Asshifa'a medicine store
WE SPECILIST WITH TRUST AND HONEST
ALL PRAISE BE TO ALLAH
BAMBANCIN GIRMAN BREAST TSAKANIN MATA
┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈
Taswirar girma, zubi da tsari na Nonon Mace ya ta'allakane ga zubin jigidar halittar ta na gado (genetically) wanda shiyasa duk ƴan gida ko ƴan ɗaki ɗaya da wuya kaga ba irin zubin nonon su guda ba, zai wahala.
A nan ina magana ne akan Nono karan kansa. Bawai batun Nono ɗaya yafi ɗaya ba, wannan nasha faɗa is normal asami hakan ai ɗarin bawani significant bane can.
__________________________________
Saide a game da zubin duk nonuwan: Mu sani
1. Yanayi na gado (Heriditary)
2. Shekarun Mace (Age)
3. Yanayin cimar da Mace ke samu (Nutrition)
4. Adadin haihuwar datai
5. Shayarwarta
6. Samuwar Juna biyu da kuma,
7. Yanayin yadda jiki ke samarwa da kuma sarrafa sinadarin estyrogin dake mamaye cigaban ƴan matantakarta
Duk waɗannan Abubuwan Bakwai '7' kowanne ɗaya nada tasiri game da yadda zubin Nononta zai ko kuwa ya kasance.
__________________________________
▪️Haka zalik girman breast ka iya canzawa lokacin haila, ana iya ganin su qara tasowa saboda a lokacin estrogen ya hauhawa, don haka ana iya ganin haka a Mace ya zamto lokaci-lokaci kaga k**ar breast din na caccanza wa.
▪️Hak**a lokacin goyon ciki wato juna biyu girmansu kan ƙaru da kuma bayan haihuwa yayin shayarwa.
▪️Wani lokacin Zubin nada alaka ga ƙibar Mace da kuma yanayin motsawar sha'awa duk s**an canza.
----------------------------------------------------------
🔴 Haka kuma cimar Mace, idan Mace bata samun isashshen abinci ko me inganci toh hakan zaisa jikinta yake qone kitsenta domin samar mata da kuzari kadda ta cutu, toh breasts shi kuma dama wadace yake da kitse (fats) wanda akarshe wannan fats din na daga wanda zai zaizaye domin hanta ta sami abinda zata samarwa mutum kuzari.
Kunga kenan shiyasa a masu ƙiba ma ake ganin suna dashi har yana neman fin karfin su tare da sanya su ciwon baya ko kafadu saboda excess fats. Shi yasa kuma Mace koda bata da ciki in kwai cima me kyau zata iya samun wadatattu.
----------------------------------------------------------
🔴 Shayarwar bata zubar da nono abinda ke faruwa galibi shine yayi shayarwa dama ya bude duk bututun fitar nono sun bude toh bayan anyi yaye toh shine s**an Motse su koma yadda suke, shi kuma nonon sanda ya cicciko yayin shayarwa dama yai stretching fatar nonon shyasa sai aga k**ar ya zube amma yadda yake haka yake. Saide wani abu guda a ƙarƙashin haka shine: in aka hada shayarwa da zama da yunwa toh kunsan nace jiki na qona fats don haka hakan zaisa aka sun qara zamowa k**ar jaka sunyi qas saboda ruwa ya ɗauke kuma ɗan kitsen duk jiki ya konesa saboda babu diet.
----------------------------------------------------------
🟡 Akwai kuma wanda haka kurum suke tun a halittar su sun sami matsala ko naqasun tsokokin dake haifar da girman nono wato hypoplasia kurum a zagwanye suke saboda babu tsokokin wadace sai yan kaɗan, irin wannan kan kasance da kananun nono kuma koda daga baya wajen shayarwa jariri kan fuskanci karancin nono, wasu kuma duk da kankantar nono still aga daya ya ɗan ɗara ɗaya, ko ya zamto kowanne ya ware gefe da gefe ansami fadin kirji a tsakaninsu.
Saide da yawa ba'a gane Mace nada hypoplastic breast sai bayan ta sami juna biyu ko haihuwa, domin ana iya ganinsu kanana amma juna biyu na samuwa kuma daga nan ainishin girmansu zai fara bayyana wanda daga nan kuma shikenan gaba sai mace ma tazo taji k**ar tana neman kai dasu.
Haka still Mace ka iya kasancewa tana da kananun nonuwa kuma take samar da isashshen ruwan nono, duk normal ne.
__________________________________
Kananun nono bai nuna larura har sai ta tabbata na larurar ne, hakan kuma yasa duk wani maganin ƙarasu da za ai amfani dashi ba lallai kowacce inta yi ta sami hakan ba. Domin wasu nasu Heriditary ne.
__________________________________
Hakanan a likitance bamu da wani Maganin sa girman nono! Illa iyaka idan larura ce da tasa jikin Macen bai samar da sinadarin estrogen toh wannan munsan bama nono ba kwai sauran matsaloli da dama domin ko haila ma masu irin wannan kan kai shekara 18 basu ganta ba, sai an nemi daukin likita.
