Real Zkr Mai fadima niasse jos

Real Zkr Mai fadima niasse jos

You may also like

Lampa Dnipro
Lampa Dnipro

Zakiru M Fadima Masoyin Manzon Allah, Shehu Tijjani, Da Maulana Alhaji Ibrahim Niasse. Mai tafiya cikin soyayya Akan fairar Shehu Ibrahim..

12/09/2024

Sakon Jajantawa Ga Al'Ummar Maiduguri Na Ibtila'in Ambaliyan Ruwa

Photos from Baye Mansur TV's post 12/09/2024
12/09/2024
04/09/2024


Marhaban Summa Marhaban, Summa Aidan Ba'ada Hazayni Marhaban, Lale Lale Da Zuwan Watan Matattaran Asiran , Ainihin Gwaiduwan Rahman , Farkon Mabayyanar Kuma Haƙiƙani Nata, Khalifan Haƙiƙi Ba Majazi Ba, Madadin Da Ya Samar Da Dukkan Da , Hasken Shiriya Nasu, Silar Arziƙi Nasu Duniya Da Ƙiyama, Wanda Ya Tattare Dukkanin Sunaye Da Siffofi, Bawan Na Gasken Gaske, Shugabanmu Masoyinmu, Natsuwar Zuciyarmu, Salamar Ƙirazanmu, Gwani Na Sallallahu Alaika Wa'ala Alika Wasallim!!!
🌲
Muna Addu'ah Ya Kara Kara Tabbatar Damu Abisa Tsantsan Tsabar Tsagwaron Ƙaunarsa, Da Koyi Da Shi Cikin Hani Da Umurnin Sa (Ƙaulan Wa Fi'ilan), Alfarmar Tsarkin Jama'an Gida Nasa, Wato Alaihimussalam Amin 🤲📿
Oyoyo Da Zuwan Gata Na Share Dukan Kuka Na!!!
✍️
Sidi Aminu Rufa'i Alhussaini
(Sirrin Shehu Yahuza Zaria)
08065030293, 07031007503
[email protected]

10/08/2024

Happy follow-versary to my awesome followers. Thanks for all your support! Yakubu B Waziri, Muhammed Gaddaf Salihu, Ibrahim Sirajo, Bangiss Mus Tafa, Muhammadu Rasulmi Ina godiya

03/08/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! Mohaman Sabiou, Emm Kay, Ibrahim Sirajo, Umar Abubakar Silame

03/08/2024

Happy follow-versary to my awesome followers. Thanks for all your support! Usman Dauda, Usman Muhammed, Audu Mohammed

25/07/2024

Happy follow-versary to my awesome followers. Thanks for all your support! Abubakar Isyaku

25/07/2024

📗 Assalamu Alaikum Warahmatullah.

🌸 Cigaba da karatun Adabul Mureed kashi na 8)

🎤BISMILLAHI RAHMANl RAHIM.

👌Yana daga cikin ladaubban muridi tsakaninsa da shehinsa, Ba'aso muridi na tarbiyya ya nunawa shehinsa ra'ayinsa yace shi ga yadda yakeso, idan shehinsa yai shawara dashi akan aikata wani abu kar yayi sauri yace ga abunda za'ayi ko kuma abar kaza' anaso yamaida al'amarin ga shehinshi, ya kudurta aransa cew,a shehinsa ya fishi sanin al'amura bakidaya, Kuma ya san shehinsa ya wadata da yayi shawara dashi, abunda yasa shehin yai shawara dashi domin soyayyan da yake yimasane kawai, matukar wasu dalilai ko hujjoji bayyanannu basu bayyanar da sa6aniba akan wannan, ( Misali abunda bai kamata bane to sai yayi bayani) in ba hakaba to anaso ya bada shawara ya fadi abun da yaga zaiyi Amma tare da ladabi kar yayi rashin kunya a wurin bayanin.,

👌Sannan anaso idan shehinsa bayanan ko baya gida yayi tafiya' to ya ruka dubawa yaya halin gidan' yaya Iyalan shehin suke ciki basu da bukatar wani abu ??? anaso muridi ya ruka duba wannan, da hiduma da wanin haka, wannan yana daga abun da zai karkatar da zuciyar shehin zuwa gareshi,
To hakanan suma yan uwa na Allah su ruka nuna soyayya irin wannan suna dubawa, in dan uwanka bayanan ka ruka duba gidanshi wajan iyalinshi in yana dashi' ko wajan iayayensa kana gaishesu, zuwanka wajansu zai de6e kewan rashin dansu, kuma shima inya dawo zaji dadi.

