Tsauni Global Media
Tsauni Global Media Kafar yada labaru ce mai zaman Kanta.
A cikin wata sanarwa, shugaban ya kuma bayar da umarnin ɗage duk wasu takunkuman da Najeriya ta ƙaƙaba wa ƙasar kamar yanke wa ƙasar wutar lantarki da kuma riƙe kadarorinta.
MALAN KAYI ABINDA YA DACE
LALLAI ALLAH YANA NAN A MADAKATA
HIRAR MUSAMMAN: Miji na yana kwashe watanni 9 zuwa 11 yana bacci bai farka ba, wani lokacin kuma idan Allah yasa ya farka, zai iya daukar wata daya, biyu zuwa uku yana yawace-yawacen sa a gari, kafin ya sake komawa bacci.
Shekaru 15 kenan muna fama da wannan lalurar.
Da Guiwa za'a tafi Sujjada ko da Hannu?
Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo
🔴 Shugaba Bazoum Mohamed har yanzu yana cikin koshin lafiya a cewar 'yan uwansa, kuma ya tsaya tsayin daka, ya ki sanya hannu kan takardar murabus din da aka mika masa.
Bisa labarin da muka samu, Janar Tchiany da jami'an sa a halin yanzu suna kewaye da rundunar tsaron kasa da kuma FDS daga kewayen birnin Yamai (Dosso, Tillabery, da dai sauransu) domin dawo da tsarin jamhuriyar.
Ana ci gaba da tattaunawa tare da Tchiany wanda ke kan gaba wajan yinƙurin juyin mulkin
MATAR DA TA KÀSHE MIJINTA
Matar da ta kashé mijinta a Bauchi sunanta
Maimunatu Sulaiman 'yar Shekara 21, sunan mijinta Aliyu Muhammad
Kamar yadda ta bayyana wa 'yan sanda masu bincike, tace cacar baki ne ya shiga tsakaninta da mijinta, sai da ta bari sun kwanta a kan gadonsu na Sunnah da nufin zasuyi bacci bayan kammala cacar bakin, sai ta dauko wuka ta caka masa a kirjinsa wanda hakan yayi ajalinsa
Yanzu haka tana nan a sashin binciken manyan laifuka na 'yan sanda State CID Bauchi, idan an kammala hada bincike za'a gurfanar da ita a Kotu
Muna fatan Allah Ya jikan Aliyu
IDAN AN BI TA BARAWO ABI TA MABI SAWU
an fara gina badalar Kano tun daga shekarar 1095 zuwa 1134 kimanin shekaru 928 da s**a wuce kuma an dauki kimanin shekaru 39 ana aikin gina ta cikin zamanin sarakunan Kano 3 Sarki Ginjimasu, Muhammadu rumfa zuwa lokacin sarkin Kano Muhammadu nazaki cikin tsakiyar karni na 14
dalilin ginata a wancen lokacin shine don bawa birnin Kano kariya daga mahara da ke zuwa cikin dare su farwa al'umma, domin samun cikakken tsaro da kwanciyar hankali ga al'ummar garin, badalar tana da kofofi 15, sannan tana da tsawon kafa 50 tana da fadin kafa 45 tana da nisan kilomita 14
lokutan baya badalar tana karkashin kulawar masarautar Kano, wanda an samu a tarihi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi l ya taba kafa kwamiti kan kula da bada a 1960 wanda ya dauki mataki mai tsauri akan masu yankarta suna gini
amma daga baya aka mayar da alhakin kulawar ta a hannun National museum Wanda har yanzu badalar hakkin kulawarta a hannun hukumar yake
kusan shekaru 100 ko sama da haka aka dena kulle kofofin badala Sannan mutanen gari suna sarar ta suna diban kasar suna buga bulo suna yin gini ko diban kasar suna ciko da ita wanda wannan shine abinda ya jawo rushewar ta wani wurin ma ya zama fili kamar babu ginin ta
tabbas Badala abar tarihi ce, abar alfahari ce wa tarihin kano da za'a nuna kamar tsofaffin wuraren tarihi na duniya irin su Great wall of china irin su pyramid of Egypt da sauran su
an dade gwamnatoci suna bada plot Allocation a jiki ko gefen badala tun lokuta masu nisa, zaka yarda Dani idan ka zagaya jikin badalar zaka tarar da gidaje ko gine ginen da sun haura shekaru 40 ko fiye da yin su
Gwamnatin kasar Germany sun taba zuwa Kano da zumar mayar da ginin badalar Kano wanda s**a fara daga sabuwar kofa amma ko Dan agundi basu kai ba abin ya gagara sabo da wahalar aikin sannan babu ma kasar da za'ai ginin
abin tambayar shine waye yake bada izinin gini a jiki, gefe, ko kan badala
Sarakunan kofa, gwamnatin jaha, national museum ko shugabannin kananun hukumomi ?
