Nr. Umar Magaji

Nr. Umar Magaji

You may also like

Med Awemi
Med Awemi
Kabir
Kabir

Health Talk /NGO Job opportunities/Scholarships /Artificial intelligence (Ai)

27/04/2024

52 days to Facebook monetization.

Type and check if it turns blue . It simply means you're able to earn money.

24/04/2024

LURA DA LAFIYAR JIKI BAYAN AN HAIHU ABU NE MUHIMMI
🤱🤱🤱🤱🤰🤰👨‍🍼🧑‍🍼🧑‍🍼🤱🤱🤱🤱

Babban hatsarin da haihuwa ke zuwa dashi dake jawo asarar rayukan Mata bayan haihuwa shine zubar jini bayan haihuwar wato Post Partum Hemorrhage a likitance dake faruwa a stage na uku na haihuwa. Wannan shine lokacin da dariya ke rikidewa ta koma kuka, murna ta koma ciki, daga murnar haihuwa akoma kukan mutuwa.

____________________1___________________

Sau tari wanda bai sani ba zai dauka fitar jariri daga jika shine haihuwa lafiya kuma shine mafi mahimmanci. Inaaaa sam wannan bashine haihuwa lafiya ba. Haihuwa lafiya shine aga bayan fitar yaro Mahaifa ta cigaba da murdawa tare da harbawa wato contracton ta yadda hakan zai sanadiyar fitowar placenta wato (mabiyiya ko abunda hausa kance uwa ta biya).

Kai wani lokacin koda uwa ta biya akwai bukatar sai mahaifa ta cigaba wannan harbawar... idan bata harba ba hakan bazaisa jijiyoyin jini su toshe ba don haka mace zata ci gaba da zubar da jini. wanda wannan shike kashe Mace. Wani lokacin hatsarin placenta din ce ma ke manne mahaifar ta yadda in aka jawo saide ta taho hade da mahaifar ta tidota inba ai da gaske ba mutuwa yanzu yanzu ce a irin wannan lokaci. Shiyasa haihuwa tsallake siradi ce ba karami ba.

________________________________________

Toh abunda zai taimakawa wannan harbawar na uterus tayisa shine ai maza maza ai stimulating nonon mace, shyasa wani lokacin ma in mace na naquda akan iya bukatar akawo yaron da take shayarwa domin ya k**a nonon hakan zai taimaka wajen contraction din mahaifarta, ko kuma inba yaro ace mijinta ya tsaya ya rika k**a nononta, inbabu duk daya saide nurses sui mata.

Toh waccan hikimar ta stimulating ni**le nada matukar mahimmanci har bayan haihuwa, wannan tasa game kallon finafinan likitoci na haihuwa zakuga da anciro yaro cikin jininsa da komi za'a dora ma uwa shi ya k**a nono domin ya taimak**ata yasa mahaifarta harbawa domin jinin haihuwa ya tsaya... wannan shine hikimar skin to skin da mukeyi, nan da nan zakuga likitoci sun dorasa a nono... saboda hatsarin daka iya biyo baya.

Haka zalika wannan jinin haihuwar duk da anfi ganin zubarsa nan da nan bayan haihuwa cikin awa 24 na yini... Haka zalika kananun ma'aikatan lafiya kusani yana iya faruwa tun daga bayan kwana 1 da haihuwa zuwa sati 6.... Matukar Macen da akasan ta haihu kasa da sati 6 tazo asibiti da complaint na zubar jini to kusani yana iya kasancewa Post Partum Hemorrhage har sai In kun gano wani abun daban... don haka a lura dakyau, kar adau zubar jini matsayin ba serious abu ba don kurum kila anyi satuttuka da haihuwa ko kwana 3 uku.

𝑨𝒎𝒎𝒂 𝒅𝒆 𝒅𝒖𝒌 𝒅𝒂 𝒉𝒂𝒌𝒂𝒏 𝒃𝒂 𝒂 𝒄𝒆𝒘𝒂 𝒂𝒏 𝒉𝒂𝒊𝒉𝒖 𝒍𝒂𝒇𝒊𝒚𝒂 𝒔𝒂𝒊 𝒃𝒂𝒚𝒂𝒏 𝒌𝒘𝒂𝒏𝒂 40 𝒔𝒂𝒏𝒏𝒂𝒏 𝒕𝒂𝒌𝒆 𝒈𝒖𝒂𝒓𝒂𝒏𝒕𝒆𝒆

___________________2____________________

Haka zalika koda baki fuskanci matsalar zubar jini ba ki daure ki shayar da babynki hakan zaici gaba da sa mahaifarki harbawa ta taso daga mararki ta koma kasan cikinki cikin sati 2 da haihuwa, hakan zai rage miki tsananin ciwon mara duk da shayarwa kwai zafi wani lokacin.

