Gwagware Ward To Ward Network 2023
Nearby public figures
Saulawa
Jikamshi Street
Pdp Headquarters Katsina
Old Benin Road Ore
Off Law School Road, Abuja
Los Angeles 820212
Bre Lga
Opposit Bodamasi Kabir Usman House Katsina
Domin yada manufofin Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin Jam'iyar APC DR. DIKKO UMAR RADDA (G
DR. DIKKO RAƊƊA YA KAMMALA GANGAMIN YAKIN NEMAN ZABEN SA NA SHIYYAR KATSINA TA TSAKIYA A KURFI.
Ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Raɗɗa, ya kammala gangamin yaƙin neman zaɓen sa na shiyyar Katsina ta tsakiya a karamar hukumar Kurfi, ranar Alhamis, 5/01/2023.
Kafin isa filin gangamin da aka shirya a garin Kurfi, tawagar ta zagaya dukkan mazaɓu goma da ke karamar hukumar Kurfi, wanda s**a hada da Tsauri A da B, Wurma A da B, Rawayau A da B, Birchi , Barkiya da Kurfi A da B domin ganawa da Magaddai, masu unguwanni, limamai da masu ruwa da tsaki domin neman alfarma da goyon bayan Jam’iyyar APC.
A dukkan mazaɓu da aka ziyarta, tawagar ta samu tagomashi da karɓuwa kwarai da gaske daga al’ummar wannan mazaɓu wanda s**a haɗa da kyaututtuka da dan takarar ya samu daga mutanen gari domin nuna goyon baya.
Bayan kammala ziyara dukkan mazaɓu, tawagar ta doshi fadar mai martaba Maraɗin Katsina, Hakimin Kurfi, Alhaji Dr. Amadu Kurfi, domin gaisuwa da kuma neman tabarraki na iyayen ƙasa, wanda hakimin ya bayyana jin daɗin shi bisa wannan ziyara tare da addua ta samun nasara.
A lokacin gangamin yaƙin neman zaben, Dr. Dikko Raɗɗa yace" zai yi kokari wajen baiwa matasa aikin yi domin tun karar matsalar tsaro, inda za'a horar dasu a haɗasu da ma'aikatan tsaro na soja dana ƴan sanda domin kare rayukan al'umma da dukiyoyin su.
Ɗan takarar gwamnan yaci gaba da cewa" Wasu shed'anu zasu zo maku inda zasu ce maku babu tsaro, saboda haka kusani matsalar tsaro sune s**a kawota, Kuma akwai wani mutum na nan shirmeme kudin tsaro da aka bada a Jihar katsina na shekara bakwai da rabi suna hannun shi saboda haka idan yazo ku tambaye shi.
Daga ƙarshe ya ƙara jaddada ma al'umma cewa" Insha Allahu idan ya samu nasara a babban zabe zaiyi kokari wajen inganta rayuwar al'ummar karkara, samar da aiyyukan yi, kara habaka harkar noma da kiwo da inganta harkokin lafiya da sauran su.
Mutane da dama ne s**a tofa albarkacin bakinsu a ya yin da ake gudanar da gangamin yaƙin neman zabe daga ciki akwai tsohon Ɗan majalisar tarayya wanda ya wakilci kurfi/Dutsan-ma, Hon. Ɗanlami kurfi, Ɗan takarar majalisar wakillai na Kurfi da Dutsin-ma, Hon. Aminu Balele Dan Arewa, Ɗan takarar majalisar dokokin Jihar katsina mai wakiltar karamar hukumar kurfi, Hon. Zaharadeen da Ɗan takarar sanata na shiyyar katsina Kanal Audulaziz Musa Yaradua da sauran su.
Gangamin yakin neman zaben zaya je hutu daga ranar Juma’a 6 ga watan Janairu zuwa ranar Lahadi 15 ga watan Janairu 2023.
AL'UMMAR KARAMAR HUKUMAR CHARANCHI SUN NUNA KARAMCHI GA DR. DIKKO RADDA LOKACIN GANGAMIN YAKIN NEMAN ZABEN SA A CHARANCHI
Ziyarar da Dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Radda, da tawagarsa s**a kai Karamar Hukumar Charanchi, tabbas ya nuna cewa ya zo gida, a inda ‘yan uwa da abokai da magoya bayansa da masu taya shi murna s**a fito domin tarbarsa daga Garin Eka da ke kan titin Kuraye cikin kayatarwa, a ranar Talata, 3/01/2023.
A Lokacin da tawwagar ta iso garin Kuraye, dubban magoya baya ne s**a yi tarba cikin wake wake da raye raye don barka da zuwa har isa fadar Sarkin Kuraye.
A dukkan mazabun da aka ziyarta, Dr. Radda ya kai gaisuwar ban girma ga Masu gari, Dagattai kafin wucewa ga fadar sarkin shanun Katsina, Hakimin Charanchi, Alh. Abashe Abdulkadir da kuma Sarkin Kurayen Katsina, Hakimin Kuraye, kamar yadda aka saba don neman tabarakin iyayen kasa da goyon bayan da kuma adduo'i.
