Ki Gyara da Kanki Maganin Infection

Ki Gyara da Kanki Maganin Infection

You may also like

Sarni07
Sarni07

Mun bude shi don siyar muku d magunguna ingantattu k**ar qarin Ni'ima,infection da sauran cututtuka.

23/06/2024

Kira koh Whatsapp 09122036030.
Me buqatar yin Register zai iya yi min mgn

Photos from Ki Gyara da Kanki Maganin Infection's post 20/06/2024

๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผanci maikon sallah afuto azazzage shi, kunsan dai illar maiko ajikin mutum ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ‘Œkufuto kusha const free domin wanke dukkan wani datti da kitse na cikin jini da bargo ๐Ÿ‘Œ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ

Masu basir ba sai anfadamuku illar maiko atare da ku ba ๐Ÿ˜„๐Ÿ‘Œ

Ku futo ku mallaki constfree.

Masu kiba da tumbi ga kuma mai ko ankara lodawa๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„๐Ÿ˜„azo asha constfree ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ

Photos from Ki Gyara da Kanki Maganin Infection's post 25/03/2024

CIWON KABA (HERNIA)

Ciwon kaba, wani ciwo ne da ke faruwa saboda gajiyawa ko raunin jikin naman da ya rufe ciki (wato naman da yake

karkashin fatar da ta taso tun daga kahon zuci har zuwa mara), wadda kan sa tsagewar wani bangare na naman. Hakan ke sa halittun jikin dan Adam na ciki, k**ar hanji ya fito ta wannan

โ€™yar kafa.

ABUBUWAN DAKAN KAWO (KABA)

Abubuwan da ke kawo ciwon kan ka su kashi biyu k**ar haka:

1. Gado (Congenital): Ana gadon ciwon tun a ciki, sai jariri ya fito da ita kabar.

2. Wanda ake samu daga baya (Acquired): Wannan nauโ€™i ne da ake kamuwa bayan an girma saboda raunin naman jiki, sanadiyar KIBA sosai ko kuma tsananin aikin da zai wahalar da jiki k**ar daukar abu mai nauyi. Duk lokacin da wani bangare na naman jikin mutun ya samu gajiyawa sak**akon daukar nauyi, ko tari na tsawon lokaci, ko ma tsananin yunkuri lokacin ba haya, duk s**an sa naman ya rabu biyu, ta yadda wani sashe na โ€™yaโ€™yan hanji zai biyo hanyar.

Shan taba sigari ma kan sa mutun ya kamu da cutar saboda tsananin tari sanadiyyar ciwon huhu da sigari ke sa wa.

IRE-IREN SA

Iren-iren ciwon: Ciwon ya fi yawa ne a mahadar kashin cinya da kugu (Inguinal and Femoral Hernia), gefen alโ€™aura.

1- Akwai wadda ke faruwa a saman layin da ya raba kirji zuwa cibiya gida biyu (Epigastric Hernia). Wannan nauโ€™in ya fi shafuwar maza a kan mata. Sama da kashi 75 na cutar a maza aka fi samun ta.

2-Sai wadda ke faruwa a cibiya, takan faru ne idan aka samu gajiyawar jijiyoyin jini da ke kawo jini ga cibiyar. Wannan nauโ€™in kan auku ga yara saโ€™annan takan bayyana sosai a shekarun 3 zuwa 4 ko ta zauna har tsawon rayuwa idan ba a dau mataki ba.

Iyaye kan lura da ciwon a lokacin da yaro ya yi tari, za ta fito a gefen cibiya.

3-Sai wadda ke faruwa sanadiyyar daukar ciki ko haihuwa ga mata a mahadar kashin cinya (Femoral Hernia).

4-Akwai kuma wadda ke faruwa sanadiyyar fida (Surgical Hernia). Wannan tana faruwa ne sanadiyyar matsalolin da ba a rasa ba, wani lokacin idan aka yi fida, musamman idan babu

kyakkyawar kulawa a gefen da aka yi fidar.

ALAMOMIN KABA

Alamomin cutar:

1- Mutun zai rika jin wani abu ya fada masa a wani bangaren jiki ko ya fice.

2- Sai kuma jin zafi, k**ar kuna a bangaren da abun ya faru.

3- Sai kumburi ko a ji dan kululu.

4- Jin zafi lokacin daukar wani abu mai nauyi, ko yayin tari. Zafin kan bazu zuwa sauran bangarorin jiki k**ar baya, kafa

ko alโ€™aura.

HANYAR MAGANCE CIWON

Hanyar magance ciwon: Hanya mafi inganci domin kawar da ciwon kaba shi ne fida, domin a gyara wannan wuri da yake rauni. Idan kuma aka ki zuwa a yi aikin, to ciwon ba ya mutuwa da kansa sai dai ya kara girma wani lokaci kuma ya rika zafi sosai, wanda hakan barazana ce ga rayuwar mutum.

Bayan aikin fida mutun zai ji rashin walwala da dan zafi na โ€™yan kwanaki, kafin ya fara jin sauki. Hakan kan dauki sati daya zuwa shida kafin a ji garau. Amma wadanda ke daukar nauyi ko aiki mai wahala, to za su dauki tsawon lokaci kafin su warke.

Allah yakara mana lafiya, marasa lafiya Allah ya Basu lafiya.

Lafiya Uwar Jiki

25/03/2024

Kuskure ne da rashin tausayi, nuna damuwa da kulawa a ce matar ka ba lafiya ka kasa sa tambayarta ya ya jikin ta ko ka nuna dan damuwa da sa hankali a kanta.

Menene asarar ka a ciki dan ka tambayeta ya jiki, ko kace mata sannu, ko ka kira kaji ya ta kara ji da jikinta bayan fitarka gida

Shi dai ciwo na kan kowa kuma ba ita ta daurama kanta ba, amma ace mace da ta soma ciwo sai gaba sai jin haushi, sai fada sai tsamgwama sai fita, sai watsi da ita kai a tunanin ka watakil tayi me dan karka nemeta ko dan shagwaba ko dan kar tayi wani abu. Haba bawan Allah kai yanzu in baka da lafiya matar ka tayi watsi da kai yadda kakeyi matta zakaji dadi ?

