Katsina News 24

Katsina News 24

You may also like

brayanacostayt
brayanacostayt
Maba
Maba

We will update you any news around the nation

16/02/2023

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a cigaba da kashe tsoffin takardun kudi na naira 200 har zuwa 10 ga watan Apirilu.

Shugaban ya amince da hakanne a jawabin sa ga al'ummar kasar nan a safiyar ranar Alhamis.

Photos from Katsina News 24's post 11/02/2022

Sakon Taya Murna Tareda Fatan Alheri.

Daga Abdullahi Hassan Katsina.
MD Wadata Ventures Nig Ltd.

Amadadina da kamfanina tareda iyalaina ina mai mika sakon fatan alheri tareda fatan Allah yasa albarka mukamin da.

Maigirma Mutawallen Katsina
Chief Akajiugo Of Enugu.

Rtd Col Abdul'aziz Musa Yar'adua Rtd.

Bisa mukaminda maigirma shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari GCFR yabashi na shugaban gudanarwa na hukumar samar da wutar lantarki a karkara ta kasa. (Rural Electrification Agency REA).

Allah yasa albarka yaimaka jagorancin cikin wannan damar ta bada gudumuwar ka da basirar da Allah yabaka cikin kasar nan, Allah yabaka ikon sauke nauyin dake kanka ya kame hannuwanka zuwa aikata abinda yake daidai ya kame hannuwanka daga aikata abinda yake ba daidai ba, Allah yabaka ikon yima kowa adalci.

Abdullahi Hassan Katsina.
Dan Gurguzu Abdu Soja Zallah.

Photos from Katsina News 24's post 24/11/2021

Daga ƙarshe dai za'a ƙaddamar da wutar lantarki ta Lambar Rimi a wata mai k**awa

Ministan wutar lantarki ya bayyana cewa za'a ƙaddamar da wutar lantarki ta lambar Rimi a watan December Goma Sha Takwas ga wata, hakan dai ya biyo bayan ziyarar da Dattijan Jihar Katsina s**a kai a Offishin Ministan.

Ministan yace Matsalar rashin tsaro ne yasanya aka samu tsaiko wajen ƙaddamar da wutar ta Lambar Rimi da kuma wasu kayan Wutar da aka sace.

Photos from Katsina News 24's post 28/08/2021

Katsina State has today Saturday 28th August received 21,040 doses of Astra Zeneca Covid-19 Vaccine. The Hon Commissioner ministry of health, Permanent Secretary, ES SPHCA, SIO, CCO, SC NPHCDA, SLO, STL CDC AFENET were on ground to receive the Vaccine at Mal Aminu Kano international airport Kano. The Vaccine is for second dose for those that received the 1st dose about 2 months ago.

Photos from Katsina News 24's post 25/07/2021

KUNGIYAR TSOFAFFIN DALIBAN MAKARANTAR GAFAI PRIMARY DAKE BIRNIN KATSINA NA SHEKARAR 1999 SUN GUDANAR DA TARON DA S**A SABAYI A SHEKARA SHEKARA, TARE DA KIRAN MAMBOBIN KUNGIYAR DOMIN CIGABAN TSOHUWAR MAKARANTARSU.

Taron Wanda ya Gudana afarfajiyar Makarantar,ya Samu halastar tsofaffin Daliban tare da Sauran Masu Ruwa da tsaki.

Da yake Jawabi Shugaban Riko na Kungiyar Nuraddeen Armaya'u ya Bayyana Anshiryasa taron ne Domin Kara karfafa Dankon Zumunci atasakininsu.

Nuraddeen Armaya'u Wanda ya Bayyana Jin Dadinsa dangane da goyan Baya da Hadinkai da Mambobin Kungiyar ke badawa, tare da Kiran Dorewar hakan.

Shugaban Rikon Kungiyar Wanda ya amaganta Akan muhimmancin taimakekeniya atsakanin Al'umma,Tare da kiraga Mambobin Kungiyar dasu Zamo masu taimakon juna, tare da hakadin Kai Atsakani domin Cimma kudurin da Akasa agaba.

Shima Tsofan Dalibin Makarantar, kuma Shugaban kamnafan Gafai Communication Alhaji Musa Yusuf Gafai Wanda ya Bayyana jindadinsa Akan Hadinkai dake tsakanin tsofaffin Daliban,tare magantawa Akan Muhimmancin Kafa Kungiyar ta tsofaffin Daliban.

Alhaji Musa Yusuf Gafai Yakuma Bayarda Tallafin Naira Budu Dari 10000 ga Abokan karatunsa Mata Domin Kara masu jari abangaren sanaoinsu.

Yakumasha Alwashin Banyarda Dukkanin goyan Baya da Hadinkai domin cigaban tsohuwar Makarantar tasu da Sauran Al'ummah Bakidaya.

Sauran wadanda S**a Maganta Alokacin taron sun Hada da ma'ajin kudin kunyar Abdulhadi Ibrahim Gudun Yan shanu,Mubarak Salisu Sakataren Kungiyar da Sauran Masu Ruwa da tsaki.

24/07/2021

NEMAN TAIMAKO.

