Alfaidha Tijjaniyya Reporters

Broadcast & Media Production Company

Photos from Alfaidha Tijjaniyya Reporters's post 09/02/2024

YANZU-YANZU: Yanzu Haka Mutanen Garin Potiskum Dake Jihar Yobe Suna Gabatar Da Sallah Da Addu'o'i Don Neman Samun Saukin Tsadar Rayuwa

©Nigeria Reporters Hausa

03/02/2024

Kwalejin koyar da shari’a da ilimin Addinin Muslunci ta malam Aminu kano wato legal zata fara gudanar da karatun Digiri, wanda ta samu hadin gwiwa da kuma sahalewa daga jami'ar Gwamnatin tarayya ta Dutsenma dake jihar katsina akan kwasasa sai kamar haka:

03/02/2024

NAHCON ta Sanar da Kudin Hajjin Bana Duk da Hauhawar Dala.

Duk yadda Shugaban Hukumar Aikin Hajjin ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi yaso kudin Hajjin Bana kada ya haura abunda Maniyyata s**a ajjiye na naira miliyan hudu da rabi, farashin dala ya hana hakan ya kasance.

Shugaba Jalal Ahmad Arabi yayi iya yinsa don masu bada hidimomi ga Alhazai su karyar da farashinsu, hakanne yasa aka samu saukin da badan shi ba da sai farashin kujerar bana ya zama sama da miliyan shidda. Da yardar Allah sai kudin Hajjin Bana ya zama kamar yadda za a gani anan kasa:

Maniyyata daga Kudancin Najeriya za su biya: Naira miliyan hudu da dubu dari takwas da casa’in da tara wato (N4,899,000); Maniyyatan Arewa kuwa za su bada Naira miliyan hudu da dubu dari shidda da casa’in da tara wato (N4,699,000); Amma Maniyyata daga Jihohin Borno da Adamawa kuwa za su biya naira miliyan hudu da dubu dari shida da saba’in da tara watau (N4,679,000) don zuwa sauke Faralin shekarar dubu biyu da ashirin da hudu (2024).

Shugaban NAHCON na la’akari ne da wa’adin da Saudi Arebiya ta gindaya ne na ashirin da biyar ga watan da muke ciki na Febrairun Shekaran nan ya zama ranar da za’a rufe biyan kudaden.

Saboda haka ya zama dole Maniyyata su gama cikasa kudinsu kafin ko kuma kada ya gota ranar Litinin sha biyu ga watannan na fabrairu don NAHCON ta iya aike kudaden zuwa Saudiyya kafin cikar wa’adin da ta gindaya.

NAHCON na da azamar ganin an samu cikakkiyar nasarar gudanar da Hajjin Bana duk da kalubalen da ake dasu da kuma jinjinawa Musulman Najeriya saboda hadin kan da s**a bayar cikin wannan yanayi na rashin-tabbas da ake ciki.

Fatima Sanda Usara,
Mataimakiyar Darakta
Sashen Hulda da Jama’a,
NAHCON

07/12/2023

Za a gina gidaje a tudun Biri, da asibiti da makarantu da Solar don sama ma mutanen garin saukin rayuwa.
- Gwamna Uba Sani

05/12/2023

Afita muy zanga-zanga har sai anfito da Wanda s**ayi wannan ta'addancin, idan tsoron mutuwa kakeyi su Kansu biyosu tayi har gida.

05/12/2023

Jerin harin da sojoji s**a kai akan bayin Allah da basuji ba basu gani ba a Arewacin Najeriya:

A Maiduguri an ce kuskure
A Nasarawa an ce kuskure
A Benue shima kuskure
A Katsina an ce kuskure
A kaduna shima an ce Wai kuskure

Yo shi wannan kuskuren akan mu ('yan Arewa) kadai zai dinga faruwa ne?

