DR AHMAD BAMBA FANS

I love prophet muhd SAW

06/12/2023

Musulunci da ban☑️

Shi'an ci da ban❌

Mu Al Umar Musulmi Qur'anin mu📖 Da ALLAH ya sau karwa Manzon sa littafi ne Mai Tsarki Wanda yake cike da gaskiya☑️

Mu Musulmai Annabin mu duk matansa Tsarka Kane ☑️

Mu Musulmai Annabin mu duk Abokan sa Masu Imani ne ALLAH ya yarda da su☑️

Ya ALLAH ka Qara Tsira da Amunci Ga Farin jakada ANNABI MUHAMMAD S A W da Iyalan gidan sa Baki Daya 🙏

29/11/2023

YAKE YAR UWA TA MUSULMA GA WATA SHAWARA GARE KI!!!

Ya ke yar uwata ki sani cewa rayuwa wata abace wadda take tafiya da sauri sanan take qarewa da wuri k**ar dai yadda k**e fatan qarewar zamanki agaban iyayenki (AURE)

Ga wasu shawari da zan baki wanda nasan in sha ALLAH zasu taimaka miki qwarai da gaske
Amma sai kinyi hakurin karantawa🙏🏻

1-Ki daina kula kowanne irin saurayi koda wani yazo yace yana son ki, ki duba riƙonsa da addini, kada ki ce sai mai kuɗi

2-Kada ki riƙa roƙon saurayinki kuɗi ko wani abu na daban domin roƙon da zaki yiwa saurayinki zai kai ki ga buɗe kafar ɓarna ne kawai

3-Banda wulaƙanta mutumin da yazo ya bayyana soyayyarsa gare ki Idan kina da wanda k**e so ko bai yi miki ba ki faɗa masa zance mai daɗi ki ba shi haƙuri

4-Idan ALLAH ya kawo miki saurayi mai tarbiyya ki riƙe abin ki gam kada ki tsaya wasa har ki rasa shi

5-Kiyi haƙuri da abin da yake faruwa dake na idan saurayi yazo gare ki soyayya tayi ƙarfi daga ƙarshe ya tafi ya bar ki Ki cigaba da roƙon ALLAH ya baki miji nagari

6-Ki daina yin dare a wajen hira Me zai hana ki hira da safiya yamma ko wani lokaci na daban wanda ba yankin dare ba karki na ganin hirar safe da maraice ƙauyanci ce

Shin me ya kai wannan ƙauyanci; ace saurayi da budurwa su zauna zaman hira da daddare har sama da ƙarfe goma su kaɗai alhalin ga shaiɗan ya turo musu jakadunsa ina ganin k**ar ba abinda zai hana a samu damar taɓa sassan jiki

7-Banda hira da samarin banza domin samarin banza na ƴan matan banza ne ke kuma mutuniyar kirki ce

8-Kada ki yarda son abin duniya ya rufe miki ido ki auri mai kuɗi marar tarbiyya, lallai idan kika aikata hakan kin yi asara kuma za kiyi nadama a gaba kaɗan bana miki fatan haka

9-Idan zaki fita daga cikin gida zuwa wani waje na daban kada ki saka matsattsun tufafi ki sanya kayan da shari'a ta yarda dasu sannan kada ki fesa turare mai ƙamshi in ba wanda yake kashe warin jiki ba

10-Ki suturta muryarki, kada ki bari wani yaji daɗinta idan ba mijinki ba ban da ɗaga wa iyayenki

28/11/2023

Da ace kun san abin da na sani game da al'amarin Lahira, da kun taƙaita dariya kun yawaita kuka.

~ Inji Manzon Rahama (SAW).

27/11/2023

DARASI GA MATAN DA S**A ZABI RAYUWAR BARIKI

1-Sunanki wai 'yar gwagwarmayar
2-Aure baya gabanki baya lissafinki
3- Sakarya an haifeki ta hanyar aure amma kina aibanta aure
4- Ke feminist ko activist ba ruwanki da aure
5- ¥ahudu da karnukansu zasu h**e kunnenki
6- Zasu daure miki gindi su baki kudi
7- Zasu yayataki a kafofin watsa labaransu
8- Zaki sanu sosai a duniya
9- Fasikai mazinata zasu fara daukanki
10- Yau kina wannan hotel din gobe kina wancan
11- Kina gwagwarmaya amma sun mayar dake karuwa
12- Zasu kwakwuleki tatas
13- Nonuwan zasu zube su dawo silifas
14- Tudun mazaunan zasu zagwanye su dawo k**ar "yadi"
15- Kin ki aure b***e ki haihu
16- Idan kin yi nisan kwana tsufa zai zo
16- Daga nan yayinki ya wuce
17- Sai cutar kansa ta k**aki
18- Zakiyi ta fama da jinya har kudin su kare
19- Daga nan zaki rasa mai taimakonki
20- Kashi da fitsari a kwance
21- Tun kina raye kin dawo abar kyama

Ki sani babu wani rufin asiri gareki face aure, ki dauki darasi da wannan baiwar Allah da ake yayata hotonta, tsufa ya k**ata da rashin lafiya, ance ta gaji da kwanciya shine sai 'yarta ta goyata a baya take yawo da ita cikin Asibiti, abin ya burge kowa, da ba ta da 'ya shikenan babu mai kula da ita

Aure rahama ne, haihuwa alheri ne, ku bar yawon bariki da gwagwarmayar karya, kuyi aure ku hayayyafa shine rufin asirinku duniya da lahira

Muna fata wannan yarinya da ta goya mahaifiyarta Allah ya kara wa rayuwarta albarka, Ya sa mu wanye da duniya lafiya

25/11/2023

---------------------------------------------------------------
*AYATUL KURSIYYU:=
---------------------------------------------------------------

*Ita ce aya mafi girma acikin littafin Allah (Al-Qur'ani)

*Wanda ya karanta ta lokacin da ya wayi gari= Za'a tsare shi daga Aljanu har zuwa yamma.

