Husaen Ad saude حسين احمد سودي

An artist

28/05/2023

ZUWA GA MUNTAZIRUN (7)
Yaushe zamu bude gidajenmu ga Imam (AF)?

Kamar yadda muka kasance cikin kuka, addu'a, muzahara, da sa'ayoyi masu dimbin yawa a lokacin da sayyid Zakzaky (H) yana a hannun azzalumai, har sai da muka tabbatar da cewa jagora ya shaki iskan 'yanci, domin mun fahimci cewa sayyid (H) shine jigonmu kuma kashin bayanmu a rayuwa. Fiye da haka ya dace garemu muyi don ganin cewa Imam (AF) ya fito daga kuncin gaiba da yake ciki, ya k**ata mu fahimci cewa, idan munyi wancan yunkurin ne don jagora yana cikin yanayi mai tsanani, toh gaiba da Imam yake ciki tafi wannan tsanani. Idan kuma munyi ne domin mafitarmu dake hannun sayyid Zakzaky ga azzalumai, toh shi kuma Imam (AF) zai share zaluncin ne gaba daya. Dayawanmu mu kan yi zaton cewa; rayuwar gaiba da Imam yake ciki, wani yanayi ne da babu takura a cikinta ba wani matsatsi, amma hadisai sun tabbatar da cewa lallai Imam zai kasance ne cikin kunci, har manzo da Ahlul bait (As) s**a rika kwatantashi da annabi Yusuf (As) a mabanbantan hadisai, hakika Imam yana fuskantar jarbawa wadda kuma ba kowa ne zai kawo karshen ta ba face mu, dalili kuwa shine; abu biyu ne zai fitar da Imam daga gaiba da yake ciki.
1- Mamayar zalunci a doron kasa.
2- Samuwar mataimakansa
Sanannen abu ne ga kowa cewa, su azzalumai sunyi nasu sun gama, domin iya bakin kokarin su sunyi na habbaka zalunci ko ina a fadin duniya, sai abunda ya rage shine, shirin mu muminai, domin Allah (S) ya boye Imam ne ba don komai ba sai don kar azzalumai suga bayansa, toh ta yaya kuma Allah zai sake bayyana shi a lokacin da azzalumi s**a fi karfi kuma a sa'i guda mabiyanshi/mataimakansa basu hadu ba? Muna fadin cewa muna jiran Imam (AF) da bakunanmu a cikin addu'a da ziyara da salloli, amma abu na gaskiya shine a halin yanzu Imam ne yake jiranmu ba wai mune muke jiransa ba. Domin ruwayoyi dayawa sunzo kan cewa; a duk daren juma'a Imam kanzo ya dubi ayyukan 'yan shi'arsa, amma sau dayawa in yazo s**an sashi kuka ne. Haka an ruwaito wani matashin bawan Allah da yai mafarki da Imam yana buga masa gida, a lokacin da ya fito ya bude sai yaga Imam ne ya ziyarceshi, take yace ya Imam a dan jira in gyara, sai yaje ya boye zunubansa sannan ya fito, koda ya duba sai yaga Imam yana tafiya, sai yai kira ya Imam dawo na bude, yace har yanzu baku shirya ba, gida na biyar kenan ina zuwa amma kowa sai yace sai ya boye wani abu, inaso in iskeku shirye a kowane lokaci. Don Allah mu yiwa kanmu adalci, shin idan Imam yazo ya buga gidajenmu zamu ce masa ya Imam shigo ne ko zamuce ya jira mu kimtsa ne?
Shin mi kakeyi musamman don taimakon Imam?
Imam zaiyi aiki da malamai (masu ilmi) wane matakin ilmi ka tanadar masa?
Imam yana bukatar sojoji, da kai da sojojin Nigeria wa yafi kwanji yafi training yafi wayewa ? Kan mu kai ga na American
Imam zai tabbatar da adalci ne, shin adalcinka a mu'amala da mutane wane mataki yake?
Imam zai yi kira ne zuwa ga Allah, a matsayinka na wanda zai taimake shi ya sikarka take tsakaninka da Allah?
Mu yiwa kanmu adalci shin dagaske mun shirya?
Idan bamu shirya ba yaushe zamu shirya, sai Imam yazo sannan koko?
Fatan Allah ya tabbatar damu a cikin rundunar Imam (AF) ya kara mana juriyar sharewa sayyid Zakzaky (H) hawaye da fiddashi kunya a gaban Imam (AF)

- Husaen Ahmad ✍

26/03/2022

*suhaila bnt Malhan* sahabiyar da Muslumci ya zama sadakinta.