Hafsat Aliyu yarinya ce yar kimanin shekara 27 tana zauna a karamar Hukumar Malumfashi dake Jahar Katsina.

Allah ya jarabci Hafsat Aliyu da lalura ta ciwon zuciya, Likitoci sun Tabbatar da cewa matukar Ana Son Hafsat ta Samu lfy sai Anyi Mata Aiki a zuciya.

Kuma aikin zaici kimanin Naira miliyan biyu da Dubu dari biyar (2.5million).
Iyayenta basu da Karfin biyan Wadannan kudade shine muke neman Mata taimako ga Mai akwai da Niyya.

Phone number 07036060383

Account number 3158970056 Halima Tukur first bank

Photos from Katsina News 24's post 23/07/2021

Abun Mamaki baya ƙarewa a Duniya; Wani Uba ya canzawa Ɗiyar shi Suna a Jihar Katsina....

Allah Mai iko wani bawan Allah Mai suna Yahuza Ibrahim Niga dake cikin ƙaramar hukumar JIBIA ta jihar Katsina ya chanzama ɗiyar shi suna daga "Buhariyya" zuwa "Kausar" wannan Al'amarin yafaru ne da sanyin Safiyar yau din nan 23-07-2021.

Da aka tambaye shi minene dalilin shi nayin hakan sai yace sanadiyyar Rashin cika Alkawarin da shugaban ƙasa Muhammadu buhari da Jam'iyyar APC s**ayi a yayin da suke neman ƙuri'un Jama'a a Shekarar Dubu Biyu da Goma Sha Biyar.

Shi dai wannan bawan Allah k**ar yanda yasanar damu cewa shi Masoyin Shugaba Buhari ne, na haƙiƙa kuma duk wanda yaji sunan Buhari yasan Mutum ne mai gaskiya, amma shidai yanzu ya dawo rakiyar shi, yace tun a shekarar 2015 lokacin Buhari yana sauran kawana 26 yashiga office matarshi tana gab da zata haihu yayi Alkawarin cewa idan Allah ya sauketa lafiya zai sak**a Ɗan suna Buhari idan namijine idan Kuma macece zai saka mata suna Buhariyya sai akasamu mace shine yasak**ata wannan sunan Amman yanzu ya chanzamata shi, bisa dalilai na rashin cika Alkawari.

Haka Kuma mahaifin yarinyar yace ya jinkirta sanya Yarinyar Makarantar Primary ne saboda yanaso zai chanzamata suna kafin ta fara zuwa Makaranta.

Shin yaya kuke kallon wannan Lamarin

16/07/2021

Jami'an tsaro sun yi awon gaba da Abduljabar

Wasu rahotanni daga jihar Kano na nuni fa cewar jami'an tsaro a yammacin ranar Juma'a sun yi awon gaba da Abduljabar Nasiru Kabara dake unguwar Filin mushe a yankin karamar hukumar Gwale.

Idan baku manta ba, a makon da ya gabata aka gudanar da wata mukabala tsakanin Abduljabar da Malaman Kano inda aka zargi Abduljabar da yin kalaman batanci ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam zargin da shi Abduljabar ya kasa karewa.

Bayan kammala waccan mukabalar Abduljabar ya bayar fa wata sanarwa inda yace ya janye dukkan kalaman da ake zargin yayi, yana mai baiwa al'umma hakuri, daga bisani kuma ya janye wannan tuban da yayi.

Tuni dai akai ta kiraye kirayen Gwamnatin Kano ta dauki mataki akansa ko kuma ya fuskanci fushin gamagarin mutane. Sai dai wasu rahotanni sun nuna an cafke Abduljabar a yammacin wannan rana.

Photos from Katsina News 24's post 16/07/2021

Shugaban Hukumar Taimakekeniyar kiwan lafiya na Jahar Katsina Alhaji Tukur Ibrahim Safana Ya Ziyarci wasu Asubitoci dake karkashin Shirin Domin tabbatar da Amfanar Al'ummah dake Karkashin Shirin.

Alhaji Tukur Ibrahim Safana yakai Ziyarar tare da Daraktocin Hukumar da Sauran Masu Ruwa da tsaki.

Asubitocin daya Ziyarta Sune Babbar Asibiti dake nan Katsina, Asibitin Turai Yar'adua,da ta K-Dara gamida Asibitin Kofar kaura dake nan Katsina.

A Dukkanin Asubitocin Daya Ziyarta, Alhaji Tukur Safana ya Bayyana gamsuwarsa Akan matakanda Asubitocin S**a Dauka Domin Ganin kwalliya Tabiya kudin sabulu.

Babban Daraktan da Tawagarsa Sun zagaya Bangarori daban daban na Asubitocin da S**a Ziyarta da S**a Hada Bangaren Kula da Mata Masu juna biyu, Shashen Kula da Kananan Yara, Dakin fida, Gamida Da kin Kwaji da dai Sauransu.

Alhaji Tukur Ibrahim safana Ya kuma Yaba da Gudummuwa da hakadin Kai da Hukumar kesamu daga Gwamnatin Jahar Katsina tare da Kiran Dorewar Hakan.

