Madrasatu Aliyyi Bn Abi Ɗalib Lit-tarbiyatil Islamiyyah Tudun Jukun, Zaria
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Madrasatu Aliyyi Bn Abi Ɗalib Lit-tarbiyatil Islamiyyah Tudun Jukun, Zaria, Non-Governmental Organization (NGO), .
MUTUMCIN ƳA MACE
Shugabar Zama:
Malama Muhibbat Hamza Sh*ttu
Mai Muhadara:
Malama Khadijah Alhassan Mansur
MADRASATU ALIYYI BIN ABI ƊALIB LIT-TARBIYATIL ISLAMIYYAH, TUDUN JUKUN ZARIA, KADUNA-NIGERIA
Hukumar makaranta mai suna a sama suna farin cikin gayyatar ƴan'uwa mata masu albarka zuwa wajen muhadarar da s**a shirya kamar haka in sha Allah:
Shugabar Zama:
M Khadijah Alhassan Mansur
Mai Muhadara:
Malama Binta Umar Musa (Alkhulafa'ur Rashideen)
Maudu'in Muhadara: Mutumcin Ƴa Mace
Rana: Alhamis 28 ga watan
Zulhijja, 1445 (4/6/2024)
Lokaci: Safe 9:30am -11:30am
Wuri: Jami'ush Sheikh Ɗalhat Assalafiy Tudun Jukun Zaria, Kaduna Nigeria
Allah Ya bada ikon halarta.
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
LABARI CIKIN HOTUNA 📸
Alhamdulillah, cikin taimakon Allah Ta'ala a yau Lahadi 3 ga watan Zulhijja, 1445H (9/6/2024), makarantarmu mai albarka ta samu baƙuncin ƙungiyar Khairun Nisa'i Islamic Development Foundation Ukhty's ƙarƙashin jagorancin Malama Aishatu Abdulmumin Al-arab Hafizahallah.
Ƙungiyar sun ziyarci makarantar domin wayar musu da kai a kan abin da ya shafi Jinin Al'ada tare da raba musu auduga (PAD). Bayan bude taron da karatun Alƙur'ani Dr. Nafisa Usman Nafaɗa ita ce ta wayar wa mata kai a kan Jinin Al'ada; daga karshe kuma jagorar tafiyar tayi jawabin manufofin kungiyar mai albarka.
Allah Ya saka wa kowa da alkhairi. Mungode
ZIYARAR KUNGIYAR KHAIRUN NISA'I
(UKHTYS) ISLAMIC DEVELOPMENT FOUNDATION
Gobe Juma'a
1st Zulhijjah, 1445H
(7/6/2024)
TILAWAR ALƘUR'ANI MAI GIRMA
TARE DA: GWANA ZAINAB TANIMU ZAILANI
TILAWAR ALƘUR'ANI MAI GIRMA
TARE DA: GWANA WASILA HALLIRU SANI
MADRASATU ALIYYI BIN ABI ƊALIB LIT-TARBIYATIL ISLAMIYYAH TUDUN JUKUN, ZARIA KADUNA-NIGERIA
LABARI CIKIN RUBUTA DA HOTUNA 📸
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh
Alhamdulillah, cikin taimakon Allah da ikonsa a ranar Lahadi ne 26th Shawwāl, 1445H (6/5/2024), kwamitin shirya muhadarori da wayar da kai ga al'ummar musulmi, musamman ƴan'uwa mata masu albarka na wannan makaranta mai albarka s**a shirya muhadarar ta tattauna da Gwanayen Alƙur'ani Mai Girma, wacce aka gabatar a Masallacin Jami'ush Sheikh Ɗalhat Assalafiy Unguwar Tudun Jukun, Zaria Kaduna - Nigeria.
An gabatar da muhadarar ce ga ƴan'uwa mata, kuma ƴan'uwansu mata s**a gabatar musu:
Mai gabatarwa: Gwana Nafisatu Idris
Shugabar zama: Malama Khadijah Muh'd Auwal
Gwanayen da aka tattauna da su:
Gwana: Gwana Zainab Tanimu Zailani
Gwana: Gwana Wasila Halliru Sani
Muhadarar ta zo da wani tsari da ba'a saba gabatar da ita ba a haka shi ne; tsarin tambaya da amsa ga dukkan gwanayen, daga bisani kuma su bada amsa. Muhadarar ta gabata da hantsi a cikin awa biyu da rabi 9:30am-12:00pm
DAGA CIKIN MANYAN BAƘINMU:
1. Mai Masaukin Baƙi: Hajiya Saratu Sani Sha'aban, wacce Dr. Salamatu Bello ta wakilce ta a zaman.
2. Uwar Taro: Malama Saudatu Yunus
3. Babbar Baƙuwa: Hajiya Amina Abdulƙadir Salanke
4. Gwanayen Alƙur'ani Mata
5. Ƴan'uwa Malamai Mata
6. Jami'an Tsaro Ƴan'uwa Mata
7. Gidajen Talabijin/Online TV's
8. Makarantun Haddar Alkur'ani
9. Ƴan'uwa Mahalarta Mata
BAYAN KAMMALA MUHADARA, HUKUMAR MAKARANTAR TA KARRAMA GWANAYEN:
1. Gwana Zainab Tanimu Zailani
2. Gwana Wasila Halliru Sani
Akwai shawarwari da aka bada in sha Allah za mu yi aiki da su, kuma muna maraba da duk masu bamu shawarwari, ko kuma idan an hango wasu ƙalubalai sai a faɗakar damu ta hanyar da ta dace. Ga masu buƙatar sautin karatun za su iya tuntubar mu ta WhatsApp; +2348143646953.
