Katsina state youths leaders of tomorrow

Hi, thanks for contacting us. We've received your message and appreciate you reaching out.

15/12/2022

Sanarwa! Sanarwa!! Sanarwa!

Amadadin shuwagabannin kungiyar KMSG na farincikin gayyatar Coordinators 34 LGA na katsina dasu da magoya bayansu zuwa wajen gagarimin meeting na kungiya domin kaddamar da masu muk**ai.

wanda za'ayi k**ar haka:-

Rana:- Lahadi 25 gawatan Janairu shekara ta 2023.

Lokaci :- Karfe 10am.

Wuri:- Elladan Hall, Tsofuwar kasuwa, Rafindadi Road katsina, katsina states.
Domin Karin Bayani atuntubi wadannan lanbobi k**ar haka:- 09029905684, 08144009868, 08109552458, 07064766017.

Sanarwa Daga:- Umar Kabeer S. A Media to the KMSG.

Allah ya bada ikon zuwa Amin.

29/10/2022

*_A yau asabar 29/10/2022 kungiya tayi taron ta wanda ta sanar a kwanakin baya sannan an tattauna maudu'ai k**ar haka_*
1.kungiya zata karrama Alh. Muhammad Bara'u dan takarar gwamna na jihar katsina karkashin jam'iyyar ACCORD PARTY wanda za'a gudanar 27/11/2022.
2.bikin cika shekara 4 da bude wannan kungiya wanda zae gudana Insha Allah acikin sabuwar shekara.
3.karramawa ga shuwagabannin kungiya
4.An tattauna akan yiwuwar mayar da kungiya NATIONAL YOUTHS LEADERS OF TOMORROW daga KATSINA STATE YOUTHS LEADERS OF TOMORROW
*_Wadanda s**a halarci taron sun hada da Chairman, vice Chairman, P. A, Speaker, P.R.O1,Secretary, vice Secretary, Gallant photographer, da wasu daga cikin members na kungiya_*
Bayan nan an samu tattaunawa akan appointment letters na co'odinators da za'a bayar ga yan LGA.
*_Bayan haka kungiya taje takai ziyara a wajen Managing director na kungiya domin duba lafiyar sa akan hadarin da ya samu wajen dawowarsa gida daga makarantar wanda har ya samu matsala a kafarsa_*
Muna rokon Allah ya taemaka manah ya shige manah gaba ya biya dukkanin bukatunmu
*_RUBUTAWA/TSARAWA:BILYAMINU SALISU LAWAL (P.R.O1)_*
By the management of KATSINA YOUTHS LEADERS OF TOMORROW

14/09/2022

KATSINA YOUTH LEADERS OF TOMORROW(KYLT)
""Neman Ilmi""
Assalamu Alaekum
Yau muna 13/09/2022
Da farko ina miqo gaesuwata ga dukkanin members da shuwagabannin kungiya
Maudu'in da zanyi magana akansa shine "neman ilmi".
Neman Ilmi abune wanda ya zama dole ga dukkanin wani dan Adam" a bangaren Ilmin addini wannan shine wanda yafi zama dole agaremu domin komin yadda kake tafiyar da rayuwarka idan har baka da Ilmin addini toh zaka kasance k**ar jaki ne acikin dabbobi kuma neman ilmin addini shine zae saka ka gane sannan ka banbance tsakanin mae kyau da kuma mummuna saedae a wannan lokacin matasanmu sun dauki wata dabi'a wadda sam ba hanya bace mae bullewa bah zakaga matashi da zarar ya fara ganin cewa ya zama selebiriti(celebrity) toh daga lokacin zae ga cewa yafi qarfin yaje neman ilmi" Idan na koma bangaren Ilmin boko wanda duk da ana samun yawancin mutane suna neman sa saedae daga lokacin da muka girma sae muna ganin cewa babu wani wanda ya isa ya lankwasa mu kawae zamuyi tunanin cewa yanxu fah we're matured zamu iya banbance mae kyau da marar kyau hakan ne yake saka da matashi ya gama secondary school idan kayi masa maganar cigaba da karatu sae ya nuna maka cewa shi ba zae iya ba saboda baya buqatar yaje ba ana takura masa neman kudin sa ya fiye masa wannan karatun saedae abunda bae gane bah shine wannan Ilmin na boko zae iya zama wata madafa ce ga sana'ar sa domin komae zae iya faruwa zae iya kasancewa Allah ya daukaka kasuwancin nasa har ya kae cewa yana fita kasashen waje wanda idan babu English a bakainka ba zaka iya kasuwancin ba saedae ka nemi taemakon wani wanda wannan taemakon zae iya kasancewa cutuwa ce a gareka amma da ilminka babu wajen da ba zaka iya shiga ba ya k**ata matasa mu tashi domin neman ilmin addini da na boko haka zae taemakawa rayuwarmu ta nan gaba fatan Ubangiji ya taemaka manah ya dora rayuwar mu akan abunda zae haskaka rayuwar.
Rubatawa/tsarawa: BILYAMINU SALISU LAWAL PUBLIC RELATIONS OFFICER1(PRO) KYLT

