Kundin Labarun Hausa
Samar Da Ingantattun Labaru Shi Ne Burinmu!!! Communications, information and broadcast
Obasanjo Ya Yi Sabuwar Fallasa Kan Adadin Man Fetur Din da Ake Sacewa a Najeriya
Tsohon shugaban ƙasa, Oluesegun Obasanjo ya faɗi irin ɓarnar da ake yi wa tattalin arziƙin ƙasar nan Obasanjo ya bayyana cewa sama da kaso 80% na ɗanyen man fetur ɗin Najeriya sace ake yi A cewar Obasanjo daga cikin ganga miliyan abu na man fetur da ake samarwa a ƙasar nan, ana sace sama da ganga miliyan 1.7m
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce sama da kaso 80% cikin kaso 100% na ɗanyen man fetur na Najeriya sace shi ake yi. Jaridar Vanguard ta ce Obasanjo ya bayyana haka ne a Abuja a wajen ƙaddamar da wani littafi mai suna, ‘Court and Politics’ wanda Dr. Umar Ardo, wanda tsohon na hannun daman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ne ya rubuta.
A cewar tsohon shugaban ƙasan, ɗaya daga cikin dalilan da s**a sa tattalin arziƙin Najeriya ya lalace shi ne yayin da sauran ƙasashe masu arzikin man fetur ke da tarihin adadin man da s**a haƙo, Najeriya ba za ta iya lissafin nata ba saboda sata.
Hangar man fetur nawa ake sacewa a Najeriya?
Obasanjo wanda ya samu wakilcin tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce satar ɗanyen mai na ɗaya daga cikin dalilan da zai sa tattalin arzikin Najeriya ya lalace. Tsohon shugaban ƙasan ya ce yayin da adadin ɗanyen mai ya kai kusan ganga miliyan biyu a kowace rana, sama da ganga miliyan 1.7 ake sacewa, rahoton Thisday ya tabbatar. Akan ko Najeriya za ta koma kan tsarin firaminista, Obasanjo ya ce babu laifi
Tsadar Rayuwa: Babangida ya gargadi Tinubu kan yiwuwar juyin mulkin soja a Najeriya?
-Gaskiya ya fito
Rade-radin cewa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya gargadi Shugaba Tinubu game da juyin mulki ba gaskiya Sai dai, akwai shafukan sada zumunta na kwaikwayo mai dauke sunan tsohon shugaban mulkin sojin da ke yada batun juyin mulkin Da yawa daga cikin masu bibiyar shafukan na kwaikwayo basu duba don bambance ko shafin da gaske na tsohon shugaban ba ne
Niger - Shugaba Bola Tinubu na shan s**a game da matsin tattalin arziki da aka shiga tun bayan da sanar da matakin cire tallafin mai da karya darajar naira. Matakan da shugaban ya dauka tun bayan rantsar da shi sun janyo hauhawar farashin kayayyaki abinci da sauran bukatun yau da kullum, kuma masu ruwa da tsaki, ciki har da 'yan adawa da shugabannin kwadago, suna ta kira kan janye matakan.
Sannan, an yi zanga-zanga a wasu jihohi a kasar saboda tsadar rayuwa. Jihohin da aka yi zanga-zanga sun hada da Oyo, Cross Rivers, Niger da Kano. Tsadar rayuwa: Yan Najeriya sun bukaci sojoji su yi juyin mulki Yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadinsu a shafukan sada zumunta saboda halin da ake ciki, yayin da wasu ke neman sojoji su yi juyin mulki. Wani a shafin X (Tuwita), (Ibrahim B. Babangida), ya sha bayyana ra'ayinsa kan yiwuwar cewa sojoji za su yi juyin mulki ga gwamnatin Tinubu.
Ga abin da ya rubuta: "Ba na goyon bayan juyin mulki, amma ina kira ga gwamnatin tarayya da ta dubi halin da 'yan kasar ke ciki, su kawo dauki kafin abin ya zama annoba."
Wani shafin YouTube ya yayata maganar bayan fadar ta a wani shiri, in da ta bayyana maganar a matsayin abin da Babangida ya ce.
Tinubu ya yi zancen mayar da tallafi da soke karya naira saboda shiga kuncin rayuwa
Gaskiyar batun juyin mulkin Babangida
Babu wata alama da ke nuna cewa tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), da ya mulki Najeriya daga 1985 zuwa 1993 ne ya fadi maganar. Kuma, shafin X din ya fi k**a da na bogi kuma babu shaidar tsohon shugaban kasar a rubutun. Sai dai, da yawan 'yan Najeriya da ke martani a rubutun ba su duba ko shafin gaskiya bane, dalilin da ya sa ake tunanin Babangida ne. Wani bincike ya kuma bayyana cewa a bude shafin a shekarar 2013 kuma ana gudanar da shi daga Minna, babban birnin Jihar Niger, kuma a nan ne gidan Babangida ya ke.
Najeriya a damalmalalle ta ke, ta na buƙatar ƙaƙƙarfan garambawul
– Ango Abdullahi
Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa, Ango Abdullahi, ya bayyana cewa tsarin da Najeriya ke a kai yanzu ya hargitse, kuma a damalmale ya ke.