JAWABIN GODIYA DA ADDU'O'I
Godiya mara adadi ga Allah Ta'ala, sannan godiya ga ƴan'uwa Gwanayenmu masu albarka, sannan godiya ga ƴan'uwa masu albarka ƴan kwamiti. Haƙiƙa alƙalamina ba shi da tawadar da zan iya rubuta kalmomin godiya gare ku, saboda kun bada gudummawa ta kowani ɓangare, duk da wasu sun fi wasu; amma muna fatan duka mu yi tarayya cikin alkhairi watan Aljanna Alfirdausi.
Ina addu'a gare ku duka, kuma ina fatan Allah Ta'ala Ya karɓa mana addu'oinmu. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara muku imani, albarka, lafiya, ikhlasi, juriya, haƙuri, natsuwa, tausayi, arziƙi mai albarka, Ya albarkaci rayuwarku, Ya shirya da ku da zuri'arku, Ya ƙara muku zaman lafiya a gidan aurenku, Ya kaɗe fitina a tsakaninku, Ya azurta ƴan matanmu da mazaje na gari masu tsoron Allah waɗanda za su tsare musu mutuncinsu, Ya jiƙan iyayenmu, matanmu, mazajenmu, ƴaƴanmu, Ya gafarar ta musu, Ya musu rahama, Ya sa suna kyakkyawan matsayi, Ya shige muku gaba cikin al'amuranku, Ya biya muku buƙatunku na alkhairi, Ya yaye muku damuwarku ta duniya da lahira, Ya kyautata ƙarshenku, Ya sa ku cika da kyau da imani, Ya sa abin da za ku fadi ƙarshe ita ce, kalmar shahada.
✍️ Yusuf Lawal Yusuf (Shugaban Makaranta)
MUHADARAR AURE TA MAZA DA MATA
Assalamu alaikum wa rahmatulla
MUHADARAR YAN'UWA MATA
Rana: Alhamis 25th April, 2024
Lokaci: 4:00pm zuwa 5:30pm
Wuri: Jami'ush Sheikh Ɗalhat Assalafiy Tudun Jukun, Zaria
Maudu'i: Matsalolin Aure da Saki, da hanyoyin magance
Malami Mai Muhadara: Dr. Alkalgawee Bangannawee
MUHADARAR YAN'UWA MAZA
Rana: Juma'a 26th April, 2024
Lokaci: Tsakanin Magriba da Isha'i
Wuri: Jami'ush Sheikh Ɗalhat Assalafiy Tudun Jukun, Zaria
Maudu'i: Hikimar shar'anta aure da matsalolin da ke hana matasa yin aure.
Shugaban Zama: Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria
Malami Mai Muhadara: Dr. Alkalgawee Bangannawee
Allah Ta'ala Ya bada ikon halarta. Amin
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
Allah Ta'ala Ya bada ikon halarta. Amin
MAKON AƘIDAH ZARIA 1445H/2024H
MADRASATU ALIYYI BIN ABI ƊALIB LIT-TARBIYATIL ISLAMIYYAH TUDUN JUKUN, ZARIA KADUNA-NIGERIA
Assalamu alaikum wa-rahmatullah
Hukumar wannan makaranta mai albarka suna farin cikin gayyatar ƴan'uwa mata zuwa wurin muhadarar sa s**a shirya kamar haka in sha Allah:
MC: Gona Nafisatu Idris
Shugabar Zama: Malama Khadijah
Muhammad Auwal (Ummu Najibillah)
Gonayen Alƙur'ani Mai Girma:
1. Gona Zainab Tanimu Zailani (Shugabar Ƙungiyar Musabaƙa ta Rabiɗah Jihar Kaduna)
2. Gona Wasila Halliru Sani (Shugabar Makarantar Abdullahi Bin Mas'ud Al'alamiyyah, Zaria
Maudu'i: Tattaunawa da Gonayen Alƙur'ani
Rana: Lahadi 26th Shawwal, 1445A.H (5/5/2024)
Lokaci: Da safe 9:30am zuwa 11:30am
Wuri: Jami'ush Sheikh Ɗalhat Assalafiy Tudun Jukun, Zaria Kaduna-Nigeria
MUHADARAR GORON SALLAH 02
Muhadarar Ƴan'uwa Maza. Shugaban Zama: Prof. Abdurrafi'i Abdulkarim. Malami Mai Muhadara: Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria. Maudu'i: "Tasirin Ilmi da Malamai Wajen Bunƙasa Rayuwar Al'umma". Rana: Asabar 13/04/2024. Lokaci: Tsakanin Magriba zuwa Isha'i. Wuri: Masallacin Baba Trader Juma'a Mosque Tudun Wada, Zaria.