________________3_______________________

Matsayinki na Mace bayan haihuwa kisani kazanta ba taki bace, baki daya tsaftarki data bandakinki da dakinki dole ki nunkata, Walau C/s akai miki ko kuwa normal da kanki kika haihu it does'nt matter.

Musamman tsaftar Mara, matse-matsi zuwa farji, dubura, kada ki wasa, saboda kinga a lokacin kina fitar da abunda muke kira Lochia wanda ake kira jinin nifasi.... wannan na dada saki vulnerable to infection. Sannan ki guji amfani da kayan matsi na matan nan da sauransu, duk da bakwaji inma ya zama dole toh karde ki kuskura kiyisa akasa da sati 12 na haihuwarki, inma bazaki iya bari ba kenan. Saboda in ma kinki muna jiye miki tsoron endometritis ko sepsis, septicemia na iya ajalinki.

________________4_______________________

Kina iya yin wanka koda aranda akai miki c/s ne, saide ya zamto kina da kayan dressings duk sanda kikai wanka gurin ya jike ki zaune ki cire audugar, da bandage din ki wanke gun da iodine ki canza sabon dressing din gun shikenan.
Inbaki da kayan yin hakan toh ki guji jiqa gurin ake kebesa in anzo wanka. Sannan duk bayan kwana 3 kya iya zuwa aduba ko anemo ma'aikacin lafiya ya duba; ade tabbatar gurin baya fidda ruwa inma yana ruwa toh atabbatar bame jini-jini bane. Saboda gudun samuwar surgical site Infection da yana iya sa kwayoyin cuta suita cin fatarki ahankali suna qarawa gurin girma kizo ki shiga masifa. Ki lura da duk wani canji da zaki gani agun, karki kasa aguiwa kima likitanki waya ki bayani

__________________5_____________________

Galibi bayan haihuwa cikin Mata kan bude, kwai cin abinci... Babu komi hakan bazaisa ki nauyi fiye da kima ba muddin kina shayarwa, nauyinki bazai canza daga yadda yake ba lokacin da k**e kafin ki ciki abaya.

_________________6______________________

Bayan kwana 3 zuwa 5 da haihuwa galibi nono ke fara cika tsir-tsir ya rika ciwo. Koda sha yaro yake yana zafi... don haka ba matsala bane ki rika matse wani kaso ba saboda ki sami relief.

Kada duk sanda kikaji ciwo kice dole sai jariri yasha nono alhalin ya koshi, wannan kesa su yawan tumbudi. Muddin kikaji jaririnki yana gyatsa tare da yawan tsilla fitsara hakan alamace ta kyakkyawar shayarwa don haka in nono na miki ciwo dalilin cika k**e matsewa kina ragesa ki zubar.

_________________7______________________

Wasu kanji ana cewa shayarwa na hana daukar ciki abunda ake kira lactation amenorrhea wanda hakan ke a amatsayin k**ar hanyar planning, amma abunda bakusani ba shine sai macen dake shayar da yaro akalla duk bayan awa 4 zuwa 6 ce ke samun wannan benefit din, wato akaikai akalla sau 6 zuwa 7 arana.

SANNAN kusani hakan na tasiri ne kurum tsawon watanni 6 kacal, wato adadin watanni Exclusive freeding, domin ga wacce ta cika watannin haihuwa cif ovulation dinta na dawowa ne bayan sati 6, wacce ta haifi bakwaini kuma ovulation dinta na dawo mata bayan sati 4, yayin da wacce tai bari ovulation na dawo mata bayan sati 2.

Don haka daga wata 6 saide ki za6i hanyar planning daban walau magani ko de wata hanyar, inkinga baki sami ciki ba toh bakya ovulating kin taki lucky ne kurum. Amma maganin ma na plannin banda shan COMBINATION PILLS Muddin kina shayarwa saboda zasu kawoma shayarwa matsala, zasu hindering milk production dalilin estrogen, saide ki amfani da magani mai progestin kawai... don haka kananun ma'aikatan lfy fatan zaku kiyaye wannan.

__________________8_____________________

Ciwon nono ba bakon abu bane galibi saboda bacteria din da ake smau asaman fata dakan shiga ta kafar nono ko ta nitsa cikin fata idan akwai karancin tsafta. Shyasa nake cewa ki gama ba yari nono kurum kija sale6ar bra din ki mayar, A'a ki samu tissue ko towel ki dangwali ruwa ki goge kan nonon sannan ki mayar, haka shima jaririn kinsa ruwa ki share masa nasa bakin.

