Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U

Mu Masarautar Sayyada Fadima AS Ne

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 16/05/2024

An tambayi wani Malami
Me Za kace Kan Matsayin Imam Ali (A.S.) ?

Sai Malamin Ya ce :-
Wane Guri ne ya fi ko'ina Daraja A Doron ฦ™asa?

Sai ya ce: ฦŠakin Allah ๐Ÿ•‹

Sai ya ce : Wane aiki ne Allah ya fi So?

Sai ya ce: Sallah.

Sai Ya ce : wace Salla ce ta fi wahala?

Sai ya ce Sallar Asubahi.

Sai ya ce : a wane yanayi ne Mutum ya fi kusantar Allah A cikin Sallah?

Sai na ce : a yanayin Sujada.

Sai Ya ce : wace gaษ“ar ce ta fi darja a jikin dan-adam?

Sai ya ce : kai.

Sai ya ce : wanne wata ne mafi daraja a wajen Allah?

Sai ya ce : watan Ramadan.

Sai ya ce: wane dare ne ya fi daraja a watan Ramadan?

Sai ya ce : Daren lailatul-ฦ™adr

Sai ya ce: wace mutuwa ce ta fi darajar a gurin Allah?

Sai ya ce : Mutuwar Shahadah.

A wannan lokacin sai idon sa ya cika da hawaye .....

Ya ce : ya kai dan'uwa!

An kashe Imam Ali (A.S.) a watan Ramadan a daren lailatul-ฦ™adr kuma a masallaci a Sallar Asubahi yana tsaka da Sujada.

An sareshi a Goshinshi da takobin da aka tsuma shi a ruwan guba ( Poison)

Shi kaษ—ai aka haifa a mafi tsarkin waje wato ka'aba๐Ÿ•‹ kuma aka kashe shi a masallaci.

Ya yi shahada ranar 21 ga watan Ramadan shekara ta 40 BH

Ya allah k**ar yadda ka ambata
Cewa kiran sunan Ali shima zikiri ne โ™ฅ

Ya allah kasa duk wanda yarubuta ya Ali โ™ฅ

Kabashi shahada mafigirma alahiraโ™ฅ kahada fuskarshi data sayyadi Ali as โ™ฅโ™ฅ

Ya aliโ™ฅya Aliโ™ฅya Aliโ™ฅya Aliโ™ฅ
Ya Ali โ™ฅya Ali โ™ฅ ya Ali โ™ฅ ya Ali โ™ฅ

13/05/2024

"Ana ษ—aukar shekaru biyu don koyon magana,
daฦ™iฦ™a sittin sun yawa wajen koyar yin shiru kuma tabbas na ฦ™arshen yafi na farko amfani."

Maulam Mu Shehu Tijjani Yakan Yi Wata Uku Bai Ce Komai Ba

Suk Zancen Da Ya Zama Wajibi Sai Ya Yishi Ishara Yake Da Hannu Kawai Amman Bazai Ce Komai Ba

A Takaice Mu Koyi Halin Shiru Yawan Magana Ba Namu Bane

Akwai Sirri Cikin Shiru Haka Maulam Mu Khalipha Sir Sanusi Murabus Baya Magana Sai Murmushi Yakan Yi Wata Daya Maganar Sa Zaka Iya Irgata

Allah Ka Gadar Mana Da Shiru Bijahi Shehu Atiku Sanka

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 07/05/2024

INNร€ LILLรHI WA INNA ILAIHIR RAJI'Uลƒ

Matashiya Khadija Abba Muhammad Ta Rasรบ Sak**akon Hadarin Mรธta A Hanyar Kano

Allah Ya Yi Wa Khadijah Abba Muhammad Daguro Rasuwa Sak**akon Hatsarin Mota Da Ya Rutsa Da Ita Akan Hanyarsu Ta Zuwa Kano Daga Turabu, Karamar Hukumar Kiri-kasamma Jihar Jigawa, Yau Talata.

Za'a Yi Jana'izarta Da Misalin Karfe 5:30 Na Yammacin Yau Talata A Kofar Gidan Alhaji Muhammadu Daguro Dake Garin Turaษ“u, Karamar Hukumar Kiri-kasamma, Jihar Jigawa.

Allah Ya Jiฦ™anta Da Rahama!

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 07/05/2024

MATSAYIN IYAYEN ANNABI (SAWA) [1]

Bahasin Qur'ani

Farko, kafin mu kai ga wancan Hadisi da Jalo Jalingo (la'anannen Allah) tare da gayyar 'yan uwansa Wahabiyawa suke dogaro da shi wurin wannan aikin shed'anci na jefa Iyayen Annabi (S) a wuta, za mu fara da bahasin Qur'ani a matsayinsa na masdarin farko na dukkan Musulmi. Shin a harshen Qur'ani, mene ne matsayin Iyayen Annabi Muhammadu sallahu alaihi wa Aalihi sallam? Wace daraja Qur'ani ya ba su?

Qur'ani ya ce suna cikin masu sujjada. Ya kira su da ismul fa'il, ASSAAJIDUN, wato masu yawaita sujjada. Sujjada ga Allah siffarsu ce.

A cikin suratush Shu'ara'i, aya ta 218 da 219 Allah yana cewa:

ุงู„ู‘ูŽุฐููŠ ูŠูŽุฑูŽุงูƒูŽ ุญููŠู†ูŽ ุชูŽู‚ููˆู…ู . ูˆูŽุชูŽู‚ูŽู„ู‘ูุจูŽูƒูŽ ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽุงุฌูุฏููŠู†ูŽ

Tarjamah:
"Wanda yake ganin ka yayin da kake tashi. Da jujjuyawarka a cikin masu sujjada."

