Miftahul Jannah
Miftahul Jannah: it's a names of prophet Muhammad S A W. Miftah means Key And Jannah Means Paradise. This means Prophet Muhammad S A W.
he is the key � of paradise. No body will enter before him S A w. Please follow this page.��� Thank you!
YAU NE ZAGAYOWAR RANAR YQKIN BADAR
A Rana Mai K**ar Ta Yau 17 aG Watan RAMADAN Aka Gwabza Yakin Badar, Babban Yakin Tarihi Na Duniya Wanda Ba'a Taba Yin Irinsa Ba, Inda Musulmai (313) S**a Gwabza Da Kafirai (1000,) Kuma ALLAH Ya ba Musulmai Nasara S**a Kashe Kafirai (70) S**a K**a Fursunonin Yaki (70.)
Duk Mai Fatan ALLAH Ya Daukaka Musulunci Akan Kafirci Kar Ya Wuce Bai Yi Sharing Ba....
Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! Isah Liman, Salisu Haruna, Danbau Musa, Adamu Muhammed Muhammed, Umar Mohammed, Abdulkadir Abdullahi
CIKIN BAYANAN IBNU TAIMIYAH GAME DA NEMAN TAIMAKO WAJEN MANZON ALLAH (S.A.W) KO WALIYAI YAYIN ZIYARAR KABARINSU.
Malamin yace:
Wasu mutane sun zo Raudar MANZON ALLAH (Sallallahu Alaihi Wassallam), sai s**a bukaci wani abu, sai aka biya musu bukatarsu nan take, Waliyai ma suna biyan bukatun mutane kuma bama haramta hakan (Iqtida'as Siratal Mustaqim shafi na 373).
Sheikh Ahmad Ibnu Taymiyah yace:
Ibn Musayab yana jiyo kiran Sallah daga cikin Raudar ANNABI (S.A.W), ko kuma amsawar Sallama daga Kabarin Waliyai, hakan gaskiya ne kuma munyi imani da shi (Iqtida'as Siratal Mustaqim shafi na 373).
Ya kuma cewa
Wani mutum ya zo ga raudar ANNABI (Sallallahu Alaihi Wassallam) sai ya roki abinci daga ANNABI (Sallallahu Alaihi Wassallam), sannan ya zauna, bayan wani lokaci sai ga wasu daga zuriyar Banu Hashim (Iyalan gidan ANNABI Sallallahu Alalihi Wassallam) s**a fito zuwa gareshi, tare da su akwai faranti na abinci sai s**a ce "ANNABI (Sallallahu Alaihi Wassallam) shi ya aiko mu da wannan abincin tare da sako cewa "Kaci kuma ka tafi, domin duk wanda ke kaunarmu to baya yin irin wannan roko "(Iqtida'as Siratal Mustaqim shafi na 290).
To kaga shi wancan mai kafafa da fariyar karatun da yake ikirarin ya karanta from cover to cover inaga karatun Jarida yake ma litattafan.
ALLAH YA KYAUTA.
ALHAMDULILLAH.
Allah ya muku lafiya Ameen
Hotunan Tafseer na 12/ga watan Ramadan 1445 wanda sheikh Muhammad Arabi Abulfathi ya ke gabatarwa a Masallacin Madinatu sheikh Ahmad Abulfathi.
Allah ya ƙarawa malam lfy Ameen
Yau Insha Allah MAULANA zai ciga da gabatar da tafsir
Prof. Ibrahim Maqari نتمّنا لكم التوفيق والنجاح حبيبي 🥰
*Yarjejeniyar: Dinke baraka tsakanin mazhabobin Musulunci..*
*Doka ta daya:*
"Musulmai al'umma ce guda daya, suna bauta wa Ubangiji daya, suna kuma karanta littafi daya, suna kuma bin Annabi daya, a kuma duk inda suke alkiblarsu daya ce, lallai Allah ya girmama su da sunan Musulunci, a wani bayani da yake a bayyane tamkar bayyanar rana, bai kamata a sauya shi da waninsa ba, bayan Allah ya zaba mana shi: (Shi ne ya sanya maku suna Musulmai), saboda haka, babu bukatar kowane irin suna, ko sifa da s**a yi kutse, wadanda suke rarraba kawuna ba sa hadawa, suke kuma nesanta al'umma da juna, ba sa kusanto da su.. Banda wadanda suke karfafa da bayyana manhaji, masu karfafa ayyukan Musulunci, su ma din, da sharadin kada su zama an canja sunan Musulunci da su, ko su zama suna gasa da sunan da Allah ya kira mu da shi, kaman yada su a farfajiyar Musulunci, don su kawar da sunan da ya hade mu gaba daya, musamman abubuwan da batattun jam'iyyun da s**a kaurace wa hadin-kan al'umma, da wasu 'yan tsirarun sunaye da wasu tsirarun batattu suke sifantawa".