__________________________________
Amma baya ga wannan abinda likita kurum zai iya shine shawartar mutum ya rika ta'ammali da abinci ko abubuwa masu estrogen,
MISALI: Mata da yawa kan amfani da hulba (fanugreek) ko a likitance munsan tana da estrogen so bamu da case da hakan, saide ko yaushe tsaftace hannu ko abin shafawar, babu wani hatsari a likitance amma de kwai hatsarin mastitis inba a tsaftace komi ba, kada kwayoyin cuta su shiga kafar nono a sami rauni agun djn taɓa samun case irin hakan ta faru dalilin shafa man ko massage da ruwan saboda saka ci.
Ko shan madara ta waken suya, karas, fennel seeds, gyaɗa da sauran abubuwa masu estrogen.
__________________________________
Ko kuma final resort shine Breast Augmentation "SURGERY" Idan duk irin wancan recommendation ɗin bai samar da result ba. Wanda galibi dama inde irin nonuwan da ake karanta muku ne ko kuke gani a videon turawa toh dama LIFT ne.
Eh mana duk breast implant ne, Kuma ku tambayi kanku mana inda da akwai wani maganin asibiti na qara girman Nonuwa waɗannan p**n stars ɗin, da celebrities ɗin dake cikin mawaƙa irinsu: Nicky, Kardashians, ds. babu abinda zai kaisu under the knife ana musu lift tare da qara CC Volume ɗin ana basu manyan breast ko kuma Butt Lift.
Wannan shine! so take it easy ƴan Mata, wani nonon sai bayan haihuwa, wani kuma haka kurum yake sai hakuri inde ba lift za ai miki ba. Karki bari depression ya k**aki.
┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈
A ƁANGAREN MAZA
Haka dukkan Maza ya dace kusan wancan bayanin na sama kuma, domin kukan musgunawa Mata da ingiza Mata cikin garari iri-iri saboda kallon finafinan batsa da aka riƙa yi, da karatuttukan shafuka marasa inganci da sahihancin bayani dake karanta abu ba a yadda yake ba.
Haka kurum Mutum duk yazo ya tsani matarsa babu gaira babu dalili.
Wa ya gaya maka nonon ƴan p**n natural nono ne? Duk asibiti suke zuwa mana, manyan kudaɗe suke biya ai musu Breast augmentation me kyau, In zaka iya biya aiwa Matarka shikenan.
__________________________________
Muna wata rayuwa ne da yanzu anfi fifita abunda ya bayyana wanda ido zai gani ya yaba ko yaji daɗi fiye dana ɓoye wato FAME (fem).
Mazaje yanzu basa shakkar kushe Matansu, ko kyararsu, ko kunyatasu ko kwatanta su da wata matar abokin su dalilin canzawar zubin jikinsu.
Don haka ko yaushe kake nazari kaga dawa kake tare? Wasu Matan tuni shekaru sun hau kansu, wasu kuma sun hayyafa ta inda bazai yiwu su taɓa komawa yadda ka santa daren farko ba.
Haka inka lura ai yanzu wasu ta haifo gasunan gabanku da yanzu suke nasu zamanin ƙila.
----------------------------------------------------------
Tsanar Mace bayan ta fara kwana biyu ke nuna tun farko koda ba'a rigima tsakanin Mata da Mijin tode kwai alamun rashin fahimtar juna zama de kurum ake gashinan.
Idan kun fahimci juna toh duk yadda jikin Matarka ya canza sai kasan ya zakai ka farfado da wani abu dake baka gamsuwa da ita a duk yadda take, Ba kuma zaka wulakantata ba domin kaima kasan ba haka kake yanzu k**ar baya ba.
__________________________________
Domin ni nasani kwai cikin Maza wadanda sam basu damu da kansu ba ballantana su kula, ƙazanta bakomi bace gani suke inde sun watsa ruwa shikenan alhalin hatta wankan sun mance cewa shima iyawa ne. Ballantana azo tsaftar al'aura da sauransu, kai ka damu da breast amma zahiri ita kukan zuci take duk sanda ka nemeta, kurum biyayyar aure take amma bata jin komi dakai.
Me kokarin gaske ce ma ke nuna k**ar tanajin daɗin wani abu don karka tsargu musamman inkana kyautata mata.
__________________________________
Sai de ta wani ɓangaren duk da hakan, baya ga kallon surar kirjin wasu Matan da mazan keyi suji nasun sun gaza... Ku kanku Matan kune ke buɗe kofar hakan lokutan da dama, Mata da kanku ke zubar da Mutuncin Mata ƴan uwanku, tare da wulakanta junanku ta hanyar rubuce rubucenku.
Inka duba youtube duk wani video dake bayanin jima'i ko rubutaccen novel na fitsara zaka ga Matan ne Authors, suke rubutawa ko ɗora videon ba Maza ba. Ba ruwan Maza da wannan aikin, na kuma ƙalubalanci duk me ja akan hakan.
Don haka please mui hakuri da juna, wani abun hakuri ake ba bukatar sai an korafi, a duk rayuwar guda nawa ce? sai saura.