Ibnu Abbas (ra) yana daga cikin wad'anda duniyar Sunnah ta yi wa shaidar sanin ma'anonin Qur'ani, ya ce a game da wannan aya:

(ูˆูŽุชูŽู‚ูŽู„ู‘ูุจูŽูƒูŽ ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽุงุฌูุฏููŠู†ูŽ)ุŒ ู‚ุงู„: ู…ูู† ู†ุจูŠ ุฅู„ู‰ ู†ุจูŠุŒ ุญุชู‘ู‰ ุฃุฎุฑุฌูƒ ู†ุจูŠู‘ุงู‹.

Wato cewa, "Da jujjuyawarka a cikin masu sujjada," ya ce: 'daga Annabi ne zuwa ga Annabi har zuwa lokacin da aka fitar da kai a matsayin Annabi."

Marubucin RUHUL BAYAN ya ce: kalmar 'fis saajidin' tana nufin:

ููŠ ุฃุตู„ุงุจ ุงู„ู†ุจูŠู‘ูŠู† ูˆุงู„ู…ุฑุณู„ูŠู†ุŒ ู…ูู† ุขุฏู… ุฅู„ู‰ ู†ูˆุญ ูˆุงู„ู‰ ุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ูˆุงู„ู‰ ู…ูŽู† ุจุนุฏู‡ุŒ ุฅู„ู‰ ุฃู†ู’ ูˆู„ุฏุชู’ู‡ ุฃูู…ู‘ู‡ (ูŠุนู†ูŠ ุฅู„ู‰ ุขุฎุฑ ู†ุจูŠ ุนุจุฏ ุงู„ู„ู‡).

"Daga tsatson Annabawa da Manzanni, tun daga Adamu zuwa Nuhu zuwa Ibrahim zuwa na bayansa, har zuwa lokacin da mahaifiyarsa ta haife shi (ma'ana zuwa qarshe Annabi Abdullahi).

(RUHUL BAYAN/J2/875)

Mai Durrul Manthur (Suyud'i) shi ma ya kawo game da fassarar ayar cewa:

ุฃุฎุฑุฌ ุงุจู† ุฃุจูŠ ุนู…ุฑ ุงู„ุนุฏู†ูŠ ููŠ ู…ุณู†ุฏู‡ุŒ ูˆุงู„ุจุฒุงุฑุŒ ูˆุงุจู† ุญุงุชู…ุŒ ูˆุงู„ุทุจุฑุงู†ูŠุŒ ูˆุงุจู† ู…ุฑุฏูˆูŠู‡ุŒ ูˆุงู„ุจูŠู‡ู‚ูŠ ููŠ ุงู„ุฏู„ุงุกู„ ุนู† ู…ุฌุงู‡ุฏุŒ ููŠ ู‚ูˆู„ู‡: (ูˆุชู‚ู„ุจูƒ ููŠ ุงู„ุณุงุฌุฏูŠู†) ู‚ุงู„: ู…ู† ู†ุจูŠ ุฅู„ู‰ ู†ุจูŠุŒ ุญุชู‰ ุฃุฎุฑุฌูƒ ู†ุจูŠุง.

"Ibnu Abi Umar ya fitar a Masnadinsa, da Bazzar, da Ibnu Abi Hatim, da 'Dabarani, da Ibnu Mardawih, da Baihaqi a cikin DALA'IL daga Mujahid, game da ayar nan 'wa taqallubaka fis-sajidin", ya ce: (tana nufin) daga Annabi ne zuwa Annabi, har ya fito a matsayin Annabi."

Haka nan a TAFSIRUL BAGWI da TAFSIRUL KHAZIN a wurin tafsirin ayar nan ta 'fis-saajidin' an kawo cewa:

ุนู† ุนุทุง ุนู† ุงุจู† ุนุจู‘ุงุณ ู‚ุงู„: ุฃุฑุงุฏ (ูˆูŽุชูŽู‚ูŽู„ู‘ูุจูŽูƒูŽ ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽุงุฌูุฏููŠู†ูŽ) ููŠ ุฃุตู„ุงุจ ุงู„ู†ุจูŠู‘ูŠู†ุŒ ู…ู† ู†ุจูŠ ุฅู„ู‰ ู†ุจูŠุŒ ุญุชู‘ู‰ ุฃุฎุฑุฌูƒ ู†ุจูŠู‘ุงู‹ ููŠ ู‡ุฐู‡ ุงู„ุฃู…ู‘ุฉ.

"Daga Ad'au daga Ibni Abbas ya ce: 'Ayar wa taqallubaka fis-saajidin tana nufin a cikin tsatson Annabawa, daga Annabi zuwa ga Annabi, har (Allah) ya fitar da kai Annabi a cikin wannan alumma."

Ibnu Kathir a BIDAYA WAN NIHAAYAH a Kitabus Sirar Annabi (sawa) a babin da ke magana kan ambaton nasabarsa (sawa) ya kawo game da wannan aya cewa:

ุนู† ุงุจู† ุนุจุงุณ ููŠ ู‚ูˆู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ : ( ูˆูŽุชูŽู‚ูŽู„ู‘ูุจูŽูƒูŽ ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽุงุฌูุฏููŠู†ูŽ ) ( ุงู„ุดุนุฑุงุก : 219 ) ู…ู† ู†ุจูŠ ุฅู„ู‰ ู†ุจูŠ ุญุชู‰ ุฃุฎุฑุฌุช ู†ุจูŠุง.

"Daga Ibnu Abbas, game da zancensa Madaukaki: wa taqallubaka fis-saajidin, (yana nufin) daga Annabi ne zuwa Annabi har aka fitar da shi a Annabi."