10/09/2022

KATSINA STATE YOUTH LEADERS OF TOMORROW (KTYLT) The Chairman Ktylt. Engr. Hon. Rafiullahi Yakubu He succumbed the date meeting on 17-9-2022,
Time: 4:00pm
Venue : Elladan Hall Tsofuwar kasuwa, Rafindadi Road katsina, katsina state.

We wishe Invites all our members ktylt to Attend it. If you know u don't have a register so you're ready to do it on the meeting.

S.A media. Umar Kabir Through the Speaker Crew ktylt.

10/09/2022

MashaAllah,
Lallai wannan batu naka abin dubawa ne da kuma hankaltuwa akan shi Mr.P.A, kayi magana mai matukar mahimmanci.

Duba da yadda zamani ya sauya iyaye da dama ba suda karfin da zasu iya biya ma dan su (Matashi) dukkanin bukatunshi na kudi na rayuwa, hakan ya zama dole ne domin kawar da duk wata bukata wadda take bukatar financing ga matashi akan ya tashi ya jajirce domin ya nemi sana'a domin ya dogara da kanshi.

Noted: Hakuri da Sana'a komin kankantar ta yakan jawo ma mutun daukaka ya kai matakin da bai taba zato ba a rayuwa.

Muna godiya Mr.P.A to our Great Capacitated Chairman Hon. Rafi'ullah Yakubu.

Comrd. Habibu Sahalu V.C KYLT✍🏼

10/09/2022

YOUTH LEADERS OF TOMORROW
K.Y.L.T. ASLM ALAIKUM (6-9-2023) yayi daidai da (12-2- 1444)
my name is Abdurrahman sani sudais as speaker crew
Bayan haka muna jaddada godiya ga Allah madaukakin sarki daya bamu ikon buden wnn kungiya domin cigaban matasan mu
LISTENING COMPREHENSION
muna buqatar hadin kanku akan tafiyar da wanan kungiya Mai Albarka sann sauran members suma sunada damar isar da sako bangaren shawara ko korafi akwai office guda da aka bude nakarbar korafin members da leaders din
GROUP WORK
1) taimakon marayu da marasa lpy nagida da assibiti cikin yardar Allah
2) taimakon matasa hankaltar dasu a rayuwa domin goben su
3) taimakawa masu kananan sana.oin hannu
4) bada shawara domin gujewa fadawa bangar siyasa
5) gujewa zaman banza acikin ungw
6) taimakawa masu karamin jari domin bunkasa kasuwanci darage zaman banza a tsakanin mu
7) ziyartar makabartu da assibitoci da tsaftace muhallin
mutane
8) taimakawa marayu dayi masu din mkrnt da da kayan karatu insha Allah
LISTENING RULES CREW
1) Bandacin mutuncin juna acikin group ko a waje
2) wajibine girmama junaa acikin kungiya
3) banda zagi ko habaici acikin group ko acikin kung I ya
4) bamu yadda da turo link din wani group ba anan ciki
4) bamu yadda dacin hanciba acikin kungiya sbd yanzu komi kyauta kada kacewa wni kudi akebiya dd sauran su
5) wajibinne idan aka fidda lokacin meeting online ya k**ata ace kowa ya haw online time din
LISTENING A QUATIONS
1) waye wanda baiyi RIJESTAR kungiya ba?
2) waye Wanda ke buqatar shiga kungiya yarasa taya zai samu hadamar shiga?
3) waye keda wasu shawarwari dazai ba kungiya?
4) waye keda damar bada gudamawa ko shawara ga kungiya?
5) waye zaiyi RIJESTAR sauran yan watani murufe ta sbd akwai sababin tsare tsare da kawo insha Allahu ka Iya mana abinda yafi karfin mu
PROM OFFICE SPEAKER CREW
ABDURRAHMAN SANI JIBRIN
(A.S.J.) SING..✍️

10/09/2022

Kungiyar matasa Shuwagabannin Gobe (KMSG).