----------------------------------------------------------
✍🏻
[Ibrahim Y. Yusuf]
🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬🥬
CIKINA WATANSA BIYAR, SAIDE HAR RUWAN NONO NA YA FARA ZUBA, SHIN MATSALACE LIKITA ??
☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘
Zubar ruwan nono irin wannan kan iya zamowa normal physiologic response, duk da leaking din ruwan nono irin wannan anfi ganinsa ko tsammaninsa a watanni 2 na karshen ciki (wata 8 zuwa 9).
A likitance ma munsan a wata 4 na ciki nono ka iya fara zuba...
Don haka ana iya gani a wata na 5 wato watanni ukun tsakiya (2nd trimester) duk da ba kasafai ake ganin hakan ba.
Akwai ruwan nonon da ake kira colostrum wanda ke ba jariri kariya da kara karfafa garkuwar jikinsa. Zai iya kasancewa mace taga kalar nonon fari qar ko kuma ruwan dorawa-dorawa wato yellow.
:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Don haka inde nonon da ake gani ba kalar jini-jini bane🧋, nonuwan ba kuma wani kullutu aciki dake sa suna yin matsanancin ciwo, ko kuwa ganin alamun fatar nonon tai ja ko kan nonon ya tsage ko ya karkace... kurum de zuba yake toh bawani abun damuwa.
Amma insuna ciwo ko ganin ruwan dake fita alamun jini jini, ko fari k**ar ruwa hade da dan jini toh wannan ne abun damuwa sai anje anga likita tukun.
Amma k**ar yadda nace in kurum ruwan nonon ne ke zubowa wani lokaci musamman yayin jima'i ko sanda take cikin motsawar sha'awa... ko in anta6a matashi, ko in ana zaune kasan fanka tana kadawa hakan babu wani matsala. Kai koda haka kurum nema in anyi aiki angaji.
::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::
Sannan bama a mai ciki ba, hatta a mai shayarwa musamman wacce ta yaye yaro amma nonon yaki tsayawa yake mata nono toh dukkan ku Inhar zubar sosai nonon yake, yana kuma 6ata muku kaya, gami da saku kuna karni.... zaku iya amfani da ganyen kabeji 🥬
Ku sami kabeji ko ganyensa inda hali asa a freedge yadda zai dau sanyi. Ko cikin randa inkuma duk ba hali sai ai amfani dashi a yadda ya samu amma de a wankesa tukun....
Daga nan sai mace ta yagi daidai girman wanda zai rufe kan nonon rijif k**ar yadda hoton kasa ya nuna... sai adau rigar nonon atareshi da ita, abarsa har zuwa wasu mintuna 40, ko awa 1 koma awa 2 ya zamto de sai kinji ya jike da zufa toh sai acire. Kya iya canza wani a lokacin ko ki bari sai anjima ki kara sa wani. Kar kuma ake takure bra din... abarta saisa-saisa yadda bazata dameki ba.
Ake yin haka sau 3 yini, safe, rana, yammah aita yi kurum har zuwa lokaci ko kwanakin da ya tsaya ya dena zubar. Wasu ma galibi aranar farko suke ganin ya tsaya.
Sannan lokaci lokaci in mai ciki ce ke ki rika cin ayaba🍌 duk sanda aka sami dama koda kwaya 1 ce amma ba dole.
Yadda zaku saka gashi nan k**ar yadda yake a hoton nan. Babu bukatar magani ko tada hankali. In namiji ne kaga sakon kana iya sanar da matarka ko yar uwarka, ko wata dakasan tana da bukatar sanin hakan.
Ko yaushe karku karanta rubutuna saboda kuji dadinsa... a'ah kuke kokarin ilmantar da wanda baiji ba, hakan shine ribata ba likes ko comments ba. Aiki da abun don Allah
Fatan kun ilmantu.
Da Zaran Matsala Ta kunno Kai A Zamantakewar Aurenku Ko Soyayyar Ku Kuyi Amfani Da Waɗannan Hanyoyin:
SHARE 🔵
Soyayya na gaskiya a kullum aci samun matsalar ake. Zaman aure yana tattare ne da matsalar zamantakewa. Duk wasu ma'aurata ko masoyan da aka gani sunada tasu matsalar.
Sai dai kuma rashin iya amfani da dabarun shawo wannan matsalar tsakanin masoya ko ma'aurata yake sa karamar matsala ta dawo babba. Ko kuma abunda zasu gyara da kansu sai su bari har wasu suji.
Idan har matsala ga gifta tsakanin masoya ko ma'aurata, ga wasu hanyoyin da zaku bi domin sasanta kanku da kanku.
1: Kada guda ya hana guda fadin abunda yake damunsu a lokacinda aka samu bacin rai.
Haka nan yunkurin cewa dole sai guda yayi magana a lokacinda bai da bukatar hakan saboda bacin rai ba dace ba.
Akwai mutanen da idan aka bata musu rai basa iya magana. Wasu ma so suke su rabu da wajen. To idan masu irin hakan ne kada guda yace zai takurawa gudan dole yayi magana ko ya tsaya ko zama.
Kawai barshi ko ka barta tayi abunda take ganin zai sa zuciyarta ya samu sanyi.
