Daily News Hausa 24

Daily News Hausa 24

Domin samun sahihai kuma ingantattun labarai daga kowanne sassa na Nigeria dama ketare

Photos from Daily News Hausa 24's post 22/12/2023

Kalli yadda mutane ke rayuwarsu a cikin ɓaraguzan gidajensu sak**akon rashin inda za su samu mafaka a Gaza duk da cewa Israil na cigaba da luguden wuta a kasar ta Palestine

Photos from Daily News Hausa 24's post 22/12/2023

Sabuwar Matashiyar Yar Wasan Hausan Kannywood kenan. Mai Suna Zahra Aliyu Dake Kokarin Fitowa acikin wani sabun Series.

Wanda ta Fito a Tauraruwar Film din Shin Kuna Ganin Zata iya Shiga jerin Jarumai Mata wadanda ake yayi?

22/12/2023

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Raji'un: Allah Ya yi wa ladanin masallacin Sultan Bello Mosque Kaduna rasuwa

Innaa Lillahi wa Innaa Ilaihi Rajiun
Allah Ya yi wa Ahmad Wazan (Naibin Ladanin Masallacin Sultan Bello Kaduna) Rasuwa a jiya cikin dare, za'a yi Jana'izar sa anjima a Masallacin Sultan Bello Kaduna bayan Sallar Juma'ah,,

Muna Rokon Allah ya karbi dukkan aiyukansa na hidima da Addinin Musulunci ya gafarta masa yasa Aljanna ce makomarsa da mu baki

22/12/2023

Tunde Sabiu ne ya ce wa Emefiele da ya sake fasalin kudin Naira; Hukumar CBN Ba Ta Da Hannu - Bincike Na Musamman

Ku tuna cewar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya bayar da kyautar Naira biliyan 61.5 kan buga sabbin takardun kudi ga wani kamfanin kasar Birtaniya, De La Rue, wanda hakan ya saba wa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari na a ba da aikin zuwa wani kamfani na gida.

Rahoto ya nuna cewa hukumar babban bankin Najeriya CBN ba ta da hannu a wannan shawarar na sake fasalin sabbin takardun kudi, inda ya ce hadimin Buhari, Tunde Sabiu ne ya ba tsohon gwamnan CBN shawarar a ziyarar da ya kai fadar shugaban kasa a Villa. a watan Satumba 2022

22/12/2023

Mutumin da aka daure shekaru 48 ya shaki iskar 'yanci bayan gano cewa bashi da laifi.

Wani mutumi da aka daure bisa kuskure ya shaki iskar yanci bayan shekaru 48 a magark**a.

An daure Glynn Simmons mai shekaru 71 a yanzu tun yana matashi dan shekaru 23.

Sai a shekarar nan ne aka gano lallai ba shi da hannu a laifin da aka hukunta shi a kai.

Photos from Daily News Hausa 24's post 22/12/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta kori jami’an da aka k**a kan na’urar ɗaukar hoto suna tambayar kuɗi daga wata ‘yar kasar Holland mai yawon bude ido.

Rahoton JaridarArewa

22/12/2023

Barkanmu da Safiyar Ranar Juma'a
22\12\2023 yanzu karfe 5:47am daga nan cikin birnin Kano Nigeria

Karfe nawa agogon garinku a daidai lokacin da kukaga wannan rubutun?

21/12/2023

Yan sanda sun fara kamen masu boye lambobin motarsu a Nasarawa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Shehu Umar Nadada ne ya bayar da wannan umarni a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Ramhan Nansel ya fitar kuma ya rabawa manema labarai.

21/12/2023

Keyamo ya nada sababbin daractoci na hukumar sufurin jiragen sama

Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da gwamnatin tarayya ta kori dukkan daraktocin sufurin jiragen sama

Ana saran daraktocin da aka nada zasu kawo kwarewar da suke da ita a ma’aikatar

21/12/2023

Ka gayawa Tinubu gaskiyar abinda ke faruwa a Nigeria

A cewar Fayemi: “Na yi farin ciki da shugabanmu ya zo nan. Wannan ita ce jam’iyyar da bai k**ata ta zama ‘yar kallo ba wajen tsara manufofi.

21/12/2023

Shari'ar Kano:Kotu Ta Bayyana Cewar Daga Cikin Kararraki 9 Da NNPP Ta Shigar Guda Daya Kawai Zata Iya Saurare

21/12/2023

Kotun koli zata sanar da ranar yanke hukunci kan zaben gomnan jihar Kano bayan sauraron lauyoyin kowanne bangare da tayi a yau Alhamis

A yau Alhamis ne kwamitin alkalai mai mutane biyar karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro ya saurari lauyoyin da ke kan lamarin.