duk inda babu gini zaka ga ya zama wurin zuba shara ko kashi misali hauren shanu daidai inda akai gidan mai na Metrix masu diban kashi ne suke zuwa su zubar da kashi a wajen har motocin su, da garewanin da suke diban kashin anan wajen suke kwana duk wanda yasan wajen yasan da haka
idan da ace ana son badala ta dawo yadda take ne a da to Rusau sai ya zagaye ta baki daya kuma na tabbatar za'a rushe ginin da yakai shekara 50 da yin sa
idan an rushe gine ginan jikin badala a wannan lokacin, shin meye gwamanti zatai da wajen, sabuwar badala zata gina ayi wa kofofin Kano (gate) a dawo da rufe garin ko kuwa filayen za'a bari aci gaba da zuba shara ko sabon Allocation za'a bawa wasu su sake ginawa ?
ya kamata gwamanti tayi duba izuwa makomar wannan wuri da a yanzu ya zama Maraya kuma ya ƙawata birni
Allah yasa mahukunta su hankalta su bar shawarar mazuga da yan bani na iya da yan idan bani ba kowa ya rasa
muzammil mandawari
24-June-2023
6-Zul-hijjah-1444
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya sauke dukkanin manyan hafsoshin tsaron kasa da Shugaban 'Yan Sanda tare da na'din Sabbi da s**a ha'da da:
1. Mallam Nuhu Ribadu, Mai bada Shawara a fannin tsaro
2. Maj. Gen. C.G Musa, Babban Hafsan Tsaron 'kasa
3. Maj. Gen. T. A Lagbaja, Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa
3. Rear Admirral E. A Ogalla, Babban Hafsan Tsaron Sojojin Ruwa
4. AVM H.B Abubakar, Babban Hafsan Rundunar Sama
5. DIG Kayode Egbetokun, Mai Rikon Mukamin Sifeton 'Yan Sanda na Kasa
6. Adeniyi Bashir Adewale, Sabon Shugaban Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Custom
Bola Tinubu ya Kara na'din Sabbin Masu Shawara kamar haka:
1. Hadiza Bala Usman, Mai bada Shawara kan manufofin Gwamnati
2. Hannatu Musa Musawa, Mai bada Shawara ta musamman kan al'adu da habaka tattalin arzikin fannin Nisha 'dan tarwa
3. Sen. Abdullahi Abubakar Gumel, Babban Mataimaki ga Shugaban Kasa a Sha'anin Majalisar Dattijai
4. Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan lamuran Majalisar Wakilai
Da Dumi-Dumi
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele daga mukaminsa nan take.
Tuni kuma aka bukaci ya mika ragamar aikinsa ga mataimakinsa har zuwa lokacin da za a kamalla bincike a kansa.
Ya kuke kallon matakin shugaban na Najeriya?
Shahararren mawakin nan dan kasar amurka watu Kanye West da matarsa sun saka tufafi wanda ya dauki hankali alokacin da zasu tafi coci a ranar Lahadi a Los Angeles da ke Amurka.
A hotunan da aka wallafa a ranar Litinin an ga mawakin sanye da bakaken tufafi har da riga mai ciko a kafada da rubutu ‘Polizei’ kalmar da ke nufin Dan Sanda a yaren Jamusanci da kuma damammen wando.
Yayin da matarsa Bianca ta saka bakaken tufafi daga kai har kafa, ta saka bakin takalmi mai tudu tare da wani nau’in soso da ya zagaye wuyanta da kafada.
📸 justjared (Instagram)
An Karrama Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe A Haifarshi Ta Kankara
A jiya lahadi 4/6/2023 wata kungiya maisuna Kankara Unity Forum tayi taron karramawa ga sabon Mataimakin Gwamna Jahar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe taron daya gudana a farfajiyar Sakatariyar Karamar Hukumar Kankara.