Dangane da halin da ya ce ƙasar ke ciki, ya bada shawarar a yi wa Najeriya ƙaƙƙarfan garambawul.
Farfesa Abdullahi, wanda tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ne, yayin da ya ke jawabi a wurin ƙaddamar da littafi mai suna “Court and Politics”, Wanda Umar Arɗo ya wallafa, a Abuja.
A taron wanda aka gudanar ranar Asabar, Ango Abdullahi ya ce, “ganin halin da ƙasar nan ke ciki, zan iya cewa shugabani da waɗanda ake mulka sun gaza wajen samar da nagartacciyar ƙasa.
“Wannan taro ni a gani na wata dama ce gare mu domin mu yi wa kan mu faɗa cewa mu duka ke da laifi.
“Yanzu ɗin nan aka ɗauke wuta. Har yanzu tsawon shekaru 64 mun kasa samun wuta fiye da shekaru 64, wadda muke amfani da ita ba ta wuce migawat 4,000 ba. Wannan ai babban abin kunya ne.
“A wata ƙasar wuta mai ƙarfin migawat 4,000 ba za ta wadaci wani babban gidan ɗaya ba.
“Waɗanda a cikin mu ke zuwa Saudiyya aikin Hajji daga lokaci zuwa lokaci, zan tunatar da ku cewa wutar lantarkin da ake amfani da iya a Masallacin Ka’aba ta kai migawat 18,000 a kullum.
“Mu kuma nan a Najeriya, ƙasa mai al’umma miliyan 220 muna samun migawat 4,000, bayan shekaru 64 da samun ‘yanci.
“Maganar gaskiya wannan laifin kowa ne, tun daga masu mulki da waɗanda ake mulka, ” inji Abdullahi.
Ango Abdullahi ya yi kira a koma tsohon tsarin shugabanci na Firayi Minista, maimakon na shugaban ƙasa wanda ake kai a yanzu.
Ya ce tsarin shugaban ƙasa ya na haifar da kashe maƙudan kuɗaɗe a dimbin wurare da hanyoyin da ba su dace ba.
Ra'ayin jaridar PREMIUM TIMES
YUNƘURIN ƘIRKIRO ‘ƳANSANDAN JIHOHI: Yaudarar shugabannin Arewa ne na marawa Yarabawa burinsu na cin gashin kai,
Wai shin irin su kungiyar tsaro irin su HISBA, AMETAKUN, VIGILANTE da ma irin Yan Sandan Sarauniya mene aikin su ne? Koma mene ne, ya k**ata Shugabannin Arewa su yi karatun ta natsu, kafin su bi yarima wajen amincewa da ƙirkiro da ƴansandan Jahohi.
Amincewa da kirkirar ƳanSandan Jihohi wani cikar burin Yankin Yarabawa ne, na cin gashin Kansu.
Domin sun jima da tsarin gina tattalin arzikin su, wanda a yanzu s**a yi wa sauran ƴankunan kasar nan fintinkau.
Samar da ƳanSandan Jihohi ko yankunan cikar burin Yarabawa ne, musamman a yanzu da suke da dama.
Shin Shugabanni da mutanen Arewa wace fahimta s**a yi wa kalaman da Sunday Igboho, Shugaban awaren kafa kasar Yarabawa ya yi a kan tsohon Shugaban kasa Shugaba Buhari, zarge zarge da mummunan fatan da yayi masa, da kuma Kiran da yayi na cewa lokaci ya yi Yarabawa su tashi su nemawa kansu cin gashin kai da kubuta daga hannu ƳanArewa Makiyaya, Yanta’adda. Abin kaico din yayi kalamun nan ne fa a Fadar Sarkin Oyo.
Farkon adashen da mutanen Arewa za su dauka, bayan tabbatuwar wannan Ƴansandan, shine tsarewa da hana mutanen su na Arewa, musamman ma matasa masu zuwa cirani dama sana’oin zamani shiga Yankunan su. Za a rika yi musu kazafi da jifan ta’addanci.
Shin a yanzu ma, yaya tsakanin makiyayan da ke wannan Yankin da kungiyoyin su irin su AMETAKUN da sauran tsagerin kungiyoyin su? Kai hatta ma mutanen Arewa masu sahihiyar sana’oin su, wa ce barazana ce ba a musu.
Koda yake yunkurin da surutan siyasa a kan bawa jahohi ko yankunan kasar nan damar samar da Yan Sandan su, abu ne da ya dade a na yin su.
Ba dalili na rashin tsaro da ya sanya a ke bukatar wannan Yan Sandan ba, kawai dalilai ne na siyasa, wanda ya samo asali tun samun yancin Nijeriya, da kuma rigingimun cikin gida da s**a faru, k**a da yakin basasa, rigingimun siyasa da ma yunkurin neman cin gashin kai irin su Biafra da Yoruba Republic.
In har Najeriya da tafi kowace kasa a fadin Africa girman tsaro, da yawan jami’an tsaro s**a gaza shawo kan wannan rashin tsaro, ta yaya sabbin Ƴansandan Jihohi zasu kawo.
Kusan fa zamantakewar ƳanNajeriya fa na daga cikin abubuwan da ke musu tarnakin cigaban ta, domin kowane Yankin na da nasa burin a kan Najeriya.
