Muhammad zabibi sani

Muhammad zabibi sani

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Muhammad zabibi sani, Health/Beauty, .

18/04/2023
smoothsell- How to buy data on MTN । Airtel data plans। How to buy data on glo 01/10/2022

smoothsell- How to buy data on MTN । Airtel data plans। How to buy data on glo How to buy data on MTN । Airtel data plans। How to buy data on glo

15/09/2022
10/09/2022
01/09/2022
31/08/2022
29/08/2022
29/08/2022

Ingancin Salatul fatihi daga Qur'ani da Hadisan Annabi S.A.W
INGANCIN "SALATUL FATIH" DAGA KITABU WA
SUNNAH
**{salatin Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ }*
A gaskiya ya k**ata duk wanda yake dalibin Ilimi
ne, to ya daina amfani da jite jiten mutani domin
gudun faadawa cikin halaka.
Domin so dayawa yan Izala domin basa son dariqa
sai su dinga karya suna mana sharri da kazafi.
Kuma sai s**e a cikin "Jawahirul ma'aani" aka
rubuto.
"bi'isa lizzamina badala"
Haka wani dan izala ya tura min message ta inbox,
ya bani haushi, amma kuma gaskiya ya bani dariya
sossai.
GA ABINDA YACE MANI:
Bilal kake wa? Ya k**ata ku dinga tsoron Allah ku
daina karya, acikin jawahirul ma'aani shafi na 164"
shehu Ibrahim yace an yi masa wahayin salatul
fatih. Waiyazubillah.
Me zaka ce akan wannan? Kuma kada kayi karya
domin ga Jawahirul Ma'ani din a hannuna. sai
najika...
**Haba!! Wani kariya ne haka?
Ba shehu Ibrahim ba, ko Shehu Tijjani { ﺭﺿﻲﺍ ﻟﻠﻪﻋﻨﻪ}
yazo duniya ya tarar da Salatul Fatih b***e shehu
Ibrahim{ ﺭﺿﻲﺍ ﻟﻠﻪﻋﻨﻪ}.
Salatu Fatih::
kamin mu shiga bayani ya k**ata musan shin:
>> Me nene SALAT??
>> Me nene FATIH???
DOMIN KALMOMI NE GUDA BIYU AKA HADASU
{salatul fatih}.
Allah yana cewa:
"wa salli alaihim inna salaataka sakanan lahum...
{Q9:103}
A wannan ayar Allah yayi wa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ umurni da yayi wa bayinsa{na kwarai}
addu'a domin hankalinsu ya kwanta.
Acikin wata ayar kuma yace:
"walaa tusalli alaa ahadin minhum mata abada.....
{Q9:56}
Anan kuma Allah ya hana Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
kada yayi wa kowani daya daga cikin su addu'a
{matattun munafuqai kenan}.
To wannan misalai sun ishe mu gane ma'anar
SALAT anan shine "ADDUA"
Na biyu kuma:
Salat na daukar ma'anar "IBADA" ko ADDU'A.
Kamar yanda Ibn kathir ya nuna. Saboda fadin
manzo s.a.w cewa:
" Izaa da'a ahadakum ilaa ta'aamin fa'in kaana
sa'iman fal yusalli....
**idan ankira{gayyace} dayanku wurin cin abinci, to
idan ya kasance yana Azumi ne to yayi Sallah...
{a nan salaat Ibaada ne kenan}.
AL~FATIH: shine "budewa" k**ar ayar farko a
qur'ani suratul "Fatiha" da surar aka bude qur'ani.
Shi yasa ma'anar "Salatul Fatih" "Addu'ar
budewa"{budewar Rahma marar iyaka}.
Kuma daya ne daga cikin sunayen Allah, kuma data
ne daga cikin sunayen Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
Shi yasa ku masu shegantaka kuna cewa SALATIN
FATI ko kuma SALATIN PARTY domin ayi dariya, to