Ita ce Ummu - sulaim 'yar Malhan 'yar Khalid, Mamar Anas bn Malik. Ta kasance mujahida madaukakiya, maabociyar hankali da hangen gaba, tana cikin sabikunal auwaluna ( na farko farkon shiga muslumci) mubayi'ar da tayi wa manzon Allah (s) tasa mijinta (;Malik dan Nadr) yayi fushi da ita fushi mai tsanani. Yace mata: kin kafurta?Tacrme: ban kafurta ba, amma na dai yi imani da wannam mutumin (manzo s)
Taci gaba da da'awah musamman a cikin mata, tana cewa " kuce la'ilaha illallahu muhammadul rasulullahi".
Mijinta ya kasance yana ce mata " kar ki bata man dana " sai tace: ba zan lalatashi ba.
An kashe mijinta a hanyarsa ta zuwa sham, bayan labarin hakan ya risketa, Abu dalha ya nemi aurenta, yana a mushriki, ta ki sai tace masa: ya Kai Abu dalha, baka san cewa ubangijin da kake ma bauta dutse bane, bai Kara ka bai rage ka? Ko Kuma katako ne kake kaiwa kafinta ya hada maka? Akwai abunda yake kara ka da shi? Ko akwabunda yake rageka da shine? Kai baka ko jin kunyar wannan bautar taka? To bani da wani sadaki da nikeso daga gareka sai muslumci, sai muslumci ya shiga ranshi. Sukayi aure akan sadaki muslntarshi.
Ta ruwaito hadisai goma sha hudu (14) daga manzon Allah (s) taje yakin Uhud, ta sha kishin ruwa a can, ta kasance tana bama wanda s**ayi rauni agajin gaggawa a wajen yakin, taje yakin Hunain, tasha wuya a can dinma sosai, amma ta daure takobi a kugunta, tare da cewa tana da juna biyu ( na Abdullahi dan Abu dalha) a cikin wannan halin, sai Abu dalha ( mijinta) yake cewa manzon Allah (s): ya manzon Allah, ga ummu Salim nan ta dauki takobi, tace: ya manzon Allah, jna dauke da wannan takobin ne domin kare kai kar wani mushriki ya kusantoni, in fasa cikin shi, in kashe mutanen da ke kyamarka ( suke gudunka). Manzon Allah (s) yace Mata: ya Ummu salim lallai kin kyauta Kuma Allah ya gani ya yaba.
Da hannunta ta kai danta Anas bn Malik gaban manzo (s) tace: ya man

01/12/2021

الأم تسقطين طفلتها من النافذة لما احرقهن فى الغرفة، كي تكون الطفلة باقية. واقعة الزارية، ديسمبر ٢٠١٥ في حسينية بقية الله زاريا، نيجيرية⁦🇳🇬⁩😭

03/11/2021

Idan akwai Wanda ya cancanci jin tausayin ka, toh kar ya wuci Wanda ke son ka da gaskiya, shine zai iya sa kansa hatsari, domin ya Samar maka farincikin.
- Husaen Ad Saude.

20/10/2021

Babu wasu qa'idoji da ke akwai na halitta, da in mutum na da su za'a ce yana da kyau ko akasin haka. Shi kyau abu ne da aka halicci ko wane mutum da shi 100% sai dai kowa maaunin gane kyaun shi shine yadda aka tsara Wanda yake ganin kyaun shi.

30/08/2021

Shi so na gaskiya a kan tsince shi ne kwatsam a cikin zuciya, ba tare da sanin ga dalilin wanzuwar sa ba. Amma mai buqatar yin soyayya da masoyin da ya dace, kan auna masoyin sa a ma'auni na hankali, sannan ya hukunta rayuwar su da yin soyayya ko haquri da soyayyar, ba don bai son sa ba, sai don guje wa qiyayya a cikin rigar soyayya (so ba don Allah ba).

Ad Saude /Facebook.