Su fa Yankin Yarabawa burin su shine a kasa Najeriya kowa yaci gashin kansa abin da ake kira decentralization, samar da Yan Sandan Jahohi na daga cikin sa.
Babu wani Yankin da yake komabaya a Najeriyar yau sai Yankin Arewa. Yaki, talauci, komabayan harkar ilimi da lafiya dama zaman lafiya ya damalmale shi.
Babu wata kiyayya a Shugabancin siyasa na baya da na yanzu dan taimakon wannan Yankin.
Kai babu wani tsari, tunani koma hadaka da wannan Yankin ya ke da a bayyane don ciyar da Yankin gaba. Kamar yadda muka ga tsarin Yarabawa a yau, irin DAWN (Development Agenda for Western State.
Mun shirya kawar da almajirai daga kan titunan Najeriya - Sharada
Shugaban hukumar kula da ilimin almajirai ta Najeriya, Sha'aban Ibrahim Sharada ya hukumarsa ta ƙuduri aniyar kawar da aƙalla yara miliyan 10 da ke gararamba a kan titunan kasar, domin mayar da su makaranta.
Sha'aban Sharada ya ce a ƙididdigar da UNESCO ta fitar ya nuna cewa akwai kimanin yara miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, don haka ne hukumarsa ta ƙuduri aniyar magance wannan matsala.
Ya ƙara da cewa hukumarsa ta aƙuduri aniyar zamanatar da karatun almajirci ta yadda almajirai za su samu ilimin boko, k**ar lissafi da karatun boko.
Ya ce a kowace shekarar hukumar za ta samar da santoci ta hanyar yi wa makarantun tsangaya rajista don cin moriyar sabon tsarin.
''Hukumarmu za ta riƙa bai wa almajirai takardun shaidar halartar kammala karatu''.
Sha'aban Sharada ya kuma ce hukumar za ta ƙirƙiri makarantu na dare ko na ƙarƙashin bishiya domin bayar da dama mutanen da s**a girma ba su yi ilimi ba, domin su samu ilimi.
Ya ce za a inganta harkokin makarantun tsangaya domin samun damar ilimantar da almajirai ilimin zamani.
ECOWAS Ta Ɗage Takunkumin Da Ta Sanya Wa Nijar Albarkacin Watan Azumin Ramadana
ECOWAS ta ɗage takunkumin rufe iyaka da yanke wutar lantarki da ta kakaba wa Nijar.
Ƙungiyar Bunkasa Tattalin Arziki Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS, ta ɗage takunkumin da kakabawa Jamhuriyyar Nijar a sanadiyyar juyin mulki da sojoji s**a yi watanni bakwai da s**a gabata.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Nijeriya, Abdulaziz Abdulaziz ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewar saƙon da ya fitar a Yammacin wannan Asabar ɗin, hadimin Shugaban Kasar ya ce an ɗage takunkumin ne domin tausaya wa talakawan ƙasar albarkacin watan Azumin Ramadana da ya ƙarato.
Abdulaziz ya ce, “Domin tausaya wa al’umma musamman a wannan lokaci da Azumin ke gabatowa, shugabannin ECOWAS sun amince da ɗage takunkumin rufe iyaka da yanke wuta da aka ɗora wa ƙasar Nijar tun bayan juyin mulki.”
ECOWAS dai ta cimma wannan matsaya ce a ranar Asabar a yayin taron da ta gudanar a Abuja, inda kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa kasar Guinea.
Tun a farkon watan nan ne Mali da Burkina Faso da Nijar s**a sanar da ƙungiyar kan niyyarsu ta barin ƙungiyar, wanda wannan sabon lamari ne tun bayan kafa ƙungiyar a 1975.
Sai dai tun a jawabinsa na farkon Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa, “dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu.
“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” k**ar yadda Tinubu ya ƙara da cewa.
Tun a makon da ya gabata ne Shugabannin ECOWAS sauka ɗaura haramar gudanar da taro a ƙarshen wannan makon domin nazari kan takunkuman da aka kakaba wa kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar.
Ceto Kasa: Lokaci ya yi da za a koma a sake tsari, shugabanni sun gaza a Najeriya
-Kungiyar Dattawan Arewa
Kungiyar Dattawan Arewa NEF, ta bayyana cewa lokaci ya yi da za a koma kan teburin dubi domin ceto Najeriya.
Shugaban taron, Farfesa Ango Abdullahi, ya bayyana haka a wajen gabatarwa da kuma kaddamar da littafin ‘Kotu da Siyasa’ wanda Dr Umar Ardo ya rubuta a Abuja.
Ya jaddada cewa ba lokaci ne na nuna yatsa ba, sai dai a koma inda Najeriya ta dace.
Ya sake jaddada kiransa na samar da tsarin gwamnati na majalisar dokoki, yana mai bayyana tsarin mulkin shugaban kasa sama da shekaru 24 a matsayin “tsarin da ya gaza” ga Najeriya.
“Lokaci ya yi da za mu koma kan allon zane, domin a ceto kasar nan. Mun yi kasa a gwiwa sosai kuma wannan dole ne a daina. Mun gaza kanmu kuma ba mu da dalilin yin korafi.