2: A Lokacinda aka batawa guda rai cikin masoya ko ma'aurata. Mai laifin ya nuna tausayawa da nadamar abunda yayi. Hakan zai sanyayawa wanda aka bata jin sauki.
3:Kada masoya ko ma'aurata s**e dole sai guda ya amsa laifinsa kamin maganar ya wuce. Akwai hanyoyin da mutum yake yarda yayi kuskure ba tare da ya furta ba.
Neman dole dole sai ya amsa laifinsa kamin a bar maganar nan ma neman karawa matsalar tsawo ne.
4:Kada samun matsalarku ku daina yarda da juna.
Babu wanda yafi karfin yayi kuskure, idan wannan shine karo na farko na aikata laifi sai a yiwa juna uzuri ya kuma yafiwa juna a wuce wurin.
5: Duk da kun samu matsala da juna, wannan ba yana nufin zaku daina ganin mutuncin juna bane. Dole ne ku ci gaba da girmama juna bayan sulhu.
Babban matsalar da ake samu ga masoya ko ma'aurata idan sun samu matsala shine na rashin baiwa juna dama domin kowa ya saurayi kowa. Hakan nan wasu bamasa tinkaran junansu domin tattaunawa sai kawai guda ya k**a gasa da guda. Wanda hakan kara rura wutar matsalar hakan zai yi.
Zama a tattauna akan matsalar daya kunno kai a tsakanin masoya ko ma'aurata shine yake karawa matsalar girman zama babba.
Don haka muddin ana bukatar a cigaba da rayuwa da juna, kada a boyewa juna kuskure, laifi rashin fahimtan da aka samu.
Abinqi ga miji
Abubuwa_guda uku miji ba ya daukarsu daga matarshi kuma ba ya iya hakuri a kai, don haka ki kiyayesu!
1- Daga mishi sauti.
2-Girman kai da jin ke wata ce, da mayar masa da magana idan yayi fushi(yana fada kina fada), da kin ba da hakuri.
3-Ya rasa so da kauna a gurinki, nuna mishi halin ko in kula, ba ruwanki da tarairaya....
Idan kika zama haka to lallai dole zai nemi duk yanda zai yi ya samu mafita daga wannan bala'en naki ya samu wacce za ta maye wadancan guraban da kika bari!
Allah_ta'ala Yabawa Ma'aurata hakurin zaman tare tare da kykywar fahinta atsakaninsu
Kamin Kiyi Ciki Ka Sannan Wadannan Abubuwan:
SHARE 🔔
Mata musamman sabbin amare ko kuma wadanda suke da burin haihuwa nan gaba ma'ana haihuwar farko. Yana da kyau ku fahimci wadannan abubuwan tun kamin cikin ya shiga domin kada ya zo muku da mamaki ko ban tsoro da fargaba.
Wadannan abubuwan kuwa sun hada da:
1: Sauyin Jiki
2: Keda zuwa ganin likita kun kulla
3: Kada Ki Yawaita Matsala Da Mijinki
4: Zaki Daina Shan Taba Ko Giya (Ga mata masu sha).
5: Zaki Kauracewa Gurbatancen Muhalli Da Kuma Gujewa Waje Mai Doyi.
6: Zaki Rika Neman Shawarwari Wajen Wadanda S**a Taba Hahuwa.
7: Zaki Rage Cin Abincin Dake Saka Kina.
8: Kiyi Kokarin Neman Tarihin Gidanku Yadda Ciki Da Haihuwa Yake Zuwa Muku.
9: Zaki Daina Shiga Tsafgar Da Zai Jawo Miki Bacin Rai.
10: Zaki Daina Sha'awar Cin Wasu Ci Maka.
Duk macen da take shirin daukan ciki yana da kyau ta san da cewa zata shiga wadannan har ma da wasu daba mu kawo ba a matsayin sabon rayuwar ta har sai bayan ta haihu.
Masu neman Haihuwa Allah Ya basu. Muda muke dasu Allah Ya shiryemu da abunda muka haifa.
Wasu Abubuwa Da Ya Kamata Duk Namiji Ya Sani Game Da Mace:
SHARE 🔔
Mata wasu halitta ne da s**a bambamta ta ko ina a hali da dabi'u da maza. Amma abun mamaki wasu mazan basu fahimci hakan ba.
Wasu mazan suna tunanin ganin mace tayi mu'amala dasu ne a irin fahimtarsu. Wanda hakan yasa maza suke yawan samun matsala da zaran sun soma mu'amala da mace.
Ga wasu halaye da dabi'un da mata suke da su da ya k**ata kowani namiji ya fahimcesu.
1: Mata Sunada Gaggawa: Mata halitatta ne da suke da gaggawa a rayuwarsu. Idan suna bukatar abu basuda jimirin hakurin jiran lokacin abun. Hakan yasa suke aikata wani abun daga baya kuma su dawo suna nadama.
2: Da Son Ransu Suke Auna Abu: Mata basa amfani da hankali wajen auna lamari.
Ita mace muddin abu ya kwanta mata arai to duk abunda za a fadamata akan wannan abun bazata saurara ba.