A babban taron da aka yi a garin Charanchi, yayin da yake nuna jin dadin sa ga dimbin jama'ar da s**a yi masa tarba, Dr. Radda ya bayyana musu kudirinsa in Allah ya bashi damar zama gwamna, tare da yin Kira a garesu da su zabi dukkan 'yan takarar jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.
Sauran wadanda s**a yi jawabi a wajen taron sun hada da dan takarar Sanatan Katsina ta tsakiya, dan takarar Rimi, Charanchi, Batagarawa, dan majalisar jiha mai wakiltar Charanchi, Darakta na yakin neman zabe, da dai sauransu.
GWAGWARE WARD TO WARD CAMPAIGN
Tawagar Dan takarar Gwamnan jihar Katsina karkashin tutar jam'iyyar APC sun sauka Karamar Hukumar Charanchi a safiyar Talata, 3/1/2023, a cigaba da ganawa da al'ummar mazabun 361 dake jihar Katsina.
Tawagar ta samu kyakyawar tarba daga dumbin masoya da magoya baya, matasa, mata da sauran
3/01/2023
DIKKO RAƊƊA DAN UWANA NE NA JINI AN KAWO MANI ZAMIYA BA IYAKA NACE A’AH INDAI GWAGWARE YANA CIKI TO BANI DA WANI MAZABI SAI SHI- SARKIN KATSINA ABDULMUMIN KABIR USMAN
Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir Usman, Ya faɗi hakan ne a lokacin da Ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina na Jam’iyyar APC ya kai mashi ziyarar ban girma a fadar shi dake Ƙofar Soro, Katsina ranar Lahadi, 1st Janairu 2023.
Dr. Dikko Raɗɗa ya bayyana maƙasudin wannan ziyara a matsayin girmamawa da neman tabarraki na iyayen ƙasa sarakuna akan takarar sa ta neman gwamna da sauran yan takarkaru na Jam’iyyar APC a jihar Katsina. Ya shaida ma sarki yadda tawagar sa s**a zagaya kananan hukumomi sha tara (19) da mazabu sama da dari da sabain (170) na jihar Katsina domin neman goyon bayan al’umma.
Ya shaida ma mai martana cewa yana da kundi wanda zai shugabanci al’umma idan Allah ya bashi nasara wanda ya haɗa da hanyoyin magance matsalar tsaro, farfaɗo da harkar ilimi, lafiya da hanyoyin samar da aiki ga matasa, mata, da masu kananan ƙarfi.
A fannin ilimi ya bayyana cewa gwamnatin sa zata assasa makarantu na gwamnati na musamman domin ɗaukar yara masu basira aƙalla guda daya a kowace shiyya, sannan harkar lafiya zasu inganta wannan fanni ta hanyar ɗaukar likitoci wanda za a basu horo na musamman domin su zauna a kananan hukumomin su saboda karancin likitoci da jihar ke fuskanta.
A kokacin da yake jawabi, Mai martaba sarki ya yi farin ciki akan wannan ziyara inda ya bayyana ta a matsayin zumunchi domin Ɗan Takarar gida yazo. Ya ce Dr. Dikko Raɗɗa mutum ne mai nagarta da sanin girman nagaba kuma dan uwa na jini, a sabili da haka yana tare dashi akan aniyar sa ta zama Gwamnan jihar Katsina.
Yayi kira a gare shi da ya ji tsoron Allah ya kare hakkin talaka idan Allah ya bashi nasara, domin Allah zai tambaye shi a gobe ƙiyama yadda ya gudanar da shugabanci. Daga karshe yayi addu’a samun nasara da fatan alkhairi.
Tawagar ta kunshi Mataimakin Gwamnan jihar Katsina, QS. Mannir Yakubu, Ɗan Takarar mataimakin gwamn
DR. DIKKO UMARU RAƊƊA YA BINNE JAMIYYAR PDP A KARAMAR HUKUMAR DANMUSA
Ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina na Jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Raɗɗa ya jijjiga karamar hukumar Ɗanmusa inda dubban magoya baya s**a yi dafifi domin tarbar shi a cigaba da yaƙin beman zaɓen sa da ya guda a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba 2022.
Tawagar wanda ta ƙunshi jigajigan Jam’iyyar APC sun isa fadar Hakimin Danmusa bayan gaisuwa da s**a fara kai ma Sarkin Fulanin Dangi, Hakimin Yantumaki, domin neman tubarraki da goyon baya daga masarautu, limamai da sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar.
Tawagar ta shafe aƙalla sama da awa ɗaya da rabi daga fadar Hakimin Ɗanmusa zuwa sakatariya ta karamar hukuma, inda Dr. Raɗɗa ya ƙaddamar da motoci guda biyu da babura talatin (30) ga Sojoji da Shugabannin Jam’iyya wanda Shugaban Karamar hukumar Ɗanmusa, Hon. Sanusi Abbas Dangi ya bada.
