Jihar katsina

This page is to bring social media users closer and unite in the common goal.

09/11/2022

Jahata jahata ce katsinawa jinin tsatson DIKKO...

Photos from Jihar katsina's post 12/09/2022

Katsina State Governor Rt. Hon. Aminu Bello Masari today attended the Northern States Governor’s joint meeting with the Northern States Emirs in Abuja. The meeting which took place at the Banquet Hall of NICON Hotels was Chaired by Governor Simon Lalong of Plateau State who is the Chairman Northern Governors Forum, while the Sultan of Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar led the Northern Emirs. The Governor was accompanied to the meeting by the Secretary to the Government of Katsina State Alhaji Muntari Lawal.

The meeting proceeded with the adoption of the major resolutions reached during the last meeting held in Abuja on the 6th of September 2022. The resolutions include the Northern Nigeria Renewable Energy Project (NNREP), National livestock Transformation Plan (NLTP), Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRES), and Kaduna Textiles Limited.

The meeting also received a presentations made by the Northern Traditional Rulers Council on Nigeria Women Project, and Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) all World Bank support projects in Nigeria.

Office of the Director-General New Media to Katsina State Governor.
12th September 2022

12/09/2022

Let's welcome our new members:
Faisal Yunusa Bayala,
Malam Aminu Abukur,
Ahmad Dangida

Muna maraba da ku a wannan dandali Mai albarka Allah ya tabbatar mamu da khairan

Photos from Jihar katsina's post 06/09/2022

𝐂𝐎𝐀𝐋𝐈𝐓𝐈𝐎𝐍 𝐎𝐅 𝐊𝐀𝐓𝐒𝐈𝐍𝐀 𝐒𝐓𝐀𝐓𝐄 𝐌𝐄𝐃𝐈𝐀 𝐒𝐔𝐏𝐏𝐎𝐑𝐓 𝐆𝐑𝐎𝐔𝐏𝐒

An sake zaman tattaunawa tsakanin shuwagabannin wannan kungiya na Jiha da Babban darakta mai kula da kafar sadarwa ta zamani na gwamnatin jihar katsina (DG Media).

Duk a cikin shirye - Shiryen kawo sabbin hanyoyin cigaban kungiyar a matakin Jiha dana kananun hukumomi ta bangarori daban daban. Zaman Ya samu halartar babban mataimaki na musamman akan harkokin sadarwa (S.S Media) Sir. AbdulHadi Ahmad Bawa.

An gudanar da wannan zama, a ofishin babban darakta mai kula da bangaren kafar sadarwa ta zamani (DG. Media), Sir. Al-amin Isah.
A sabon gidan Gwamnatin jihar katsina, yau litinin 05/9/2022.

04/08/2022

KAN TSARO A JIHAR KATSINA...

Wace shawara zaka/ki iya badawa Dan cin galabar lamarin.

Allah Yasa shawarwarorin su Kai ga Mai Girma Gwamna Aminu Bello Masari. Allah ya bashi ikkon amfani dasu.

Photos from Abdulkarim Yahaya's post 05/10/2021
02/10/2021

Idan kunga inda na KUSKURE ku gyra Mani ta hanyar girmama juna...

Daga Mai girma gwamna Aminu Bello Masari

A wani lokaci da kungiyar Coalition ta kai mashi ziyarar ban girma.

Allah daukaka jihar Katsina
Allah ya daukaka Nigeria baki daya.

Photos from Jihar katsina's post 25/09/2021

congratulations 🌹
Congratulations 🌹
Congratulations 🌹

Congratulations to the beneficiaries of the three month social media program ( certificate) sponsored by Katsina state government through the Hassan Usman katsina Polytechnic ( HUK ).

It was yesterday 24 09 2021 the certificates were given to the participants at the Entrepreneur center of the Polytechnic.

Much appreciation to the katsina state Governor H.E Aminu Bello Masari , HUK, S.A Political Hon. Shu'aibu Charranci, Chairman of the Coalition of katsina state social media support groups S.A katsina zone new media and his counterpart of Funtua zone.

The voluntarily service of photography and coverage offered by the Mobile Media Crew was commendable and appreciated. Thanks alot.

The zeal and desire to learn exhibited by the participants who came across different political parties, Senatorial zones was commendable and unifying.

Second Admission List.pdf 21/08/2021

SANARWA SANARWA SANARWA!!!

