Muryar Arewa Muryar Yanci'

Muryar Arewa Muryar  Yanci'

Wannan Shafin Ambude Shine Domin Cigaban Al,ummar Arewa

Photos from Muryar Arewa Muryar  Yanci''s post 08/11/2023

Duk fa Wanda Yasan Bayyi Wannan Airdrop din ba ya daure yayi suna biya

Yanxu Nayi swapping Nawa zuwa Renec

Kuyi da sauri kafun su rufe,

Kayi downloading na carax wallet saii kaje kayi paste na wannan link din a Ciki bayan kayi creating na wallet,.

https://www.luckx.io/join/Yaro12

Babu wahala sai kayi KYC na Wallet Din Shima Ba Wahala.

Idan Kuma kayi propeacy Airdrop sai kayi amfani da wallet din.

Invition Code Yaro12

Allah Yaa Bamu Saa.

Photos from Muryar Arewa Muryar  Yanci''s post 22/09/2020

KISAN GILLAR 'YAN BINDIGA: Sama Da Mata Dubu 22 Sun Zama Zaurawa, Kananan Yara A Kalla Dubu 44 Sun Zama Marayu A Jihar Zamfara

Daga Comr Abba Sani Pantami

Kimanin zaurawa dubu 22 aka samu a jihar Zamfara da ke Najeriya sakamakon kisan gillar da ‘yan bindiga s**a yi wa mazajensu, lamarin da ya mayar da kananan yara akalla dubu 44 marayu kamar yadda Kungiyar Matasan Arewa ta AYF ta sanar.

Shugaban kungiyar na kasa Gambo Ibrahim Gujungu ya bayyana cewa, a cikin shekara takwas kacal aka samu wannan adadi mai tayar da hankali.

Kungiyar ta AYF ta kuma ce, ‘yan bindigan sun kashe maza magidanta akalla dubu 11 tsakanin wannan lokaci.

Gujungu ya bayyana kashe-kashen da ake fama da su a Zamfara da s**a hada da sace jama’a domin karbar kudin fansa da fyade da sace shanu da lalata kadarori a matsayin abin damuwa, yana mai cewa, a can baya, yankin arewa maso yammacin Najeriya ya kasance mai zaman lafiya.

Yana da wahala a yi kwana guda ba tare da an samu irin wannan aika-aikatar ba a yanzu” a cewar shugaban na AYF.

Kungiyar ta gargadi mummunan abin da ka iya kasance nan gaba muddin aka ci gaba da zura ido ba tare da daukar matakin da ya dace ba kan wannan batu na kashe-kashe a Zamfara.

Photos from Muryar Arewa Muryar  Yanci''s post 22/09/2020

TURKASHI: Ana Bin Kowane Dan Najeriya Bashin N155,000. Inji hukumar kula da Bas**a ta kasa (DMO) ___________________________________________________

"Ofishin Kula da Bas**a na Kasa (DMO) ya ce yawan bas**an da ake bin Najeriya ya karu zuwa tiriliyan 31 a watan Yuni, 2020.

"Ofishin ya ce bas**an za su karu a bana saboda rancen da kasar ke nema daga kasashen duniya.

Bashin da aka karbo daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da sauransu ne s**a sa
yawan bashin karuwa zuwa Naira tiriliyan 31.

Hukumar kula da dukiyar masu taurine bashi (AMCON) ta kwace bashin sama da miliyan N600na Hydro Hotels over N600m debt

Ana ganin yawan bashin zai karu a bana saboda rancen da za a karbo daga hukumomin kasashen duniya.

-Buhari:

Zuwa watan Maris 2020, bashin ya kai tiriliyan N28.6 wanda ya kunshi dukkannin bas**an Gwamnatin Tarayya, Jihohi da Birnin Tarayya.

A baya-bayan nan yawan bashin ya kai tiriliyan N31.009 ya kai Dala biliyan 85.897, yayin da tiriliyan N28.628 na watan Maris ya kai biliyan N79.303.