Sannan idan kan nono ya tsage muddin yana miki ciwo karki azabtar da kanki cewa dole sai kinba yaro ya k**a ahaka. Ki bashi dayan... shi kuma mai tsaguwar ki rika matse ruwa daidai da wanda ake sha kina zubarwa, Is normal.

___________________9____________________

Koda babu tsaguwa abunda ke jawo muku ciwo yayin shayarwa shine; dorawa jariri iya kan nono ya k**a. Inde zaki ke dosana masa ni**le dole kiji zafi, Ar**la wannan sahin duhun baki daya shine zaki tabbatar labbansa na tabawa, shi jariri bada lebe yake jawo nono ba... shyasa mace dake shayarwa koda mijinta zaice zai k**a nononta ya tsotsa saide taji zafi bazai ta6a iya zuqowa ba dan besan ya zai ba yazo amma in jariri ya k**a sai kaga har biyo kumatunsa yake. Don haka ki samu contact me kyau har gemun jaririnki yake dungurar nonon

___________________10____________________

Zaki iya shayar da jaririnki har shekaru biyu. Hakan zai baki kariya daga ciwon cancer nono data sassan haihuwa, tare da kiyayeki daga hatsarin kamuwa da ciwon jijiyoyin jinin zuciya [coronary artery dx]

Kai kuma megida ka nuna karamci asamo mata kayan marmari da fruits🍌🍋🍊🍉🍇🍏🍓🥬🥒🥭🍍 da nama akai-akai musamman hanta har sati 6 bayan haihuwa.

__________________11_____________________

Kuskure ne baiwa mace maganin dakatar da zubar ruwan nono. Kusani physiologic process ne don haka akoya ma macen dabaru, inciwo yake abada maganin ciwo. Amma banda basu hormonal drugs don Allah akiyaye kwai illa karkuje ku lalata musu pituitary gland ku kashesu da ransu, domin shikenan kurum hakan na faruwa mace ta dena haila, ta den ovulation, ta dena jin sha'awa, ta dena komi irin na mutane rayuwarta ta zama maleji. Akwai abunda ke kira sheehan syndrome abunda ake gudu kenan. Ashir dinku da bawai mace maganin tsaida ruwan nono saide in kasan kai gynecologist ko medical doctor ne.

__________________12____________________

Galibi abunda na kance ga masu zubar ruwan nono shine; suke ragesa ahankali suna shan maganin rage zogi Irinsu ibuprofen.

Inkuwa yaye zatai ko kuwa jaririn ne ya mutu... toh a samo kabeji madaidaici... inda hali asa cikin freedge yadda zai dau sanyi. Ko cikin roba ko randa sai asaka ice block... inkuma duk ba halin ķanqara ko freezer sai ai amfani dashi a yadda ya samu amma de a wankesa tukun.

Daga nan inyai sanyi saiki yagi ganyen daidai girman wanda zai rufe nononki rijif k**ar yadda hoton kasa ya nuna...

Saiki dau rigar nononki ki mayar wato kitareshi da ita, musamman adan tsuke number bra din yadda zata kamesa amma ba tsam inde zai dameki da ciwo ba... sai ki barsa kici gaba da harkokinki har zuwa awa 1 koma awa 2 ya zamto de sai kinji ya jike da zufa toh sai acire. Kya iya canza wani a lokacin ko ki bari sai anjima ki kara sa wani. Kar kuma ake takure bra din... abarta saisa-saisa yadda bazata dameki ba.

K**e yin haka sau 3 yini, safe, rana, yammah... kita yi kurum har zuwa lokaci ko kwanakin da kikaga ya tsaya ya dena zubar.

_______________________________________

Fatan bayanin ya ilmantar. Nagode muku bisa yadda bakwa gajiya da bibiyar rubutuna, Allah yai albarka, ya taramu a aljanna baki daya. _______________________________________

"✍🏼
[Ibrahim Y. Yusuf]
𝗜𝗯𝗿𝗮𝗵𝗶𝗺 𝗬. 𝗬𝘂𝘀𝘂𝗳

23/04/2024

Wannan hoton cikin mutum ne, ruwa ya taru tsir-tsir, sannan Hanta ta kumbura suntum, idanu sun kaɗa sunyi yellow shar 🥎 ga haki, ga rashin iya cin abinci, ga azababben ciwon ciki ba dare ba rana, me hana bacci da sukuni, zama ba daɗi haka kwanciya ba daɗi.... Ga jini baya tsirgawa hanta wanda in hakan ya cigaba lalacewa zatai.... "BUDD CHIARI" Kenan.