Photos from Daily News Hausa 24's post 21/12/2023

Wakilan jam'iyyar APC tsagin Gawuna dakuma na jam'iyyar NNPP tsagin Abba Kabir sun isa kotu.

Idan baku mantaba yaune kotun koli ta sanar zatayi zaman sauraron karar da jam'iyyar NNPP din ta shigar kan kalubalabtar hukuncin da kotunan baya s**ayi kan zaben na jihar kano, kotun zatayi wannan zama ne domin sauraron korafi daga kowanne bangare kafin daga baya ta sanar da ranar yanke hukunci

Wa kuke yiwa fatan nasara?

21/12/2023

Hankula sun tashi a garin Chibok yayin da mayakan Boko Haram s**a farmake su cikin dare.

Sun bankawa gidaje wuta tare da salwantar da rayuka da jikkata mutane da dama.

Rundunar 'yan sanda, sojoji da 'yan sa kai, sun yi musayar wuta yayin da s**a kai dauki.

21/12/2023

Barkanmu da Safiyar Ranar Alhamis
21\12\2023 yanzu karfe 5:45am daga nan cikin birnin Kano Nigeria

Karfe nawa agogon garinku a daidai lokacin da kukaga wannan rubutun?

20/12/2023

Yan Majalisun Jihar Ribas 24, Masu Biyayya Ga Wike, Sun Janye Sanarwar Zasu Tsige Gwamna Fubara

20/12/2023

Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacce aka fi sani da Shi'a, ta bukaci gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaba Joe Biden da sauran shugabannin kasashen duniya da su goyi bayan tsagaita bude wuta cikin gaggawa a rikicin da ke ci gaba da faruwa tsakanin Hamas da Isra'ila

20/12/2023

Cibiyar Justice on Religious and Ethnicity in Nigeria (CJREN) ta zargi gwamna Babagana Zulum na jihar Borno da cire Kiristocin jihar daga tallafin da gwamnatin tarayya ke baiwa ‘yan kasa da mazauna jihar

20/12/2023

Wani matashi mai shekaru 19 mai suna Mohammed Ibrahim, mazaunin Sabon-Layi da ke wajen birnin Bauchi a jihar Bauchi, ya daba wa budurwarsa mai suna Emmanuella Ande wuka har lahira bayan wani rikici da ya barke a tsakaninsu kan kudi naira 5,000.00.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa kafin faruwar lamarin, Mohammed ya sace kusan Naira 400,000 na mahaifinsa domin ya kashewa Emannuella, yar asalin jihar Filato, bayan sun shirya haduwa a Fatakwal, jihar Ribas

20/12/2023

A Qalla Manyan Sojin Qasar Najeriya Su 113 ne s**a aje aiki a yau. Hakan yazone Dai dai Lokacin da ake Qara Fuskantar Matsalar Tsaro a Qasar nan

20/12/2023

Zargin ya Biyo Bayan da Wasu Jigo a Jam'iyyar Hamayya keyi bisa cewa Gwamnatin Tasu tazo Karshe.

Daga Majiya Mai Tushe Ba iya wannan Ma'aikata ne ake zargin Muqarraban Gwamnatin Kano da Hafzi da wasu Abubuwan da Dama. Inda wasu Tuni Kwamashinan Yan Sanda na Jahar ya k**a.

Wannan Zargi na Waware wasu kadarorin Dai da Cefanar Dasu da ake zargin MD Na Radio Kano, yazo ne Qasa da Kwana 4 da ake fara tunanin Sauraron Qarar da Gwamnan ya shigar akan kujerar Gwamnan da akace bashine yaci zabe ba.

Me Zaku iya cewa?

20/12/2023

Mawakin Ya Bayyana Hakan ne. A Satin daya Gabata a Taron da Yayi Da Matasa Maza da Mata Yan Kannywood da Yan Social Media.

Bayan Cecekuce da ake kan lamarin Daukakar sa. Yace Tabbas Yan Media sun taka Rawar azo a Gani akan Lamarin Harkar Wakokinsa.

Har Gobe idan Dauda Adamu Abdullahi Rarara yasa Challenge anayi, Shin zaku iya yarda da Maganar da yafada

20/12/2023

Tsohon Shugaban Nijeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida, marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua sai Admiral Murtala Nyako a lokacin wani aikin Hajji.
Allah ya jikan Shehu, ya karawa IBN da Nyako lafiya.

Allah ya jikan magabatanmu, ya kyautata karshenmu.

~Dandalin Tarihin Magabata

Photos from Daily News Hausa 24's post 20/12/2023

An Samu wani Hadin Mota Yanzu Akan Titin Kura Local Government dake Kano wajen Kauyen Daka Tsalle.

