Katsina Trends

Follow us for more Exclusive Contents
Katsina and beyond
DM for Collabs and Promo

22/08/2024

YANZU-YANZU: Bello Turji Ya Sha Alwashin Daukar Fansa Kan Ƴan Bindigar Da S**a Kashe Sarkin Gobir, Ya Ce Ba Zai Huta Ba Har Sai Ya Ga Bayansu.

20/08/2024

Wata Motar KTSTA ta taso daga Tashar Jabi Park dake a garin Abuja dauke da mutane 18 a ciki harda mata masu ciki 2 inda ta sauka a tashar KTSTA dake a kofar yandaka, Inda passengers din s**a sauka cikin koshin lafiya kuma s**a bayyana wa wakilan mu cewa sunji dadin tafiyar. No be to hear bad news everyday, today you deserve to hear a good news.

20/08/2024

Ya sunan namijin Akuya?

19/08/2024

Wace Unguwa ce tafi kyawawa a garin katsina?

02/08/2024

Yan zanga-zanga sun kunnawa motar jami'an tsaro wuta a gidan Gwamnatin jihar Katsina.

02/08/2024

Yadda zanga-zanga ta koma tanzoma a jihar Katsina.

Photos from Katsina Trends's post 31/07/2024

LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda Kwamishiniyar Mata ta tari wasu kungiyoyin mata guda 6 da s**a kawo mata ziyarar bazata domin kara mata kwarin gwiwar cewa suna tare da ita kuma suna goyon bayan ta.

31/07/2024

Wasu guggun 'yan mining din avacoin sun dauko hayar kwararren lauya kan halin da s**a tsinci kansu a hada haɗar kasuwanci da sukurkucewar farashi?

Sun dauko wani kwararren SAN daga Jihar Abeokuta, domin kare muradunsu. 😎🤣😂

31/07/2024

KUNGIYOYIN MATA guda 6 ne s**a bayyana hakan a wata ziyarar bazata da s**a kai ma Kwamishiniyar mata Haj. Hadiza Abubakar Yar'adua a ma'akatar mata dake a sakatariyar Jihar Katsina a jiya Talata 30 watan July 2024, Inda s**a yabi kokarin ta a ma'akatar Ilimin bai daya da sakandare wanda ya kawo ci gaba a Ilimin bai daya da sakandare, inda s**a roki da ta cigaba da kalar wannan kokarin wajen kawo ma matan Jihar nan cigaba.

Sannan sun roki da ta bawa Ilimimantar da yaya mata mahimmanci da tallafi da shire-shiren da zasu habbaka kasuwancin mata a jihar duba da yadda mata ke fama da dawainiyar marayu da kuma hidimomin yau da gobe.

A nata bangaren kuma Kwamishiniyar mata ta Jihar Katsina ta bayyana jin dadin ta da wannan ziyarar, sannan tace wannan ziyarar ta kara mata kwarin gwiwa, kuma da yardar Allah zatayi fiye da bakin kokarin ta da aka santa dashi domin ciyar da matan Jihar da ma Jihar baki daya gaba, domin idan akayi la'akari da gudunmuwar da mata suke bayarwa ga cigaban al'umma, domin suke yin tarbiya, sanan zata bawa Ilimin yaya mata kulawa ta musamman domin a samu wanda suma a gaba zasu zama Kwamishinoni.

Haka zalika shima Permanent secretary na ma'aikatar ya tabbatar ma matan da cewa za suyi aiki ka'in da na'in domin ciyar da matan Jihar a gaba.

Daga karshe sun mika godiyarsu ga mai Girma Gwamnan Jihar Katsina Mal. Dr. Dikko Umaru Radda CON a bisa wannan hangen nesa da yayi wajen kawo masu wadda tasan darajar su, sannan s**ayi addu'ar kariyar ubangiji a gareta da kuma daukakata a duk inda ta samu kanta.