Babban Daraktan yakumaja Hankalin Ma'aikatan Kiwan lafiya a Dukkanin Asubitocin Daya Ziyarta domin sauke Nauyin Daya rataya akansu, na Bada Ingataciyar kulawa ga Al'ummar dake cikin Shirin.

Photos from Katsina News 24's post 02/07/2021

NIMASA Ta Tallafawa Wadanda Lamarin Yan Bindiga Ya Shafa A Katsina.

Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa Da Harkokin Mulki ta kasa wato NIMASA,ta Samar da tallafin kayayyaki ga wadanda lamarin yan bindiga ya shafa a Jihar Katsina.

Darakta a Hukumar ta NIMASA Alhaji Kabir Murnai,shine ya hannanta kayayyakin ga Kwamishinan Harkokin Wasanni Da Walwalar Jama'a Alhaji Sani Aliyu Danlami a Madadin Shugaban Hukumar ta NIMASA.

Da yake hannanta kayayyakin,Alhaji Kabir Murnai yace tallafin nada nufin rage radadinda wadanda lamarin yan bindiga dadi ya shafa a jihar Katsina.

Alhaji Kabir Murnai ya kara da cewar Hukumar ta samar da irin wannan tallafi a jihohi daban-daban na kasarnan domin tallafawa wadanda lamarin yan ta'adda ya shafa a kasarnan.

Daraktan yayi magana mai tsawo akan irin ayyukan jin kai daban-daban da Hukumar ta NIMASA take gudanarwa.

Alhaji Kabir Murnai wanda dan Asalin Jihar Katsina ne kuma mai rike da Sarautar Wakilin Katsina,ya nanata kudirinshi na cigaba da nemowa Jihar abubuwan alkairi domin samun Karin cigaba.

A nashi jawabin a madadin Gwamna Aminu Masari,Kwamishinan Wasanni da Walwalar Jama'a Alhaji Sani Aliyu Danlami,ya yabawa Hukumar ta NIMASA akan samar da tallafin.

Alhaji Sani Danlami wanda shine Shugaban Kwamitin Kula Da Yan Gudun Hijira na Jiha,ya bada tabbacin cewa kayayyakin zasu isa ga wadanda aka samawa su.

Ya kuma yi rokon Karin addu'oin dorewar zaman lafiya a Jiharnan da ma Kasa baki daya domin Karin cigaba.

Photos from Katsina News 24's post 01/07/2021

CIGABA A BANGAREN ILIMI!

Zauren Jama'ar Jahar Katsina (Katsina state people's forum) ta Raba Lutattafan karatu ga wasu makarantun sakandiren Al'ummah Dake Jahar Katsina.

Galadiman Katsina Justice Sagiq Abdullahi mahuta Ya Kaddamar da Rabon Litattafan, Agurin taron Daya gudana a Goruba Road Katsina.

Da yake Jawabi Shugaban Zauren na Jama'ar Jahar Katsina Engineer Musa D Abdullahi yace karamcin Nada nufin lallafama Harkar koyo da koyarwa ajahar nan.

Makarantun da S**a Anfana sun Hada da K**arantar Al'ummah ta Malumfashi, Bindawa, Kafur, Gafai, da Sauransu.

Engineer Musa Yayi Kira ga Makarantun da S**a Anfana dasuyi kyaykyawan Amfani da Litattafan domin cigaban Ilimi ajahar nan Bakidaya.

Sauran wadanda S**a Maganta Alokacin taron sun Hada da kwaminshinan Ilimi na Jahar Katsina da Sauran masu Ruwa da tsaki Tare dayin Godiya Akan kokarin Kungiyar wajen tallafama Har Kar Ilimi.

29/06/2021

Komai Nisan Jifa:Jagoran Yan IPOB Nnamdi Kanu Ya Shiga Hannu.

Jagoran Masu Ikirarin Kafa Kasar Inyamurai wato IPOB Nnamdi Kanu ya shiga hannun hukumomin Najeriya,bayanda ya tsallake ya bar kasar.

Ministan harkokin Shari'a Abubakar Malami SAN,shine ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya gudana a Ma'aikatar ta harkokin shari'a.

Malami yace a halinda ake ciki tuni an tuso keyar kanu zuwa Najeriya daga kasarda ya buya kuma za'a shigo da shi a yau dinnan,a yayinda za'a gurfanar da shi a Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya dake Abuja.

Masu Karatun The Fact 24 muna dakon ra'ayoyinku akan batun.

Photos from Katsina News 24's post 07/06/2021

CIGABA : Kakakin Rundunar Kare Lafiyar Yan Kasa Ta Jihar Katsina Ya Samu Karin Girma.

Kakakin Rundunar Civil Defence a Jihar Katsina Muhammad Tukur Abdara ya samu Karin girma daga matakin Assistant Superintendent of Civil Defence ASC,Zuwa mataki na gaba wato Deputy Superintendent.

Kwamandan rundunar a Jihar Katsina,shine ya dora Karin girman ga DSC Abdara a lokacin bikin dora Karin girma ga jami'an hukumar da s**a samu karin girma.

Karin girman dai bai rasa nasaba da jajircewar DSC Abdara ta fuskar gudanar da aikinshi lura da yadda sashenda yake jagoranta ke tafiyar da ayyukanshi.