3: Kalamansu Idan Sun Fusata: Maza da dama sun kasa fahimtar kalaman da suke fitowa daga bakin mace a lokacinda ranta ya baci basu da tasiri a zuciyarta bayan ta huce.
Mace tana iya furta ko wani irin kalma ga mutum a lokacin da ranta ya baci ba tare da la'akari da illar kalmar ba. Amma tana wucewa kuma ko a jikinta. Kai data furtawa kalmar kana kunci ita kuma har ta manta abunta.
4: Bata Saurin Baiwa Namiji Yadda: Mace tana daukan lokaci kamin ta amince da namijin daya nuna yana sonta. Sai dai kuma da zaran ta amince masa babu mai iya bakanta shi a wajenta ta yarda.
5; Batason Wanda Take So Yayi Nisa Da Ita: Mace idan tana son namiji batason yayi nisa da ita. Idan kuma yayi nisa da ita bata samun natsuwar cewa a inda yake bada mace yake ba.
6: Basa Mantuwa: Yana da matukar wahalar gaske mace ta manta abunda kayi mata na alheri ko sharri. Don haka duk namiji ya kula da abunda zai yiwa mace ko zai furta mata.
7: Idan Tana Sonka Matsala: Wani halin da mata suke da shi shine akan soyayya. Idan mace tana sonka masifa ne. Haka idan mace na kinka bala'i ce.
Saboda tsabar son da mace take maka zata iya kasheka ko ta turaka gidan yari. Haka ma idan tana kinka.
8: Game Da Kyauta: Mace idan kana yawan mata kyauta tana maka ganin wawa musamman idan wani abu bai taba shiga tsakaninku ba. Mata suna matukar son mutumin dake musu kyauta, musamman idan sunada ra'ayin namijin.
9: Kambamata: Duk muninn mace tana so kace mata tanada kyau. Babu wani kalmar dake saurin saka mace farin ciki irin ka cemata tana da kyau kuma bata tsufa.
10: Jima'i: Mace na sha'awar Jima'i ne kadai da namijin datake so ba k**an maza ba. Namiji zai iya Jima'i da macen da baya so domin ya kwantar da sha'awar sa. Mace sha'awar ta na motsawa ne kadai idan tana tare da wanda take so.
Wadannan wasu halayen da dabi'un mata ne daba duk maza s**a sansu ba.
❤️RAYUWAR MA'AURATA ❤️
ZAMA DA MIJI
Kixama Mai kirkiro firar daxai yi nishadi Kuma kisa shi dariya😀👌Amma ke Koda kinajin dariyar karkiyi kiboye Taki xakiga Yana kallonki Yana nishadi Yana kashe Ido to ke Kuma Kara kashe voice dama so k**e kwalliya ta biya kudin sabilu
🌲🌸🌲🌸🌲🌸
By admin 🖍️
MAGANIN GIRMAN GABA,DA KARFIN MAZA:
🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌
SHARE ⏰
Yadda zaka magance matsalar inzali da wure shine ta hanyar amfani da maganin gargajiya na asli wanda babu kwaya a cikin sa,domin samun ingantaccen kuzari na har abada.
Wannan hanya zata magance maka matsalar raunin gana saurin inzali dàttin mara.
Citta mai kogo 🌾.
Namijin goro 🌰.
Tafarnuwa 🌰
Kanumfari 🍂
Yadda za'a hada shine idan aka samo namijin goron sai a busar dashi sannan a samu yayan citta mai kogo, se asamu tafarnuwa da kanumfari a hada a dake sosai.
Zaka iya zubawa a cikin zuma ka rika shan chokali 1 sau biyu a rana.
Za kuma ka iya sha a cikin nono ko madara ta ruwa chokali 1 sau biyu a rana.
Tsawon sati 2,amma kafin ka fara ganin aikin sa,sai kayi k**ar tsawon kwana 3 kana sha,domin yana bin jiki ne.
SHARADI!!!
🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌🍌
Idan Har Kataba samun kanka a Istimnai wajibine Kanemi maganinsa kafin amfani da wannan hadi. Bazeyi aiki ba matukar Kataba Istimnai.
Ma'anar Istimnai
Amfani da Hannu ana wasa da AL'aura ko kallon abubuwan batsa dan biyawa kai sha'awa.
Me Bukatar Hadadde aimana magana +2348037538596 or m+2348066627317. Kota WhatsApp ne, Zamu aikoma har Jihar da ake Bukata ta hannun direbobi.
Wasu Kalamai Guda 15 Da Duk Namiji Na Son Jinsu Daga Bakin Matarsa:
SHARE ⏰
1: Na aminta da Kai
2: Nayi Sa'an miji
3: Ina alfahari da Kai
4: Ina matukar sonka
5: Ina son ina tare da Kai a kullum
6: Kaine farin cikin rayuwata
7:Yi hakuri
8: Ina marmarinka
9: Ina kewarka
10: Na gode
11:Allah Ya Kara budi
12:Ka iya kwaliya
13:Ka kula da kanka
14: Bazan iya rabuwa da kai ba
15: Daren jiya daban ne
AMFANIN ALBASA GA LAFIYAR DAN'ADAM
Ga kadan daga cikin amfanin ta:
1. Albasa tana taimakawa ga mutumin da yasuma idan aka fere ta aka sanya masa a kafar hancin sa yana shaka, in shaaAllah zai samu tashi in ba ta ajali bace.