👌Yana daga cikin ladaubban muridi tsakaninsa da Shehinsa. Idan muridi yana jin isa azuciyarsa ko griman kai saboda ayyukan da yake aikatawa na ibada ko yawan Sallah ko yawan karatu sai yana jin kanshi, ko kuma yana ganin halinsa ya gyaru' To yaje ya gayawa shehinshi dan ya nuna masa maganin wannan matsalar, idan ya 6oyewa shehinsa wannan to itaciyar riya da itaciyar munafunci zasu 6ullo a zuciyarshi....

Kubiyo mu hadu a karatu na gaba .. ✍️

🕋 Zawiyyan MAULANA Sheikh Ibrahim Mansur Imam Kaduna.

23/07/2024

Shi kuma Wannan Abinda yake yi masa Kaikayi Cikin Mimiyyah sune wadannan Baitukan Toh Suma Ga Amsar sunan Asha Karatu Lafiya:-

Alhj AS Mai Gari

صحبه قوم خيار هم ملوك في الأنام

Sahabbansa mutane ne wadanda suke zababbu wanda za’a iya kiransu sarakaine acikin Halitta

Wannan Baitin bashi da wani Ishkaali Domin kuwa dukkanmu mun yarda Mutane ne da s**ai Imani da Allah da kuma Manzon Allah SAW kuma s**azo cikin Al’ummar Annabi SAW da Allah ya yabesu da Fadinsa:

كنتم خير أمة أخرجت للناس تأمرون بالمعروف وتنهون عن المنكر
وتؤمنون بالله

Ma’ana:
Kun kasance Mafiya Alkhairin Al’ummatai da Allah ya fitar ga Mutane Kuna Umurni da kyakkyawan Aiki kuna Hani da Mummunan Aiki kuma Kunyi Imani da Allah.

Inda Basa yin kyawawan ayyuka kuma basuyi Imani da Allah ba ai da Sheikh Tijjani bn Uthman bai siffantasu da Baitin daka Tsallake baka rubuta shi ba shine:-

شغلهم في الله دأبا
أو صفات أو أسام

Ma’ana:-

Maida Hankalinsu akan lamarin Allah ne akoda yaushe, ma’ana Tunaninsu kullum cikin Allah ko suyi tafakkuri cikin Siffofin Allah ko cikin Sunayen Allah. Ma’ana dai ko da yaushe suna qudurce cewa Halitta baki daya Allah ne yake sarrafa ta.

علمهم عرفانهم
كالأنبيا دون ملام

Ma’ana:-
Iliminsu da Saninsu ga Allah a iya kwatanta shi dana Annabawa ba tare da Zargi ba

Anan wajen wasu suke Tunanin Sheikh Tijani Bn Uthman yana cewa Sahhabban Sheikhu RTA Suna kan Matsayi irin na Annabawa Alaihumus Salaam.
Amma abinda ya kamata mu sani shi ko da yaushe Larabci da Balagha suna Koya mana wata Qa’idah da take cewa:-

أَلْمُشَبَّهُ دُونَ الْمُشَبَّهِ بِهِ

Ma’ana:-
A koda yaushe Abun Kamantawa Yana kasa da Abunda aka kamanta shi dashi ne.

Misali shine idan na ganka kana Sauri a tafiya zan iya cewa Na ganka kana Gudu Kamar Mota. Wannan ba yana nufin daidai kake da mota ba awajen Gudu duk mai Hankali yasan Mota tafika Gudu.