“Musamman a siyasance, ba mu da dalilin yin korafi. Wannan taron a gare ni wata dama ce da za mu tattauna da kanmu game da gazawar da muka yi a kasa baki daya
Zargin fitar da N30bn: Ku yiwa ƴan Najeriya cikakken bayani
– Peter Obi ga FG
Mista Peter Obi na jam’iyyar Labour Party, LP, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bayyana cikakken bayani kan zargin kashe Naira biliyan 30 kowannen su ga gwamnonin jihohi 36 domin magance hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kayan abinci.
Wannan ma k**ar yadda ya ce dole ne gwamnati ta dakatar da dabi’ar rashin amfani na jefar da karanci da rancen kudi a cikin matsalolin gaggawa, da cin abinci.
Bukatar Obi ta biyo bayan ikirarin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya yi na cewa wani “rahoton da ba a tantance ba” ya nuna cewa gwamnonin jihohi sun karbi Naira biliyan 30 kowanne daga asusun tarayya domin rage wahalhalun da tattalin arziki da yunwa a yankunansu.
Sai dai Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi watsi da rahoton inda ya ce babu kanshin gaskiya a ikirari da Akpabio ya yi na cewa jihohin tarayya sun samu karin Naira biliyan 30 kowacce a waje da kason kudaden shiga da aka kayyade.
Obi, a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin sa na X a ranar Juma’a, ya ce ya k**ata a bayyana cikakkun bayanai game da yadda aka raba kudaden don amfanin shugabanci nagari da gaskiya.
A cewarsa, hakan zai baiwa talakawan da ake son tallafa musu, su bi su da kuma tabbatar da an yi amfani da shi yadda ya k**ata domin amfanin su.
Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su tabbatar da cewa an zuba jarin da aka samu cikin gaskiya da adalci a cikin sana’o’in da za su yi amfani da su domin rage wahalhalun da suke ciki.
“Kwanan nan, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa wani gagarumin tallafin kudi na Naira Tiriliyan 1.1, wanda ya kai Naira Biliyan 30 kowanne an baiwa gwamnonin Jihohin kasar nan domin su taimaka wajen magance wahalhalun da kasar nan ke ciki.
“Yayin da za a yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta bayar da irin wannan gagarumin tallafi, duba da irin mawuyacin halin da mutane ke ciki, ya dace, domin samar da shugabanci na gari da kuma tabbatar da gaskiya, a yi karin bayani kan yadda aka raba tallafin, domin jama’a, talakawan da ake son tallafa musu, su bi su, su tabbatar an yi amfani da shi yadda ya k**ata domin amfanin jama’a.
Matakai takwas da za ku bi don sayen shinkafar kwastam mai rahusa
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya kwastom ta fara sayar da shinkafa kan farashin mga 'yan kasar.
Matakin na daga cikin ayyukan rage radadin tattalin arzikin da 'yan NAjeriya ke fuskanta
Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya shaida wa BBC cewa shinkafar da hukumar ke sayarwa, shinkafa ce da jami'an hukumar s**a k**a a lokacin da aka shigar da ita kasar ba bisa ka'ida ba.
Ya ce hukumar ta kai shinkafar kotu inda s**a samu sahalewar kotu domin sayar da ita ga talakawan kasar.
Abdullahi Maiwada ya ce an fara sayar da sayar da shinfara ne a yau Juma'a a jihar Legas, a matsayin gwaji kafin daga baya hukumar ta fadada aikin zuwa sauran jihohin kasar da take da irin wadannan kaya da ta k**a.
Kakakin hukumar ya ce suna sayar da buhu mai nauyin kilogiram 25 na shinkafar a kan kudi naira 10,000.
Matakan da hukumar ke bi wajen sayar da shinkafar
Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na bin wasu matakai na tantancewa kafin ta sayar da shinkafar ga al'umma k**ar haka.
Amfani da NIN - Ya ce hukumar na amfani da lambar da ke jikin katin dan kasa ta NIN wajen tantance mutanen da take sayar wa shinkafar, don haka dole sai wanda ke da lambar NIN zai samu damar sayenta.
Mutanen da ke kusa da inda hukumar ta k**a kaya- Abdullahi Maiwada ya ce hukumar na sayar da shinkafar ne kawai ga mutanen da ke kusa da inda ta k**a shinkafar, ''don haka duk mutmin da ya zo daga nesa ba zai samu sayen shinkfara ba'', in ji shi.
Masu sana'ar hannu - Kakakin hukumar Kwastam din ya ce daga cikin rukunin mutanen da hukumar ke sayar wa shinkafar su ne masu sana'ar hannu. Ya ce an yi hakan ne domin tallafa musu wajen bunkasa sana'o'insu.
Malaman makaranta - Hukumar ta ce malaman makaranta na daga cikin rukunin mutanen da za su amfana da sayen da sayen shinkafar da hukumar kwastam ke sayarwa.
Masu sharar t**i - Abdullahi Maiwada ya kara da cewa su ma mutanen da ke sharar t**i na daga cikin rukunin mutae da hukumar ba domin sayar musu da shinkafar.