Yana daga cikin tausayi ka nuna kulawarka ga iyalin ka in bata lafiya hakan zai tabbatar mata da son da kake mata.

Ke kuma ki sani................

Mace mai yawan lauyayi na gaskiya ko na qarya tana fita daga kan namiji, sannan kiji tsoron Allah ki bar amfani da ciwo wajen cutar da zuciyar mijin ki ta hanyar tauye masa hakki a shimfida, ki bar amfani da ciwo wajen cutar da aljihun miji, ki kiyaye kullum cikin kaza na ciwo k**e.

Matuqar zaki zama mace mai yawan ciwon chan da nan tabbas miji zai gaji dake b***e ya baki kulawa ko domin kin dawo dashi dabi'ar ki, kinga kuwa dole yayi watsi dake da ciwon duka dan ya gaji da langwamewarki ta dabi'a sai ki qarita da kan ki ba sannu b***e ya jiki.

โœ๏ธCopy

25/03/2024

Cutar kumburin ฦ™ashin ฦ™ugu (PID) cuta ce ta ษ—aya ko fiye daga cikin manyan gabobin haihuwa na sama, waษ—anda s**a haษ—a da mahaifa, tubes na fallopian da kamuwa da ovaries na gabobin haihuwa na mace.

Akwai babban haษ—arin rashin haihuwa idan kun jinkirta jiyya ko kuma kuna da maimaitawar PID. Amma wani bincike na dogon lokaci a Amurka ya nuna cewa mutanen da aka yi nasarar yi musu maganin PID suna da adadin ciki iri ษ—aya da sauran jama'a. PID Yana lalace bututun fallopian wani lokaci ana iya bi da su ta hanyar tiyata.
Rashin haihuwa-daya cikin mata 10 da ke da PID ba za ta iya haihuwa ba. PID na iya haifar da tabo daga bututun fallopian. Wannan tabo na iya toshe tubes kuma ya hana kwai takin. Ciwon ciki na Ectopic - Tabo daga PID kuma zai iya hana kwai da aka haifa daga motsin cikin ma
Dalilan PID

Yawanci yana faruwa ne lokacin da kwayoyin cutar da ake kamuwa da su ta hanyar jima'i s**a bazu daga al'aura zuwa mahaifa (mahaifa), tubes na fallopian ko ovaries.
Kasancewa mai yin jima'i kuma ฦ™asa da shekaru 25.
Samun abokan jima'i da yawa.
Kasancewa cikin jima'i tare da wanda ke da abokin tarayya fiye da ษ—aya.
Yin jima'i ba tare da kwaroron roba ba
Douching akai-akai, wanda ke ษ“ata ma'auni mai kyau da ฦ™wayoyin cuta masu cutarwa a cikin farji kuma yana iya rufe alamun
Samun tarihin cutar kumburin ฦ™ashin ฦ™ugu ko kamuwa da cuta ta hanyar jima'i
Ki Gyara da Kanki Maganin Infection
Alamun
Yana buฦ™atar ganewar asali na likita
Alamomin gama gari sun haษ—a da ciwon ฦ™ashin ฦ™ugu da zazzaษ“i. Za a iya samun fitar ruwa daga farji.
Mutane na iya dandana:
Wuraren zafi: a cikin ฦ™ashin ฦ™ugu, ciki, ฦ™ananan baya, ko farji
Yanayin zafi: na iya faruwa yayin jima'i ko lokacin fitsari
Jiki duka: sanyi, gajiya, ko zazzabi
ฦ˜aฦ™walwa: taushin motsin mahaifa, fiษ—ar farji, ko warin farji
Gastrointestinal: tashin zuciya ko amai
Hakanan na kowa: ciwon ciki ko ciwon hail
Dubai comment section domin ganin maganin matsalar

23/03/2024

Daga cikin abubuwan da miji ke lura da sa hankali akai dan tabbatar da matsayin sa a wajen ki da irin son da k**e ma sa yakan matuqar sa hankali a :-

Yanayin yadda k**e girmamashi :- girmamawa a wajen namiji wani babban yanqi ne na so da ฦ™auna a wajen sa. Yanayin yadda k**e bashi irin yadda yake so ne ko dai bakimasan ya ake girmama miji ba.

Yanayin yadda k**e darajta :- shin akwai abunda kika fifita sama dashi ko shine no.1 din ki, ko wasu ko wani abu sun fishi, kina iya fifita shi akan komi ko dai shi ne aqarshe.

Yanayin yadda k**e kiyaye umurni da hanin sa :- in yace ga abunda za'ayi ko yadda yake so ko a bari, ra'ayin kanki k**e bi, ko yana fadi kina musu ko sai kinga dama kiyi ko ki bari, ko sai lokacin da k**e so ko sai yadda k**e so, ko bazama kiyi ba.

Yanayin yadda k**e masa magana :- cikin girmamawa da mutuntawa ko cikin gatsali, reni, daga murya, yana fada kina faษ—a ko yana magana kina jira ki mayar masa da amsa.

Yanayin yadda k**e kula da buqatar sa shimfida :- cikin shauqi da nuna sha'awar sa k**e, ko tamkar sai ya roฦ™a k**e bashi, kina samar da excitement a cikin mu'amalar ku ko dai lami akeyi ko a garau garau ake qarewa.

Yanayin boundaries ( iyakar ki ) a rayuwar sa :- kina shisshige masa a komi ko dai kin na tsayar da kanki in da ya dace ki tsaya, ko aษ—alarbakhur ce ke komi da ruwanki, hatta tsakanin sa da mahaifiya da 'yan uwa sai kin shiga ko sai kin san me yake ciki dasu.

Yanayi hakuri, kawaici da juriyar ki :- in aka samu matsala tayaya k**e handling din situation, cikin fusata, biyema kowa, cikin mutunci ko tashanci k**e yi in an samu matsala.