METROLOGICAL INSTITUTE OF SCIENCE AND TECHNOLOGY KATSINA

Na sanar da al'umma cewa ta fitar da sunayen Wadanda s**a nemi izinin shiga makarantar domin karatu cewa ta fitar da sunayen Wadanda ta amincemawa da samun damar yin karatu na biyu (Second list),domin haka sai a duba jadawalin sunayen dake tare da wannan sanarwa.

Allah ya bada saa.
18/8/2021.

Second Admission List.pdf Conveniently share files to you and your friends. All files can be easily controlled for permissions. A secure storage system guarantees your file security.

Photos from Jihar katsina's post 23/07/2021

Congratulations

Muna taya Chairman Dahiru Mani da sauran yan'uwa shiga Baban komitin Gudanar da ZABEN shuwagabannin jamiyar APC ta kasa daga Shiyyar Arewa maso yamma ALLAH ya hadaku da ALKHAIRAIN da ke ciki Amin ya Allah.Allah yasa ayi Lafiya a gama Lafiya.

26/06/2021

BAYAN BUHARI YA KAMMALA WA'ADIN MULKIN SA, ZAKAJI ANA CEWA....

1. A lokacinsa ne aka bada, Federal University of Technology Jigawa

2. A lokacinsa ne aka bada, Federal University of Health Science Benue

3. A lokacinsa ne aka gina Federal University of Transportation Daura

4. A lokacinsa ne aka gina Federal University of Agriculture Zuru

5. A lokacinsa ne aka gina Army University Biu

6. A lokacinsa ne aka bada Federal University of Technology Akwa Ibom

7. A lokacinsa ne aka bada Federal University of Health Science Azare

8. A lokacinsa ne aka bada Federal University of Health Science Ila Orangun Ogun State

9. A lokacinsa ne aka gina National Institute of Technology Abuja

10. A lokacinsa ne aka gina Federal Polytechnic, Daura

11. A lokacinsa ne aka gina Federal Polytechnic, Kaltungo

12. A lokacinsa ne aka gina, Federal Polytechnic, Delta

13. A lokacinsa ne aka gina, Federal Polytechnic, Oyo

14. A lokacinsa ne aka bada, Federal Poly Wanune, Benue State

15. A lokacinsa ne aka bada, Federay Poly Shandam, Plateau

16. A lokacinsa ne aka bada, Federal Poly Monguno, Borno State.

17. A lokacinsa ne aka bada, Federal Poly Ugep, Cross River State

18. Shine ya kammala ginin Second Niger Bridge

19. Shine ya sake Gina hanyar Abuja-Kaduna-Kano

20. Shine ya Gina Layin Jirgi na Ibadan zuwa Lagos

21. Shine ya Gina Layin Jirgi na Itakpe zuwa Warri

22. Shine ya sake Gina hanyar Kano-Maiduguri

23. Lokacinsa ne muka fara ganin shinkafa yar gida a cikin buhu kamar 'yar waje

24. Lokacinsa ne aka fi samun wutar lantarki tunda aka dawo mulkin Dimokradiyya

25. Shine ya gina layin Jirgin kasa daga Kano-Kazaure-Katsina-Maradi

26. Shine ya sanya bututun iskar gas tun daga Kogi har Kano

27. Shine yayi ginin hanyar Kano-Katsina ya kuma mai data hannu biyu

28. Shine yayi aikin ruwan sha na zlXobe Dam, daga Dutsinma zuwa Katsina

29. Shine yayi aikin layin Jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja

30. Lokacinsa aka gyaran Airport ta Enugu

31. Lokacinsa ne aka sake Gina hanyar Zaria-Funtua-Gusau

32. Lokacinsa ne aka dauki matasa 500,000 ake basu N30,000 duk wata har na tsawon shekara 2 a tsarin N-Power

33. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren bada bashin noma da ake kira Anchor Borrowers Program don inganta harkar noma a Arewa da Nigeria

34. Lokacinsa aka fi daukar ma'aikata a kowane bangare na Gwamnati

35. Shine ya gina tashar wutar lantarki mai karfin 40MW a kashimbilla

36. Shi ya kammala tashar wutar lantarki a Zungeru 700MW hydro power station.

37. Lokacinsa ne ya sanya hannun kan dokar cin gashin kai ta kananan Hukumomi, amma 'yan majalisun jihohi da bangaren shari'a na jihohi da Gwamnoni s**a ki aiwatarwa, kuma jama'a su kayi shiru.