31/07/2024

Ƙwamishinan ƴan sanda na Jihar Katsina ya bayyana hakan ne a wani zama da akayi na masu ruwa da tsaki da kuma Gwamnatin Jihar Katsina inda yace: "Jami'an hukumar ƴan sanda a shirye suke wajen bada tsaro ga mutanen da zasu shirya zanga zangar matuƙar s**a cika sharuɗan da hukumar ta tanada, na aikawa sunansu da sauran mutanen da zasu Jagoranci zanga-zangar"

A ɓangare ɗaya suma shugabannin ƙungiyoyin da s**a nuna rashin goyon bayan gudanar da zanga-zangar sun bayyanama Gwamnati dalilansu akan janyewar.

Mai girma muƙaddashin Gwamnan jihar Katsina Mal. Faruk Lawal Joɓe, yayi ganawa ta musamman da shugabannin ƙungiyoyin, ƴan kasuwa, direbobi, masu gidajen mai da sauran ƙungiyoyin fararen hula na matasan jihar Katsina da s**a nuna rashin goyon bayansu akan zanga-zanga da ake ƙoƙarin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Yayin ganawar muƙaddashin Gwamna Mal. Faruk Lawal Joɓe ya bayyana mutane jihar Katsina a matsayi masu ƙaunar zaman lafiya da biyayya ga umarnin Gwamnati, bayan haka yayi ƙarin haske aka wasu daga cikin shirye shirye na taimakawa al'umma da kayan abinci tare da jari da Gwamnatin jihar Katsina haɗin gwaiwa da gwamnatin tarayya s**a shirya a lokuttan baya a ƙoƙarin Gwamnati na kawoma al'umma sauƙi, da kuma irin matakan da yanzu Gwamnatin ke dauka wajen fiddo da tsare tsare da zasu ragema al'ummar jihar Katsina raɗaɗin tsadar kayan masarufi da ake fama dashi a ƙasar nan, domin ganin sun samu sauƙin rayuwa musamman akan al'amuran da s**a shafi tsadar kayan masarufi da kawon ƙarshen matsalar tsaro a jihar Katsina.

Ganawar ta samu halartar, shugaban majalissar dokoki, Rt. Hon Nasir Yahaya Daura, shugaban ma'aikata na gidan Gwamnatin jihar Katsina, Hon. Jabiru Salisu Abdullahi, ƙwamishinoni, chiyamomin ƙananan, ƴan majalissar dokoki, shugaban Jami'an tsaro na farin kaya, shugaban sojoji, ƙwamishinan ƴan sanda, shugaban hukumar kiyaye haɗurra, da sauran manyan jami'an Gwamnatin da ƙungiyoyin matasa.

30/07/2024

DA DUMI-DUMINSU: Wani kusa a Gwamnatin Jihar Katsina ya musanta labarin da DW Hausa ta wallafa na cewa an bawa kungiyoyin Matasa kudi domin hanasu zanga-zanga, Inda ya bayyana cewa labari ne marar tushe bare makama.

Daga
Katsina Trends

27/07/2024

Katsinawa yau ne zata fashe a karkanda stadium!

21/07/2024

An kaimu makura da matsalar rashin tsaro a kauyukan Katsina inji mutanen dake ZANGA-ZANGA a hanyar Malumfashi da s**a tare hanya ba shiga ba fita.

Source: DCL Hausa

Photos from Katsina Trends's post 20/07/2024

ZANGA ZANGAR LUMANA A KARAMAR HUKUMAR MALUMFASHI, JIHAR KATSINA.

Yanzu-yanzu masu zanga-zangar lumana a Marabar Ƙanƙara, da ke ƙaramar hukumar Malumfashi, jihar Katsina, sun datse hanya ba shiga ba fita, domin nuna ɓacin ransu kan hare-haren ta'addanci da ɓarayin daji ke kai masu a gonakinsu.

Masu zanga-zangar sun datse hanyar da ta taso daga Katsina zuwa Malumfashi da kuma wadda ta taso daga Funtua zuwa Malumfashi, lamarin da ya jefa matafiya cikin hali na rashin tabbas.

