Koyan Mining, Crypto da Hausa

Koyan Mining, Crypto da Hausa

Hammado TV - YouTube 19/11/2023

Subscribe this YouTube channel my brother's and sisters https://www.youtube.com/://www.youtube.com/

Hammado TV - YouTube Share your videos with friends, family and the world

Kamisu Idris - YouTube 13/09/2023

Kamisu Idris - YouTube Kamisu Idris

06/09/2023

Za'a gabatar da sallar janazan Marigayi Sheikh Abubakar Giro da misalin karfe biyu na rana (2:00pm). A masallacin Idin Sarki dake garin Argungu a jahar kebbi, Naijeriya Insha Allah

06/09/2023

Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un

Allah ya yiwa Sheikh Abubakar Giro Argungu Rasuwa.

Marigayin ya rasu ne bayan jinya da yayi na 'dan lokaci a Birnin kebbi. Za'a masa sallar janaza Gobe alhamis insha Allah. Zamu sanar da lokaci nan gaba.

Daga Ibrahim Baba Suleiman
JIBWIS NIGERIA

12/08/2023

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raajiun!

Our prayers are with the victims of Zazzau Central Masjeed's roof collapse during Asr prayer yesterday, where around 10 people passed away & many were injured. We pray to Allah (SWT) to accept the deceased as Shuhadaa & heal the injured.

Photos from Koyan Mining, Crypto da Hausa's post 21/07/2023

HOTUNA: Maimartaba sarki Hadejia Alh Dr. Adamu Abubakar Maje C.O.N da tawagarsa wanda ta kunshi shugaban karamar hukumar Hadejia da tsoffin masu bawa gwamna sharawa da, Hakimai.

Sun ziyarci Jami'ar As-salam Global University Hadejia, (AGUH).
domin ganewa idonsa yadda aikin yake gudana.

Maimartaba sarkin wanda yasamu tarba daga Manajan site din,
Baffa Maina Hadejia, Amadadin Director Project na kungiyar Izala ta kasa Engr. Ashiru Babandede.

Ya zagaya cikin site din domin ganin yadda aikin yake gudana, maimarta sarki yayi farin ciki tare da, rokon Allah yasaka dukkanin wadanda suke bada gudunmawarsu domin wannan aikin alkhairi Amin.

14/07/2023

Abubuwan da Manzon Allah (S) ya hana game da kaburbura (4):

16. Kwanciya a kan kabari domin wannan cutarwa ne ga mai shi. In ji Manzon Allah (S).
17. Yin tafiyayya don ziyarar kabari daga wuri mai nisa.
18. Addu'ar neman bukata a wurin kabari. Idan Allah aka roka kenan. Yin hakan bidi'a ne. Idan kuwa mai kabarin aka roka ya wuce bidi'a ya zama Shirka.

Bari mu dakata a nan mu biyo da bayanin yadda hanin yake a cikin Hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam

14/07/2023

MAGANIN KAMBUN IDO DA SAURAN CHUTUTTUKA :

TAMBAYA TA 2980

Assalamualaikum Allah ya gafarta malam don Allah malam neman shawara nake, yau kusan shekara uku kenan ina fama da rashin lafia haryanzu ban warke ba sai dai dan sauki wanda be wuce na kwana 1 zuwa 2 ba, tunfarko naje asibiti anyi duk awon da zaayi baa samu komai ba har likitocin suna ganin kamar kawai ina sama kaina ciwo ni kuma inajin abinda nakeji bayan haka ta yadda nakiyiwa mutane bayanin abinda nakeji yasa wasu s**a gane halin da nake ciki akace ciwon yana da alaka da aljannu daga nan na shiga neman maganin iska sosai malam har bansan adadin maganin da nayi amfani dashi ba har karatu anyiman,malm har takai ga na daina neman ko wane irin magani na hakura ina ta addua da duk zikirorin da akeyi don neman kariya malm banajin waka banayin kallo don Allah malam ni yanzu shawara nake nema sabo da haryanzu inajin jiki da yawan ramewa kamar me wata babbar rashin lafia kuma duk ciwon da ake zaton zai sani wannan ramar anyi awo babu shi ina sannan kullum cikin faduwar gaba nake kusa wannan faduwar gaban shine ke zoman da duk sauran ciwon da nake ji,malam Allah ya kara basira nagode.suna na Ibrahim zubairu daga katsina.

AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Akwai chututtuka da dama wadanda Dan Adam ke iya fama dasu har tsawon lokaci amma ido ko na'ura basu iya ganinsu. Hakanan koda jinin mutum aka gwada ba za'a gano komai ba.

Daga cikin wadannan chutukan akwai Shafar aljanu (Massul jinni) da Sihiri da kambun ido (wacce wasu suke cewa maita). Kuma kowacce daga nau'o'in nan takan zo bisa siffofi da yanayi mabambanta.

Amma kasancewar anyi maka ruqyah sau daya ko biyu ba'a ga aljani ya motsa ba, shima bazai zama alamar dake tabbatar maka cewa babu aljani acikin jikinka ba.

Hakanan idan sihiri ne, akwai hanyoyin da ake bi domin fahimtar nau'insa, idan aka fahimci nau'insa in sha Allahu za'a fi sanin hanyar maganceshi.

Amma ga wata fa'idah nan ka jarraba :

Ka samo lemon nan da ake kiransa TANGERINE guda 57, idan baka sameshi ba, kayi amfani da lemon tsami guda 56 sai ka dauki kowanne ka yankashi gida biyu, (ba zaka matseshi ba) sai ka zubasu duk acikin ruwa mai kyau (ruwan sama zaka nemo, shine yafi).

Ka tofa Suratul Fatiha 57, Ayatul kursiyyi 313, Qul huwallahu Qafa 114. Suratul Falaq 114. Suratun Nas 114.

Idan ka kammala wannan tofin, sai ka ajiye ruwan nan ya kwana ahaka.sai washe gari zaka fara amfani dashi. Bayan kowacce sallar farilla kasha kofi 1 ko biyu, sannan kullum zaka shafe jikinka da wannan ruwan safe da dare.. Idan ruwan ya Qare sai ka zubar da wannan bawon lemon awaje mai tsarki ko ka binneshi (saboda albarkacin tofin da akayi akansu, kada ka zubar a bola)

In sha Allahu zaka ga abun mamaki da albarkar Alqur'ani. Idan sihiri ne ajikinka, zai karye cikin sauri. Idan kuma aljanubne, daga lokacin da ka fara wannan aikin zasu fara Qonewa suna mutuwa, suna fita daga jikinka da izinin Allah. Idan kuma sharrin maita ne (wato kambun ido) da yardar Allah zaka samu lafiya, lafiyar jikinka da karfin jikinka zai dawo.

Don Allah ku bayar da wannan fa'idar ga duk Budurwar da ta dade bata samu mijin aure ba, ta sanadiyyar sihiri ko sharrin aljanin soyayya (Ashiqul jinn) ko mutumin da ya dade yana fama da wata jinyar da aka kasa gano maganinta,. Ko irin family din nan wanda zaka ga kusan kowa yana da Aljanu ajikinsa (koda aljanun gado ne ko na sihiri) In sha Allahu duk zasu samu lafiya.

Domin neman Qarin bayani ko shawarwari ko hadaddun magunguna ana iya tuntubar Zauren Fiqhu akan wadannan lambobin 07064213990 09020317676 ko kuma ta adireshinmu na email [email protected].

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (31/05/2022).

14/07/2023

Innah lillahi wa Innah ilaihir raji'un

Duk Mai Rai MAMACINE

A Yau Juma'a Muntashi Da Rasuwa Malam Amiru Maja Baki

Shine Yake Jawa Sheikh Lawan Abubakar Shuaib Triumph Baki A Tafsir Dinsa

Za'ayi Janazar A Masallacin Juma'a Na Triumph Fagge Kano

Lokaci Ana Idar da Sallar Juma'a

Yan Uwa Ku Saka Shi Cikin Addu'ar Ku

Muna Rokon Allah Ta'ala Ya Bashi Aljannah Firdausil Aalah Amin

Koyan Mining, Crypto da Hausa Koyan Mining, Crypto da Hausa

14/07/2023

I have reached 12K followers! Thank you for your continued support. I could not have done it without each of you. 🙏🤗🎉

Photos from Koyan Mining, Crypto da Hausa's post 10/05/2023

INNÀ LILLAHÍ WA'INNÀ ILAIHÍ RAJI'UÑ.

Dattijo Malam Ibrahim Bura, Wanda Ya Riƙi Sheikh Kabir Gombe Ya Rasù A Gombè

Allah Ya Yi Wa Dattijo Malam Ibrahim Bura, Wanda Shi Ya Riƙi Sheikh Kabir Gombe Rasùwà Jiya Talata.

