Aleeyou Masnawa

Aleeyou Masnawa

You may also like

Mr Thangi
Mr Thangi
Mrs.INTAKE
Mrs.INTAKE

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Aleeyou Masnawa, Writer, Katsina.

05/01/2024

Cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan jihar ta fitar ta ce makaɗan gangin sun fito daga unguwannin Rijiyar Lemo da Kurna, kuma a lokuta da dama su ne ke ingiza wutar dabanci a Kano.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/3vm9SMR

Rashin lafiya ce ta hana minista Sadiya amsa gayyatar da mu ka yi mata - EFCC - Daily Nigerian Hausa 05/01/2024

Rashin lafiya ce ta hana minista Sadiya amsa gayyatar da mu ka yi mata - EFCC - Daily Nigerian Hausa Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, ta ce tsohuwar ministar harkokin jin kai, magance bala’o’i, da ci gaban al’umma, Sadiya Umar Farouq, ba kin amsa gayyatar da aka yi mata ta yi ba k**ar yadda wani bangare na kafafen yada labarai s**a ruwaito. Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, w...

02/10/2023

Cikakken Jawabin Shugaba Bola Tinubu.

‘Yan uwana ‘yan Najeriya,
Ina farin cikin yi muku jawabi a yau, ranar cikar kasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban kasarmu mai albarka, kuma zallar dan uwanku dan Najeriya.

2. A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, muna jinjina ga iyayenmu da s**a kafa Najeriya, mazansu da matansu. Ba don su ba, da ba a samu kasar Najeriya ba. Gwagwarmayarsu, sadaukarwarsu, da jagorancinsu ne s**a haifar da ‘yantacciyar kasar Najeriya mai mulkin kanta.

3. A wannan lokacin, muna karfafa wa juna gwiwar cewa a matsayinmu na ‘yan Najeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunkule da kuma a daidaikunmu. Babu wanda ya fi wani a cikinmu. Nasarorin da Najeriya ta cimma su ne abin alfaharinmu. Kalubalen da muka jure wa su ne ke karfafar mu. Kuma babu wata kasa ko wani iko a duniya da zai iya dankwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan kasar taku ce, ‘yan uwana. Ku so ta, ku karrama ta a matsayinta ta kasarku ta kanku.

4. Najeriya ta isa kasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarinta. Allah ya azurta mu da kabilu, addinai, da al’adu dabam-dabam. Sai dai dankon zumuncin dake tsakaninmu ya na da matukar karfi ko da yake ba ganin sa ake ba. Mun hadu kan buri guda daya na samar da zaman lafiya da cigaban al’umma, da fata guda na bunkasar arziki da hadin kai, da kuma manufofin hadaka na juriya da adalci.

5. Samar da kasa da aka dora bisa harsashin aiwatar da wadannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabanbata ya zamo aiki mai matukar albarka da yake fama da kalubale. Wadansu mutanen sun ce bai k**ata a samu ‘yantacciyar kasar Najeriya ba. Wasu sun ce kasarmu za ta rushe. Har abada su na bisa kuskure. A nan, kasarmu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.

6. A bana, mun tsallake wani siradi mai muhimmanci a tafarkinmu na tabbatar da cigaban Najeriya. Zaben da muka yi wa gwamnatin dimokradiyya ta bakwai a jere, na nuna cewa kasarmu ta yi riko da tsarin dimokradiyya da aiki da doka.

7. Ranar da na k**a mulki, na dauki alkawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar kasa ta mu. Daga cikin alkawurran har da yi wa tattalin arzikinmu garanmbawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.
8. Na ce daukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin dora kasarmu kan tafarkin walwala da bunkasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo karshen tallafin man fetur.

9. Ina sane da wahalhalun da s**a biyo baya. Idanuna suna gani kuma zuciyata ta na kunci. Ina son in bayyana muku dalilin da ya sa wajibi mu cigaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Wadanda ke son a cigaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kudaden waje, mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje a cikin fadama. Ni ba haka nake ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan muna son gidanmu ya yi kwari, ya dade dole ne mu gina shi kan tsandauri.

10. Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da ci gabanmu da daukakarmu ke bukata. A yanzu muna dauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin kasarmu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurinsu. Zamu samar da Najeriyar da za a mayar da yunwa, fatara, da wahala su zama tsohon labari.

11. Ba na farin cikin ganin al’ummar kasar nan na fama da wahalar da ya k**ata a ce an sauke ta a shekarun da s**a wuce. Zan so a ce babu wadannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari.

12. Gwamnatina na yin bakin kokarinta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana muku matakan da muke dauka domin rage wannan radadin da magidanta da iyalai ke fama da su.

13. Mun fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.

14. Bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.

15. Domin kawo ci gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunkasa bangarorin dake da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi s**a karbi kudi domin ba da tallafin sassauta radadin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da gobe.

16. Bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matukar muhimmanci. Dangane da haka ne muka bude wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar Gas a fadin kasar nan. Wadannan motoci za su caji kudi mai sauki da bai k**a kafar yadda ake biya yanzu ba.

17. Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa kasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bada horo a fadin kasa domin koyarwa da bada sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da kasarmu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samarwa tattalin arzikinmu mak**ashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.

18. Na dauki alkawarin tsaftace barnar da ta yi wa Babban Bankin Kasa dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na nada na gab da gabatar da rahotonsa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance afkuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokinmu na tasarrufi da kudi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kudi kadai.

19. Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da adalci. Na kaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a kasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaki ga ci gaban kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.

20. Domin bunkasa samar da aikin yi da kudin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da s**a nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun kara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.

21. Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan wadanda ake bai wa tallafin kudi kai tsaye domin rage masu radadi.

22. Gwamnatina a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunkasa hadin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An dora wa manyan hafsoshin sojin muhimmin aikin farfado da karsashin rundunonimu.

23. A nan, nake jinjina da yabo ga dakarun tsaronmu, da suke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron kasarmu. Da yawansu sun riga mu gidan gaskiya. Muna tuna su a yau tare da iyalansu. Za mu bai wa dakarunmu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kansu a madadin al’ummarmu.

24. Zamu ci gaba da nada mutane bisa muhimman muk**ai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a cigaba da kulawa da mata, matasa da masu bukatu na musamman a wadannan nade-naden.

25. Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Kasa murna kan rawar da s**a taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da bata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya dora musu na tantance wadanda za a nada da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

26. Haka kuma ina taya bangaren Shari’a murna a matsayinsu na ginshikin dimokradiyya da adalci.

27. Ina kuma taya murna ga kungiyoyinmu na ci gaban al’umma da kungiyoyin kwadago bisa sadaukarwarsu ga dimokradiyyar Najeriya. Ba ko da yaushe ra’ayinmu kan zama daya ba amma ina mutunta shawarwarinku. Ku ‘yan uwana ne kuma ina girmama ku.

28. ‘Yan uwana ‘yan Najeriya, tsoro ko kiyayya ba za su kawo mana ci gaba ba. Za mu iya samun ingatacciyar Najeriya ne kadai ta hanyar kwarin gwiwa, tausayi da kuma sadaukar da kai a matsayin dunkulalliyar kasa guda.

29. Na yi alkawari zan ci gaba da mayar da hankali tare da bauta muku cikin amana. Ina kuma gayyatar kowa ya bada gudunmawa wurin ci gaban kasarmu abar kaunarmu. Za mu iya. Ba makawa za mu yi. Kuma tabbas za mu yi nasara!!!
30. Baki dayanku ina taya ku murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

31. Nagode da sauraro.
32. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.

"Ku zo ku auri 'ya'yana": Mahaifiya ta bukaci samari su nemi auren 'yayanta mata 04/07/2023

"Ku zo ku auri 'ya'yana": Mahaifiya ta bukaci samari su nemi auren 'yayanta mata Wani bidiyo ya nuna wata mata tana gayyato samari da su zo su nemi auren kyawawan ƴaƴanta mata. Ta bayyana cewa sun daɗe babu miji ga shi suna ta ƙara tsufa.

28/05/2023

Poster 4:
National Identity Enrolment:

From 2007 to Oct 2020. 39 million enrollees.
Then NIMC transferred to Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami) for Supervision in Oct, 2020.

From Oct 2020 to May 2023. Over 100 million enrollees.

More than 61 million citizens enrolled in 2 years and 7 months.

Tababa da rashin tabbas sun mamaye sabon jirgin Najeriya 27/05/2023

Tababa da rashin tabbas sun mamaye sabon jirgin Najeriya Jirgin sama kirar Boeing 737-800 wanda ya sauka a filin jirgin saman Abuja domin kaddamar shi a matsayin Nigeria Air, bincike ya nuna cewa jirgin mallakar kamfanin jiragen saman Habasha ne.

Photos from BBC Hausa's post 27/05/2023
27/05/2023

Ya k**ata a ƙirƙirar wa tsoffin matan shugabannin ƙasa wani gata bayan sun bar mulki — Aisha Buhari
https://dailynigerian.com/hausa/k**ata-tanadar-tsoffin-matan/

12/05/2023

Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami) presenting a copy of his book- "Skills Rather than Just Degrees," to brother Qariy, Goni, Afif Muhammad Taj

12/05/2023

PUBLIC NOTICE

The NDLEA online assessment platform will remain open today Thursday, 11th May, till 6:00 am tomorrow Friday 12th May, to allow applicants in all batches who received an email but were unable to take the test due to technical difficulties to do so.

To login, please ensure that you enter your ID in this format: NDLEA-SUPT-2023-1234567890. Also use a reliable internet connection. Applicants should kindly refresh their browsers if they encounter time out errors, as a result of the heavy traffic on the server, which it is actively filtering.