27/08/2021

Masoyin da ya shiga birnin so ta hanyar da ya k**ata, kan samu abun so a matsayin masoyi. Akasin shi Kuma kan samu abun ki a matsayin masoyi ( kiyayya a cikin rigar soyayya).

Husaen Ad saude /Facebook

26/08/2021

An gina zuciya kan abu 2: soyayya da qiyayah.
Na farko ya cancanci Allah shi kadai, na biyu Kuma bangaren shedan shi kadai.

Ad Saude/Facebook.

24/08/2021

Ita kanta soyayyar wata nau'in Ibada ce, domin Allah bai halicci mutane ba, sai don su bauta mai, hakaza Bai halicci mutum ba, face yana da zuciya, haka Kuma bai halicci zuciya ba, sai da soyayya a cikin ta.

Ad Saude /Facebook.

22/08/2021

Mala'iku dubu hudu su ka zo su yi yaqi tare da Imam Husaen (as), ba'a basu izni ba, sai s**a koma bayan kashe shi (as), s**a tsaya bakin kabarin shi suna kuka daga ranar zuwa yau har ranar tashin Al-qiyamah. -- Imam sadiq (as).

ad Saude /Facebook.

18/08/2021

Raddi ga masu yin azumin Ashura

Ibn M Abdallah Naga hadisan ka, na ibn Abbas, Amma abin lura a nan shine: a sahihul bukhari (2004) an ruwaito manzo s yayi, amma nana Aisha a hadisi na (3831) ta ruwaito cewa bayan an sakar da Ramadan ya koma wand yaso yayi Wanda baiso ba baiyi, sannan ibni Masud a sahih Muslim (1133) yana cewa: manzon Allah ya bari bayan an saukar da Ramadan. Sanan a sahih bukhari (2002) ya kawo nana Aisha tace: quraishu yaga sunayi a lokacin jahiliyya, toh ya akai sai da yaje madina sannan yaga yahudu nayi har ya tambaya?. Sannan a sahih Muslim (1134) shi ibni Abbas an tambaye shi yace tasu'a, saboda manzo yayi ance mai ranar yahudawa ce sai ya canza.
In muka lura duk hadisan suna Karo ne da juna, Kai har ma wani wuri ance manzo s ya tambayi yahudawa sun Mai bayani yayi, wani wuri Kuma sai aka ce mai yahudawa keyi a ranar Kuma sai ya fasa har ya maida sai tasu'a, toh Kuma wani wuri ance tun da aka saukar da Ramadan ya bar yi, wani wuri Kuma ance shekarar shi takarshe ce yayi aka ce mai ranar yahudawa ce, yaece badi zai yi tasu'a, Kuma bai yi ba ya bar duniya. Sannan ban ko taya zaace manzon Allah sai yahudawa su zasu sanar da shi addini yayi ba, shida "la yandiqu anilhawa" ne, toh amma nan yayi gaban kan shi ne, Kai wajen ma yahudawa yaje s**a fada mai ana azumi kaza shi sai ya rika yi, Kuma fa ance manzo s da ya dawo madina yaga suna yi, bacin shi manzo a Rabiul Auwal ya dawo, kaga in dai zamu aza kan wannan hadisan ne toh lallai ba ababen dubawa bane, tunda shi kanshi ibni Abbas da ake jinginawa da hadisan in haka ne yayi tuka da warwara a ciki. Allah ya tabbatar da mu a kan tafarkin sa.

Ad Saude /Facebook.

15/08/2021

*BUGUN ZUCIYA 4 (CI GABA)* a cikin tarihin Jhon dan Hawai.

