Albaniy Babura

Albaniy Babura

Mun Bude Wannan Shafi Ne Domin Yaāda Da'awarMu Ta SALAFIYYAH�

17/02/2023

*SHEIKH ALBANY DA'AWA GROUP*

*_GODIYAR ALLAH_* {1}

Yaku bayin Allah! Allah madaukakin sarki Ya gaya mana cewa nuna godiya gare Shi, shi ne makasudin halittarmu. Allah yana cewa

وَاللَّهُ أَخْرَجَكُم مِّن بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ لَا تَعْلَمُونَ شَيْئًا وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

*(“Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikkunan iyayenku, ba da kuna sanin komai ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukata, tsammaninku za ku gode.”)*

Yaku bayin Allah! Kuma Allah Ya halicci dare da yini ne don a yi tunani kuma a gode masa Allah yana cewa

وَهُوَ الَّذِي جَعَلَ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ خِلْفَةً لِّمَنْ أَرَادَ أَن يَذَّكَّرَ أَوْ أَرَادَ شُكُورًا

*_(Kuma Shi ne Wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa ga wanda yake son ya yi tunani ko kuwa ya yi nufin ya gode.”)_*

Allah ya Kuma ya rarraba bayinsa zuwa gida biyu: Masu godiya da marasa godiya, sai Ya ce:

إِنَّا هَدَيْنَاهُ السَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرًا وَإِمَّا كَفُورًا

*_( “Lallai ne mu, Mun shiryar da shi ga hanyar kwarai, ko ya zama mai godiya, ko kuma ya zama mai butulci.”)_*

*_Allah Ya nuna Yana daukar masu gode maSa a matsayin masu bauta masa,_* wadanda kuma ba su gode masa ba su cikin masu bauta masa. Ya ce:

وَاشْكُرُوا لِلَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ

*_(“Kuma ku gode wa Allah, idan kun kasance Shi kuke bauta wa.”)_*

Sannan Allah Ya yabi Manzo na farko da Ya aiko duniya cikin fadinsa:

ذُرِّيَّةَ مَنْ حَمَلْنَا مَعَ نُوحٍ إِنَّهُ كَانَ عَبْدًا شَكُورًا

*_( “Zuriyar wadanda Muka dauka tare da Nuhu. Lallai ne shi ya kasance wani bawa mai yawan godiya.”)_*

Ina roqon Allah dacewa da shiriya zuwa kowane alheri, ga kaina da ku, lallai shi Allah mai iko ne a bisa kowane abu. Allah ya albarkace ni tare da ku da abin da muka ji na Alqur’ani ya gafarta mana zunubbanmu, lalle shi mai yawan gafara ne mai jin qai

*الله تعالى أعلم*

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_
*Telegram*

https://t.me/joinchat/SoaVkBryqONVNGyU8dDpLQ

DAKA *SHEIK ALBANY DA'AWA GROUP* GA MASU SAN SHIGA GROUP KO AIKO DA TAMBAYA ZASU IYA TUROWA TA WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA Ta *Whatsapp* 08179713163

03/09/2022
02/08/2022
Want your school to be the top-listed School/college in Jigawa?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Jigawa