Mutanen da s**a fi tsananin bukata - Kakakin hukumar ya shaida wa BBC cewa dama makasudin sayar da shinkafar shi ne rage wa al'immar radadin tsadar rayuwa da ';yan kasar ke fuskanta, don haka ya ce s**a fi bayar da fifiko kan mutanen da ke cikin tsananin bukata.
Mata - Wasu rukunin mutanen da za su amfana da shinkafar kwastam din mai cike da rahusa su ne mata, musamman marasa karfi, wadanda ke rike da kananan yara.
Kungiyoyin addini - Kungiyoyin addini na daga cikin al'umomin da za su amfana da wannan sayar da shinkafa da hukumar kwastam ke yi, k**ar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Hukumar ta kuma gargadi 'yan kasar da ke da aniyar sayar da shinkafar ga 'yan kasuwa, da su guji yin hakan.
Abdullahi Maiwada ya ce duk wanda ya yi haka zai fuskanci fushin hukumar, sannan kuma ya ce hukumar za rika sanya idanu a kasuwanni domin ganin ko 'yan kasuwa za su sayi shinkafar domin sayarwa.
Tsadar Rayuwa: Babbar Matsalar Tinubu Gwamnoni Ne,
-Kungiya Ta Fadi Abin da Gwamnonin Ke Yi a Boye,
An zargi gwamnonin jihohin Najeriya da kawo cikas a tsare-tsaren Shugaba Tinubu musamman a wannan yanayi da ake ciki Wata Kungiyar ta ce gwamnonin ke dakile shirin shugaban wurin inganta tattalin arzikin kasar don ganin ya tsaya da kafafunsa Shugaban kungiyar, Dakta Godwin Abutu shi ya bayyana haka a jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu a birnin Tarayya Abuja
FCT, Abuja – Wata kungiyar kare al’umma a Najeriya ta zargi gwamnonin jihohi da kawo cikas a kokarin Tinubu na kawo sauyi a kasar. Kungiyar ta ce gwamnonin ke dakile shirin shugaban wurin inganta tattalin arzikin kasar ya tsaya da kafafunsa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Abuja a jiya Alhamis 22 ga watan Faburairu, cewar Tribune.
Shugaban kungiyar, Dakta Godwin Abutu ya zargi gwamnonin da alkawarin iska musamman a halin da ake ciki, People Daily ta tattaro.
A cewarsa: “Dukkanmu mun yi ta kiran a cire tallafin mai a kasar, ganin yanzu an cire dole mu tsaya mu tabbatar da hakan." Sun bayyana babbar matsalar gwamnonin Ta kara da cewa: “Babbar matsalar gwamnonin ita ce madadin su yi amfani da tsarin wurin kawo ci gaba a yankunansu amma sai suke kara lalata lamarin wurin rike albashin ma’aikata.
“A ran Alhamis mun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce an bai wa ko wane gwamna biliyan 30 don karya farashin kaya, amma har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
Kungiyar har ila yau, ta ce ana iya tuna a watan Disambar 2023 an ba da kayan abinci amma sai s**a rarraba kayan ga wadanda s**a sani ba tare da mabukata sun samu ba.
Matasa sun yi barazana a Borno
Kun ji cewa wasu matasa sun fito zanga-zanga a jihar Borno tare da yin barazana ga gwamnati kan halin kunci da ake ciki. Matasan da s**a gudanar da zanga-zangar a garin Dikwa da ke jihar sun yi barazanar shiga kungiyar Boko Haram idan ba a dauki mataki ba. Wannan na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke cikin mawuyacin halin kuncin rayuwa da tsadar kayayyaki.
Jama’a Sun Daka Wa Motocin Abinci Wawa A Hanyar Abuja
An yi awon gaba buhunan shinkafa da kwalayen taliya da sauran kayan abinci daga motocin
Jama’ar gari sun tare hanya suna tare motocin kayan abinci musamman na kamfanin Dangote suna daka musu wawa a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar Alhamis.
Wani ganau, Alhassan Abdullahi, ya shaida wa wakilinmu cewa ’yan daban sun tare motoci da dama da s**a dauko kayan abinci daga Abuja zuwa Kaduna a daidai Mahadar Suleja da ke kan hayar.
A cewarsa, mutanen sun wasushe buhunan kayan abinci, musamman shinkafa daga motocin kafin sojoji su kawo dauki.
“Sai dai sojoi s**a so s**a fara harbi a iska domin tarwatsa bata-garin, amma duk da haka mutane da dama a cikinsu sun yi awon gaba buhunan shinkafa da kwalayen taliya da sauran kayan abinci.
“Ga shi mun ji an ce gobe yan acaba za su yi zanga-zangan da s**a shirya yi jiya, amma s**a dage,” in ji shi.
Sojoji sun yi gargaɗi ga masu kiran juyin-milki a Nijeria
Rundunar sojin Nijeriya ta yi gargadi ga masu kira da a yi juyin mulki saboda wahalhalun da ake fuskanta a kasar.
A halin yanzu, Najeriya na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a tarihi, lamarin da ya janyo zanga-zanga a sassa daban-daban na kasar.