A lokacin da tawagar ta ɗan takarar gwamnan ta isa filin taron, babu masaka tsinke domin kuwa dubban masoya, maza da mata ne s**a yi cincirindo wajen gane ma idon su tsarabar da ɗan takarar ya zo masu da ita.
A lokacin da yake jawabi, Dr. Dikko Raɗɗa ya fara da nuna farin cikin shi a fili don ganin yadda al’ummar Ɗanmusa s**a amsa kiran Jam’iyyar APC. Ya bayyana karamar hukumar a matsayin wadda Allah ya albarka da wasu muhimman mutane wanda aka amfana da su da cigaban da s**a kawo amma sabanin wasu mutane da s**a samu dama basu taimaki al’umma ba.
Ya cigaba da cewa, ya san babban abun da ya dami al’ummar Ɗanmusa wanda shine matsalar tsaro, a sabili da haka ya basu tabbacin cewa yana da kyakyawan tsari da yayi na sha’anin tsaro wanda cikin amincewar Allah zai zamo silar kawo karshen matsalar a jihar Katsina. Sannan, yasha alwashin ba matasa da mata jari na yin sana’oi domin bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma samar da aikin yi ga al’ummar Katsina baki daya.
Taron ya samu halartar Dan Takarar Gwamnan, Dr. Dikko Radda, Dan Takarar mataimakin gwamna, Hon. Faruq Jobe, Shugaban Kwamitin yakin neman zaben APC na jihar Katsina, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Hon. Bala Abu Musawa, Hon. Garba Sai baba, Hon. Sanusi Abbas Dangi, Col. Abdulaziz Musa Yar’adua, Hon. Abdulkadir Zakka, Hon. Musa Adamu Funtua, Hon. Jabiru Tsauri, Hon. Abdullahi Aliyu Musawa, Hon. Abubakar Sukaiman Korau, Hon. Usman Banye, Injiniya Surajo Yazid Abukur da sauran su.
DUTSINMA TAYI GWAMNA IBRAHIM SHEMA, YANZU KUMA ZATA YI GWAMNA DIKKO UMARU HAYINGADA- INJI DR. DIKKO RADDA LOKACIN GANGAMIN YAKIN NEMAN ZABE A DUTSINMA
A cigada da gangamin yakin neman zabe da dan takarar gwamnan jihar Katsina keyi a karkashin Jamiyar APC, a yau Jumua, 30 ga watan Disamba 2022, Dr. Dikko Umaru Radda ya jagoranci tawagar zuwa Karamar Hukumar Dutsinma.
Tawagar Dan takarar gwamnan ta samu nasarar shiga lungu da sako inda aka ziyarci mazabun Dabawa, Makera, Kutawa, Karofi, da Kuki Kafin wucewa garin Dutsinma don gudanar da babban taron Karamar hukuma.
A Dukan mazabun da aka ziyarta, Dr. Radda tare da tawagar sa sun samu tarba daga dubban magoya baya da magoya da su kai tururuwa don nuna goyon bayansu ga dan takarar gwamnan.
Dan takarar gwamnan ya gana da al'ummar yankunan da magaddai inda ya bayyana masu kudurorin dake gareshi idan Allah ya bashi damar zama gwamna wanda s**a hada da inganta tsaro da samar da ayyukanyi da bunkasa ayyukan gona da sauransu.
Hakanan Dr Radda ya kai ziyarar bangirma da neman tabarakin iyayen kasa a fadar Yan Dakan Katsina Hakimin Dutsinma.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan jihar Katsina yayi Kira da a zabi dukan yan takarar da Jamiyar APC ta tsaida a zabuka masu zuwa yana mai cewa Jam'iyar APC tayi ayyukan raya kasa a matakin kasa da jiha da karamar hukuma.
Tawagar Dan Takarar gwamnan a yau ta samu rakiya ta Musamman daga Gwamnan jihar Katsina, Rt. Aminu Bello Masari da mataimakinsa Qs. Mannir Yakubu da yan majalisar jiha data zartaswa da masu bada shawara da mataimaka na musamman.
Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Radda, ya jaddada kudirinsa na shigewa gaba wajen yaki da rashin tsaro a jihar Katsina.
Dr. Radda ya yi wannan ikirari ne a lokacin da yake ganawa da dimbin jama’ar da s**a tarbe shi a karamar hukumar Safana a ci gaba da gudanar da gangamin yakin neman zaben 2023, a yau Alhamis, 29/12/2022.
Dr. Radda ya jagoranci tawagar yakin neman zaben tun daga Katsina zuwa Zakka domin ziyartar fadar Gatarin Katsina, Hakimin Zakka, daga Zakka zuwa Kukar Samu ta garin Batsari, daga Kukar Samu zuwa Babban Duhu, Daga Babban Duhu, Dr. Radda ya jagoranci tawagar kamfen din zuwa garuruwan Baure, Ummadau, Tsakiya, R***a inda daga karshe kuma ya tsaya a filin taron gangamin kamfen a garin Safana.