Yanayin kulawar ki gareshรฌ :- damuwar ki shine ko dai damuwar ki kawai kanki da buqatar kine, ko dai kedai ya samo ya miki ne kawai ba ruwanki da me yake ciki b***e ki sa hankali dan ki samar masa da nitsuwa.

Yanayin yadda k**e mu'amala da iyaye da 'yan uwan sa :- cikin mutunci da nuna kulawa k**eyi ko kina musu kallon 'ya cima zaune ko 'yan cin arziฦ™i da takura ne, ko kyamar su k**e da nuna basu kai ki mutunta ko ki musu kyakkyawan mu'amala ba.

Matuqar ya lura kika kiyaye wadannan yadda yake so a lokacin da yake so, tabbas zaki samu mazauni mai lasisi a zuciyar sa.
Copy

Photos from Ki Gyara da Kanki Maganin Infection's post 01/03/2024

Assalamu Alaikum

WANKIN CIKI BAYAN MACE TAYI BARI NA JUNA BIYU (DILATION AND EVACUATION AFTER PREGNANCY MISCARRIAGE)

Wankin ciki wani aiki ne wanda likitoci suke yiwa mace wacce ta sami matsalar bari na juna biyu (miscarriage), domin a fitar da sauran sassan jikin jaririn wadanda s**a rage a cikin mahaifarta. Dalilin dayasa ake yin wankin ciki shine, idan har akwai ragowar sassan jikin jaririn da aka yi barinsa a cikin mahaifar, to, zasu haddasa ma matar da tayi barin zubar jini maras iyaka, ciwon mara, ciwon ciki, kamuwa da kwayoyin cuta (infection), da kuma rashin iya daukar wani cikin.

A likitance, ana kiran wankin ciki da suna dilation and evacuation (D & E). Maโ€™anar dilation ita ce bude farjin mace ta hanyar tattale shi, excavation kuma yana nufin kwashewa da fitar da tarkace daga cikin mahaifa. Mafi yawa ana yin wankin ciki ne idan mace tayi bari a cikin wata 3 na farkon samun ciki (first trimester), saboda a wannan lokacin jikin jaririn baiyi kwari ba don haka sassan jikinsa zasu makale a bagon mahaifa suki fita.

Likita yakan yi amfani da wata naโ€™ura mai tsini wajen bude farji wacce ake kira โ€œcervical (osmotic) dilatorโ€. Duk da cewa tana da tsini, amma kuma kanta yana da laushi ta yadda ba zata haddasa samuwar rauni ba a cikin farji lokacin da ake tura ta, ko kuma rauni a cikin mahaifa. Saโ€™annan likita yakan yi amfani da wani almakashi ne mai tsini wanda ake kira โ€œforcepsโ€ domin k**awa da kuma tattaro tarkacen da suke cikin mahaifar, kuma ya fitar da su.

Kafin ayi wankin ciki, akan yi awon hoto na ultrasound domin sanin halin da mahaifar take ciki. Saโ€™annan a lokacin da zaโ€™a yi wankin cikn, a kan yi wa mace allurar kashe radadi (anesthesia), da kuma ta kashe kwayoyin cuta (antibiotic). Kuma akan wanke farji da sinadarin hana yaduwar kwayoyin cuta (antiseptic solution). Aikin wakin ciki bai cika dadewa ana yin sa ba domin baya wuce minti 30, sai dai idan an sami wata matsala.

Kasancewar tarkacen sassan jikin jariri wadanda aka cire a lokacin wankin ciki suna damfare ne a jikin mahaifa, mace takan fuskanci matsalar ciwon ciki, ko mara da kuma zubar jini bayan an gama aikin. Zubar jinin yakan dauki sati 2 kafin ya tsaya. Wannan yana faruwa ne a lokacin da mahaifa take warkewa kuma take komawa cikin yanayinta na asali. Idan ba matsala aka samu ba, to, mace zata warke cikin sai 1 ko 2. Saโ€™annan akan sake yin awon ultrasound domin a tabbatar da cewa aikin yayi nasara.

Ana so mace ta cigaba da shan magungunan kashe kwayoyin cuta, bayan an gama aikin. Kuma ta sami hutu daga yin ayyuka masu wahala, saโ€™annan ta guji yin saduwar aure da mijinta har sai ta warke. Kuma koda ta warke, akan bayar da shawarar cewa su dauki matakai na hana daukar ciki har sai ta murmure sosai na kimanin wata 2 zuwa 3 bayan wankin cikin.

YADDA AKE GANE SAMUWAR MATSALA BAYAN WANKIN CIKI (COMPLICATION AFTER DILATION AND EVACUATION)

Alamomin da zasu nuna cewa akwai matsala bayan wakin ciki suna da yawa. Amma fitattu daga cikinsu sune:

1. Zazzabi, da murdawar ciki, da ciwon mara mai tsanani wanda ya wuce sati 2 bayan anyi wankin cikin. Kuma ko mace ta sha maganin kashe radadi baya yi mata aiki.

2. Zubar jini mai tsanani, wani lokaci hade da gudaji wanda ya sabawa irin yadda alโ€™adarta ta saba zuwa, ta yadda zata iya jika sanitary pads guda 1 zuwa 2 a cikin awa 1 ko 2.

3. Tashin zuciya, wani lokaci har da amai.

4. Zubar ruwa mai yauki, ko karni, ko wari daga farji, hade da kumburin ciki da jin radadi a farji.

ABUBUWAN DA SUKE HAIFAR DA MATSALA BAYAN ANYI WANKIN CIKI (RISK FACTORS OF D & E)

Kamar ko wane aiki na asibiti, shima wankin ciki yana da nasa abubuwan da s**an sanya a sami matsala. Kadan daga cikinsu sune:

1. Samun rauni a cikin farji ko kuma a cikin mahaifa. Duk da kasancewar ana daukar matakai masu inganci wajen yin aikin wankin ciki, domin a kauce ma hadarin samun rauni, wani lokaci akan yi rashin saโ€™a raunin ya samu. Abinda yake haifar da raunin shine kasancewar bangon mahaifa yana da laushi sosai, kuma wani lokaci jikin jariri yakan damfare sosai a cikinsa. To, idan anzo bambare shi daga jikin bangon mahaifar, mai yiwuwa ne ya daye fatar bangon mahaifar, daga nan sai rauni ya samu. Idan kuma raunin a farji ne, to, mai yiwuwa ne kayan aikin da ake amfani dasu su karce fatar farjin. Amma a gaskiya baโ€™a cika samun rauni a farji ko kuma a mahaifa ba a lokacin wankin ciki.