Titin dai ana kiransa da Zaria Road, Ga wanda yasan motar nan Ana sanar da su Garzaya wajen, Mutum Biyu ne acikin

Photos from Daily News Hausa 24's post 20/12/2023

Wannan ita ce, gonar Daya daga cikin sahabin manzon Allah S. A. W Salmanul Faris. Dake birnin madina..| Allah ya karawa Annabi Daraja.

Allah ya Bawa Dukkan Musulmi Damar zuwa Ziyara

Photos from Daily News Hausa 24's post 20/12/2023

Mustapha Sani Abacha, Yaro Guda 1 Tilo da Aka Haifa a Villa. Shida Amaryar sa Safa Tijjani Usman. Wannan Shi ake kira Qwarya Tabi Qwarya.

Wane Fatan Kuke Musu?

20/12/2023

Mace Mai Yin Tik-tok Fasiƙâ Ce - Matashin Malamin Shi'a Shêikh Hussaini Muktar.

Ticktok igiyace daga cikin igiyoyin Sheɗan Amfaninsa kaɗan ne ga Mumini...

“Shehin malamin ya ƙara cewa; Haramun ne yin Tik-tok ga wanda bai da tabbacin cewa ba zai ga haramun ko sau ɗaya ba a cikinsa ba Wato idan mutum yasan cewa; idan ya bude zai ga wata mace tana rawa ko Kuma tasaka sutura mai jawo sha'awa kalas harammun ne ya ringa shigarsa sai dai idan yashiga ɗin zabi hanyar da bazai ga haramun ba wannan ya inganta gareshi

Bugu da ƙari matashin malamin ya ce Haramunne ace mace musulma tayi bidiyo tana murmushi da dariya da barkwanci da wasa da surutun banza a Tik-tok sabida Hakan kira ne ga babban saɓon ubangiji sannan idan mace musulna tasan wannan hukunci Kuma ta c igaba toh ita fasiƙace Mai bayyana sabon Allah.

Mé zakú cé?

20/12/2023

SARAUTAR SHAMAKI, A FADAR KANO A TAKAICE.

Daga Alh Nasiru Wada Khalil.
Nasiru Wada Khalil

A bisa tsari Shamaki shi ne Babba kuma shugaban duk wani bawan Sarki, Amfara Shamaki kiyasi (1899)Zamanin Sarkin Kano Dabo (Stilwell:30).

Gidan Sarautar Shamaki yana daga bangaren Arewa a cikin gidan Sarki.

Shi ne yake tsayawa a hannun damar Sarki idan ana tafiya a kan doki.

Sannan kuma a fada yana wajen zama a hannun dama kusa da Limamai kuma ko da ya tashi ko baya nan, wani baya zama a wurin k**ar yadda Nasiru Wada Khalil ya kawo a cikin littafinsa na Bayi a Gidan Dabo.

Ayyukan Shamaki suna da yawa matuka wadanda s**a kun shi lura da dukkanin Bayin Sarki da suke fada, tun daga kan Sarakunan kofa masinjoji, Leburori, gadina, masu shara, da sauransu.

Haka kuma shi ne mai kula da dawakan Sarki, da dukkan kayan dokunan.

Shi ne kuma mai nemawa Hakimai izinin ganin Sarki,
Sannan kuma duk matsalar da ta shafi kyauyuka shi ne mai shigar da ita gaban Sarki.

Chiroman Shamaki Kabiri Inuwa Dan Indo (2005) :
Ayyukan Shamaki sun hada da lura da kayan sarauta irin su wukar yanka takalmin gashin jimina tagwayen masu da sauransu a lokacin da sarauta ta fadi kafin a nada sabon Sarki.

HAKIMAN SHAMAKI;

(1)Chiroman Shamaki
(2)Babban Zagi
(3)Sarkin Dogari
(4)Majasiddi
(5)Madakin Shamaki
(6)Mak**an Shamaki
(7)Turakin Shamaki
(8)Jarman Shamaki
(9)Barden Shamaki
(10)Garkuwan Shamaki
(11)Malafa
(12)Sarkin Makera
(13)Barwan Shamaki
(14)Kenkedi
(15)Sarkin Hawa
(16)Sarkin Yakin Shamaki
(17)Jakadan Garko
(18)Sarkin Ruwa
(19)Sarkin Kofa
(20)Sarkin Busa
(21)Mai Dawakai
(22)Galadiman Fanisau
(23)Sarkin Mota
(24)Sarkin Kakaki
(25)San Kira
(26)Sarkin Kitso
(27)Magajin Banga
(28)Magajin Gwanso
(29)Galadiman Shamaki
(30)Sarkin gado
(31)Sarkin Kaji
(32)Shamakin Mai Babban Daki

Daga shafin Labbo Kundumm

20/12/2023

Barkanmu da Safiyar Ranar Laraba
20\12\2023 yanzu karfe 5:34am daga nan cikin birnin Kano Nigeria

Karfe nawa agogon garinku a daidai lokacin da kukaga wannan rubutun?