DAREN ASHURA
An nakalto cewa;ya kasance yana rika ma imam (as) takobi a daren Ashura.A lokacin da Imam (as) ke ma shabbansa huduba da cewa; (ku saurara; Ina jin daga yau mutanan cen basu sake bamu rata ba,ni Ina mai izini a gareku ,da na sawwake maku,ku tafi ku barni,bakuda wani laifi wurina,kuyi amfani da duhun darennan ku tafi:)
Sai sahabban imam Husain (as) s**ai maganganu tsayayyu da ke nuni ga rashin su na barin shi,har sai sun mutu suna masu kare shi.Jon ya kasance baice komai ba a lokacin ,yai zaune yana jiran wayuwar gari,tare da yiwa kansa alkawarin cewa ba Wanda zai taba imam(as) da cutarwa yana zufa,a inda yake zaune,ya rika Jin wata murya na Masa rada a kunne cewa:
(An baka izini,tunda kabimu, zaka iya tafiya)
Da ya juyo yaga imam Husain me ke Mai huduba.......Yayi ta tunani taya zai iya barin imam Husain bayan makiya sun kewayeshi ta kowane barayi,sannan uban gidanshi(Abuzar)ya tarbiyyance shi son Husaini da babansa da mamar sa da dan uwansa (as)har sai da son ya shiga ransa?shin zai iya sabunta hannun da ya lankwasa Masa,da zuciyar da yasa Masa tausayi acikin ta?Ah Ah Bai taba yuyuwa.....
Yace ma Imam (as):
Ya dan manzon Allah, kuman dare in maku rana?! Wallahi ni kaskantacce ne,jiki na mai wari ne, launi na baki ne, ka 'yanta ni da Aljannah, na daukaka daga kaskanci, nayi kamshi, nayi hasken fuska. Wallahi ba zan bar ku ba, har sai wannan bakin jinin nawa ya cakudu da jinanen ku.
FITAR SA FILIN YAKI

Sahabban Imam (as) sun ci gaba da yaqi daya bayan daya,suna yin shahada, jhon Yana daga cikin su. Ya nemi izinin Imam (as) ya fita a kan doki, yana mai waka yana cewa:
Ya fajirai suke jin saran baki*
Da takobin da aka Kira da karfe*
Kariya ga tawagar gidan Muhammad (s)*
Ina mai basu kariya da magana da hannu*
Da neman ladan haka ga mai sak**ako*
Daga Allah daya abun dayantawa*
Ya kashe mutum ashirin da biyar (25), daga makiya, har sai da karshe s

13/08/2021

zuciya 4

John (sahabin Imam Husaen (as) bakar fata)

Sunan sa Jhon, dan Hawai, dan kafadata, dan A'awar, dan Sa'adata, dan Auf, dan Ka'ab, dan Hawai. Maruwaita sun samu sabani a kan kasancewar sa cikin sahabban manzo (s).
Jhone bawan Fadl dan Abbas, dan A/mudallib ne bakar fata, Imam Ali (as) ya saye shi, dinary dari da hamsin (D150), ya bayar da shi ga Abuzarril gifary, domin yayi masa hidima, sannan kuma ya bashi tarbiyya. Ya sanar da shi, ma'anar muslumci na hakika, Wanda manzo (s) yazo da shi. Imam Ali (as) yaso ya Samar mashi da ruhi ysarkakke, da ilhama amintacciya, sai ya zabar masa rainon wannan madaukakin sahabi, Abuzarr. Ya kasance tare da shi, har yai wafati yana mai Masa hidima, daga baya sai ya koma wajen Imam Ali (as), zuwa Imam Hassan, zuwa ga dan uwan sa Husaini (as). Lokacin da za'a tafi karbala, yana a gidan Imam Sajjad (as), sai ya fita tare da shi.
Zamu ci gaba Inshaallah.

Ad Saude/Facebook.

12/08/2021

zuciya 3

Tarihin zuhair bn Kayn

Sunan sa Zuhair, dan Kayn, dan Kais, Al'anmary Al'bajily. Daya daga cikin manyan dattijan kabilar bajilah, a Kufah, ya kasance mutum mai daraja a cikin jama'ar sa, Kuma jarumi a cikin su. Haifaffen dan Iraki.