Wannan kungiya me suna a sama ta k**an yanda ta furta cewa zata fara renon matasa ne don su zamo shuwagabannin gobe, to a karo na farko kenan da wannan kungiya me alvarka ta bada lambar yabo ga wadan su matasan ta da s**a fara zama jajirtattin yan wasan kwallon kafa.

10/09/2022

KATSINA YOUTHS LEADERS OF TOMORROW.

SANA'A SA'A......
Taken Rubutu na kenan.

Bismillahi.
Hakika ko shakka babu matasa sune kashin bayan cigaban kowace al'umma. Matukar dai matasan nan mutanen kirkine. To ana sa ran za'a samu shugabanci nagari a cikin wannan al'umma.

Idan muka dubi yanayin da ake ciki a wannan zamani zamuga cewa a wannan kasa tamu an bar matasan mu baya a bangaren samar da abin dogaro da kai. Sabanin wasu kasashe da s**aci gaba inda zakaga matashi bayan samar ma kanshi hanyar dogaro da kai har wasu ma ya sama masu saboda a samu shawo kan matsalar zaman banza da rashin aikinyi. Mu dauki kasar China da Japan a babin misali.

A kasarmu Nigeria ne zakaga da wuya kasamu matashi mai kudi na kashin kanshi, sai dai gado. Ko kasan cewa Mark Zuckerberg mai manhajar FACEBOOK matashi ne, har yanxu bai shekara Arba'in (40) ba? Amma yanxu yana cikin jerin mutane 10 da s**afi kowa kudi a duniya. Ka taba tambayar kanka ya akayi yakai wannan matsayi? Bafa gado aka bar mashi ba!

Da yawan matasan mu a yanzu sunfi ganema karatun boko dan idan sun gama su samu aiki surika amsar albashi (ba ina s**ar karatun boko bane) amma ko kaji labarin wani dalibi a cikin satin nan ya mayar da Certificate din shi na degree a Jami'ar LAUTECH tare da rokon su mayar mashi da kudaden daya kashe tsawon shekaru 5? Meyasa??

Daga karshe ina kira ga matasa da cewa ko zamu rungumi karatun boko to muhada da sana'a saboda abinda bature yake cewa 'FOR RAINY DAY', bahaushe kuma yace 'GIDA BIYU MAGANIN GOBARA'. Ko kana da kyau kaqara da wanka, yazama ko kayi karatun baka samu aiki ba to kana dai da sana'ar da zaka dogara da ita. Yazama dai ginar da kayi intayi ruwa Rijiya idan batayi ba kuma Masai.

Inayi mana fatan Alkhairi.

Aliyu Abdullahi
P.A to the Chairman Matasa Shuwagabannin Gobe Reshen Jihar Katsina.
09/09/2022.

07/09/2022

DUBBAN MATASA A JIHAR KATSINA SUNA JIN BAKIN CIKIN ABUBUWAN DA SUKE FARUWA A YANKIN KATSINA DA KASA BAKI DAYA MARASA DADI.

Daga: Kungiyar "Katsina Youths leaders of tomorrow"

Kwana bakwai da cire sanarwa kungiyar KYLT zata dauki sabbin membobi a dukkan Kananun hukumomi 33 da katsina 34 dubban matasa sun nuna sha'awar su domin suma su bada gudunmawa ga al'ummar su da kuma yankin su.

Kungiya a duk inda take in aka ginata a kan kyakkywar turba tana cin nasarori a duk abunda ta saka a gaba. yankin mu na katsina da kuma arewa ya shiga mugun yanayi babu dogon bayani abunda kowa ya sani ne. yankin katsina da arewa yana bukatar motsin matasa domin kawo gyara da dawo da martabar yankin da al'ummar yankin data zube.