Sannan wannan bai sauka daga Doron Shari’ah ba domin akwai hadisi ingatacce da yake maganar data fi wannan baitin shine Hadisin da yake cikin Sunan Abi Dawood wanda aka Karbo daga S. Umar RTA yace Annabi SAW:-

‎إنَّ مِن عبادِ اللهِ لَأُناسًا ما هم بأنبياءَ ولا شُهداءَ، يغبِطُهم الأنبياءُ والشُّهداءُ يومَ القيامةِ بمكانِهم مِن اللهِ تعالى، قالوا: يا رسولَ اللهِ، تُخبِرُنا مَن هم؟ قال: هم قومٌ تحابُّوا برُوحِ اللهِ على غيرِ أرحامٍ بَيْنَهم، ولا أموالٍ يتعاطَوْنَها، فواللهِ إنَّ وجوهَهم لَنُورٌ، وإنَّهم على نُورٍ، لا يخافونَ إذا خاف النَّاسُ، ولا يحزَنونَ إذا حزِن النَّاسُ، وقرَأ هذه الآيةَ {أَلَا إِنَّ أَوْلِيَاءَ اللَّهِ لَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ}

Ma’ana:-
Lallai daga Bayin Allah akwai wasu Mutane Su ba Annabawa ne ba kuma ba Shahidai bane amma Annabawa da Shahidai suna Burin (muqaminsu) Ranar Alqiyama Saboda Muqamin (Mutanen) awajen Allah Ta’ala, Sai Sahabbai s**a ce a Ya Manzan Allah Labarta mana su wanene (wadannan)? Annabi SAW Yace: Wasu mutanene da suke Soyayya Dan Allah ba dan wani dangane daya hada su ba, kuma ba dan wata dukiya da zasu bawa juna ba, Na Rantse da Allah Fuskarsu Tana Haske, kuma suna kan (Minbari) na Haske, Basajin Tsoro (Ranar Qiyama) Idan mutane s**a ji Tsoro, Kuma Baza suyi Baqin ciki ba idan mutane s**a shiga baqin ciki, sannan Annabi SAW ya karanta musu Ayar: “Amma lallai waliyyan Allah babu tsoro a tare dasu kuma baza suyi bakin Ciki ba.”

Wannan Hadisin Ingatacce ne tare da haka yana da Shawahid Cikin Musnad Na Imami Ahmad, Sharhus Sunnah Na Baghawy, Mustadrak Na Imami Hakim kuma ya ingantashi kamar Yadda Zahaby Ya Inganta masa.

Bari na kara maka da wanda kafi yarda dashi Wato Albany ya inganta shi cikin Saheehu Abi Dawood Hadisi mai Lamba na 3,527

Toh kaga a wancan baitin fa Tashbihi Akayi shiko nan babu Tashbihin a fili. Saboda shi a baitin cewa akayi Kamar na Annabawa ne ba’ace Annabawa ne su ba, kuma ba’ace Iliminsu daya da Annabawa ba. Aiko bahaushe yana cewa “KAMA DA WANE BATA WANE”

Bari ma dai, Mu a Tijjaniyyah yana Cikin Aqeedarmu Abinda Sheikh Muhammadu Abdul Wahidi An-Nazeefy ya fada Cikin Littafin Al-Yaqutatul Fareedah cewa:-

فما نشق المختوم مدرك أنبيا
ولو ذرة منه لذاب تبدت

Ma’ana:-
Sheikhu Tijjani RTA bai Shaqi Matsayin Annabawa ba, wanda da za’ace zai Shaqi kwayar Zarra daga cikin Maqamin Annabawa ai da Zai Narke ne.

Wannan Baiti ya nuna mana Karara cewa ko Sheikhu Tijani RA wanda shine Shugaban Sheikhu Ibrahim Niasse RA bai kai ga matsayin Shaqar Maqamin Annabawa ba b***e kuma Sahabban Sheikhun RAnhum.