Ajawabin shi Hon. Anas Isah Kankara wanda shine Mai masaukin baki yace ya nuna farin cikin shi akan samun Mataimakin Gwamnan Dan asalin Karamar Hukumar Kankara.
Haka zalika shugaban karamar hukumar yayi fatan Allah ya maida kowa gidanshi lafiya
Bayan Kammala jawabin Hon. Anas Isah shugaban kungiyar Prof. Yahaya Aliyu yace sun Karrama Hon Faruk Lawal Jobe ne domin taya shi murna gamida da bashi goyon baya akan zamanshi Zaɓaɓɓen Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina kuma kasancewar yana daya daga 'Ya'yan wannan kungiya dake fadi tashin kawo cigaba agarin Kankara.
Prof. Yahaya yakara cewa, wannan karraawa ta kasance itace akaro na biyu inda ko ashekarun baya lokacin ya da Gwamna mai barin Hon. Aminu Bello Masari ya bashi mukamin mai bashi shawara afannin harkokin kudi na Jihar Katsina
Shuagaban kungiyar ya yayi fatan Allah ya sanya yasa bayan kammala wa'adin shi na shekaru takwas Hon Faruk Lawal yagajeshi.
Shima Malam Abdulbashiru Unguwar makawo da Babban Limamin Juma'a na JIBWIS Malam Yahaya Kankara s**ayi Nasiha akan yiwa shuwaganin biyayya da kansu suma shuwaganin akan mabiyansu.
Haka zalika an mikawa Hon. Faruk Lawal kyautuka na musamman na Gwamna Jahar Katsina Dikko Umar Radda PhD. da kuma nashi na Karan kanshi Mataimaki.
Daga cikin wadanda s**a bayar da wannan lambar karramawa akwai kungiyar Kankara Unity Forum tare ,Kungiyar Nakasassu ta karamar Hukumar Kankara da kuma Kungiyar Zumunta Youth club Kankara.
Kanwan Katsina Hakimin Ketare Alh Usman Bello Mni wanda ya jawabi amaimaikon Hikimai biyu dake Karkashin karama hukumar Kankara.
Basaraken bayan nuna godiya ga Allah yakuna isar sakon Al'ummar dayake abangaren
Àkwai shugaban jamiyyar APC na Karaduwa, tare da wakilin Senator Muntari Dandutse.
Mataimakin Gwamnan Hon Faruk Lawal Jobe Yayi dogon jawabi inda ya bukaci Jama'a da su cigaba da yima su Addu'a don ganin Gwamnati ta samu nasarar aikin ta.
Yakuma ya fadawa Al'umma sai anyi hakuri domin kawo gyara Jihar Katsina.
Mai girma Hon Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa wannan Gwamnati zata bayarda Muhimmanci Sosai ga Mata da Matasa.
Mawakan zaman Waɗanda s**a hada da matashinan M20 Hon Sule 'yar tsamiyar Sarkisuma sun gabatar da irin baiwar da Allah Ubangiji yabasu,domin kau sun wake Hon. Faruk Jobe.
Kadan daga cikin Waɗanda s**a halarci taron sun hada da Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kankara Justice Adamu Bello Kankara wanda yasamu wakilcin Sabon Garin Mabai,Kawan Katsina Hakimin Ketare Alh Usman Bello Kankara mni,dukkanin Magaddai dake Karkashin mulkin masarautun Karamar Hukumar Kankara, Yan Kasuwa,kungiyo Dadama da saura Al'umma
Daga Karshe Malam Nazir Liman Abdullahi ya gudanar da Addu'a rufe taro.
CIGIYA ! CIGIYA!! CIGIYA !!!
Assalamu alaikum barkanmu da Wannan lokaci.
A Ƙarƙashin Ma'aikatar SOCIAL WELFARE Muna bayar da cigiyar wannan baiwar Allah tare da ɗanta ga 'yan'uwanta ko waɗanda s**a santa ko s**a san wani nata cewa tana hannunmu yanzu haka.
Ita dai wannan baiwar Allah tana ɗauke da lalurar mutanen ɓoye, kuma ta taso daga garin Kano ne, in da ta hannun N.U. R.T.W ta buƙaci a kawo ta garin Maifaru na ƙaramar Hukumar Mai'adua ta jihar Katsina, bayan an kawo ta ne kuma ta yanke jiki ta faɗi, ta daina magana.
Sannan An bincika a Maifarun in da ta ce a kawo ta amma babu wanda ya san ta.