Wasu dai na cewa idan ba a magance al’amura a kan lokaci ba, to sojoji za su iya hamɓarar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Da yake mayar da martani, babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce masu yin wannan kira ba sa kaunar kasar, yana mai gargadin cewa doka za ta yi aiki a kan su.
Musa ya ce rundunar sojin kasar za ta ci gaba da yin abin da ya k**ata domin kare dimokuradiyyar kasar.
Daily Trust ta rawaito cewa Musa ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan da ya kaddamar da babbar kofar shiga runduna ta 6, da sojojin Najeriya da na jami’an ‘yan sanda, dukkansu a hedikwatar shiyya da ke Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers.
Yayin da ya amince cewa kasar na fuskantar kalubale, ya ce kiraye-kirayen juyin mulkin bai dace ba saboda kasashe suna samun ci gaba da sauri ne a karkashin tsarin dimokuradiyya..
Dalilan da s**a sa za mu binciki gwamnatin Buhari - Ndume
Majalisar Dattijan Najeriya ta bayyana dalilan da ya sa ta yanke shawarar binciken tsohuwar gwamnatin Buhari.
A zaman da ta yi ranar Talata ne majalisar ta tsayar da shawarar gudanar da bincike kan yadda tsohuwar gwamnatin ta kashe wasu kudi da s**a kai tiriliyan 30 da ta karba daga Babban Bankin kasa CBN.
Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno kuma mai tsawatarwa na Majalisar Dattijan, ya ce ƴan majalisar na da damar yin bincike, kuma a cewarsa " binciken zai soma ne daga CBN"
Ya kuma ce binciken na iya faɗaɗa ya kai har inda ba a yi tsammani ba.
Sanata Ndume ya ce za su bibiyi bayanai na wadanda aka ba kuɗin da kuma yadda aka kashe su da abin da aka yi da kudaden.
Ya ce binciken zai iya wuce tunanin mutane na za a binciki gwamnatin Buhari, "wataƙila abin ya wuce inda ake tsammani, kawai dai ba mu sani ba sai an yi binciken za a gane," in ji shi.
Kuɗaɗen dai na bashi ne da Babban Bankin Najeriya ya ba gwamnati domin gudanar da ayyuka ko biyan wasu buƙatu.
Sanata Ndume ya ce sai bayan an karɓo kuɗaɗen kafin gwamnatin ta gabatar wa majalisa domin neman amincewarta, wanda ya ce ba ta da hurumi.
"Kundin tsarin mulki ya ba mu dama ne mu amince da abin da za a yi ba abin da aka riga aka yi ba," in ji Sanata Ndume.
Majalisar dattijan ta yi iƙirarin cewa fitar da kuɗaɗen da su ba bisa ƙa'ida ba ƙarkashin jagorancin tsohon shugaban Babban Bankin Godwin Emefiele ne ya jefa ƙasar cikin ƙarancin abinci da ta ke fuskanta.
Majalisar ta cimma matsayar kafa kwamitin da zai gudanar da bincike kan yadda aka kashe kudaden da ba a ba majalisar damar sanin haƙiƙanin yadda bayanan yadda aka kashe su ba.
Kwamitin zai kuma binciki naira tiliyan 10 na shirin tallafa wa manoma na Anchor Borrowers da kuma dala biliyan 2.4 daga dala biliyan bakwai na sauran shirye-shiryen gwamnati na tallafi.
Tsadar Siminti: Gwamnati Ta Yi Barazanar Daukar Mataki 1 Da Zai Jefa Dangote Da BUA Cikin Matsala
Gwamnatin tarayya ta ce tana duba yiwuwar bude iyakokin kasar don fara shigowa da siminti da nufin karya farashinsa a kasuwanni Wannan gargadi ne da ministan gidaje da raya karkara, Arc. Dangiwa ya yi wa kamfanonin da ke sarrafa siminiti a Najeriya Dangiwa ya ce ma damar Kamfanonin s**a gaza karya farashin simintinsu, to za su ba da damar shigo da shi daga ƙasashen waje don ya zama gasa
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ce za ta duba yiwuwar bude iyakokin kasar don shigo da siminti idan masu sarrafawa a Najeriya s**a ki rage farashin sa a kasar. Gwamnatin ta ce ba za ta lamunci karin kudin siminiti saboda babu wani sinadarin hada siminti da ake amfani da dala wajen sayo shi, The Nation ta ruwaito.
Ministan gidaje da raya karkara, Arc. Ahmadd Dangiwa, ya ce kayan hada simitin da s**a hada da limestone, laka, kasar silica da gypsum dukkansu a Najeriya ake samun su.
Dangiwa ya bayyana hakan a ranar Talata, 20 ga wata a Abuja, a wani taron gaggawa da gwamnati ta gudanar da masu kamfanonin sarrafa siminiti a kasar. Ya ce bai k**ata kamfanonin su fake da kudin iskar Gas ba saboda shi ma a Najeriya ake samun sa, kuma babu uzuri na cewar kudin hakar sinadarai sun karu. Ministan ya ce tun farko an hana shigo da siminti Najeriya saboda ba kamfanonin cikin gida damar fadada kasuwancin su.