*Wanda ya karanta ta da yamma= Za'a tsare shi daga Aljanu har ya wayi gari.

*Wanda yake karanta ta bayan kowace sallah ta farillah= Babu abin da zai hana shi shiga Aljannah, sai dai In bai mutu ba.

*Wanda ya karanta ta lokacin kwanciya barci= Ba zai gushe ba face tare da mai tsaro daga Allah, kuma wani Shaiɗani ba zai kusance shi ba har ya wayi gari.

Falala mai girma, Allah ma'abocin falala ne mai girma.

25/11/2023

THE S*X YOU MUST NOT HAVE.

1. You must never agree to have s*x with a married man no matter what he promises or professes. Never!

2. Never agree to have s*x with your boss. If the harassment becomes too much, resign and trust God for a better job.

3. If God put people under your care to mentor or Pastor, it is better you die than to have s*x with them. Never take advantage of God's people no matter what.

4. Don't have s*x with a married woman. If you are getting too much attached via chatting, official or academic rapport, break up the closeness or whatever name you have for it.

5. Never have s*x with your lecturers. S*x for grades or marks is for nonentity. You are not. Never must you be.

6. If you are a marketer, never agree to sleep with a prospective client just to meet your official target. Never!

7. Don't have s*x with your in-laws. If he or she stays with you and you are finding it difficult to resist the pull, let him or her leave. I mean latest tomorrow.

8. Don't have s*x with your neighbour or colleague. A neighbour is a neighbour. A colleague is a colleague. Don't get your life more complicated.

9. Don't have s*x with your platonic friend. If the relationship is no longer platonic, break up the thing.

10. I believe God created s*x to be between male and female. Stay away from having s*x with your same gender. God is against homos*xuality and so should you.

11. Don't have s*x with your sibling or relatives. In**st is vile.

12. Don't have s*x with your girlfriend. Don't have s*x with your boyfriend. God did not create s*x for love relationships. He created it for MARRIAGE.
S*x is for procreation
The only s*x you should have is with your Legally married partner

🙏👏
Class dismissed 🥂

23/11/2023

"𝗡𝗜 𝗗𝗨𝗞 𝗪𝗔𝗡𝗗𝗔 𝗬𝗔𝗬𝗜 𝗠𝗜𝗡 𝗕𝗔 𝗗𝗔𝗜𝗗𝗔𝗜 𝗕𝗔 𝗡𝗔 𝗬𝗔𝗙𝗘 𝗠𝗔𝗦𝗔." Shiekh Ja'afar Mahmud Adam Kano
-
Duk wanda na yiwa ba daidai ba ya yafe min, duk wanda na yiwa ba daidai ina fatan don Allah ya yafe min"
-
"Ko mace ko namiji, ko wanda na sani ko wanda ban sani ba, ko wanda yake zuwa karatu ko wanda baya zuwa, ko malami ko sauran mutane, duk wanda na yiwa ba daidai ba ya yafe min"
-
"Ni duk wanda ya yi min ba daidai ba ko wanene na yafe masa, da mace da namiji, dana kusa dana nesa"

Furucin marigayi shiehk Jaafar mahmud adam kenan na ƙarshe-ƙarshe gab da za'a kashe shi.
Muna fata allah ya gafarta masa.
Idan mutuwan mu taxo allah yasa mu cika da imani.YASA ALJANNACE MAHADARMU Mutuna Da Sheikh Jafar

22/11/2023

Ɗan Uwa!

Ka sani cewa; sana'a bata raina mutum, sai dai mutum ya raina sana'a. A halin yanzu, kasa a ranka babu sana'ar da kafi ƙarfin kayi, duk inda zaka samu kuɗi ta hanyar halal don taimakon kanka da wasun ka, ka rungume ta.

A cigaba da fafutuka, daga nan har Birnin Sin, bakin rai bakin fama.

Allah ya albarkaci neman mu.

_Sheikh Sheikh

22/11/2023

A RANAR ALQIYAMAH:
Kowanne Mutum Mumini Yana da Wani Lokaci na Musamman Wanda Zai gana da Ubangininsa, daga Shi Sai SHI (SWT).
Ubangijinka Zai Yi Maka tambayoyi Musamman akan Zunuban ka Wadanda ka aikatasu aboye.
Zai ce maka: Shin Ka san Cewa Ni Ne Na HALICCE KA, Kuma ina tare da Kai ako Yaushe?
Kuma na san abinda akayi Shi afili da Kuma Wanda aka yi Shi aboye?".
"Ka san cewa alokaci kaza Kaine ka aikata kaza-da-kaza, ina kallonka, amma na rufa maka asiri ne?".
Nan take Sai Kunya ta K**a mutum..
Sai Ubangiji Allah Yace maka : "AI TUNDA NA RUFA MAKA ASIRI ADUNIYA, TO BA ZAN TONA MAKA ASIRI A LAHIRA BA..
JEKA NA GAFARTA MAKA"
Allahu Akbar!!!
Ya Allah Ka gafarta Mana dukkan Zunubanmu kayi mana afuwa, Don falalar ka da Rahamarka wacce ta yalwaci komai da kowa.