Allah Ta'ala Ya bada ikon halarta. Amin
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
MUHADARAR GORON SALLAH 01
Cibiyar Markazul Wa'ayil Islamiy Lit-ta'alimi Wal-Irshad Wal-Buhuthil Ilmiyyah Tudun Jukun Zaria, suna farin cikin gayyatar ƴan'uwa maza zuwa wurin muhadarar da za ayi in sha Allah bayan Sallar Asubahi 5:30am. Malami: Sheikh Prof. Ahmad Bello Dogarawa Hafizahullah. Maudu'i: "Taimakekeniya a halin matsi da ƙuncin rayuwa a musulunci; misalai daga rayuwar magabata na ƙwarai". Rana: Alhamis 11/04/2024. Wuri: Jami'ush Sheikh Ɗalhat Assalafiy Tudun Jukun, Zaria Kaduna-Nigeria.
Allah Ta'ala Ya bada ikon halarta. Amin
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
HUKUNCE-HUKUNCEN SALLA ƘARAMA
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh
Muna farin cikin sanar da ƴan'uwa masu albarka cewa, in sha Allah gobe Asabar 27 ga watan Ramadan, 1445A.H (6/4/2024) da misalin ƙarfe 5:45am za a tattauna da malaminmu Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria Hafizahullah a kan abin da ya shafi Hukunce-Hukuncen Salla Ƙarama. Domin kallo da sauraro kai tsaye za ku iya following ɗin mu ta shafin mu na Facebook:
https://www.facebook.com/profile.php?id=100079672941426&mibextid=ZbWKwL
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
Azumi babbar makaranta; wasu su koyi ilmi mai yawa mai amfani, kuma su sami sakamako mai kyau, wasu su gudu kafin kammala makaranta, wasu kuma a gama da su; amma da mummunan sakamako. Allah Ya sa mu dace.
✍️ Sheikh Basheer Lawal Muhammad Zaria
🌙 TILAWAR ALKUR'ANI A RAMADAN
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh
Ƴan'uwa mata masu albarka, ina fatan kuna lafiya. Allah Ya ƙara muku albarka a duk inda ku ke, Ya tsare mana ku Ya suturta mana ku. Amin
Bayan haka, ina farin cikin sheɗa ƴan'uwa cewa, in sha Allah 1 ga watan Ramadan, 1445A.H za mu fara Tilawar Alƙur'ani da muke yi duk Ramadan daga 1 ga wata zuwa 25 ga watan Ramadan.
Lokaci: Ƙarfe 7:00am zuwa 9:00am
Wuri: 1. Makarantar Ma'ahad Ulumiddinil Islamiy Hayin Dogo Tudun Jukun, Zaria
2. Makarantar Ma'ahad Ulumiddinil Islamiy Layin Telex Tudun Jukun, Zaria
Allah Ya bada ikon halarta. Amin
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
MADRASATU ALIYYI BIN ABI ƊALIB LIT-TARBIYATIL ISLAMIYYAH COLUMBIA STREET TUDUN JUKUN, ZARIA KADUNA-NIGERIA
Assalamu alaikum wa rahmatullah
Hukumar makaranta mai suna a sama suna sanarda ƴan'uwa mata masu albarka cewa, an ɗage tattaunawar da aka shirya tare Gwanayen Alƙur'ani Mata: Gwana Zainab Tanimu Zailani da Gwana Wasila Halliru Sani zuwa bayan Sallah Ƙarama. Ɗage tattaunawar ya samo asali ne saboda hatsarin mota da ɗaya daga cikin Gwanayen tayi wato Gwana Zainab Tanimu Zailani Hafizahumallah.
Alhamdulillah, a yau Asabar 21 ga watan Sha'aban, 1445A.H (02/03/2024) wasu daga cikin kwamitin da s**a shirya tattaunawar sun samu zuwa duba ta da jiki har gida kuma jikin da sauƙi; abin da ke damunta a yanzu shi ne buguwar da ta yi a Kai, sai kuma Ƙirji da ke damunta, duk sun koma asibiti a ɗasu. Muna roƙon Allah Subhanahu wa Ta'ala Ya ƙara mata lafiya, Ya sa kaffara ne, Ya ƙara tsare gaba da ita da sauran ƙawayen tafiyarta da suke kwance a asibiti; cikinsu har da waɗanda s**a samu karaya. Amin
✍️ Yusuf Lawal Yusuf
Assalamu alaikum wa rahmatullah
A madadin hukumar wannan makaranta, muna jajantawa Gwana Zainab Tanimu Zailani bisa hatsarin da s**a yi a hanyarsu ta koma gida daga Zaria zuwa Kaduna, acikin tawagar akwai waɗanda s**a samu karaya, amma ita malama jikin nata da sauƙi. Bayan haka kuma wani abin takaici a wurin da s**a yi hatsarin aka sace mata wayarta. Muna addu'a Allah Ya basu lafiya, Ya ƙara tsare gaba.
ALBISHIRINKU ƳAN'UWA MATA DA KE ZARIA!