Ni kadai ko kai kadai baza mu iya kawo gyara ko sauyi a cikin al'umma ba dole sai an hada karfi waje guda tare da kishi kafin asamu nasarar kawo wani sauyi.

Kungiyar KYLT ba kungiyar siyasa bace kungiya ce da aka kafata akan kyawawan manufofi guda 4 wanda sune kalu b***n wannan al'ummar tamu ta katsina da kuma yankinmu na arewa. manufofin kungiyar KYLT sun banban ta dana sauran kungiyoyin jihar katsina domin KYLT ba kungiyar hada taro ayi hotuna asha shayi a watse bane kungiya ce ta jajirtattun matasa domin aki muka dakko yan uwa.

Har yanzu kofa a bude take yan uwa matasa kuzo mu hada karfi waje guda batare da nuna banbanci ko bangaranci ko yare ba. kar mu bari acimu da yaki makiya sun sako al'ummarmu a gaba anyi damarar wargaza jiharmu ta katsina da kuma arewa da karfi da yaji.

Kar karai na kanka dan uwa matashi ko matashiya, akwai gudummawar da zaka baiwa al'ummar ka. ka hada kai da kungiyar KYLT domin tabbatar da kyawawan manufofin ta a lungu da sakon jihar katsina da yankinmu na arewa.

Munada shugabanci mai karfi a kananu hukumomi 25 muna kan hada shugabanci a ragowar kananun hukumominmu na jihar katsina guda 9.

Atuntubi wadannan numbobi domin hada karfi waje guda mu tunkari matsalolin yankin mu.

0902 990 5684
09162783102
07046513492

06/09/2022

KUNGIYAR MATASA SHUWAGABANNIN GOBE, KATSINA STATE YOUTHS LEADERS OF TOMORROW, ZATA SAKE DIBAN SABABBIN MEMBOBI, A DUK KANANUN HUKUMOMIN JIHAR KATSINA 33 HAR DA KATSINA 34.

Daga: kungiyar "katsina sate Youths leaders of tomorrow"

Kungiyar katsina Youths leaders of tomorrow, Karkashin jagorancin shugaban kungiyar na jiha , hon Rafiullahi yakubu zata sake diban sababbin membobi a duk fadin kananun hukumomin jihar katsina har da jihar katsina domin fadada ayukanta na alkhairi akan matasa a lungu da sakon jihar katsina baki daya. kungiyar zata debi sababbin membobin ne a kananun hukumomi k**ar haka :

1.bakori
2. Batagarawa
3. Batsari
4. Baure
5. Bindawa
6. Charanci
7. Danmusa
8. Dandume
9. Danja
10. Daura
11. Dutsi
12. Dutsin-ma
13. Faskari
14. Futua
15. Ingawa
16. Jibiya
17. Kafur
18. Kaita
19. Kankara
20. Kankia
21.Katsina
22.Kurfi
23.Kusada
24.Mai adua
25.Malumfashi
26.Mani
27.Mashi
28.Matazu
29.Musawa
30.Rimi
31.Sabuwa
32.safana
33.Sandamu
34.Zango

Diban sababbin membobin, ya biyo bayan kiran kiranyen matasan jihar katsina baki daya, da suke aikawa kungiyar, sakonni daban daban, domin suma a basu damar baje kolin baiwar da Allah ya basu wajan ganin sun bada tasu gudun mawar ,domin cigaban matasan jihar katsina baki daya.

kungiyar tana maraba da dukkanin masu sha'awar son kasancewa membobin ta maza ko mata. a duk fadin jihar katsina da kwaye, domin bada tasu gudun mawar wajen cimma kyawawan manufofin ta. Domin neman karin bayani, zaku iya tuntubar lambobi k**ar haka:

WhatsApp kawai banda kira
09029905684
09162783102
08067915067
07064766017

Kira kawai banda WhatsApp
07046513492

Sign: ✍️ KYLT MANAGEMENT

06/09/2022

MAKOMAR ILIMIN MATASA A NAJERIYA

Daga: KATSINA YOUTHS LEADERS OF TOMORROW

A najeriya iya sanina babu wata ƙasa da na cancanta na wanzu face wannan ƙasa tamu Najeriya, don haka nake godewa Allah da na kasance ɗanta mai alfahari da ita da kuma son cigabanta. Wannan ne ya sa kowane loƙaci bana gushewa da yiwa wannan ƙasa kyakkyawan fatan nasara duk da kuwa an kusan barin gini tun ran zane , wato makomar matasa a wannan loƙaci.