Wasu daga cikin mutanen da aka yi hira da su sun bayyana cewa ɓarayin daji sun sace tare da kashe mutane da dama a gonakinsu jiya, kuma har yanzu ba a sami gawarwakinsu ba domin yi masu sutura.

Hotunan da labarin faruwar lamarin: Alh. Ahmed Abdulkadir

19/07/2024

DA DUMI-DUMINSU: Sabuwar Kwamishiniya ta Ma'aikatar Mata ta Jihar Katsina Hajiya Hadiza Abuakar Yara'dua ta bayanna hakan ne a wata sanarwa data fitar a shafinta na Instagram, inda tace:

"Ya ku al’ummar Katsina, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, an dora mini wani sabon aiki a ma’aikatar mata. Wannan sauyi yana aiki nan da nan. A lokacin da nake Kwamishinan Ilimi na farko da na Sakandare, mun sami nasarori masu ma’ana, wadanda s**a hada da gyara gine-ginen makarantu, daukar malamai da horar da malamai, da kuma tsare-tsare masu yawa na bunkasa karatun boko da ingancin ilimi. An yi wannan ƙoƙarin ne tare da goyon bayan al'umma ba tare da katsewa ba, da aminci da sadaukarwar dukkan ma'aikatan ma'aikatar da goyon bayan abokanmu na kawo cigaba AGILE da TESS.

Yayin da nake shiga sabon aikina, ina tabbatar muku da cewa zana ci gaba da bada himmar da aka sanni da ita a ma’aikatar mata.

ZA MU MAYAR DA HANKALI NE WAJEN KIRKIRO DA AIWATAR DA SHIRYE-SHIRYEN DA ZA SU DAGAWA MATAN KATSINA KARFIN GWIWA, TARE DA TABBATAR DA SAMUN DAMA DA GOYON BAYAN DA AKE BUKATA DON CI GABA.

Ci gaban mata yana da matukar muhimmanci, domin raya karfin mace yana nufin ci gaban al’umma. Lokacin da mace ta samu ilimi, ba da iko da tallafi, suna ba da gudummawa sosai ga ci gaban zamantakewa, tattalin arziki da al'adun al'ummarmu. Ina mika godiya ta musamman ga mai girma Malam Dikko Umar Radda PhD, CON, bisa wannan damar da ya samu na yin aiki a wani matsayi. A tare za mu yi kokarin ganin Katsina ta zama wurin da aka ba da fifiko ga ilimi da karfafa mata don ci gaban al’ummarmu.

Nagode da dama da goyon baya, ƙarfafawa da amincewa."

15/07/2024

Daga Bakin Sheikh Albani zaria

12/07/2024

WATA SABUWA: Sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP a jihar DR. Mustapha Inuwa yace "Ba za su bari mutum daya ya kashe jam'iyyar PDP a jihar Katsina ba"

05/07/2024

YA SUNAN DAN ISKAN UNGUWAR KU?
😂🤣🤣

Photos from Katsina Trends's post 02/07/2024

DA DUMI-DUMINSU: A yau talata Mai Martaba Sarkin Katsina Alh. Abdulmuminu Kabir Usman ya halarci Sallar rokon ruwa da aka gudanar a masallacin idi na kofar guga da misalin karfe 9 na safe. Allah ya karba ya gafarta mana kurakuren mu, badan halinmu ba, ya bamu damina mai Albarka.

Daga
Katsina Trends

30/06/2024

Da DUMI-DUMINSU: A karo na biyu zamu kawo maku babbar baje koli da zata baku damar siyan kayan amfani da masarufi akan farashi mai sauki. A don haka muke kira ga yan kasuwa domin su hanzarta suyi rijista kafin guraban da muke dasu su cika.

26/06/2024

Hirar mu da BinB akan "KATSINA YOUTH & SME'S EXPO" kuna iya kallon cikakkiyar hirar a Channel dinsu na YouTube ga link dinnan a comment.