A MAJMA'UZ ZAWAA'I na Haithamy a Kitabut Tafsir, ya kawo game da wannan aya cewa:

ุนู† ุงุจู† ุนุจุงุณ : ( ูˆูŽุชูŽู‚ูŽู„ู‘ูุจูŽูƒูŽ ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽุงุฌูุฏููŠู†ูŽ ) ( ุงู„ุดุนุฑุงุก : 219 ) ู‚ุงู„ : ู…ู† ุตู„ุจ ู†ุจูŠ ุฅู„ู‰ ู†ุจูŠ ุญุชู‰ ุตุฑุช ู†ุจูŠุง.

"Cewa daga tsatson Annabi har ka zama Annabi."

Kuma ya ce Bazzar da 'Dabarani s**a ruwaito, kuma mazajensu ingantattu ne.

Qurd'abi ma ya kawo a Tafsirinsa AL-JAMI'U LI-AHKAMIL QUR'AN game da ayar cewa:

- .... ( ูˆูŽุชูŽู‚ูŽู„ู‘ูุจูŽูƒูŽ ูููŠ ุงู„ุณู‘ูŽุงุฌูุฏููŠู†ูŽ ) ( ุงู„ุดุนุฑุงุก : 219 ) ู‚ุงู„ ู…ุฌุงู‡ุฏ ุŒ ูˆู‚ุชุงุฏุฉโ€ ููŠ ุงู„ู…ุตู„ูŠู†โ€ ุŒโ€ ูˆู‚ุงู„ ุงุจู† ุนุจุงุณโ€ :โ€ ุฃูŠ ููŠ ุฃุตู„ุงุจ ุงู„ุขุจุงุก ุŒ ุขุฏู… ูˆู†ูˆุญ ูˆุฅุจุฑุงู‡ูŠู… ุญุชู‰ ุฃุฎุฑุฌู‡ ู†ุจูŠุง.

Wato "Mujahid da Qatadah sun ce ana nufin a cikin masallata ne. Amma Ibnu Abbas ya ce, ai ana nufin daga tsatson ubanni, Adamu da Nuhu da Ibrahim har aka fitar da shi a matsayin Annabi.

DON HAKA IYAYEN ANNABI MUHAMMAD (SAWA) BA 'YAN WUTA BA NE, SAJIDAI NE ALAIHIMAS SALATU WAS SALAM!

In an lura, a wannan fassara ta ayar, ba ma batun jefa su wuta ake yi ba, a'a sam! Nunawa ake yi Ubanninsa (sallalahu alaihi wa Aalihi wa sallam) Annabawa ne. Tirqashi!! Wannan darasi ne a wani lokacin insha Allah!!!

07/05/2024

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! ๐ŸŽ‰ Umar Abba, Babaiyali Adamu, Usman Muhammed Wakilawa

07/05/2024
04/05/2024

Suwaye Ahlul Fatra ?

Wasu Al'umane Dabasu Riski Kiran Kowane Irin Annabi Ko Manzo Azaminsuba

Haka Abunyake Tsakanin Annabtar Annabi Isa Da Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad S.A.W. Wanda Ansamu Kusan Shekara Dari Shida Tsakaninsu

Dayawan Malamai Suntafi Akan Cewa Iyayen Manzon Allah S.A.W Sunacikin ( Ahlul Fatra )

Wannan Tasa Ake Samun Sabanin Tsakanin Wanda Suke Kallon Hadith Dakecikin Littafin Muslim

Dakuma Wanda S**a Dogarada Ayar Alqur'ani
Maigirma Datake Cewa

ูˆูŽู…ูŽุง ูƒูู†ู‘ูŽุง ู…ูุนูŽุฐู‘ูุจููŠู†ูŽ ุญูŽุชู‘ูŽู‰ูฐ ู†ูŽุจู’ุนูŽุซูŽ ุฑูŽุณููˆู„ู‹ุง

Ma'ana Bazamu Taba Azabtar Dakuba Harsai Munturo Muku Maikira Kunbujire Masa

Hakan Tasa Wasu Suke Kallon Rashin Ingancin Wancan Hadith Saboda Yaci Karo Da Ayar Alqur'ani Maigirma

Idankuma Harza'ace Hadith Din Ya Inganta Wasu Malamai S**ace

Kenan Manzon Allah S.A.W Ba Mahaifansa Das**a Haifeshi Sayyidi Abdullahi Da Sayyida Amina Yakenufi Ba

Saboda Ka'idace Ta Malaman Hadith Cewa Siffa Tafarko Datake Nuna Raunin Hadith Shine Yaci Karo Da Ayar Alqur'ani Maigirma

Akarshe Inaganin Fifita Wancan Hadith Din Akan Ayar Alqur'ani Tamakar Jinginawa Ubangiji Siffar Zalincine Shikuma Allah Baya Zalinci

Kuma Ko Ahankalce Ai Kaima Kasan Bazai Taba Yiyuwa Manzon Allah S.A.W Yaceci Iyayen Kowa Yabar Nasa Iyayensa Awutaba
Allah Kasamu Acikin Cetonsa S.A.W Ameen

BARKANMU DA SAFIYA

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 02/05/2024

โ€ขโ€ขโ€ขโ€ข โ€ขโ€ขโ€ขโ€ข
โˆ†
โˆ†โˆ†
โˆ†โˆ†โˆ†
Daga """ยฉZAUREN SHIRYEโœ“ SHIRYE""""

โ€ขAssalamu alaikumโ€ข masoya Annabi da iyalan shi k**ar kullum yauma munzo muku da wani shiri wanda zai sa musan suwane ne Ahlul baiti abinda muka sani mu kara sani wanda Ni ยฐยฐยฐnaseebat mai madafaยฐยฐยฐ zan ringa kawo muku shi.

