Daily news

Daily news

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Daily news, Shopping & retail, .

21/09/2024

Cire Tallafin Mai ya rage yawan man fetur da Najeriya ke amfani da shi zuwa lita miliyan 30 a kullum

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur ya rage yawan man fetur da Najeriya ke sha a kullum zuwa kusan lita miliyan 30.

Da yake magana a ranar Alhamis din da ta gabata yayin ganawarsa da tsaffin ‘yan majalisa a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin ya ba da karin haske kan yadda ake amfani da man fetur a kasar nan kuma ya dakile fasakwaurin mai.

Shugaban ya jaddada cewa, bai kamata ‘yan Najeriya su mayar da hankali wajen rage farashin man fetur kadai ba, har ma su ba da fifiko kan samar da makamashi a matsayin mafita na dogon lokaci kan kalubalen da ke fuskantar bangaren mai da iskar gas.

“Mutane na korafin halin da man fetur ke ciki. Na farko, dole ne mu tabbatar da tsaron mai. Eh, muna da danyen mai a kasa, Amma muna da karfin hakowa, tacewa da rarraba shi? Shin mun bincika madadin hanyoyin makamashi tare da albarkatun da muke da su? " Tinubu ya ce.

Daily news

20/09/2024

𝗖𝗥𝟳 🐐

20/09/2024

Shugaba Tinubu zai zauna a gida ya mayar da hankali kan magance matsalolin da ke addabar Najeriya saboda haka ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya ba karo na 79.

Me kuka fi son shugaban ya fi mayar da hankali a kai?

20/09/2024

Kamfanin Coca-Cola ya bayyana shirin zuba jarin dala biliyan 1 a Najeriya nan da shekaru biyar masu zuwa.

A cikin sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Coca-Cola ta sanar da hakanne bayan Ganawa da shugaba Tinubu.

Sanarwar ta ce: “Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na samar da ingantaccen tsarin hada-hadar kudi da tattalin arziki mai saukin kai da kasuwanci wanda zai jawo hankalin masu zuba jari kai tsaye daga kasashen waje.

“Shugaban ya yi wannan alkawarin ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin da Kamfanin Coca-Cola ya bayyana shirin zuba jarin dala biliyan 1 a Najeriya nan da shekaru biyar masu zuwa.

“An sanar da hakan ne a wani taro da shugaban kasa ya yi da tawagar shugabannin duniya na kamfanin Coca-Cola, karkashin jagorancin Mista John Murphy, shugaban kamfanin kuma babban jami’in kula da harkokin kudi, da Shugaban Kamfanin Bottling na Najeriya, Ambasada Segun Apata.

“Shugaba Tinubu ya yabawa kamfanin Coca-Cola kan hadin gwiwar da ta dade tana yi da Najeriya da kuma inganta damar zuba jari da ta dauki ma’aikata sama da 3000 aiki a fadin cibiyoyin samar da kayayyaki tara.

Daily news

20/09/2024

An harbo makaman roka zuwa arewacin Isra'ila daga Lebanon - IDF

Ƙarin bayani -daily news

Photos from Daily news's post 20/09/2024

Wasu daga cikin jiga, jigan siyasar gidan tsohon sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Dr. Mustapha M. Inuwa daga karamar hukumar Danmusa sun fice daga Jam'iyyar PDP sun koma Jam'iyyar Apc.

A ranar Juma'a 20/9/2024, jiga, jigan siyasar gidan tsohon sakataren Gwamnatin daga kara mar hukumar ta Danmusa su ka fice daga Jam'iyyar ta PDP su ka koma Jam'iyyar ta Apc.

Jiga, jigan siyasar gidan tsohon sakataren Gwamnatin da su ka fice daga Jam'iyyar ta PDP su ka koma Jam'iyyar ta Apc sun hada da tsohon sakataren ilmi na karamar hukumar Danmusa Alh. Bello Ibrahim, da Alh. Abba Mai Auduga.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Danmusa Hon. Aminu Garba Danmusa (Sai Baba), shugaban Jam'iyyar Apc na karamar hukumar Danmusa Alh. Rabe Jafaru.

Dan takarar shugaban karamar hukumar Danmusa Hon. Ibrahim Namama, da Alh. Dan Asibi, su ka jagoranci amsar jiga, jigan siyasar gidan tsohon sakataren Gwamnatin da su ka fito daga karamar hukumar Danmusa.

A jawabin shugaban jam'iyyar Apc na karamar hukumar Danmusa Alh. Rabe Jafaru yace wan nan fari ne s**ayi wasu daruruwan 'yayan Jam' iyyar ta pdp, a karamar hukumar Danmusa na nan zuwa nan gaba kadan zasuyi bikin amsar su.