Masu karatun The Fact 24 ko meye Fatanku ga DSC M.T Abdara?.

07/06/2021

Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Yi Wa Manyan Hafsan Sojoji 29 Ritaya Duk Da Musantawa Da Hedkwatar Tsaro Ta Yi

Rundunar Sojin Kasar Najeriya ta amince da hutun manyan sojoji 29 wanda daga nan za su yi ritaya bayan nadin Janar Farouk Yahaya a matsayin babban hafsan Sojojin Nijeriya.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da ta fito daga Rundunar Sojin ta Najeriya.

Daga cikin wadanda aka yi wa ritayar akwai AA Sarham, BM Shafa, UM Mohammed da wasu manyan sojoji 26.

Manyan sojoji ashirin da tara aka tirsasa yin murabus daga aiki bayan nada Manjo Janar farouk Yahaya a matsayin shugaban rundunar sojin kasa na Najeriya.

Wannan murabus din ya ci karo da ikirarin hedkwatar tsaro na makon da ya gabata wanda s**a ce babu sojan da za a yi wa ritaya duk da nada Yahaya a matsayin shugaban sojin kasa da Buhari yayi.

Yahaya mai mukamin Manjo Janar daga jihar Sokoto ya samu mukamin shugaban sojin kasa na Najeriya a ranar 27 ga watan Mayu bayan mutuwar Ibrahim Attahiru.

A wata takarda da Premium Times ta gani, ta nuna cewa an amincewa sojoji masu mukamin manjo janar 29 su tafi hutu, lamarin da zai bude hanyar ritayarsu.

Wannan ritayar ta zo ne kasa da makonni biyu bayan nada Yahaya a matsayin shugaban rundunar Sojin ta Najeriya.

Ga jerin sunayensu:

1. JB Olawumi
2. JO Akomolafe
3. CO Ude
4. G Oyefesobi
5. MO Uzoh
6. CC Okonkwo
7. MSA Aliyu
8. UM Mohammed
9. BM Shafa
10. NE Angbazo
11. YP Auta
12. SA Yaro
13. J Sarham
14. HE Ayamasoawei
15. OF Azinta
16. BA Akinroluyo
17. KAY Isiyaku
18. AT Hamman
19. AM Aliyu
20. HPZ Vintienagba
21. HR Momoh
22. JR Unuigbe
23. AA Jidda
24. OI Uzomere
25. MH Magaji
26. LA Adegboye
27. MA Masanawa
28. OA Akinyemi
29. AM Dauda

Photos from Katsina News 24's post 06/06/2021

JAMI'AN TSARO KARKASHIN JAGORANCIN DCP ABBA KYARI SUN SAMU NASARAR KASHE WANI KWAMANDAN YAN IPOB WANDA AKEMA LAKABI DA DRAGON.

Ana cigaba da farin ciki a Owerri Babban Birnin Jahar Imo a yau Lahadi, bayan jami'an tsaro Karkashin jagoranci Abba Kyari, Sufeto-Janar na Rundunar sirri ta Yansanda, s**a samu nasarar kashe wani rikakken Dan ta'adda, da akafi sani da Suna Dragon.

Jami'an tsaro da s**a hada da Sojoji da Yansanda, Wanda dasu aka hada Kai wajen gudanar da aikin, sun nuna farin cikin su akan samun nasarar kashe Dragon a yau din nan.

Dragon da Yan tawagar sa, sun yi yunkurin Kai hari a Shalkwatar Rundunar Yansanda dake Owerri, bayan kone gidan Kwamishinan Yada Labaru na Jahar Declan Emelumba- a cewar Kakakin Rundunar Yansanda na Jahar Bala Elkana.

Dayake yiwa Yan Jarida jawabi a Shalkwatar, Elkana yace Dragon shine Shugaban Rundunar Sojin IPOB, Wanda ya gaji Ikonso ne da aka kashe a lokuttan baya.

Elkana ya kara dacewa, tawagar Yan ta'addan itace musabbabin Kashe Yan sanda guda 4, a ofishin Rundunar na Omuma da Kuma harin ofshin Orji dake Owerri.

Kakakin Rundunar yace an samu nasarar kwato bindigu kirar Ak47 da harsashi da karamin bama-bamai na Rundunar da sauran su.

Photos from Katsina News 24's post 05/06/2021

A YAUNE RANAR MUHALLI TA DUNYA!

A Ranar 5 ga watan Juni na kowace Shekara, majalissar Dinkin Dunya taware Domin wayar da Kai Dangane da Tabbar da ingancin muhalli.

A Jahar Katsina, Yan Majalisu,Masu Rike da masarautun Gargajiya,yan kasuwa,Kungiyoyin Fararen Hula,Yan Siyasa da Sauran al' ummah Sunbi sahun takwarorinsu na Dunya wajen Bikin Wannan Rana ta Muhalli na wannan Shekara.

Ta Hanyar Dasa Itatuwa agurare daban daban da acikin Birnin Katsina.

Gamida Zagayawa a wasu Bangarorin Birnin na Katsina domin tsince ledoji da Sauran Abubuwanda ka iya Haddasa Gurbacewar Muhalli.