Ya Muntaqimul Azizul Jabbaar duk Wadanda keda Hannu a Cikin Wannan Mummunan Hari na Ta'addanci da Aka kaiwa bayin ka a Kaduna Ranar Lahadi Kayi Daga² Kayi Dugu² Kayi Rugu² dasu Dan Arziqin Manxon Allah S.A.W

Allah kana Ganin Halin da Arewa ke Ciki, Rayukan mu an Maishe su kamar kiyashi, 'yan ta'adda Suna Kashe mu Inda S**a Gaza Jami'an Sojoji Suje da Kansu su Qarasa
😭😭😭😭😭😭😭😭

Ya Ubangiji Bamu da Wani Gata Sai Kai Kadai, mun kawo Qarar mu Gare ka, Allah ka Bamu Mafita Kay mana maganin Abunda ya Addabe mu, Ameen. 🙏

Muhammad Labaran Sadeeq Giwaa

04/12/2023

KUNGIYAR 𝐓𝐈𝐆𝐌𝐄𝐈𝐍 RESHEN JIHAR KADUNA BA ZATA LAMUNCI HARIN DA RUNDUNAR SOJAN NAJERIYA TA KAIWA MASU TARON MAULUDI A KADUNA BA.

Kungiyar ta 𝐓𝐢𝐣𝐣𝐚𝐧𝐢𝐲𝐲𝐚 𝐆𝐫𝐚𝐬𝐬𝐫𝐨𝐨𝐭𝐬 𝐌𝐨𝐛𝐢𝐥𝐢𝐳𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧 𝐚𝐧𝐝 𝐄𝐦𝐩𝐨𝐰𝐞𝐫𝐦𝐞𝐧𝐭 𝐈𝐧𝐢𝐭𝐢𝐚𝐭𝐢𝐯𝐞 𝐎𝐟 𝐍𝐢𝐠𝐞𝐫𝐢𝐚 𝐓𝐈𝐆𝐌𝐄𝐈𝐍 ta Bayyana Alhinin ta dangane da Harin ta'addanci da Rundunar Sojan Najeriya ta Kaiwa Al-umar Musulmi Mabiya Dariqar Tijjaniyya dake Gudanar da Bikin Mauludin Annabin Rahma S A W a Kauyen 𝐓𝐔𝐃𝐔𝐍 𝐁𝐈𝐑𝐈 Dake Karamar Hukumar Igabi, Wanda yayi Sanadiyyar Rasuwar Mutane 87 da Jikkatar Wadansu da Dama

Kungiyar tayi Kira ga Gwamnatocin Jihar Kaduna da ta Tarayyar Najeriya da Dukkan Hukumonin da Alhakin Harin ya rataya A Wuyan su dasu Gaggauta Daukar Matakai Kamar Haka:

1- A Fito da Wadannan 'yan ta'addan Jami'an Sojoji da S**a kai Wannan Mummunan Hari kuma a Hukunta su duka Duniya ta Shaida Irin Hukuncin da Akai Masu.

2- Gwamnati ta Gaggauta Biyan Iyalan Wadanda Aka Kashe Diyyar Rayukan Marigayan.

3- Gwamnati ta Dauki Kyakykyawan Mataki Wajen Kula da Lafiyar Wadanda S**a Jikkata Har Allah ya Basu Lfy.

4- Hukumar Sojan Najeriya ta Ja Kunnin Jami'an ta Don Kauce Ma Afkuwar Irin Hakan a Nan Gaba.

Idan Aka Sami Jinkirin Aiwatar da Wadannan Abubuwa Guda 4 to Wannan Kungiya Zata bi Dukkan Wasu Hanyoyin da S**a Kamata Domin Nema wa Wadannan Bayin Allah Hakkin Su a Hannun Koma Waye.

Sanin Kowa ne Cewa Mu Tijjanawa Mutane ne Masu Fafutukar Tabbatar da Zaman Lfy, Hadin Kai da Kawo Cigagan Wannan Kasa tamu Mai Albarka a Duk Inda Muke, Amma Wlh ba zamu bar Jinanen 'yan Uwan mu Ya tafi a Haka nan ba.

Daga qarshe muna qara Jaddada Kira ga Gwamnatin Tarayya da Hukumomin Soji da su gaggauta biyan Iyalan wadannan bayin Allah diyya,
Domin koda bisa kuskure ne kamar yadda suke fada bazai Hana biyan diyyar Rayukan su ba,

Muna Addu'ar Allah ya gafarta ma wadanda s**a rasu,
wadanda s**a Sami raunuka kuma
Allah ya basu lafiya Alfarmar Shugaba S A W.