Kunsan Me ya jawo hakan? Shan slimming Tea! Kwarai da gaske Bush Tea.... Da kuke ɗiba da sunan rage ƙiba ajika. Bayin Allah "There is no shortcut to weight loss" duk wanda ya baka magani wai kasha a kwana kaza ko sati zaki slimming karki kuskura kisha ko likita ne kuwa.... I tell you.

Ba wata hanyar losing weight me sauƙi ta yanzu yanzu, infact koda akwai irin wannan maganin da zai zuge ki cikin kankanin lokaci ki kiyaye shi, umba haka ba za a iya ƙarewa da irin wannan yanayi.

Kai bama maganin Rage ƙiba ba hatta magungunan gargajiya dinnan na sha ka tafi a t**i, rana, basir ds da ake sayar muku mutum ya kuka da kansa zai iya qarewa da wannan yanayin

Jijiyoyin jinin Hanta ne ke toshewa su manne dalilin irin wannan Tea din karshe su bar mutum a wahala.

✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf

22/04/2024

Shan magungunan Malaria da typhoid ba tareda awun jini ba, ba namu bane sabida wadannan alamomin:

1- Zazzabi
2- Ciwon kai
3- Tashin Zuciya
4- Amai
5- Gudawa
6- Ciwon jiki
7- Atini
8- Dachin Baki
9- Rashin Cin Abinci
10- Rashin Karfin jiki.
11- Kasala
12- Kumburin ciki
12- mutun yaji ya rasa abinda yake masa dadi.

Wadannan abubuwan basu tsaya ga alamomin Malaria da Typhoid su kadai ba suna daya daga cikin alamomin HIV da Ciwon Hanta.

Ina mai baku shawarar ku tabbatar kunyi gwajin jini kafin ku fara shan Magani...

Lafiya Uwar Jiki

22/04/2024

Daga shafin: Physio Hausa

Ko me ke kawo karkacewar baki kwatsam?

Shanyewar ɓarin fuska larura ce da ke faruwa sak**akon matsala a jijiyar laka ta bakwai (7) da ta fito daga ƙwaƙwalwa zuwa fuska.

Wannan jijiyar laka na iya samun matsala k**ar shaƙewa, dannewa, lahani daga harbin ƙwayoyin cuta ko kuma bugu daga waje a kan hanyarta da ta fitowa daga ƙwaƙwalwa zuwa fuska domin kai saƙonni zuwa ɓarin fuska, jakar yawu, jakar hawaye, tsinin harshe, da wata tsoka da ke dai-daita sauti da ke can cikin kunne, da dai sauransu. Idan ɗaya daga cikin waɗannan matsaloli ya faru, aikin jijiyar zai yi sanyi/rauni sai ɓarin fuska ya shanye.

Yadda za a gane ɓarin da fuska ta shanye:

1) Karkacewar baki: wanda zai sa wahalar rikewa ko zirarewar abinci ko abinsha daga baki.

2) Zubowar yawu ta ɓarin da bakin ya shanye.

3) Sakkowar gira da kuma yawan zubar hawaye.

4) Gaza ko wahalar rufe ido sosai.

5) Samun wahalar bayyana labarin zuciya a fuska, k**ar murmushi, fushi da sauransu.

6) Matsalar kasa ɗaga gira ko tattare fatar goshi.

7) Ƙaruwar ƙara ko sauti a kunnen ta ɓarin da fuskar ta shanye.

8) Rashin jin ɗanɗano a tsinin harshe, da sauransu.

Abubuwan da ke janyo shanyewar ɓarin fuska:

1) Shanyewar ɓarin jiki, wasu masu shanyewar ɓarin jiki kan zo da shanyewar ɓarin fuska.

2) Ciwon siga.

3) Fashewar jijiyar jini a cikin kai.

4) Ciwon kunne.

5) Matsananciyar mura.

6) Bugu/rauni a kai ko fuska.

7) Doguwar tafiya a kan abin hawa tare da iska mai karfi na bugun ɓarin fuska tsawon lokaci.

Wannan matsala ta shanyewar ɓarin fuska na ci wa masu fama da ita tuwo a ƙwarya, k**a daga wahalhalu wajen cin abinci ko shan abinsha, zubar hawaye ko yawu wanda ke sa su jin kunyar bayyana fuskarsu a cikin jama'a, wanda hakan kan sa su ƙaurace wa jama'a, ko kuma tilasta musu rufe fuskarsu domin gudun tsangwama.

Wannan jinya ta shanyewar ɓarin fuska ana warkewa sarai k**ar ba a yi ba. Don haka, idan kina/kana fama da wannan matsala tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti ma fi kusa da kai.