A lokacin da ya isa garin Tsaskiya, ya bayyana ma al'umma cewa, sun zo ne domin ganin halin da suke ciki domin kuwa an shaida masu cewa ba zasu iya zuwa ba saboda babu tsaro, amma ya tabbatar da cewa in dai akwai alumma a garin, to babu abun da zai hana su zuwa in dai da gaske yana San shugabancin Katsina.
A duk wuraren da ya ziyarta Dr. Radda ya bayyana cewa duk wani shugaban da zai yi yaki da matsalar rashin tsaro da jihar ke fama da shi, dole ne ya kuduri aniyar shigewa sahun gaba a fagen daga. Ya bayyana yaki da rashin tsaro a matsayin wani nauyi daya rataya a wuyan kowa, don haka akwai bukatar hadin gwiwa tare da yin nuni da cewa dole ne kowa da kowa ya tashi tsaye domin samun nasara a wannan fanni.
Dan takarar gwamna na jam'iyyar APC ya bada tabbacin inganta harkar noma tare da samar da kananan sana'o'i domin samar da ayyukan yi ga matasa da mata a fadin jihar nan.
"DIKKO RAƊƊA NE MUTUN NA FARKO DA YA FARA BA YAN GUDUN HIJIRA A BATSARI TIRELA BIYU TA KAYAN ABINCI A 2019, DON HAKA BA SAI KAZO BA, MU ZAMUYI MA AIKI" - INJI SARKIN RUMA HAKIMIN BATSARI
A ci gaba da gangamin yakin neman zabe, a yau Laraba, 28 ga watan Disamba 2022, tawagar Ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina a Karkashin Jamiyar APC, Dr. Dikko Umaru Raɗɗa ta sauka a karamar hukumar Batsari.
A lokacin da tawagar ta isa karamar hukumar ta Batsari, Ɗan takarar gwamnan Dr. Raɗɗa jagorance ta zuwa kai gaisuwar ban girma da neman tabarakin iyayen ƙasa a Fadar Gado Da Masun Katsina, Hakimin Wagini, Alh. Dikko Muazu Ruma dake a garin Wagini inda ya gana da Hakimin da sauran Dagattai na gundumar Kafin zarcewa zuwa fadar Sarkin Ruma, Hakimin Batsari dake a garin Batsari inda anan ma ya gana da hakimi da magaddai.
Bayan gaisuwar ban girma da neman tabarakin shuwagabanin alumna, tawwagar ta wuce zuwa filin da aka shirya ganawa da alumna a filin taro.
Da yake jawabi ga dimbin jama’ar da s**a tarbe shi, Dr. Raɗɗa ya jajantawa al’ummar Batsari kan matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin tsawon shekaru tare da bada tabbacin yin kokarin sa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar idan aka zabe shi. Ya shaida cewa, ko da kuɗin jihar zasu ƙare a kan kawo karshen matsalar tsaro, to zai yi amfani da su domin kawo zaman lafiya a jihar Katsina. Ya kuma basu tabbacin kawo kyakywan shugabanci wanda jihar zata yi alfahari dashi.
Dr. Radda ya kuma yi amfani da damar wajen sanar da al'ummar yankin yadda ya kuduri aniyar kawo sauyi a harkar noma da kuma bullo da kananan masana'antu da sarrafa kayan gona a fadin jihar.
Yayin da yake kira ga al’ummar yankin da su zaɓi daukacin ‘yan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, Dakta Dikko ya gode musu bisa kyakkyawar tarba da s**a yi masa da mukarrabansa.
Sauran wadanda s**a yi jawabi a lokacin yakin neman zaben sun hada da shugaban jam'iyyar APC na jiha, Alh. Sani Aliyu Daura, Shugaban kwamitin yakin neman zabe Dikko/Jobs, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Shugaban Karamar hukama, Hon. Yusuf Mamman Ifo, Dan takarar Sanata na Katsina ta tsakiya, Col. Abdulaziz Musa Yar'adua da sauran 'yan takarar APC na shiyyar.
Ya zama wajibi ga al'ummar karamar hukumar Daura muba jam'iyyar Apc kuri'a, domin duk abinda al-ummar Daura ke nema an masu.
Al'ummar Daura sun bayyana haka ne, ranar Lahadi 11/12/2022, ya yin da jirgin yakin neman zabe na Dan takarar Gwamnan Jihar karkashin tutar Jam'iyyar Apc, Dr. Dikko Umar Radda ya sabkar karamar hukumar.
Daga cikin ayyukan raya kasa da Al'ummar Daura su ka bayyana Gwamnatin Apc tayi masu, sun hada da samar da hanyoyi da mugudanun ruwa a cikin garin na Daura.