19/12/2023

Malaman addinin musulunci na son nasarar Gawuna a kotun ƙoli.

Malaman da s**a fito daga Tijjaniyya, Izala da Kadiriyya sun fito sun nuna goyon bayansu ga ɗan takarar na APC.

Sun buƙaci kotun ƙoli da ta tabbatar mutanen Kano sun samu adalci.

19/12/2023

Yanzu haka matemakiyar Gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe, tana halartar bikin bude taron kwanaki biyu, na karawa juna sani na shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna, kan tsantseni da sarrafa kudade cikin kula da k**ata a kananan hukumomin su, wanda ma'aikatar kananan hukumomi ta shirya da hadin gwiwar hukumomin yaki da yiwa tattalin arziki ta'annadi,da sauran hukumomi s**a shirya.

Ku dakaci cikakken rahoton

19/12/2023

Jami'an civil defense 1,200 aka tura jihar Adamawa saboda bikin kirsimeti

Mai Magana Da Yawun Hukumar NSDCS Reshen Jahar Adamawa,Nyako Baba Ne Ya Bayyana Haka Ga Manema Labarai

Inda Ya Bayar Da Tabbacin Cewar Jami'an Hukumar Zasu Hada Hannu Da Sauran Jami'ai Wajen Ganin Anyi Bikin Kirsimeti Lafiya

19/12/2023

Wannan shi ne Malam Nasir Anka, 'yan bindiga sun yi garkuwa da shi a kwanaki a jiharsa ta Zamfara, amma bayan sun karbi Naira milyan 2 daga hannun 'yan uwansa a matsayin kudin fansa, sun kashe shi.

Allah ya gafarta masa. Ya sa ya huta.

19/12/2023

Sakaci da aiki ya janyowa masu gadin asibiti rasa aikinsu a jihar Kano.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta sallami masu gadin a kokarinta na inganta bangaren lafiya.

An dai kawo mai nakuda asibitin ne amma aka nemi masu bude kofa aka rasa lamarin da ya sanya matar haihuwa a cikin mota a waje.

19/12/2023

Barkanmu da Safiyar Ranar Talata
19\12\2023 yanzu karfe 5:20am daga nan cikin birnin Kano Nigeria

Karfe nawa agogon garinku a daidai lokacin da kukaga wannan rubutun?

18/12/2023

Yan bindiga sun kashe malamin makaranta bayan karbar miliyan biyu a jihar Zamfara

uk Da Cewar Yan Bindigar Sun Karbi Kudi Har Naira Miliyan Biyu A Hannun Yan Uwan Marigayin Malamin

Amma An Samu Gawarsa A Cikin Daji Bayan An Tabbatar Da Irin Azabtarwar Da S**a Yi Masa Kafin Mutuwarshi

18/12/2023

hukumar NAFDAC ta fara wani mataki na Haramta wasu magungunan kashe kwari a Najeriya

Kame wadannan haramtattun kayayyakin ya biyo bayan Kai Wasu simame a wuraren daban-daban da Ake Zargi

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC, ta ce ta lalata tireloli 135 da kwatainoni na jabun magunguna da wadanda S**a lalace ko wa’adin su ya kare da Bude su a kan t**i da aka kiyasta Kudin su kimanin Naira biliyan 16.

Darakta Janar ta hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, itace wadda ta bayyana hakan a Abuja ranar Litinin, ta ce tun daga lokacin ne hukumar NAFDAC ta fara wani mataki na hana maganin kashe kwari a kasar.

18/12/2023

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Fintiri

Photos from Daily News Hausa 24's post 18/12/2023

Qasar Nijar Yau Take Cika Shekara 65 Da Zama Jamhuriya. Wane Abune Zaku iya Tunawa tsakanin ku da Maqotan ku Nijar?

Zaku iya Auren matan Nijar?

18/12/2023

Ranar Alhamis 21/12/2023 Kotun Koli zata Fara Sauraren Shari'a kan zaben gomnan jihar Kano tsakanin Dr Nasiru Yusif Gawuna na Jam'iyyar APC da Engr Abba Kabir Yusif na jam'iyyar NNPP

Videos (show all)

Wani Matashi Mai Suna Umar Aliyu Abubakar Kofar Waika. Dan Karamar Hukumar Gwale Dake Jahar Kano,  ya Kirki Abun Sarrafa...
Kaikayin matse matsiKurajen gabaKurajen fata.Da duk wani nau'in sanyi ga magani
Ku saurari wannan
Mata ku jaraba amfani da wannan maganin
Ku saurari wannan, musamman mata
Mata ku saurari wannan

Telephone

Website