2. Rashin fitar da tarkace gaba daya daga cikin mahaifa (retained products of conception). Idan aka yi rashin saโ€™a wani bangare na sassan jikin jariri bai fita ba daga mahaifa, to, zai haifar da zubar jini, kila ma har da kamuwa da kwayoyin cuta (infection). Shima wannan baโ€™a cika samun sa ba.

3. Daskarewa jini a cikin mahaifa. Wannan yana faruwa ne idan mahaifa ta kasa takurewa (contraction) domin ta fitar da jinin da ya taru a cikinta bayan an gama wankin ciki. Hakan zai sanya daskararren jinin ya toshe kofar mahaifa, sai ya kume a ciki, ya haddasa ciwon ciki, da ciwon mara, da kumburin ciki, da tashin zuciya. Idan haka ta faru, to, sai an koma wajen likita domin ya bayar da magani ko kuma ya yi amfani da kayan aikin da s**a dace domin fitar da daskararren jinin.

MENENE YA KAMATA MACE TAYI BAYAN BARIN JUNA BIYU

Idan mace tayi bari, yana da kyau ta tuntubi likita domin ya bata magani ko kuma shawarar da ta dace, ko da kuwa tana tsammanin cewa jaririn ya fita gaba daya daga cikin mahaifarta. Dalili kuwa shine ita ba zata iya gane fitar shi gaba daya ba, har sai anyi gwaji. Kuma mata da yawa a group dinnan s**an ce basu son wankin ciki domin yana da zafi. Amma abin lura anan shine, idan har likita ya gano cewa a kwai sauran tarkace a cikin mahaifa, kuma sai anyi wankin ciki zaโ€™a fitar da shi, to, yin wankin cikin ya zama dole kenan, matukar matar tana bukatar ta daina zubar jini, ciwon mara, ciwon ciki, kuma ta iya samun wani juna biyun.

WalLahu A'aโ€™lam.
Ki Gyara da Kanki Maganin Infection

Photos from Ki Gyara da Kanki Maganin Infection's post 18/02/2024

Yadda Za Ki Sa Namiji Ya Nutse Cikin Kaunar Ki:

Ki Gyara da Kanki Maganin Infection

Da yawan mata sun rasa gano bakin zaren yadda za su sahihiyar hanyar da za ta sa namiji ya so su so na gaskiya.

Wasunsu sun dauka kyau da kwalliya ne kadai maganadisun mace na yi wa soyayyar da namiji kamun kazar kuku.

Abubuwa bakwai da ke sanya fata tsufa
Abubuwa 5 da za su sa budurwa ta so ka
Eh toh! Suna cikin abubuwan da kan karkato da wasu mazan, amma kuma maza sun bambanta ta fuskar ababen da suke so a tattare da mace, duk da cewa akwai wasu abubuwan da s**a yi tarayya a kai.

Wasu maza da muka zanta da su sun fede mana biri har wutisya game da abubuwan da kan sa su nutse a kaunar mace. Ga biyar daga ciki:

โ€“ Kunya

Ki kasance kin dabiโ€™ar jin kunya domin siffantuwar ki da kunya babban ado da ke saurin jan hankalin namiji ya ji kaunar ki ta mamaye zuciyarsa.

Kar ki sake ki zama daga cikin fitsararrun mata domin babu namijin kirki da zai so ki kasance uwar โ€™yaโ€™yansa. Na tabbata ke kanki mutumin kirki za ki so ki aura.

Wani matashi da muka zanta da shi, Abdulrahim Ushata ya ce, โ€œZa ki yi ta jin ana cewa ai maza ba su son mace mai kunya, kunya na cutarwa.

โ€œWannan duk zancen mutane ne, kunya ita ce ke kara daraja da martabar โ€™ya mace.

โ€œKunyarki ce za ta sa mutum ya ji kullum yana kara son sanin wani sabon abu game da ke saboda kunyar za ta sa ya ji yana fahimtar abin da k**e so kuma zai yi ta kokarin jan ki a jika da kuma tarairayar ki.

โ€œHakan zai sa kullum soyayyarku ta yi ta kara armashi, k**ar a ranar kuka hadu saboda kullum sabon abu ne zai gani a tattare da ke.โ€

โ€“ Ilimi da hazaka

Abubakar Salis ya bayyana wa Aminiya cewa maza na son mace mai ilimi da himma da kuma fahimtar alโ€™amuran yau da kullum.

Ki kasance kin fahimci alโ€™amuran da s**a shafi rayuwa, musamman a cikin alโ€™umma ta yadda za ki yanke hukunci yadda ya dace; Kar ki yadda ki zama kifin rijiya, wadda dan kankanin abu ma sai ya daure mata kai.

โ€œBa lallai sai kin rika fitowa da sak**akon jarabawa mafi kyau ba, ya dai zama ke ba sakarya ba ce, kina da raโ€™ayinki kuma a duk inda k**e za ki iya bayyanawa ba tare da fargaba ba, sannan ya zama kina da sani a kan abubuwan da ke wakana a rayuwa.

โ€œKi san abubuwan da s**a shafi kasarki da za ku iya zama ku tattauna a kai; Hakan ba zai sa ku gundurar juna ba saboda ko ba zancen soyayya ba, akwai abubuwan da ku ke tattaunawa a kai.โ€

โ€“ Faraโ€™a
A cewar Imran Gambo, mace mai faraโ€™a ta fi saurin burge namiji sama da wadda za ta fito fuskarta a daure babu faraโ€™ ko miskala-zarratin.

