Matattarar Rayyan
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Matattarar Rayyan, Grocers, .
Kada kayi abota da mutum uku:
1- Munafuki. 2-Maha'inci. 3-Marowaci.
Allah ya tsare mu daga wadannan halaye da ma'abotansu.
By BMD.
Ya kai wata bakwai Amurka da Faransa suna rokon kafa sansanin soji a Najeriya'
Wasu mutanen Arewacin Najeriya da ke nuna kishin ƙasar sun nuna fargabarsu kan rokon da Amurka da Faransa ke yi na neman kafa sansanin soji a Najeriya.
Cikin wata tattaunawa da BBC Farfesa Jibirn Ibrahin wanda shi ne mai magana da tawagar wadannan mutane ya ce akwai tashin hankali bai wa waɗannan kasashe wurin zama a Najeriya.
"Yanzu yakai wata bakwai muna jin ƙishin-ƙishin ɗin cewa Amurka da Faransa na ta rokon a basu wuri su kafa sansanin sojinsu. To yanzu maganar ta ƙara ƙarfi shi yasa muka fito muke ba da shawara ka da a sake a yi hakan.
" Wannan haɗari ne ga ƙasarmu bai kamata sojojin Faransa da na Amurka su kafa sansani ba a ƙasarmu," in ji Farfesa Jibrin.
Yace an fatattaki sojojin ƙasashen biyu daga Nijar da Mali da Burkina Faso saboda gazawa s**a koma Chadi nan ma aka kore su to yanzu suna neman inda za su zauna ne su riƙa sanya idanu kan wadannan kasashe.
Ya ce gwamnatocin ƙasashen da s**a kori sojojin Faransan da Amurkan, sun ce sun gaza ne a kan cimma manufar da aka girkesu a kai ta yaki da masu iƙirarin jihadi a don haka s**a sallame su.
To ko Najeriya s**a zo "ba za su taimakawa matsalar tsaro ba sai dai ta sake taɓarɓarewa," in ji shi.
Ya ƙara da cewa cikin yarjejeniyar da s**a ambata suke so a cimma akwai maganar cewa "babu mai bincikar abin da s**a shigo da shi Najeriya. Duk wani laifi da s**a yi wa 'yan Najeriya babu mai tuhumarsu.
"Babu wanda zai iya shiga sansaninsu. Kawai ƙasa suke so su kafa a cikin ƙasarmu. Kuma mu ƙasa ce mai cikakken 'yanci," in ji Farfesa.
BBC News.
Kamewa da haƙuri ado ne ga talaka, godiya da ihisani kuma ado ne ga mawadaci.
HAUSATV – IRIB HAUSATV WEBSITE Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da kaddamar da hare-hare na musamman guda 10 kan sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar
Allahumma Salli Ala Muhammad Wa Ãli Muhammad.
Duk wanda ya tabuka ya yi kokari, to da taimakon Allah zai kai ga gaci. Wanda ya yi shuka to da sannu zai yi girbi.
~ By: BMD.
Bayan sauke wajibai (farillai); to hidimtawa mutane ce hanya mafi saurin kaiwa zuwa ga Allah.
~Sayyid Fadlullahi.
Kafin ka zargi Iran me ya sa bata shigar wa Palasdinawa yaki ba, to ka fara zargin Saudiyya domin su Palasdinawan Ahlussunna ne.
Me yasa Iran ba ta kai wa Isra'ila hari ba sai da aka tsokane ta? Abin da ya hana Saudiyya kai harin shi ya hana Iran.
A~ By: BMD.
Sharuddan fada da gaskiya:
Sharara karya, karyata gaskiya, musanta hakika (reality) da magana bisa jahilci.
~By: BMD.
Iran ba sai kin matsa wa kasashen Musulmi a kan ku hada kai ba! Bar su kawai yau-da-kullum za ta fahimtar da su nan gaba.
~By: BMD
أين تذهبون والحق فيماتكرهون؟
Ina za ku je ne? Gaskiya dai tana inda ba ku so (gaskiya tana tare da wadanda kuka tsana).
~By: BMD.
Kada kiyayyarku da mutane ta hana ku yi masu adalci! Ku yi adalci shi ya fi kusa da tsoron Allah.
~Alkur'ani.
Ko ku fadi gaskiya Iran ta kara samun karbuwa, ko ku yi karya mutuncinku ya kara zubewa, ko kuyi shiru munafunci ya kara bayyana.
Alhamdu lillahi! Iran ta fara maida martani kan Isra'ila bisa harin ta'addancin da ta kai mata a karamin O/Jakadancinta a Siriya.