Bari ma dai Shi Sheikhu Tijani ma ya fada cikin Jawahirul Ma’ani “Duk Girman Waliyyi bai kai Matsayin Sahabi ba b***e yakai ga Annabawa”

Sanann Baitin Qarshe daka kawo ba daidai bane yadda yake Shine:-

سلمن تسلم وإلا
تلتقي سوء الحمام

Ma’ana:-
Ka sallamawa (Hukuncin Allah) in ba haka ba zaka hadu da Mummunan Qarshe

Wannan ma babu Wani Ishkaali shi falalar Allah yana bada ita ne ga wanda yaso

ذلك فضل الله يوتيه من يشاء والله ذوالفضل العظيم

Duk wanda ko Yaqi Sallamawa Hukuncin Allah ai kuwa tabbas yana tare da mummunar cikawa.

©Aliyu Uthman Bashir

Photos from Real Zkr Mai fadima niasse jos's post 16/07/2024

Sheikh Muhammadul Mushry RTA Yana Cewa:-

تملكني حب الخليل جبلة
فما صد قلبي عن هواه ولا مشا

وما زادني قرب الخليل وبعده
ولا وصلة فى الدهر إلا تعطشا

وإن قيل لي يوم القيامة فاغتبط
فهذا الذي تهوى فخذ منه ما تشا

لقلت لهم حسبي من الشيخ نظرة
وحسبي بها نزلا وحسبي بها عشا

وإن كان حبي للخليل يضرني
فيا رب عجل لي من الضر ما تشا

Wadannan Sune wanda Idan ka Dafa Alqur’ani ka rantse cewa Sharifai ne Kuma Malaman Al-ummah ne bazaka taba kaffara ba.

Toh sune s**a Sallamawa Sheikhu Ibrahim Niasse RTA, Idan wadannan Masu Asalin Zasu fadin irin wadancan Baitukan, Toh Sai Irina Mara sa Asali Nayi wasa da Soyayyar wannan BAWAN ALLAHn ??

Photos from Real Zkr Mai fadima niasse jos's post 14/07/2024

Innalillahi Wainna ilaihi Raji'un
Lahaula wala quwata Illah billah
Hasbinanllahu wani imal wakil
Kullu nafsun Za ikatul mautu
Kamar Yadda muke fada Akullin
Kowani irin hali muka Shiga godiya Tafara zuwa kafin komai Sai Tuba Astaga furullah dama mu babu mu koma babuku maulana Sai dai Allah
Muna masu fata hanyar da kuka dau Ramu Akai kada mugota haka kar hijabin mutuwa Ya Shiga Tsakaninmu daku fatan Alkairi gareku Allah Ya bamu Albarkarku dan irin zaman da kukayi Afadar Sahibul wusuni wal Jamali S A W
WAL'ABDULILLAH

21/06/2024

𝐈𝐒𝐇𝐀𝐑𝐀 𝐃𝐀 𝐍𝐀𝐒𝐈𝐇𝐀𝐑 𝐒𝐇𝐄𝐈𝐊𝐇 𝐌𝐔𝐇𝐌𝐌𝐀𝐃𝐔𝐋 𝐌𝐔𝐒𝐇𝐑𝐈 𝐀𝐋𝐌𝐔𝐑𝐓𝐀𝐍𝐈 𝐑𝐓𝐀

Siradul Mustaƙim (hanya madaidaiciya) wanda aka faɗa cikin suratu Fatiha shine: Komawa zuwa ga Zatin Allah da komawa cikin Soyayyar Manzon Allah SAW, da kuma BAQA’I tare da zatin Allah Da Narkewa cikin Zatin Allah (batare da Hululi da Ittihaadi ba domin Allah ya tsarkaka ya sauka ko ya haɗu da jikin Abun Halitta) da Narkewa cikin Soyayyar Manzon Allah SAW, Da Neman Sanin Allah (Ma’arifah) ta hanyar Shi da Siffofinsa da Sunayensa. Da Tabbatuwa akan Bin Sunnar Manzon Allah SAW.

Duk wanda ya dawwama akan haka a duniya toh ya tabbatar zai Samu Istiqaama, wanda kuma bai dawwama akan Haka ba toh bazai samu ba, duk lokacin da istiqaamarka ta ragu a rayuwar duniya toh zaka haɗu da tawaya a gobe ƙiyama.

