Fagen wasannin kwallon kafa
Ku kasance damu domin samun labarai masu inganci na fadin duniya
A Hukumance: Barcelona ta ƙara tabbatar da Xavi zai cigaba da zama a ƙungiyar. Abun tunawa tun bayan lokacin da ya ce zai tafi:
Ƙungiyar tayi nasara 10
Canjaras 3
Rashin nasara 2
“Aikin bai kammala ba.”
• Fagen wasannin kwallon kafa
Xavi: “Na canza shawarata ne saboda na samu ƙwarin gwiwa sosai daga shugaban ƙungiyar nan, Manajoji da kuma ƴan wasa. Wannan aikin bai kammala ba tukuna.
“Ni kaina, abokan aikina, dukan mu muna jin cewa muna da ƙarfin da zamu cimma abu mai muhimmanci tare kuma mu cigaba da yin wannan aikin tare.”
•Fagen wasannin kwallon kafa
Laporta: “Xavi ya nuna soyayyar sa ta cigaba da zama a Barca, domin ya cigaba da wannan aiki mu haɓɓaka tare. Muna farin ciki. Kuma labari ne mai daɗi ga Barca.
“Kwanciyar hankali shine matakin nasarar kowanne aiki, Xavi cikakken masoyin Barca ne. Dukan mu tare. Barca tana saman zukatanmu.”
• Fagen wasannin kwallon kafa
A Hukumance: An tsayar da lokacin da za a fara kakar wasan Premier League ta 2024 zuwa 2025.
Za a fara gasar ta 2024/25 ne a ranar 17 ga watan Ogusta 2024, kwanaki 90 bayan an kammala gasar Premier League ta bana a ranar 19 ga watan Mayu.
Wasan zagayen ƙarshe a kakar wasan 2024 zuwa 2025 zai kasance ne a ranar 25 ga watan Mayun 2025, yayin da dukkan wasannin za a buga su a lokaci guda kamar yadda aka saba. Sannan an goge hutun tsakiyar kaka daga kalandar domin a samu damar fara gasar Premier League a tsakiyar watan Ogusta.
Za a bayyana yadda wasannin gasar a kakar wasan 2024 zuwa 2025 zasu kasance a ranar 18 ga watan Yunin 2024 da misalin ƙarfe 9 na safe agogon Nigeria.
•Fagen wasannin kwallon kafa
Jurgen Klopp ga Darwin Nunez bayan tashi daga wasan da Everton ta doke Liverpool da ci 2-0 a daren jiya.
Fagen wasannin kwallon kafa
Jude Bellingham ya fita daga sahun ƴan wasan Real Madrid da zasu fafata da Real Socieded gobe a gasar Laliga.
Fagen wasannin kwallon kafa
Carlos Ancelotti bai taɓa rashin nasara ba a tarihin haɗuwar sa da Bayern Munich.
Nasara 6, Canjaras 2.
• Fagen wasannin kwallon kafa
Diego Simeone: “Idan kaje Bayern, baka da wani zaɓi da ya wuce nasara. Shin kaga yadda Bayern suke wasa? Eh zasu zo gareka kuma basu da wani buri da ya wuce su ci ƙwallo. Basa taɓa rasawa. Suna da wani ɗan ƙwallo da ake kira Kimmich, lokaci na ƙarshe da naga ya rasa ƙwallo a hannun sa shine lokacin da ya ba ɗansa yayi wasa da ita.”
• Fagen wasannin kwallon kafa
Chelsea ta fara neman ɗan wasan tsakiyar bayan da zai maye gurbin Thiago Silva, a halin yanzu ƙungiyar tana duba yiyuwar kawo Castello Lukeba ɗan wasan Rb Leipzeg, wanda yakai £60m a kasuwa.
• Fagen wasannin kwallon kafa
A hukumance: David Raya ya lashe kyautar Golden Glove Award na wannan kakar a gasar Premier.
● Fagen wasannin kwallon kafa
Alkalin wasa dan kasar Faransa Clément Turpin ne zai jagoranci wasan Bayern Munich da Real Madrid a mako mai zuwa.
Ya jagoranci wasan karshe na gasar Zakarun Turai a 2022.
●Fagen wasannin kwallon kafa
Arsène Wenger: "Ina ganin Xavi ya yi aiki mai kyau a Barçelona. A ra'ayina, kawai yq sanar da barinsa kulab din nan ba da jimawa ba."
"Barçelon ba ta da sa'a ne kawai a kan PSG da Real Madrid, amma sun nuna cewa suna kara girma, cewa kungiyar tana girma tare iyawa."
"Idan ka yi tunanin shekarun 'yan wasan su, za su iya samun karin karfi ne kawai, shi ya sa nake ganin da na so Xavi ya zauna."