38. Lokacinsa ne ya sake gina hanyar Ibadan zuwa Lagos.

39. Shiya Gina Dala dry port

40. Money market

41. Trader moni

42. Pallatives

43. Shi ya magance matsalar rashin yankewar man fetur da ake fuskanta duk disambar karshen shekara

44. Ciyar da yara a makaranta

45. A lokacinsa ne Nigeria ta fara kera wayar salula ta farko

46. A lokacinsane aka tallafawa Manoma da kudi da Kuma kayan aiki

47. A lokacinsane ne aka gina gidaje matsakaita 440 a duk fadin kasar.

48. Institute of Transport Technology Kumo

49. Institute of Transport Technology Kano

50. A lokacinda ne aka samu karin gidajen gyaran Hali guda shida.

51. A lokacinsane ne aka karbo kananan hukumomi 17 dake hannun Yan ta'addan Boko Haram

Shugaba Muhammadu Buhari muna godiya, Allah Ya sa ka gama da duniya lafiya Amin

Photos from Jihar katsina's post 18/06/2021

...

IS REALLY WORKING..

A Jibiya Street Layout Katsina By MD KASROMA ENGR SURAJO@18/06/2021.

Copied and edited from Bashir Ya'u facebook wall..

Photos from Jihar katsina's post 17/06/2021

A shekaru da dama baya, wasu garuruwan jihar nan, har da babban birnin jihar watau Katsina, sa zarar aka zo irin wannan lokacin na damina, al'umma da dama suna shiga cikin zullumi da kwana tsaye, sakamakon ambaliyar ruwa da ake samu duk damina.

Zowar wannan Gwamnatin ta APC karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, akayi Kyakkyawan nazari kan wannan ambaliyar ruwa da take jawo asarar dukiya wasu lokutta har da rayuka.

Wannan nazari da akayi, shi ya gano dadaddun hanyoyin da ruwa yake bi a irin wadannan lokutta, amma hidimar karin yawa da kara muhallan zama tasa duk an tare su kuma ba a buda masu wasu ba. Wannan ya sanya Gwamnati ta dora wa Ma'aikatar kula da Muhalli ta jiha wadda ke karkashin kulawar Kwamishina Alhaji Hamza Suleiman Faskari, alhakin nemo mafita kan wannan matsala.

Daga cikin hobbasa na farko da akayi shi ne na dauke ruwan dake shiga sabuwar Unguwar Kofar Kaura ta hanyar gina manyan magudanun ruwa a hagu da daman titin Yahaya Madaki (daga Kofar Kwaya zuwa Kofar Kaura), sai kuma na Shararrar Fayis aka fitar dashi ta gefen Daki Tara. Haka kuma aka dauki wata hanyar ruwan tun daga Yaranchi har zuwa cikin koramar dake Yammawa bayan KTC.

Duba da yanayin yawan ayyukan da ake bukata cikin fadin jihar, yasa Gwamnati ta nemi hadin guiwa da hukumar NEWMAP wadda ke karkashin Bankin Duniya domin a sami damar kai dauki duk inda ake bukata a fadin wannan jiha.

Ana cikin wannan kokarin ne, sai Allah Ya kawo ibtila'in ambaliyar ruwa na garin Jibia wanda yayi mummunar barnar da ba a taba gani ba a shekarar 2019.

Bayan da Gwamnatin Jiha ta gama kammala cika ka'idojin NEWMAP tare da bada daunin bangaren da aka dibar mata, sai aka kaddamar da ayyukan manyan magudanun ruwa da gadoji hade kwalbatoci a garuruwa daban daban, wanda s**a hada da Jibia, Katsina, Malumfashi da kuma Funtua a cikin watan Yuli na shekarar 2020.

Ya zuwa yanzu, an fara kammala wadannan ayyuka kuma tuni an fara ganin sakamakon su, musamman yanzu da ruwan sama ya fara sauka.

Wadannan hotuna na kasa👇an dauki wasu a Kofar Sauri, wasu a Jibia wasu kuma a Funtua. Har da Bidiyo ga wanda Allah Yaba ikon budawa.



Daga SSA media Abdulhadi Ahamad Bawa aka samo

11/06/2021

Congratulations

On your recent appointment as Chairman katsina state Pilgrims Board may almighty Allah guide you through your stay..

