Dauda Kahutu Rarara Fans

Dauda Kahutu Rarara Fans

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dauda Kahutu Rarara Fans, Musician, No 97 Ibrahim Tayo Road, Kano.

19/02/2024

Allah ya zama Gatanka Baba Gawuna na Baba Ganduje

05/11/2023

Tsula ya Sallama

29/10/2023

Uban jam iya Uban kowa

29/10/2023

Bazamu zura Ido ana cin mutuncinka muyi Shiru ba
Alh Dauda Kahutu Rarara

29/10/2023

Ya Allah ka karemu da Sharron Makita na fili Dana ɓoye

01/10/2023

JAWABIN MAI GIRMA, SHUGABA BOLA AHMED TINUBU, GCFR, SHUGABAN KASA KUMA BABBAN KWAMANDAN ASKARAWAN NAJERIYA A CIKAR JAMHURIYAR TARAYYAR NAJERIYA SHEKARU 63 DA SAMUN ‘YANCIN KAI, RANAR LAHADI 1 GA OKTOBA, 2023

‘Yan uwana ‘yan Najeriya,

Ina farin cikin yi muku jawabi a yau, ranar cikar kasarmu shekaru 63 da samun ‘yancin kai, a matsayina na shugaban kasarmu mai albarka, kuma zallar dan uwanku dan Najeriya.

2. A wannan rana mai muhimmanci mai cike da fatan alheri, muna jinjina ga iyayenmu da s**a kafa Najeriya, mazansu da matansu. Ba don su ba, da ba a samu kasar Najeriya ba. Gwagwarmayarsu, sadaukarwarsu, da jagorancinsu ne s**a haifar da ‘yantacciyar kasar Najeriya mai mulkin kanta.

3. A wannan lokacin, muna karfafa wa juna gwiwar cewa a matsayinmu na ‘yan Najeriya, Allah ya yi mana baiwa a dunkule da kuma a daidaikunmu. Babu wanda ya fi wani a cikinmu. Nasarorin da Najeriya ta cimma su ne abin alfaharinmu. Kalubalen da muka jure wa su ne ke karfafar mu. Kuma babu wata kasa ko wani iko a duniya da zai iya dankwafe mu daga isa matsayin da ya dace da mu. Wannan kasar taku ce, ‘yan uwana. Ku so ta, ku karrama ta a matsayinta ta kasarku ta kanku.

4. Najeriya ta isa kasa a bar misali bisa yanayin zubi da tsarinta. Allah ya azurta mu da kabilu, addinai, da al’adu dabam-dabam. Sai dai dankon zumuncin dake tsakaninmu ya na da matukar karfi ko da yake ba ganin sa ake ba. Mun hadu kan buri guda daya na samar da zaman lafiya da cigaban al’umma, da fata guda na bunkasar arziki da hadin kai, da kuma manufofin hadaka na juriya da adalci.

5. Samar da kasa da aka dora bisa harsashin aiwatar da wadannan manufofi masu daraja kan al’ummomi mabanbata ya zamo aiki mai matukar albarka da yake fama da kalubale. Wadansu mutanen sun ce bai k**ata a samu ‘yantacciyar kasar Najeriya ba. Wasu sun ce kasarmu za ta rushe. Har abada su na bisa kuskure. A nan, kasarmu ta kafu kuma a nan za ta tabbata.

6. A bana, mun tsallake wani siradi mai muhimmanci a tafarkinmu na tabbatar da cigaban Najeriya. Zaben da muka yi wa gwamnatin dimokradiyya ta bakwai a jere, na nuna cewa kasarmu ta yi riko da tsarin dimokradiyya da aiki da doka.

7. Ranar da na k**a mulki, na dauki alkawurra kan yadda zan shugabanci wannan babbar kasa ta mu. Daga cikin alkawurran har da yi wa tattalin arzikinmu garanmbawul domin samar da tsaro ga rayuka, ‘yanci, da walwalar al’umma.

8. Na ce daukar tsauraran matakai ya zama wajibi domin dora kasarmu kan tafarkin walwala da bunkasar tattalin arziki. A ranar na sanar da kawo karshen tallafin man fetur.

9. Ina sane da wahalhalun da s**a biyo baya. Idanuna suna gani kuma zuciyata ta na kunci. Ina son in bayyana muku dalilin da ya sa wajibi mu cigaba da daurewa a cikin wannan mawuyacin hali. Wadanda ke son a cigaba da tallafin man fetur da mummunan tsarin sauyin kudaden waje, mutane ne da ke son gina tafka-tafkan gidaje a cikin fadama. Ni ba haka nake ba. Ni ba zan gina mana gida a bisa tubalin toka ba. Idan muna son gidanmu ya yi kwari, ya dade dole ne mu gina shi kan tsandauri.

