Isah Lawan Jhn

Isah Lawan Jhn

I am a physicist

31/03/2024

1. Ki gargadi 'yar ki kada ta kuskura ta
zauna a cinyar wani, koda kanin babanta ne
ko Almajirin gidansu.
2. Kada ki dinga canja kaya a gaban
'ya'yanki wadanda s**a kai k**ar shekara
biyu. Ki dinga cewa su fita.
3. Kada ki yarda wani babban mutum ya
dinga kiran 'yar ki da "Mata ta" ko
"Amarya ta" dds.
4. Idan 'ya'yanki suna wasa da wasu yaran,
ki dinga lura wane irin wasa sukeyi. Saboda
wasu yaran suna wasa da al'aurar junansu.
5. Kada ki matsawa 'yar ki zuwa wajen
wanda ba ta so ta je wajensa. Kamar
wani me siyar da kayayyaki ko
mak**ancinsu.
6. Ki saka lura sosai idan kika ga dan ki ko
'yar ki sun shaqu da wani mutum a waje
kuma suna son zuwa wajensa.
7. Kada ki bari dan ki ko 'yarki su dinga
yawo ba riga ko wando a cikin gida b***e su
fita waje.
8. Idan kin yiwa 'yar ki kwalliya, to ki gaya
mata iya gidajen da za ta shiga.
Kuma daga nan ta dawo gida. Kada ta zauna
a rariya ko shige-shigen gidaje.
9. Idan ki ka ji an yiwa abokin dan ki ko
kawar 'yarki wani abu mara dadi, to kema ki
binciki na ki sosai. Ki tuhume shi.
10. Idan 'ya'yanki mata sun fara girma, ki
koya musu yadda ake kula da jini. Da yadda
ake kula da budurci da hadarin kawar da
shi. In ba haka ba zata fara koyar munanan
dabi'u a wajen kawaye.
11. Ki kula da irin kayan wasan da yaranki
suke amfani da su. Kamar yartsana me
hoton tsiraici da mak**antansu.
12. Ki koyawa 'yar ki me shekara uku yadda
ake wanke muhimman gurare ajiki, har da
kirji kuma ki gaya mata kada ta bari kowa ya
ta6a mata nan wajen da nan wajen.
13. Ki tabbatar duk wani hoto ko abin
amfani wanda zai 6ata tarbiyyar yaro kin
nisanta shi da inda yaranki za su gani.
14. Duk sanda 'yarki ko danki ya kawo miki
karar wani babba ya cire masa
kaza ko ya ta6a masa kaza, to kada ki dau
mastalar da wasa.
A bi duk matakan da s**a dace don
tabbatar da
abinda ya faru.
15. Ku tuna Tarbiyyah tana farawa ne daga
gida

*Pls kutura zuwa wani group din don sauran iyaye mata su ankarar da iyalansu* 👏🏼👏🏼👏🏼

11/08/2022

BSC. PHYSICS; ilimin Kimiyyar Ƙwayoyin Halitta Da Mak**ashi..

'Arewa Students Orientation Forum'

Physics Duniyar Science..

Babu ko Tantama kan Zamowar ilimin Physics Uba ga duniyar Science Dan haka nema Ɗaliban BSC. PHYSIC Kan zamowa na musamman kuma zaƙaƙurai a fannonin Kimiyya , Bsc. Physics maɓuɓɓuga ne ga dukkan Wani Nau'in Ƙere-ƙere a duniya Da Samar da ababen rayuwa na zamani shekaru aru-aru.

Bsc. Physics Kimiyyar ƙwayoyin halitta da mak**ashi da kuma mu'amalar da ke tsakanin su biyun, an rarrabe zuwa traditional Field (fannonin Physics na gargajiya) k**ar su acoustics, optics, mechanic, thermodynamics, da electromagnetism, haka nan kuma akwai ɓangaren modern Physics (na zamani) da s**a haɗa da atomic da nukiliya physics, da cryogenics, solid-state physics, particle physics, da kuma plasma physics dasauransu.

Kimiyyar Physics kimiyya ce da ke da alaƙa da Properties, canje-canje, hulɗa, da dai sauransu na Ƙwayoyin halitta da mak**ashi wanda ake ɗaukar mak**ashi a matsayin ci gaba (classical physics), ciki har da wutar lantarki, zafi, na'urorin gani, makanikai, da dai sauransu, kuma yana hulɗa da ma'aunin atomic na yanayi wanda a cikinsa ake ɗaukar mak**ashi a matsayin mai discrete (Ƙwayoyin kimiyyar lissafi), gami da irin waɗannan rassa k**ar su atomic, nuclear, da sulfur-state physics ka iya zamowa Gagara badau da sai dai ace mutum yayi iyakar iyawar sa.

a fannonin da s**a haɗa da injiniyoyi, acoustics, optics, zafi, wutar lantarki, magnetism, radiation, da kimiyyar atomic da nukiliya Physics shine kimiyyar yadda abubuwa ke aiki da wanzuwa a duniya da tsarawa da sarrafa yadda za'a ci moriya da ƙirƙire-ƙirƙiren zamani dana da can baya

Bsc. Physics shine kimiyyar daɓi'a da ke nazarin ƙwayoyin halitta, ainihin abubuwan da ke tattare da su, motsinsu da halayensu da sararin samaniya da lokaci, da abubuwan da s**a danganci mak**ashi da kuzarin Motsawa, Physics yana ɗaya daga cikin mafi mahimmancin ilimin kimiyya, tare da babban burinsa shine fahimtar yadda duniyar Kaunu ke wanzuwa.

