Kabiru Abdullahi Gidan Maɗinka
Nearby public figures
Zamfara
Samaru Area Gusau
No30 Tudun Wada Kwatarkwashi Road Gusau
Bypass Road
Gusau
All kind of male and female traditional and modern design in difference fashion style
MAFITA DOMIN INGANTA JIHAR ZAMFARA.
Jihar Zamfara na ɗaya daga cikin jahohin Najeriya masu albarkatun ƙasa. Jihar tana alfahari da tarin albarkatu masu yawa da kuma ɗimbin jama'a masu aiki tuƙuru da juriya.
Matsalar dake damun jihar shi ne shugabanci da halayen ƴan jihar wajen gyara kura-kuran da s**a yi a baya domin samun cigaba tare da sabunta cigaban jihar Zamfara da Al'ummarta don ɗorewar cigaba da inganta rayuwar jihar da kasuwancin ta.
Sauran sun haɗa da ƴan-fashi-da-makami dake zaune a daji da cikin-gari da ƴan-fashi-da-ƙwaƙwalwa dake amfani da siyasa wajen raba kan al'ummar jihar Zamfara, rashin aikin yi da kuma fatara a tsakanin magidanta da matasan da ke cikin ta.
Alkalumma na baya-bayannan da Hukumar Kididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar, ta sanya jihar Zamfara a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da s**a fi fama da talauci a Tarayyar Nijeriya, inda kashi 78% na mazauna jihar ake kallon matalauta ne (MPI, 2022). Don haka akwai buƙatar a samar da mafita mai ɗorewa ga wannan barazana.
Kasancewar gwamnatin Gwamna Dauda Lawal mai ci a yanzu, da kuma bayanin Mai Girma Gwamnan, na ceto da sake gina jihar Zamfara, akwai kyakkyawan fata daga al’ummar jihar da s**a yi, a bayan fama da rashin shugabanci da rashin kulawar shuwagabannin da s**a gabata, kamar yadda mafi yawan ƴan jihar ke gani.
Magani ɗaya ne, wanda ke buƙatar haɗin kai ga ɗaukacin al’ummar jihar Zamfara da nufin magance irin waɗannan matsalolin, tare da magance matsalolin da aka ambata a jihar, shi ne cigaban Zamfarawa.
NA FARKO:
Al'ummar jihar Zamfara su cire tunanin wofintar da su da ake akan wasu marasa kishi, da tayar da husuma a tsakanin al'ummar ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin jihar ta Zamfara, garin Gusau ya ƙunshi dukkan jinin ɗan jihar Zamfara, kuma har yanzu garin Gusau ƙauye ne, idan aka yi la'akari da wasu biranen jihohin ƙasarnan, kuma mu ƴan Gusau ba mu jin cewar mun fi kowa kamar yadda wasu ke yaɗawa, kawai ana son a raba kan Al'ummar jiharmu ta Zamfara ne.
Da wannan ne ake ƙoƙarin raba hankalin Zamfarawa saboda biyan buƙatar ƴan-jari-hujja, cigaba ba zai samu ba dole sai da haɗin kai na bai-ɗaya, mu haɗa kanmu domin kawar da gaba da tsana da ake hura wutarsu a tsakaninmu ta fuskar jingina ƴan Gusau akan kiran sauran ƴan'uwansu Zamfarawa da sunan ƙauyawa, wannan wofintar da hankali ne na ƴan jihar domin ƙyamatar da waƴanda za su tabbatarma su da ƴantacciyar rayuwa.
NA BIYU:
Babban jarin ɗan adam shi ne ilimi, fasaha, ƙwarewa da sauran halaye kyawawa da ke tattare a cikin al'umma ko ƙungiyoyin ɗaiɗaikun mutane waɗanda s**a gudanar da rayuwarsu don cigaban al'ummarsu, waɗanda ake koyi da su, ko mutum ɗaya jajirtacce don samar da ingantacciyar rayuwa ta fuskar ilimi, domin samarwa al'ummar jiharmu ta Zamfara ilimi tare da magance talauci domin samun cigaban tattalin arziki mai dorewa, da haɓaka ingantaccen tsarin aiki a cikin ilimi.
NA UKU: Samar da dai-daito wajen samun lafiya mai inganci ga kowanne ɗan jihar Zamfara.
(NA HUƊU: Ƙarfafawa matasa gwiwa don samun ƙwarewa da basirar ƙirƙiro hanyar dogaro da kai a ƙarkashin shugabanci na gari, domin halin da jihar zamfara ke ciki a baya, ya zama abin da ake kira jari-hujja, ta hanyar shugaba adili ne kawai mafita da ake buƙata don haɓaka ƙwazon al'ummar wannan jiha waɗanda su ne sinadaren sauye-sauyen al'umma, wannan ne zai haifar da yanayi mai ingaci, in da Zamfarawa za su samu damar haɓaka sabbin dabaru, ɗabi'u da nagartaccen ilimi wajen warware matsalolin da a ke fuskanta.