13/11/2023

Duk yadda aure yake akwai rufin asiri a ciki.

In baki yarda ba

Ki tambayi wacce bata da aure.

12/11/2023

Maciya bashin MTN
An Biya muku bashi
Amma kusani Kada Ku karaci.domin dakwai haramci cikinsa

06/11/2023

ALAMOMIN SON MANZON ALLAH ✍️

Ga Kadan 👌 daga cikin su

1 ANNABI idan ya bada Umarni Dole kayi Biyayya💕☑️

2 ANNABI idan ya bada Labari Dole ka Gaskata💕☑️

3 ANNABI yace Bari Kuma kabari yai maka Gargadi ka yarda💕☑️

4 Karka Bautawa ALLAH sai Akan Koyarwar Manzon ALLAH Abun da ALLAH ya Shar'anta💕☑️

Shi son ANNABI bafa Abaki yake ba da zaka cika Duniya da ihun kana son ANNABI
Kullum Shekara kana Shirya Maulidi

Amma Dabi'un ka Mu Amalar ka da ibadar ka ba irin yanda ANNABI yace ba
Kana batawa kanka lokaci ne Kuma Wlh Babu Lada❌

Ya ALLAH ka Qara Mana Qaunar Manzon ALLAH S A W ♥️♥️🥰

06/11/2023

Nasiha a Takaice:
✍️ Mansur Sokoto
Maimaitawa daga rubutun 13 R. Awwal 1442H
(30/10/2020)

Ko ka san...?
Ibnul Qayyim _rahimahullah_ ya ce: Bala'i gaba daya yana tattare ne a cikin halaye uku:
1. Girman kai, wanda ya fitar da Shaidan daga aljanna. Shi ne tushen kafirci.
2. Kwadayi wanda ya fitar da kakanmu Adam daga cikin ta. Shi ne mafarin sabon Allah.
3. Sai kuma Hasada wacce ta halaka yayanmu Qábila; ya kashe kanensa Hábila. Ka ji tushen ta'addanci.
Duk wanda Allah ya kare shi daga wadannan ukun zai gama lafiya.
📚 Al-Fawá'id (84).

06/11/2023

WASU MUHIMMAN KALAMAI DA ANNABI ﷺ YA FAƊA AKAN MATA
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

GAREKU MATA!

🔷 Annabi (SAW) Ya ce: " Ita mace ba ta kasancewa mafi kusanci ga mahaliccinta (a wani wuri) fiye da cikin gidanta."

[Silsilatus-sahiha 2688]

___________________________________

🔷 Annabi (SAW) Ya ce: " Duk macen da ta shafa turare, sai ta wuce wasu mutane don su ji kamshin (jikinta) to ita mazinaciya ce."

[Sahihu sunanin Nasa'i 5141]

___________________________________

🔷 Annabi (SA W) Yace: " Duk macen da tasa turare ta fita zuwa Masallaci, baza’a amsa mata Sallar taba har sai tayi wanka."

[Silsilatus sahiha 1031]

___________________________________

🔷 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Duk wanda ALLAH ya azurta shi da mace tagari, hakika ALLAH ya taimake sa da rabin addini, sai ya kiyaye dokokin ALLAH wajen samun sauran rabin addininsa."

[Sahihut Targheeb-1916]

___________________________________

🔷 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Duk matar da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba, to haramun ne ta ji kamshin aljanna.”

[Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209]

___________________________________

🔷 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " kada wata mata ta bayar da izinin (shiga) gidan mijinta, alhali yana nan, sai da yardarsa .”
[Muslim 1026]
___________________________________

🔷 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Mutane biyu sallar su ba ta wuce kawunan su:

1→ Bawan da ya gujewa mai gidansa har sai ya dawo.

2→Matar da take sabawa mijinta har sai ta daina."

[Sahihut targib 1948]

___________________________________

🔷 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Mace ba za ta taba sauke hakkn ALLAH ba har sai ta sauke hakkin mijinta gabaki daya."

[Sahihut targib 1943]

___________________________________

🔷 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Da a ce zan umurci wani ya yi wa wani sujjada, to da na umurci mace ta yi wa mijinta sujjada."

[Sahihut targib]

____________

01/11/2023

"Abu na farko da zaka gane cewa duniya ta ruɗeka, ya zama cewa kai addini bai dame ka ba."

✍️ ~ Sheikh Guruntum

Photos from DR AHMAD BAMBA FANS's post 29/10/2023

ABIN TAKAICI RUNDUNAR ƳAN SANDAN JIHAR BAUCHI TAKAMA UBAN DA YAKASHE ƊANSA

Uba yayi sanadiyar mutuwar ɗansa ɗan shekaru uku da haihuwa sak**akon dukan kawo wuka da yayi wa yaron kan sa ya fashe.

Uban yace sun rabo da mahaifiyar yaron wanda yanzu haka tana gidan su wanda bayan ya saketa ta ɗibe yaran ta ta tafi da su gidan mahaifin ta, amma daga bisani bayan yaran sunyi wayo ta mayar da su wajena domin naci gaba da kula da su.

Kwata kwata Mai domin da yaron gida na bai wuce sati Uku ba, lamarin yafaru na dakesa wanda yayi sanadiyar mutuwar sa a yanzu.