~ Mahadi Sheikh Safwan ~
Stat

08/11/2023

𝐈𝐍𝐍𝐀𝐋𝐈𝐋𝐋𝐀𝐇𝐈 𝐖𝐀 𝐈𝐍𝐍𝐀 𝐈𝐋𝐀𝐈𝐇𝐈 𝐑𝐀𝐉𝐈'𝐔𝐍!!!
😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

On Behalf of the Management & entire Staff Of Alfaidha Tijjaniyya Reporters, I Sincerely Expressed My Condolence to the Family of 𝐌𝐀𝐔𝐋𝐀𝐍𝐀𝐇 𝐒𝐀𝐇𝐈𝐁𝐔𝐋 𝐖𝐀𝐐𝐓𝐄𝐄 𝐑.𝐓.𝐀 & Entire Followers Of Tijjaniyya Doctrine All over The World, Over the Passing Away of 𝐒𝐡𝐞𝐢𝐤𝐡 𝐌𝐮𝐡𝐚𝐦𝐦𝐚𝐝𝐮𝐥 𝐀𝐪𝐢𝐛 𝐒𝐡𝐲𝐤𝐡 𝐈𝐛𝐫𝐚𝐡𝐢𝐦 𝐍𝐲𝐚𝐬𝐬 𝐑.𝐀

The Son Of
𝐌𝐀𝐔𝐋𝐀𝐍𝐀𝐇 𝐒𝐇𝐘𝐊𝐇𝐀𝐋 𝐈𝐒𝐋𝐀𝐌, 𝐀𝐋𝐇𝐀𝐉𝐈 𝐈𝐁𝐑𝐀𝐇𝐈𝐌 𝐍𝐘𝐀𝐒𝐒 𝐑.𝐀

We Prayed that May Allah Elevate his Status among the guided People & look after the Family he left.

O Allah, Forgive Us & Him, comfort Him in his grave & Lighten his Stay {in the grave}

Ameen ya Arahmar - Rahimeen 👏👏👏

06/11/2023

𝐈𝐍𝐍𝐀𝐋𝐈𝐋𝐋𝐀𝐇𝐈 𝐖𝐀'𝐈𝐍𝐍𝐀 𝐈𝐋𝐀𝐈𝐇𝐈 𝐑𝐀𝐉𝐈'𝐔𝐍!!!
😭😭😭

Allah yayi wa Shahararren Malamin Addinin Islama Kuma Babba daga Cikin Shehunan Dariqar Tijjaniyya A Najeriya,
Sheikh Dr. Yusuf Ali Kano (Sarkin Malaman Gaya) Rasuwa.

Sheikh Dr. Ali Babban Masoyin Manxon Allah S A W Ne na gaske.

Allah ya gafarta Masa, ya Sada shi da Annabin Rahma S.A.W yasa Jannatoul Firdausi ce Makomar sa, ya kuma baiwa Iyalai, 'yan Uwa, Almajirai, Muridai, Masarautar Gaya, Jihar Kano da Dukkan Al'umar Musulmin Najeriya Haqurin Wannan Babban Rashi, Ameen

Alfaidha Tijjaniyya Reporterss

03/11/2023

Big shout-out to my newest top fans! Mahmood Ahmad Aliyy

03/11/2023

𝐁𝐔𝐃𝐀𝐃𝐃𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐆𝐀𝐘𝐘𝐀𝐓𝐀!!!

Gamayyar Zawiyyoyi da Kungiyoyin Darikar Tijjaniyya Dake fadin Jihar Kaduna

Suna farin cikin gayyatar al'umar musulmi zuwa wajen taron Addu'o'i ga yan uwanmu Musulmi dake Qasar PALASTINE wanda zai gudana kamar haka:-

𝐑𝐚𝐧𝐚: Lahadi 21 Rabiut - thany 1445AH - 5th November 2023.

𝐖𝐮𝐫𝐢: Masallacin Juma'a Kasuwan Bacci T/Wada Kaduna (Inda Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) yake Tafsiri).

𝐋𝐨𝐤𝐚𝐜𝐢 :9:00 zuwa 1pm

ALLAH yabada ikon halarta Ameen.

Allah ya Daukaka Addinin Muslumci da Musulmi, Ya qasqantar da kafirci da Kafirai Alfarmar Shugaba S A W 👏

Sanarwa:
TIJJANIYYA GRASSROOTS MOBILIZATION
(TIGMEIN)

Photos from Alfaidha Tijjaniyya Reporters's post 20/10/2023

𝐒𝐇𝐔𝐆𝐀𝐁𝐀 𝐃𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐀𝐋-𝐔𝐌𝐌𝐀𝐇
𝐆𝐨𝐯. 𝐄𝐧𝐠𝐫. 𝐀𝐛𝐛𝐚 𝐊𝐚𝐛𝐢𝐫 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟

A yau Juma'a 20/10/2023 Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Engr. Abba k Yusuf ya tura Rukunin farko na Dalibai 'yan Asalin Jihar Kano da Gwamnatin sa ta Dauki nauyin Karatun su Zuwa Kasar India.