Ga Jerin Wasu Daga Cikin Courses Ɗin da'akeyi a Physics:

1st Semester Level One:

Mechanics

Electricity And Magnesium

Physic Practical 1

Elementary Mathematics ¡

Elementary Mathematics ¡¡

Introduction to Computer science

Organic chemistry

2nd
Behaviour Of Matter

Physic Practical 1

Probability 1

Elementary Mathematics 3

Physical Chemistry

Practical Chemistry

200 level 1st

Renewable Energy

Physic Practical

Electric Circuits and Electronics

Elementary Modern Physic

Mathematical Method

2nd

Electronic Practical

Waves and optics

Thermal Physic

Elementary Differential Equation

Probability 3

300 level 1st

Vector And tensors

Solid State Physics

Energy and Environment

Physics and Electronic laboratory

Complex analysis

Analytical Mechanic 1

Quantum Physics

Electricity And Magnetism

Design Studies

Introduction to acoustics

Introduction to geophysics

Semiconductor device

Electronic circuits

Siwes

Level 400:

Quantum Mechanics 1

Mathematical Methods in Physics1

Computational Physics

Statistical and thermal Physics

Electromagnetic Waves

Analytical Mechanic 2
Dss.

(a Lura cewa Courses suna iya sauyawa Daga Makaranta zuwa makaranta, kuma wannan mun tsakuro kaɗan ne)

Wasu Kaɗan Daga cikin Branch Na Physics:

Classical Physics

Modern Physics

Nuclear Physics

Atomic Physics

Geophysics

Biophysics

Mechanics

Acoustics

Optics

Thermodynamics

Astrophysics

Wasu Kaɗan Daga cikin Ɓangarorin Da za'a iya cigaba da karatu bayan Bsc. Physics

MBA in Data Science
MBA in Information Technology

MSc in Materials Science and Engineering
M. Sc Vacuum Sciences
M. Sc Acoustics
MSc in Applied Physics
MSc in Physics
M. Sc Applied Electronics
MSc in Atmospheric Science
MSc in Nanotechnology
MSc in Astronomy/Planetary Science/Astrophysics
MSc in Aeronautics
Master in Atomic and Molecular Physics
MSc in Particle/Nuclear Physics
MSc in Geophysics
MSc in Molecular Physics
MSc in Optical Physics
MSc in Medical Physics
MSc in Biophysics

Wasu Daga cikin Short-term Courses/ Training Bayan BSc Physics:

PG Diploma in Data Science
PG Diploma in Astronomy
PG Diploma in Nanotechnology
Diploma in Medical Lab Technology
PG Diploma in Community Health Nursing
Certificate in Lab Assistant/Technician
Diploma in Operation Theatre Technology (OTT)
PG Diploma in Machine Learning/Artificial Intelligence.

•Shin BSc Physics Yanada tasiri a wannan zamanin?

A wannan zamanin, ana amfani da Physics a kowane fanni na rayuwa, Bayan kammala wannan kwas, ɗalibai suna da damar aiki daban-daban ga kaɗan Daga Ciki:

Petroleum and gas

Science

Engineering

Business and finance

Technology

Construction

Physicist

Physics Lecture

Lab Assistant

Research Associate

Subject Matter Expert

Technician

Radiologist Assistant

Quality control manager

Research associate

Statistician

technician

academic counselor

Dss.

©ASOF-2022
Whatsapp 08086251045

Photos from Kaduna Post's post 02/08/2022
Photos from Dokin Karfe TV's post 01/08/2022
31/07/2022

MAZA GA SAKO MAI KARFI!

MATSALAR DA MATA KE FUSKANTA.

'Mafi yawan samarin yanzu duk mutanen banza sunfi yawa a cikinsu, burinsu kawai su taɓa yarinya ko su ƙwanta da ita, ko tanaso ko bataso ta hanyar shirya mata muguwar yaudara da sunan zasu aureta, ko wasu dabaru Idan taƙi yarda sai su rabu da ita, dama iskanci ya kawosu ba aure ba.

Karki yarda ya taɓaki, b***e har ya samu damar ƙwantawa dake, zina bala'i ce masifa ce, tsiya ce.

Ki bari yayi fushi ɗin ya tafi gwanda ya barki da mutuncinki, karki bari ya taɓa miki mutunci karki yarda sai an shafa fatiha kin tabbatar an kammala komai koda kuwa ya kawo lefe kuma ya bada sadaki, wannan ba aure bane sai an ɗaura, to kome yakeso kiyi masa karki kuskura ki bari ya latsaki keba dabba bace, dabbace kaɗai ake latsawa kafin a siya ko a ƙwanta da ita babu aure, idan kika yarda kin zama dabba, koda kuwa zai aure kine, da gaske, karki kuskura ki yarda.

Idan kuna ko ƙwanto, ku sami ƴan mata ku tambayesu zakuji da iskanci yanzu samari suke zuwa gurinsu, shine babban ƙalubalen da suke fuskanta, zai wahala kaga yarinyar da wani baije mata da maganar iskanci ba, abin da ciwo babu daɗi ƙwata-ƙwata.

Wallahi muji tsoron Allah, muma zamu haihu koda ace babu kamun ubangiji.
Allah ya shirya mu, baki ɗayan mu, ya rabamu dason zuciya da shiriritar banza da wofi.'

Imam Anas.