10. Gyara abu ne mai ciwo, amma shi ne abin da ci gabanmu da daukakarmu ke bukata. A yanzu muna dauke da wahalhalun da za su kai mu zuwa ga makomar da za a raba arzikin kasarmu mai yalwa bisa adalci ga kowa da kowa maimakon wasu tsirarun mahandama su tattare a wurinsu. Zamu samar da Najeriyar da za a mayar da yunwa, fatara, da wahala su zama tsohon labari.

11. Ba na farin cikin ganin al’ummar kasar nan na fama da wahalar da ya k**ata a ce an sauke ta a shekarun da s**a wuce. Zan so a ce babu wadannan wahalhalun a yanzu. Amma dole ne mu daure idan muna son samun makoma ta gari.

12. Gwamnatina na yin bakin kokarinta wurin sassauta wannan wahala. Yanzu zan bayyana muku matakan da muke dauka domin rage wannan radadin da magidanta da iyalai ke fama da su.

13. Mun fara daukar matakan sauya tsarin tafiyar da gwamnati domin samar da daidaton tattalin arziki, yaki da hauhawar farashi, bunkasa ayyukan masana’antu, samar da tsaron rayuka da dukiya, da kuma tallafa wa talakawa da sauran mabukata.

14. Bisa tattaunawarmu da ‘yan kwadago, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki, muna gabatar da karin albashi na farko inda za mu kara mafi karancin albashin gwamnatin tarayya ba tare da kara hauhawar farashi ba. A tsawon watanni shida masu zuwa, kananan ma’aikatan Gwamnatin Tarayya za su samu karin Naira Dubu Ashirin da Biyar kowanne wata a albashinsu.

15. Domin kawo ci gaba a yankunan karkara, mun kafa asusun tallafi kan samar da kayayyakin more rayuwa domin jihohi su bunkasa bangarorin dake da muhimmanci a yankunansu. Tuni jihohi s**a karbi kudi domin ba da tallafin sassauta radadin hauhawar farashin abinci da sauran bukatun yau da gobe.

16. Bunkasa tattalin arziki ta hanyar rage farashin sufuri na da matukar muhimmanci. Dangane da haka ne muka bude wani sabon babi a fannin sufuri ta hanyar samar da motocin haya masu amfani da iskar Gas a fadin kasar nan. Wadannan motoci za su caji kudi mai sauki da bai k**a kafar yadda ake biya yanzu ba.

17. Ba da jimawa ba kayan aikin sauya motoci masu amfani da fetur zuwa gas za su fara isowa kasar nan saboda mun dauki matakan takaita lokacin da aka saba dauka kafin shigo da su. Kuma za mu kafa wurin bada horo a fadin kasa domin koyarwa da bada sababbin damarmaki ga masu harkar sufuri da kuma masu kafa masana’antu. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da kasarmu ta rungumi hanya mafi inganci wurin samarwa tattalin arzikinmu mak**ashi. Samar da wannan sauyin, kafa sabon tarihi ne.

18. Na dauki alkawarin tsaftace barnar da ta yi wa Babban Bankin Kasa dabaibayi. Wannan aikin an riga an fara. An kafa sabon shugabanci a Babban Bankin. Kuma mai bincike na musamman da na nada na gab da gabatar da rahotonsa kan kurakuran da aka samu a baya da kuma hanyoyin da za a magance afkuwar hakan nan gaba. Daga yanzu, dokokinmu na tasarrufi da kudi za su amfani kowa da kowa ne maimakon masu iko da masu kudi kadai.

19. Dokar haraji mai hikima na da muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da adalci. Na kaddamar da kwamitin sauya fasalin tsarin haraji domin inganta tattara haraji a kasar nan da kuma magance dokoki marasa adalci ko masu kawo tarnaki ga ci gaban kasuwanci da bunkasar tattalin arziki.

20. Domin bunkasa samar da aikin yi da kudin shiga ga mazauna birane, mun samar da asusun zuba jari ga kamfanonin da s**a nuna alamar makoma ta gari. Haka kuma mun kara zuba jari a kanana da matsakaitan kamfanoni.

21. Daga wannan watan, za a kara gidaje miliyan 15 kan wadanda ake bai wa tallafin kudi kai tsaye domin rage masu radadi.

22. Gwamnatina a ko da yaushe za ta ci gaba da bai wa tsaron al’umma muhimmancin gaske. Mun bunkasa hadin kai da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro. An dora wa manyan hafsoshin sojin muhimmin aikin farfado da karsashin rundunonimu.