22/04/2024

1- Ciwon cikin bangaren dama
2- Tashin Zuciya
3- Amai
4- Zazzabi
5- Kasala

Yana da muhimmancin a tuntuɓi likita a asibiti idan aka yawaita jin wadannan alamomin, kada asaya karban maganin dauke ciwo a kemis.

Sabida alamomi ne na cutan appendix ita appendicitis kuwa amfiso a ganoshi da wuri kafin yakawo matsala, domin za ta iya fashewa.

Allah ya tsare mu gabaki daya.

Lafiya uwar jiki

22/04/2024
22/04/2024

Kukaranta Alamomi 7 da zaku gane koda ta fara samun matsala:

Masana harkar lafiya sun bayyana cewar koshin lafiyar koda na daga cikin sirrukan dadewa a duniya ba tare da gajiyawar jiki ba, Koda

Masana harkar lafiya sun bayyana cewar koshin lafiyar koda na daga cikin sirrukan dadewa a duniya ba tare da gajiyawar jiki ba,

Koda na taka muhimmiyar rawa wajen tace wa da cire sinadarai ma su guba daga abubuwan da mutum ya sha. Koda na da alaka da sarrafa yanayin jinin jikin ta mutum,

Bisa la'akari da muhimmanci koda a jikin mutum ne yasa muka bunciko muku wasu daga cikin alamomi 7 da ke nuna cewar koda ta samu matsala, k**ar yadda masana su ka tabbatar.

1. Kumburi da taruwar ruwa a sassan jiki: Daya daga cikin alamomi na sahun farko da ke nuna cewar koda ta fara samun matsala akwai taruwar ruwa a cikin jiki da kale haifar da kumburi. Sassan jiki da wannan matsala ta fi bayyana su ne; sahun kafa, hannaye, kafafu, ciki, da fuska.

2. Sukurkucewar mafitsara: Yayin da mutun ya fuskanci ba ya iya rike fitsari k**ar yadda ya saba a baya, ya gaggauta zuwa asibiti domin gudanar da bincike a kan yanayin aikin kodar sa.

3. Gagarumin canji a launin fitsari: Launi, kala, da zarnin fitsari na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen fahimtar aikin koda.

Idan fitsari yana kumfa ko tsananin zarni ko wari ko mutum ya ke jin zafi yayin fitar fitsari ko ganin jini a fitsari alamu ne da ke nuni cewar aikin koda ba ya tafiya yadda ya k**ata.

4. Kuraje a fata: Duk da akwai abubuwa da yawa da kan iya haddasa fitowar kuraje a jikin mutum, gazawar koda wajen tace wasu sinadarai ma su guba kan iya haddasa fesowar kuraje a jiki.

6. Hawan jini: Masana lafiya sun bawa ma su matsalar koda shawarar su ke yawan ziyarar asibiti domin duba yanayin jininsu, saboda koda na taka rawa wajen daidaita sinadaran fatashiyom da sodiyom, sindaran da ke da alhakin da alhakin daidaita yanayin jini a jiki.

7. Yawan gajiya da kasala: Yayin da koda ta fara samun matsala, mutum kan tsinci kansa cikin yawa

22/04/2024

Shan ruwa akai akai yana inganta lafiyar jiki .

22/04/2024

Kudaina shan maganin infection ba bisa ka'ida ba, Kin wuni, kin kwana kin sake wuni da fant daya dole kiji gaban ki yana kaikayi

22/04/2024

Wanke gaban ki da medicated soap k**ar su Dettol yana kawar ni'imar gurin, sannan ya kawo barazanar infection.

22/04/2024

Ya maganar tazarar haihuwa? Akoi bukatar bayani ko Tinibu ya gama karantar da mu ?

22/04/2024

2- Sinadaran folic acid da folate yana kare mata masu juna biyu daga samun karancin sinadaran jajayen jini

Wanda karancin sa zai iya kawo matsalar:
- Zubewar ciki
- Na'uda kafin lokoci
- Mutuwar yaro a ciki
- Mutuwar Uwa.

Mata ku dinga sha idan aka baku...

22/04/2024

Sinadaran folic acid da folate: binciken masana ya nuna sinadaran yana iya rage hatsarin kamuwa da ciwon cancer.