Ku komar da Zuƙatanku zuwa ga Allah, ku rayar da lokutanku da neman kusanci ga Allah da ɗebe kewa dashi da soyayyar Manzon Allah SAW, Ku Sani Rayuwar nan Taƙaitacciya ce Kuma Gashi abun nema acikinta suna da yawa.

Ku tashi kuyi ƙoƙari a duniyar nan idan mutum Ya mutu ba zai samu damar furta LA ILAHA ILLALLAHU kafa ɗaya tak ba. Duniya wajen Aiki (Ibaadah) ne babu Hisabi Lahira kuma wajen Hisabi ne Babu Aiki.

Allah Ya Tabbatar da duga-duganmu akan Siraɗil Mustqeem.

©️Aliyu Uthman Bashir

15/06/2024

BAITOCIN SHEHOU IBRAHIM A RANAR ARFA HAJJINSA NA FARKO 'OU RIHLATI SHEHOU IBRAHIM!!!
🌹DAGA🌹
SIDI AMINU AHMAD RUFA'I
(SIRRIN SHEHU YAHUZA ZARIA)
🌹📚🖊️🌹
ﺑــﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻯ ﺍﻟﻔﺎﺗﺦ ﺍﻟﺨﺎﺗﻢ ﻧﺎﺻﺮ ﺍﻟﻬﺎﺩﻱ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﺣﻖ ﻗﺪﺭﻩ ﻭﻣﻘﺪﺍﺭﻩ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ
ﻳﺎﻫﻤﺔ #ﺍﻟﺸﻴـﺦ ﺍﺣﻀﺮﻱ ﻟﻨﺎ ﺑﻬﺬ ﺍﻟﻤﺤﻀﺮﻯ ﻭﺍﻟﺘﻌﻄﻔﻲ ﺑﻨﻈﺮﺓ ﺗﺎﺗﻲ ﻟﻨﺎ ﺑﺎﻟﻈﻔﺮﻱ
Rana:Alkhamis
Date:10/Dhoul~Hajji/1441 Dea Dea Da 30/July/2020
🌲
Mowlanmu Shehul Islam Wa Sa'adatul Anam Yayi Hajjinsa Na Farko Yana Dan Shekara 39 A Shekara Ta 1355 Hijiriyya Dea Dea Da 1939 Miladiyya Kusan Shekara Tamanin Da Wani Abu Da Ya Gabata. Sannan A Wannan Aikin Hajine S**a Hadu Da Sarki Mai Albarka Wato Sarkin Kano Alhaji Abdullahi Bayaro Bayan Abunda Ya Faru Stakaninsu Ya Nemi Ya Zo Nigeria Kuma Ya Amsa Bayan Shekaru 9 Da Haduwansu A Makka. Afwan Karmu Cikaku Da Surutu Bari Muciratu Zuwa Riskuwa Da Wa'innan Abyatu Da Yayi A Irin Wannan Rana Masu Cike Da Taraki .Yan'uwa Gasu Kamar Haka;-
🌲
وقفت يـو الثلثا بعرفه أذكر ربى ذكر عبد عرفه
Nayi Stayuwan Ranar Talata Inata Zikiri Ubangiji Kai Daga Jin Irin Zikiri Da Nake Ni Kasan Nasan Wanda Nake Ambata Wato Nasan Allah
🌲
دعوت للنفس وللإخوان وللمكان بل وللزمان
Nayiwa Kaina Addu'ah Nayiwa Yan'uwana Musulmi Duka Addu'ah Nayiwa Makkan Addu'ah Bari Har Zamaninma Sai Da Nayi Masa Addu'ah
🌲
نزل ربي ليبا هي البلا بملإ الحج وحين نزلا
Da Addu'ah Tayi Addu'ah Sea Ya Sauko Don Ya Yaye Bala'ai Anan Filin Hajji A Lokacin Da Ya Sauka
🌲
قال أفيضوا فالذنوب غفرت لكلكم كذا العيةب سترت
Sai Yace Kowa Yayi Albishir Duk Zunubanku (Mahalarta Aikin Hajji Na Wannan Shekara) Na Yafe Ga Kowannan Ku Haka Nan Aibin Kowa Na Boye Na Suturta Bazan Bayyana Ba
🌲
شعثل وغبرا جءتمو نى اليوما أعتقتكم لا ذنب بل لا لوما
Mutanan Nan Masu Tara Gashi Ya Duddunkule (Sufaye) Da Masu Datti (Masu Dadewa Basuyi Wanka Ba) Duk Sun Zo Min Yau Dinnan Na Yantasu Babu Zunubi (Duk Laifin Da S**ayi Ko Zasuyi) Garesu Bari Babu Wani Zargi Garesu
🌲
فعند ذا تنفس الكبير ورفع البلا العبى القدير
Daga Nan Ne Yayin Da Ni Na Gafartawa Bayi Sea Da Yayi Numfashi (Madallah Da Wannan Gafara) Sai Ya Dauke Balakai
🌲
قد فاز أحبابى مدى الأزمان تفضلا وعدا من الرحمان
Haqiqa Masoyana Sun Rabauta Matukar Zamani Don Falala Da Alqawari Daga Ubangiji Arrahmanu
🌲
فافتقر الكل إلى الكل فحق إجابتى إذ كان سحق ومحق
Sai Kowa Yazama Mai Bukata Izuwa Kowa Ijabata Ta Tabbata Domin Ko Lamarin Ya Kasance Sahqu Ne Da Mahqu (Fana'i Da Baqa'i) Ubangiji Ya Karar Dani Ya Wanzar Da Shi
🌲
ودكت الجبال إذ ناجيت وجءته وإننى ما خءت
Sai Duwastun Nan Na Garin Makka Har Qa'aban Duk S**a Zama Gari S**a Rudiddige Yayin Da Na Kira Sai Naje Masa Kuma Lallai Ni Banje Masa Ba
🌲
كأننى فى حضرة الديان أتوب عن وقتى وعن مكانى
A Lokacin In Kaganni Zakace Nine A Hadara Inata Yafewa Lokacina Da Yan Lokacin Na Yafewa Gari Na (Mutanan Gari Na)
🌲
فقال لى مباسطا جذ ما ترى فقلت يا كعبة قلبى ما أرى
Sai Ubangijina Yana Mai Sakin Fuska Yace Dani Duk Abunda Ka Gani Cikin Halitta Ka Kwashe Na Baka Sai Ni Nace Ya Qa'abar Zuciyata Ni Banga Komai Ba
🌲
والله ما أرى ولا أرى ولا ٱريد شيءا إذ أطلت المقولا