23. A nan, nake jinjina da yabo ga dakarun tsaronmu, da suke ba mu kariya tare da tabbatar da tsaron kasarmu. Da yawansu sun riga mu gidan gaskiya. Muna tuna su a yau tare da iyalansu. Za mu bai wa dakarunmu kayan aikin da za su sauke nauyin da ke kansu a madadin al’ummarmu.

24. Zamu ci gaba da nada mutane bisa muhimman muk**ai daidai da tanadin tsarin mulki na yin adalci ga kowa. Za a cigaba da kulawa da mata, matasa da masu bukatu na musamman a wadannan nade-naden.

25. Zan yi amfani da wannan dama domin taya Majalisun Dokoki na Kasa murna kan rawar da s**a taka wurin kafuwar wannan gwamnati ba tare da bata lokaci ba ta hanyar gudanar da ayyukan da tsarin mulki ya dora musu na tantance wadanda za a nada da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

26. Haka kuma ina taya bangaren Shari’a murna a matsayinsu na ginshikin dimokradiyya da adalci.

27. Ina kuma taya murna ga kungiyoyinmu na ci gaban al’umma da kungiyoyin kwadago bisa sadaukarwarsu ga dimokradiyyar Najeriya. Ba ko da yaushe ra’ayinmu kan zama daya ba amma ina mutunta shawarwarinku. Ku ‘yan uwana ne kuma ina girmama ku.

28. ‘Yan uwana ‘yan Najeriya, tsoro ko kiyayya ba za su kawo mana ci gaba ba. Za mu iya samun ingatacciyar Najeriya ne kadai ta hanyar kwarin gwiwa, tausayi da kuma sadaukar da kai a matsayin dunkulalliyar kasa guda.

29. Na yi alkawari zan ci gaba da mayar da hankali tare da bauta muku cikin amana. Ina kuma gayyatar kowa ya bada gudunmawa wurin ci gaban kasarmu abar kaunarmu. Za mu iya. Ba makawa za mu yi. Kuma tabbas za mu yi nasara!!!

30. Baki dayanku ina taya ku murnar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

31. Nagode da sauraro.

32. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.
Aliyu Samba 🖋️

30/09/2023

Tsohon shugaban kasa
Muhammadu Buhari yayi Alkawarin zai kawar da matsalar tsaro kafin ya mika mulki ga sabuwar gwamnati

Shin Buhari ya cika wannan Alkawarin?

30/09/2023

𝕄𝕌ℍ𝔸𝕄𝕄𝔸𝔻𝕌
ℝ𝔸𝕊𝕌𝕃𝕌𝕃𝕃𝔸ℍ
(𝕊.𝔸.𝕎)

Photos from Dauda Kahutu Rarara Fans's post 25/09/2023

YANZU-YANZU: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranar Laraba A Matsayin Ranar Hutu Domin Gudanar Da Shagulgulan Mauludin Annabi Muhammadu SAW

Daga Usman Umar Katsina

25/09/2023

Ya Allah ka bamu zaman lafiya Mai Dorewa a Nigeria

26/07/2023

ALLAHU AKBAR: Wannan Shine Alaramma Sa'eed Haruna 'Yankaba , Shine Mai Ja Wa Marigayi Sheik Ja'afar Adam Baki A Lokacin Rayuwarsa

Allah Ya Jikan Malam Ja'afar, Ya kuma karawa Alaramma Sa'eed lafiya da nisan kwana.

05/10/2022

Kai Baba Dan Audu fa Ya Bude wuta sai yazama Sarkin Gida

01/08/2022
Photos from Dauda Kahutu Rarara Fans's post 31/07/2022

Gaskiya wannan Wankan ya tafi da Gayu Rahama Sadau

28/07/2022

Rashin Tsaro
Talauci
Yunwa
Allah ka Yayemana
Albarkacin Manzon Allah S.A.W

27/07/2022
19/07/2022

𝐌𝐮𝐡𝐚𝐦𝐦𝐚𝐝𝐮
𝐑𝐚𝐬𝐮𝐥𝐢𝐥𝐥𝐚𝐡
(𝐒.𝐀.𝐖)

16/07/2022

𝐌𝐞𝐲𝐞 𝐆𝐚𝐬𝐤𝐢𝐲𝐚𝐫 𝐋𝐚𝐛𝐚𝐫𝐢𝐧 𝐝𝐚𝐤𝐞 𝐂𝐞𝐰𝐚 𝐌𝐚𝐝𝐚𝐠𝐰𝐚𝐥 𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐬𝐮?

01/07/2021

Innalillahi wa inna ilahir raj’un, ALLAH ya yi wa Haj Zainab Musa Booth rasuwa, gobe za a yi jana’iza a gidan ta da ke kallon Premiere Hospital a Court Road da karfe takwas na safe (8:00am). ALLAH ya jikanta da rahama, ya sa aljanna ce makomarta, amin.