2. Albasa na taimakawa wajen warware ko magance matsaloli irin su farfadiya, ciwon zuciya, ciwon ciki, ciwon suger, asthma, ulcer ta kirji, shock musamman idan aka hada ta da tafarnuwa.
3. Albasa na taimakawa masu matsalar bugawar zuciya heart attack idan suna yanka ta danya suna ci a abinci.
4. Albasa tana maganin daskerewar Jijiyoyin jini na zuciya.
5. Albasa tana taimakawa masu ciwon sugar wajen warkarwa musamman a samu babbar albasa ayi kwadon lansir da ita aci kullum.
6. Albasa tana taimakawa masu Hawan jini da masu matsalar zagayawar jini.
7. Albasa idan aka saka ta cikin Zuma amma sai an yanka ta kullum aci su a haka tana maganin zazzabi, mura, ko ciwon makogwaro, masu ulcer da matsalar urinary tracts infection ma suna iya chi kullum in shaaAllah za a samu lafiya.
8. Albasa na maganin ko taimakawa wajen maganin ciwon Kai na gefe ko daga goshi, idan aka kirba ta ko ita kadai ko da tafarnuwa aka sanya a inda kan yake ciwon.
9. Wanda Zuma, ko cinnaka, ko kunama ta harbe shi shima za a sama sa wannan a daure da bandage in shaaAllah za a samu lafiya.
10. Albasa tana tsaida habo a rika shakar garin ta ko haka nan a sanya ta a hanci arika shakarta.
11. Albasa na taimakawa wajen narkar da abinci.
12. Albasa na taimakawa wajen warkar da kunar wuta idan aka kirba ta aka dora akan kunar akwai zafi amma za ta bushe ba za ta tashi ba kuma za ta warke cikin kankanin lokaci da yardar Allah.
13. Albasa tana zama rigakafi ga mata wajen Cancer nono, hanji, da cututtukan mahaifa.
14. Albasa tana magance matsalar Jijiyoyi.
15. Albasa na taimakawa wajen magance matsalar amosanin kashi.
16. Albasa na magance yawan ciwon ciki na yara, musamman yellow din idan aka yanka ta slices aka tafasa ta sai a tsame idan ruwan ya huce aba yaro cokali daya karami duk bayan hour daya.
16. Albasa na taimakawa wajen magance matsalar cunkushewar kirji idan aka kirba ta aka hada ta da man kwakwa aka juye a cikin towel aka daure kirji da shi aka sanya t-shirts da za ta matse kirjin zuwa wani dan lokaci a cire ayi wanka.
17. Albasa tana taimakawa wajen magance matsalar tari, idan aka samu babbar albasa sai a raba ta biyu a sanya brown sugar akan ko wace sai a bar su zuwa hour daya sai a cinye duka sau biyu za ayi a rana.
18. Albasa tana taimakawa wajen magance matsalar ciwon kunne, idan aka kirba ta aka samu k**ar safa ko tsumma ko towel aka saka a ciki aka daure sai a dora akan kunne din da ke ciwon, an samun lafiya in shaaAllah.
19. Albasa tana tsayar da jini idan aka samu yankewa kuma za ta zama k**ar antiseptic za ta kare fata daga kamuwa da wasu cututtuka a dalilin raunin. Kokuma ayanka albasa daya cikin container a zuba zuma a rufe k**ar da daddare zuwa safe a tace sai a rika shan 5ml sau uku a rana idan babba ne.
20. Albasa tana fitar da guba daga jiki misali ko zazzabi ko mutum yaji jikin sa ya kasa gane masa ko in kana so ma kaji canji a jikin ka to ka jaraba wannan.
21. A samu albasa daya a yayyanka ta slices amma kanana sai a hada man kwakwa Mai kyau sai a jera a kasan tafin kafa sai a samu farin kyalle ko bandage fari saboda ina son aga irin dattin jiki da za a fitar sai a daure kafar sai asa safa sai a kwanta da safe idan aka tashi sai a cire za a ga abubuwa ayi haka k**ar kwana bakwai za aga dattin na raguwa kuma jikin ana kara samun lafiya ko kuma ana kara jin dadin sa. Adaure a jaraba wannan kowa ma yana iya yayi.
22. Albasa na taimakawa wajen magance matsalar amai, asamu farar albasa ko yellow sai a matseta wato ayi juice din ta sai a zuba cikin tea na na'a na'a cupi daya amma a bari sai tea din ya huce sai asha cokali biyu kanana na tea din na'a na'a bayan minti 5-10 sai asha juice din albasa din Shima cokali biyu kanana sai kuma bayan minti 5-10 asha tea din na'a na'a din haka dai har a daina aman in shaaAllah, don yana daukar k**ar minti 20 kafin aman ya tafi duka.
23. Albasa tana tsaftace Gurbataccen iskan da muke shaka, idan aka yanka ta slices sai a ajiye a kusurwar daki ko gida duk wata bacteria ko virus da iskan ya kwaso zata cire ta da yardar Allah.