23/03/2024

Alhamdulillah

22/03/2024

FASSARAR SHAWARWARIN ƘUNGIYAR LAFIYA TA DUNIYA (WHO) AKAN KULA DA LAFIYA LOKACIN AZUMIN SHEKARAR 2024
WHO ta bada shawarwari kashi biyar a wannan shekara ta 2024, wanda mutane ya k**ata subi wajen tabbatarda wanzuwar lafiya lokacin azumin Ramadan. Shawarwarin sune:
1. A ci abinci mai lafiya (balanced diet)
2. A rage cin gishiri
3. A ci gaba da motsa jiki
4. Kada a sha taba
5. A dafa abinci ta hanya mai inganci ga lafiya
Ga karin bayani a kan kowane a taƙaice:
1. Cin abinci mai lafiya: A ci abinci da yake ƙunshe da dukkan nau’oi da ake buƙata na abinci mai lafiya, wato “balanced diet”. A rage soyayyen abinci ko mai maiƙo da yawa lokacin buda baki da suhur. Kar a manta da shan wadataccen ruwa.
2. A rage cin gishiri : (A tuna bayan illan cin gishiri mai yawa wajen hawan jinni, yana iya saka jin kishirwa sosai—wannan bayanina ne).
3. A ci gaba da motsa jiki: A ci gaba da motsa jiki da Ramadan, zai agaza wajen narkarda abinci kuma yasa ƙoshin lafiya.
4. Kada a sha taba: Yana da muhimmanci a guji shan taba, kowane iri don wanzuwar ƙoshin lafiya.
5. A dafa abinci ta yanya mai inganci ga lafiya : Maimakon soya abinci, a dafa, ko a gasa ko a surara abinda zai yiwu ayi hakan (Soya abinci yana kara “inflammation” a jiki)

13/03/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! Mujittaba Sani, Abdulsalam Major Hussaini

Telegram: Contact @avagoldcoin_bot 05/03/2024

AVA-COIN

Da 👉AVACOIN zakaci dubu 100k cikin sauki.

Kunsan me yasa nace haka?, zaku fahimta Indai Kuna amfani da telegram.

AVACOIN wani sabon mining ne da zaka tara USDT Ina nufin nace Dollars masu tarin yawa, saidai shifa wannan Mining din Faka Faka ne.

Da zarar ka tara points 400k zaka samu damar mallar USDT 65 wanda kimarsa ta kusa kai dubu 100k

Ku Danna link din kasa ku fara.

👇👇👇👇👇👇👇👇

https://t.me/avagoldcoin_bot?start=a5ba071e9d4b41ce54a7

idan Ma Kana Ganin Dannawa Zai Baka Wahala Ko Batama Lokaci Kayi Amfani da wannan Dabara

Jeka Play Store Ko App Store Kai Download din Auto Clicker ita Ance Sarkin Aiki Ce kana Kunnata Zata Dannema Shi Gaba daya Babu Ruwan Ka Dannawa

Jiya Kuma Ina Cigaba da Buncike Naga Wani Wajan Boost da Ake iya Siyan Booster din Su Akan Farashin $30 Kuma Wata Uku Yake Ana Amfani Dashi Kafin Wa,adın sa Ya Kare

Ga Shawara Kodai Kaje Kai Amfani da Auto Clicker Wajan Tara AVA-COIN Ko Kuma idan Ka Tara 400k Adadin Ka’idar da Zaka iya Juyashi Ya Koma $65 Saika Raba Kudin Biyu

$30 Ka Sayi Boost da ita $35 Kuma Ka Cire Kai Budidi Badada dasu 😃

Duk Wanda Beyi Rajista Ba Ga Link nan Zai iya Shiga Ya fara yanzu ga link a kasa

https://t.me/avagoldcoin_bot?start=a5ba071e9d4b41ce54a7

Telegram: Contact @avagoldcoin_bot

05/03/2024

Shin ko kasan cutar Basir?

03/03/2024

Ko da baka San Harkar crypto ka gwada wannan
AVA-COIN

idan Ma Kana Ganin Dannawa Zai Baka Wahala Ko Batama Lokaci Kayi Amfani da wannan Dabara

Jeka Play Store Ko App Store Kai Download din Auto Clicker ita Ance Sarkin Aiki Ce kana Kunnata Zata Dannema Shi Gaba daya Babu Ruwan Ka Dannawa

Jiya Kuma Ina Cigaba da Buncike Naga Wani Wajan Boost da Ake iya Siyan Booster din Su Akan Farashin $30 Kuma Wata Uku Yake Ana Amfani Dashi Kafin Wa,adın sa Ya Kare

Ga Shawara Kodai Kaje Kai Amfani da Auto Clicker Wajan Tara AVA-COIN Ko Kuma idan Ka Tara 400k Adadin Ka’idar da Zaka iya Juyashi Ya Koma $65 Saika Raba Kudin Biyu

$30 Ka Sayi Boost da ita $35 Kuma Ka Cire Kai Budidi Badada dasu 😃

Duk Wanda Beyi Rajista Ba Ga Link nan Zai iya Shiga Ya fara yanzu ga link a kasa

Invite your friends and get bonuses for each invited friend! 🎁

referral link: https://t.me/avagoldcoin_bot?start=a5ba071e9d4b41ce54a7

TikTok · Umar Magaji 03/03/2024

Menene Ciwon kunne?