Marigayi Ibrahim Bura Wanda Ke Zaune A Unguwar Pantami Kuma Yake A Matsayin Uba Ga Sheikh Kabiru Gombe Tun Kuruciyarsa.

Añ Yí Jana'izarsa Da Misalin Karfe 10:00 Na Safiyar Gobe A Masallaciñ A Babban Masallacin Bølari, Gombè.

Allah Ya Jikansa Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa

Photos from Koyan Mining, Crypto da Hausa's post 01/05/2023

SHUGABAN JIBWIS NA ƘASA SHEIKH BALA LAU YA GABATAR DA TA'AZIYAR RASUWAR SHEIKH KABIR AHMAD AZARE

Daga Abdussalam Muhammad Auwal

Ranar Lahdi 30/4/2023 tawagar ƙungiyar Izala ta ƙasa ta samu isowa garin Azare don gabatar da ta'aziyar rasuwar Marigayi Sheikh Kabir Ahmad Azare wanda ya rasu bayan fama da jinya. Kafin rasuwar sa shine Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Bauchi, kuma Shugaban Majalisar Malamai na Shiyyar Katagum.

Tawagar wacce ke ƙarƙashin jagorancin Shugaban IZALA na jihar Kano Prof. Abdullahi Saleh Pakistan sun gabatar da ta'aziyar ne bisa wakilcin shugaban ƙungiyar na ƙasa Sheikh (Dr.) Abdullahi Bala Lau dake ziyarar aiki yanzu haka a ƙasashen ƙetare.

Baya ga jagoran tafiyar Prof. Abdullahi Saleh Pakistan, daga cikin ƴan tawagar akwai babban sakataren JIBWIS na ƙasa Sheikh (Dr.) Muhammad Kabiru Haruna Gombe, sakataren ƙungiya na jihar Kano, Daraktan Agaji ma Jihar Kano sai kuma Admin Sec. na JIBWIS Gombe State da sauran su.

Tawagar ta samu ƙyaƙƙyawar tarfa daga manyan Malamai shugabannin JIBWIS na ƙaramar hukumar Katagum, wanda s**a haɗa da shugaban ƙungiyar Alhaji Ibrahim Attah, da Shugaban Majalisar Malami Malam Magaji Bappha Sulaiman tare da Sakataren sa Malam Adamu Musa Shabiri, sai kuma National Secretary na Working Committee Malam Lamara Azare, da Ɗan Masanin Azare Alhaji Aminu Ibrahim (Deputy National Logistic Officer na Majalisar Agaji) da sauran Malamai sa Shugabanni.

Da yake jawabi yayin ziyarar, sakataren JIBWIS na ƙasa Sheikh Kabir Gombe, yayi alƙawarin sanar da Shugaba Bala Lau don ɗaukar nauyin auren ƴaƴan Marigayin mata guda uku da za ayi sati mai zuwa. Haka nan yayi alƙawarin samarwa ƴaƴan marigayi da s**a kammala karatu aikin yi don kulawa da gidan, kamar yadda uwar ƙungiyar ta saba yi ga mutane da dama. Daga ƙarshe yayi ƙira da cewa duk sanda wani abu ya taso ayi ƙoƙarin sanar da uwar ƙungiyar ta ƙasa don ɗaukar matakin daya dace.

A nasa jawabin, Shugaban tafiyar Prof. Pakistan bayan addu'o'in neman gafara ga Sheikh Kabir Azare, yayi ƙira ga ƴaƴan sa da su dage wajen yin addu'a ga mahaifin na su kamar yadda musulunci ya tanadar, daga ƙarshe ya h**e su da su cigaba da sadar da zumunci ga ƴan uwan mahaifin na su don samun dacewa daga wajen Allah.

Da yake mayar da jawabi, Shugaban JIBWIS na ƙaramar hukumar Katagum Alhaji Ibrahim Attah, yayi godiya ga Sheikh Bala Lau ya naɗa tawaga musamman don zuwa ta'aziyar, ya kuma yi addu'ar yadda s**a zo lafiya Allah Ya mayar da su gida lafiya.

Sauran wanda s**a gabatar da jawabai yayin ziyarar sun haɗar da Malam Lamara Azare da Malam Shamsu Sh*tu Azare.

Muna addu'ar Allah ya mayar da su gida lafiya, ya saka musu da alkhairi bisa wannan ta'aziyar da s**a zo mana.