24. Albasa tana maganin ko hana cizon kwari idan aka sata a jiki.
25.Albasa tana hana zubewar gashi idan aka kirba ta aka kara ruwa kadan a rika wanke kai da shi duk sati sau daya.
26. Albasa tana hana kwari cin shuka ko flowers idan akayi feshin ta.
27. Albasa tana hana gara cin kaya.
28. Sanya albasa a jiki na hana fata kuraje.
29. WHO hukumar lafiya ta duniya ta amince da amfani da albasa wajen jinyar matsalar tari, ciwon huhu, ciwon na kirji, cunkushewar kirji, mura dasauran wasu matsaloli.
Allah ya kara muna Lafiya.
SHARE 🤶👴
Kasan cuwar mu na ‘yan adam a doran ƙasa, Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu. Saboda haka samarin da suke ƙoƙarin ganin mallakan zuciyar ‘ya mace ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyin guda takwas da ake bi don sace zuciyar budurwa.
1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.
2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya k**ar ɗawisu.
3. KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin duk wata ‘ya mace, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge budurwa.
4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar da ba ta fi rana ɗaya ba, ko kwana biyu a ce kana zuwa ganin ta ko kuma kana kiran ta, idan ya yi yawa ne a ce kun haɗu sau uku. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare. Wani lokacin idan haɗuwa ta yi ƙaranci sai ka kirata a waya. Amma fa ka sani yawan zuwa gun mace ko masoyiyarka ce wani zubin nasa gundura. Ma’ana za ta ji duk ta gaji da ganin ka, musamman idan ya zama soyayyar taku ba ta yi ƙarfi ba.
5. KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN ƘAWAYE: Ka guji yawan kula yarinya cikin sahun ƙawayenta ko kuma cikin jama’a. Hakan zai karama kima, sannan da nesan ta kanka ga barin wulakanci. Wata kila lokacin da ka je mata cikin jama’a ko ƙawayen ta, ta ji tana son ka. To amma watakila a lokacin shigar da ka yi bai yi mata ba. Hakan zai sa ta guje ka, wanda yin haka a soyayya wulakanci ne ga masoyi.
Mafi kyawu shi ne ka jira ta keɓance ko kuma ta koma gida. Idan ba haka ba, to sai dai idan sun kai koda su biyar ne, to kuma ya zama dole ku kasance ku biyar koda sauran ba sa san ‘yan matan. Saboda su kasance masu ɗauke masu hankali a lokacin da kuke hira kuma suma sauran ‘yan matan yin haka zai nuna cewa wadda kake so ba ta fita daban a cikin su ba. Duk abin da sauran ƙawayenta s**a ce a kanka da shi za ta yi amfani.
6. BARKWANCI: Idan ka kasance mai raha ga masoyiyarka to nan da nan za ka sace zuciyarta. Misali ka riƙa ce mata a duk lokacin da ka zo hira da ita, amincin so gareki ya tauraruwan zuciyata, ɗaya tamkar da goma cikin sahun mataye, a do da kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zukata fara’a. gimbiya adon ‘yan mata. Da sauran su. Kana mai ambaton haka cikin murmushi da shauƙi irin na soyaya kuma dole ne hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a soyayya muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.
7. KUƊI DA KULAWA: Mata suna son samun saurayi mai tashen kudi da kulawa cikin bukatunsu a koyaushe. Idan ta samu wanda ya haɗa waɗannan abubuwa kuma ya tafiyar da su yadda ya k**ata, to abu ne mai sauƙi ya sace zuciyar budurwa. Akwai mazan da suke roƙon ‘yan matansu kuɗi; wannan ba soyayya ba ce, sai a kira shi a kwaɗayi.
8. KYAUTATAWA: Sai dai kuma duk da na yi bayani kan cewa kwaɗayi bashi da kyau a soyayya, hakan ba shi yake nuna ba za ka kyautatawa masoyiyarka ba. Hasali ma idan kai haka, to za ka ƙara ƙarfin shaƙuwa ne tsakanin ku da juna. Sai dai idan za a yi kyautaa duba me masoyiya take da buƙata a daidai wannan lokaci. Misali, kar ka kawo mata hoda a lokacin da take buƙatar turare, atamfa, yayin da ita kuma leshi take so.
Sanin haƙiƙanin abin da budurwa ke so, ko da ku fara soyayya da ita, ko ba ku fara ba, yana taimakawa ƙwarai wajen sace zuciyarta.
Samfurin Kalaman Soyayya
Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda k**e so na. Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata.
Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin cikina. Ina nan riƙe da amanar soyayyarki har ƙarshen rayuwata. Na saka a raina ba zan taɓa mantawa da ke ba.
Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke ƙawatu wa da kallonsa, hanci ya ji daddaɗan ƙamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba.
Jin daɗi da walwala ba za su taɓa samuwa a tattare da ni ba matuƙar babu soyayyarki a cikin zuciyata.
Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke lambun zuciyata
A DAURE A KARANTA PLEASE
Watarana wani Gaye neman auren wata baiwar Allah a wani gari. Duk lokacin da yaje hira takan kawo mishi ruwan sha a jug.