TikTok · Umar Magaji Check out Umar Magaji's video.

29/02/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abdu Sadik, Muhammad Jime

24/02/2024

Muhammadurrasulullah
(S.A.W)

Photos from Nr. Umar Magaji's post 23/02/2024

EAR PROBLEM (CIWON KUNNE):

GABATARWA:
Da farko shi kunne kanshi an kasa shi bari uku (3) :
1- Outer Ear (Wajen Kunne).
2- Middle Ear (Tsakiyar Kunne)
3- Inna Ear (Cikin Kunne)

Kuma ko wannen su zai iya samun matsala amman mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining akai Middle Ear ne (Ciwon tsakiyar kunne Wanda a turance a Kira da (Ot**is Media).

ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE (OTITIS MEDIA)?

Yana daga cikin abubuwan da suke kawo ciwon tsakiyar kunne:
1- Kwayar cututtuka k**ar su:
a- Bacteria
b- Virus
c- Fungi
Amma mafi yawa Bakteriya ne, wadannan kwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta makogoro zuwa tsakiyar kunne. (Akwai hanyar data hadasu dama).

2- Anasamun ciwon kunne ta dalilin shigan wani Abu k**ar Burbushin Kura , Gashin mage da sauransu (Allergies).

ALAMUN CIWON TSAKIYAR KUNNE:

1- Mutun zaiji k**ar wani abu ya cika masa kunne.
2- Rashin ji sosai
3- Zubar da ruwa a kunne
4- Jin zafi a cikin kunne .
5- kaikayin Daji Kamar ana Masa kida
6- Zazzabi da ciwon kai.

MENENE ALAKAR MURA DA CIWON KUNNE :

Gaskiya akwai alaka tsakanin mura da ciwon kunne , mafi yawan mura yana k**a hanci da makogoro kuma idan Baku manta ba munce akwai hanyar da tahada tsakanin Makogoro da Hanci da kuma tsakiyar kunne .

Kamar yadda mukace kwayoyin cutar Bakteriya , da virus da fungi da kuma burbushin kura su suke kawo ciwon kunne.
To wadannan kwayoyin cutar su suke kawo Mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da tahada tsakanin makoro, hanci da kunne.

SHIN DIGAWA KUNNEN MAN ZAITUN YANA MAGANI CIWON KUNNE :

Kuskure ne digawa kunne man zaitun, bama man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su Gentamycin bai k**ata a digawa kunne ba, in bada izinin likita ba.

Dalili shine wani lokocin ana samun fujewan dodon kunne (Rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to ko wanne irin abu idan yawuce can ciki zai iya kawo matsala.

MAGANIN CIWON KUNNE :

Tabbas duk wani ciwon kunne da kwayoyin cutar bakteriya ta kawosu ana amfanida ANTIBIOTICS wajen treatment , hakanan wanda aka samu da dalilin Burbushin kura ana amfani da ANTIHISTAMINES.

GARGADI:
Dayawa daga cikin mutane idan kunnensu yana ciwo kawai zuwa suke chemist a wanke musu kunne.

Bincike ya nuna akwai sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shine hana wasu kwayoyin cuta na bakteriya da mak**antan su girma da shiga cikin kunne, a garin wanke daudan kunne idan aka wanke wadannan sinadaran to daga nan anbudewa kwayoyin cuta kofa ne.
Shi wannan wankin kunnen yanada Qaidoji.

WASU ZA KAGA SUNA YAWAN KWAKULE KUNNE:

Amfanin "dauɗar kunne" da illar ƙwaƙwale ta.

"Dauɗar kunne" wani ruwa ne mai ɗan danko da dodon kunne ke samarwa domin bai wa kunne kariya, saɓanin yadda Bahaushe ke cewa "dauɗar kunne" ce . Saboda haka "dauɗar kunne" ba dauɗar kazanta ba ce, face wata hanya ce da kunne ke samar wa kansa kariya daga baƙin abubuwa da ka iya shigowa daga waje.

Allah da ikonsa, k**ar yadda kunne ne ke samar da wannan "dauɗar kunne", haka nan kunnen ke da ikon yashe wannan "dauɗa" da kansa.