โ€ขAmma wannan shiri yasha banban da wanda ake gabatarwa domin shi wannan zai zo muku da sigar tambyar junan mu wanda amsoshin zamu ringa samun su a comments section daga bakin mu ni daku baki daya.

โ€ขWani lokacin za'a kawo tmbya duk wanda s**a amsa akwai kyauta ba dan komai ba sai dan farantawa juna ta hanyar wannan tambaya da amsa kuma hakan zai kara mana kwarin gwuiwa ni daku baki daya.

โ€ขDuka wannan shiri zai zo muku a wannan masarauta mai albarka, muna fatan za'a bamu hadin kai yan uwa wajan amsa tmbyar yadda ya k**ata da kuma yin like da comments da kuma share dan samun albarkar kowa da kowa akan haka.

โ€ขShirin zai fara daga gobe juma'a insha Allah 3 may 2024 Bisa sahalaewar jagoranci wannan masarauta ta Sayyida Fadima As.

โ€ขAllah ya bamu istigama da sabati ya kara mana kaunar juna cikin Allah ya rabamu da aikin dana sani ya haska ka rayuwar mu har karshen ta ya sakawa iyayen mu da Alkairi.

ยฎ Naseebat mai madafa

30/04/2024

ABIN LURA GA MAI HANKALI!!!!

Alqur'ani ya fada mana, ALLAH Yana ma Mahaifiyar Annabi MUSA A.S Wahayi!
"ูˆุฃูˆุญูŠู†ุง ุฅู„ู‰ ุฃู… ู…ูˆุณู‰" ู‚ุตุต7

Sanna Qur'ani yafada mana Ita ma Mahaifiyar Annabi ISA A.S ma Ana mata WAHAYI
ูˆุฅุฐ ู‚ุงู„ุช ุงู„ู…ู„ุฆูƒุฉ ูŠุง ู…ุฑูŠู… ุฅู† ุงู„ู„ู‡ ุงุตุทูุงูƒ... ุขู„ ุนู…ุฑุงู† 42

Wani wuri Allah yace:
ูุฃุฑุณู„ู†ุง ุฅู„ูŠู‡ุง ุฑูˆุญู†ุง... ู…ุฑูŠู… 17

To mu bi muji ita kuma Mahaifiyar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Ya take???.

Su IYAYEN Annabi SAW Ba maganar Azaba akeba, Domin Allah Yace:

ูˆู…ุง ูƒู†ุง ู…ุนุฐุจูŠู† ุญุชู‰ ู†ุจุนุซ ุฑุณูˆู„ุฉ ุงู„ุฅุณุฑุงุก 15

Bazamu tabayin Azaba (Ga Mutane ba) har sai mun aiko musu Manxo. Tambaya Wane Manxo ne aka aiko ma Iyayen Annabi ????
Ba maganar Shirka akeba domin su Masu Sujjadane Ga Allah, Qur'ani ya fada mana.

ูˆุชู‚ู„ุจูƒ ููŠ ุงู„ุณุงุฌุฏูŠู†.... ุงู„ุดุนุฑุงุก 219

Wannan Ayar ta Tabbatar ba Mushrikai a Cikin su Baki daya, Yanxu maganar Matsayin su ake Da irin Martabarsu, Acikin littafin Ibnul Qayyim Al Jauziyyah wato "Zadul Ma'adi"
ุฒุงุฏ ุงู„ู…ุนุงุฏ .... ุงุจู† ุงู„ู‚ูŠู…....
Akan Taguwar da Annabi SAW Ya hau yayi HIJIRA..
ุฎู„ูˆุง ุณุจูŠู„ู‡ุง ูุฅู†ู‡ุง ู…ุฃู…ูˆุฑุฉ
"Kubata Hanya Umarni Ake mata!!!".

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi wasallam yayi HIJIRA daga MAKKA Zuwa MADINA Ya hau (RAKUMA) Taguwa lokacin da ya isa Madina Sai Sahabbai S**ayita Guri da fatan tareda Shaukin Su sauke Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam A gidajensu, Anata k**a ragamar Rakumar domin ta tsaya, Abin Al'ajabi Sai Annabi Sallallah Alaihi Wa Alihi Wasallam yace:

ุฏุนูˆู‡ุง ูุฅู†ู‡ุง ู…ุฃู…ูˆุฑุฉ
Ma'ana: Kubarta "UMARNI AKE BATA!!!"

Abinda Annabi yake nufi ALLAH Ke bata Umarnin inda Zata Tsaya!.

Idan Har RAKUMAR da Annabi Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallam ya hau Zuwa HIJIRA ('Yan kwanaki) Har ta kai Matsayin Karbar Umarni Kai tsaye daga Wurin ALLAH S.W.T. To ina ga MAHAIFIYARSA SAYYIDATUNA AMINAH Alaihas Salam Wacce Ta dauki CIKIN SA Wata da Watanni Har Wata TARA (9)????? Ita minene Nata MATSAYIN???

Fansar Uwata da Ubana Gareku ya sayyidatuna AMINAH
Da Sayyidi ABDULLAH Alaikumus Sallam

Suleiman Muhammad Muttaqah

28/04/2024

-MU KARANTA WAฦŠANNAN HADISAN.