Samar da Jami'ar sufuri da gwamnati tarayya da asibitin mata da kananan yara, da Kuma makarantar kimiyi da fasaha ta gwamnatin tarayya watau Daura polytechnic, samarma matasa aiyyukan yi da dai sauransu.
Da yake gabatar da jawabinsa Dan takarar Gwamnan Dr. Dikko Radda ya yi alkawalin, idan Al'ummar Karamar hukumar Daura ta zabe shi, zai kula da rayuwar Mata, Matasa, Marayu, da Kuma tsare dukiyar al'umma da sauransu.
Mutane da dama ne s**a tofa albarkacin bakin su daga ciki akwai Dan takarar Sanata na shiyyar Daura Hon. Nasir Sani zangon Daura, Dan takarar majalisar tarayya mai wakiltar Daura sandamu Mai'adua Hon Aminu Jamo.
Sauran sun hada da shugaban jam'iyyar Apc na Jihar katsina Alh. Sani JB Daura bayan ya kammala jawabin shi ya amshi wasu yan takarkaru na jam'iyyar ADC Wanda s**a ajiye takararsu s**a dawo Apc.
Dan takarar ya samu tarba daga Dandazon dubban Al'ummar karamar hukumar Daura ciki har da shugaban karamar hukumar Hon.Bala Musa, Dan takarar majalisar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Hon. Nasir Yahya, Jigo na jam'iyyar Apc Sarkin Sudan, shugabannin Jam'iyyar Apc na karamar hukumar Daura.
A cikin tawagar Dan takarar Gwamnnan sun hada da Darakta Janaral na yakin neman zabe Arc. Ahmed Musa Dangiwa, Dan takarar mataimakin Gwamna Hon. Faruq Jobe.
Daga cikin kungiyoyi sun hada da Kungiyar Gwagwariyya/Masariyya karkashin Jagorancin Dr. Abubakar Tsanni Soja, kungiyar Dikko Support Group karkashin Jagorancin Hon. Abubakar Matazu, kungiyar Yusuf Jirdede support Group. Dadai sauran su.
Manyan baki da su ka halarci yakin neman zaben a karamar hukumar Daura Sanata Abu Ibrahim, Tsohon gwamnan jihar Barno kanal Abdulmumin Aminu Mai ritaya, Kwamishina na ma'aikatar kananan hukumomin da masarautu Hon Ya'u Umar Gwajo gwajo da sauransu.
AL'UMMAR SANDAMU, ZAMU RIKE KU A CIKIN MUTUNCI, ZAMU TALLAFAWA MATAN KU, MATASANKU, DA DATTAWANKU, BA TARE DA CUTA KO CUTARWA BA~INJI DR. DIKKO UMAR RADDA
A yau asabar, 10/12/2022, dantakarar Gwamnan jihar Katsina a karkashin Jamiyyar APC, da 'yan tawagarsa, sun samu tarba daga dimbin al’ummar Karamar hukumar Sandamu, a cigaba da yakin neman zabe na Jamiyyar na Jihar Katsina a shekarar 2023.
Shugaban karamar hukumar ta sandamu, Hon. Usman Nalado, ya bayyana cewa al'ummar Sandamu tabbas tsakaninsu da jam'iyyar Apc sai godiya, domin jam'iyyar ta gina masu jami'ar sufuri (University of Transportation), babban Asibitin Sojojin sama (Air force Refferal Hospital) da hanyoyi da dama domin saukaka tafiye-tafiye ga al'ummarsu, Don haka ya kara shaida masu cewa idan suna so su cigaba da samun cigaba, to su marawa jam'iyyar Apc baya ta hanyar zaben dukkanin 'yantakarar a ranar zabe mai zuwa.
Ɗan takarar majalisar jiha na karamar Hukumar Sandamu, shima dayake gabatar da jawabinsa ya yaba ma shugaban karamar hukumar abisa ayyukan da yakeyi domin kyautata rayuwar al'umma, ya kara da kira ga al'ummar Sandamu da su zabi Dr. Dikko Radda da dukkan 'yantakarar jam'iyyar Apc a zabe mai zuwa na 2023.
Shima Ɗan takarar majalisar tarayya na Daura, Sandamu da Maiaduwa, Hon. Aminu Jamo, yayi ma 'yan tawagar barka da zuwa mahaifarsa ta Sandamu, ya kuma kara da yin kira ga al'umma da su zabi Dr. Dikko Radda, a lokacin zabe mai zuwa domin tabbas Dikko Radda, Dan amana ne, kuma ina tabbatar maku da cewa duk abinda ya fada maku zaiyi, to insha Allahu zai aikata shi domin na sanshi tun tuni.
Arch. Ahmed Musa Dangiwa, Darakta Janar na yakin neman zaben APC a jihar Katsina, yayi kira ga Al'ummar Sandamu da su zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Dr. Dikko Radda a zabukan 2023
domin sun cancanta kuma zasu kawo cigaba mai dorewa a karamar Sandamu.