Yaa Ubangiji yatsaremu da aikin da nasani

26/10/2023
25/10/2023

*💝A MATSAYINKI NA MACE BUDURWA IN DAI KINSAN KINA SOYAYYA TO KI KULA DA WANNAN SAQO KI KARANTASHI.*

*_KISAN DA WAYE K**E SOYAYYA_*
*Kashi na 01.*

*💝🧕_(1). Ki tsayar da saurayi guda daya tak na kirki bisa la'akari da ayyukan sa da halayensa na zahiri._*

*💝🧕_(2). Ki tabbata kina sonsa sosai kuma shima yana sonki sosai._*

*💝🧕_(3). Kada ki yarda ki daɗe da saurayi, ko ki shaƙu dashi ko ki nuna masa tsananin so ba tare da iyayensa sun gana da iyayenki ba. In yaƙi turosu ki rabu dashi tunkafin yagama sace‎ zuciyarki._*

*💝🧕_(4). Kizama mai bin shawarar iyayenki, da neman shawararsu a harkar soyayya, kada kibi shawarar Ƙawaye ko saurayi ko bin shawarar zuciyarki._*

*💝🧕_(5). Kada ki yarda a kawo miki gulmar saurayinki ke kuma ki dauka ko ki k**a zargin sa. A'a sai kinyi bincike na adalci ko kin gani da idonki._*

*💝🧕_(6). Kada ki kuskura ki yiwa saurayinki ƙarya ki zama mai fada masa gaskiya, da yimasa bayanin komai iya saninki._*

*💝🧕_(7). Ki zama me yawaita addu'ah da bawa Allah zabi a dukkan Lamarin ki._*

*💝🧕_(8). Ki kiyaye zargi da binciken laifinsa matuqar ya sanar dake komai bai ɓoye miki gaskiya ba.*_

*💝🧕_(9). Ki dauka dan adam tara yake bai cika goma ba, kinga zai iya kuskure, dan haka sai kiyi masa afuwa.*_

*💝🧕_(10). Ki zama mai kare mutuncin kanki, da kuma kula da matsayinki ba tare da girman kai ba ko jan aji ga masoyi.*_

Masha Allah Allah yasa mudace Ameen summa ameen

25/10/2023

HANYOYIN MAGANCE HAUHAWAR FARASHI DA SAUKAKA RAYUWA A NIGERIA

1. Tarbiyantar da rai akan tsoran Allah da kuma dakonsa a kodayaushe

2. Yawaita Istigfari

3. Yarda da cewa talauci da wadata a hannun Allah suke.

4. Tarbiyyantar da rai akan daidaita hidimomi

5. Gwamnati ta hana boye kaya.

6. Kauracema sayen kayan da s**a Yi tsada

7. Barin bukatun da ba su zama dole ba.

8. Neman shawara daga masana

9. Tuna mutuwa

10. Kange mutane daga cin riba da sanar da su falalar bada rance ba tare da ruwa ba
11. Saukaka kudin shigo da kaya (Custom duty).

11. Cikakken dogaro ga Allah.

13. Taimakon juna da kuma fitar da zakka a yadda Musulunci ya tsara.

14. Shugaba ya kayyade farashin da za a dinga ciniki da shi, idan aka samu tsawwalawa daga ‘yan kasuwa.

15. Koyawa ‘yan kasuwa hukunce-hukunce da s**a shafi saye da sayarwa.

16. Kayyade farashin dala, da kuma sanya ido akan yadda ake sayar da ita.

17. Gyara matatun man fetur

18. Kallon na kasa da kai.

19. Neman taimako daga wanda zai iya ba shi gudunmawa.

20. Tsara abin da mutum zai kashe duk wata.

21. Maigida ya duba yadda ake amfani da abubuwan da ya sayo a cikin gidansa.

22. Gyara kamfaninnikan gwamnati da wadata kasar da wutar lantarki.

23. Tuna cewa shugabanci nauyi ne da Allah zai tambayi shugaba akansa.

24. Samar da tsaro.

25. Karanta tarihin hauhawar farashi a kundayan tarihi.

IN AKWAI WANDA YAKE DA KARI MUNA BUKATA

22/10/2023

Kar Kuyi Wasa Da
Sallah Akwai Miliyoyin
Mutane Cikin Kabari,Suna Burin Su Dawo Duniya Suyi Sujjada
Koda Guda Daya Ce.

22/10/2023

Kaji Tsoron Mai Tsoron Allah!
Kaji Tsoron Mai Roqon Allah!
Kaji Tsoron Mai yi Don Allah!
Kaji Tsoron Wanda Zai Barka da Allah.

19/10/2023

GOBE JUMA'A

Kada ka rasa sallar asuba a cikin Jam'i ♥️

Saboda Annabi (s, a, w) yace: "Sallah mafi falala a gun Allah ita ce Sallar asubar ranar Jumu'ah a cikin Jam'i".