*Taron Makka 2024, a gefen dakin Allah mai alfarma, karkashin kungiyar رابطة العالم الإسلامي*
Alhamdulillah da wannan Ni'ima ƴar Maulan mu ke nan,Sayyida Hafsat Sharif Sale.
RAMADAN TAFSEER RANA Ta 11
Allah ya ƙarawa Sayyidina Lafiya Ameen. Allah ya kara ɗaukaka Ameen
MALAMI CIKIN JERIN MANYAN MALAMAN DUNIYA.
Sheikh Prof. Ibrahim Maqari (H), ALLAH yasa ayi taro lafiya, a kammala lafiya.
Milyoyin zukata na kewarka.
ALLAH YA DAWO MANA DA KU LAFIYA. Ameen.
YADDA AL-QIYAMA ZATA WAKANA
Mihimman Al'amura guda (17)...
Annabin mu (ﷺ) yace idan Aka busa ƙahon farko mutuwa za'ayi yayinda IS'RAFIL yabusa ƙaho na farko duk halittun cikin sammai da ƙassai gabakiɗaya zasu mutu
Saidai waɗanda Allah ya so
'Sune matan aljannah da kananan yara na cikin aljannah sune kaɗai bazasu mutuba
Sa'annan za'a sake busa ƙaho na biyu Alokacin ne kowa za'a tadashi daga kabarinsa Alkiyama ta tsaya, Allah ya cika Alƙawarinsa
Tsakanin busa ƙahon farko da busa na biyu mafi rinjaye shekara 40 ne
1. Halittar Wanda ƙasa zata fara tsagewa ya fito Na farkon tashi shine sayyadina Rasulullahi Annabi Muhammadu (ﷺ)
2. Acikin mala'iku wanda za'a fara tashinsa shine israfil saboda Aikinda zeyi (busa na biyu)
3. Farkon tashi Acikin dabobi itace Braƙa domin Annabi (ﷺ) ita zaihau zuwa filin mahashar
4. Farkon wanda za'a fara saka masa kaya Ranar alkiyama shine Annabi Ibrahim
Saboda kowa da tsiraici zai tashi Annabi Muhammadu (ﷺ) shine kadai zai tashi da suturarsa cikakkiya
5. Wanda za'a fara sakawa rigar yan wuta Shine iblisu (Sheɗan)
6. Farkon wanda za'a fara yimasa hisabi shine Annabi Nuhu (A.S)
7. Abinda za'a fara Aunawa Adaura a sikeli dagacikin Aikin mutum shine kyakkyawar dabi'a
8. Farkon abinda za'a fara yi wa ɗaa Namiji hisabi Akansa shine sallahn shi
9. Farkon Abinda za'a fara yiwa ya'ya mata hisabi Akansa shine sallah Da haqqoqin mazajensu
10. Farkon hukuncinda za'a farayi shine hukunci Akan zubarda jini
shine Mafi munin hukunci don Allah yana hushi da masu zubarda jini za'ayi musu hukunci da tsanani
11. Wanda zai fara karɓar takardar sakamakonsa da Hannun dama shine Sayyidna Umar bn Alkattab (R.A)
Acikin Alami babu wanda zai fara samun littafin sakamako tsakanin Annabawa da mutane idan ba sayyidna umar ba
Kuma shine farkon wanda zai fara musafaha da Allah, Zai ba zatin Allah hannu,
______________
Alokacinda Sayyidna umar zai shiga Aljannah za'ayi tambaya Sayyidna ABUBAKAR yana ina? Sai mala'iku s**e
KALLON FINAFINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS). A CIKIN WATAN RAMADAN: Ku Nuna Mana Tsantsa Kishin da kuke yiwa Addinin musulunci wajen yaɗa wannan Saƙo ga sauran Al'ummar Musulmi domin Su Amfana
FINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS). A CIKIN WATAN RAMADAN.