Saboda haka a dube ta sosai ko Allah zai sa a dace da saninta ko sanin wani nata.
Allah ya sa a dace, idan an dace ɗin sai a kira wannan lamba:
08032684590
Ana iya SHARING domin haɗa hannu a aikin lada.
Allah sa mu dace
Gwamnatin Jihar Kano ta jagoranci rushe Gine Ginen da aka yi a jikin filin polo dake Unguwar Nassarawa..
An gudanar da aikin ne da misalin karfe 2 na tsakar daren Ranar Juma'a Karkashin Jagorancin Hukumar Rayawa da Tsara Birane ta Kano (Knupda).
Tsohon Shugaban karamar Hukuma ya mayar da litar mai naira 300 a gidan man sa
Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Zaria dake jihar Kaduna, Hon Barr, Lawal Balarabe, ya saukakawa Al'umma masu ababen Hawa, inda ya rage kudin ko wace lita daya daga 550 zuwa naira dari uku 300 a gidan mansa na Faisalco dake garin Zaria..
Wane fata zaku yi
Daga:Saifullahi Lawal Imam.
Dubun wasu masu kwacen waya ya cika, yayin da s**a yi arangama da matasa masu fushi da fushin wani a kano
A karon farko na wannan damuna an sami saukar ruwan sama mai yawa a gari Mai'adua ta jihar Katsina, yaya abin yake a yankunanku?
YANZU-YANZU: Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke matashi Ibrahim Musa, wanda ya kashe mahaifiyarsa da wuka bayan ya caccaka mata.
Rundunar tace ta kamashi ne a karamar hukumar Dawakin Tofa dake jihar Kano.
MASU KUDI SUN TAFI DA LADA!!!
Wannan Shi ne Alhaji Yusuf Fantiya Attajirin da ya fi temakawa Sunnah da kudinsa a jihar Kano Shekaru masu yawa da su ka wuce
Alhaji Yusuf Fantiya shi ne ya Gina Masallacin Sunnah na kofar Wambai shi ya bayar da filin da aka Gina Masallacin Usman bin Affan da ke Gadon kaya
Shi ya bayar da filin da aka Gina Masallacin Al'muntada daka Dorayi shi ya bayar da filin da aka Gina Masallacin Malamin mu Dr Bashir Aliyu Umar (OON) na Alfurqan da ke Unguwar Nasarawa Kano a Lokacin an ta ya filin Masallacin Million Dari biyu (200) amma ya qi siyarwa ya bayar aka Gina Masallacin na Alfurqan
Shi ya Gina Masallacin kofar gidansa Wanda mutane da yawa suke tururuwar zuwa
Shi ne Attajirin da Lokacin da zai ta shi ya chanja gida makotansa s**a dinga zanga zangar basu yarda ya tashi ba Saboda yadda yake temaka musu
Shi ne Attajirin da in zai yi rabon ragon Laiya yana duba makotansa su arba'in (40) hagu da dama ya raba musu Ragon Laiya wadan nan kadan kenan daga cikin abubuwan alkhairinsa
Muna addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi ya kara masa Lafiya da nisan kwana mai amfani.
Abbas Adamu - 27 - 4 - 2023 -
ABUN GWANIN SHA'AWA:Kankara Women Foundation Multi-purpose Cooperative Ta Shirya Walimar Ciyar Da Yara Marayu 50 Gami Da Basu Kayan Sallah.
A ranar22/3/2023 wata gidaunaya mai suna Kankara Women Foundation Multi-purpose Cooperative ta gudanar da wani gagarumin aikin lada agarin Kankara.
Kungiyar Karkashin Jagorancin Malama Aishat Abdulrashid Kankara ta gayyaci Al'umma zuwa taro walima domin ciyar da yara marayu dake yankin Karamar Hukumar Kankara.
Taron walimar ya gudana a farfajiyar makarantar firamaren Sheik Abubakar Muhmud Gumi dake kan hanyar zuwa garin Funtua daura da Ofishin Jami'an tsaron 'yansanda reshen Karamar hukumar ta Kankara.
Awannan karon a ciyar da kimanin yara marayu hamsin ne Waɗanda s**a hada da maza 30 mata 20 s**a amfana da wannan taimakon ci,sha da kuma samun tufafin sawa kamar yadda sauran masu iyaye ke yi ayayin gudanar da shagulgulan murnar bikin Sallah.