● Fagen wasannin kwallon kafa
Granit Xhaka: "Arsenal ta lashe Gasar Premier League ta zinare (Wadda ba'a taba iya gani ba) a 2004, me yasa mu (Bayer Leverkusen) ba zamu iya yin haka a 2024."
● Fagen wasannin kwallon kafa
Manchester United na sha'awar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar bayan Inter Alessandra Bastoni Kuma suna shirin miƙa tayin da yakai £52m akan ɗan wasa.
•Fagen wasannin kwallon kafa
Wannan itace rigar waje da Barcelona zata dinga amfani da ita a kakar wasa mai zuwa ta 2024 zuwa 2025.
• Fagen wasannin kwallon kafa
Kylian Mbappé ya amince ya zama lamba 9 na Real Madrid. Makusantansa sun tabbatar da cewa yana son taka leda a wannan matsayi, a tsakiyar kai hari. Inji - [Diario AS].
● Fagen wasannin kwallon kafa
Babu wani wasa a tarihin gasar Premier League da akafi raba jan Kati sama da wasan hamayyar birnin Liverpool (Mercyside Derby), Inda aka bada Jan Kati (23).
• Fagen wasannin kwallon kafa
Shugaban Laliga Javier Tebas yana farin ciki da zuwan Mbappe Real Madrid: “Da farko domin Real Madrid, na biyu kuma a matsayina na masoyin Real Madrid, Tabbas abun farin ciki ne kasancewar (Mbappe) a Madrid ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa a duniya. ba zan iya cewa shi ƙwararre ne ba domin Vinicius da Bellingham ma ƙwararru ne. Amma yana ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa a duniya.”
• Fagen wasannin kwallon kafa
Enzo Fernandez ya buga wasanni 46 a gasar Premier League tun bayan zuwan sa Chelsea, Wasanni 14 kawai ya iya samun nasara.
• Fagen wasannin kwallon kafa
Ɗan shekaru 20 Abdul Fatawu ya kafa tarihi, bayan ya zama ɗan wasan ƙasar Ghana na farko da ya taɓa zura ƙwallaye uku a wasa ɗaya (Hat-trick) a gasar Championship ta England a wasan da Leicester ta doke Southampton.
Fagen wasannin kwallon kafa
John Obi Mikel: "Ban fahimci yadda mutane za su ce Modric ya fi De Bruyne ba. A ganina De Bruyne ba kawai za'a bayyana yafi Modric kyau bane, harma ya kamata ace ya fi Modric kyau nesa ba kusa ba."
De Bruyne shine mafi kyawun dan wasan tsakiya a duniya. Dubi kididdigar, De Bruyne ya samu damar zura kwallaye da taimakawa fiye da Modric. Kar ku manta De Bruyne yana taka leda a gasar Premier, mafi girma Lig a duniya kuma mafi wahala a duniya, yayin da Modric ke buga gasa mafi rauni." (Talksport podcast)
● Fagen wasannin kwallon kafa
Real Madrid Vs Bayern Munich a zagayen (Semi Final) na gasar zakarun nahiyar Turai!
Real Madrid ta shiga har filin wasa na Etihad ta doke Manchester City.
Real ta kai wasan (Semi Final) a gasar zakarun Turai.
Manchester city 0-1 Real Madrid
Rodrygo 12
Kalma daya akan wannan hoton?
Shin akwai mutumin daya kak Dembele farin ciki a daren jiya kuwa?
Cristiano Ronaldo ya Jefa kwallaye biyu da bugun tazara cikin mintuna 20..
🐐
FFagen kwallon kafa
Wannan shine hoton da Kylian Mbappe ya wallafa a shafinsa batan an cire shi a minti na 63 a wasan PSG.
Da dukkan alamu yaron ya shirya komawa Madrid a wannan kakar.
Fagen kwallon kafa
Kwallaye 4 kadai akazura aragar kungiyar kwallon qafa ta arsenal tunda shekarar 2024 ta shiga.
Fagen kwallon kafa
Kwallayen Macherano takwas kacal amma ya lashe kofuna 25 yayin da shi kuma Harry Kane yaci kwallaye 422 ba tare da lashe kofi ko daya ba.
Fagen kwallon kafa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Kaduna
France Road Mekera Kakuri
Kaduna
This page is for football enthusiasts around the world
Kaduna, 80023
Bossify is helping individuals reach their goals and pursue their dreams. Virtually anyone with an internet connection and a commitment to self-empowerment through learning can com...
Lokoja Road Rigasa Kaduna
Kaduna, 8000
Domin kawo muku wasan nin dambe daga sassan nigeria bakiya daya
Igabi Road/Giwa Street
Kaduna
Wannan Kamfani Ne Da Aka Kafa Shi Don Sada Masu Ciniki Da Masu Kasuwanci, Gami Da Labaran Nishaɗi