A lokacin da yake jawabinsa Dr. Dikko Radda ya fara da godiya bisa ga karamcin da s**a samu daga al'umma garin Sandamu, tare da shaida masu cewa idan Allah ya bashi nasara zaya mutunta su zai tsare hakkin al’ummar jihar Katsina. Yace, "Jam'iyyar APC ta kawo maku tallafi iri-iri kamar su Spower da Npower ga matasa da shirin bada kudin ga masu karamin karfi" kuma ina tabbatar maku da cewa idan kuka zaɓe mu ba zamu cuce ku ba, kuma bazamu bari a cuceku ba, in Allah ya yarda.
Ya ce, Duk wadanda kuka ga suna fada damu ko adawa damu, toh ba komai bane dalilin shine don munce zamu kyautata ma talakawan jihar katsina, Insha Allah a karkashin jagorancin mu talaka sai yaci roman demokrafiya.
A karshe Dantakarar Gwamnan ya roki alfarmar al'ummar karamar hukumar Sandamu dasu goyi bayan jam'iyyar APC madadin dukkanin yan takarkarun jam’iyyar APC tun daga sama har kasa.
Daga cikin wanda da s**a halarci yaƙin neman zaben akwai tsohon Sanatan shiyyar Funtua, Sen. Abu Ibrahim, tsohon Gwamnan jihar Borno, Kanal Abdulmuminu Aminu, Barista Ahmad Elmarzuq, mataimakin shugaban jam'iyyar APC, Alh bala Abu Musawa da sauran manyan baki.
SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YAYI MA DR. DIKKO UMARU RAƊƊA FATAN SAMUN NASARA A ZABEN 2023
A daren jiya ne, ranar Juma’a, 9/12/2022, Mai girma Shugaban Tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya karɓi baƙuncin tawagar Zaɓaɓɓen Ɗan Takarar Gwamnan jihar Katsina a Jam’iyyar APC, Dr. Dikko Umaru Raɗɗa, a gidan sa dake Daura, Katsina.
Ɗn takarar na Gwamna, Dr. Dikko Raɗɗa, ya shaida ma Shugaba Muhammadu Buhari cewa, sun zo ne domin suyi mashi maraba da zuwa da kuma sanar da shi yadda al’amuran yaƙin neman zaɓen Jamiyyar APC a jihar Katsina ke gudana, wanda a cewar shi, suna zagayawa kowane Mazabu dake fadin jihar Katsina domin ganawa da al’ummar mazabun domin ganin wane irin hali suke ciki.
Ya cigaba da cewa, bisa ga yadda idansu s**a shaida masu daga kamfen din da aka fara, al’ummar Katsina na tare da Jamiyyar APC saboda duk inda s**a shiga ana masu marhaba da kyakyawar tarba. Ya sanar da Shugaba Muhammadu Buhari cewa sha’anin tsaro a jihar Katsina an samu sauƙi bakin gwargwado bisa ga kyakyawan shugabanci irin na Shugaban Ƙasa.
Daga ƙarshen, Dr. Raɗɗa ya tabbatar ma da Shugaban Kasa cewa, zai kare haƙƙi da mutuncin al’ummar jihar Katsina idan Allah ya bashi nasarar zama Gwamnan.
Da yake maida martani, Shugaba Buhari ya nuna jin daɗin shi matuƙa bisa ga wannan ziyara da aka kawo mashi, ya kuma Shaida ma Ɗan Takarar cewa yana samun labaru akai-akai game da sha’anin yaƙin neman zaɓen Jamiyyar APC a jihar Katsina.
Shugaba Buhari ya yi kira ga yan jamiyyar APC da su haɗa kai domin ganin an ɗinke duk wata ɓaraka da ba a rasa ba, domin a cewar shi sai an zama tsintsiya maɗauri daya sannan za a samu nasara. Ya bada tabbacin cewa, zai bar kyakyawan tarihi a sha’anin siyasa da demokradiya a Najeriya domin zai bada cikkaken goyon baya don ganin anyi sahihi da ingantaccen zabe, zai mutunta duk wani zaɓi da yan Najeriya s**ayi a zabukan 2023.
Daga ƙarshe ya tabbatar ma da ɗan takarar da tawagar shi cewa, zai dawo Daura idan wa’adin mulkin shi ya kare, a sabili da haka yana addu’a cewa Dr. Dikko Radda zai samu nasarar zama Gwamnan jihar Katsina a shekarar 2023.
Tawagar Ɗan Takarar sun haɗa da, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon. Tasi’u Maigari Zango, Mataimakin Ɗan Takarar Gwamnan jihar Katsina, Hon. Faruk Lawal Joɓe, Shugaban Kwamitin Yakin neman Zaɓen APC, Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, Mai ba Jamiyyar APC ta Ƙasa shawara akan harkokin Shari’a, Barista Ahmed El-Murzuq, Hon. Nasiru Sani Zangon Daura, Hon. Jabiru Tsauri, Barista Hannatu Musawa, Hon. Abdullahi Aliyu Musawa, Hon. Usman Banye, Abubakar Badaju Jikamshi, da Shugaban Kungiyar Gwagware Media Reporters, Isah Miqdad.