Wallahi Banga Komai Ba Kuma Komai Ma Bai Ganni Ba Kai Nagani Kuma Kai Kadaine Ka Ganni In Zan Dauka Kai Zan Dauka
🌲
فقدت نفسى وفقدت الكلا فصار منى واردى لا حولا
Na Rasas Da Kaina Na Kuma Rasas Da Komai Sai Na Zama Na (Risku) Ga Ainihin Ma'anan Nan Na Lahaula Wala Quwwatu Illa Billah
🌲
كونى خديم المصطقى العدنان ليس بمحتاج ألى برهان
Kasancewata Hadimin Mai Kaka Adnan Wato Sallallahu Ta'ala Alaihi Wassalam Bayada Bukatuwa Ga Kawo Hujja
🌲
Alhamdulillah Muna Tawassali Da Stayuwan A Filin Arfa Da Kuma Abunda Wa'inan Baitoci S**a Kunsa Na Taraki Ta Kaimu Inda Take So Ba Inda Mu Muke So Ba Ta Kuma Bamu Abunda Take So Ba Abunda Mu Muke Soba Sirrin Samuwan Da Quwwa Irin Na Ma'aboci Nata Da Kuma Karewa Irin Na Yayanata Ameen@Wassalamu Alaikum Warahmatullah!!!