19/07/2022

HOW MATHEMATICIANS WRITE A LOVE LETTER

Dear Someone,

Yesterday, I was passing by your rectangular house in trigonometric lane. There I saw you with your cute circular face, conical nose and spherical eyes, standing in your triangular garden. Before seeing you, my heart was a null set, but when a vector of magnitude from your eyes at a deviation of theta radians made a tangent to my heart, it differentiated. My love for you is a quadratic equation with real roots, which only you can solve by making good binary relation with me.

The cosine of my love for you extends to infinity. I promise that I should not resolve you into partial functions but if I do so, you can integrate me by applying the limits from zero to infinity. You are as essential to me as an element to a set. The geometry of my life revolves around your acute personality.

My love, if you do not meet me at parabola restaurant on date 10 at sunset, when the sun is
making an angle of 160 degrees, my heart would be like a solved polynomial of degree 10. With love from your higher order derivatives of maxima and minima, of an unknown function.

Yours Truly,
Me as:PYTHAGORAS

01/07/2022

RAYUWA A TERTIARY INSTITUTION...
Shirin Ƙungiyar 'Arewa Students Orientation Forum'

Acikin Shirin Na Wannan Mako Abdulhakim Mustapha yabayyana Yanda Yayi JAMB So Uku Amma Sai a ta Ukun yasamu damar zuwa jami’a amma fa tsawon shekara ukun Ba'a zaman kashe wando Yayi su ba yagama NCE...

: KAI TSAYE ZAMU FARA DA GABATARWA!

Mustapha: Sunana abdulhakim mustapha malumfashin jahar katsina, Dalibi a
Makarantar isa kaita College of Education

ASOF: ATAQAICE MENENE TARIHIN KARATUN KA?

: Na yi primary school a heritage dake malumfashi, Lokacin da nakai primary 4 sai aka maidani Sallau model primary school aka Dawo dani Primary 2
Inda har nagama a 2009, natafi Great Ambassador international college Malumfashi

: WANNE KALUBALE KAFARA FUSKANTA A SIKANDIRE?

:
Rashin iya turanci, Makarantar basa Hausa
Sak**akon haka duk abinda s**ayi banaganewa sai kadan daga ciki
Hakan yasa lokacinda zamuje jss2 akaimin Repeat

: DA WANNE BURI KASHIGA SIKANDIRE?

: Lokacin da naje Ss1 nayi burin zama Masanin Bangaren Noma Wato "Agricultural Science" Amma lokacin damuka fara karatun ss1 sai na fahimci wulakanta mata musamman musulmai da a keyi Yayi yawa sai na dau alkawarin zama lauya.
Daganan na maida hankali Akan Duk Abunda yashafi bangaren lawyer

: KANASO KACE MATA NA FUSKANTAR TSANGWAMA TA FUSKAR ILIMI KENAN?

: eh Yadda naga ana hana mata sanya hijabi a makarantar mu kuma gasu musulmai

: MEYA CHANJA RA’AYINKA NA ZAMA LAWYER?

: Lokacin da naje ss2 zamuje excursion donganin yadda aikin shari’a yake gudana asannan ne mahaifina yasancewa ba bangaren Science nake karanta ba sai ya Mayar dani Science

: ME YAJA HANKALIN KA DAFARKO KAKESON AGRICULTURE?

: Yadda naga mahaifina yana noma ya saida asamu kudi dayawa, na fahimci cewa noma yana kawo kudi sosai

: REPEAT DIN DA'AKAYI MAKA SO BIYU BE KASHE MAKA KWARIN GWIWA BA?

: Gsky da farko ba abinda naji amma na biy

26/06/2022

🚨 Real Madrid’s expected lineup for next season according to

Irin Mafarkin Da Zaki Gane Aljanu Suna Tare Dake Ko Sun Aureki 21/06/2022

Irin Mafarkin Da Zaki Gane Aljanu Suna Tare Dake Ko Sun Aureki Irin Mafarkin Da Zaki Gane Aljanu Suna Tare Dake Ko Sun Aureki

18/06/2022

YAR JAMI'A
Tun daga lokacin da kika fara sha'awar wucewa makarantar gaba da secondary zaki yita kokarin ganin kin shawo Kan mahaifan ki domin subar ki, ki wuce karatu.

Bayan an yita dauki ba dadi daga karshe sun barki ki rubuta jamb(UTME), kin Kuma samu gurbin karatu a jami'a, ko college of education, ko polytechnic, ko college of Health science dai dai sauran su zaki Karan ci abun da ranki keso ko abunda aka baki shawara.

Kafin ki tafi mahaifin ki ya kiraki ya yimaki nasihar daki tsare mutun cin kanki karki bashi kunya, ki tsaya kiyi abunda yakai ki, haka mahaifiyar ki itama ta baki shawara irinta 'ya da uwa akan ki tsare mutuncin ki.
Mutanen unguwa kowa na fadin albarkacin bakin shi da masu fadin alkhairi dama masu fadin akasin haka, Yan'uwanki na murnar yar'uwarsu tasami damar da zata taimaki al'ummarta, kawayenki na maki fatan alkhairi da tayaki murna cewa zaki wuce karatu, a haka za'azo duk abunda k**e so shi za'a siya a hada maki kitafi makaranta, inda ba uwa, ba uba, ba yaya, ba unty, ba uncle, ba malamin islamiyar ku, ba Wanda zaice maki yi ko bari.