Congratulations once again

Source: Mallam Sulaimana

10/06/2021

Coalition of katsina State Social Media Support Groups

Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari ta bada kudi Naira Miliyan Saba'in da Biyu (N72m) ga Hukumar kula da asibitoci ta jiha (Health Services Management Board) domin biyan kudaden alawus na watanni ukku na farkon wannan shekara ta 2021 (first quarter) na daliban dake karatun koyon aikin likitanci a ciki da wajen kasar nan.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Hukumar Dr AbdulJalil Umar Abdullahi ya bayar. Ya kuma kara da cewa dalibai Dari Hudu da Shidda (406) ne za su amfana da wannan kudi.

Ya kuma shaida wa daliban cewa godiyar da za suyi wa Gwamnatin shi ne su maida hankali wajen karatun da yake gaban su domin su sami nasara.

Dr AbdulJalil ya kuma yaba wa Gwamnatin bisa Kyakkyawan yanayin da take samarwa wanda ke habaka kiwon lafiya a wannan jiha.

An samo ga SSA AbdulHadi Ahmad Bawa

✒ State Director facebook monitoring of the katsina state coalition of Social Media support Groups 👉 AAbdulkarim YahayaYAbdulkarim Yahaya

Photos from Jihar katsina's post 30/05/2021

Yau 30 05 2021, taro ya gudana a DAURA MOTEL HALL inda ake KADDAMAR ko ince rantsar da Shuwagabnin Kungiyar COALITION... a reshen Daura.

Chairman na kungiyar ta jihar Katsina Dahiru Mani yayi jawabi kan dalilin kafa kungiyar inda yai bayani kan hadin kai da tallafama gwnatin kan ci gaban jihar Katsina da Nigeria baki daya. Ya kuma yi Kira ga gwamnati da Kara zumar taimakon samarin jihai daga karshe yai adu'a kan ci gaban jihar Katsina da Nigeria baki daya.

Dan majalisa Mai wakilatar Daura a matakin jiha, yayi maraba da zuwan duk Wanda ya harci taron sannan yayi Kira ga shuwagabanin kungiyai daga matakin jiha har zuwa kananan hukumomi da suyi adalci gun tafiyar da kungiyoyin ya kuma yi Kira kan hadinkai ya kuma yi adu'ar samun zaman Lafiya ga jihar Katsina da Nigeria baki daya.

Daraktan kungiyar, kuma Mai ba Gwamna Masari shawara kan siyasa , Shima yayi bayani da Jan kunne ga duk mambobi na kungiyar kan yada labaran gaskiya da gujema aibanta jamaa daga bisani yai adu'ar samun nasara ga dukkan alumma.

Mai Girma kwamishinan kananan hukumomi Alhaji Gwajo yayi bayani da Kira ga yan kungiyai da su Kalli jamiyar APC ba mutane masu madafan ikko ba domin zababu wadinsu zai zo karshe amma jam'iya na nan daga karshe shima yayi fatan alkahiri ga jihar Katsina da alummarta da Nigeria baki daya.

APC na karamar hukumar Daura yayi bayani cewa yayi maraba da wannan kungiyar bisa lura da tazo daga ofishin "S.A POLITICAL". ya Kara da cewa za suba kungiyar goyon baya dari bisa dari ma damar bata sabama kundin tsarin mulkin Nigeria ba. Ya kuma ba mambobin shawara da su dinga neman kujerun siyasa suma, watoh su kwatanta takara suma. Daga karshe yayi fatan alkhairi ga mambobi da jihar Katsina.

Daga karshe taron ya samu halarta mambobinshi daga Shiyyar Funtua da katsina.

Allah ya maidamu gidajenmu lafiya
Allah ya zaunar da katsina da Nigeria Lafiya baki daya.

Katsina City News 26/05/2021

Binciken musamman:

KATSINA, MA’AIKATA, ALBASHI DA CIWO BASHI............

Mu’azu Hassan

City News

Jihar Katsina na daya daga cikin Jihohi masu yawan mutane a Nijeriya. Tana da yawan jama’a kusan miliyan 10.

Tana daga cikin Jihohi da s**a fi yawan ma’aikatan gwamnatin Jiha da na Kananan Hukumomi.

Jihar tana da tarnaki da matsaloli masu yawa. Masu mulkinta sun samu wasu nasarori, sun kuma yi kurakurai.

Duk da halin da tattalin arzikin duniya ya shiga, wanda kuma ya shafi Nijeriya sosai, ya kuma taba duk Jihohi har da Katsina, akwai inda Jihar ta yi zarra, kuma ta zarce tsara a kasar nan.