Ayayin jawabinta Malama Aishat Abdulrashid Kankara ta fara da nuna godiyar ta ga Allah daya basu damar kirkirar wannan gidauniya,
Shugabar tace an kirkiri a shekarar 2013 domin bayar da taimako ga al'umma Musanman yara marayu,marasa galihu da kuma nakasassu.
Malamai Aishat ta kara dacewa abangaren marayu gidaunayar na gudanar da aikace aikacenta afannonin das**a shafi daukar nauyin karatun su tundaga matakin Firamare, Sakatare har yazuwa manyan makarantun.
Ba'ada bayan nan Gidauniyar na bayar da tallafi abangaren samar da lafiyar ga Marayun aduk lokacin da bukatar ta taso.
Fannin mara galihu kuma Malama ta bayyana irin gudumuwar Gidauniyar da cewa suna gayyatar al'umma musanman mata domin basu horon koyan sana'o'in Hannu gamida basu jari domin dogaro dakai.
Shugabar Gidauniyar ta bayyana cewa suna da abubuwan da Lokaci bazai bada damar bayyana su ba amma insha Allah ahankali Al'umma zasu fahinci ayyukan gidaunayar.
Daga Karshe tayi kira ga shuwagabani masu rike da madafan ikon na bangarorin Sarakuna, Gwamnati, 'Yan Kasuwa harma da daidaikun mutane dasu tallafa ma wannan gidauniya da dukkanin abubuwan da Allah ya huwace masu domin ceto marayu dake fuskantar matsalolin rayuwa.
Shugaban hukumar ilmin bai daya shiyyar karamar hukumar Kankara Alhaji Kabir Aliyu wanda yasamu wakilcin Darektan tabbatar da Bayar da ingantaccen ilmin na hukumar Malam Sa'idu Kankara ya bayyana godiyar Shugaban hukumar gami da jinjinawa masu tafiyar da gidaunayar ya Kuma tabbatar da bayarda haɗin Kai aduk lokacin da wata bukata ta taso.
Wakilin Limamin Juma'a na JIBWIS Malam Bashir Sh*tu ya yayi nasiha mai ratsa zuciya akan muhimmancin taimakon maraya.
Daya daga cikin Iyayen Gidauniyar Alhaji Surajo Hassan kira yayi ga Al'umma maza da Mata dasu ba wannan gidauniya goyon baya ta hanyar taimaka masu abubuwan da suke bukata.
Wani bawan Allah Mai suna Malam Isah Male Kankara ya baiwa gidaunayar Kyautar fili domin tasamu marsagunnin ta na dindindin.
Waɗanda s**a halarci taron sun hada da Kungiyar bayar da taimakon ta Agaji ta JIBWIS reshen Karamar Hukumar Kankara,Abdulganiyu Musa shehu, Malam Rulwanu Kankara,Malam Nuraddeen Kankara.
DA ƊUMI-ƊUMI: Binani ta lashe zaɓen gwamnan Jihar Adamawa
Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta sanar da ƴar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Ahmed, wacce aka fi sani da Binani a matasayin wacce ta lashe zaben gwamna a jihar Adamawa na 2023.
Kwamishinan zabe na jihar Adamawa, Hudu Haruna Ari ne ya bayyana hakan a yau Lahadin bayan kammala zaben cike-gurbi da ya gudana a jiya Asabar.
Binani dai ta kasance mace ta farko a tarihin Nijeriya da ta zama gwamnar jiha, inda ta doke gwamna mai ci, Ahmadu Fitiri ta kuma kawo ƙarshen zango ɗaya take da ya yi yana ɓullar jihar.
Kamsilan Mazaɓar Dan-maidaki Kankara Hon. Hassan Sufiyanu 'Yargoje Ya Gwangwaje Marayu Da Kayan Sallah.
A ranarJuma'ar data gabata 14/4/2023 kamsila mazabar Dan-maidaki karamar hukumar Kankara Jihar Katsina Hon. Hassan Sufiyanu 'Yargoje ya Gwangwaje marayu da kayan Sallah.
Taron raba kayan ta gudana a Farfajiyar Sakandiren Al'umma (COMMUNITY DAY SECONDARY SCHOOL) 'Yargoje dake Kan titin Zuwa garin Kankara da misalin karfe 2:30 na rana.