wallahi kuna cikin Hatsari babba!!!
Domin mayarda ayoyin Allah da Annabi{s} abin
wasa ko ayi dariya KAFURCI ne, koda kullum
Azumu da karatun qur'ani kakeyi Allah zai rusa
ayyukan mutum gabadaya saboda wannan
wallahi...
Allah yace mamaki da yana mamaki:
ﻗﻞ ُُﺃﺑﺎِﻟّﻠﻪَﻭَﺁﻳﺎَﺗﻪِﻭﺭ ﺳَﻮﻟﻪِﻛﻨُﺘﻢُ ﺗﺴﺘْﻬَﺰْﺅِﻭُﻥ ??? ﻻﺗﻌَﺘْﺬَﺭﻭﺍﻗﺪَﻛ
ﻔَﺮَﺗﻢُ ;;;
shi yasa a kula....
** wanda Allah ya bada Salatul fatih ta hannun sa,
akan Tartibin da muke amfani dashi, shine
"Muhammadu Al~bakari{RA} ta hanyar {KASHFU}
Amma inda rigimar take shine yawancin yan Izala
suna cewa ta yaya Allah zai bada wani abu addinin
musulici bayan Allah yace:
"Al yauma akmaltu lakum dinukum wa atmamtu
alaikum ni'imati waraditu lakumul islama dinan.?
Domin acikin ayar Allah yake cewa a yau na cika
maku addininku, daga nan aka kulle wahayi....
Abakar Gumi" yayi maganganu akan haka sossai
cewa ta yaya Allah zai ce wa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ "A YAU NA KAMALLA MAKU ADDININKU"
amma wani yazo waishi anyi masa wahayi{yayi
surutai dayawa "zomo}.
Shine "KABIRU GOMBE" shima yana cewa, to a
tambayi Muhammad Bakari" shin wahayin Salatul
fatih, kamin "Alyauma akmaltu lakum dinikum" ne
akayi ko kuma bayan saukar ayar "Al'yaumal
akmaltu"
Domin ba'a saukar da wata aya ba, a bayan
Al~yauma akmaltum.
DAYAKE SU YAN IZALA DASU DA MALUMAN SU
DUK BASA KARATU......
{suratul ma'ida:3}
"Al yauma akmaltu lakum dinukum wa atmamtu
alaikum ni'imati wa radeetu lakumul islam dinan.
** Duk wanda yace bayan wannan ayar babu
wahayi to Jahili ne, dakiki ne wawa ne kuma
mahaukaci....
A ranar da aka saukar da wannan ayar: {Q5:3}
ranar Juma'a ne, a Arfa" manzon Allah{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } yana zaune akan Rakumin shi.
> Bayan saukar ayar "Alyauma Akmaltu" Allah ya
saukar ayar karshe na suratul Nisa'i. 176:
"yastaftunaka qulillahu yuftikum fil kala............ Ilaa
akhiriha.
> Bayan wannan da kwana Hamsin{50days} Allah
ya saukar da aya ta dari da ashirin da takwas
{128:suratu Taubah}
"lakad jaa akum Rasulun min anfusikum azizun
alaihi maa anintum harisun Alaikum bil mu'mineena
ra'ufun raheem wa'in tawallau fakul hasbiyallah
laa'ilaaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul
arshil azeem..
Bayan wannan da kwana talatin da biyar{35days}
sa'annan Allah ya saukar da aya ta dari biyu da
tamanin da daya{281:Baqara}
"wattaqu yauman tur'jauna fihi ilallah summa
tuwaffa kullu nafsin maa kasabat wahum laa
yuzlamun:
Duk wa'annan bayan "Alyauma akmaltu" ne ko
kuma su ba wahayi bane??
Sa'annan kamin Annabi{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } yayi
wafati, bayan ayoyin qur'ani gabadaya sun gama
sauka, Allah yayi masa wahayi na "Hadithil Qudsi".
Na kawo wannan ne domin yan izala dake yawan
cewa bayan wannan aya aka rufe wahayi.{Jahilai}
Intaha....
Abubakar Gumi yayi suratai sossai akan salatul
Fatih.Acikin littafin sa
"AQIDATUL SAHIHA"{shafi na 22} yace:
*hazaa walam yarwi an ahadin min a'immatil
hadeeth lafzu SALTUL FATIH" walam yasnidhu
ahadin ilan Nabiyy{s} fi hayatihi walaa ilaa ahadin
min sahabatihi wa tabi'eena wa tabi'i tabeen.
{GUMI}
Ma'ana: babu mutum ko kwaya daya daga cikin
malaman hadithi da ya kawo irin wannan lafazi na
salatu fatih ko isnadi zuwa ga Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ . Haka ma sahabbai da tabi'ai da tabi'i
tabi'eena...
Wannan yana daga cikin abinda ya jawo mana
fitina, domin wasu yan Izala basu maganar hankali
sai hauka da tada hargitsi sakanin al'ummah
Annabi{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } kuma sun san gaskiya
amma suke karyata wa, idan kaji maganar da Gumi
yayi kamin mutuwar shi zaku tabbatar da sun
gaskiya suke karyatawa.
"SALATI" addu'a ce kake rokon Allah ya biya maka
bukatunka.
Bukatar kuwa shine yayi wa Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ salati domin mu bamu iya ba.
DUK DUNIYA BABU MUTUMIN DA YA TABA YIN
SALATI, SAI DAI KA ROKI ALLAH YAYI WA ANNABI
SALATI DOMIN SHI KADAI IYA SALATIN.
To addu'a kuma sai kuce dole sai mutum yayi
amfani da lafazi daya kawai?
Yaushe Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yace haka?
Allah bai ce mana dole sai munyi anfani da wasu
kebantattun lafuza ba wallahi!
Abinda yace: id'uni astajib lakum" ku kirani zan
amsa maku, to abinda wahabiyawa basu gane ba
shine:
Yau idan na ga dama sai ince:
YA ALLAH KA BANI KUDI IN SAYE MOTA"
fadin haka haramun ne??
Ba haramun bane kuma Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
bai yi irin wannan addu'ar ba, kowa da irin abinda
yake bukata, na'am acikin qur'ani akwai addu'oi
dayawa k**ar irinsu:
* Rabbana Atina
* Rabbigfirli
* Rabana zalamna anfusana
* Rabbi shirahli sadri
* Rabbi zidni iliman etc........
Amma Allah bai tilasta mana cewa dole muyi
amfani da su kadai ba.
Ina naga dama sai ince: ya Allah ka bani sa'a domin
inci exams..
Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ baiyi irin wannan addu'a
kuma babu zai ce min KALA"
To haka abin yake ga "Salati". Lokacin da Allah
yace wa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yayi ma wasu
mutane addu'a yace masa:
"wa salli alihim inna salataka sakanan lahum*
Ma'ana: kayi masu addu'a....
Shin da Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ zai yi masu
addu'ar, SALATUL IBRAHIMIYYA ya karanta
masu??? To ai Salati aka ce!!
Inda Allah yana nufin kada mu karanta wani salati
daban, dole sai wanda Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya
koyar kawai da sai ya fada a cikin qur'ani, da sai
Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya fada a Hadithi.
"DUK AYYUKAN DA ALLAH YA WAJABTA MANA
AKAN MUYI SU, KADA MU KARA KADA MU RAGE
KADA MU CANZA WANI LAFAZI, ALLAH YA BAMU
SUNE TARE DA SHARUDAN SU,BAMU
TAMBAYESHI BA.
Misali SALLAH:
Sai da ya gaya mana sharudanta. Yace:
> wa aqimussalata"
> "Inna salata kanat alal mu'mineena kitaban
mauquta:
>Yace: walaa taqrabus salata wa antum s**ara"
>yace: hatta tagtasilu.
> wa akimu wujuhakum inda kulli masjidin, wad uhu
mukhliseena...
>Annabi s.a.w yace: Sallu k**a ra'aitumuni usalli"
> Assalatu Imamu din.. etc...
IDAN KAYI IRIN NAKA TO SALLARKA TA LALACE.
AZUMI:
>"kutiba alaikumussiyam".
>YAUSHE?"shahru ramadAN"
> Walaa tubashiru hunna"
> washrabu hatta yatabayyana lakumul hatul
abyadu minal haitil aswadu minal fajr.
> uhilla lakum lailata siyam rafasu ila nisa'ikum...
> summa atimmussiyam ilallail....etc
ASSIYAMU:TARUKU TAAM:
Sharutan azumi ne ake gaya mana.
HAJJI:
"wa atimmul hajja wal umrata lillah fa'in uhsirtum
famastaisara minal hdyi walaa tuhliku ru'usakum
hatta yablugal hadyi mahillah faman kana minkum
mareedan aw bihi azan min ra'asihi fafidiyatun min
siyaam aw sadaqatun aw nusuk fa'izaa amintum
faman tamatta'a bil Umrati ilal hajji famastaisara
minal hadyi famanlam yajjid fa siyamu salasati
ayyam fil hajj wa saba'atun izaa raja'atum Tilka
asharatun kamila, zaalika liman lam yakun ahluhu
haadiril masjidil haraam wattaqullah wa'alamu
annallaha shadidun iqaab.
DA AYOYIN DA KE BAYAN DUKKA HUKUNCE
HUKUNCE HAJJI DA UMRA NE.
To haka Allah ya keyi, amma da aka saukar da
ayar "SALATI"
"INNALLAH WA MALA'IKATAHU YUSALLUNA ALA
NABIYYI..zuwa karshe
Allah bai ce ga hukunci salati ba, kada ku karanta
salatul fatih, bai ce haka ba saboda addu'a ce,
addu'a kuma duk lafazin da ya dace kana iya
amfani shi.
To shi yasa Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ bai ce komi
akai ba,kuma manyan Sahabbai din basu tambaya
ba domin sun san addu'a ce, wasu daga cikin
sahabbai basu san yanda zasu yi salati ba s**a
tambayi manzo ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yanda zasuyi sai
ya basu SALATUL IBRAHIMIYYA amma bai ce kada
a karanta wani daban ba.
Yan'uwa don Allah ku karanta wanna Hadithi da
kyau kuyi tunani akai da basira zaku gane cewa ba
iyankance salatin Annabi{s} ba, kuma salatul
Ibrahimiyya Annabi {s} ya karanta masu shi ne
saboda Tawadu'u.
Abu sa'idul Badri{R} yace muna zauna tare da
sa'ad bin Ubadah{R} sai Annabi s.a.w ya zo
wurinmu, sai Basher bin Sa'id {R} ya tambayi
Annabi s.a.w cewa: ya Rasulullah!!!
Allah yayi umarni da mu dinga yi maka salati, to ya
zamuyi mu karanta?
SAI ANNABI{ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠ YAYI SHURU!!!
Sauran Sahabbai s**a ce:
"HAR MUKAYI NADAMAR "INA MA DA{bashir bin
sa'id}BAI YI MA ANNABI{ ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ } IRIN
WANNAN TAMBAYA BA!.
Sai Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ yace: kace Allahumma
salli alaa muhammad......har karshe "innaka
hamidun majid.
SABODA TAWADU'U
Amma sauran manyan Sahabbai sun san cewa
ba'a hana mutum ya karanta wani salati daban ba,
sai suna karanta irin nasu, wallahi su duka sun
kirkiro salatai daban daban wanda baya cikin
wanda Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya karanta.