Wannan kuma jajircewa ce ta masu mulki da kin koyi da wasu Jihohin. Sun yi abin da suke ganin shi ne ya yi masu daidai.

A Jihar Kaduna, Gwamnan na hawa a 2015 ya kafa kwamitin da za a ga bayan ma’aikatan Jihar. Kwamitin da rahotonsa ya kai ga sallamar sama da ma’aikata dubu 30, a Jihar kuma har yanzu ba a gama ba.

Kaduna ta ciwo bashin da har ta kure cin bashi, kamar yadda Hukumar da ke kula da cin bashin Jihohi s**a tabbatar. Kaduna na cikin Jihohin da aka haramtawa cin bashi, don ta ci har iya wuya.

Kaduna ga korar ma’aikata, ga cin bashi, duk da kuwa albashinsu bai kai na Jihar Katsina ba.

A Jihar Kogi, su albashi sai abin da ka gani a lokacin da ya iso. Kamar yadda ma’aikatan Jihar s**a tabbatar mana, suna bin watanni, kuma babu ranar biya. Wayon da Gwamnan ya yi shi ne, kullum kwamitoci ke aiki a kan albashin ma’aikata. Da wannan ake fakewa, sai an gama aiki za a fara biya a kan lokaci. Shi ma ya dakatar da dubban ma’aikata sai an gama bincike. Wani lokaci a Jihar sai a yi ‘bonanza’, a ce ga dan wani abu ga kowa cikin albashi kafin a gama bincike.

Wasu Jihohin suna biya, amma yawan albashin bai kai ko kusa da na Katsina ba, kuma ba su da yawan ma’aikata kamar Katsina. Misali a Zamfara, mai Digirin farko a Jiha dubu 30 yake dauka. A Karamar Hukuma dubu 20 da doriya, mai Sakadandire dubu shida.

Wata Jihar wadda ke tsare albashi ita ce Jihar Jigawa, yawanta da ma’aikatanta bai kai na Katsina ba, amma a bincikenmu albashinta yana daidai da tsarin mafi karancin albashi na kasa.

A wasu Jihohin tuni s**a bar daukar mai Sakandire aiki da Diploma. Misali a Jihar Kano, in kana da karatun Sakandire kar ka je neman aiki. In kana da Diploma kar ka je nemin aikin dindindin a gwamnatin Jiha, sai dai na wucin-gadi (casual) ne.

Akan dauki masu Diploma da NCE a sashen koyarwa.

A wannan binciken mun tattara duk albashin Jihohin kasar nan don wannan rubutun, wanda yana da sauki da wahala ga duk mai bukatar tabbatarwa.

Mun ba da misali da Jiha hudu ne kawai a matsayin misali.

Da yawan Jihohi sun manta da wani abu wai shi karin girma ga ma’aikaci don kar kudinsu su karu. Kullum za a yi ta kafa kwamitin daukar lokacin da janye tunani. A ce sai ya gama aiki za a yi karin girma. Wasu ma sun fito karara sun ce ba su da kudi, ba sauran karin girma, sai Baba ta gani.

A Katsina, har yanzu ana daukar masu Sakandare da matakin albashi mafi karanci. Jihohi da yawa sun bari.

A Katsina har yanzu ana karin girma a kai, a kai, wanda Jihohi da yawa sun bari.

A Katsina ba a kori ma’aikata ba, kuma ba a kafa kwamitin wasa da hankali ba. Jihohi da yawa suna cikin wannan taskun.

A Katsina suna bin matakin albashi mafi karanci kamar yadda dokar kasa ta ce. Jihohi da yawa sun ki biya, wasu sun fara s**a ce sun jinjigine.

A Katsina ana biyan albashi kafin a shiga makon wani sabon watan. Jihohi da yawa sai abin da s**a gani.

A wannan yanayi yana da kyau ma’aikatan Katsina su gode wa Allah da ya tsare masu aikinsu da albashinsu, ya zama ba a samu matsala irin ta wasu Jihohin ba.

A bangaren bashi kuwa, duk wanda ya nemi bayani a ofishin Hukumar da ke kula da bai wa Jihohin kasar nan bashi da ake kira DMO, zai ga bashin da ake bin kowace Jihar. Za ka rubuta ne ka bi har a ba ka amsa. Neman bayani a kan yadda mutum zai amshi bashin kyauta ne, ko Sisi ba ka biya.

Zai ga cewa yanzu Jihohin kasar nan hudu ne kacal ba su ci bashi har iya wuya ba. Katsina ce ta farko.