ZUHAIR KAFIN KARBALA
An ruwaito daga makusantan sa suna cew: muna tare da shi, wajen dawowa daga Hajji, a shekaran da Imam Husaen (as) yaje Iraki, mun kasance muna tafiya tare da Imam (as), babu abunda Zuhair ya tsana, k**ar ya sauka masauki guda tare da Imam (as), saboda tun farko shi ba usmaniye ne. Imam (as) ya aika Masa dan sako, da yazo yace Masa: ya Zuhair, Husaini yana Kiran ka. Sai ya ki zuwa, sai matar sa (Dalhatu diyar Amru) tace Masa: Ya subhanallah! Imam Husaen (as) dan Fatima zai aiko Kiran ka kace baka zuwa, Mi ke damun ka? Da kaje kaji abinda zai ce sai ka dawo, Zuhair ya tafi ba dan ya so ba. Bai dade ba sai gashi ya dawo, fuska a sake, hakoran sa waje, yana fara'a, yayi umurni aka cire tantunan da, ya maida cikin na Imam Husaen (as), Sannan yace ma matar sa: na sake ki, (ya umurce ta da ta koma gida, tare da dan uwanta), domin ni na bada raina zuwa ga mutuwa, tare da Imam Husaen (as). Yace ma abokan tafiyar sa: Wanda yaso a cikin ku zai iya biyo ni, Wanda ba zai je ba Kuma mun rabu lafiya. ya sake cewa: zan baku wani labari, Munyi yaki da lanjar, Allah ya bamu nasara, muka samu ganimomi, sai Salmanul-farisy yace mana, "kunyi murna da nasarar da Allah ya baku, da Kuma ganimomin da kuka sama?" Sai muka amsa, eh! Sai yace," toh idan kun fuskanci matashi daga iyalan manzo (s), ku kasance masu tsantsar farinciki, da kasancewa wa'anda za'a kashe a tare da shi, fiye da murnar wannan nasarar da ganimar da kuka samu. Toh ni zan maku bankwana, ya koma cikin tawagar Imam Husaen (as), tare da dan ammin sa, Salman dan Madrib.
RANAR DAREN ASHURA
Imam Husaen (as), ya aika dan'uwan sa Abbas (as), zuwa ga dan Sa'ad, yace: kaje ku hadu da su, ka tambaye su, mi ya kawo su, kuma mi suke bukata? Sai Abbas (as) ya hau doki,

11/08/2021

Yau mun bada tarihin sayyida zainab, saboda na zuhair bai ida kammala ba, muna kan shi Inshaallah. Ai mana afwa.

11/08/2021

*Bugun_zuciya_2*
Tarihin sayyida zainab (sa).

Sunan ta Zainab, diyar Imam Husaen, dan Ali dan Abi dalib (as), anaata lakabi da zainabul kubra,Haura'a, Àlimatu, badlatu karbala, Aqila, ummul-musa'ib, Garibah, Dahira, Sayyida.
An haife ta 5 ga jimada ula, shekara ta 5 bayan hijra,a Madina, ta bar duniya 15 ga watan Rajab, shekara ta 62 bayan hijra.
Ta Auri dan kawun ta, Abdullahi bin jafar bin Abi dalib (as). Sun haifi 'ya'ya guda 5, Aun, Muhammad,Abbas,Ali, ummu-kulsum.
Sayyida zainab (sa), ta kasance jaruma, wadda ta taka babbar rawa wajen saurar Imam Husaen (as) a Karbala, ta hanyar rawar da ta taka wajen cigabantar da saurar, ta bayyana wa duniya zahirin gaskiyar faruwar lamarin, tare da bayyana manufar su a kan addini.
Lokacin da Imam (as) ya fita tare da wasu 'yan kadan na makusantan sa, da sahabban sa,domin yin jihadi a tafarkin Allah, daga aikin Yazidu Dan ma'awiya, sayyida zainab takasance a tare da shi, sannan ta fuskanci duk azabobin da aka fuskanta a tafiyar, Kuma ita ganau ce a karbala, Kuma jikin ta ya shaida mata dukkan musibu, da cutarwada ta faru a wajen, Idanun sayyida zainab (sa) sun gane mata ranar Ashura, inda dukkan makusantan ta s**a fafata, kuma aka shahadantar da su, day bayan daya, k**a daga 'ya'yan ta, 'yan uwan ta, da sauran dangin su Hashimawa, aka cire kawunan su daga gangunan jukunnan su, aka masu kaca-kaca da wukake, aka barta da zawarawa, tare da jariran marayu, cikin yanayin matsananciyar yunwa da kishin ruwa, suna masu jimamin rashin mazajen su. A lokaci guda dakarun Yazidu na zagaye da su ta ko Ina, karshe s**a sa ma tantunan su wuta, s**a ci zarafin mata, da yara kanana, sayyida zainab (sa) ta sa juriya a cikin fuskantar wannan babbar jarbawa, da dakewa, sannan ta hakura da duk zaluncin da akai mata, ta bar wa Allah (s) hukunci.
An shiga da tawagar mata da 'ya'yan Imam Husaen a kufa bayan kisan shi a karbala, da umarnin Abdullahi bin Ziyad, (Wanda shine gwamnan garin a wancan lokacin), mutane s**a fito kallo, mata s

10/08/2021

Tarihin shahadar sayyida Ruqayyah Yar imam Husaini (as).

