Kowa Naka Printers

Kowa Naka Printers

Welcome to KOWA NAKA PRINTERS! We provide passport photographs, business card printing,posters,photo

05/01/2022

Art work @
Kowa Naka Printers

04/09/2021

HAKKIN MIJI AKAN MATA DA HAKKIN MATA AKAN MIJI

AN kasa hakkokin maaurata zuwa kashi uku
na daya hakkin miji akan mata
na biyu hakkin mata akan miji
na uku hakkin tarayya tsakanin maaurata
Hakkin mata akan miji sune:



1.ciyarwa gwargwadon iko.

2.tufatarwa daidai iko.

3.shayarwa.

4.kayan kwalliya.

5.kayan tsafta.

6.gurin kwana.

7.kula da lafiya.

8.hakkin saduwa.

9.ilmantarwa.

10.girmamawa.

11.mutuntawa.

12.tausasawa.

13.yabawa ga abinci ko kwalliya ko tsafta.

14.nuna damuwa da ita.

15.sakar mata fuska da murmushi.

16.gaya mata kalmomi masu dadi na yabo.

17.zama hira da tattaunawa da ita.

18.kiranta da suna mai dadi.

19.yawan yi mata kyautar ba zato ba tsammani.

20.fita unguwa ko taro ko ko tafiya da ita.

21.taimaka mata aikin gida ko dan kadan.

22.bata damar zabin abincin gida a wasu lokuta.

23.bata damar zabin tufafin da zata sauya.

24.mutunta iyayenta da danginta.

25.A bata hakuri idan anyi mata ba dai dai ba.

26.A yaba mata idan tayi daidai.

27. kada a zageta ko a muzantata a gaban yayanta.

28.banda duka.

29.banda zagi.

30.banda saurin fushi.

31.ka zama miji mai tsafta.

32.ka zama miji mai kula da goge baki.

33.miji mai kwalliya.

34.miji bamai almubazzaranci ba.

35.miji bamai mai kwauro ba.

36.miji bamai shan taba ba.

37.miji bamai mai shan giya ba.

38.miji bamai yawon dare ba.

39.miji bamai neman mata ba.

40 Kada ka zama miji mai hira da wasu mata a gaban iyalansa.

41.miji mai yawan fada.

42.kada ka zama miji mai kauracewa shimfidar iyali.

43.kada ka zama miji mai nuna rashin damuwa da halin da iyalansa suke ciki.

44.kada ka zama miji mai tsananin kishi.

45.kada ka zama miji mai yawan zagi.

46.ka nuna wa matarka cewa gamsu da yanayinta.

47.ka bata dama ta fadi raayinta.

48.kayi shawara da ita akan harkokin gida da wajen cikinta.

49.ka dinga sumbatar ta daga lokaci zuwa lokaci.

50.yin wanka tare a wasu lokuta.

51.rera mata waka da kirari.

52.yin wasa da guje-guje.

53.kada ya zama miji mai zargi.

54.kada miji ya zama mai mugunta.

55.kada miji ya zama mai kushe.

56.kada miji ya zama mai bakin ciki da abinda iyalansa suke dashi.

57.kada miji ya zama mai ragwanci.

58.mijin ya zama mai lafiya wajen biyan bukatar aure.

59.miji ya zama mai kaunar yayansa.

60.miji ya zama mai girmama kawaye da aminan matarsa.

Na biyu hakkin miji akan mata sune:

1.Ta rike masa amana.

2. Tayi masa biyayya akan duk abinda ba sabon Allah bane.

3. Ta kula da dukiyarsa.

4. Ta kula da Sallah akan lokaci. Da addua zaman lafiya.

5. TA girmama shi a gaban idansa.

6. TA kare girmansa a bayan idansa.

7. Ta so abinda yake so, koda ba abin so bane a wajenta.

8. Ta ki abinda yake ki, koda ba abin ki bane awajenta.

9. Ta damu da duk abin da ya damu dashi.

10. Ta kau da kai daga abinda ya kauda kai, daga gareshi.

11.Tayi fushi , da dukkan abinda yayi fushi da shi.

12.Ta yarda da duk abinda ya yarda da shi.

13.Idan ya bata kadan taga yawansa.

14.Idan ya bata da yawa tayi godiya.

15.Ta farka daga bacci kafin ya farka.

16.Sai yayi bacci kafin tayi.

17.Tayi hakuri idan yayi fushi.

18 Tayi taushi idan yayi tsauri.

19.Ta lallashe shi idan ya hasala.

20.kada ta nuna raki a gabansa.

21.kada tayi kuka alhali yana dariya.

22.kada tayi dariya alhali yana kuka.

23.kada ta tsaya kai da fata sai yayi mata wani abu.

24.kada ta matsa masa da bukatu.

25.kada ta dinka ganinsa kamar yaran gida.

26.kada ta dinka yi masa gyara barkatai.

27.kada ta dinka kushe tsarinsa.

28.Ki dinka zuga shi a gaban danginta.

29.Ta dinka girmama shi a wajen kawayenta.

30.Ta dinka nuna masa abu mai kyau.

31.Ta dinka boye abu mummuna.

32.Idan ya kawo wata damuwa gareta, ta taimake shi ya warware ta.