Da yawan Jihohi an riga an shafa masu bakin fenti kar a kara ba su bashi.

In mai bincike ya tambaya zai ga cewa duk bashin da Katsina ta ciwo basuss**a ne na inna-rididi, kuma wasu na Bankunan Musulunci ne marasa wani hatsari a gaba.

Wasu Jihohin ana fargabar duk wanda ya hau hayaniyar biyan bashi ta ishe shi. Ya zuwa yanzu Jihar Katsina ba ta cikin wannan fargabar.

Duk wanda zai zo fargabarsa ita ce, ma’aikata, kudin shiga da kuma albashi.

Bincikenmu ya tabbatar cewa da Katsina na kan gaba a kasar nan wajen rike albashin ma’aikata, karin girma kiyaye dokar mafi karancin albashi da daukar kananan ma’aikata a cikin aikinta.

Kuma tana cikin Jihohin kasar nan hudu da ba su ci bashi ya sarke su ba. Ya dace ma’aikata su gode wa Allah a kan haka.

Wannan binciken da hadin gwiwar Matasa Media Links Ltd aka yi shi, don jaridun

Share by Bashir Ya'u S.A NEW MEDIA KATSINA ZONE

POSTED BY Abdulkarim Yahaya State Director facebook monitoring of the coalition of katsina State Social Media support Groups

Katsina City News.
katsinacitynews.com

Jaridar Taskar Labarai

www.jaridartaskarlabarai.com

The Links News

@ www.thelinksnews.com

07043777779.08137777245

Katsina City News Straight from Katsina city

Photos from Jihar katsina's post 23/05/2021

HANYAR KATSINA -MANI KE NAN

GWAMNA AMINU BELLO MASARI TA AIKINSHI YAKE.

AN SAMU HOTUNA GUN S.A NEW MEDIA KATSINA ZONE Bashir Ya'u

KARA WALLAFAWA Abdulkarim Yahaya, State Director facebook monitoring of the coalition of katsina state social media support groups

Photos from Jihar katsina's post 22/05/2021

MAI GIRMA GWAMNA MASARI YA JE DUBA AIKIN TSANGAYRA AIKIN GONA TA UMARU MUSA YAR'ADUWA DA AKEYI A LAYIN MINISTA MALUMFASHI 👇 👇
-------------------------------------------------------------

A bisa kudurin Gwamnatin Jiha na kammala duk ayyukan da take kai, Gwamna Aminu Bello Masari ya kai ziyarar duba aikin tsangayar aikin gona ta Jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ake ginawa a Layin Minista ta karamar hukumar Malumfashi.

Wannan katafaren gini mai hawa ukku zai kumshi dukkan bangarori guda biyar da aka shirya budewa a wannan tsangaya, wanda ya hada da ofisoshi, azuzuwa, dakunan gwajegwaje, manyan dakunan daukar karatu (lecture halls) da dai sauran su.

Bayan kammala duba aikin, Gwamna ya nuna rashin gamsuwa da yadda aikin yake tafiya, ta dalilin haka, ya bada umurnin a tabbatar da an isar da sakon shi gare shi na cewa an bada aikin nan bisa ka'idoji wanda s**a hada har da lokacin kammalawa, saboda haka wajibi ne ya maida hankali ya kammala shi cikin lokacin da aka dibar mashi.

Tun farko a nashi jawabin, Mai ba Gwamna Shawara a kan Ilimi mai zurfi Malam Muhammad Bashir Usman Ruwan Godiya ya kara yaba wa Gwamna Aminu Bello Masari a kan yadda yake bada kula da muhimmanci a kan duk lamurran da s**a ilimi wanda hakan yasa ya amince da bada wannan aiki a kan kudi sama da Naira Miliyan Dari Shidda kuma ya zuwa an biya Dankwangilar kashi Hamsin da Daya (51%) na wannan adadi.

Ya kuma shaida wa Gwamnan cewa sakamakon takardar da shi Gwamnan ya rubuta zuwa Gidauniyar Tallafawa Ilimin gaba da Sakandare (TETFUND) ta neman dauki, yanzun haka Gidauniyar ta bayar da ayyukan gine gine har kashi ukku a wannan wuri kuma sun fara wannan aiki yana kuma tafiya ka'in da na'in.

Daga bisani kuma Gwamna Masari ya duba wadannan ayyukan tare da yaba ma wannan Gidauniyar kan wannan gagarumin karamci.