Rukunin na farko Wanda ke Qunshe da Mutune 150 wadanda Ilahirin su 'ya 'yan talakawa ne, Sun tafi ne Domin Yin Karatun Digiri na 2 (Masters Deegree) A Fannoni Mabamban ta, tare da Bada $200 Domin Shan Ruwa a Hanya ga Kowannen su.

Idan Za'a Iya tunawa dai Gwamnatin tsohon Gwamnan Jihar ta kano Kuma Madugun Dariqar Kwankwasiyya, 𝐒𝐞𝐧. 𝐄𝐧𝐠𝐫. 𝐃𝐫. 𝐑𝐚𝐛𝐢'𝐮 𝐌𝐮𝐬𝐚 𝐊𝐰𝐚𝐧𝐤𝐰𝐚𝐬𝐨 ce ta Fara Qirqirar Irin Wannan Shiri a Baya Domin taimakawa 'ya 'yan talakawa Wajen Zama Wani Abu a Wannan Qasar dama Duniya Baki daya. Wanda daga Bisani Gwamnatin data gaji ta Kwankwason tayi watsi da Irin Wannan Shiri da aka qirqira Don Amfanar talakawan Jihar.

A Halin yanxu dai Gov. AKY Ya dawo da da yawa daga Cikin tsare² da talakawan Jihar ke Amfana dasu.

Hakan ne yasa da yawan 'yan Najeriya ke Ganin GOV. AKY Ya Zamo Zakaran Gwajin Dafi a Cikin Ilahirin Gwamnonin Najeriya Wanda talakawan Kowace Jiha ke fatan Samun Irin sa.

Tuni dai Da yawan 'yan Qasar S**a Fara yiwa GOV. AKY Laqabi da Shugaba Domin Al-ummar Sa.

Alfaidha Tijjaniyya Reporters

20/10/2023

𝐌𝐀𝐔𝐋𝐔𝐃𝐄𝐄𝐍 𝐍𝐀𝐁𝐈𝐘 ﷺ

𝐄𝐧𝐠𝐫. 𝐃𝐫. 𝐑𝐚𝐛𝐢'𝐮 𝐌𝐮𝐬𝐚 𝐊𝐰𝐚𝐧𝐤𝐰𝐚𝐬𝐨 Na Farin Cikin Gayyatar "yan Uwa Musulmi Masoya Annabi Muhammadu S A W Zuwa Wajen taron Mauludin Shugaba S A W A Gidan sa dake Miller Road Kano

Gobe Asabar 6 Rabi'u thani 1445AH
21/10/2023

ALLAH ya kaimu ya bada Ikon zuwa, Ameen.

20/10/2023

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un
😭😭😭

Allah Yayi wa 𝐌𝐀𝐆𝐀𝐉𝐈𝐍 𝐆𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐙𝐀𝐙𝐙𝐀𝐔 𝐀𝐦𝐛. 𝐌𝐚𝐧𝐬𝐮𝐫 𝐍𝐮𝐡𝐮 𝐁𝐚𝐦𝐚𝐥𝐥𝐢 Rasuwa.

Kafin Rasuwar Marigayin Shine Jakadan Najeriya a Kasar Morocco, Haka kuma shine Magajin Garin Zazzau na III. Kuma Qanine Ga Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli CFR

Allah ya gafarta Masa yasa Jannatoul Firdausi ce Makomar sa Damu Baki Daya, Ameen.

15/10/2023

KWAMITIN MAULIDI NA

ZAWIYYAR YAN'ALEWA DAURA

SUNA FARIN CIKIN GAYYATAR AL'UMMAR MUSULMI ZUWA WAJEN MAULIDIN FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

KARO NA ASHIRIN DA TARA (29)

WANDA INSHA ALLAH ZAI KASANCE KAMAR HAKA

RANA: JUMA'A 12/04/1445 DAIDAI DA 27/10/2223
LOKACI: 9:30 ZUWA WAYEWAR GARI
WURI: ZAWIYYAR YAN'ALEWA DAURA

ALLAH YA BADA IKON HALARTA

SANARWA DAGA:

SAUTUL FAIDHATI ALTIJJANIYATI LIZAWAYA DAURA

13/10/2023

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN

Allah ya yiwa Sanata Dr. Bello Maitama Yusuf CON, ( Sardaunan Dutse ) rasuwa yanzun nan a birnin Kano ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Allah ya jiƙansa da rahama ya gafarta masa.