Idan ka Karanta ka Turawa Sauran Ƴan Uwa Domin Su Amfana.
Kwai wasu muta ne, Suna Bacci amma Mala'iku suna rubuta musu ZUNUBI.
Suna Addu'a Mala'iku na rubuta musu ZUNUBI.
Suna Cin abinci Mala'iku na rubuta musu ZUNUBI.
Suna Tafiya Mala'iku na rubuta musu ZUNUBI.
Suna Kwance Mala'iku na rubuta musu ZUNUBI.
BLue FiLms Fina-finai ne da Wasu Tsageru Daga Cikin Yahudawa Suke Shiryarwa Wanda Yana da ILLa Sosai.
Domin Yanzu Anyi IttiQakin Cewa Ba Abin da Yake Saurin Rufta Mutum Zuwa Zinace-zinace K**ar Shi KaLLon BLue FiLms Ɗin Wanda Zamani Yazo da shi, Ba Ga Namiji ba, Ba Kuma Ga Mace ba.
Babban Abin Takaici Yanzu Yan Mata Sunfi Kowa Qwarewa Wajen Iya KaLLon Wnnn LaLaci na BLue FiLms.
HUKUNCIN SA:
KaLLon Tsaraici Haramun Neh a Shari'ar MusuLunci in Banda Na Matarka Ko Na Mijin ki, BaLLantana Kuma KaLLon Saduwa Tsakanin Mazinata, Wnnn Abune Mai MatuQar Muni Sosai.
Allah Yana Cewa:
"Ka Gayawa Muminai Maza su Rintse Idanuwansu Daga KaLLon Haram Kuma Su Kiyaye Daga Yin Zina".
'Yan Uwa Mu Kiyaye, Duk Wanda Yake KaLLon Irin Waɗannan Abubuwan to LaLLai Yayiwa ALLAH Tawaye.
A Wani Gurin ALLAH Yana Cewa:
"Kada Ku Kusanci Zina hakika ita Zina ALfasha Ce Kuma Mummunar Hanya ce".
Kunga Saboda HaLakan da Take Cikin Zina, Sai ALLAH Yace Kada Mu Kusanceta, shi Kuwa Irin Wnnn KaLLon Yakan Sanya Masu Yinsa su Afka Cikin Zina Kai Tsaye.
Manzon Allah (S.A.W) Yana Cewa:
" ALLAH ya Tsinewa Mai kallon Tsaraici da Kuma Wanda Ake KaLLon Tsaraicin nasa".
Daga Qarshe Ina Qara Jawo HankaLin Masu Yi su Tuba su Daina.....!!!
Don ALLAH Daure ka Rubuta Ameen Bamusan tawa Za'a Karɓa Ba...
Sannan KaLLon Fina-finan Batsa Yana Kai Mutum Zuwa ga Aikata Mummunar Ɗabi'ar Nan ta Istim'na'i Wacce Itama Tana da iLLoLi Ga Lafiya.
Ya ALLAH Ka Tsarkake
ALLAH YA KARAWA MALAM MU LAFIYA AMEEN. ALLAH YA KARBI AIKIN MU BAKI DAYA AMEEN
Alhamdulillah anga jaririn wata a Saudiya Gobe ce zata zama daya ga watan Ramada.
Allah ya karbi ibadin mu Ameen 🥰
HIMMA BATA GA RAGO.
Wannan shi ne Alhaji Bala Wunty, wanda ya dauki nauyin ginin Katafariyar Masallacin Maulana Sheikh Dahiru Bauchi Islamic Center.
SHIN WANNE ADDU'A DA FATAN ALKAIRI ZA KU YI MASA?
Watan rahama ya riske mu Alhamdulillah
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Amieenu Musa Maigatari, Laouali Maman
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Brenya Abdul-Rauf, Auwalu Lado Doka, Naziru Rilwanu, Haruna A Abubakar Glm
Insha Allahu Za’a Bude Masallacin Maulana Sheikh a Ranan Juma’a 08/03/2024 a Bauchi
Sheikh yana Gayyatan Yan Uwa Musulmi , Allah ya bayar da Ikon Halarta. Amin
Hukuncin karanta Basmala a sallah
SADAUKARWA: Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Nigeria, M***i Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Alhussaini (R.T.A) ya bayar da tallafin Naira dubu Hamsin-Hamsin ga marasa lafiyan da Harin Bom na Soji ya rutsa da su a garin tudun Mauludi
ALLAH YA KARBA DAGA GARESHI BISA WANNAN HIDIMA MAI GIRMA.