Sakataren Gwamnatin Jiha Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da sauran manyan jami'an Gwamnatin Jiha s**a rufa wa Gwamnan baya.

An Samo labarai da hotuna daga SSA MEDIA NA GWAMNA MASAbdulHadi Ahmad Bawawawa

AN KAWO LABARAN A WANNAN FEGI DAGAbdulkarim Yahayaya, State Director facebook monitoring of the coalition of katsina state social media support groups

Cc
Dahiru Mani
Bashir Ya'u
Muhammad Sani Masari

Photos from Jihar katsina's post 22/05/2021

GWAMNA MASARI YA JE DUBA MAKARANTAR ISLAMIYA DA KASAR TA GINA A GARIN KAFUR...

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara yin godiya ka kasar Kuwait a kan yadda take daukar dawainiyar ginawa da kuma gyaran makarantu ta wani shiri nata na farfado da tarihi da kayan gado na Musulunci.

Gwamnan yayi wannan godiyar a garin Kafur bayan da ya kammala duba ginin wata babbar Islamiyya da wannan kasa take ginawa ta hannun wata kungiya mai suna 'Revival of Islamic Heritage Society'.

Kungiyar yada addinin Musulunci ta 'Islamic Enlightenment Foundation of Nigeria' wadda ke karkashin jagorancin Sheikh Salisu Abdullahi Bakori take kula da wannan aiki.

A nashi jawabin, Sheikh Salisu ya shaida wa Gwamna Aminu Masari cewa, da zarar sun kammala aikin wannan Islamiyya za su isa Makarantar kurame dake garin Malumfashi domin gyara ta daga nan kuma sai Makarantar makafi ta Katsina.

Credit
AbdulHadi Ahmad Bawa SSA Social Media

Copied from Bashir Ya'u SA NEW MEDIA KATSINA ZONE.

EDITED AND REPOST BY Abdulkarim Yahaya, State Director facebook monitoring of the coalition of katsina state social media support groups.

22/05/2021

GWAMNA MASARI YA JE DUBA MAKARANTAR ISLAMIYA DA KASAR TA GINA A GARIN KAFUR...

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara yin godiya ka kasar Kuwait a kan yadda take daukar dawainiyar ginawa da kuma gyaran makarantu ta wani shiri nata na farfado da tarihi da kayan gado na Musulunci.

Gwamnan yayi wannan godiyar a garin Kafur bayan da ya kammala duba ginin wata babbar Islamiyya da wannan kasa take ginawa ta hannun wata kungiya mai suna 'Revival of Islamic Heritage Society'.

Kungiyar yada addinin Musulunci ta 'Islamic Enlightenment Foundation of Nigeria' wadda ke karkashin jagorancin Sheikh Salisu Abdullahi Bakori take kula da wannan aiki.

A nashi jawabin, Sheikh Salisu ya shaida wa Gwamna Aminu Masari cewa, da zarar sun kammala aikin wannan Islamiyya za su isa Makarantar kurame dake garin Malumfashi domin gyara ta daga nan kuma sai Makarantar makafi ta Katsina.

Credit
AbdulHadi Ahmad Bawa SSA Social Media

Copied from Bashir Ya'u SA NEW MEDIA KATSINA ZONE.

EDITED AND REPOST BY Abdulkarim Yahaya, State Director facebook monitoring of the coalition of katsina state social media support groups.

Photos from Jihar katsina's post 21/05/2021

Katsina state Governor Alh Aminu Bello Masari has sworn-in two new Perrmanent secretaries in the state civil service.

The new Permanent Secretaries are Alh Abdullahi Abubakar Gagare for Ministry of Budget and Economic Planning and Barrister Hassan Yusuf for Ministry of Justice.

Speaking shortly after administering the Oath of office and that of aligience, Governor Aminu Masari reminded them of the Oath they have taken.

The Governor who described the two appointees as committed civil servants urged them to live up to expectations in the discharge of the new tasks.

The swearing in ceremony was attended by the state Deputy Governor Alh Mannir Yakubu, the SGS Dr.Mustapha Muhd Inuwa and the Head of State Civil Service Alh Idris Usman Tune among others.

Bishir Ya'u
Special Assistant On New Media Katsina Zone to the Executive Governor of Katsina State
21/5/2021.

Singed by Abdulkarim Yahaya
State Director facebook monitoring of the coalition of katsina state social media support groups.