-Maulana Imam Ali (AS) Yace, โ€œIna ji Muku Tsoron Abubuwa Guda Biyu, Bin Son Rai da Kuma Tsawaita Buri, Domin Shi Bin Son Rai Yana Kange Mutum Daga Bin Gaskiya, Tsawaita Buri Kuma Yana Mantar da Mutum Lahira.โ€

-Manzon Allah (S) Yace, โ€œWanda Ya fi Jaruntaka A Cikin Mutane Shine Wanda Ya Samu Galaba Akan Bin Son Ransa.โ€

-Maualana Imam Ali (AS) Yace, โ€œBin Son Rai Shine Mabuษ—in Fitinu.โ€

-Shugabana Imam Sadik (AS) Yace, โ€œKu Guji Bin Son Ranku Kamar Yadda Kuke Gudun Maฦ™iyanku.โ€

-Mai Girma lmam Kazeem (AS) Yace โ€œIdan Alโ€™amura Biyu S**a Bijiro Muku, A Cikinsu Kuma Baku San Wanda Yafi Alkhairi da Kuma Dai-dai Ba, Sai Ku Duba A Cikinsu Wannene Yafi Kusa da Son Ranku? To Sai ku Saษ“a Masa, Saboda Mafi Yawan Abun da Yake Dai-dai Shine Ku Saษ“awa Son Ranku.โ€

-Jagoran Rahama Manzon Allah (S) Yace, โ€œDa Yawa Bin Shaโ€™awar Lokaci Kaษ—an Yana Haifarwa Mutum Nadama da Baฦ™in Ciki Na Lokaci Mai Tsawon Gaske.

-Mai Martaba Imam Ali (AS) Yace, โ€œDuk Wanda Yabi Son Ransa to Sai ya ฦ˜asฦ™anta.โ€ A Wani Hadisin Kuma Yace, โ€œDuk Wanda Ya ji Daษ—i da Saษ“awa Allah to Sai Allah Ya Gadar Masa da ฦ˜asฦ™anci.

-Mai Daraja Imam Baฦ™ir (AS) Yace Manzon Allah (S) Yace: Allah Maษ—aukaki Yana Cewa lna Rantsuwa da Girmana da Kuma ฦŠaukaka ta Cewa, Wani Bawa Bai Fifita Son Ransa Ba Akan Abinda Nake So Face Na ฦŠaiษ—aita Alโ€™amuransa, Kuma Na ฦ˜untata Masa Duniyarsa.

-lna Rantsuwa da Girmana da Kuma ฦŠaukaka ta Cewa Wani Bawa Bai Fifita Abinda Nike So Kan Son Ransa Ba Face Malaโ€™ikuna Sun Tsare shi, Kuma Na Lamunce Masa Arziฦ™insa.

-Faษ—in Allah Taโ€™ala A Cikin Alฦ™urโ€™ani Mai Girma, โ€œDuk Wanda Yaji Tsoron Tsayuwa Gaba ga Ubangijinsa Ya Kuma Hana Kansa Daga Bin Son Rai to Aljanna Itace Makomarsa.โ€

-Allah Yasa Mu Dace Ameen

23/04/2024

๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€๐ŸŒน๐Ÿ•Œ๐Ÿ•‹ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…๐Ÿ•‹๐Ÿ•Œ๐ŸŒน๐Ÿ“ฟ๐Ÿ™ู…ูุญูŽู…ูŽู‘ุฏู๏ทบ๐Ÿฅ€

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 23/04/2024

ANNABI SHAKIRARI DA KABBARA

MAI CIN GARI DA KABBARA

YA HAU TUDU YA GANGARA

YA KARYA MASU KANGARA

MAI BIN ABIN DA YAU KIRA

TUBKARSA BABU WARWARA

BAKIN SA BABU FARFARA

MAI KYAN GIRA NA WANDARA

MAI HANA RABBI TUNZURA

IDAN KIYAMA TA TSAYA

GARESHI ZAMU TATTARA

YA JE GA RABBI YAI KIRA

ACE DASHI YAU BA JIRA

DANKA NA FARI KAUSARA

HANNUN SA NADA GWARARA

BAKIN SA NADA BISHARA

HARSHANSA NA DA NIZARA

SHI AKA BAIWA TABARA

SHINE YA KARYA GADARA

YAYI AGAR YA GAGARA

CIKINSA BABU DANGWARA

KAFARSA BABU GWANTARA

GOSHIN SA BABU TATTARA

GASHIN SA NA DA WARWARA

'YAN YATSU ZARAZARA

ANNABI MAI ISA DA ASA

DA BISA MAI HANKADE MAKE KASA

YA KAI KEYARSU KASA

YA HAU YA TUMURMUSA SUN CIKA BAKI DA KASA

SUN ZAMA KAMAR MAGURKUSA

DAGA YAU BABU SA IN SA ANNABI GAGARA GASA

SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 20/04/2024

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJ,UN

Rayuwa Kenan Allah Yajikan Mahaifiyar Wayannan Yara Allah Yasa Tahuta Tarasu Sak**akon Rashin Daukewar Jini Tabar Yara Jarirai 2 Gashi Babu Abin Dazaa Dinga Basu Shiyasa Yan Uwan Wayannan Marayun S**azo Wannan Masallaci Na KN MASJIDUN Domin Neman Taimakon Yan Uwa Musulmai Kamar Yanda Aka Saba Mahaifiyar Su Allah Yayi Mata Rasuwa Yau Kwana 6 kenan Da Rasuwarta Mahaifinsu Dama Baya Raye Tin Kafin A haifesu Allah Yayi Masa Rasuwa Sak**akon Hadarin Mota Bayan Ansamu Wacce Zata Dinga Kula Dusu Saidai Harga Allah Batada Halin Dazata iya Chiyar Dasu Shiyasa Muke Neman Taimakon Yan Uwa Musulmai Dan Allah Mutemaka Muceto Rayuwar Marayun Allah
Dan Allah Mai Abinci ko Madara Ko Kayan Sawa Ko Kudi Dan Allah Temako Baya Kadan Baya Yawa Abin Da Allah Yahore Muku Dashi Zakuyi