Allah Ya bamu iko 🙏

16/10/2023

QARSHEN DUNIYA

Anzo Zamanin Da Shiru Yafi Alkhairi Akan Magana Saboda Tsira Da Imani
------------------------
Zamanin Da Aka Mayar Da Gaskiya ƙarya, Aka Mayar Da ƙarya Gaskiya,
-----------------------
Zamanin Da Aka Ajje Komai Ba'a Mahallinsa Ba, Zamanin Da Jahilai Ke Amsa Sunan Malamai, Aka Mayar Da Malamai Kuma Jahilai,
------------------------
Zamanin Da Aka Mayar Da Addini Hanyar Neman Abin Duniya.
-------------------------
Zamanin Da Mutane S**a Koma Bautawa Son Zuciyar Su S**a Sauka Daga Karantarwar Shugaban Halitta Annabi Muhammadu مُحَمَّد ﷺ ( SAW )
---------------------------
Zamanin Da Aka Mayar Da ddini Ra'ayi Da Son Zuciya,
----------------------------
Zamanin Da Makusanta Allah S**ai Shiru Da Baƙin Su, Su Kuma Tawagar Sheiɗan S**a Baza Komar Su
----------------------------
Zamanin Da Aka Mayar Da Addini Qungiyoyi Da Firqoqi Kuma Kowa Na Da'awar Fahimtar Sace Dai Dai Wanda Yabar Tasa K**ar Ma Yabar Musulunci,
---------------------------
Zamanin Da Mutum Yasan Gaskiya Zai Take Ta,
---------------------------
Zamanin Da Mutane Sukewa Mutane Hukunci Akan Makomar Su.
----------------------------
Zamanin Da Dalibai Suke Zagin Malaman Su Saboda Ya Fadi Abinda Baiyi Daidai Da Ra'ayinsu, Ba
----------------------------
Zamanin Da Ake Qyamar Zama Da Dan'uwa Musulmi Saboda Sa6anin Fahimta Amma Akeyin Mu Amala Da Kafuri ( Innalillahi Wa inna Ilaihi Raju um )
--------------------
Zamanin Da Ake Neman Ilmi Badon A Gyara Lahira ba Sai Don Asamu Hujjojin Da Za a Ci Mutunchin Wasu Mutane
---------------------------
Zamanin Da Zurfin Aqida Yafi Zurfin Ilmi Sanin Allah Da Sanin Sunnar Manzon Allah ( S.A.W )
--------------------------
Allah Ubangiji Yayi Mana Kyakykyawan Qarshe Yasa Mugama Da Duniya Lapiya Ya Yafe Mana Kurakurenmu
AMEN YA HAYYU YA KAYYUM
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️

15/10/2023

The messenger of God upon whom be peace says:
I swear an Oath by Allah on Three qualities and I will tell you about them, so memorize them.
1. The wealth of a servant is not decrease by a charity.
2. A servant is not wronged by oppression and he endures it patiently, but that Allah increases him in honor.
3. And no servant opens the door of begin but that Allah open for him the door of poverty.

Tirmidhi 2325

15/10/2023

Assalamualaikum "Yan uwa musulmi mabiya wannan shafi
Ina Mai sanar daku sabon shafin mu.wanda zaku ke samun ilimintarwa fadakarwa k**ar yadda muka saba
Domin shiga ciki ka Danna wannan koren rubutun ALLAH YASA MU DACE
KUNDIN KARATUKKAN MALAN AHMED TIJJANI YUSUF GURUNTUM🙏 https://www.facebook.com/profile.php?id=61552549463842

Kundin Karattukan Mallan Ahmed Tijjani Yusuf Guruntum'' Supermarket/Convenience store

14/10/2023

Wato jama'a Sai munyi taka tsamtsam da lamarin rayuwa bashin damuke daukowa Na recharge card dakwai haramci cikinsa mukula

14/10/2023

Ko ka san cewa ƙasar FALASƊIN ita ce ƙasar da aka kira ta da ƙasar ANNABAWA!??👇

01: Falasɗin ta kasance ƙasar Annabawan Allah, amincin Allah ya tabbata a garesu baki ɗaya.

02: Annabi Ibrahim (a.s) shine ya fara yin hijira zuwa ƙasar Falasɗin.

03: Allah Ta’ala ya tseratar da Annabi Lut (a.s) daga azabar da ta afkawa Mutanensa a ƙasar Falasɗin.

04: Annabi Dawud (a.s) ya rayu a wannan ƙasar, kuma ya gina masallaci a nan.

05: Annabi Sulaiman (AS) ya kasance yana zaune a ƙasar nan, kuma yana mulkin duniya baki ɗaya.

06: Annabi Musa (A.S) ya gaya wa sahabbansa game da wannan ƙasa da kuma shiga wannan gari mai tsarki (Falasɗin). Ya kira wannan gari da mai tsarki saboda kasancewarsa ya barranta daga shirka da kuma kasancewarsa ƙasar Annabawa.

07: Mu'ujizozi da dama sun faru a wannan gari, ciki har da haihuwar Annabi Isah ɗan Maryam amincin Allah su tabbata a gareta.

08: A lokacin da Mutanen Annabi Isa (AS) s**a so su kashe shi sai Allah Ta’ala ya dauke shi zuwa sama daga Qudus (watau Jerusalem).

09: Ɗaya daga cikin alamomin tashin ƙiyama shine dawowar Annabi Isa (AS) duniya a wannan ƙasar.

10: Annabi Isa (AS) zai kashe Dajjal a wani waje da ake kira (Bab Lud) a wannan ƙasar.

11: Falasɗin ita ce ƙasar da za a tashe kowa, Allah ya yi masa hisabi.

12: Daga wannan birnin ne Yajuju da Majuju za su fito su yaƙi Mutanen duniya da hargitsa duniyar.

13: Bayan haka ƙasar Falasɗin tana da darajar kasancewarta ALQIBLA ta farko ta Musulmi bayan an wajabta salloli biyar. Daga baya aka umurci Annabi Muhammad (ﷺ) da ya juya fuskarsa daga Masallacin Aqsa na (Jerusalem) zuwa Ka’aba na (Makkah) yayin Sallah. Masallacin da wannan lamari ya faru har yanzu ana kiransa da sunan Masallacin (Al-Qibla).

14: Bayan haka kuma anzo da Manzon Allah (ﷺ) daga Makka zuwa BAITUL-MAQDIS (Jerusalem) kafin a dauke shi zuwa sama a daren Mi'iraji.