Da shigarki kika aje akwatin ki, to kinada zabi guda biyu kodai kiyi amfani da hudubar iyaye ki zabi kawayen kirki kiyi abunda ya kawo ki, ki tsare mutuncin ki Dana iyayen ki dasuna can gida al'ummah na masu kallon yahudawa saboda sun kawo ki karatun da zaki taimaki al'ummah dashi, ki fuskanci kalubale daga Yan iska Bata gari daga cikin dalibai mata da maza da wasu gurba tattun malamai, Wanda Allah zai kareki daga sharrin su.

Ko Kuma ki dauki hanyar ganin cewa ke yanzu kin waye ki zabi kawayen banza kina ganin cewa yanzu ke kinsan 'yancin kanki, ki manta da amanar da kika dauko wa iyayen ki cewar zaki kare mutuncin ki, ki fara shaye shaye, Da bin maza, karfe shidda na yamma wani kato yazo yadau keki kije ki kwana dakin shi, sai shidda na safe ya maidoki, iyayen ki na ganin kina can kina karatu Amma Basu san kina can kina kwana dakin wani kato ba, ku Kuma kisamu kawaye ku kwana Kuna le***an Kuna sabama Allah, mala'ikun rahamah su kwana suna tsine maku albarka, shikenan rayuwa ta lalace karatun yagagara sannan aure ma yazo yagagara mahaifin ki yace kibar mashi gidanshi daga karshe sai karuwan ci.

Allah Ya tsare
Daga karshe 'yar uwa karatu yanada mahimman ci Amma kisani mutuncin shine farko nagode
(If you educate a man you educate an individual, but if you educate a woman you educate a nation.)

Rubutawa:
Saifullahi Usman
Asof Katsina State coordinator.

18/06/2022

🔙 in 2019, Rodrygo Goes was presented as a Real Madrid player at the Bernabéu! 🇧🇷🤍

12/06/2022

TSAKURE CIKIN LITTAFIN JAMI'A RUNBUN ILIMI

Wanda Umar Kabir Dakata ya rubuta

Kashi na Uku

MAKARANTUN JAMI'A A NAJERIYA.
Tarihin ilimin jami'a a Najeriya ya samo asali ne daga Hukumar Elliot a shekarar 1943, wacce ta kai ga kafa Kwalejin Jami'ar Ibadan (UCI) a shekarar 1948. UCI reshe ne na Jami'ar London (Ibukun) ya kuma yi ikirarin cewar an samu matsaloli masu yawa a UCI tun daga lokacin da aka kafa jami'ar, k**a daga tsauraran matakan tsarin mulki, karancin ma'aikata, da kuma karancin masu yin rajista zuwa yawan masu neman karatun.
A watan Afrilun shekarar 1959, Gwamnatin Tarayya ta sanya kwamitin bincike (Hukumar Ashby) don ba ta shawara a kan manyan makarantun kasarnan, kwamitin ya gabatar da bukatar shekaru biyu na farko. Kafin gabatar da rahoton, gwamnatin yankin Gabas ta kafa tata jami'ar ta Nsukka (Jami'ar Najeriya, Nsukka a shekarar 1960). Aiwatar da rahoton Ashby ya haifar da kafa Jami'ar Ife (wacca a yanzu ake kiranta da Obafemi Awolowo University, Ile-Ife) a shekarar 1962 ta yankin Yammaci, Sai Kuma Jami'ar Ahmadu Bello, dake Zariya wacce aka kafa a shekarar 1962 gta yankin Arewa, da kuma Jami'ar Legas (1962) ta Gwamnatin Tarayya. Jami'ar Ibadan ta zama cikakkiyar jami'a a shekarar 1962, Wannan yana nufin cewar UCI, Ibadan da Jami'ar Legas sun zama farkon jami'o'in tarayya guda biyu a Najeriya - sauran ukun sun kasance na yanki. A cikin shekarar 1970, sabon yankin Midwest da aka kirkira ya zaɓi jami'ar da aka sani da Jami'ar Benin. Jami'o'i shida da aka kafa a wannan lokacin 1960-1970 har yanzu ana kiran su jami'o'in ƙarni na farko. Babalola yace sun lura da cewar a wannan lokacin, jami'o'i a Najeriya suna cikin kulawar gwamnati sosai. Nadin kananan membobin majalissar, da na Mataimakin Shugabanta, ya kasance suna da nasaba da siyasa.
A Tsarin bunkasa Kasa na Uku (1975 1980), gwamnati ta kafa jami’o’i bakwai maimakon guda hudu da aka gabatar a shirin, sannan kuma ta karbe jami’o’in yanki hudu a shekarar 1975. Su ne Jami’o’in Calabar, Ilorin, Jos, Sokoto, Maiduguri, Port Harcourt da Jami'ar Bayero, dake Kano - duk an san su da jami'o'i na ƙarni na biyu. An kafa jami'oi na ƙarni na uku tsakanin 1980 zuwa farkon 1990. Su ne: Jami'o'in Fasaha na Tarayya a Owerri, Makurdi, Yola, Akure da Bauchi. Yayin da aka samu jami’o’in jihohi a jihohin Imo, Ondo, Lagos, AkwaIbom, Oyo da Cross-River.
Jami'o'in ƙarni na huɗu sune waɗanda aka kafa tsakanin 1991. Wadanda s**a hadar da karin jami'o'in jihohi, jami'o'in bude Najeriya, da jami'o'i masu zaman kansu da yawa.