Domin dama tun kamin a gayamasu Salatul
Ibrahimiyya sun kasance sun yin Salati ga
Annabi ﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠﻴﻪﻭﺳﻠﻢ
Imaman Ahlussunnah wal jama'ah hudun na
gaskiya{Imam malik, Abu Hanifa, Shafi'i, Hambal
{R.jamee'a} su dukka sun karanta salatai da irin
nasu lafazi, babu shi acikin wanda Annabiﺻﻠﻰﺍﻟﻠﻪﻋﻠ
ﻴﻪﻭﺳﻠﻢ ya karanta.
Kuma mu Alhamdulillahi.......
YAN'UWA ALBAISHIRINKU!!!
SAYYIDINA ALI {R.A} SHI YA FARA KARANTA
SALATUL FATIH....
Domin naji Abubakar Gumi{tsohon najadu} yana
cewa:
::"walam yarwi an ahadin min a'immatil hadeeth
lafzu SALTUL FATIH"{aqidatul sahiha GUMI}
Ma'ana:: daga cikin Maluman Hadithi babu ko
dayansu da YA RUWAITO LAFAZIN "SALATUL
FATIH"
To ku saka masa hannu a idonshi kuce masa
makaryaci domin yayi karya....
Sayyadina Ali karramallah wajhahu ya karanta
SALATUL FATIH" ya koya wa Salamatul Kindiyy
{R.anha} Itama ta koya wa wasu sahabbai.
Bari in fara bada hujjah da maluman da s**a kafa
wahabiyanci, almajiran Ibn Taimiyya.
IBN KATHIR BA DAN DARIQA BANE!!!
Kowa ya sani Almajirin Taimiyya ne.
Ka je ka duba tafsirin Ibn kathir: karkashin aya
k**ar haka:
"innallaha wa malaikatahu yusalluna alannabiyy ya
ayyuhallazina amanu sallu alaihi wa sallimu
taslima"
Bayan fassarar ayar sai ya kawo hadithin:
ﺣﺪﻳﺚ ﺁﺧﺮﻣﻮﻗﻮﻑ: ﺭﻭﻳﻨﺎﻩﻣﻦﻃﺮﻳﻖﺳﻌﻴ
ﺪﺑﻦﻣﻨﺼﻮﻮﺭﻭﺯﻳﺪﺑﻦﺍﻟﺤﺒﺎﺏﻭﻳﻳﺰﻳﺪ ﺑﻦﻫﺎﺭﻭﻥ،
ﺛﻼﺛﺘﻬﻢﻋﻦﻧﻮﺡ ﺑﻦﻗﻴﺲ : ﺣﺪﺛﻨﺎ '' ﺳﻼﻣﺔﺍﻟﻜﻨﺪﻱ :
Wa'nnan sune s**a ruwaito hadithin daga
Salamatul Kindiyy{sahabiya ce Allah ya kara yarda
da ita.
Tace: sayyidina Ali{RA} ya kasance yana koya
mana{da wasu mutane} wannan addu'a:{ ﻛﺎﻥﻳﻌﻠﻢ
ﺍﻟﻨﺎﺱﻫﺬﺍﻟﺪﻋﺎﺀ }:
Amma salatin na da tsawo..
ﺍﺟﻌﻞ ﺷﺮﺍ ﺋﻒﺻﻠﻮﺍﺗﻚ ، ﻭﻧﻮﺍﻣﻲﺑﺮﻛﺎﺗﻚ، ﻭﺭﺃﻓﺔ ﺗﺤﻨﻨﻚ ،
ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻋﺒﺪﻙ ﻭﺭﺳﻮﻟﻚ
''ﺍﻟﺨﺎﺗﻢﻟﻤﺎﺳﺒﻖ ، ﻭﺍﻔﺎﺗﺢﻟﻤﺎﺃﻏﻠﻖ ، ﻭﺍﻟﻤﻌﻠﻦ ﺍﻟﺤﻖﺑﺎﻟﺤﻖ، ,,,,,
,,,,,,,,
Ij'al sharaifa salawatka wa nawaamee barakatika
alaa Muhammadu Abdika wa rasulika
Al khatimu lima Sabaka, wal Faatih limaa Ughlika,
wal mlinal Haqq bil Haqq...... Ilaa akhiriha
duba littafin:
Imam Qaadiy Iyyadh {Ash-shifa} juzu'i na 2 shafi
70\72.
> Yusufun Nabhaaniy{R} a littafin:
:"Afdhalul-salawaat alaa sayyidil saadaat"{ya kawo
wani rawaya na salatul fatih}
> Imam Ibn Jazuli {R}
{Dalaa’ilul khairaat}
>Imam Al-qisdalaaniy{R}
"Al-mawaahibul ladunniyya
> Al-Sayyid Muhammad bin Hadi bin Hassan bin
Abdul-Rahman Al-Saqafy- Al-Hussainy{R} littafin:
An-Nafahaatul Anbiyaa’u fees-Salaati alaa Khairil
bariyyat"
> Imam sakhawi {R} littafin:
Al-qaulul badeeah fis salaati alal
Habeebi shafee’u" shafi 44-45.
aciki zaku ga Hadithin:
Sayyada Salamatul Kindiyy{R} itace wadda
sayyidina Ali {R} ya fara koyawa "salatul fatih"
Muhammad bin Abdulrahman bin Muhammad
bin Abubakar Al Sakhaawiy Al Shafi’iy{ an haife shi
a Sakhaa, Misra. 831 A.H ya rasu a 902 A.H} yace
isnadin wannan salatin ya inganta har zuwa kan
Annabi s.a.w.
{{Al-qaulul badeeah: 45} >>1963

25/08/2022
25/08/2022
23/08/2022
23/08/2022

Videos (show all)

Website