Yayin taron bayar da wannan kaya Mai gayya Mai aiki Hon. Hassan Sufiyanu Yargoje ya fara da bayyana godiya ga iyayen kasa da irin gudumuwar da suke bayarwa ga Al'umma,sannan ya cigaba da bayyana Nasarorin da Daya samu Acikin Shekara guda Dayayi Akan mulkin ka1msilan wannan mazaba.
Kamsilan yacigaba da bayyana Inda acikin Shekara guda yayi gyaran Riyojin burtsatse Dayayi awasu kauyukan das**a hada da Garin Yargoje,Gureta, Sabon gida,hadi da gyaran hanyar Gidan gwanki,Gidan Damo da sauran we wurare.
Bugu da kari Hon ya bayyana cewa kafin zuwa Shekara mai zuwa da yardarb Allah duk inda basu samu daya daga cikin aikin ba to da yarda
cikin Shekara daya data rage zasu maida hankali garesu domin suma su amfana.
Hon. Kamsila yayi kuma rabawa marayu su 30 Waɗanda s**a rasa iyayensu awannann mazaba kayan Sallah dinkakku domin suma suji dadi kamar yadda takwatorinsu masu iyaye da rai zasu kasance.
Abangaren shuwaganin Jam'iyyar APC ma awannan mazabar Hon. Hassan ya Rabama L.G Exco #5000 ko wannen su suma Exco mazabar ta Dan-maidaki su 26 kowane ya samu N2000
Afannin mahalarta taron sun hada da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Hon Faruk Lawal Jobe wanda yasamu wakilcin Dr. Mohammed Umar Zango,Dan-maidaki,Limamai ba garin Yargoje,shugaban Jam'iyyar APC na Mazabar Dan-maidaki,Women Leader Ra mazabar Dan-maidaki matasa na kauyukan dake karƙashin mazaɓar.
YANZÙ - YANZÙ: A cikin daren nan, hukumar shari'ah na jihar Bauchi ta janye mukabalar da ta shirya tsakanin dodon 'yan bidi'ah Sheíkh Dr Idris Abdul-Aziz Baùchi da 'yan bidi'ah mùshrikaí matsafà
Akwai cikakkèn bayaní zuwa gobe akan dalilin da yasa s**a janyè sabòda tsoron tonon Asiri’ Cèwar Dattí Assalafy
NIGERIAN UNION OF TEACHERS
MAI'ADUA LOCAL GOVERNMENT BRANCH
TA RABA KAYAN TALLAFI GA MALAMAI DA 'YA 'YAN KUNGIYAR RESHEN KARAMAR HUKUMAR MAI'ADUA.
Ayau Litinin 27/03/2023 Kungiyar Malaman Makaranta wacce akafi sani da sunan Nigerian Union of Teachers (NUT) reshen karamar hukumar Mai'adua ta gudanar da rabon kayan Azumi ga Malamai da 'ya 'yan Kungiyar karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Comrade Salmanu Abba Mai'adua kamar yanda ta sabayi a duk shekara idan azumi yazo.
Wannan na daga cikin ayyukan jinkai da tallafawa malamai da Kungiyar ta saba yi a duk lokaci bayan lokaci, wanda hakan ke kara sanya azama da kwazo wajen karawa ma'aikatan kaimi da azama domin kula da aikinsu akan lokaci tare da aiki tukuru.
Daga karshe Malaman sun jinjinawa shugabanin Kungiyar tamu (NUT) Comrade Salmanu Abba Mai'adua
Bayan haka Al'umma sun yaba kwarai da gaske wajen ganin tsayawa kai da fata wajen taimakawa Malamai adukkan lokacin da wata matsala ta faru ga Malami abangaren aiki da rayuwa.
Daga karshe Kungiyar Malaman makaranta NUT reshen Karamar hukumar Mai'adua tana kara godiya ga Malamai da shuwagabanin na Karamar hukumar Mai'adua yanda s**a bada gudunmawa a bangaren ilimi.
Mungode
Mungode
AMINU ADO MAI'ADUA
DEPUTY CHAIRMAN
MAI'ADUA LOCAL GOVERNMENT BRANCH
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Telephone
Website
Address
No. 4 Lambun Khadija G. R. A Along Daura Road Katsina
Katsina, 820212
We are Professional in Content Provider and Others Multimedia productions
Nitel Dutsinma
Katsina, FEDERALUNIVERSITYIDUTSINMA
Am George Habila popurlaly non as Lilgee the hausabadest making be good music that movtivete people