Rannan da yaje hira sai kakar ta tace: "yau ga kunu mai daɗi na damawa angonah maza ki kaimar kice inji Amaryar shi ce ya sha".
Haka kuwa akayi tazo ta tambayeshi tace: "yau kaka tamaka kunu mai daɗi wai idan zaka sha".
Gayen yayi murmushi yace mai zai hana ni sha?
Sai ta koma cikin gida ta ɗauko wa gayen kunun, da tazo daf da zata tsuguna ta ajiye kunun a kusa dashi saita zame ta fadi ƙasa jug din kunun ya suɓuce a hannunta inda kunun ya zuba a jikin gayen ya ɓata mishi wata sabuwar galilar shi mai tsadar gaske.
Hankalin budurwar ya yi matuƙar tashi akan ta ɓata mishi kayan shi. Budurwarnan tama rasa meye zata cemar. Shi kuma gayen tsabar ɗokin yadda yake sonta ko ajikinshi hankalin shi yana kanta ne yana cewa da ita: "sannu my dear, inadai bakiji ciwoba sannu ko, yanata kokarin dagata da rarrashin ta".
Da ya tayar da ita taga yadda kunun ya ɓatamar kayanshi taje ta debo ruwa tana zubamar tana bashi hakuri yana wankewa ita kuma hankalin ta a tashe.
Gayen yaga yadda ta ɗaga hankalin ta cikin murmushi sai yace mata: "haba sweetheart! Meye hakane kam so k**eyi ki ɓatamin rai? Don kunu ya zube a jikina shine k**e wani kuka, gaskiya ki daina kada raina ya ɓaci". A haka abun yawuce k**ar ba'a yiba.
Bayan wani ɗan lokaci sai Allah Ya yi aurensu, inda har s**a samu karuwan yara.
Watarana maigidan yadawo daga kasuwa zai ci abinci. Baiwar Allah taje ta kawo mishi abinci ta ajiye, saita ta koma dauko mishi ruwan sha. Da ta dauko mishi ruwan shan daman ya tuɓe garen shi ya ajiye a kan kujera, sai cikin kuskure garen ya harde kafar matar ta faɗi kasa har goshin ta yafashe ruwan data riƙo a jug ya zube a jikin maigidan nata.
Nan take maigidan ya miƙe ya murtuƙe fuska yana muzurai k**ar wani kafiri, k**ar wanda acid ta zuba mashi a jiki. Ya nata bambami bai damu da taji ciwon ba yana: "ke dai wallahi bansan ranar da zakiyi hankali ba, kwata-kwata baki da nitsuwa a rayuwarki, idan banda wawta da rashin hankali meye zai jawo haka? Ke dai kam Allah Ya yi wadaranki wallahi jaka kawai".
Karshe dai ɗan wannan abunda yafaru sai da maigidannan ya saki matar tashi akan ta zuba mishi ruwa sanadiyyar hardewa da tayi ta faɗi kasa.... 😢 😢 😢
Yan'uwa masu hankali, mu dubi yadda wannan al'amari ya faru da idon basira, Mu yi nazarin wannan abin da idon basira, lokacin da yake nemanta da aure, kunu ne mai zafi ma tazubamar a jikin sabbin kayanshi kuma a layi bama a gida ba ammana koya damu harma nuna wa ya keyi ae bakomai, ta daina damuwa. Amman sai gashi bayan sunyi aure, ordinary ruwa wanda bamai zafi ba ya zama k**ar ruwan dalma ko acid. Mu dubi wancan lokacin inda damuwar shi ina dai ba taji ciwo ba, amman yanzu ga goshinta na jini koya damu dajin ciwon nata shi dai kawai ta zuba mishi ruwa a kayan shi tamar laifi.
Yan'uwa maza masu hankali, ya k**ata mu gyara, ya zamto soyayyar bawai a layi aka baro ta ba, a kaita gida shi yafi dacewa.
Allah Yasa masu irin wannan halin su gane su gyara su tuna cewa umurni ne Allah Ta'ala Yayi na a kyautatawa mata inda Yake cewa: ".... Wa ashiruhunna bil ma'aruf".
Allah Ya mana jagora Ya bamu ikon Kyautatawa Ameen
Abdullahi ✍️
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Contact the practice
Telephone
Website
Address
Opening Hours
Monday | 09:00 - 11:00 |
Kano
Kano, 700322
We sale and deliver branded and unbranded drugs, medical equipment, food items and all other needs
Zawaciki Layin Primary
Kano, 517
Munbude wannan shafi ne domin taimaka wa Yan uwa masu fama da larure larure da jinyace jinyace Da matsaloli kala kala k**ar hawan jini ciwon sugar matsala
Gwarzo Road, Kabuga Underpass, Opp. Batayya Plaza/NAPEL Filling Station
Kano
Remarkable Drugs, Remarkable Care. Your Health, Our Mission.
Kano, 261222
It's our goal to help men who experience ED overcome this hurdle at an affordable cost.
No 1 AM Panda Street Badawa Layout Kano
Kano
A private nutrition firm that is well-equipped and provide nutrition and wellness serves to all