15: Dukan Annabawa sun yi sallah anan, bayan da Annabi Muhammad ﷺ ya jagorance su sallah. Shine dalilin da yasa Falasɗin ta zama ƙasar dukkan Annabaw

13/10/2023

Akwai ranar da kowa zai guje ka amma Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama zai zo don cetonka. Kar ka manta da yi masa SALATI.

10/10/2023

MU NE MATSALAR KASARMU

Sheikh Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Bauchi yace:

Malam ka dubi yanda kasarmu ta lalace, idan wani abu ya faru, sai aje a nemo wani mai fashin baki a gidan radio yazo yayi fashin baki, sai kaga inda matsalar kasar tayi daban, inda fashin bakinsa yayi daban, shima wanda yake fashin bakin yana bukatar ayi masa fashin baki

Ai ka kalli kasar ka kalli makomar kasar, duk wanda zai kalli Kasarmu da hangen nesa ya kalli abinda zaije ya dawo ya san abubuwa a kasar sun lalace, matsalar Kasarmu shi ne hanyar cin abincin kasar, (matsalar kasar shi ne hanyar samun kudin kasar) ka gane???

(1) Lalacewar Ilmi shi ne hanyar samun kudin wadansu, lalacewar makarantun Gwamnati shi ne hanyar samun makurantun da ba na Gwamnati ba, idan makarantun Gwamnati s**a gyaru to makarantu private ba zasu samu mutane ba, kuma Malam wallahi wadannan masu makarantun private babu wanda zai sha kansu, ba Kwamishina ba ko Ministan Ilmi ba zai sha gaban su ba, wannan matsalar ta ilmi itace hanyar cin abincin su.

(2) Matsalar Man fetur itace hanyar samun kudin masu harkar mai, saboda wanda ya ke sana'ar mai idan aka samu wahalar mai abinda zai samu a sati biyu, in za'a je a latsa ne a gidan mai a samu sai ya shekara bai samu wannan kudin ba, don haka matsalar mai itace hanyar cin abincin sa.

(3) Matsalar wuta itace hanyar samun kudin wasu, wadannan masu harkar man fetur Wallahi ba Ministan Man fetur ba ko shugaban kasa sai yayi da gaske zai iya shan gaban su,

(4) Matsalar tsaro shi ne hanyar samun kudin wasu masu tsaron, idan aka zauna lafiya ba zasu samu kudin da suke so ba, saboda haka matsalar tsaro shine hanyar samun kudinsu wannan shi ne gaskiya, saboda haka matsalar mu itace hanyar samun kudinmu saboda haka matsalar bazata kare ba.

(5) Yanzu kasan iyakan kudin da ake samu ga matsalar Cronavirus?, wadansu sanadiyar hanyar arzikinsu shine hanyar Cronavirus, to idan ka dubi wannan itace matsalar kasarmu, yaushe ne Kasar zata gyaru?

Mu da ya k**ata mu hada kudi da

06/10/2023

Ana Haifarmu Ake Lillibemu, Muna Mutuwama Za'a Lillibemu😭Ya Allah ka Lillibemu da Rahamarka Albarkacin safiyar jumma'a 👏🤲

03/10/2023

Faman Ada'ahu Dakhalal Jannah ☑️🌴🍏🍍
Waman Asani Dakhalan nari 🔥💥

Duk Wanda yabi Manzon ALLAH S A W ♥️♥️ zai shiga Aljannah

Duk Wanda yasaba Masa zai shiga Wuta 🔥

ALLAH kabamu ikon yiwa Annabi'Da'a 🙏

02/10/2023

Matar Aure !

-Ki dinga yiwa Mijinki Kyak-kyawar Tarɓa a lokacin da ya dawo gida.
A wannan lokacin da ake wahalar kuɗi tare da tsadar kayan abinci.

-Ki dinga adana kayan abinci, banda ɓarna, domin duk mijin da yake ƙoƙarin kawo cefane idan kina ɓarnar kayan abincin zaki sanya masa ɓacin rai, kuma tamkar butulci k**e wa Allah domin wasu a wannan lokacin da yunwa suke wuni ko da yunwa suke kwana.

-Ki Iya Girke-girke kala-kala na zamani dana gargajiya.

-Ki Dinga Ƙoƙarin Canzawa Mijinki Kwanukan Cin Abinci akan lokaci.

-Ki Dinga Kula Da Tsaftar Kitchen.

-Ki Dinga kula da nau'ikan Abinci mai ƙara lafiya.

Kar ku zauna har sai lokacin da miji zai ƙara aure wai sannan zaku tsiri wnn🙄

Suma Maza yana da kyau idan Allah Ya H**e su dinga yiwa mace kyautar da zata samu damar yin abubuwan haka.

Ina Addu'ar Allah Ya H**e Mana.