33.Idan ya nuna baya son wani abu ta daina.

34.Ta kwantar masa da hankali a lokacin damuwa.

35.Ta sassauta masa idan yana cikin bakin ciki.

36.Ta tsaya da jinyar sa idan yana rashin lafiya.

37.Ta taimake shi lokacin da yake neman taimako.

38.Idan yana cikin kunci ta sassauta bukatu.

39.Tayi masa rakiya lokacin fita ta tareshi a lokacin da ya dawo.

40.Ta tausasa harshe a lokacin da take magana dashi.

41.Ta zama mai tsaftar gida iya iyawarta.

42.Ta tsara dakinta sosai yadda zai birge.

43.Tayi masa bankwana a lokacin balaguro.

44.Tayi ado karshen iyawarta.

45.Ta bayyana halaye masu kyau.

46.Ishara ta ishi mai hankali ta kula wannan sosai.

47.Ta bayyana kanta a matsayin mace.

48.Ta iya murmushi da lafazi mai kwantar da rai.

49.Ta cika zuciyarsa da sonta idansa da kwalliyarta.

50.Tayi kokarin jan hankalinsa da abin da yake so.

51.Ta mayar masa da kyakkyawa idan yay i mata mummuna.

52.Ta yafe masa idan ya munana mata.

53.Ta karbi uzurinsa.

54.kada tayi sallar nafila sai ta sanar masa.

55.kada ta dau azumi sai ya sani.

56.kada ta fita daga gida sai ya sani.

57.Ta iya girki kala-kala.

58.kazantar jiki ta dade tana kashe aure a kula.

59.kada ta shigar da wani gidansa sai da izni.

60.kada ta nemi saki ko rabuwa haka kawai
Na uku shine hakkokin tarayya tsakanin maaurata.

1 Nunawa juna kauna da soyayya.

2 Tarayya da juna cikin abinda ya sami dayan ko na farin ciki ko bakin ciki.

3 kowa ya dinka yiwa abokin zaman sa kwalliya da tsafta.

4 kowa tsakanin maaurata ya zama mai kishin da uwansa.

5 a sami amincewa juna.

6 kowa ya bawa kowa daga cikin hakkin jin dadi da juna ta hanyar da shari'a ta amince.

7 kyakyawan zamantakewa tsakanin juna.

8 hakuri da juna9 Amincewa juna.

9 Farantawa juna rai.

10 su zama kamar abokan juna da yin shawara da juna.

11 Nuna juna kauna daga bangaran kowa daga cikin su.

12 Girmama iyayan da yan uwan juna.

13 Taimakon juna a lokacin da wani daga ciki ya gamu da jarrabawa.

14 Wani su dinka tona asirin juna a waje.

15 Banda cin Amanar juna.

16 kada su dinka bayyana wani mu'amalar su ta auratayya.

17 Akwai gado a tsakanin su idan daya daga cikin su ya fara rasuwa.
Wannan sako ne ga dukkan maaurata su zauna suyi nazarin wannan sako kowa yaga abinda yake yi a ciki, domin mu gudu tare mu tsira tare
Allah ya bamu ikon kiyaye hakkin juna.
YA cika zukatan mu da kauna da soyayya da girmamawa tsakanin mu da iyalinmu.

02/01/2021

May The New year Be a Blissful one!

04/09/2020

انا لله وانا اليه راجعون!
The inevitable is uncompassionate! Four Family members of Malanmadori lost in an auto-crash this evening!
O Allah! Grant them eternal rest in Jannah! You are the Forgiver of all! Have mercy upon these gentle souls,and grant their Family the fortitude to bear this irreparable loss! YAA RABBAL AALAMIIN!!!😭😭😭 ,Fatima, Farida,and Hanan. Our heartfelt condolences to the Family.💔

Photos from Kowa Naka Printers's post 17/04/2020

Allah Ka Kawo mana dauki...

03/01/2020

*GORON JUMU'AH:*

```HADITHI YA TABBATA DAGA ANNABI(صل الله عليه و سلم) YAKE CEWA```: _*KU YAWAITA SALATI GARE NI A RANAR JUMU'AH,DUK WANDA YAYI MIN SALATI DAYA(1) ALLAH ZAI YI MASA SALATI GOMA(10)*_
SANNAN A WANI HADITHIN ANNABI(صل الله عليه و سلم) YAYI UMARNI DA KARATUN _SUURATUL KAHFI_ A KOWACCE JUMU'AH KAFIN FADUWAR RANADOMIN TANA ZAMOWA GARKUWA GA MUTUM A RANAR KIYAMA.
*اسأل الله لى و لكم خير هذه اليل و ما بعدها.*

Photos from Kowa Naka Printers's post 08/11/2019

OUR BRANDS...

05/11/2019

WE WELCOME OUR ESTEEMED CUSTOMERS TO OUR FACEBOOK PLATFORM!!!

Telephone

Website

Opening Hours

Monday 09:00 - 21:00
Tuesday 09:00 - 21:00
Wednesday 09:00 - 21:00
Thursday 09:00 - 21:00
Friday 09:00 - 21:00
Saturday 09:00 - 21:00
Sunday 09:00 - 21:00