Duk da cewa ni ba masanin tarihi ba ne, amma a tunanina kuma ina tsammanin hakan ga duk mai lafiyyen tunani matasa abu alfahari ne ga kowace al'umma. Don haka ma malam Bahaushe ya yi mai kirki da"Yana Manyan Gobe" ma'ana , saura su bisa sirdi mai kyau shi ne zai sa a yiwa wannan mutane zaton cigaba da samun nasarori.

A wannan ƙasar ,ba abinda za mu ce, sai dai mu godewa Allah, domin Ya ba mu tarin matasa masu basira da hikimomi kala_kala wanda k**ar zai zamo ɓata loƙaci idan na yi ƙoƙarin zayyano su. Sai dai kash! An zo inda ba a son ji wato rashin kyakkyawan jagoranci. Wannan duk yawan matasan akwai yiwuwar zama taron yuyuyu .
Domin idan mu ka yi la'akari da yadda ake gudanar da mulki sai ka ce mulkin k**a- karya ko mulki irin na namun daji.
A duniyance kuma a yau an daina yaƙi na fito na fito sai dai a yaki Mutum a jahilcinsa .A kasar ɗaliban jami'o'i za su ɗauki tsawon watanni takwas suna gida a zaune, malam jami'a za a hana su albashin wata takwas. Ai kawai sai dai ace Allah Ya tsare Gatari da sauran shuka. Kuma babban Abin takaici shi duk jagororin sun ɗauke ƴaƴansu zuwa ƙasashen waje domin zama mutane ƴaƴan talakawa ko oho.kawai ta shirya mana zaɓe ake yi.

Don haka ina kiran ƴan'uwana da mu san cewa, duk wani ɗan siyasa da yake buƙatar kuri'arka to ka yi mai wannan tambayar

Wane tanadi da shiri ka yi wa rayuwata a yau da gobena

Sign by
Khalifa s Alhassan
Ass secretary
(KYLT)

06/09/2022

Babban dalilin da ya sa kake ganin k**ar ba ka yi nasara a rayuwarka ba shi ne kana kwatanta kanka da wasu ne, kana raina kanka ne ka hango wasu da suke sama da kai.

Rayuwa ba tseren fifiko ba ce, kokari za ka yi ka inganta kanka amma ba kwatanta kanka da wasu ba —wato ka inganta kanka fiye da yadda kake jiya. Kenan rayuwa tsere ce a tsakanin kanka (within yourself only) ba wai da wasu ba.

Ina mai tabbatar maka cewa ka yi nasara sosai a rayuwarka. Idan ba ka yarda da ni ba ka duba baya yadda kake jiya da kuma yadda kake a yau, sannan ka yi alkalanki da kanka.

Idan jiyanka ta fi yau din ka kyau, kada ka damu wannan kaddara ce ta rayuwa — ka gode wa Mahaliccinka bisa hakan, idan ma yau din taka ta fi jiya, ka sake gode miShi don Shi Sarkin kyauta ne.

Ka yi kokari ka fi yadda kake jiya ba wai ka fi wani ba. Masana s**a ce kowa yana da irin ta shi kaddadar, kada ka kwatanta kanka da kowa sai dai kanka kawai tsakanin jiya da yau.

Idan ka dauki wannan shawarar tawa za ka samu salama a cikin zuciyarka sannan ka daina wahalar da kanka wajen hangen wasu, bugu da kari kuma ka sake gode wa Mahaliccinka bisa ni'imar da Ya yi maka don Ya kara maka wasu.

Alhamdulillah!

Khalifa s alhassan

06/09/2022

DOMIN KISHIN JIHAR KATSINA DA KEWAYE MATASAN MU SU ZAMA JAKADU NA KWARAI A DUK INDA S**A TSINCI KANSU.