Imran ya ce mata marasa faraโ€™a na saurin gundurar mutum kuma ba sa raina abin yin fada a kai sannan ga saurin fushi.

Sai dai ya ce, โ€œIdan an ce mace ta zama mai faraโ€™a ana nufin ta kasance mai sakin fuska ne amma ba ta zama sakarya tana bude hakora barkatai ba; ya dai zama fuskarki a sake take yadda ba za ta firgita mutane ba.

โ€œA Musulunce ma ai murmushi sadaka ne, saboda murmushin da aka raina kan iya zama sanadiyar yayewar damuwar wani,โ€ inji Imran.

โ€“ Tausayi

A cewar Muhammad Umar, tausayi dabiโ€™ar mutanen kwarai ce shi ya sa ake so mace ta kasance tana da shi.

Ya ce idan namiji ya fahimci cewa akwai tausayi a zuciyar mace, hakan na kara narkar da shi a cikin kaunar ta.

โ€œTausayin kuma ya zama ba a kansa kadai ba, har a kan sauran mutane, musamman in ya ga kina son taimakon mutane.

โ€œHakan zai kara masa son ki saboda ya san cewa ba shi kadai ba, โ€™yaโ€™yansa ma sun yi dacen uwa ta gari mai tausayi.โ€

โ€“ Son yara

A cewar Rufai Ahmad, โ€œa matsayinki na mace yana da kyau a ce kina da kyakkyawar muโ€™amala tsakaninki da yara saboda wata rana za ki zama uwa ke ma.

โ€œIna son mace mai son yara. In na ga tana wasa da su yakan kayatar da ni, saboda a lokacin ne wasu abubuwa game da ita ke bayyana, musamman yadda za ta mayar da kanta daidai da yanayin da yaran za su ji dadin kasancewa tare da ita.

โ€œHakan shi zai nuna ma shi cewa yaran shi sun yi dacen uwa.โ€

Kadan ke nan daga cikin abubuwan da maza ke so a tattare da mace.

Ina fatan wadanda s**a karanta za su amfana da abubuwan da aka lissafo, za su kuma yi aiki da su.

17/02/2024

Zaman family house yana hana mace sake da samun daman yin abubuwa da dama ma miji da zai qara musu kusanci, yakan sa auren ya gundureta, yana haifar da rashin jituwa tsakanin miji, mata da 'yan uwan sa, yana haifar da sa ido, gulma, kyashi, hasada, kishi, munafurci da gaba.

Yakan sa namiji ya zama a tsakiyan da duk bangare sunaga baya kyauta musu, yana haifar da rashin kusanci tsakanin miji da mata, ya kan iya hana ma'aurata sani da fimtar halin juna, yakan jawo reni ko matarka ta rena mahaifiyarka ko 'yan uwan ka su rena matar ka, ko matarka ta rena ka, yakan iya haifar da tsangwama walau mahaifiyar ka ta tsangwameta ko 'yan uwanka su tsangwameta.

Duk da zaman family house yana da dadi, haifar da kusanci, debe kewa, da hadin kai amma sai a inda aka samu daidaiton zukatan masu zaman gidan amma in dai ba'a samu ba tabbas zai haifar da duka ko wasu daga cikin abunda aka lissafo a sama.

Zaman family house in ba ya zama dole ba gaskiya zama a gidanka yafi, gidan hayama da ake da yawa ya aka qare b***e zaman family house.

Allah ya horema mazaje dake zama ko niyyar zama a family house dan lalura hanyar da zasuyi muhallin su dan samun jin dadin zama da iyalan su.

17/02/2024

An riga an wuce lokacin da zaka bar uwar yayanka babu sana'a , babu aiki ko komawa makaranta ..

Cikin ukun ya k**ata kayi biyu ko daya , matan da bata aiki ko sana'a bamu fatan wani abu ya faru da mijinta ya barta da yara , komai yawan kudin gadonta sai ta rasa yanda zatayi dashi tunda bata saba juya kudi ba , har ta shiga business da batasan kanshi ba ata damfarar ta kudin su kare..

Dayawa marayu dake jin jiki yawanci iyayensu mata basu sana'ar komai basu kuma aikin komai ..

Idan kayi empowering matar ka ka taimaka wa yayan ka Dan dole idan ka bar yaya a hannun ta ko hannun danginka ta kulasu ..

Koda itace ta riga mutuwa gadonta na yayanka ne kaga kuwa still komai nata ya dawo hannun yayanka , maza Ku cire son zuciya Ku taimakawa matanku wajan ginasu da rayuwar yayanku ..

Bazaku gane halin da marayu suke shiga bayan mutuwar babansu ba sai kayi bincike akai sosai ka gane sillar faruwar hakan ..

Wasu suna kin barin matansu suyi aiki ko sana:a sabida wai kar sufi karfinsu ko kar ta fi mijin kudi ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ

Kaji wani banzan tunani don Allah , itafa gagararriyar mace ko batada ko sisi sai tayi halinta ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ

16/02/2024

Kuyi rijistan GHT kuci kaji yadda ranku yakeso so๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฅณ๐Ÿฅณ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚

16/02/2024

ยฎ ABIN DA YAKE KASHE MATANMU NA HAUSA KENAN...ยฎ

Idan kin san baxa kiyi comment ba kada ki karanta min post rashin comment ke lalata group
โ€ข
โ€ข
โ€ข
Na dade ina irin wannan nazarin game da rayuwar matan qasar hausa akan menene dalilin da yasa suke saurin tsufa da zaren an yi musu aure sun je gidan miji...
โ€ข
Zaka ga yarinya qarama wacce aka haifeta a gabanka da zaren ta isa aure an kaita d'akin miji shekara daya kawai zuwa biyu bayan ta haihu idan ka ganta abin zai baka tsoro da mamaki domin zaka ganta duk ta tsufa ta yank'wane k**ar wata Anty...
โ€ข
Abin da yake bani mamaki shine kafin 'yan matan suyi aure sun iya k**a jikinsu da daukar wanka da kwalliya... Watakila wannan shine dalilin da yasa samari s**a yi mata chah a lokacin tana gidansu... Amma da zaren ta shiga d'akin miji shikenan wannan k**a jikin da wannan wankan da kwalliya duka sun zama tarihi...
โ€ข
Musamman idan ta samu juna biyu ko kuma ta haihu a wannan lokacin wata matar ko abincin da ta dafa wani namijin mai tsantsami ba zai iya ci ba b***e har yayi hira ko hada shimfida da ita ba... Kuma a irin wannan yanayin ba kowane namiji bane zai iya zama da irin wadannan matan ba dole sai dai cikin biyu ayi daya ko dai ya saketa ko kuma ya qaro aure...
โ€ข
Da yawa matanmu haka suke basu damu da ado da gyaran jikinsu ba k**ar yadda suke a lokacin suna 'yan mata... Dalilin kenan da yasa mazajensu ke gudunsu suna bin' yan matan waje ko karuwai... Domin matansu basu yi musu irin wannan kwalliyar da suke gani a wajen 'yan matan waje...
โ€ข
Kullum zaka tarar da mace da d'aurin kirji kai a chukurkud'e ya tsufa ba kitso ba sarta... Yadda take a hargitse haka 'ya'yanta da d'akinta da gidanta suke babu kulawa... Idan mijin yayi magana domin ta gyara sai tace:-
โ€ข
"Kawai dai Baban Auwal ka gaji da ni ne duk shi yasa kake ta yimin irin wannan tsangwamar... To ya kake son nayi ni inji ce da zanyi ta aiki ba na gajiya? Jiya fa nayi wanka kuma na share d'akin nan sannan nayi wa yaran nan wanka"...
โ€ข
Babu yadda mijin ya iya dole sai dai

Photos from Ki Gyara da Kanki Maganin Infection's post 14/02/2024

SHAWARA GA MASU OLSA"

Da yawa a cikin mutane idan azumi yazo suna shan wahala saboda ciwon olsa har barin azumi suke yi"

GA WASU SHAWARWARI"

1 Kada ka yi amfani da abinci ko abin sha masu maiko dayawa"abinci ko abin sha mai yaji" abinci ko abin sha masu daci" abinci ko abin sha masu tsami" abinci ko abin sha masu gas" abinci ko abin sha masu dauke da acid,

BAYAN KA YI SUHUR"

2 A wannan lokacin kada ka koma bacci" saboda a lokacin da mutum yake bacci gabobin chiki masu narka abinci da sarrafa abinci a ciki bazasuyi aiki yadda ya k**ata ba" domin abincin da kaci zai zama maka guba ta dalilin rashin narkewa akan lokaci"

KADA KA CIKA CIKI DAM A LOKACIN BUDA BAKI KO SUHUR"

Idan zakaci abinci an fiso a raba ciki gida uku" 1 gida daya na abinci" 2 gida biyu na ruwa" 3 gida uku na iska"

Amma idan ka cika cikin ka dam da abinci hakika cikinka bazai samu daman narka abinci ba" b***e ya sarrafu dai dai"

4 A kiyaye yin buda baki da ruwan sanyi" shan ruwan sanyi a dai dai lokacin buda baki yana da illah ga sassan jiki sosai" don haka a fara da dibino" ko lemo" ko ayaba" ko kankana" da sauransu" sannan abi da ruwan dumi"

5 Shan ruwan zafi lokacin da babu komai a ciki yana zama sanadin kashe kwayar cuta wacce take zama sanadin kawo ulcer ( H-plory ) Shan ruwan zafi yana inganta narkewan abinci" yana inganta gudanar jini" yana rage maiko a jiki" yana saukaka ciwon ciki,

Allah madaukakin sarki ka bawa kowani marar lafiya sauki mai inganci" alfarman annabi muhammad S'A'W'

Allah kasa muna daga cikin masu samun kyautar gidan aljanna" Allah ka yi rahama ga dukkan mamatanmu Amin.

14/02/2024

FADAKARWA DANGANE DA CIWON SANKARAR MAMA (Breast Cancer)!!!

"""''''''''''''"""""""""'''"""""""
A bangaren mata Ku ban hankalinku kacokan domin tunasarwa a kan hanyoyin kariya daga ciwon daji na mama domin ciwone da kullum yake Dada yawaita:-

1- Babbar hanyar kare kai daga kamuwa daga Kansar Mama ita ce ta yawan shayarwa. Wato masana sun yi amanna cewa shayar da yaro a kalla tsawon shekara biyu yana iya kare mace daga Kansar Mama. Domin da yawa yanzu mata sun zama malalata wata dakyar take iya shayarwa xuwa shekara wata ko sai dai akeba yaro madara wai ita kar nonuwanta su zube.
Toh kusani yawan yaran da mace ta shayar, yawan kariyarta kenan.

2- Sai kuma rage kiba.
Masana sun tabbatar da cewa mace mai kiba tana cikin hadarin kamuwa da ciwon Sankarar Mama, musamman idan wata a danginta ta taba yin ciwon.
Don haka sai an rage maiko a abinci a rika kuma yawan motsa jiki.

3- Sai rage shan kwayoyin nan na ba da tazarar iyali wato pills,
domin su ma wadannan kwayoyi an tabbatar suna iya jawo wannan ciwo na Sankarar Mama.
Idan da hali ke nan, a bi wasu hanyoyi ba ta wadannan kwayoyi ba zai fi.

4- Daina shan taba sigari da kuma barasa ga mata hanyace ta kare kai domin suna kara hatsarin kamuwa. Kai ko hayakin tabar yana da kyau mace ta kaurace mai musamman masu mazajen da basa kunyar sha ko a daki.