01/10/2023

IDAN KANA SON KA TSIRA A NIGERIA

Datti Assalafiy ✍️
👇
(1) Ka sani ba'a yin kudi da albashin Gwamnati a Nigeria, sai dai idan ka samu dama a cikin Gwamnati kayi satar dukiyar al'ummah wanda a karshe zakayi nadama marar amfani a duniya da lahira

(2) Don haka tunda albashin Gwamnati ba zai wadataka ba wajen biyan bukatun kanka da na iyalanka, mafita a gareka shine ka hada da sana'a ta halal komin kashinta da kuma noma da kiwo, zasu rufa maka asiri Insha Allah

(3) Ka dage kayi karatun zamani a fannin da zamani ke bukata, wato kimiyya da na'ura mai kwakwalwa da fannin kiwon lafiyar mutane da dabbobi, fannin noma da kiwo da makanikanci, ma'ana yanzu ana neman ilmin da zai sa ka koyi sana'a ne, kar ka tsaya bata lokaci wajen karanta political science

(4) Ka sani cewa Masana kimiyyar zamani sunyi taro a Kasar Saudiyyah, Professor Isa Ali Pantami ya halarci taron, anyi amannar cewa nan da shekaru 15 kaso 75 cikin 100 na mutane ma'aikata a duk fadin duniya zasu rasa guraben ayyukansu a masana'antun Gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu, za'a maye gurbinsu da Artificial Intelligence da Robotics domin a rage yawan kudin da ake kashewa mutane ma'aikata

(5) Dan uwana talakan Arewa ka rage yawan bacci cikin dare, duk wanda kaga yayi arziki ko ya tara ilmi mai amfani sai da ya hana idonsa bacci, dukkan sirri na daukakar rayuwa da arziki yana cikin Qiyamullaili

(6) Ka yi hankali da mutane, ka zama mai tsananin rike sirri har sai kaji tamkar kai kanka baka yadda da kanka ba b***e wani makusanci, yanzu muna lokaci ne na tsananin cin amana

(7) Yanzu an dena kiwon dabbobi an koma kiwon mutane, ka zama mai yawan canza hanya idan zaka tafi wani guri ko gari, duk lokacin da kazo hawa abin hawanka ka leka kasan tayun motarka ko babur dinka, idan kaga alamar an tona rami to ka duba da kyau saboda miyagu suna da hanyoyin cutarwa da yawa

(8) Wani Malamina da yake bani horo akan Cyber Forensic yace min ka zama mai yawan gani da sauraren mutane, amma ka zama mai taka tsantsan waje

28/09/2023

Ka'idojin mu'amala guda [7]
1. Hakuri da juriya
2. Tabbatar da abu kafin yadashi
3. barin abinda baruwanka
4. kanisanci jayayya mutane zasu
soka
5. Kada kayi girman kai ga mutane
6. adalci ga abokan muamala
7. Kyautatawa juna

25/09/2023

Sheikh Mh'd Kabir Gombe

MANYAN LIKITOCIN DUNIYA GUDA 11 NE

1. Alqur'ani Mai Girma

2. Yawan shan ruwa

3. Bacci wadatacce da daddare

4. Iska mai kyau

5. Tafiyar rabin awa a kasa kullun

6. Abinci mai gina jiki madaidaici

7. Hasken rana

8. Zuma

9. Habbatus Saudah

10. Yarda da qaddara mai kyau koh maras kyau

11. Furta "Laa'ilaaha illallah"

KARIN BAYANI

Idan kayi zargin kanka kace "Astagfirullah"

Idan kaji radadi "Alhamdulillahi"

Idan abu yabaka mamaki "Subhaanallah"

Idan kana cikin farin ciki "Salatin Annabi ﷺ"

Idan kana cikin bakin ciki "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"

Idan kaga abun mai ban sha awa kace "Mashaa Allah Tabarakallah"

Ka fara komai da "Bismillahi"

Ka rufe komai da "Alhamdulillahi"

Ina rokon Allah Ya yarda da ni da ku babu komai bayan yardar Sa sai Aljannah In shaa Allahu...

23/09/2023

Istigfari, Salatin Annabi da tasbihi yana rage bacin rai, zafin zuciya da yawan ashar.
Allah Ya shiryar da mu 🙏

23/09/2023

Mu Koya Daga Al-Qur'ani.

SURATUL SHU'ARA'I
a lokacin da Annabi Musa A.S ya Fadawa Fir'auna Sakon Allah cewa"

أَنْ أَرْسِلْ مَعَنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ
Ma'ana:
Ka saki Bani Isra´ila tare da mu." ai ka sake su ka Dena Azabtarda su, su komo tareda mu.

Fir'auna yace"

قَالَ أَلَمْ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثْتَ فِينَا مِنْ عُمُرِكَ سِنِينَ
Ma'ana:
Shin, ashe ba mu yi renonka ba (Kai Musa) a cikinmu (ai, agidan mu) kana jariri, kuma ka zauna a cikinmu (ai,ka girma agaban mu) shekaru daga lokacin rayuwarka?"

Watau Fir'auna Yana yima annabi Musa Gori kenan, Kun San agidan Fir'auna Allah ya reni annabi Musa AS.

Fir'auna ya sake cewa"

وَفَعَلْتَ فَعْلَتَكَ الَّتِي فَعَلْتَ وَأَنْتَ مِنَ الْكَافِرِينَ
Ma'ana:
Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhali kai kana daga butulai?"
Ai ka kashe mana mutum duk da mu muka reneka, kana mai Mana Butulci da abinda muka.

Kun San ai Annabi Musa AS ya kashe wani bakibde a rashin Sani wajen kokarin ya Hana shi wannan bakibden Yin zalinci, to shine Fir'auna yake Goranta mishi da wannan abun.

Sai Annabi Musa yace"

قَالَ فَعَلْتُهَا إِذًا وَأَنَا مِنَ الضَّالِّينَ
Ma'ana:
Ai, Na aikata shi a lokacin ina daga masu jahilcin hushi." Watau ba da niyya na aikata hakan ba, ai tsananin Fusata da nayi ne lokacin da naga zai yi zalunci shine sai na Buge shi da hanu don in hana shi zalunci, a ta dalilin haka sai ya rasa Rayuwar shi amma bada niyyar in kashe shi nayi ba.