FA'IDODJIN DA AKE SAMU DANGANE DA KYAKYKYAWAN ILIMI A JAMI'A
Fa'idodin da ake samo daga kyakkyawan tsarin ilimin jami'a ba zai taɓa misaltuwa ba. Dukkannin kayan cigaban tsarin zamantakewar al'umma suna tattare da kyakkyawan ilimin jami'a. Gudummawar ilimin jami'a ga cigaba ya zo ta hanyoyi daban-daban. Da farko dai, yana taimakawa cigaba saurin masana'antu na tattalin arziki. Wannan yana yin ta ne ta hanyar samar da ƙwararrun ma'aikatan da sukeda ƙwarewar gudanarwa. A wata hanyar kuma, kyakkyawan ilimin jami'a yana taimakawa wajen bunkasa canjin al'ummomi zuwa al'ummomin ilimi. Wannan yana iyi taimakawa wajen samar da kwarrarrun ma'aikata masu ilimi ya kuma taimaka wajen samun ma'aikatan ilimi waɗanda zasu ba da gudunmawa matuka ga haɓakar tattalin arziki.
Bayan haka ingantaccen ilimin jami'a yana taimakawa wajen cusa kyawawan halaye da haifar da sauye-sauye na ɗabi'a waɗanda suke da muhimmanci ga zamantakewar mutane, yana haifar da zamanantar da cigaban al'umma baki ɗaya. Hakanan yana taimakawa, ta hanyar koyarwa da kuma taƙaitaccen bincike, a cikin ƙirƙirowa, ƙwarewa, yaɗawa da amfani da ilimi. A ƙarshe, ingantaccen ilimin jami'a yana taimakawa wajen kafa ƙasa mai ƙarfi kuma a lokaci guda yana taimakawa wajen dunkulewar duniya. Bugu da Kari yana bawa mutane damar more rayuwa mai haɓaka, Haka Zalika suna ba da babbar dama ga al'adu da siyasa.

Photos from Rariya Hausa's post 09/06/2022
02/06/2022

Camavinga playing with the children of Luka Modric. 😍

01/06/2022

Bale with his family. 🏴󠁧󠁢󠁷󠁬󠁳󠁿

31/05/2022

Karim Benzema and his son, Ibrahim 🤍🖤

28/05/2022

Tsarin Admission a JAMB CAPS...

1•Admission is Progress, CHECK back Later

2•Not Admitted

3•Admission is not given yet

Tun Bayan Da Hukumar JAMB tafara Bayar Da Admission Ga Wadanda S**ayi Jarrabawar JAMB Na Shekarar 2020 Dalibai Dayawa Sun Shiga Rudani Ganin Cewar Su Har Yanzu Hukumar Bata Kai ga Basu Admission ba; Shin Hakan Yana Nufin Cewa Sam-Sam Bazasu Samu Admission Bane?

Bahaka Bane Dukkan Dalibin dayayi JAMB a Shekarar Data gabata kuma yaci adadin Maki (Mark) din Da'ake Buqata a Makarantar Daya Nema, Kuma yabi Tsarin Makarantar Na Halartar POST-UTME Ko Online Screening/Registration to Dan Zuwa Yanzu yaga Hukumar JAMB Bata bashi admission ba Yasha Kurumin sa, Kamar Sabon Soja a, (Sambisa) Nan gaba Kadan Insha Allah Shima zaishiga jerin Wanda zasu ga anbasu Admission.

•°• ADMISSION IN PROGRESS;

Idan Admission Dinka Yana Nuna in progress check back later; Hakan Yana Nufin Cewa ka Samu Admission?

Eh Kwarai Dagaske! Wannan Wata Manuniya ce datake Nuna Makarantar da kake Nema ta aika Sunan ka Cikin jerin Sunayen da za'a Bawa admission, dan Haka Cikin Wasu ’Yan Kwanaki Dalibi zaiga yachanja Zuwa admission Daga in progress.

•°•NOT ADMITTED

Idan Admission Dinka Yana Nuna Not Admitted Shin me Hakan Yake Nufii? Hakan Yana Nufin Kawo Yanzu Hukumar Bata Baka admission ba tukunna amma Zata iya baka a Nan gaba

Meyak**ata Dalibi Yayi idan yaci gaba da Ganin NOT ADMITTED? Abu Guda Daya da Dalibi zeyi Shine ya Tabbatar Da Yayi Uploading Na SSCE results dinsa a JAMB Portal.

ASOF. Tana Fatan kowa Yasamu Admission dinsa Barkan Mu Da Shigowa watan Ramadan.


WHATSAPP
08086251045

25/05/2022

CIKAKKEN BAYANI AKAN JAMB-REGURLARIZATION

Arewa Student's Orientation Forum (ASOF)

Lokacin Da kaje/Kika Je, JAMB CBT CENTER Aka ambaci Regularzation Sai kuji Wani sabon Al'amarin Da Baku sanshi ba, Kokuma Baku Da Cikakken Bayani Akan sa.

--JAMB REGURLARIZATION; tsari ne Na samar Da Admission Ga Wanda Hukumar, JAMB Bata basu Admission ba, a Lokacin Das**a samu Admission Na Makarantar Su(Banda Na JAMB)

Eh Admission Na Makarantar su, Misali Jami'a, Kokuma NCE Ko Diploma.

---MEYASA HAKAN?

•Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba Da Sikandire (JAMB) a Dokar ilimi ta Kasa itace take Da Hurumin tantancewar Farko Sannan ta Baka admission Kafin Makarantar ka.

a Farko-Farkon Lamari Dalibai Sun kwana Da tsammanin Cewar Jami'a Ce Kadai Ake Shiga da JAMB kafin daga Bisani, s**a Fara Sanin Mafi Yawa Daga Cikin Makarantun gaba da Sikandire, Baza su baka admission ba, Sai KAYI JAMB.

