Fahad Halilu

Fahad Halilu

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Fahad Halilu, Design & Fashion, .

Zamu kafa kwamitin Bincinke da kuma biyan diyyar dukiya da rayukan da aka rasa a fadan Yarbawa da Hausa>>Gwamnatin Oyo 16/02/2021

https://www.facebook.com/498142173713123/posts/1571726126354717/?app=fbl

Zamu kafa kwamitin Bincinke da kuma biyan diyyar dukiya da rayukan da aka rasa a fadan Yarbawa da Hausa>>Gwamnatin Oyo February 16, 2021 by hutudole Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana cewa zata kafa Kwamitin bincike dan gano Asalin dalilin fadan da ya barke tsakanin Yarbawa da Hausawa.   Gwamnan jihar, Seyi Makinde ne ya bayyana haka a jiya, Litinin inda kuma yace duk wanda aka samu da laifi za’a hukuntasu.   Ya bay...

14/02/2021

Sojoji Ne Ba Sa So Yaki Da Ta’addanci Ya Kare, Cewar Sheikh Gumi

Daga Suleiman Abba (TBABA)

Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi zargin cewa sojojin Nijeriya na amfana da yaki da kasar ke yi da ta’addanci shi ya sa ba sa so matsalar ta kare.

Malamin ya yi zargin cewa zunzurutun kudaden da ake kashewa wurin yaki da ta’addanci ya sa yawancin manyan sojoji ba sa kaunar a kawo karshen matsalar.

“Sojoji ba sa taimakawa ko kadan saboda su ke cin amfana da tabarbarewar sha’anin tsaro,” inji shi a lokacin hirar da gidan talabijin na ARISE TV ya yi da shi.

Sheikh Gumi ya bayyana haka ne yayin karin haske game da ziyarar kwanan nan da yake kaiwa dazuka don yin da’awa ga ’yan bindiga su rungumi zaman lafiya su daina ta’addanci.

“A shirye ’yan bindigar suke su ajiye makamansu su koma rayuwarsu yadda s**a saba a baya muddin Gwamnatin Tarayya za ta biya bukatarsu da bata taka kara ta karya ba: ta gina musu makarantu da sibitoci ta samar musu da ruwan sha.

“Suna yawan kokawa cewa sojoji na kashe mutanen da babu ruwansu. Shi ya sa s**a fara daukar makamai. Ko ta ina suke samun makamai? S**a fara yin garkuwa mutane wanda shi ya haifar da wannan aikin soji.

“Amma a shirye suke su ajiye makamansu su koma rayuwa kamar sauran ’yan Najeriya idan za a gina musu makarantu da asibitoci a samar musu da ruwan sha.

“Akwai kuma zargin cewa sojoji ba sa so a kawo karshen rikicin saboda da biliyoyin Nairori da ake ba su don yakar ta’addanci. Saboda haka su ma sojojin ba sa taimakawa.

“Ina yaba wa ’yan sanda da Shugaban ’Yan Sanda musamman saboda ya taimaka mun je mun gana da waddannan mutane; amma su sojoji babu alamar za su taimaka, ba su ba da hadin kai ba; ban san dalili ba.”

Photos from Fahad Halilu's post 14/02/2021

Ƙabilar Yarbawa Sun Farmaki 'Yan Uwanmu 'Yan Arewa, Tare Da Kashe Mutane Da Dama A Garin Ibadan Dake Jihar Oyo
...Muna kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta kai musu ɗaukin gaggawa, don kuɓutar da 'yan Uwanmu 'yan Arewa.

Daga Ƙungiyar “Arewa Media Writers”

Ƙabilar yarbawa a garin Ibadan dake jihar Oyo, sun farwa 'yan uwanmu 'yan Arewa dake zaune a garin da harin ta'addaci tun jiya da dare, wanda zuwa yanzu an yi asarar rayukan da ba'a san adadin su ba.

Ƙungiyar “Arewa Media Writers” ta samu sahihin labarin Abin da ya faru, in da 'yan ta'addan s**a farmaki 'yan uwanmu 'yan Arewa, s**a kashe maza da mata yara da manya da ba zasu ƙirgu ba.

'Yan'uwanmu 'yan Arewa da yawa basu iya kwana a gidajen su ba, saboda mummunan harin ta'addacin da s**a kai musu.

Da wannan dalilin ne Ƙungiyar Marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa Comr Abba Sani Pantami, take kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gaggauta kai wa 'yan uwanmu 'yan Arewa ɗauki, kan wannan mummunan harin ta'addacin da akai musu, don gujewa abin da zai iya zuwa ya dawo.

Muna Addu'ar Allah ya zaunar mana da ƙasar mu lafiya Amin.

Photos from Fahad Halilu's post 10/02/2021

Gwamna Zulum Zai Dawo Da 'Yan Gudun Hijira 9,800 Daga Kasar Kamaru Zuwa Nijeriya

Daga Comr Abba Sani Pantami

Gwamnan jihar Borno, Fafesa Babagana Umara Zulum, tare da jami'an Ma'aikatar Harkokin Agaji da Ci gaban Al'uma ta Nijeriya na ziyara a garin Marwa na Kamaru don mayar da wasu yan Nijeriya 9,800 yan asalin Borno gida.

Mutanen dai na cikin wasu yan gudun hijirar Nijeriya 46,000 da s**a yi hijira zuwa wani sansani a Minawao a Kamaru.

Yan Nijeriyar 9,800 na cikin rukunin farko na yan kasar da s**a nuna son a kwashe su daga sansanonin yan gudun hijira zuwa wasu gidaje da gwamnatin Borno ta gina a garuruwan Bama da Banki.