Photos from Katsina News 24's post 01/06/2021

Gwamnatin Masari Ta Tallafawa Wadanda Iftila'in Yan Bindiga Ya Shafa Da Suke Zaune A Cikin Birnin Katsina.

Kwamishinan Wasanni da Walwalar Jama'a Wanda kuma shine shugaban kwamitin kula da yan gudun hijira na jiha Hon.Sani Aliyu Danlami ya mika tallafin kayan abinci ga wadanda Iftila'in yan bindiga ya shafa da suke zaune a cikin birnin katsina.

Wadanda s**a amfana da tallafin wadanda mafi akasarinsu mata ne sun karbi tallafin ne a lokacin wani taro da ya gudana a ofishin NA dake Kofar Soro a nan cikin birnin Katsina.

Honourable Danlami ya nuna damuwa akan halayyar wasu matan da suke kwanciya a wurarenda basu k**ata ba k**ar a bakin tituna da Kofar shaguna da dai sauransu.

Daga nan sai ya bayyana cewa ko kadan gwamnati ba zata lamunci hakan ba domin kauracewa wani abu da ka iya faruwa da rayukansu.

Yayi kira a garesu akan kada su gajiya wajen yin addu'oi akan Allah SWT ya kawo karshen matsalolinda ke addabar jiharnan.

Kwamishinan ya kuma yi kira a garesu akan suyi kyakkyawan amfani da tallafin su kuma kauracewa saida kayan.

Hon.Danlami ya yabawa Gwamna Aminu Masari akan yadda yake nuna damuwarshi wurin wadanda lamarin matsalar tsaro ya shafa sai yayi addu'ar Allah ya bashi kwarin gwuiwa ta fuskar shawo kan matsalar.

Photos from Katsina News 24's post 31/05/2021

Limamin Masallachin Haramain Na Makka Ya Yabawa Gwamna Ganduje Kan Hidimtawa Musulunci

- An nadawa Gwamna Alkyabbar girmamawa 'yar asali

Limami a Masallachin Haramayn na Birnin Makkah Mai Tsarki kuma shugaban Cibiyar Nazarin Larabci na Jami'ar Ummul Qura Farfesa Hassan Ibn AbdulHamid Al-Bukhari ya yabawa Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa hidimtawa Musulunci da Gwamnan ke yi tare da gwamnatinsa.

Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya jagoranci tawagar wasu mashahuran malaman Jami'ar Ummul Qura, zuwa ga fadar gwamnatin Jihar Kano, yau Litinin, don sanar da Gwamnan abinda ya kawo su Jihar, bisa gayyatar Jami'ar Bayero ta Kano.

"Alhamdulillah tun mu na can mu na samun labaran aikhairin da gwamnatin ka ke yi wajen tallafawa cigaban Addinin Musulunci. Mun yi murna matuka da wannan labari da muke samu. Kuma mun zo mun gani ma da idonmu," ya ce.

Ya kara yabawa yadda Gwamnan na Kano ya ke abubuwa saboda ci gaban al'ummarsa. Sa'annan nan ya tabbatar da cewa kullum a shirye su ke da su tallafawa Jihar ta Kano.

An bayyana cewar sun zo Kano ne bisa gayyatar jami'ar Bayero ta Kano, kan wata horaswa ta musamman da za su yi ga Alkalai da kuma daliban ilimi. Wannan ce kuma horaswa irin ta ta hudu da su ka yi a kasar nan.

A nasa jawabin Gwamna Ganduje ya bayyana yadda danganta ta jima tsakanin Jihar Kano da kasar Sa'udiyya tun shekaru da yawan gaske da su ka wuce.

Ya ce "...irin wannan dangantaka ce dadaddiya kuma mai inganci tsakaninmu, ta sa har Kasar ta Sa'udiyya ta bude wani ofishin jakadanci a nan Kano. Wanda duk wata alakarmu da wannan kasa mai Tsarki ta Sa'udiyya ta nan ne mu ke farawa."

"Alhamdulillah mu na da wani shirin na musamman dama da kasar Sa'udiyya wanda mu ke tura Malamai a na yi musu bita ta sati biyu ko uku. Daga baya bayan nan mun tura mata guda 100 domin su ma su amfana da irin wannan horaswa. Matan kuma Malamai ne na makarantun Islamiyya," in ji Gwamnan.

Nan gaba kuma za a kara tura mutane wajen irin wannan horaswa. K**ar

26/05/2021

Yansanda Sun Hallaka Yan Ta'adda Hudu (4) A Katsina.

Jami'an Yansanda A Karamar Hukumar Batsari Ta Jihar Katsina sun samu nasarar hallaka yan ta'adda guda hudu.

Hallaka Yan Ta'addan ya biyo bayan samun labarin sirri da yan sandan s**a samu cewar Yan Ta'addan dauke da manyan Mak**ai sunyi yunkurin kai hari a Kauyen Dangeza ta Karamar Hukumar.

Da jin labarin ba tare da bata lokaci ba yansandan s**a yunkura akan dakile harin Wanda hakan yasa s**a samu nasarar hallaka yan ta'adda hudu.

K**ar yadda wata Takarda da Kakakin Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina SP.Gambo Isah ya fitar,an samu nasarar samun mashina uku da yan ta'addan suke a samansu.