🌲
SIDI AMINU AHMAD RUFA'I
(SIRRIN SAHEHU YAHUZA ZARIA)
08065030293, 07031007503
Sidiaminurufai .com

11/06/2024

Aslm Yan uwa masu Al barka munsaba zuwa muku da maganganu maga bata To Yau ba dasu muka zo mukuba wani Al Kairine da Aka samu A palmpay Amma da Sharadi kamar haka idan ka taba budewa bazasu bakaba sai dai wanda ba taba bu dewa ba ana samun naira dubu Ashirin da biyu 22000 da farko dai Kafin ka fara kamin magana ta WhatsApp ga number na Allah ya bakowa sa,a 08086296462 faka faka Allah Ya bawa mai Rabo sa,a amen

07/06/2024

📗Littafin ADABUL MURID (Ladabin muridi ga shehinsa)..
{Wanda su MAULANA Sheik Ibrahim Mansur Imam s**a karanta shekarun baya cikin tsoffin ajiyan karatuttukan baya shekara ta (2009).
Domin mu karanta mu anfana dasu, Allah ya bamu fahimta aciki.

Waba'ad:

🍇Assalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'ala wabarakatuhu.

🍏 MUQADDAMA:

🍇Ubangiji Tabaraka wata'ala wanda ya halicci dan Adam ya fadi dalilin halittansa kamar yadda yazo acikin littafi mabuwayi' "Ban halicci mutun da aljan ba sai dan su bautamun", Ni ba kamar sauran sarakuna nakeba wadanda suke neman karin arzuki cikin dukiya da kuma wadanda zasu ciyar dasu abunci maidadi da abunsha maizaqi"

🍇Sannan' Yanzu ku kuna zaton kawai mun haliccekane kawai don wasa' Menene WASA shikenan sai dai rana ta-futo-ta fadi gari ya waye kaci abunci kai hira, kayi aure shikenan don haka muka yika..., ?
To' Allah TWA ya halicci mutanene don suji tsoronsa su bautamashi, shi tsoran Allah dinnan' shine mabudin duk wani abun neman bawa zahiri da badini, sannan yana kewayawane acikin da'irori guda uku kamar yadda SHEHU ya fadi:-

▶️1. Biyayya ga manzan Allah SAW zance da aiki, Shari'a da haqiqa:
Shari'a' kabi manzan SAW a maganganunsa' Dariqa kuma kabishi a ayyukansa.

▶️ 2. Lazumtar Zikiri da izini ingantacce daga shehunnai cikakku.

▶️ 3. Yin abotaka da masanin Allah..

🍇To Qa'ida tsoron Allah da tafiya zuwaga Allah baya yiwuwa dole ne sai wani ya koya maka, sai ka sa wani agaba ka bishi' Qa'ida kuwa Ko ba tafiya zuwaga Allah ba tafiya ta duniya ma wanda kakeso ya kaika gari Dole kabi umurninsa, inda yabi dole kabi inda ya tsaya dole ka tsaya abunda yace dole kayi abunda ya hana dole ka bari, idan ba hakaba tafiyan bazata yiwuba, ba yadda za'ayi jagora yana tafiya aga wani ya zauna ko ya juya, ko kuma shi jagora yayi Gabas wanda yakebi yayi yamma' dole yazama ana binsa sau da kafa, yadda yabi haka za'abi abunda yace haka za'ayi, to shi wannan jagora wanda zai gaba abishi yanada sharudda da ladubba da ake masa, shine z

Photos from Real Zkr Mai fadima niasse jos's post 07/06/2024

Masoyi ya ziyara ce masoyinsa
Mukuma Allah Ya bamu Albarkar
Ku gaba daya
WAL ABDULILLAH

06/06/2024

IN ABULFATHI NE SHEHIN KA...
*
**
***
Allah subhanahu wa ta'ala ya karrama mutane akan sauran halittu a tudu da ruwa (koguna), a ciki ya ware Al'ummar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya fifita su fiye da sauran Al'umma har ma Annabi Musa yaso Allah ya karɓi manzancin da ya bashi ya musanya masa da kasancewa cikin al'ummar Annabi SAW.