20/09/2024

Yankin arewa maso yamma ne ya fi kowane yanki yawan haihuwa har yanzu a Nijeriya – Daily news

20/09/2024

Litar mai ya kai dubu biyu (2,000) a wasu ƙasashen -inji Tinubu

Shugaban kungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce shugaban Bola Tinubu ya nemi zai dauki dawainiyarsu da kudin jirgi su je ran-gadi zuwa wasu ƙasashen dake zagaye da Najeriya ko yankin Afrika ta yamma domin ganewa idanunsu yadda farashin mai yake a ƙasashen,

Tinubu a lokacinda kungiyar ƙwadago ke matsa masa lamba kan rage farashin mai shine ya yi masu martani inda ya ce "idan s**a bincika za su ga har Naira dubu Biyu (2,000) ake sayar da lotar mai a wasu ƙasashen" inji Ajaero

Ya kuka ga wannan bayani na shugaba Tinubu? Daily news

20/09/2024

...............

06/09/2024

YANZU-YANZU: Mawaƙi Ali Jita ya cire Jar Hula ya fice daga NNPP Kwankwasiyya zuwa APC ta hannun Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Barau Ibrahim Jibrin.

Jita dai yana cikin jiga-jigan Ƴan Kwankwasiyya daga masana'antar fina-finan Hausa, shi ne ya yi fitacciyar waƙar nan ta 'Abba Gida-gida Abba ne.

Me zaku ce?

Photos from Daily news's post 06/09/2024

1 goals. 1998 goals

06/09/2024

Tinubu mutum ne mai tausayi, bai ji dadin halin da aka shiga kan tsadar fetur ba - Fadar shugaban kasa

06/09/2024

KURIAR JIN RAAYI !!

Dukkan masu Hasashe sun tabbatar da cewa Cikin waɗannan Mutanen Jam'iyyar PDP zata tsayar da Ɗan Takarar ta da zai Gaji Kujerar Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi Wa kuke da kwarin Gwiwa akan Idan ya lashe zaɓen fidda Gwanin zai yi nasara a zaɓe Gama Gari cikin sauki?

1. Hon Auwal Jatau Wanda ya Fito Daga Shiyar Bauchi ta Arewa. Wanda a Halin Yanzu Shine Mataimakin Gwamnan Jahar Bauchi.

2 Barr Ibrahim Kashim Wanda ya Fito Daga Shiyyar Bauchi Ta Kudu Wanda a Yanzu haka Shine Sakataren Gwamnatin Jahar Bauchi ,

3. Hon Farouk Mustapha Wanda ya Fito Daga Shiyyar Bauchi ta Arewa yayi babban daraktan Yakin neman zaben Kauran Bauchi a zaɓen da ya gabata ma 2023 a yanzu Kuma Shine Kwamishinan Ayyuka na Musamman da raya Karkara na Jihar Bauchi

4. Sanata Abdul Ningi Wanda ya fito Daga Shiyyar Bauchi ta Tsakiya A Halin Yanzu shine Zaɓaɓɓen Sanatan Bauchi Ta tsakiya A ƙarƙashin Jam'iyyar PDP

KBC News

06/09/2024

ALLAHU AKBAR: Yau 06-09-2024 Marigayi Sheik Abubakar Gero Argungu Ke Cika Shekara Guda Cif Da Rasuwa

Allah Ya gafarta masa.

Telegram: Contact @firecoin_app_bot 03/06/2024

https://t.me/firecoin_app_bot/app?startapp=r_6452111094
Join me in mining Firecoin and get 4000 free coins! 🔥from note coin

Telegram: Contact @firecoin_app_bot

Telegram: Contact @STRIKEAirdropBot 24/05/2024

Karkuyi wasa dawanan withdraw akeyi dakahada 27 refaral zakafida dola 💲💸💶💷

Telegram: Contact @STRIKEAirdropBot

16/04/2024

Agayamaka jam iyarshi Koko akyaleka zakusamu kurine tare

16/04/2024

Shifah garinkwaki Yana copy and paste na post din wancan Dan adawar usmaniyya da naali neh

16/04/2024

Zamu fara idan kacimana mutunci mucinaka ehe aha

16/04/2024

Mike abun bakin ciki garigar aro Wanda kowa Allah yaso shizaiba

16/04/2024

Shifa garin kwaki yakasa fahimtar yan.takararnan duk Yan jam iya dayane

16/04/2024

Kaida kake cima wani mutunci Dan wani yaji Dadi tokasani kaimafa Kanada naka mutunci gefe kyalekaka akayi bawaidan naka mutunci bai ciyuwaba aha

Photos from Daily news's post 02/04/2024

Photo The speaker is talking about how we can change the governance structure of our city rimi local government soon🙏🏻🙏🏻

Website