Ga Account Nombar Masallacin

2328144624
UBA Bank
KN MASJIDUN MUSULUM AND MUSULUM MASALLACI B.

Ko Kuma Account Din Wacce Zata Rikesu Kai Tsaye

2206015657
UBA Bank
Hauwa'u Garba

Ga Mai Bikatar Karin Bayani Zaku iya Samunsu A Kano Bacirawa Gidan Malan 3 Ko Kuma Kuce Gidan Ya,u Direba Shine Mahaifinsu Ko Kuma Akira Wannan Nombar 0834638905 Allah Yasa Mudace ๐Ÿ™

Dan Allah Ko Group 5 Mutura Hakanma Sadakane ๐Ÿ™
By
Malama Sadiya Habu
๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡
https://www.facebook.com/profile.php?id=61550002191413

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 17/04/2024

Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Annabi๐Ÿ’œ Muhammadu ๐Ÿ’œSallallahu Alaihi๐Ÿ’œ Wasalam๐Ÿ’œ Sallallahu๐Ÿ’œ
Dan uwa masoyin Annabi Muhammadu SAW karka wuce baka ce SAW ba

12/04/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Uthma Mma Ayama, Ummi Adamu, Waziri Abdullahi Maimalari

Wata Rana NANA AISHA (R.A) tana yanka naman akuya, sai ta cewa manzon Allah (S.A.W) Ya riqe mata ta yanka,,, sai ma'aiki ya Riqe mata naman tana yankawa, suna hira mai dadi ta soyayya har ta gama yankawa Bayan ta gama yankawa ta dora a wuta, ammah har wajen yammah naman yaqi dahuwa, ko juyawa na alama an sashi a wuta baeyi ba

Abin ya damu NANA AISHA (R.A) sai taje ta samu manzon Allah (S.A W) yana zaune tace masa ya Rasulullah (S.A.W) ni kam wani irin nama ne haka??? Tun safe na dora a wuta Amma har yanzu yaki dahuwa.

Sai manzon Allah (S.A.W) ya sakar mata murmushi cikin nishadi, kuma yana kallon fuskarta Sai yace Ya AISHA ai babu wani abu da zai rabeni, koh ya taba jikina wuta ta k**ashi, Ai Wannan naman ba zai taba dahuwa ba saboda na riqe shi.
!
Masoyan rasulullah kunji fah don haka mu kara damke shi, mu so shi da gaske, ALLAH ya tabbatar damu cikin Masoyansa Na haqiqa,
Allah Ya barmu da kaunarsa

Dan ALLAH kar ka wuce bakayi Shearing ba..

PLEASE Follow my PEGE

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 10/04/2024
09/04/2024

SANARWA(Official);

MAULANMU Ya Tabbatar Da Cewa Za'a Cika Azumi Talati(30), Saboda Rashin Ganin Wata a Yau.

Shugaban Mu'assasa Alh. Ibrahim Sheikh ฦŠahiru Bauchi, Shi Ya Faษ—i Hakan a Madadin Maulana Sheikh(R.A).

Saboda Haka Za'a Yi Sallar Idi Ne a Ranar Laraba(10-04-2024).

(Sanarwa Daga: M Daha Azhary Bauchi, 08033868941).

ALLAH Ya ฦ˜arbi Ibadunmu, Ya Sa Muna Daga Cikin 'Yantattun Bayi, Don Albarkar SHUGABA(S.A.W)๐Ÿ™๐Ÿ™๐Ÿ™

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 06/04/2024

~Duk Ranar da Maulanmu shehu dahiru Usman bauchi RTA yayi wafati
:
______ ko ba'a fadawa kowa ba wallahi sai kowa yaji ajikinsa.
:
Saboda haka kuyi hakuri ku Daina gaggawa domin wallahi bazaku san cewa irin su maulan mu shehu dahiru Usman bauchi RTA Wata garkuwa bane ba garemu Yan Nigeria da ma Africa Baki daya ba sai Ranar da yayi wafati,

Ya Allah ka karawa maulan mu shehu dahiru Usman bauchi RTA lafiya da Nisan kwana albarkarcin annabi sallalllahu alaihi wasallam ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ

Amma kucigaba su Sheikh Abul fathi sani Attijjani ne gasu Nan daidai daku wallahi zasu ci uwar kowa da hujjah har inda ba,a xungurowa kunsanshi zai rushe shi shi ba damuwarsa ba ne

03/04/2024

*DALILAN SHAN AZUMI GUDA GOMA SHA BIYU (12)*

*Sharia ta Amincewa masu larura susha azumi:*
ยป Wasu zasu Rama.
ยป Wasu su ciyar.
ยป Wasu baza su ramaba, kuma bazasu ciyar ba

GASU KAMAR HAKA:
1. Mara lafiya, zaisha azumi idan ya warke sai yarama.