Daga cikin amfanin "dauɗar kunne" akwai:

1. Cafke dukkan nau'in ƙura, ƙasa, ƙwari ko yayi kafin su kai ga cikin kunne.

2. Kashe kwayoyin cutar Bakteriya, da sauransu.

Saboda haka kada ka yi amfani da waɗannan abubuwa don ƙwaƙwale dauɗar kunne:

1. Magogin kunne wato 'cotton bud' a turance.

2. Tsinken tsintsiya

3. Mirfin biro

4. Kan ashana

5. Gashin kaza, da mak**antansu.

Sanya waɗannan abubuwa cikin kunne don ƙwaƙwalo "dauɗar kunne" na da haɗarin:

1. Ƙara cusa "dauɗar" zuwa can cikin kunne.

2. Kareraya gasun cikin kwararon kunne, wanda suke amfani wajen kare kunne daga baƙin abubuwa daga waje.

3. Cusa irin waɗannan abubuwa na da haɗarin shigar da ƙwayoyin cuta cikin kunne.

4. Raunata gangan kunne yayin da irin waɗannan abubuwa s**a zarme cikin kunne.

5. Shafe ko manne "dauɗar kunnen" a kwararon kunne.

Haka nan, zira waɗannan abubuwa cikin kunne don susa ko ƙwaƙwalo "dauɗar" akai-akai zai share kwararon kunne, kuma share ƙwararon kunnen na nufin share kariyar da Allah ya shirya wa kunne. Saboda haka, dukkan baƙin abubuwa na iya kutsa kai cikin kunne kai tsaye.

Kada ka ɗauki ɗabi'ar sa magogin kunne cikin kunne don goge "dauɗar kunne" kullum.

SHAWARA: Tuntubu likitan kunne (ENT DR.) da zarar ka fara jin wani ɓaƙon yanayi a kunnenka, ko neman shawarwari kan tsabtace kunne daga "dauɗar kunnen".

ALLAH UBANGIJI YA BAMU LAPIA, YALWATUWAR ARZIQI MAI AMFANI, DA KUMA ZAMAN LAPIA AMIN YARAB.

Kuyi Sharing Dan wassu ma su amfana
Mungode

Nr.Umar Magaji

Want your practice to be the top-listed Clinic in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Shin ko kasan cutar Basir?
Shin ko kasan cutar Basir?
Menene Ciwon kunne?#LafiyaUwarJiki #arewa #foryoupage #fypシ゚viralシ
ASTHMA, what is it?#arewa
Nurses Anthem #ScholarsJourney #kannywoodmedia #arewa #arewapeople #facebookreels #nurses #naijanurses
Alhamdulillah.. ✅ Ko wacce rana huhu yana shakar isa adadin lita milliyan biyu kyeuta.ALLAH abin godiya.
Karatun Miftahud Dhalibi | By Dutsen Tanshi Majlis Bauchi | Facebook
#arewa #nurses

Category

Telephone

Address

Kano
Other Medical & Health in Kano (show all)
best Medix 24 hours pharmacy and store best Medix 24 hours pharmacy and store
Kano
Kano, 700322

We sale and deliver branded and unbranded drugs, medical equipment, food items and all other needs

HHHP herbal medicine HHHP herbal medicine
Jigawa
Kano

Farin jakada traditional medicine Farin jakada traditional medicine
Zawaciki Layin Primary
Kano, 517

Munbude wannan shafi ne domin taimaka wa Yan uwa masu fama da larure larure da jinyace jinyace Da matsaloli kala kala k**ar hawan jini ciwon sugar matsala

Vaccine doses Vaccine doses
Kano

About the important of covid 19 vaccine doses

Asshifa'a medicine store Asshifa'a medicine store
Kano

WE SPECILIST WITH TRUST AND HONEST

Firdausi Medicine Store, Kabuga Kano Firdausi Medicine Store, Kabuga Kano
Gwarzo Road, Kabuga Underpass, Opp. Batayya Plaza/NAPEL Filling Station
Kano

Remarkable Drugs, Remarkable Care. Your Health, Our Mission.

𝐦𝐨𝐡 𝐬𝐮𝐫𝐚𝐣 𝐦𝐨𝐡 𝐬𝐮𝐫𝐚𝐣
Kano

My WhatsApp number 08168440841

Doctor Salahm Doctor Salahm
Kano, 1122

Gtc dbt student Gtc dbt student
Makoda
Kano, FISH

Arewa photography Arewa photography
Kano, 261222

It's our goal to help men who experience ED overcome this hurdle at an affordable cost.

Gold Dietary and Wellness Clinic LTD Gold Dietary and Wellness Clinic LTD
No 1 AM Panda Street Badawa Layout Kano
Kano

A private nutrition firm that is well-equipped and provide nutrition and wellness serves to all