- Femi Babafemi

11/10/2022

Congratulation
Congratulation
Congratulations

With a Full pleasure, Happiness and Appreciation
We collectively the Family of Alhaji Ummaru Matawalle And Zuriar Malan Barmo Thanks mr President Muhammad Buhari for this great honour given to our Family with the conferment of National Honour (OON).
We wish to send our gratitude and to pray Almighty Allah Subhanahu Wataala to guide,protect and to give you good health and long life Ameen.
We Can't Avenge what You Did To us our Boss. But we will work Hard to Repay Goodness by the Grace of God
Alhaji Abbas Umar Masanawa was a great pillar of our great Family he is a Father, Uncle, Brother and a mentor that always seen and foreseen the affairs of the family.
Congratulations
And thank you once again

Umar Faruk Abubakar

05/10/2022
Photos from FEDERAL FIRE SERVICE's post 05/10/2022
Burkina Faso: Faransa ta yi tir da harin da aka kai ofishin jakadancinta bayan juyin mulki 05/10/2022

Burkina Faso: Faransa ta yi tir da harin da aka kai ofishin jakadancinta bayan juyin mulki Wasu fusatattun masu zanga-zanga a Burkina Faso sun kai hari a ofishin jakadancin Faransa da ke Ouagadougou babban birnin kasar.

Timeline photos 05/10/2022

ABU ta cika shekara 60 da kafuwa.

Wace irin rawa jami'ar ke takawa a Najeriya?

Al'ummar Burkina Faso sun yi zanga-zangar bukatar shigowar Rasha kasar 05/10/2022

Al'ummar Burkina Faso sun yi zanga-zangar bukatar shigowar Rasha kasar Dubunnan al'ummar Burkina Faso dauke da tutar kasar Rasha sun gudanar da zanga-zanga a Ouagadougou babban birnin kasar a jiya talata, a wani yunkuri da ke nuna bukatarsu ga kawo sojojin Moscow kasar…

05/10/2022

A ƙarshe! Yana da kyau MATA su fukanci cewa zuciyarsu ta NAMIJI ɗaya ce. Namiji kuwa zuciyarsa ta Mata Hudu ce!

12/09/2022

Schools Resumes.
Ya Allah provide school fees for parents. Make it ease for them and for us.

Jami'an NDLEA Sun Cafke Mai Tsohon Ciki Dauke da Tulin Miyagun Kwayoyi 12/09/2022

Jami'an NDLEA Sun Cafke Mai Tsohon Ciki Dauke da Tulin Miyagun Kwayoyi Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta damke wata mata mai tsohon ciki mai shekaru 25 dauke da kwayoyi methamphetamine a garin Auchi jihar Edo.

Hukumar SSS ta gano kakin Soji da makudan kudade a gida da Ofishin Tukur Mamu 12/09/2022

Hukumar SSS ta gano kakin Soji da makudan kudade a gida da Ofishin Tukur Mamu Hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta sanar da samun tarin kakin Soji da makudan kudade a gida da ofishin Tukur Mamu yayin sumamen da s**a kai masa.

12/09/2022
25/04/2022

Hadari sa gaban ka inda kakeso 😅🤣

15/04/2022

Sannu zainabu

01/04/2022

Alhamdulillah Ramadan Mubarak

01/04/2022

Dear sweetheart kisani cewa duk randa kika kuskure kika bawa abokiyar ki number ta wai muyi. Soyayya to kinsani ita zuciya bata da Kashi fa😎✌️

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Katsina
Other Writers in Katsina (show all)
Fortizo Food & General Enterprise Fortizo Food & General Enterprise
Kwado
Katsina

FORTIZO food and General Enterprise,is into food processing, content writing, copyright.

Real S Mabai page Real S Mabai page
Katsina

I really appreciation to open this page in order to described my manifesto so I thank God to give me appoturnity to open it!!!

Rahusa market by Adam y zango ytk Rahusa market by Adam y zango ytk
Ytk1#########
Katsina, ANYTHINGDEYFINE20K

End kidenfing noth

Abban Aslam Daura Abban Aslam Daura
Katsina

Shoes and bookshop

Umar Sulaiman Saleh Umar Sulaiman Saleh
No. 488 G. M. G Street, Kahutu B, Danja
Katsina

Whoever trusts in Allah, Allah will be sufficient for him!

Birnin kuka Geedah Birnin kuka Geedah
Aduwa Daya Birnin Kuka
Katsina, ASB

Abdul Aziz M Sani Abubakar, Mai Trader, Birnin-Kuka, Mashi Local Government, Katsina State, Nigeria.

Arewa Status Quo Arewa Status Quo
Katsina, 2020

First of all invite your friends to this page thank you

Abdul suraj Abdul suraj
Dan Rimi Oppsite Albarka Chemist
Katsina, 459533

Slm

Mu San chuwan kammu Mu San chuwan kammu
R***a Safana
Katsina

Sandamu birnin geza Sandamu birnin geza
Sabuwar Abuja Sandamu
Katsina, NORTHWEST

New investment

Masa'ud Kabir murja Masa'ud Kabir murja
Yan Katako
Katsina, 0000

PRODUCTS

Wanderer Wanderer
Katsina

•I'm tryna pass my hardest moments•👻🏅 •Ooeh everyone believe am fine• 💖💜🤍