Takardar tayi roko ga al'umma akan kada suyi kasa a gwuiwa wurin cigaba da samar da sahihan bayanan sirri ga jami'an tsaro wanda zai taimaka wurin kare yunkurin kai hare-haren Yan Bindiga Dadi a Jiharnan.

26/05/2021

SO HANA GANIN LAIFI: Wani Dan Shekara 23 zai angwance da 'yar Shekara 45 a Jahar Adamawa

Tuni dai hotunan wadannan masoya ya gama dandalin Sadarwa na Zamani musamman na Facebook, inda ake ta tofa Albarkacin Baki, sak**akon Wannan Aure.

Shidai wannan Matashi ya kasance Dan Shekara 23 ne a yayinda ita kuma ta kasance yar Shekara 45 inda za'a gudanar da Auren a Jahar Adamawa a ranar Lahadi mai zuwa.

Idan dai ba'a manta ba, irin haka tasha faruwa musamman a Arewacin Najeriya, inda Manyan Mata da Kuma Maza ke Auren kananan yara domin cigaba da rayuwar Aure.

Wanda har a kwanakin baya, wata Baturiya Janifer ta taso tun daga Kasar Amruka, domin Auren wani saurayi Suleman Panshekara, da s**a hadu a kafar Sadarwa ta Zamani.

Haka Zalika, suma samari sun ta yin koke, inda s**a zargi Manyan Mutane da Aure masu Yanmata, maimakon Auren Sa'annin su.

17/05/2021

NA BAWA ISRA'ILA WA'ADIN SA'A 24 TA DAINA KASHE FARAREN HULA—Kim Jong'un

Shugaban ƙasar Koriya ta Arewa, mr kim jong'un ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da hare haren da Isra'ila ke kai wa a kan fararen hula, a zirin Gaza.

Mr Kim, ya ce k**ata yayi ace an zauna a kan teburin sulhu domin warware wannan rikici mai makon amfani da ƙarfin soji, kuma ya k**ata ace ƙasashen duniya sun takawa Isra'ila burki amma tunda sun kasa mu ba zamu bari wannan zaluncin yaci gaba ba.

Saboda haka.mun bawa Isra'ila wa'adun sa'a 24 ta dakatar da kai gare hare a kan fararen hula ko kuma ta ɗan ɗana kuɗarta, domin kuwa a shirye muke da mu bada ko wace irin gudun mawa domin taimakawa fararen hula in ji Kim Jong'un, k**ar yadda kamfanin dillancin labarai ba ƙasar ya bayyana.

10/05/2021

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un.

Allah yayiwa Khalifan Sharif Shaikh Abba Abu Rafin-Dadi rasuwa.

Kalifan Sharif Sheikh Abba Abu ya rigamu gidan gaskiya a yau litinin kuma za'ayi jana'izarsa da misalin karfe 11:00 na safe idan Allah ya kaimu.

Za'a gudanar da jana'izar ne a nan filin tanki gidan Sharif Sheikh Abba Abu in Allah ya yarda.

Allah ya jikanshi ya gafarta mashi.

Photos from Katsina News 24's post 09/05/2021

Gwamnatin Masari Ta Tallafawa Yan Kasuwa 385 Da Iftila'in Gobara Ya Shafa a Central Market.

Gwamnatin Jihar Katsina ta samar da tallafin kayan abinci ga yan kasuwarda Iftila'in gobara ya shafa a babbar kasuwar Katsina.

Kwamishinan Wasanni da Walwalar Jama'a na jihar Alh.Sani Aliyu Danlami ne ya kaddamar da rarraba tallafin a farfajiyar kasuwar.

K**ar yadda kwamishinan ya bayyana,tallafin ya biyo bayan umarni daga gwamna Aminu Masari domin rage wasu daga cikin wahalhalunda yan kasuwar ke fuskanta.

Alhaji sani Aliyu Danlami ya bukaci yan kasuwar akan su kara jajircewa wajen addu'oi akan Allah ya kawo karshen matsalar tsaro dake addabar jiharnan.

A jawabinsa,Shugaban Kungiyar yan kasuwa na Jihar Katsina,Alhaji Mujittafa Lamis Gafai,ya yabawa Gwamna Aminu masari akan Samar da tallafin.

A nashi bangaren,Shugaban kungiyar yan kasuwa na Babbar Kasuwar Alh.Abbas Labaran Albaba ya sanar da yan kasuwar cewa nan ba da jimawa ba zasu dara domin kuwa gwamnatin masari daf take da tallafa masu.

Photos from Katsina News 24's post 06/05/2021

Tinubu Ya Samar Da Tallafi Ga Marayu Da Sauran Mabukata 4000 A Katsina.

Babban jigon Jam'iyar APC Bola Ahmed Tinubu ya Samar da tallafin buhunan shinkafa mai nauyin KG5 ga marayu da masu karamin karfi gami da wadanda ayyukan yan bindiga Dadi ya shafa a Jihar Katsina.

Shugaban kwamitin rarraba kayayyakin Alh.Salisu Mamman ne ya kaddamar da rarraba kayayyakin a wani taro da ya gudana a Katsina.