Wannan Dokar Hukumar JAMB takara karfa fa ta Ne a 'Yan Shekarun Nan.

Wannan Shine Dalilin Da Makarantun gaba da Sikandire Dayawa S**a Soke Tsarin Pre-ND a Diploma Dakuma pre-nce, a NCE, Sak**akon ko daka Kayi daya daga Cikin Su, Har Ila yau Ana Buqatar Ka sake Rubuta Jarrabawar JAMB kafin Makarantar ta baka Admission, Bayan hukumar JAMB ta baka.

Kamar yanda Nafadi a Yanzu Hukumar JAMB tana Cigaba da kalacin Dukkannin Sauran Makarantun gaba da Sikandire, Kan Suma subi wannan tsarin Na Cewar Makaranta bazata fara bada admission ba, har sai Dalibi yafara samun Admission DAGA JAMB.

a Karon Farko Dokar Tafi Tsanani ne Akan NCE, Polytechnic Dakuma Jami'o'i, Amma daga Bisani Hukumar JAMB ta shigar Da tsarin Zuwa Wasu Makarantun Monotechnics, Ma'ana kebantattun Makarantu a wani Bangare Guda Daya, k**ar irin su kwalejin Aikin Noma(College of agriculture) Da kwalejin koyon Aikin shari'a(Legal)
a Yanzu Za'a Iya cewa tsarin JAMB kafin Admission, ya Kara de kowanne Bangare Da sashi Na Makarantun gaba da Sikandire, a Fadin Nigeria, in Banda school of Nursing, Kokuma College Of health Da wasu Yan Kadan.

---Menene Amfanin JAMB REGURLARIZATION?

Amfanin Sa ya kasu Bangare Biyu Ga Wanda Yayi diploma da Wanda Yayi Jami'a.

Wanda Yayi Diploma; Dalibin da yayi Diploma, Ko NCE Wanda a Lokacin Hukumar JAMB Bata Bashi Admission ba, Kokuma Ma beyi jamb din ba a shekarar, to a Lokacin Dayake, bukatar Shiga Jami'a, ta Hanyar Direct Entry, Dole sai yayi REGURLARIZATION, domin Hukumar JAMB tafara Bashi JAMB Number.

Dalibin Da Yayi Jami'a; Zai Yuwu Ace Dalibi ya kammala Jami'a batare da Hukumar JAMB ta Bashi Admission ba, Sai de Dalibi Bazai samu halartar Yiwa kasa Hidima ba(NYSC) Har sai Yayi JAMB REGURLARIZATION.

Hukumar JAMB itace take Amincewa da Cewar ka, kammala Jami'a Kuma zaka iya yin Hidimar kasa ko A'a.

JAMB REGURLARIZATION a takaice; Yana Nufin wani tsari ne Na Hukumar JAMB, da takeso dole tasan Dukkan Daliban Dasuke karatu a Makarantun gaba da Sikandire, domin ta a Dana Bayanan Su (Matriculation List)
a Wannan Shekarar hukumar JAMB ta Kara Gargadin Makarantu da Kada Su Kara Bawa, Wani Dalibi Admission ba tare Da hukumar tafara Bashi ba.

Kusani Dalibai babu wani Admission, halatacce inde Sunan ka, baya cikin Matriculation List Na JAMB.

Mai karatu Zai Ce to Yaya batun Masu Part time fa, Kokuma karatu daga gida (Distance learning)

Sai Nabaka Amsar Cewa dukan su hukumar JAMB ce take fara basu Admission, domin akwai Nasu tsarin Na Daban, Wanda ya hada hadda Daliban Das**ayi Jami'a a Wasu kasashen(ABROAD STUDY) Dakuma Masu Part Time ko affiliate program.

NB: Dalibai Musani Cewa JAMB REGURLARIZATION Bashi bane Change of Admission Letter.

Zaku Iya fada Mana Wasu abubuwan Das**a Shige Muku Duhu, Domin Yin Bayani Akai.

Ku Tuntube Mu Ta👇
📧 Email>[email protected]
📱WhatsApp>08086251045
©ASOF 2022

22/05/2022

TSAKURE CIKIN LITTAFIN JAMI'A RUNBUN ILIMI

KASHI NA BIYU

Wanda Umar Kabir Dakata ya wallafa a kokarinsa na ganin ya taimakawa dalibai domin su san yadda zasu gudanar da harkokin karatunsu cikin sauki da nassara.