KATSINA YOUTHSLEADERS OF TOMORROW (KYLT)

Kungiyar KYLT kungiya ce da aka kafata domin tunkarar lamuran matasan jihar katsina da kewaye, tanada kyawawan manufofi.

Kungiyar kylt tanada tsarin shugabanci tun daga kan shugaban kungiya na jihar (State Chairman) da shugaban kungiya na karamar hukuma(local government coordinator ) har zuwa shugaban kungiya na gunduma
(Ward leader).

Kungiyar KYLT kungiyace wacce take gudana karkashin shuwagabannin
kungiyar tare da tafiyar da al’amuran kungiyar a karkashin su.

MANUFOFIN KUNGIYAR KYLT

1. Wayar wa matasa kai akan illa da hadarin dake cikin shiga kungiyoyin ta’addanci domin a yanzu yankin mu na arewa makiya na gida dana waje suna dab da maida mana shi cibiyar ta’addanci. ta'addanci ya yawaita a Arewacin Nigeria akwai bukatar mu motsa domin yaki da tunanin ta'addanci a kwakwalen matasan mu musamman masu tasowa.

2. Wayar wa matasa kai akan illa da hadarin dake cikin kungiyoyin (ASIRI) wanda abaya munajin labarin su ne a wasu yankuna na kasar nan amma yanzu sun tarar damu har cikin gidajen mu. kungiyoyin Asiri sun yawaita a Arewacin Nigeria. yana daga cikin ayyukan su zubar da jinin al'ummar saka mutane a mummunar hanya k**ar fyade ga kananun yara luwadi madigo yankar wani sashin jikin mutum tone kabari hada rigima domin a zubda jini dss.

3. Wayar wa da matasan mu kai akan hadarin dake cikin (SHAYE SHAYEN MIYAGUN KWAYOYI)
wanda yana daya daga cikin abunda yake karawa ta’addanci tagomashi a yankin mu na
Katsina. matasa sune kashin bayan al'umma amma in sukzama nagari masu amfanarwa ba masu cutar da al'ummar ba. Shaye Shayen Miyagun Kwayoyi bazai taba barin matasa su zama abun alfahari ga al'ummar su ba,

Kadan knn daga cikin manufofin wannan kungiya, Allah ya bamu sa' a yabamu nasara ya bamu ikon aiwatar da wannan aiki domin kawo cigaba ga al ummarmu.


KYLT MANAGEMENT

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Tsohuwar Kasuwar Road
Katsina
Other Youth Organizations in Katsina (show all)
JOBE - Funtua Supports JOBE - Funtua Supports
Kofar Matah
Katsina, 1234

Jobe For Funtua Zone

Katsina State Association of Loyal Youths Multi-Services -Kasalyms Katsina State Association of Loyal Youths Multi-Services -Kasalyms
Khalilul Rahman Plaza, Near Hajj Camp, Daura Road
Katsina

Babangida Usman Kankara Babangida Usman Kankara
Katsina, 575757

Officially

Kasaye Kasaye
Katsina
Katsina

We are the feature leaders and we are the backbone of every nation

GUGA - Sabuwa Support Group GUGA - Sabuwa Support Group
Katsina

This Youth Forum is an initiative of the #AbduljabbarSurajoGuga. It’s a key platform where young people can contribute to public policy discussions on social media through their co...

Jihar katsina Jihar katsina
Old Government House Of
Katsina

This page is to bring social media users closer and unite in the common goal.

Kofar Durbi Youth empowerment and reformation Initiative Kofar Durbi Youth empowerment and reformation Initiative
Nagogo Road Kofar Durbi
Katsina, 820212

KYERI is a youth organization primarily and was registered with state government on May 16' 2022

Kofar Sauri Youths Initiative Forum Kofar Sauri Youths Initiative Forum
Dauda Mani Road Kofar Sauri
Katsina, 820211

Old Boys Students Association of Charanchi Old Boys Students Association of Charanchi
Charanchi, Katsina
Katsina, 1313

A widest official platform for charanchi students association

Mai fakarawa fans Mai fakarawa fans
Katsina

The more you know the more you realize you don't know ✍️🤼✍️✍️✍️

Yoruba YOUTH organization yankara Yoruba YOUTH organization yankara
Yankara Faskari Local Government
Katsina, 1234

For unity and peace