Tijjaniya: Ba ai Boko Haram da ita ba
Tijjaniya: Ba ai mai tatsene da ita ba
Tijjaniya: Ɗariƙa ce mai san zaman lafiya
Tajjaniya: Ɗariƙa ce Mai Son Allah da Maonzan sa Sayyiduna Rasulullah.
Tijjaniya: Ɗariƙa mafi yawan biya a Afrika.
Ƴan Tijjaniya ba sacewa Annabi mutum kamar kowa!
Ƴan Tijjaniya: Bas**e iyayen Annabi suna huta ba!
Ƴan tijjaniya: kullum ambaton Allah shi ne a zukatan su.
Kana baƙin ciki da kiran Allah
Kana baƙin da yabom manzan Allah
Kana baƙin cikin daga ganin mabiya Shehu Ahmadu Tijjani da Barhama inyass.
Kai cho da zuciyar da ba Allah a cikin face san zuciya da nuna iyawa.
Ya Allah munayi dan kai ne, ya Allah muna tawassili da kyawawan sunayen ka tsarkaka ya Allah muna fuskantar Annabin rahama da kai, ya Annabin rahama mu muna fuskantar Allah da kai. Ya Allah muna masu tawassili da salinhan bayin ka da Sabban Manzon ka ya Allah ka rusa duk mai san rusa Ɗariƙar Tijjaniya ya Allah ka yaƙe su da dukiyar su da lafiya da ilimi su ya Allah. Allahuma Ameeen
MAULANA SHEIKH SHARIF IBRAHIM SALEH ALHUSSAINI RTA SHUGABAN MAJALISAR MALLAMAI TA AFURKA
Manyan Mallamai na kasashen Afurka ne s**a hallara a kasar Morocco
Mu'assata ta shugaban kasar MUHAMMAD VI ta shirya taron karawa juna sani, Maqalar taron ya maida hankali ne akan raya thaqafar Addinin Musulunci
Imam Abba Saleh Ibrahim Saleh shi ya wakilci Maulana Sharif Saleh CON, Imam, babban limamin Masallacin Jumuah na Zawiyar Sharif Ibrahim Saleh dake Maiduguri,jihar Borno, Nigeria.
Daga cikin wadanda s**a halarta sun hada da;
*Sheikh Ali Sheikh Abulfathi
*Sheikh Ibrahim Makari
*Sheikh Bashir Sheikh Dahir
Da wasunsu
Bayan haka Wasu daga cikin dalibai yan Nigeria sun ziyarci Imam a masaukinsa
ALLAHU AKBAR: Ziyara kenan da Sheikh Imam Nazifi Alkarmawy (H) ya kai ga babban Malamin Addinin Musulunci na Duniya, Maulanmu Sheikh Shariff Ibrahim Saleh Al-Hussaini (R.T.A), tare da rero kasidar da ya rubuta domin wannan ziyara mai girma a gareshi.
ALLAH YA ALBARKACEMU, ALBARKAR WANNAN SHARIFI JIKAN MANZON ALLAH (S.A.W).
WANDA DUK YA CIRE SUFAYE A CIKIN AHLI SUNNAH, BAI KASANCE MASANI BA.
Ahli Sunnah suna da Makarantu ta fuskoki mabambanta, misali:-
• Ta fuskar ilmin tauhidi akwai :Asha'ira, Maturidiyya da sauransu.
• Ta fuskar ilmin Fikihu akwai: Malikiyya, Hambaliya, Shafi'iyya hanafiyya da sauransu.
• Ta Fuskar Ilmin Hadisi akwai Bukhari, Muslim, Abu Dawda, Tirmizi, Nasa'i Ibnu Majah da sauransu.
• Ta fuskar Ilmin Kira'a Akwai: Hafs, Warsh, Nafi, da sauransu.
• Ta fuskar abinda ya shafi Tazkiya (Gyaran zuciya) haka zalika Ahli- Sunnah na da makarantu Irinsu Kadiriyya, Tijjaniyya, Shazaliya, da sauransu.