Allah Ya jiƙan Malam, Ya masa rahamah, Yasa aljanna ce makomar sa. Muma idan tamu tazo Allah Ya sa mu cika da kyau da imani.

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

01/05/2023

Najeriya kasarmu ta gado
Na saurari muryar Ambasada Olaniyo; jakadan kasarmu a Sudan inda ya ce ofishin jakadancinsa ba shi da hannu sam sam cikin maganar daukar motocin da za su kwashe dalibai. Kai tsaye Min. for Humanitarian da NEMA suke hulda da kamfunan motocin.
Yanzu haka dai tun jiya motoci na tsaye dauke da yan Najeriya amma suna jiran a tura masu deposit sannan su tashi.
Dalibanmu da suke kan bodar Egypt su kuma suna jiran clearance daga hukumar Najeriya kafin su samu izinin shiga.
Duk shugaban da Allah ya ba shi ikon ya kashe cuwa-cuwa (corruption) a Najeriya to, wannan zai yi nasarar mulki.
Ya Allah! Ka ba mu mafita ga matsalolinmu, ka yaye mana damuwarmu.

17/10/2020
29/08/2020
21/06/2020

Ku saurari wannan sako daga bakin malam. Allah ya bada lada. Ameeeen!

08/03/2020

Malam Jafar Adam Akan kashe mutum

08/03/2020

Malam Jafar Adam, Akan kisan Mutum

03/03/2020

Assalamu Alaikum Warahmatullah

Muna farin Cikin Gayyatar Al'ummar Musulmi Zuwa Wajen Muhadara da za'a Gabatar Kamar Haka:

👉 Rana: Yau Talata 03/03/2020

👉 Wuri: Masallacin Dan Fodio Unguwan Sunusi

👉 Lokaci: Bayan Sallar Magrib

⛔ Maudu'i: Harkar Fana-finai Sana'a Ko Fasadi

💎 Mai Gabatarwa: Sheikh Musa Yusuf Assadussunah (Hafizahullah)

Allah Yabada Ikon Halarta da Amfanuwa da Abunda Za'a Saurara

01/03/2020

Ina muku barka da zuwa wannan shafin namu, insha Allah in kuna tare damu zaku dunga samun nasihoshi daga manyan malaman kasar nan. Mungode.

01/03/2020

Dr. Isah Aliyu Pantami

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Ku saurari wannan sako daga bakin malam. Allah ya bada lada. Ameeeen!
Dr. Isah Aliyu Pantami

Category

Telephone

Website

Address

No 2 Opp. Juma'at Mosque Dorayi Quarters, Gwale Local Government.
Kano
Other Health/Beauty in Kano (show all)
KMY Enterprises Nig ltd KMY Enterprises Nig ltd
Kano

New arrival ������ ����� 08097887047 08080572430 Whatsapp or call

Purple_glitz_makeover Purple_glitz_makeover
Nomansland Kano
Kano

Makeup is a beautiful thing�� please let’s try to always look good at all time���

Al-islah universal College Al-islah universal College
Along Panshekara Road, Chiranchi, Kumbotso LGA
Kano

Kwankwasiya jajira t/Fulani Kwankwasiya jajira t/Fulani
JAJIRA
Kano, ABDUL

KW jjr td

Farha cap. Design Farha cap. Design
Kuntau
Kano

Siyan daya ko sari. Inasaida hijabai Yara da manya

Håbíbį chø7 Håbíbį chø7
Håbíbįchø7@gmail. Com
Kano

Real meenal kano Real meenal kano
Burget Rimin Kebe
Kano

Muna dinkunah nazamnni masu kyau dogayan riguna hijab dinkin atamfa lace dasauransu located kano

Yan uwan juna Yan uwan juna
K/wanbai
Kano, 09031692899

Herbs And Spices ..SpiceDoctor Herbs And Spices ..SpiceDoctor
Kano

Your health status is our concern...Deals with different herbs,spices and more

Ma aruf auwal abdullahi Ma aruf auwal abdullahi
Tudun Murtala
Kano, NASSARAWA

Waleed

Looking Good Hair Beauty Saloon Looking Good Hair Beauty Saloon
No27 Badawa Market, Badawa Nassarawa Local Govt Area
Kano

What we do.plating of hair,fissing,nails,eyelashes and many more

Dœçtêr Aræyûwå Nê Dœçtêr Aræyûwå Nê
Kano

Kuyi following dA sharing na wannan shafin namu