Ga mai neman Karin bayani 08133614498

MAKARANTUN KWALEJI
Makarantace ta gaba da sakandire da ake gabatar da darussa daban-daban, sannan ana bada shaidar kammala karatun NCE, ND, HND da dai sauransu.
Wani lokaci, layin da ke tsakanin kwaleji da jami'a na iya zama ɗan ƙarami. Misali, Kwalejin William & Mary a Virginia ana kiranta kwaleji, amma suna ba da digiri na biyu a fannin kasuwanci, shari'a, ilimi da kimiyyar teku. Kwalejin St. Joseph dake New York tana ba da digiri na biyu a fannin ilimi, kasuwanci, rubuce-rubuce da dai sauransu. kwalejin Sa'adatu Rimi dake Kano itama tana bada takardar digiri a fannin ilimi da sauransu, haka nan kwalejin FCE dake Kano tana bada takardar Digiri. Haka nan yawancin cibiyoyin da ke ba da HND,ND ana kiransu kwalejoji.
9. MARAKARANTUN GABA DA SAKANDIRE (TERTIARY INSTITUSION) A NAJERIYA
Ilimin (tertiary institution), shi ne matakin Ilimin bayan kammala karatun sakandire, Masana a bangarori da dama suna bada shawara a kan kar dalibin da ya kammala sakandire ya ajiye karatu ya koma neman kudi, domin hakan illa ne ga rayuwar matasa da kasa baki daya. Su kan kafa hujja da cewar kasa na ginuwa a yayin da matasan cikinta ke kokarin hawa tsanin da zai inganta wannan kasa, a duk lokacin da matashi ya zama ba shi da burin daya wuce ya gina kasar shi, zaka same shi yana kokari wajen ganin yakai ga shiga irin wadannan makarantu, saboda sune suke yaye likita, lauya, dan sanda, shugaban kasa, soja da sauran dukkan wani mai amfani acikin al'umma. A kasar Nigeria zamu raba makarantu,(Tertiary institutions) zuwa gida uku :
1. CERTIFIED BUT NOT ACCREDITED.
Rukunin makarantu, Jami'o'i, da sauransu Heigh education, wadanda masana sun gamsu da irin kokarinsu amma ba a basu izinin tabbatuwa a matsayin tertiary institution ba. Rukunin wadannan makarantu, sunada rigista a matsayin cibiyoyin ilimi amma ƙungiyar NUC ba ta yarda da kwasa-kwasan da suke koyarwa ba. Mafi yawan cibiyoyin da ke karkashin wannan rukunin mallakar mutane masu zaman kansu ne, duk da haka akwai wasu cibiyoyin mallakar Gwamnati da suke gudanar da wasu kwasa-kwasan da ba'a amince da su ba, wadanda ba za ka gane ba sai ka shiga cikinsu.
2. ACCREDITED BUT NOT CREDIBLE
Wannan rukuni na cibiyoyi suna gudanar da harkokinsu na koyo da koyarwa, sannan suna da damarmaki na gabatar da kwasa kwasai da dama.Bugu da ƙari, wasu daga cikinsu suna ba da izinin shiga ga waɗanda ba su yi UTME ba. Dalibai na biyan kudi ne a maimakon jarrabawar UTME din. Yawancin ma'aikatu a Najeriya suna gujewa mutanen da s**a kammala karatu a cikin irin wadannan makarantu. Saboda rashin tabbacin ingantaccen ilimi da ake samu a cikin wadannan cibiyoyi, wadannan makarantu akwai masu zaman kan su da wasu cibiyoyin gwamnati suna ƙarƙashin wannan rukunin.
3. ACCREDITED AND CREDIBLE
Waɗannan su ne mafi kyawun cibiyoyi a Najeriya. Yawancin lokaci suna ba da izinin shiga kan cancanta, kuma koyaushe suna guje wa abubuwan da ka iya ɓata musu suna. A zahiri manufar su ita ce horar da ɗaliban da za su iya zama mafiya ƙwarewa a cikin ayyuka da fannoni daban-daban. Yawancin ma'aikatu a cikin Najjeriya koyaushe suna son wadanda s**a kammala karatun waɗannan ingantattun cibiyoyin. A cikinsu akwai mallakar gwamnati da kuma 'yan cibiyoyi masu zaman kan su suna karkashin wannan rukunin.

20/05/2022

Karatun Ilimin Kimiyyar Lissafi a Nigeria
(Bsc. Mathematics)

(Ƙashin Bayan ilimin Kimiyya Da Fasaha)

Ilimin Lissafi ya ƙunshi jigogi da yawa; Don haka, zaku iya zaɓar kowane babban jigo k**ar statistics, operation Management, accountancy, actuarial sciences,
Dasauran Ɓangarori Masu yawa.

Kasancewa daliɓin Lissafi, zaku iya yin aiki a Data Analysis wanda a halin yanzu ake buƙatar fannin sosai.

Ilimin Lissafi yana ba da damammaki da yawa a kusan dukkan fannoni komai saida Ma'auni Dakuma lissafi.

Ilimin lissafi batu ne da ɗalibai s**a daɗe suna tsoronsa a ko'ina a faɗin duniya, ƙaruwar guraben ayyukan yi ga waɗanda s**a kammala karatun ilimin lissafi, yasa ansamu ƙarin ɗalibai Masu zaɓin yin BSc Maths; babban zaɓi ne na aiki, kuma ba shi da iyaka, Idan kai mutum ne mai son warware daidaito da matsaloli, to BSc. Mathematics shine zaɓinka!

Idan Ilimin Kimiyyar Lissafi Yanada wahala Abun tambayar Shine shin amfanin ilimin Kaɗan Ne?

Wataƙila SBD Muhimmancin sa dakuma tsadar zata iya sawa yayi wahala Kamar yanda muka Sani a kasuwa Duk Mai amfani dayawa yana tsada; tayuwu ilimin lissafi yana biyan tsadar sa ne dawuya kasancewar sa ilimin da Babu Abunda baya shiga cikin sa, da ilimin lissafi za'a iya warware kowacce Irin Ta ƙaddama da matsala.

Kamar kowane fanni, BSc. Mathematics yana buƙatar Jajircewa da aiki tuƙuru, Ko da yaushe an san ilimin lissafi abu ne mai wayo, wanda ya sa ɗalibai da yawa kuka, Duk da haka, ba duka bane yake Basu wahala, Da zarar an maida hankali dakuma Fayyace Fomulolin warware jimlar zai zama mafi sauƙi.