Sai Annabi Musa AS yace'

فَفَرَرْتُ مِنْكُمْ لَمَّا خِفْتُكُمْ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكْمًا وَجَعَلَنِي مِنَ الْمُرْسَلِينَ
Ma'ana:
Saboda haka (ne daga wannan lokacin sai) na gudu daga gare ku a lokacin da na ji tsoronku, sai Ubangijina Ya ba ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni."

Watau Annabi Musa Yana Qara Kiran Fir'auna da Tausassan Lafazi a domin ya karbi Sakon Allah, a domin ya fahimci cewa Allah ne ya Aiko shi ba saboda ya tuba ya Dena zalunci da bautarda banu isra'ila da yake yi.

To amma daga Qarshe de Fir'auna bayi imani ba sai de 'yan kadan daga mutane s

20/09/2023

GYARA KAYANKA BAI ZAMA SAUKE MU RABA BA

A yau Laraba Kotu zata yanke hukunci kan zaben Gwamnan jihar Kano tsakanin Abba na jam'iyyar NNPP da Gawuna na jam'iyyar APC

Zuwa gareka dan Kwankwasiyya: Idan an bayyana sunan Gawuna a matsayin wanda yayi nasara to kayi hakuri ka masa fatan alheri, ka zauna lafiya a gidanka ko gurin sana'arka

Idan kuma an tabbatar wa Abba Kujeransa kai dan Gawuna kayi hakuri ka zauna a gidanka ko gurin sana'arka, ka masa fatan alheri

Kun ga dai yadda aka fara jibge jami'an tsaro wanda ya hada da Sojoji da 'yan sanda, 'yan Demokaradiyya akan kare Demokaradiyyarsu zasu iya murkushe kowa, saboda babu Allah a tsarinsu, kar ka je kayi mutuwar banza

Ka sani cewa duk wani yunkuri da zakayi na tayar da hankali ba zaka taba ganin 'ya'yan Gawuna da 'ya'yan Abba da na Kwankwaso a gurin ba, saboda suna da hankali da wayo

Ka sani cewa Allah bai halicceka don kayi Demokaradiyya ba, Musulmi yana yin Demokaradiyya don ta zama laluri ne, amma ba tsarin mulkin da Allah da ManzonSa suke so bane, duk wanda ya rasa ransa don kare Demokaradiyya da wahala ya hadu da Allah lafiya

Muna fatan Allah Ya tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano da Arewa baki daya

Send a message to learn more

20/09/2023

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

GYARA KAYANKA MUHIMMANCIN ISTIGFARI 15:

1. Yawaita Istigfari yana sa qaruwar Arziƙi.

2. Yawaita Istigfari yana sa hasken fuska.

3. Yawaita Istigfari yana sa kusantar Allah.

4. Yawaita Istigfari yana sa kwanciyar hankali.

5. Yawaita Istigfari yana sa hasken zuciya.

6. Yawaita Istigfari yana sa buƙata ta biya.

7. Yawaita Istigfari yana sa fahimta.

8. Yawaita Istigfari yana sa warkewa daga cuta.

9. Yawaita Istigfari yana sa natsuwa.

10. Yawaita Istigfari yana sa sauƙin rayuwa.

11. Yawaita Istigfari yana sa riba a kasuwanci.

12. Yawaita Istigfari yana sa yardar Allah.

13. Yawaita Istigfari yana sa haihuwa ga mara ɗa'.

14. Yawaita Istigfari yana sa kariya ga mahassadah.

15. Yawaita Istigfari yana sa komai ya zama Alkhairi.

Ƴan uwa mu yawaita Istigfari, a zaune, a kwance, akan hanya, a tsaye, wallahi Istigfari babban makami ne, kuma babban mafita ne. Allah ya taimake mu, Allah yasa mudace duniya da lahira Bijahi Rasulillahi (S.A.W)🤲🤲🤲

Want your university to be the top-listed University in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Allah ya sassauta mana

Telephone

Website

Address


Abuja
SDG
Other Colleges & Universities in Abuja (show all)
Lincoln College of Science Management & Technology Lincoln College of Science Management & Technology
Lincoln Building Along Jikwoyi/Karshi Road, Jikwoyi
Abuja, 900110

We are now in Nigeria to offer purely practical courses to train you with the needed skills to earn money and get employed before you graduate. Installmental payment options and sc...

Aliyu Isyaku official Aliyu Isyaku official
Dutsinma Street
Abuja

This is a good page if you can join it you will be a smiler

MAZA MASU AJI MAZA MASU AJI
40/40
Abuja

Always open

De YOUNG Brakers De YOUNG Brakers
No 42 Sule Mai Ganga Street Un/sule Romi, Kaduna
Abuja, CHOICEBRIGGS

De YOUNG Brakers group is all about the youth, entertainment, awareness, informations, empowerment and culture. Young breakers we break through the challenges.

Abdallah wakilin so Abdallah wakilin so
Abuja

GOD USE ALL FOLLOWERS

IAAS Uof IAAS Uof
Abuja

Rayms1 Rayms1
Abuja

Vote vote Sputnik ultimate search contestants number 075 by Monday adams,stage name Rayms

Adeleke.Faruq Adeleke.Faruq
Onipetesi
Abuja

I.dark.in.complexion

Kicksmajor Kicksmajor
Kurami Bakori
Abuja

Assalamu alaikum.

Aliyu haidar Aliyu haidar
Zawiyya
Abuja

Caps pages