04/10/2023

Innalillahi wa inna Ilaihi Raji’un

Muna Jajanta ma Iyayen Dalibai da aka dauka a makarantu dake Jahar Katsina da Zamfara dama sauran yan uwanmu da ake daukan iyalansu a fadin wannan kasa,
Allah ubangiji ya kubutar dasu.

Muna kira ga Shugabannin da abin ya shafa da suyi kokari wajen ceto wadannan bayin Allah, domin an Zabe su ne don su kare Rayuka da dukiyoyin Al’umma kuma sunyi Alkawarin hakan tare da rantsuwa da Qur’ani, to lalle su sani Allah zai tambayesu akan Alkawarin da s**a dauka.

Sannan Sauran Al’umma wajibinmu shine muyi ta Addu’a duk bayan Sallolinmu da niyyar Allah ya cecesu su koma ga iyayensu, Allah kuma ya kawo mana karshen wannan fitina a kasarmu Albarkan Manzon Allah S A W.

Sayyadi Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi

Photos from Alfaidha Tijjaniyya Reporters's post 02/10/2023

HOTUNA: Dubban Al'umar Musulmi ne s**a Halacci Gagarumin taron Maulidin Annabi Muhammad SAW a Babban dakin taron na Minar E dake Lah**e Pakistan don Murna da zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammadu ﷺ.

Allah ya kara daukaka addinin Musulunci da musulmai, ya kara mana soyayyan Annabi ﷺ. Ameen 🤲

02/10/2023

YANZU YANZU: Al'ummar arewa, sunyi ƙira ga BBC Hausa kan cewa Nan da awanni 24, idan basu ɗora zanga-zangar lumana da al'ummar Arewacin Najeriya da Sukeyi ba a shafukan su na sada zumunta, zasu daina bibiyar labaran su mai gaba ɗaya.

Wani ƙira zakuyi wa BBC Hausa...?

30/09/2023

Online Maulid ❤️
Idan Kana Cikin Masu Farinciki Da Zuwan ANNABIﷺ To Kafaɗi Ɗaya Cikin Dabi'un Sa.

Photos from Alfaidha Tijjaniyya Reporters's post 29/09/2023

CIKIN HOTUNA: Yadda 'yan uwa musulman Kabilar lgbo s**a yi zakayen murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad S A W

Allah ya karawa annabi Daraja

29/09/2023

Dan Takaran Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar Ya Taya Al'ummar Musulmi Murnar Maulidi

Murnar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW) duk 12 ga watan Rabi'ul Awwal na nufin tunatar da juna game da koyarwar sa a tsakanin mu musulmi sannan Kuma mu nuna muhimmancin bin koyarwar.

Saboda haka, yayin da muke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad S.A.W a yau, dama ce a wurin mu don mu Kara jajircewa game da yada akidar zaman lafiya da kuma cikakken tawakkali ga Allah.

Saboda haka, Ina taya al'ummar musulmin Najeriya da sauran sassan duniya murna game da Maulidin Ma'aiki na wannan shekara. Allah Ya dawwamar da zaman lafiya ga dukkan al'umma. Ya kara mana soyayyar Annabi Muhammad. S.A.W. Ameen. -AA

26/09/2023

29/09/2023

Kamfanin BUA na taya Al'umar Musulmin Duniya murnar maulidin Annabi Muhammadu ﷺ

29/09/2023

Hukumar NITDA na taya Al'umar Musulmin Duniya murnar maulidin Annabi Muhammadu ﷺ

29/09/2023

Yau rana ce mai matuƙar muhimmanci ta samuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW), wanda ya tafiyar da gabaɗaya rayuwarshi wurin koyar da zaman lafiya da ƙaunatar juna.

Ya kamata mu mayar da kowacce 12 ga watan Rabi'ul Awwal a matsayin ranar da za mu yi bitar rayuwa da mu'amalarmu. Annabi Muhammad (SAW) ya h**e mu da mu ƙaunaci juna, hatta ga maƙiya. Shi samfuri ne na soyayya kuma rahama ga dukkan halittu.