Tallafin dai nada nufin saukakawa wadanda s**a amfana su gudanar da azumin Ramadan a cikin sauki.

Sauran mambobin kwamitin da s**a shaida kaddamar da rarraba kayayyakin sun hada da Kwamishinan Wasanni Da Walwalar Jama'a Alh.Sani Aliyu Danlami da takwaransa na Raya Karkara Alh.Mustapha Mahmud Kanti Bello da sauransu.

05/05/2021

Meza kuce Dangane da Wannan Zane na Kafar Dan Kwallon Real Madrid Sagio Ramos?

Photos from Katsina News 24's post 05/05/2021

Kungiyar kwallon fa ta Chelsea dake kasar Ingila Tayi Nasarar Doke Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid dake Kasar Spain daci 2 da Nema awasan karshe Nacin kofin Zakarun Turai.

Wannan nasara taba Chelsea Damar Bukaga wasan karshe na gasar cin kofin daza Kara da Takwararta Manchester City.

05/05/2021

Za A Zabtare Wani Kaso Daga Cikin Albashin Ma'aikata Da Kuma Ƴan siyasa Domin Taimaka Ma Ƴan kasuwa A Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana aniyarta na cirar wani kaso daga cikin albashin ma'aikatan jahar domin cike gurbin asarar da gobarar da aka yi a babbar kasuwar Katsina ta janyo.

Gwamna Aminu Masari ne ya bayyana haka a yayin da ya ke amsar bayani daga Kwamitin da ya kafa domin binciken musabbabin gobarar da kuma yawan dukiyar da aka yi asara, wanda Kwamishinan ma'aikatar ayyuka da gidaje da kuma sufuri, Tasi'u Ɗanɗagoro ya jagoranta.

Masari wanda a ranar Larabar nan ya amshi sak**akon binciken da kwamitin yayi, ya ce kashi sama da 80 na dukiyar Katsina tana zuwa ne ga ma su riƙe da manyan muƙamai a gwamnatance da kuma ma'aikata, don haka ne ya yanke shawara a kan su ma su riƙe da manyan muƙaman gwamnati da ma'aikata da su bayar da gudunmuwarsu domin tallafa ma waɗanda gobarar ta shafa.

A ƙarshe duba ga irin dumbin matsalolin da jahar ke fuskanta na ƴan ta'adda da kuma asarar dukiyoyi da rayukan mutane, Mari yayi kira ga al'umma da su koma zuwa ga Allah domin tuba gare shi.

A cikin bayanin da Kwamitin yayi, ya bayyana zunzurutun kuɗi har sama da naira milyan ɗari 9 da 2 da aka yi a sararsu sak**akon gubatar.

04/05/2021

ASHAM DA TAHAJJUD: An K**a Namiji Da Hijabi Cikin Mata A na Sallah

Kungiyar 'yan Bijilante ta k**a wani katon gardi da hijabi a cikin mata yayin sallar Asham a cikin wani masallaci da ke yankin unguwa Uku ƴan Awaki.

Wata matashiyar budurwa da ta tafi Sallar Asham da wayar ta, bayan an idar da Sallar ta duba ba ta gan ta ba, sai ta fara zargin makociyar ta da su ka yi Sallah a wuri daya.

Matashin da ake zargi mai shigar mata bayan ya dauki wayar, sai ya tafi bayan bandaki ya na cire kayan matan, su kuma ƴan banga s**a k**a shi.

Matashiyar da aka dauke wa wayar ta bayyana wa majiyar Zuma Times Hausa cewa, "Har mu ka rabu da matashin ina tsammanin ƴar uwa ta ce mace". Inji matashiya.

Kwamandan Bijilant na yankin, Adamu Abubakar Fiya-fıya ya shedawa wakilin mu Abba Ibrahim Lafazi cewa, "Akwai bukatar ƴan agajin masallatai su kara zage dantse yayin Asham da Tahajjud.

03/05/2021

Sak**akon Jarabawar tsayawa takarar shugabancin Kananan Hukumomi a Kaduna ya Fito.

Ana ci gaba da samun mabanbantar ra'ayoyi dangane da sak**akon Jarabawar Masu Sha'awar tsayawa takarar shugabancin Kananan Hukumomi da ya fito sa aka gudanar a Jihar Kaduna.

Mutane sama da dari ne dai s**a Fafata a wannan jarabawa, wanda ke zama zakaran gwajin dafin zaben fidda gwani da za a yi a ranar biyar ga watan Mayun da muke ciki na shekara ta 2021.

Sak**akon zaben wanda aka fitar ranar Asabar da ta gabata ya nuna cewa mutane 75 daga cikin 115 da s**a fafata ne dai s**a samu nasara wadanda kuma za su fafata a zaben fidda gwanin.

Kazalika mutane 38 kuma sun fadi kasa warwas sak**akon rashin kuzari da s**a nuna, lamarin da kenan ke nuni da cewa ba su babu batun shiga zaben fitar da gwanin.

Daya daga cikin su da ya gaza samun nasara, Muhammad Sani Abdulmajid ya ce gaskiya lamarin akwai rashin Kyautatawa a ciki duba da cewa ya samu maki 52.8, wasu kuma daga wasu kananan hukumomi da makin su bai kai haka ba an ce sun ci.