Zulum ya jagoranci tawagar daga Najeriya kan wata yarjejeniya da aka sa wa hannu tsakanin Najeriya da Kamaru da ofishin jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan yan gudun hijira, wanda za a yi a garin na Marwa a arewacin Kamaru.

Gwamnan yankin arewa na Kamaru, Mijinyawa Bakare ne mai masaukin baki a tattaunawar.

Cikin tawagar ta Najeriya akwai Sakatare na din-din-din na ma'aikatar ayyukan agajin ta Najeriya Malam Bashir Nura Alkali da Darektan ma'aikatar Ali Grema wasu jami'an gwamnatin jihar Borno.

10/02/2021

Dalilan Da Ya Sa Za Mu Maye Gurbin Lambar BVN Da Ta Katin Zama Dan Kasa, Cewar Ministan Sadarwa Sheikh Pantami

Daga Comr Abba Sani Pantami

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa, dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke shirin maye gurbin lambar BVN da lambar zama dan kasa.

Ministan ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen gudanar da kafin dan kasa dake Babban Birnin Kasar, Abuja, inda ya kara da cewa, zai gana da kwamitin farfado da tattalin arziki da gwamnan babban bankin Nijeriya domin mika bukatar hade BVN da lambar katin zama dan kasa. A cewarsa, lambar BVN manufarta shine ita ce, samun kulawa da sa ido, yayin da lambar katin zama dan kasa doka ce.

Ya ce, “karfin doka ba za a taba hada shi da manufofi na wata cibiya guda daya ba.”

Ministan ya kara da cewa, lambar BVN yana takaita ne ga wadanda suke da asusun banki, yayin da lambar dan kasa doka ce ga duk wanda yake zaune a Nijeriya.

“Lambar BVN shi ne kididdigan bayananmu na biyu, yayin da lambar katin zama dan kasa shi ne ke da matsayi na farko a kan kowani dan kasa da kuma kowata ci bya da ke cikin Nijeriya,” inji shi.

Pantami ya yi alfari da Nijeriya a matsayin uwa da yankin Afirka wacce ya kamata ta kare kulawa da bayanai da kuma daukan matakai sabra da tsaro wanda za a iya samu a cikin bayanan kididdiga wanda zai kai kashi 99.9.

Ya ce, “sakamakon wannan dadilin ne ya sa Nijeriya ta tilasta bin hanyoyin da ba a samu kididdige mutane cikin sauki wanda ta haka ne za a samu dakile wasu daga cikin hanyoyin rashin tsaro.

“Za mu tabbatar da cewa, an samu cikakken tsaro a cikin kasar nan, sannan ba za mu taba amince ba wani ya ballo da wani shiri na daban, domin ‘yan kasa sun amince da mu.”

Da yake bayar da dalilan da gwamnatin tarayya ta bukaci kamfanoni masu zaman kansu su gudanar da katin zama dan kasa, ministan ya bayyana cewa, yin hakan yana daga cikin tsarin kasashen duniya.

Ya jaddada cewa, akwai bukatar hukumar

Photos from Fahad Halilu's post 10/02/2021

Gwamnatin Kano Ta Zabi Sarkin Kano A Matsayin Wanda Zai Kula Da Mukabala Tsakanin Sheik Abduljabar Da Malaman Kano

Daga Jamilu El Hussain Pambegua

Gwamnan jihar Kano, Dakta Ummar Abdullahi Umar Ganduje ya zabi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero don kula da muhawarar da za a yi tsakanin Sheikh Abduljabar da Malaman Kano.

Sannan Gwamnatin ta Jihar Kano din ta zabi fadar Mai Martaba Sarkin Kano a matsayin wajen da za a gudanar da tattaunawar.

Gwamnan Ganduje ya ce "mun zabi fadar Mai Martaban ne tunda batu ne na addini".

Photos from Fahad Halilu's post 10/02/2021

Karamar Hukumar Sabuwa Dake Jihar Katsina, Ta Zama Mafakar 'Yan Bindiga
..Kungiyar "Arewa Media Writers" Tana Kira Ga Gwamnatin Jihar Katsina, Da Shugabannin Tsaro Dasu Dauki Matakin Gaggawa Akan Yadda 'Yan Ta'adda S**a Addabi Al'ummar Karamar Hukumar Da Sauran Yankunan Dake Fama Da Matsalar Rashin Tsaro

Daga Kungiyar "Arewa Media Writers"

A zantawa da kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" tayi da wani mazaunin yankin mai suna Jamilu Tela Sayau, ya shaidama kungiyar cewa a kowace rana ta Allah sai 'yan ta'adda sun shigo garuruwan Sabuwa, Sayau, Dungun Mu'azu, Tashar bawa, Galadima, sun kashe mutane, sun kwashi dabbobi, sun fasa shagunan mutane sun kwace wayoyin jama'a tare da yin garkuwa da mutane, don neman kudin fansa.

Haka zalika ya kara dacewa ko'a ranar Talatar da ta gabata 4- ga watan Feb, 2020, saida 'yan bindiga s**a kawo wani mummunar hari a garin Sabuwa, inda s**a yima mutum 13 kisan gilla s**a tafi da shanun wani mutun mai amalanken dibar yashi.

Al'ummar wannan yanki a halin da ake ciki yanzu hankalinsu ba kwance yake ba tashe yake, saboda a kullum mata da kananan yara basu iya barci a cikin gidajensu sai a wajen gari da saman bishiyoyi, sakamakon yadda 'yan ta'adda suke cin karensu ba babbaka.

A karshe kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" na kara Kira da jan hankali ga Gwamnati da jami'an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki dasu gaggauta daukar matakin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi yankin Arewa gaba daya.

Fatan kungiyar "Arewa Media Writers" taga yankin Arewa ya zauna lafiya, dama kasar Nijeriya baki daya.

Website