•Ko akwai wani Mutum Na musamman dayak**ata yanemi BSc. Mathematics?

✓Amsar ita ce duk wanda ke da sha'awar gaske da batun ilimin lissafi, ko ilimin yaren computer, zasu iya shiga wannan fannin.

Daliban da ke tunanin yin BSc. Maths ya k**ata su tabbatar da cewa suna da halayen Juriya a karatu dakuma Naci da yawan bibiya, ga Wasu matakai:

Mai da hankali: Shin za ku iya tsayawa mai da hankali a wani wuri na musamman? Math jigo ne da ke buƙatar mayar da hankali, bawai kawai Abu me wuya bane
Sauran sun haɗa Da:
Calmness
Patience
Confidence
Observation Skills.

Wasu daga cikin Darussa ko subjects a matakin Farko:
Algebra
Differential Calculus & Vector Calculus
Vector Analysis & Geometry
Integral Calculus & Trigonometry
Advanced Calculus
Mathematical Methods
Differential Equations
Mechanics
Probability Theory
Linear Programming and Optimization.

Koda Yake Ga Tsarin Jadawalin ga kowacce Shekarar Karatu a Nigeria: (Wasu Daga Ciki muka ambata a Dunƙule bamu fayyace Elective Da Core ba)

♦Level 100 Both First And Second Semester:

Introduction To Computing

Sets and Number

Trigonometry and Coordinate Geometry

Differential and Integral Calculus 2

Mechanics

Heat and Properties of Matter

Algebra 2

Conic Sections and Applications of Calculus

Vectors and Dynamics

Statistics Introductory

♦Level 200 Both First And Second Semester:

Mathematical Methods I

Real Analysis I

Abstract Algebra I

Linear Algebra I

Numerical Analysis I

Discrete Probability Distributions

Elementary Differential Equations I

Real Analysis II

Abstract Algebra II

Linear Algebra II

Continuous Probability Distributions and Distribution Techniques

Fortran and Structured Programming

♦Level 300 Both First And Second Semester:

Mathematical MethodsII

Advanced Real Analysis I

Theory of Rings & Fields

Complex Analysis I

Analytical Dynamics I

Mathematical Modeling 3

Axiomatic Set Theory

Number Systems and Algebraic Structures

Numerical Analysis II

SIWES (Tsawon Second Semester)

♦400 Level Both First And Second Semester:

Differential Equations

General Topology I

Theory of Finite Groups

Advanced Real AnalysisII

Hydrodynamics I

Quantum Mechanics

Biomathematics

Graph Theory and Combinatorics

Functional Analysis

General Topology II

Group Representations and Characters

Measure and Intergration

Partial Differential Equations

Hydrodynamics II

Complex Analysis II

Differential Geometry

Electromagnetic Theory and Waves

Analytical Dynamics II

Operations Research

Note: Mu Lura Cewa wannan Tsakure ne mukayi kuma abubuwan na iya chanjawa Bisa ga La’akari Da makarantun.

Bugu Da Ƙari Ga Kuma Wasu Ɓangarori Da Ɗaliban Math Zasu iya Karatu a matakin karatu na Gaba:

Master of Computer Applications

Master of Business Administration

PG Certification in Data Science

Master of Science in Data Science

PG Certification in Machine Learning

PG Certification in Machine Learning & Deep Learning.

Batun Aiki kuwa abun Ba'a Cewa Komai Domin kuwa ko ina kuma ko yaushe ana Rububin Ɗaliban daskayi Bsc mathematics Matuƙar sun kammala karatun Da Ƙwarewar su.

Ga Kaɗan Daga Cikin inda Ɗaliban Math Zasu iya Aiki:

Accountancy & Professional Service
Management Consultant
Underwriter
Actuarial Profession
Bank PO
Investment Banking
Retail Banking
Multimedia Designer
Public Administrator
Policy Analyst
Lecturer/Professor
Meteorologist
Computing & IT
Engineering Scientist
General Management
Operational Research
Space Scientist
Developer
Portfolio Manager
Statistician

©ASOF 2022
WHATSAPP
08086251045

Want your school to be the top-listed School/college in Jigawa?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Kofar Gabas Jahun
Jigawa

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00
Other Jigawa schools & colleges (show all)
Hassan Yusuf Hassan Yusuf
Jigawa

Nigeria

M shareef fans M shareef fans
Abanderi
Jigawa, SCHOOL

Business

Hamsat Hamsat
Taraya Ranja Quarters
Jigawa

Please we create this page for educational reason only to learn

Collage of health science school of hygiene kano Collage of health science school of hygiene kano
Jigawa

Prevention is chiafer and better then care

Ilmur-ramli wal hisab Ilmur-ramli wal hisab
Ringim
Jigawa, 41522

Mun bude wannan Page din Domin Karawa Share fage ga masu son kiyar ramli

Kabeer Kalid Kabeer Kalid
Kiyawa Local Government Gurduba Word
Jigawa, 693505

Muazu Muazu
Jigawa

Who is a hero Who is a hero
Jigawa

Its our duty as Muslims to properly apply the guidance given in the Qur'an and hadith in our daily manners. You can read 'about' us, suggest to friends, share anything you like to...

Khadija University Majia. Khadija University Majia.
Hadejia Road Majia Town Taura LG
Jigawa

K*M VIBES TV✅ Official page of Khadija University Majia Students ✨Commitment to Excellence✨

My gallery My gallery
Hadejia
Jigawa

Muhammad Naseer Salisu Muhammad Naseer Salisu
Jigawa, 6295

Jigawa