2. Matafiyi, zaisha azumi saboda tafiya, saiya Rama daga baya.

3. Mace mai jinin al'ada zatasha azumi idan tayi tsarki, saita Rama.

4. Mai jinin haihuwa, idan jini yadauke sai tarama.

5. Mai ciki, wacce taji tsoron wani abu zai sameta, koya sami dan cikinta.

6. Mai shayarwa, wacce taji tsoron cutuwa gareta ko dan da take shayarwa.

7. Tsoho ko tsohuwa wadanda tsufa ya hanasu yin azumi, sai su ciyar kawai babu ramuwa akansu.

8. Mahaukaci, idan ya warke sai ya rama idan kuwa, babu waraka ya sauka akansa babu ramuwa babu ciyarwa.

9. Qaramin Yaro, azumi ba wajibi bane akansa, sai dan sabawa.

10. Mai farfadiya, idan farfadiya tazowa mutum yana azumi, bazai ramaba idan ya farfado.

11. Mai ciwon Qishirwa, wanda bazai iya azumi ba, sai ya dinga ciyarwa kawai.

12. Mai ciwon yinwa Ulcer (olsa) wanda, baya iya daukar lokaci mai tsawo sai yaci abinci, shima sai ya dinga ciyarwa.

SHARHI:
Mai ciki da mai shayarwa, suna matsayin marasa lafiya idan sun sami dama sai su Rama. Amma, wasu Malamai suna ganin idan ciyarwa ma s**ayi yayi dai-dai.
WALLAHU A'ALAM.

Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. kuyi follow din Shafin mu
Humira Yahaya

01/04/2024

โ€ขAntaba Tambayar Marigayi Umar Abdul'aziz Baba Fadar Bege(Kafin Wafatinsa) Akace Masa~ Wacce Shawara Zakabawa Irinka(Masu Yabon Annabi)?

Sai Fadar Bege Yace" Inabawa Duk Wani Mai Yabon Annabi(SAW) Shawarar Dafarko Ya Tsarkake Zuciyarsa Yayi Yabon Don Allah Don Annabi(SAW) Kada Yayi Yabon Don Neman Wani Abun Duniya Kokuma Don Neman Suna, Kada Sha'iri Yatsaya Yashirya Kasida Danufin Sai Kasidarsa Tafi Takowa Haryana Kokarin Saka Kalamai Marasa Kyau Kuma Wadanda Bana Ilimi Ba.

Fadar Bege Yakara Dacewa"Kar Mutum Yasake Yazama Maiyin Begen Annabi(SAW) Batareda Yayi Karatu ba Domen Hakan Barnane Kuma Badaidai Bane, Kafin Mutum Yafara Yaje Yafara Sanin Sira(Tarihin Annabi) Sannan Yayi Kokarin Duba Littittafan Magaba Wadanda S**a Wake Annabi(SAW) Haka Idan Mutum Ya Rubuta Kasidar Kafin Yafara Rereta Yafara Zuwa Wajen Malamai Domen Adubata Idan Da Gyara Ayi Idan Kuma Babu Saiyaje Yaitaiwa Annabi(SAW)

Fada Yace" Kada Sha'iri Yana Hassada Da Dan'uwansa Sha'iri Kuma Kada Manya Suna Danne Kanana, Kada Kana Zagi Ko Kyamar Wani Don Yayima Kuskure Koda Zakai Fadan Kayishi Cikin Salo Na Nasiha Wadda Zaiji Cewa Baka Kyameshi Ba, Kuma Kada Muna Karya Alkawari Wanda Muka Daukarwa Masoya Annabi(SAW) Yayin Zuwa Wajen Taron Mauludin Annabi(SAW) Ko Majalasin Biki Ko Suna, Domen Rashin Cika Alkawari Ba Halaiyar Masoya Annabi Bane.

Wasu Shawarwari Kenan Wanda Fadar Bege Yabawa 'Yan uwa Sha'iran Annabi(SAW) Kuma Wannan Shawarar Dazamuyi Kokarin Aiki Da'ita Tabbas Zamukara Samun Cigaba Da Hadin Kai Atsakaninmu Bakidaya, Kuma Koda Masu Inkarin Harkar Bazasu Samu Damar Yimana Wasu Abubuwa Wanda Zamuji Ba Dadi Ba, Muna Fatan Allah Yasa Muyi Munji Kuma Zamuyi Aiki Da Wannan Shawarar, Shi Kuma Allah Yakara Jaddada Rahama Agareshi Amin.

01/04/2024

๐ŸŒดMAULUDIN IMAM HASSAN (3)
************************
,
HAIHUWAR SA
--------------------------
,
An haifeshi ne a madina bayan hijira kenan, amma sai dai an sami saษ“ani da kan lokacin da shekarun da aka haifeshi
,
Mafi rinjayen zance shine an haifeshi ne a watan RAMADAN shekara ta 3 bayan hijira k**an yanda ALLAITH Bn SA'ADIN YA TAFI AKAN HAKA
,
yace FAฦŠIMA ฦณAR ANNABI ta haifi Hassan ne a cikin watan ramada shekara ta uku bayan hijira
,
Kuma ta haifi Husaini A watan sha'aban a shekara ta 4 bayan hijira daga makka zuwa madina
,

Zan ci gaba

Elmusaddiq kano

31/03/2024

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN ร—3
Allah yayiwa sheikh buhari kamba rasuwa shugaban madalisar tijjaniya ta jahar kebbi.
anyi jana,izarsa da misalin karfe 3:pm
shiyar mallamawa muna rokon Allah ubangiji ya gafarta masa ya karbi bakuncinsa da dukkan musulman da s**a rigamu gidan gaskiya.๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ

31/03/2024

Wannan hotone mai dunbun Tarihi , Wannan hoto da kuke gani Shine lokacin da Maulana Sheikh Alhaji Sharif Rabiu Usman Baba R T A , ya dauki kofi a gasar waka da Tsohon Gwamnar Jihar Kano Engineer Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a lokacin Munkinsa na farko 1999 zuwa 2003 Wanda Maulanmu shiyayi na daya (1) Malam Rufa'i Ayagi ya zama na biyu (2) sai kuma Malam Auwalu Umar Gawuna yazo a matsayin na Uku (3) .