19/06/2021

Muhammadu Rasulallahi
S.A.W

08/06/2021

Ya Allah kabamu Zaman Lafiya Mai👏 Dorawa A Nigeria 🇳🇬

06/06/2021

Good morning Friends
Real Fati Wash

05/06/2021

Ba Za Mu Lamunci Kisan Da Inyamurai Ke Yi Wa 'Yan Arewa Ba, Cewar Matasan Arewa
An bayyana cewar ko kaɗan jama'ar Arewa ba za su lamunci cin mutunci da kisan da Inyamurai ke yi wa 'yan Arewa a Kudancin Najeriya ba da sunan fashe haushi domin neman ƙasar Biyafira.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugaban Ƙungiyar cigaban matasan Arewacin Najeriya na kasa Kwamared Kamal Nasiha Funtuwa, a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a garin Kaduna dangane da cigaba da kisan da tsagerun Inyamurai ke yi wa 'yan Arewa a Jihohin su.
Kamal Funtuwa ya kara da cewar idan Inyamurai suna neman ƙasar Biyafira ne to ba ta hanyar kisan 'yan Arewa ba ne zai sa su samu biyan bukata, inda ya bada misali da kisan gillar da tsagerun s**a yi wa tsohon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Adamawa Ahmad Gulak a Jihar Imo, abin da ya bayyana da babban takaici.
"Ya k**ata tsagerun Inyamurai su sani cewa da akwai tsagerun da s**a fi su iya tsageranci a arewa, sannan su sani akwai Inyamurai da yawa dake rayuwa a Arewacin Najeriya a duk lokacin da aka ce za'a mayar da martani a Arewa abin ba zai yi musu Kyau ba".
Dangane da kiran da kungiyar Dattawan Arewa ta ACF ta yi na cewar 'yan Arewa su kauracewa shiga yankunan Inyamurai domin kariya daga dukiya da rayukan su, Kwamared Nasiha Funtuwa yace wannan kiran ai yazo a kurarren lokaci ne tun tuni ya k**ata ayi shi, domin sanin halin rashin mutunci na Tsagerun Inyamurai ne ya sanya a baya gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya s**a basu wa'adin ficewa daga yankin Arewa.
Shugaban matasan ya kuma yi tsokaci akan kalaman da shugaban kasa Buhari ya yi na faɗin cewar tura ta kai bango ba za'a amince da rashin kunyar tsagerun Inyamuran ba, inda yace kalaman Buhari abin dubawa ne domin a baya bai yi irin wannan kalamin ba, tun da a yanzu ya furta za'a zuba ido domin ganin matakin da zai ɗauka.

05/06/2021

KYAN ALQAWARI
IDAN KUKA ZABEMU ZAMU 2015 KAWO KARSHEN BOKO HARAM A NIGERIA 🇳🇬

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Yayiwa yan Nigeria Alqawarin Zai kawo karshen Boko haram a Nigeria in aka zabeshi a Matsayin Shugaban kasa
Yau Buhari shekararsa 6 a karagar mulki shin Buhari yakawo karshen boko haram?

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Category

Address

No 97 Ibrahim Tayo Road
Kano
Other Musicians in Kano (show all)
Zaks k Zaks k
Kano
Kano

Musical Artist @Matasan Hausa Empire

Isee Boii Isee Boii
Abdu D Street
Kano, 700232

Hausa Musician🎤 lyrical📝 Instagram, Tiktok, Audiomack, YouTube 🌍 👇👇👇 @isee_boi🎤

Zone Zaddy Zone Zaddy
Kano
Kano, 700401

#NoExit

elnazir_mai_nazari elnazir_mai_nazari
Kano

El~Nazir Hausa Musician

Imamu fasaha Imamu fasaha
Kano

Ni Mawaki Ne

Real_Kawu_Dan sarki Real_Kawu_Dan sarki
Minicipal
Kano

NI KAWU DAN SARKI BANIDA KOWA SAI JALLA WAHIDI

Salis sasco Salis sasco
Kano

Always is my name SASCO@

It's abdul It's abdul
Kano

Simple man

Ibrabno Ibrabno
Kano

I am a singer | song writer | rapper | Nigeria �

Hafeez m rashide Hafeez m rashide
Layin Mai Anguwa Dan Dinshe
Kano, 09066875965

garin kano kofar waika waje

A winner man A winner man
Kano City, K/na'isa
Kano

Sageer na hauwa fillo Sageer na hauwa fillo
Dorayi Layin Makaran Sallau
Kano, [email protected]

Abun na Allah ne Ba wai na mutum ba