Sunan ta Ruqayyah diyar Husaen dan Ali (as)
Sunan mahaifiyar ta ummu ishaq.
An haife ta shekara ta 57 BH.
Ta kasance ta shaku da baban ta (as), Yana daukar ta a ko wane lokaci yana sunbatar ta, hakaza mahaifiyar ta, ta kasance tana kamshi irin na mahaifin ta (as).
Ta kasance a cikin tawagar baban ta (as) tun daga makka zuwa kufa, har zuwa karbala, ta kasance daga cikin yaran da Imam Husain da s**a kwashe kwanakin nan cikin kukan yunwa da kishin ruwa 😭
Bayan shahadar baban ta ta kasance cikin Wanda aka kora har zuwa dimaskas, ta kasance a hanya tana tambayar Ina mahaifi na?? Sai ace mata yayi tafiya🏇 amma gobe zai dawo🥺 sai ta sake tambaya😢 Ina ya tafi?? Mi yasa bai tafi da ni ba?? Haka take tsawon tafiyar nan kuka bai yanke a idon ta ba😭😭 bayan sun isa shaam, ta samu yin barci🛌 a nan tayi mafarkin mahaifin ta a sadda aka shahadantar da shi😰😓😢 Farkawar ta ke da wuya ta fashe da kuka😢 tana Kira😢😓 nan take sauran mata s**a barke da kuka😭 Jin haka yasa yazidu yai tambaya🤴 mi ke faruwa ? Aka fada masa diyar Imam Husaen ce ke neman baban ta😓😰, Ko da yaji haka, sai yasa a kawo mata kan babanta😰😓 aka kawo mata shi a cikin kwano rufe da hankici🥫 da gani tace ni ba abinci nike nema ba🍛, baba na nike nema🧔, da ta bude hankicin sai taga Kai, tayi tambaya, wannan kan fa?? Da ta sake dubawa sai taga baban ta ne😭😭 Ya Allah😭🥺 ta sa kananan hannuwanta masu albarka🙌, ta dauki kan🥺 ta sunbata, tace baba! Wa ya kashe ka? Wa ya cire kan ka? Mi yasa ban kasance tare da Kai ba?.......😭😭 Wuri ya dinke da kuka😭😭 haka tasa kan ga qirjinta tana kuka, har zuciyar ta ta buga🥺🥺 Imam zainul Abidin (as) yace da sayyida zainab (sa) janye ta Allah ya dauki ranta😫😫 Innalillahi wa inna ilaihi raji'oun 🥺😭🙆

Zamu kawo na zuhair bn qayn gobe Inshaallah.

A'azamallahu ujurana bi musabina bil husaen As wa alihi.

16/07/2021

New track by Husaen Ahmad and Chall Më YaqUb
# Ameerul mumineen. Stand On Justice BoysHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سوديHusaen Ad saude حسين احمد سودي

12/07/2021

Muna masu yi maku barka da wannan lokaci 🎶🎶🎶

Sannan muna sake tunatar da ku video din waqar mu ta ghadeer 🎶

________Ameerul_mu'umineen_______

Cikakken video din yana man tafe zuwa gare ku Inshaallah 🌹🌹🎶

Ku kasance tare damu, da Kuma taya mu yadawa.

Mun gode.🙏

Photos from Stand On Justice Voice's post 08/07/2021

New track with my friend 💙

Coming soon....

04/05/2021

Struggle for Palestine is matter of humanity not religion or sects

29/03/2021

Domin samun Sabuwar Wakarmu ta Nisfus Sha'aban ku shiga wannan link
https://t.me/had787898guy

25/03/2021

What have you sacrifice for the Palestine to be free!?

23/03/2021

Itz sha'aban month of Imam Mahdi (AF) and mazloum sheikh zakzaky (H) the parade by Hurras of the Islamic movement in Nigeria before Zaria massacre.

17/03/2021

paper presentation, yaum Ali, katsina (FOSA).

