato Exchangers kusan guda 10 s**ayi listing Pi Network tare da farashinsu, akwai wanda farashin Pi guda daya yake a Dalar Amurka 50, kimanin Naira dubu 35

Abinda ya bawa kowa mamaki, saboda ana Pi closed mainnet ne, wata ana lokacin da Pi Core Team basu bada dama ayi kowace irin mu'amala da Pi ba

Amma bamu sani ba ko akwai wata tattaunawa da yarjejeniya da Pi Core Team s**ayi da wadannan exchangers din, na tabbata Pi Core Team zasuyi jawabi nan da kowani lokaci akan wannan sabon al'amari

Na ga wadanda s**a jima basa mining Pi duk sun dawo bayan sun ji labari Exchangers sunyi listing Pi

Mun ce muku kuyi mining kun daukemu bamu san abinda mukeyi ba, har kuna zagin mu tare da yi mana habaici, tukunna ma kuka gani, sai an je Pi Open Mainnet, Pi Chainmall sunfara International transaction, Pioneers suna sayen kaya daga Kasar China ana aiko musu gida

Mu kam ba abinda zamu ce game da Pi Network wanda ya wuce ALHAMDULILLAH 🙏

28/12/2022

" Alamar da ake gane mutum mai rauni shi
ne wanda a kullum yake fifita son ransa,
sai kuma mutum mai hankali wanda a
kullum yake danne son ransa yayin da
mutum mai ilimi a kodayaushe yana cikin
gwagwarmayar da son ransa ne"
- Iman Hamza Yusuf

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Jigawa?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Category

Website

Address

Jigawa