Amma ya ce idan gwamnatin ta bude iyakokin kasar aka fara shigo da siminti gadan-gadan, watakila hakan zai ankarar da kamfanonin irin illar da za su fuskanta. KARA KARANTA WANNAN Aiki na shine na biyu mafi wahala a duniya, Gwamnan CBN Cardoso Dangiwa ya kuma ba su misali da kamfanin BUA wanda ya ce a shirye yake ya karya farashin siminiti zuwa naira dubu bakwai. Da wannan ya ce bai ga dalilin da zai sa sauran kamfanonin su ƙi amince da rage farashin su ba k**ar yadda BUA ya yi alkawari.
Dangiwa ya fadawa kamfanonin cewa: "Ba Najeriya ce kadai ke fuskantar matsalolin da kuka zayyana ba, hasali ma wasu sun zarce namu, amma matsayin masu kishin kasa, dole mu saukakawa mutane. "Ya zama wajibi ku yi karatun ta-nutsu domin gwamnati ta hana shigo da siminti saboda a taimake ku, yanzu kuma muna da bukatar naku taimakon." Tun da fari, shugaban sashen kasuwanci na kamfanin simintin Dangote, Rabiu Umar ya dora alhakin tashin farashin siminiti akan karin kudin gas da kayan aiki. A karshe dai ministan ya ce gwamnati za ta kafa kwamiti da zai duba yiwuwar kayyade farashin siminiti da nufin karya farashinsa a kasuwa.
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa kamfanonin da ke sarrafa siminti sun kafa wa Shugaba Tinubu sharuda kafin su rage farashin simintin. Shugaban kungiyar masu sarrafa simintin, David Iweta ya nemi Tinubu da ya dawo da dokar da tsohon shugaban kasa, marigayi Umaru Musa Yar'adua ya kafa akan samar
Sanatoci Sun Lalubo Yadda Gwamnatin Buhari Ta Haddasa Asarar Naira Tiriliyan 17
-Gwamnati Ta Gaji, Ta Shirya Binciken Bashin N23tr da Emefiele Ya Ba Gwamnatin Buhari
Ministan tattalin arziki ya ce gwamnatin Bola Tinubu ba za ta yi saurin biyan bashin da CBN ya Najeriya aro a shekarun baya ba Wale Edun ya nuna dole sai an binciki kudin da gwamnatin tarayya ta karbi bashi daga babban bankin kafin a fara biyan tukuna Gwamnati mai-ci tana kokarin tsaida salon da Muhammadu Buhari ya rika bi wajen samun tiriliyoyin kudi daga CBN
Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyanna niyyarta na binciken Naira tiriliyan 23 da babban bankin kasa na CBN ya ba Najeriya aro. Ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun ya shaida haka a wajen wani taro da ma’aikatarsa ta shirya jiya a cewar jaridar Punch.
Gwamnati za ta kara hako danyen mai Wale Edun ya kuma shaida cewa an bukaci kamfanin NNPCL ya kara adadin danyen man da ake hakowa saboda kudin shiga ya karu. Ministan ya bayyana niyyar gwamnatinsu na gabatar da kudiri a majalisar tarayya domin a inganta harajin da ake tatsa daga jama’a. Idan har an soke tsarin afuwar biyan haraji k**ar yadda majalisa ta bukata, Edun ya ce za a huta da karbar aron kudi a hannun CBN.
Gwamnatin Najeriya ta ci bashin makudan kudi daga hannun bankin CBN a lokacin Buhari lamarin da aka soka a kasar.
Edun wanda aka nada a Yunin bara ya ce sai sun yi bincike kafin su fara biyan bashin kudin da aka karba daga hannun bankin CBN.
Babban bankin kasa na CBN ya nuna dole ayi watsi da tsarin ba gwamnati aron kudi kuma abin da muka amince da shi kenan." "Mun k**a hanyar, an gaji kusan N22.7tr da za a biya. Muna bincike, k**ar zan biya bashi ne sai in bincika nawa ake bi na."
Kwanaki sabon gwamnan CBN, Yemi Cordoso ya tabbatar da za su daina ba gwamnati aro har sai sun dawo da bashin da s**a karba. Majalisa ta ce Buhari ya jawo asara Ana da labari Sanata Muhammad Sani Musa ya soki afuwar da aka yi wa manyan kamfanoni wajen biyan haraji a shekarun baya. Kwamitin majalisar dattawa ya ce ya k**ata a dakatar da shirin a kawo sabon tsarin karbar haraji ganin FIRS ta rasa kusan N17tr
Hukumar kwastam ta Najeriya za ta raba kayan abincin da aka k**a a faɗin ƙasar
Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta ce tana shirin raba wasu kayayyakin abincin da aka k**a a faɗin ƙasar, yayin da ake ci gaba da fama da matsalar karancin abinci a kasar.
A cewar jami’in hulda da jama’a na hukumar, CSC Abdullahi Maiwada, za a raba kayan abincin ne bayan an tabbatar da cewa mutane za su iya amfani da su.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce an ɗauki matakin ne "domin rage wahalhalun da 'yan Najeriya ke fuskanta da kuma inganta hanyoyin samun kayan abinci, hukumar kwastam za ta taimaka wajen raba kayan abincin da hukumar ta k**a kai tsaye.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a sanar da tsarin da za a yi amfani da shi a ofisoshin hukumar da ke fadin kasar, tare da jajircewa wajen tabbatar da adalci. Mun sha alwashin cewa za a gudanar da wannan aikin domin tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga waɗanda s**a fi bukata.”