5- Duk matar da ta kai a kalla shekaru Ashirin da biyar yana da kyau ta koyi yadda ake duba mama.
Wannan wata hanya ce da mace za ta iya ita kadai a dakinta ko ita da mai gidanta, domin duba mamanta a madubi ko akwai wani canji a jiki.

YADDA AKEYI KUWA SHINE:

Mace ta tube a gaban katon madubi ta dora
hannayenta kan kugunta, ta duba ta ga ko akwai wani yanayin
canjin fata ko kurji ko kullutu ko kari a jikin mamanta. Bayan nan sai ta juya ta gefe ta sake yin haka (wato ta duba gefen dama da hagu). Daga nan sai ta sake kallon mudubin, ta sa hannunta na hagu a bangaren dama ta fara latsa gefe zuwa ciki, kasa zuwa sama da karkashin hammata, taji ko za ta ji wani kullutu ko k'ari.
Sai ta sake dawowa kan maman ta matso shi ko za ta ga wani ruwa ya fito (idan ba shayarwa take ba kenan).

Idan ta gama sai ta je bangaren hagu ta yi k**ar yadda ta yi a dama. Sai kuma ta daga maman duk biyun ta duba yanayin fatar karkashin a lokaci guda ko akwai wani miki.
Idan babu komai shi ke nan ta gama sai bayan a kalla wata hudu 4 kafin ta sake. Amma idan ta ji wani kullutu ko ta matso wani kalar ruwa ko ta ga wani canjin yanayi a fatar to dole sai ta je asibiti an kara bincike.

Allah yasa adace!!!

Photos from Ki Gyara da Kanki Maganin Infection's post 14/02/2024

KIWON LAFIYA

Daga Dr Mukhtar Abdullahi Tsafe

CUTAR AL'AURA TA MATA. (VAGINITIS DISEASE)
๐Ÿ‘‡๐Ÿพ

VAGINITIS : Wata cutace da mafiya yawan jama'a suna kiranta da Vaginal Infection sabida wannan matsalar tana addabar gaban mace . Amma a Hausance ana kiranta da Ciwon Sanyin Mata.

Wannan cutar wassu kwayoyin cutar Bakteriya da Fungus dake zaune acikin Gaban mace su suke kawoshi.

Ana Iya samun wannan ciwon a lokocin juna biyu (ciki) da shayarwa , haka kuma za'a iya samun ciwon ta hanyar jima'i .

CAUSES OF VAGINITIS:
๐Ÿ‘‡๐Ÿพ

1- Bacteria Vaginosis : wannan wani kwayar cutace dake rayuwa cikin farji yakan haddasa matsalar Sanyin mata .

2- Candidiasis : wannan wata kwayar cutace Wanda yake haddasa Sanyin Gaba. Wadannan kwayoyin cutar suna zama cikin farji kuma basu cika cutarwa ba, wadannan kwayoyin cutar suna son waje mai gumi domin su girma dan yaduwa.

3- Trichomonas Vaginalis : wannan itace wacce take yaduwa ta hanyar jima'i. Ita wannan kwayar cutar parasite ce take kawoshi .

4- Irritation Vaginitis : ita wannan ana kiranta da Allergic , wassu abubuwanda jikin mutun bai daukesu ba, anasamunsa wajen amfanida k**ar su condom, sabulu , ko maganin shafawa.

SIGN AND SYMPTOMS

1- Kuburin Farji
2- Canxa Launin Farji zuwa Ja.
3- Kaikayin Farji
4- Warin Farji
5- Kurajen Farji
6- Zubar da Farin ruwa a Farji.
7- Zafin Lokocin Jima'i
8- Zafin Fitsari.

PREVENTION OF VAGINITIS:
๐Ÿ‘‡๐Ÿพ
1- Avoid Vaginal Douching : A cikin Farji akoi wassu kwayoyin bakteriya wadanda basa cutarwa kuma sunada amfani , amfaninsu shine suna taimakawa wajen bada kariya ga Farji , sai kaga wassu matan s**an wanke Farji da Sabulu ko detol haka , wadannan abubuwanda ake amfani wajen wanke farji yakan kashe bakteriya masu amfani na Farji , Sai masu cutarwa su samu daman shiga. A kiyaye wanke Farji Da Sabulu dakuma wadansu abubuwa Wanda bamusan Kansu ba.

2- Uses of Underwear : Amfani da wandon pants , wassu matan s**an bar wandonsu yayi datti , Barin datti ko amfani pant masu datti yakan bawa kwayoyin cuta

14/02/2024

๐๐€๐”'๐”๐Š๐€๐ ๐€๐๐ˆ๐๐‚๐ˆ 6 ๐ƒ๐€ ๐‡๐€๐ƒ๐€ ๐’๐” ๐€ ๐‚๐ˆ ๐Š๐„ ๐™๐€๐Œ๐€ ๐†๐”๐๐€:

Ga mutanen da ke son hada nau'ukan abinci domin rage ฦ™iba da ฦ™arin kuzari ko mazakuta yana da kyau a fara tuntuษ“ar masana abinci.

Masaniya kan lafiyar abinci a Najeriya, Habiba Haruna, ta yi wa BBC bayani kan na'ukan abinci shida da idan an haษ—a suke iya zama guba ga wani.

1- ๐Š๐ˆ๐…๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐Œ๐€๐ƒ๐€๐‘๐€
Kifi da madara suna da sinadarai masu gina jiki kuma hade su wuri ษ—aya ba zai karษ“i wasu ba - zai iya zama matsala.

Wani yanayin jikinsa ba zai so sanadari iri daya ba kuma nau'i daban-daban idan s**a hadu za su iya zama matsala.

Wani zai iya zama guba gare shi ya dinga yin amai wani kuma zai haddasa masa gudawa saboda hade nau'in abu biyu masu amfani iri daya a jiki.

2- ๐Œ๐€๐ƒ๐€๐‘๐€ ๐ƒ๐€ ๐€๐˜๐€๐๐€
Haษ—a madara da ayaba yakan iya zama guba ga wasu duk da cewa wasu za su hada su ci su kwana lafiya.