21/05/2021

KU WAIWAYA BAYA FA YAWANCIN WADANDA S**AI TAFIYAI SUNA SON SU SHA JAR MIYA KAMAR YADDA KUKA SHIGE CIKI CIKI KUNA SHA KUMA KU TUNA TA INDA AKA HAU...

19/05/2021

MASARI MAI DAUKAR AIKI BA MAI KORAR MUTANEBA....

Photos from Jihar katsina's post 13/05/2021

WALIMAR SALLAH 👐

A YAUNE CHAIRMAN DAHIRU MANI, DA WASU MA'ABOTA KAFAR SADA ZUMUNTA TA ZAMANI S**A HADA WALIMAR MURNAR SALLAH A FILIN GDSS KOFAR YAN DAKA KATSINA.

TARON YA SAMU HALARTA DAN MAJALISAR KAliyu Albabaabaabaaba ALRRafindadi UwaisaiAbdulHadi Ahmad BawaawaawaBashir Ya'ua'Hamisu Haraaraaraaraaraara sauran yan uwa da yawa da ba zan iya kawo sunayensu a nan ba.

Anyi fadakarwa sosai gami da yima jihar Katsina da Nigeria baki daya adu'ar zaman Lafiya da ci gaba Mai dorewa.

Da fatan duk kun koma gidajenku lafiya, Allah ya zaunar da katsina da Nigeria Lafiya amen ya Allah.

Photos from Jihar katsina's post 11/05/2021

Coalition of Katsina State Social Media Support Groups Kafur Local Govt Chapter

Ongoing rehabilitation of two blocks of six classrooms at Government Day Secondary School Dutsin Kura, Kafur Local Government by His Excellency Rt Hon Aminu Bello Masari led administration

Prompt payments of workers salary despite country's financial problems.

You are indeed making it different again sir

May

from Yusuf Garba cin facebook wall.

by the State Director facebook monitoring of the coalition of katsina State Social Media support Groups Abdulkarim Yahaya

Photos from Jihar katsina's post 10/05/2021

WANI GWAMNA NA KORAR MA'AIKATA BABA MASARI NA DAUKA

MASARI TA AIKINSHI YAKE

Gwamnatin jihar Katsina ta Gama shire shiren Fara biyan wasu sababin malamai Guda 774 kudin albashi.

Gaskiya Mai girma Gwamna Masari ka cancanci yabo a lokacin da wasu Jihohin ke korar aiki sannan Kake daukar wasu aiki ka kuma biyasu albashi.

Allah mun gode maka
Allah mun gode maka

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Old Government House Of
Katsina

Other Youth Organizations in Katsina (show all)
Katsina state youths leaders of tomorrow Katsina state youths leaders of tomorrow
Tsohuwar Kasuwar Road
Katsina

Hi, thanks for contacting us. We've received your message and appreciate you reaching out.

JOBE - Funtua Supports JOBE - Funtua Supports
Kofar Matah
Katsina, 1234

Jobe For Funtua Zone

Katsina State Association of Loyal Youths Multi-Services -Kasalyms Katsina State Association of Loyal Youths Multi-Services -Kasalyms
Khalilul Rahman Plaza, Near Hajj Camp, Daura Road
Katsina

Babangida Usman Kankara Babangida Usman Kankara
Katsina, 575757

Officially

Kasaye Kasaye
Katsina
Katsina

We are the feature leaders and we are the backbone of every nation

GUGA - Sabuwa Support Group GUGA - Sabuwa Support Group
Katsina

This Youth Forum is an initiative of the #AbduljabbarSurajoGuga. It’s a key platform where young people can contribute to public policy discussions on social media through their co...

Kofar Durbi Youth empowerment and reformation Initiative Kofar Durbi Youth empowerment and reformation Initiative
Nagogo Road Kofar Durbi
Katsina, 820212

KYERI is a youth organization primarily and was registered with state government on May 16' 2022

Kofar Sauri Youths Initiative Forum Kofar Sauri Youths Initiative Forum
Dauda Mani Road Kofar Sauri
Katsina, 820211

Old Boys Students Association of Charanchi Old Boys Students Association of Charanchi
Charanchi, Katsina
Katsina, 1313

A widest official platform for charanchi students association

Mai fakarawa fans Mai fakarawa fans
Katsina

The more you know the more you realize you don't know ✍️🤼✍️✍️✍️

Yoruba YOUTH organization yankara Yoruba YOUTH organization yankara
Yankara Faskari Local Government
Katsina, 1234

For unity and peace