A Gane Mana Hanya: Kan Kudirin Tsarin Faraminista A Najeriya:
Shugaban Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Liberty Ya Bukaci A Gudanar Da Kuri'ar Raba Gardama na Jin Ra'ayin Jama'an Najeriya
Shugaban Rukunin Gidajen Radio Da Talabijin na Liberty Dakta Ahmed Tijjani Ramalan Ya Goyi bayan kudirin dokar da aka gabatar gaban Majalisar Dokoki ta kasa dake neman a mayar da Mulkin Kasar nan karkashin Tsarin Faraminista.
Kudurin dokar wanda ‘Yan majalisar wakilai 60 s**a Gabatar ya rika ya tsallake karatu na farko a zauren majalisar a ranar Larabar da ta gabata.
Kamar Yadda Aka sani a halin yanzu Najeriya na na Amfani ne da tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken Iko.
Bambancin da ke tsakanin Salon Mulkin biyu ya ta’allaka ne kan yadda ake zabar shugabanni.
A karkashin tsarin shugaban kasa mai Cikakken iko Al'ummar kasa ne ke zabar shugaban kasa kai tsaye, yayin da a tsarin Faraminista kuwa ‘yan majalisa, ne ke zaben Shugaban Gwamnati (Wato firaminista) inda ake Raba madafun iko.
A Zantawa da Muryar ‘Yanci a ranar Asabar Shugaban Kamfanin ATAR Commucation Da Ya Mallaki Gidajen Rediyo da Talabijin na Liberty Dakta Tijjani Ramalan, ya bayyana kudirin dokar a matsayin “Mataki mai matukar muhimmanci wajen sake fasalin siyasar Najeriya kasancewar kashi 99 Cikin 100 na ‘yan Najeriya na bukatar ganin an aiwatar da wannan Sauyin"
Akan haka ya bukaci kungiyoyin fararen hula da kuma ‘yan Najeriya masu kishin kasa su shirya taruka domin tattaunawa da yin muhawara akan wannan kudurin Doka, tareda kira da a amince da shi ta hanyar bukatar hukumar zabe Mai zaman kanta INEC ta gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a Karkashin sa idon Majalisar Dinkin Duniya.
To sai dai Wasu na ganin cewa kasancewar Majalisun kasa da na Jihohi ne manyan masu cin gajiyar Tsarin Shugabancin Mai Tsada zasu iya kawowa yunkurin Cikas.
Ramalan ya ce tsarin shugaban kasan da ake amfani da shi a halin yanzu ba shi da wani Alfanu ga Al'ummar kasar nan, yana mai cewa 'yan Najeriya ba za su iya "jiran har nan da wasu shekaru 7 ba" ana jiran wannan Kudirin Doka da 'yan majalisar wakilai 60 s**a gabatar ba.
Yace k**ata yayi a lokacin zaben Raba Gardaman ayi kokarin ganin an amince da Tsarin ‘Yan Majalisu a Shiyyoyin Siyasa Shida, tareda baiwa Kananan Hukumomin Kasar nan cikakken ‘Yancin Cin gashin kai, a kuma tabbatar an fara Amfani da tsarin daga Shekarar 2027.
"Ina karfafa wa 'yan Najeriya gwiwa akan su shiga cikin muhawarar ta hanyar tarurruka a Jihohi, garuruwa da Kananan Hukumomi da Gundumomi da mazabu domin ganin an gudanar da wannan tsarin tareda su"
Da hakan ne ‘Yan Najeriya zasu yanke shawarar tafiyar da tsarin majalisar tare da wasu gyare-gyare ko kuma fito da tsari mafi kyau a Najeriya,” in ji Ramalan.
"Kamata yayi Duk wani tsarin da za'a Samar ya magance matsalolin da muke fuskanta, tareda daukan Darasi daga kasashen Burtaniya, Swizland da wasu kasashen da suke da kyakyawan Shugabanci.
"Abin da ke da mahimmanci shi ne samar da kyakkyawan shugabanci wanda bashi da tsada kuma akwai bukatar ’yan Najeriya na gida da na Mazauna kasashen waje su bada gudunmawa domin kawo sauyi a kasarmu"
Dakta Ramalan ya rike muk**ai daban-daban daga 1990 zuwa 2023, Daga ciki ya taba rike mukamin a Shugaban manyan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Kaduna, Daraktan Hulda da kafafen yada labarai na kwamitin yakin neman zabe mai zaman kansa, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na kasa a jihar Kaduna, mai ba da shawara na musamman a ma'aikatar yada labarai ta jihar Kaduna. Ya kuma taba rike Shugaban Rusashiyar Jam'iyyar UNCP daga 1990 zuwa 2023
Har ila yau, ya taba zama shugaban hukumar zartarwa na Gamayyar ma'aikatan dake kula Tekun Najeriya, ya kuma taba rike mukamin shugaban hukumar kula da Tsaron teku da kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya NIMASA, mukamin da ya rike har zuwa shekarar 2007.
Click here to claim your Sponsored Listing.