Ayaba tana da sinadarin potassium, idan mutum yana da ฦ™arancinsa kuma ya hada da madara ba zai samu matsala.

Amma wasu idan s**a haษ—a da madara da ayaba yana haifar masu da matsala k**ar ฦ™aiฦ™ayin wuya, wasu kuraje ko borin jini a jiki ko samiha.

Wasu zai janyo masu kasala.

3- ๐‹๐„๐Œ๐Ž๐ ๐“๐’๐€๐Œ๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐Œ๐€๐ƒ๐€๐‘๐€
Madara da lemon tsami ba su shiri domin nan take madara za ta tsinke idan aka haษ—a da lemon tsami.

Idan mutum ya hada lemon tsami da madara ya sha zai iya zaman masa guba. Zai iya sa wasu zafin zuciya.

4- ๐†๐˜๐„๐ƒ๐€ ๐ƒ๐€ ๐Œ๐€๐ ๐™๐€๐ˆ๐“๐”๐
Gyaษ—a na da amfani sosai ga jikin ษ—an adam kuma akan yi amfani da ita a fannoni da dama.

Gyaษ—a na da sinadarin protein mai gina jiki da kuma sinadarin carbonhydrate mai kara kuzari.

Gyaษ—a na cikin abubuwan da ke narkar da abinci, musamman masu son rage kiba suna amfani da gida a abinci.

Man zaitun kuma duk da yana da amfani musamman maganin cutuka da dama amma kuma hadawa da gyaษ—a yana haifar da wani yanayi ga waษ—anda ba su son man zaitun.

5- ๐’๐‡๐€๐ ๐Œ๐€๐†๐€๐๐ˆ ๐ƒ๐€ ๐‹๐„๐Œ๐”๐ ๐Š๐–๐€๐‹๐๐€

Shan magani da wani nau'in kayan zaฦ™i mai gas kan iya haifar da mummunan illa ga mutum.

Masaniyar ta ce wani lokaci shan magani da Fanta ko Coca-Cola zai iya kashe mutum saboda gas.

Ta ce duk wani lemon zaฦ™i mai gas ba a son a hada da magani a sha.

6- ๐ƒ๐€๐๐˜๐„๐ ๐๐€๐Œ๐€ ๐ƒ๐€ ๐ƒ๐€๐๐˜๐„๐ ๐Š๐–๐€๐ˆ

Haษ—a ษ—anyen nama da ษ—anyen kwai zai iya haddasa matsala ga jikin wasu ฦดan adam.

Yakan iya zama guba ga wasu, wasu na iya yin amai da gudawa saboda bai dace da yanayinsu ba.

ฦŠanyen nama zai iya haifar da illa idan har ba a bi hanyoyin sarrafa shi ba domin rage karfin sinadaran da yake ษ—auke da su.

Masaniyar ta ce ษ—anyen kwai ba ya da wani amfani a jikin ษ—an adam, domin yadda aka sha haka zai tsaya a jiki ba tare da wani amfani ba sai idan an dafa ko an soya ba. "Ba a aman ษ—anyen ฦ™wai," in ji ฦ˜wararriya masaniya kan lafiyar abinci a Najeriya Habiba Haruna.

Masaniyar ta ba mutane shawara su ci abin da s**a san zai masu amfani kuma ba zai haifar masu da matsala ba.

Kokarin gwada wani abu sabo zai iya amfani ga wasu amma kuma zai iya zama illa ga wasu.

Yadda ake da zabi da dama na nau'ukan abinci haka kuma yanayin mutane ya bambanta. Dole mutum sai ya yi taka-tsantsan da nau'ukan abincin da zai haษ—a ya ci.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Kuyi rijistan GHT kuci kaji yadda ranku yakeso so๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿฅณ๐Ÿฅณ๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜‚
Yan uwa ko kunsan da 6500 zaku samu hanyar da zaku dogara da kanku kuna zaune acikin gidanku ko office inku ko school an...

Telephone

Website

Address

Tudun Murtala Kwanar Yan Ghana Street
Kano
Other Spa, Beauty & Personal Care in Kano (show all)
Gowns Nd kamshi By Fadeela Gowns Nd kamshi By Fadeela
Kano

We offer the best gowns & turban cap for you nd yr princess ๐Ÿฅฐand also TURARENWUTAโ€™s,khumrah nd kh

Beloved Beauty care Beloved Beauty care
Dakata Close To Warshu Specialist Hospital
Kano

Your skin is your best choice to take care of with our naturally sourced organic products(oriflame)G

BLY textile BLY textile
State Road, Tarauni
Kano

Goods and services

Looking Good Hair Beauty Saloon Looking Good Hair Beauty Saloon
No27 Badawa Market, Badawa Nassarawa Local Govt Area
Kano

What we do.plating of hair,fissing,nails,eyelashes and many more

Ziflux hair Ziflux hair
Zungeru Road
Kano

@Zifluxhair we deal on all kinds of hair, Kano Nigeria.

IYKE Cosmetics IYKE Cosmetics
Kano

We sell all kinds of scents, creams, powders, perfumes and much more

Arewa beauty Arewa beauty
Zoo Road
Kano

Casuals,bridal,and special makeup and henna

abdulraheemmuazu1 abdulraheemmuazu1
Lamido Terrace
Kano, 700282

Your skin is a reflection of how well your body is eliminating the toxins that build up on a daily b

Tayyis glamour kn Tayyis glamour kn
Tudun Yola Darul Hadith Ibrahim Bakanike Street
Kano

We specialized in bridal, casual and special makeup at affordable price we offer home services too

GloNelly beauty therapy GloNelly beauty therapy
Address :murtala Mohammed Way Opposite Mtn
Kano, 123

FineThings By August FineThings By August
Kano

Retail and wholesales of everything fine.Fancy mobile phone cases,ropes and ring holders. Bikers short. Sunglasses. Bracelets. Oil perfumes. OversizedTeeโ€™s. Fashion Items.Human hai...