Photos from ‎Husaen Ad saude     حسين احمد سودي‎'s post 31/01/2021

Kar ku damu
Kukan ya samo asali ne daga emotion na sabuwar waqar da ke duba daga gare ni zuwa gareku cikin satin nan, ku kasance da ni domin kashe kwalkwatar idonku, tana fitowa soon inshallah.

28/01/2021

الحمدلله علي كل حال

11/01/2021

# Mun sama challenge boyz zata fashe don't miss it on 15th jumada thaney.

08/01/2021

H_A_D_GUY on the beat_stand_on_justice_boyz_chairman.

24/12/2020

At lokoja last week

19/12/2020

At kogi state today 5 years of Zaria massacre 2020 no to injustice on Justice boyz # 1000+ modered forget.

12/12/2020

1000+ of people were killed by Nigerian soldiers on 12/12/2015 at Zaria, include students,paragnent female,young children, ladies, born alot with fire,burred alot in massgrave, continues up to date wich make it 5 years of genocide,do not be silent against humanity if you are real man.

07/12/2020

I'm going to be there Inshaallah

06/12/2020

MUNANA 10 SAKAMAKO 10
manzo (s) yace:
Idan al'umma ta s**a kebantu da abubuwa goma (10),Toh Allah ta'ala zai axabtar da su
Gasu k**ar haka:
1-Idan s**a bar karanta Addu'a,bala'o'i zasu sauka.
2-Idan s**a bar yin sadaka,za'a samu yawan cutuka.
3-Idan s**a hana zakka,dabbobi zasu riqa mutuwa.
4-Idan s**a shugabantar da azzalumi,za'a yanke ruwan sama.
5-Idan zina ta yawaita,za'a yawaita mutuwar fuji'a.
6-Idan cin riba yayi yawa,girgizar qasa zata yawaita.
7-Idan s**a riqa hukunci bada abinda Allah ya saukar ba,Allah zai sallada maqitansu kansu.
8-Idan s**a bar cika alqawari,Allah zai jarabce su da kashe-kashe.
9-Idan s**a tauye mudu, Allah zai jarabce su day fari.
10-ya karanta wannan ayar"ظهر الفساد في البر والبحر بما كسبت ايدي الناس ليذيقهم بعض الذي عملوا لعلهم يرجعون"
Fassara "Barna ta bayyana a batan qasa da teku saboda abinda mutane s**a aikata da hannayensu, Allah zai dandana masu wani bangare na azaba ko zasu juyi"-noor 41.
Ku ci gaba da kasancewa da page din mu na Husaen Ad saude حسين احمد سودي domin ci gaba da kawo maku tunatarwa inshallah.
Zamu kawo maku hadiyyoyi guda arba'in (40) da ba'a tsallakewa lahira sai da su Inshaallah.

20/11/2020

The pencil work was already done successfully 👍 I'm proudly artist

15/11/2020

Do you know?

15/11/2020

Are you ready by now ?

11/10/2020

If we never move this wahala never end fight for freedom nah.

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address

Mobil Quarter Area
Katsina
HADGUY
Other Musicians/Bands in Katsina (show all)
Dan Hausa amanar bashir mai shadda Dan Hausa amanar bashir mai shadda
Daura
Katsina

Following my real account

Jazuga fashion Jazuga fashion
Katsina

Muna gudanar da dinkuna da kuma koyarwa acikin sauki da ragusa.

Mus'ab khaleed Mus'ab khaleed
Multipurpose Women Center
Katsina

Artiste connect�

Jamilu habibu Jamilu habibu
Babban Duhu
Katsina, 0814318

m_orezy m_orezy
Katsina, STATE

Smart Boy Young boy Funtua Smart Boy Young boy Funtua
Katsina, 666666

Music

Saifullahi m auwal Saifullahi m auwal
Sake
Katsina, 6993

Itz Moses AD Itz Moses AD
Danmusa Local Government
Katsina

Abdul Alaskan waka fans Abdul Alaskan waka fans
Katsina, BATAGARAWA

Nigeria

AbdullhafiX AbdullhafiX
Layin Taha
Katsina, AUL£

Yaro mai tashe Yaro mai tashe
Sabuwar Anguwa Kofar Kaura
Katsina, AYISHIKAWAI

Artist