Daga:
ZAMU TABBATAR DA CEWA TSARO YA DAWO, ILIMI YA INGANTA, DAN TALAKA ZAI IYA ZUWA MAKARANTA KAMAR YADDA DAN MAI KUDI KE ZUWA- DR. DIKKO RADDA A MAI'ADUA
Tawagar dan takarar Gwamnan jihar Katsina da Jamiyyar APC sun samu kyakyawar tarba daga al’ummar Karamar Hukumar Mai’adua, a cigaba da gangamin yakin neman zaben Jamiyyar na Jihar Katsina a shekarar 2023, a yau Juma’a, 9/12/2022.
Shugaban Jamiyyar APC na Maiadua a lokacin jawabin maraba, ya shaida cewa idan Allah ya kaimu ranar zabe zasu fito kwansu da kwalkwata domin zabar APC. Ya cigaba da cewa Gwamnanatin APC tayi rawar gani wajen gina hanyoyi wanda karamar hukumar ke amfana da su kamar hanyar da ta tashi daga Fago ta biyo ta Katsayal zuwa Koza, da sauran su.
Shugaban Karamar Hukumar Maidua, Hon. Shehu na Allahu, ya bayyana cewa Jamiyyar APC tayi ayyukan alkhairi wanda duk Afrika babu wanda yayi, wanda s**a hada da ciyarwa, tallafi, ta habbako da tattalin arzikin noma. Daga karshe yace, da amincewar Allah zasu bada gagarumar gudunmuwa domin ganin an samu nasara a zaben 2023.
Shima dan takarar Majalisar Dattijai na shiyyar Maiadua, Hon. Nasiru Sani Zangon Daura, ya shaida cewa suna godiya kwarai da gaske bisa ga tarba ta musamman da s**a samu daga al’ummar Maiadua. Yace alamu sun nuna cewa wannan zaben Jamiyyar APC ke da nasara cikin yardar Allah.
Darakta Janar na yakin neman zaben APC a jihar Katsina, Arch. Ahmed Musa Dangiwa, ya shaida cewa yana fatan cewa Mai’adua zata linka kuri’u da s**a bada a zabukan 2019, tare da kiran su da su zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Dr. Dikko Radda a zabukan 2023. Ya yi kira da masu ruwa da tsaki cewa a tabbatar da kowa ya kawo runfunan zaben su domin samun nasar APC a dukkanin matakai.
Da yake maida martani, Dr. Dikko Radda ya fara da godiya bisa ga kyakyawar da s**a samu, tare da shaida masu cewa idan Allah ya bashi nasara zaya tsare hakkin al’ummar jihar Katsina. Yace, "sadda na fito takara, nace Allah ke bada mulki, wurin shi ake neman mulki, abun da yasa suke fada da mu, don munce zamu kare maku mutunchin ku”.
Ya cigaba da cewa, "Zamu tabbatar da cewa tsaro ya dawo, ilimi ya inganta, dantalaka zai iya zuwa makaranta kamar yadda dan mai kudi ke zuwa makaranta, in Allah ya yarda matasa, mata da gajiyyayu zamu baku jarin da zakuyi sana’a. Idan zamu gina asbiti guda uku sabuwa, to Maiadua tana sahun farko".
Ya ce, lokacin cin mutunchi a siyasa ya kare, don haka azo ayi siyasa mai tsafta domin cin roman demokrafiya, daga karshe ya roki alfarmar su akan neman goyon bayan su a madadin duk yan takarkarun jam’iyyar APC daga sama har kasa.
IDAN ALLAH YA BAMU NASARA ZAMU KAWO CIGABA DA BA A TABA GANI BA A JIHAR KATSINA- Inji Dr. Dikko Umaru Raɗɗa lokacin gangamin yakin neman zabe a karamar hukumar Zango
Tawagar dan takarar gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar APC, Dr. Dikko Radda, sun isa karamar hukumar Zango domin cigaba gangamin yakin neman zaben 2023 a yau, Alhamis, 8 ga watan Disamba, 2022.
Tawagar ta samu kyakkyawar tarba daga dumbin magoya baya da masoya a lokacin da tawagar ta isa fadar Mulkan Daura, Hakimin Zango domin neman albarka.
Shugaban Karamar Hukumar, Hon. Babangida Yardaje, yayi jawabin maraba wanda ya tabbatar da cewa al'ummar Zango sun amfana da gwamnatin APC don haka zasu maida alkhairi a akwatin zabe.
Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Katsina, Rt. Hon. Tasi'u Maigari zango, ya shaida cewa duk alkawarin da s**a dauka a Karamar Hukumar Zango a 2019 sun cika shi, domin sun kammala aikin T**i daga Zango zuwa Rogogo, an samar da ruwan sha a karkara, sannan a kalla an samar da wuta a kauyuka sama da goma a Zango. Domin haka, yana fatan cewa APC zata samu kuri'u masu rinjaye da amincewar Allah.
Dan takarar gwamnan Jihar Katsina a Jam’iyyar APC, Dakta Dikko Radda, a lokacin da yake jawabi ya shaida cewa, gaskiya ta fito fili, amichi ya bayyana don haka babu batun yaudara a wannan kakar zaben . Yace babu wani wanda zai chanza ma mutanen Zango tunani domin kuwa Jam’iyyar ta shimfida abun alkhairi a wannan gari. Ya cigaba sa cewa, idan Allah ya yarda marayu da gajiyayyu zasu samu gata idan Allah ya bashi nasara a zaben 2023.
Daga karshe yayi addu'a duk wadanda ke takarar gwamnan jihar Katsina, Allah ya maida kowa aniyar shi koh ta alkhairi koh akasin haka.
TARON KADDAMAR DA KUNGIYAR GWAGWARE WARD TO WARD NETWORK 2023 A TARE DA BADA TALLAFIN JARIN SANA'A GA MATA 200
A jiya Lahadi ne 04-12-2022 aka kaddamar da kungiyar Gwagware Ward To Ward Network tare da bada tallafin naira N5000 ga mata 200 wanda kungiyar ta dauki nauyi.
A yayin jawabin shi, mataimakin shugaban kungiyar, Malam Naufal Ahmad yace manufar kungiyar shine fadakar da al’umma akan zabar shugabanni masu nagarta, tare da wayar masu da kai akan muhimmancin zabe da kuma bada tallafi ga masu karamin karfi.
Malam Naufal yace a matsayin su na matasa yasa s**ayi tunanin su bada lokacin su da kudinsu da duk damar da suke da ita da gudummuwarsu don ganin Dr. Dikko Radda ya samu nasara a zaben 2023.
Ya jaddada muhimmancin mata da rawar da rawar da suke takawa a zabe shiyasa s**a zakulo su don su basu tallafin da zasu inganta sana’oin su domin dogaro dakai.
Yace an kirkiro da wasu tsare-tsare da kungiyar zata aiwatar anan gaba da zasu amfani al’umma baki daya.
Shima da yake jawabi, Ko’ordinetan kungiyar, Hon. Ibrahim Tijjani Damale, ya gode ma Allah da ya bada ikon kaddamar da kungiyar.
Yace shuwagabanin kungiyar sun dade suna taka rawa dangane da nasarar jam’iyyar APC tun daga zaben shekarar 2015.
Ibrahim Tijjani yace kungiyar tana da membobi tun daga matakin ƙananan hukumomi har zuwa runfar zaɓe.
Ya gode ma shugaban ƙungiyar, Alhaji Kabir Kabir Ibrahim wanda shi yake daukar dawainiyar da yawa aikace-aikacen da suke gabatarwa.
Shima a nashi jawabin, shugaban gamayyar kungiyoyi masu goyon bayan Dikko/Jobe, Alhaji Yusuf Ali Musawa ya jinjina ma kungiyar bisa gudummuwar da suke ba takarar Dikko Radda da jam’iyyar APC.
Yace ashirye yake ya haɗa hannu da ƙungiyar musamman ganin cewa manufofin su da tsare tsaren su yayi dai dana Dikko Raɗɗa.
Da yake jawabi, Babban direktan yaƙin nemnan zaben jam’iyyar APC a Katsina, Arc. Ahmad Dangiwa wanda ya wakilci Dikko Radda, ya nuna alfahrin shi bisa manfofin kungiyar.
Kazalika ya yaba da tsare-tsaren kungiwar wanda acewar shi yasha bambam dana sauran kungiyoyin dake bada gudummuwar.
Arc. Dangiwa yace shima Dr. Dikko Radda ya fiddo da tsare-tsaren da dabarun da zai tallafa ma matasa domin su dogara da kansu.
Yayi kira ga mata da su zabi jam’iyyar APC wanda acewar shi itace kadai mafita ga ‘yan najeriya.
Daga karshe ya godema kungiyar bisa gudummuwar da take ba jam’iyyar APC, sannan ya roki matan da s**a amfana da tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar da ya kamata.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Katsina
Katsina
Katsina
Katsina State Gubernatorial Flag-bearer Social Democratic Party (SDP) for the 2023 Election
Shinkafi B
Katsina
Dr. Mustapha Muhammad Inuwa is the leader with Qualities to make Katsina State a new world in 2023. A leader that is: 1. Educated 2. Honest 3. A leader with Visions and Missions 4....
Katsina
YADA MANUFAR SURAJO AMINU DAMA AIYUKAN ALKHAIRIN SA SHINE AIKINMU
Katsina
Dikko Radda was born on September 10th, 1969, in Hayingada–Dutsinma Local Government, Katsina State,