Wannan ranar ta Mauludi, dama ce da zamu ƙara ƙaimi da addu'ar zaman lafiya a wannan jiha tamu mai albarka ta Zamfara da ma Nijeriya gabaɗaya.

Barka da zagayowar Ranar Mauludi.

His Excellency Gov. Dauda Lawan Dare,
Executive Gov. Zamfara State, Nigeria
27/09/2023

29/09/2023

Hukumar ƴan sandan Najriya na taya Al'umar Musulmin Duniya murnar maulidin Annabi Muhammadu ﷺ

28/09/2023

𝐈𝐧𝐧𝐚𝐥𝐢𝐥𝐥𝐚𝐡𝐢 𝐖𝐚 𝐈𝐧𝐧𝐚 𝐈𝐥𝐚𝐢𝐡𝐢 𝐑𝐚𝐣𝐢'𝐮𝐧
😭😭😭

Yanzu nake ganin mummunan labarin rasuwar manyan ƴaƴan Sharif Rabi'u Usman Baba, Sharif Muhammad Fatihu da Sharif Hassanu a Sakamakon Hadarin Jirgin Ruwa da S**ay a kan Hanyar su ta Zuwa Wajen Mauludin Annabi Muhammadu ﷺ

Allah tabaraka wata ala ya haskaka qabarinsu Allah yasada su da Masoyn mu Annabi Muhammadu ﷺ ♥️❤️

Intamu tazo Allah kasa mu cika da Imani Albakacin Manxon Allah ﷺ ♥️♥️

Photos from Alfaidha Tijjaniyya Reporters's post 25/09/2023

DA ƊUMI ƊUMI:

Ɗaruruwan Al'umman
Musulmine s**a halarci taron Maulidin Manzon Allah (SAW) yau Litini a Birnin Madinatul Munawwara tare da buga handiri gami da rera yabon ma'aiki masu ratsa zuciya.

Alfaidha Tijjaniyya Reporters

21/09/2023

ZURU 1445/2023

21/09/2023

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah ya yiwa daya cikin matan Khalifa Sarkin kano Muhammad Sunusi na daya. Hajiya Mariya Sunusi (Ya Delu) rasuwa, mahaifiyar Malam Isa Sunusi pilot.

Allah ya jikan ta da rahma ya gafarta mata Amin

Want your business to be the top-listed Media Company in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Masha ALLAHALLAH Ya Saka wa Sarki Khaleefah Sir Muhammad Sanusi II da Alkhairi,

Telephone

Address


No. 001 Zawiyya Giwa, Giwa L G
Kaduna
Other Media/News Companies in Kaduna (show all)
KSMC KSMC
#1 Wurno By Rabah Road
Kaduna, 800101

Kaduna State Media Corporation (KSMC) has a vision to make KSMC a world class media organization with a mission to provide compelling broadcasting services in a fully digitized en...

24 hours news 24 hours news
Anguwan Rimi
Kaduna

Anguwan rimi kaduna

DC HAUSA.com DC HAUSA.com
Bandirawo City
Kaduna, 123456

labaran duniya

Ecotech Fuelless/Noiseless Technology Ecotech Fuelless/Noiseless Technology
Kawo
Kaduna, 46543

This ecotech fuelless generator is a new source of power that is completely safe free ,durable and e

Hausa Blog News TV Hausa Blog News TV
Kagoro Road Sabon Garin Tudun
Kaduna

Hausa Blog News TV, karanta sabbin labarai . Manufarmu ita ce mu samar muku da labarai a cikin sa'i, da sa'i, da kuma isar da bayanai masu dacewa waɗanda ba su da son zuciya.

Military Gist/News Military Gist/News
Kawo
Kaduna, 60000

Iswap/BokoHaram/Bandits Gossip

Hankaka News Hankaka News
Kaduna, 2234

Domin Samun Ingantattun Labarai.....

AL IHWAN hausa AL IHWAN hausa
Kaduna

wannan shafin,an Samar da shine don isarwa alumma ingantattun labaru.

ATP Radio ATP Radio
Art Ikara
Kaduna, SHOWMAN

independent Magazine, ATP Radio

Hadiza Gabon Hadiza Gabon
Malali
Kaduna

Film production

BalooJr Media BalooJr Media
Kaduna

This page is to enlighten, educate,inform and entertain the audience through the media.����?

Celebrity news Celebrity news
Kaduna

Latest amebo and news of celebries