A cikin hakan dai Allah ya fifita sufaye akan sauran Al'ummar Annabi SAW ta hanyar kebantar su da tsantsar IBADA cike da TAƘAWA, a cikin sufayen Allah ya fifita Tijjanawa bayan taƙawa ya ƙara musu da FALALA, a cikin su dai har yau Allah ya fifita yan faidha da samun madarar MA'ARIFA.

Alhamdulillah wanda yake rike da faidhar Shehu din daga lokacin wafatin Shehu zuwa tashin kiyama kamar yadda Sayyadi Aliyu Cisse ya tabbatar shine Shehu Abulfathi RTA, shi kuwa yana cewa "Halara ce ta tattaro Al'umma ta ba Annabi SAW, ta ba Shehu Tijjani RTA, ta ba Shehu Ibrahim Niasse RTA, amma ni zaɓi ta bani akan in zaɓi jama'a na", don haka duk wanda ya tsinci kanshi sahun muridan Shehu Abulfathi RTA, shehin ne ya zaɓe shi ba shinenya zaɓi shehi ba.

Da haka ne Allah ya kebance mu da shagala da abinda ke gaban mu, ba zaka taba samun Muridin Shehu Abulfathi wanda ya shagala da jayayya da munkirai ko ya shagala da makiyya ba, hasalima wayanda s**a cutar da shehi yayin rayuwar sa, ba zaka ji cikakken muridin sa yana kula su ba ballantana ya zage su.

Mu abinda shehi ya bar mana gado shine MADINATU, Inda muke jaddada alakar mu da Allah da Manzonsa, kuma ya gina mana madinar a zuciyoyin mu, duk inda muke muna aiwatar da abinda ake yi Madinatu na zahiri.

Shehu Abulfathi Allah ya saka maka da alheri, Allah ya saka maka da alheri, Allah ya saka maka da alheri.

✍️✍️✍️ Sidi Sadauki ❤️

*** O'oh Ahmad Aliyyy ***

13/12/2019

Happy jamma. Atul mubaraka

Want your business to be the top-listed Shop in Jos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Yuseef Hassan, Sani Sulaiman, Pepe Seck, Musa Ibrahim, Ab...
SHEIKH IBRAHIM NIASSE RTA YA LAMINCE MANA. A wannan wasiƙar ta ƙasa Sheikhu RTA Yace:-“Yan uwana, da Maƙwabtana, da Khad...
Alhamdulillah wal abdulillah Zaman mimiya knn  Jiya dadadareAllah ya kara hada kanmu Ya komaKafaman Da ira madahu kafin ...
Alhamdulillah WalAbdulillah hadara ta Kara kudade da faila bjh shugaba S a w
Alhamdulillah
ALLAH Kabudaman saboda babul futuhi

Telephone

Website

Address

Katako Febuna
Jos
Other Shopping & Retail in Jos (show all)
Pro-Cess Gallery Pro-Cess Gallery
Tina Junction, Jos. Jo's North
Jos

IN RETAIL AND WHLOE SALE .. We deal on all kind of Ladies and Men Shoes, Hand Bags, Purse, Wallets and Belts.. ONLINE AND OFFLINE

NDL Clothing and Accessories NDL Clothing and Accessories
Zarmaganda
Jos, 930272

We Sell Quality and Affordable Fabrics with so much Trust and Dedication.Customer Satisfaction is

Kinemaster fund vedio Kinemaster fund vedio
World Democrate Block Industry
Jos

Itz ay JOE Itz ay JOE
@bladi Jos �
Jos

Usman Abdullahi Bappa Usman Abdullahi Bappa
Jos

Provision stock

Yung.cheekz.9 pro Yung.cheekz.9 pro
Jos

A shoe coupler

Pela's collection Pela's collection
Millionaires Qtrs Jos
Jos

Queen Debbie's Prime Enterprise Queen Debbie's Prime Enterprise
Jos

Perfumes, sneakers, bags, clothing, sandals and many more

Flair thrift Flair thrift
Jos

We sell affordable first grade thrift gowns and tops

Usman Auwal ishaq Usman Auwal ishaq
109\ 10
Jos

NSZaks World NSZaks World
Jos

"Look Classy Always" A world You get yourself Unique Outfits