Amma dayawa a yau akan ha'inci mabiya, ta hanyar kokarin nesanta makarantun gyaran zuciya na tasawwuf da matafiya ta Ahli Sunnah, alhali idan kabi tarihi na ilmi, zaka samu hatta manyan jagororin Wahabiyawan yau suna alakanta kawunansu zuwa ga makarantun Tazkiyya na Ahli Sunnah, kamar dai Sheikh Ahmadu Ibnu Taymiyyah da ya kasance Bakadire.
SABODA HAKA YA KYAUTU AKE AJE ABUBUWA DAGA MAHALLANSU DAGA BARIN JIRKITAWA.
GWANAYE A CIKIN BAYARWA.
Tallafin kudade Naira Miliyan 100 ga Al'ummar Palasdine, daga Khalifa Sheikh Muhammadu Mahy Niasse.
Himma ta kare wajen bayin ALLAH, ALLAH ya karba daga gareshi, ya laddafawa Palasdinawa halin da suke ciki.
FITATTUN SUFAYE 001
• Suna: Sheikh Sheiriff Ibrahim Saleh Al-Hussaini (R.T.A).
• Matsayi: Shugaban Majalisar Koli ta Addinin Musulunci ta Jamhuriyar Nigeria.
• Shi mutum ne da ALLAH yayiwa dimbin falaloli da ba kasafai ake samun irinsa ba, ya kasance Jikan MANZON ALLAH (S.A.W), da ya nakalci ilmai kusan na dukkanin fannonin Addinin Musulunci, nakalta ta kwarewa da fasahar ban al-ajabi.
• Ya rubuta litattafai da basu gaza dubu guda ba, wanda cikinsu an wallafa sama da guda dari 4, inda kusan dayawa daga jami'oin dake kasashen Musulunci ke matukar fa'idantuwa da talifansa, haka zalika majalisan manyan Malaman Musulunci a fadin Duniya ke karantar da litattafansa, tare da amfanuwa da fatawoyinsa.
Yana da Almajirai kusan a ilahirin kasashen Musulmin Duniya, sannan abu ne mawuyaci wani ya iya haddade yawan Ferfesoshi, Daktoci cikin Almajiransa a fadin Duniya wadanda su ke amfanar da musulmi ta fuskoki mabambanta.
Ya kasance Sufi ne Mabiyin Makarantar Ahli-Sunnah na gyaran zuciya, wato Darikar Tijjaniyya, kuma ya kasance cikin Almajiran Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A).
ABIN DA YAFI SHAHARA DA SHI
Riko da Sunnonin MANZON ALLAH (S.A.W) aikace, da s**a gadar masa da dabi'un: Hakuri, Karamci, Kawaici, Yafiya, Zumunci, Amana, Gaskiya da sauransu.
ALLAH YA KARA MASA LAFIYA DA TSAWON KWANA ALBARKACIN MANZON ALLAH (S.A.W).
Fassara cikin harshen turanci.
Alhamdulillah
Wannan itace wasikar da maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh rta ya rubuta sannan ya aikota ga zawiyyarsa dake Maiduguri wadda aka karantata a wajen taron maulidin.
Allah ya kara masa lapiya da tsawon rai.
Ameen.
Maulana sheakh Sharif sale Shugaban masu fatawa na Najeriya... Allah ya kara lfy da nisan kwana Ameen.
Assalatu Wassalamu Alaika Ya Rasulillah
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Contact the business
Telephone
Address
MUNICIPAL
Maiduguri
Shi kanuri_1in-G. Ad3 kabila au t3lam done sha not3namah dinam na adinnawosom kuru ad3son sakkatay3
Bulumkutu Abuja, Abba Kagu MaRoute Street
Maiduguri, 600001
We provide genuine news about education, recruitments, and much more. like our page for everyday new
Maiduguri, NO23502MAIDUGURI,BORNOSTATE
Abadam Social Network is a new media platform which created to bring you an ubdate of day to day act
GRA
Maiduguri, 600233
The official page of the Nigerian Medical Association, Borno State Chapter. It is meant to foster unity; disseminate information; advocacy as well as a goldmine for knowle...
Maiduguri International Airport Road
Maiduguri
V. Special Assistant on Social Media to the Vice President elect Sen. Kashim Shettima.
Rail Way Terminus
Maiduguri
Music is an agreeable harmony for the honor of God and the permissible delights of the soul. 💖🙇
Maiduguri, 600243
At Northeast Punchline, we are mainly focused on stories, happenings and news in Northeast, Nigeria.