Photos from Katsina Trends's post 24/06/2024

LABARI CIKIN HOTUNA: Taron Katsina Youth & Katsina Youth & SMEs Expo daya gudana a Babban filin wasa na Muhammad Dikko (Karkanda) Stadium a ranar Talata 18th June 2024, wanda ya samu halartar Haj. Amina Zayyana shugabar kungiyar Katsina Inner wheel Development Initiative, da Hon. Isah Miqdad Ad Saude, Wakilin Guga Global Foundation, Wakiliyar Commissioner ta Basic and Secondary Education da sauran dubban mutane.

21/06/2024

Alh@mdulillah taro ya tashi lafiya, Taron "Katsina Youth & SME's Expo" wanda Katsina Trends ta shirya ya samu halartar dubban Jama'a daga ciki da wajen jihar nan.

17/06/2024

Gobe ne idan Allah ya kaimu da rai da lafiya.

17/06/2024
16/06/2024

Saura kwana Biyu fa, Ranar Talata ne Karfe 2 a Muhammad Dikko (Karkanda) Stadium.

16/06/2024

A madadina da dukkan ma'aikatan wannan kafar ta Katsina Trends mai Albarka muna mika sakon Barka da Sallah zuwa ga daukacin mabiyan mu. Da fatan Allah ya karbi dukkan Ibadun mu sannan ya bamu ikon ganin bayan Sallah lafiya.

Want your business to be the top-listed Advertising & Marketing Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Yan zanga-zanga sun kunnawa motar jami'an tsaro wuta a gidan Gwamnatin jihar Katsina.
Yadda zanga-zanga ta koma tanzoma a jihar Katsina.
I'm Officially Informing you that KATSINA YOUTH & SME's EXPO 2.0! Is going to be a day full of exciting activities, deli...
An kaimu makura da matsalar rashin tsaro a kauyukan Katsina inji mutanen dake ZANGA-ZANGA a hanyar Malumfashi da suka ta...
An kaimu makura da matsalar rashin tsaro a kauyukan Katsina inji mutanen dake ZANGA-ZANGA a hanyar Malumfashi da suka ta...
Daga Bakin Sheikh Albani zaria
Hirar mu da BinB akan "KATSINA YOUTH & SME'S EXPO" kuna iya kallon cikakkiyar hirar a Channel dinsu na YouTube ga link d...
Alh@mdulillah taro ya tashi lafiya, Taron "Katsina Youth & SME's Expo" wanda Katsina Trends ta shirya ya samu halartar d...
Mi kuke gani idan har Hukumar Katsina State Hisbah Board  tayi koyi da kalar wannan tsarin da ake amfani dashi a Jihar K...
Hisbah Aikin Allah #katsina #katsinastate #hisbahkatsina #GwagwareMediaReporters
Ba'a san malamai da ki da karasarwa ba. #katsina #hisbah #abuammar  #GwagwareMediaReporters #katsinastate
BIKIN MADE IN THE NORTH FESTIVAL 🎎 YA GAMU DA CIKAS YAYINDA DA JAMI'AN HISBAH SUKA KAIMA MAHALARTA TARON DA BASUJI BASU ...

Telephone

Address


Katsina
820221

Opening Hours

Monday 09:00 - 22:00
Tuesday 09:00 - 20:00
Wednesday 09:00 - 20:00
Thursday 09:00 - 20:00
Friday 09:00 - 16:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00
Other Advertising Agencies in Katsina (show all)
Umar JBY Umar JBY
Sabongida Qtrs Along Jibia Road Katsina
Katsina

Educating and public enlightenment of youth on politics.

VIBA VIBA
No. 2 Goruba Road, GRA Katsina
Katsina, 820212

Vehance Intelligence Business Associates

Muktar bawa ventures Muktar bawa ventures
G2/A1/bawa Ventures
Katsina

Chase Digital Marketing & E-commerce Development Chase Digital Marketing & E-commerce Development
6, BIRREL Avenue, SABO YABA, LAGOS, Yaba
Katsina, 260103

Welcome to chase digital marketing services! I’m a Shopify website developer and marketing expert, dedicated to boosting your online business. From stunning store designs to effec...