Kazalika Daraktan yaki neman zaben Kwamared Lawal Chanchangi wanda shi ma ya nuna sha'awar tsayawa takarar, ya ce an yi son kai tare da nuna karfin tuwo wajen zabar wadanda za su fafata zaben fitar da gwanin.

A hannu guda kuma ɗaya daga cikin wadanda s**a tsallake rijiya da baya Ibrahim Isma'il daga karamar hukumar Kaduna ta kudu ya gode wa Sarki Allah bisa wannan nasara, inda ya ce bai ui mamakin wannan sak**ako ba.

02/05/2021

Za Mu Cigaba Da Biyan Sabon Tsarin Albashi Ga Ma'aikatan Jihar Jigawa, Komai Tsananin Matsin Tattalin Arziki

Gwamnatin jihar Jigawa ta bada tabbacin cigaba da biyan sabon tsarin albashi da fansho da kuma sauran hakkokin maaikata koma tsananin matsin tattalin arziki.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bada tabbacin hakan a jiya Asabar lokacin bikin ranar ma'aikata ta bana da aka gudanar a dakin taro na Sir Ahmadu Bello dake Dutse.

Gwamna Badaru Abubakar, ya ce duk da matsain tattalin arziki da gwamnatoci suke fuskanta a kasa da duniya , gwamnatin jiha tayi kyakkywan tanadin katta kwana domin ganin ba a samu matsala ba wajen biyan albashi da sauran hakkokin maaikata.

Gwamna Badaru ya kara da cewar gwamnati za ta cigaba da tallafawa kananan hukumomi domin ganin suna biyan albashi akan lokaci inda yace koda a watan jiya sai da gwamnatin jiha ta cikawa kananan hukumomi miliyan 418 domin biyan albashin ma'aikata.

Daga nan ya bukaci maaikata da sauran alummar jihar nan su dage da yin adduoi domin magance kalubalen tsaro da kuma matsin tattalin arziki dake damun kasar nan.

Tun farko a nasa jawabin shugaban kungiyar kwadago ta jiha Comrade Sanusi Alhassan Maigatari ya yabawa gwamnatin jiha saboda biyan albashi da fansho akan lokaci duk da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta, Comrade Sunusi Alhassan yace kungiyar tana alfahari da yadda gwamnatin jiha take biyan albashi da fansho duk kuwa da halin matsin kudaen da ake fama da shi.

Ya ce ma'aikata na daya daga cikin wadanda s**a amfana da aikin calculator ta gwamna domin kuwa suna samun albashin kafin 25 ga kowane wata.

Inda ya roki gwamnati data cike gibin maaikatan da ake dasu a maaikatu da hukumomin gwamnati tare da nada wakilan hukumar gudanarwar asusun adashen gata na fansho na jihad a kananan hukumomi.

Taken bikin na bana shine cutar corona da matsalar tattalin arziki da kalubalen samun aiki mai gwabi da bada kariya ga masu karamin karfi da kuma kyautata rayuwar alumma.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Meza kuce Dangane da Wannan Zane na Kafar  Dan Kwallon Real Madrid Sagio Ramos?
Jimkadan Bayan Shan Ruwa Wakilin Al'ummah Radio & TV yayi kwallin Kura da Wannan Al'ada Ta Fulani.
TAFSIRIN ALQUR'ANI MAI GIRMA KENAN DAGA MASALLACIN MARIGAYI MALAM ABDULLAHI KOFAR YANDAKA.Inda Malam Muhammad Famfo Keja...

Category

Telephone

Website

Address

Dutsin Amare
Katsina
Other TV Channels in Katsina (show all)
Rics Rics
Liyefi Palace
Katsina, PAUL

Nishadi gwarjo TV Nishadi gwarjo TV
Salahawa
Katsina

Nabude wannan Shane da.abubuwa k**arhaka videoyi dapoto dawakoki dalabarai dadai sauransu

Arewa news tv Arewa news tv
Mallamawa
Katsina, DAURA

Arewa

HMD TV HMD TV
Kofar Kaura
Katsina

Thank

Smart∆ngle Smart∆ngle
Katsina

Kahutu Gari Ya waye TV Kahutu Gari Ya waye TV
Danja
Katsina

Irinkudi News Tv Irinkudi News Tv
Maiduguri Road Katsina
Katsina

Sell of data and airtime vtu

Hausa Toon Tv Hausa Toon Tv
Katsina, 202020

Kuddana like domin samun shirye shirye na comedy madlipz

Mass fkm tv Mass fkm tv
Faskari
Katsina, 000886

Barkada Zuwa mass fkm tv

M J aboki hausa tv M J aboki hausa tv
Katsina

Mashaallah muna godeya gaduk mabiyan chennel namu allahya bamutare ammeeeeen

Makudawa TV Makudawa TV
Makudawa
Katsina

Wannan itace hanya mapi sauki daxaku samu damar shiga youtube channel namu kai tsaye batare da kunsha wahalaba

TAFI KWABO TV TAFI KWABO TV
Katsina

Shafin Wayarma jama a dakai Baanfa Zagi ko cin mutunci