Dalilin karuwar:

"Bashin ya karu da tiriliyan N2.38 (Dala biliyan 6.59) a cikin wata uku.
Bas**an sun karu ne sakamakon karbo rancen Dala biliyan 3.36 daga Asusun Lamuni na Duniya (IMF) domin aiwatar da kasafin kudi; karin bas**an da aka karba a cikin gida domin samar da kudaden aiwatar da sabon kasafin 2020; takardun rance na Sukuk; da kuma takardun Promisory notes da aka bayar domin biyan hakkokin masu fitar da kaya zuwa kasashen waje.

Abubuwan da bas**an s**a kunsa:

Bas**an da aka karbo na tiriliyan N16.360 daga kasashen waje su ne kaso mafi tsoka (kashi 51.97%) na bashin da Najerya ta karbo.

An karbo bas**an ne daga IMF, Bankin Duniya, Bankin Raya Afirka (AfDB), Eurobonds da bas**an kasashen waje na Diaspora bonds.

Rance daga kasahen waje ya kai tiriliyan N3.948, kashi 12.54% na bashin da aka karbo daga hukumomin raya kasashe na Sin, Faransa, Japan, Indiya da Jamus.
Kashi na uku shi ne rancen kasuwancei na tiriliyan 11.168, kashi 35.48%. Wannan shi ne na biyu wurin yawa bayan wanda aka karbo daga hukumomin duniya da Eurobonds da kuma rancen Diaspora bonds.

Ci gaba da karuwar bashin:

Rancen da ake shirin karbowa daga Bankin Duniya da AfDB da Bankin Raya Kasashe na Musulunci (IsDB) domin aiwatar da kasafin 2020 zai sa bashin da ake bin kasar karuwa.

An ba wa hukumar kwastam ta kasa wani bangare na kudin domin zamanatar da ayyukanta a tashoshin jiragen ruwa da Dala tiriliyan 3.1.

Yawancin bas**an masu dogon zango ne da aka riga aka fara biya, sauran kuma sabbi ne da za a fara biya daga 2022.

Wa’adin kammala biyan bashin Sukuk da sauran rancen cikin gida shekara biyar zuwa bakwai ne.

-Bashin da ake binka:

Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta ce an yi tsare-tsare domin biyan bas**an. Kasafin kudin 2020 ya ware fiye da tiriliyan N3, kusan rubu’in kasafin domin biyan bas**a.

Idan aka raba bashin tiriliyan 31 a tsakanin ’yan Najeriya da yawansu ya kai miliyan N200, to ana bin kowane dan kasar bashin N155,000.

Bashin zai kara yawa idan aka karbo rancen Bankin Duniya da AfDB da IsDB na gaba a wannan shekarar.

Me zakuce?

Photos from Muryar Arewa Muryar  Yanci''s post 20/02/2020

Wai Sai Yaushe Gwamnatin Najeriya Zata Dauki Mataki Akan Rayukan Mutanen Arewa Da Dukiyoyinsu

Kullum Yan,ta,adda Na Kai Hare Hare Tsakani Katsina Neja Zamfara Kaduna Borno Da Ssuran Yankunan Arewa

Amma Gwamnati Taqi Daukar Matakin Kare Rayukan Mutane Da Dukiyoyinsu Wannan Wace Irin Gwamnatice Wadda Bata Damu D Rayuwar Talakawantaba

Allah Yabamu Zaman Lafiya Yayi Muna Maganin Azzaluman Shugabanni Ameen

19/02/2020

Assalamu Alaikum Al,ummar Arewa Muna Cikin Baqin Ciki Halinda Yankinmu Yake Ciki Na Rashi Tsaro Muna Barar Addu,a Ga Musulmin Duniya Su
Tayamu
Addu,a Allah Yabamu Zama Lafiya Mai Dorewa Ammen

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Sokoto