A ƙarshe Zamfara ta samu haziƙan matasa haziƙan mutane. Idan aka tashi tsaye, jihar za ta samu gagarumin cigaban bunƙasar tattalin arziki a kowane fanni na rayuwa.
A matsayin wani ginshiƙi na haɓaka tattalin arziƙi, ƙasashen da s**a cigaba da masu tasowa, suna ba da fifiko ga bunƙasa jarin ɗan'adam ta hanyar ba da lokaci da ƙoƙarin da ya dace. Za a karfafawa mazauna yankin gwiwa da su shiga cikin cigaban kansu tare da ɗaukarsu a matsayin masu ruwa da tsaki don cigaban jihar.
A karshe, za a yi amfani da dukkan hanyoyin da za su bi don ƙarfafa cigaban ɗan'adam a jihar Inahaa-Allah.
Allah Ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa.
Kabiru Abdullahi Gidan Maɗinka.
AL'UMMAR AREWA MUNA KOMA!!!
Da wayewar safiyar yau hankalin al’ummar Arewa ya kaɗu, ganin yadda ake juya masu baya, musamman kafafen sadarwa da s**a haɗa da Jaridun da gidajen Talabishin da suke yaɗa labarai, sun kawar da kai daga yaɗa zanga-zangar lumana da al’ummar yankin Arewa ke yi a kafafen sada-zumunta.
(Mu mutanen Arewa mun ji kunya)
(Abin da zai ƙara ba ku mamaki shi ne, mafi yawan ma’aikatan kafafen yaɗa labarai daga Arewa suke, musamman BBC HAUSA). har yanzu babu rahoton komai daga gare su, don nuna yanda ƴan'arewa ke neman yancinsu.
Yanzu ne ya kamata mu gane cewa matsalar Arewa ba komai ba ce face mutanenta. Wannan lamari ya ba mu kunya matuƙa, amma idan aka ce a yankin Kudu ake yi, kafin kowa ya sani sune za su yaɗawa.
Muna Allah waddai da Gidajen waɗannan ƴan-jaridun.
1st October
Ranar yanci Daga kangin Bautar Fararen Fata!
Zuwa kangin wasu azzaluman shuwagabanni Bakaken Fata.
Yaa Rabb Ka yi muna maganinsu, Ka shiryar da su, Ka canja muna su idan ba su da niyar shiryuwa.
Ka ba mu zaman lafiya da gamawa lafiya.
1-Zagin Yaro kullum nasa ya lalace.
2-Tsangwama ga Yaro na jawo masa rashin walwala.
3-Kushe Yaro kullum nasa shi ya raina kansa.
4-Kunyata Yaro nasa shi ya dinga dari-dari da kansa.
5-Koyawa Yaro juriya nasashi yazama mai
hakuri.
6-Idan ana yaba Yaro yakan tashi da kishin zuci.
7-Idan ana kyautatawa Yaro yakan sanyashi ya zama mai gaskiya.
8-Tarbiyya ga Yaro takan sanyashi ya zama amintacce.
9-Idan aka amince da Yaro yakan
sanyashi yaji dadi.
10-Sakin fuska ga Yaro shike jawo
shi cikin Jama'a. Saboda haka lyaye a
kiyaye.
Allah ya shirya mu da zuri'armu ameen.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the public figure
Telephone
Website
Address
Gusau
Gusau
We supply healthy and high quality Nigerian foods to Nigerians and Africans stores in Diaspora
Customs Road Tudun Wada Gusau
Gusau
ENTREPRENEUR Muslim🕋🕌 Hausa/Fulani👳🏻
T. P No 22 Tudun Wada Premier Road Behind Old Prison Service
Gusau, 860211
We are an agro processing company dedicated to provides ng high quality processed agro products.
No. 5 IBB Village, Unguwar Gwaza Gusau
Gusau, 632101
An bude wannan manhaja musamman domin yada karance-karancen addinin Musulunci dakuma isar da sako
Lalan Gusau
Gusau
🛍🛍A one stop shop for amazing Handbags•Sneakers•Slippers.Kidswear & more ☎️07012384055 📍Zamfara.
Shop 9, Gamzaki Plaza, Gamzaki
Gusau
*1ST GRADE (LIKE NEW) PRE-OWNED MEN'S, LADIES' AND CHILDREN WEARS *CAREFULLY SELECTED *PAYMENT VALIDATES ORDER *NATIONWIDE DELIVERY *1 WEEK STOCK PILING ALLOWED
Opposite NYSC Samaru
Gusau
Supply of the quality products for your consumption// honoured by UDUSOK// work hard and dreams big📌