A lokacin Manya Manyan Masana a bangaren Sanin Ilimai na Waka sune s**ayi Alkalanci , Sannan s**a tabbatar da cewa lallai ,Maulanmu Sharif Rabiu Usman Baba R T A ya San waka , kuma ya iya waka , har wasu daga cikin su kecewa saboda irin Sanin da Maulanmu yayiwa waka k**ata yayi ace yana daga cikin Manyan Alkalan waka a wannan gasa da ta gudana a lokacin .

Alhamdulillah muna kara godiya ga Allah madaukaki da yayi mana wannan Jagora kuma Uba na alfahari da fita kunya a ko'ina . Muna rokon Allah ya kara Masa Kusanci , Allah ya kara yalwata Makwancin sa , Yasa Makwancin sa ya Zama Riyadun min riyadul Janna . Mu kuma Allah ya bamu Albarkacin irin baiwar da Allah yayi musu , Allah ya kara had a kanmu ya tsaremu daga santsin halara.

Muna fatan duk inda Masoyin Maulanmu yake zaiyi farin ciki da ganin wannan hoto da kuma sannin wannan tarihi a takaice , Sannan muna rokon Ku da kuyi mana sharing Dan ragowar Masoya suma su amfana.
Sulaiman Iliya Jibril Dan Amanan Shariff Rabiu Usman Baba R T

31/03/2024

Shekh Ibrahim Balarabe Jega
A Yau 20 Ga Watan Ramadan Shekh Balarabe Jega Yake Cika Shekara 69 Da Karba Kiran Allah

Shehu Balarabe Jega Ya Rasu A Hjira 1376
ุนุงู… ุฅู‚ุจุงู„ ุงู„ุฎูŠุฑุงุช
Ranar Lahadi 20 Ramadan Bayan Sallahar La'asar

Shehu Balarabe Jega Ya Tafiyar Da Rayuwarsa Cikin Hidimar Addinin Allah Da Yada Faila Ta Shehu Ibrahim Inyass R.T.A
Idan Kaduba Littafansa Zakasan Irin Gudummawar Da S**a Bayar A Faila

Shine Wanda Yayi Wadannan Littafai
ุฏุฑุฑ ุงู„ููƒุฑ
ุบูˆุฑู† ู‚ุถูŠุฉ
Da Sauran Littafan Da Ya Wallafa

Shekh Balarabe Jega Shine Babban Aminin Shekh Balarabe Gusau
Wanda Su Din Jiki Biyu Ne Da Ruhi Daya

Muna Fatar Albarkar Shekh Balarabe Jega Da Shekh Balarabe Gusau Allah Yabamu Lfy Da Zaman Lfy

Ya Allah Wadannan Bayi Naka Sun Sadaukar Da Komai Nasu Dan Gina Ya'yan Muslimi Tareda Basu Shiriya

Ya Allah Kaqara Masu Karama
Ya Allah Kabamu Albarkar Su Dan Tsarkin Zuciyar Annabi S,a,w

โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ
Abba Ahmad Siddiq Tafkitara
Mak**an Zawiyya

Photos from Ina Masoya Sayyada Fadimatu Zahara'U's post 30/03/2024

Wannan Itace Sayyada Halimatu Sadiya Matar Maulana Sheikh Alhaji Sharif Rabiu Usman Baba R T A kuma itace Mahaifiya ga Khalifa Sharif Nura Sarkin gida da Yayan shi Sharif Muhammad Nafsuzzakiya Allah ya kara musu yarda Amin , Tarasu tun Shekara Goma Shatakwas (18)da s**a gabata tarasu ne a Ranar Alhamis 27, ga watan Sha'aba 8, 1427. Wanda yayi dai dai da Shekarar 2006 Watan bature .

Muna rokon Allah ya kara mata Rahama da kusanci da Manzon Allah S A W Amin .
Wato wani irin baiwa da kuma Iko na Allah , Shine tarasu ranar Alhamis, (1) Maulana AKARAMUNNASI mijin ta shima Ranar Alhamis(2) Sannan 'Ya'yan ta suma Ranar Alhamis (3) Khalifa Fatihu da Sharif Nafsuzzakiya.

Duk masoyin Manzon Allah S A W dayaga Wannan rubutu ya kuma karanta , to ya daure yayi musu hadiyan Salati duk Wanda ya iya ko wani irine hadiya ga ruhin su , Sannan kuma duk Wanda ya karanta ya karu to yayi mana Sharing Dan Yan Uwa Masoya suma su fa'idantu .

Allah ya biya mana bukatun mu na Alkhairi saboda Albarkacin su a fadar Shugaba Annabi Muhammad S A W .
Sulaiman Iliya Jibril Dan Amanan Shariff Rabiu Usman Baba R T A

30/03/2024

Akwai wasu muhamman abubuwa guda biyar wadanda aka bawa Manzon Allah (S.A.W)
babu wani Annabi da ya samu ko da daya daga cikin su

Manzon Allah (S.A.W)yana cewa an aiko ni ne ga dukkan al'ummar duniya amma su sauran Annabawa kowanne ana aikensa ne ga mutanensa

Kuma ana razanar da abokan gabata a ko ina suke ko da kuwa tsakanina da su akwai tafiyar wata daya

Kuma an halatta mini ganima su kuma sauran Annabawa an haramta musu sai dai su kona

Kuma an sanya kasa ta zama masallaci a gareni da al'ummata a ko ina sallah ta same su sai tsaya anan su yi amma sauran Annabawa da jama'arsu dole sai dai suyi ta a masallaci

Kuma an za6eni cik**akin Annabawa
babu wani Annabi baya na dukkan wadannan abubuwa da aka fada Manzon Allah (S.A.W) kadai ne ya ke6anta dasu

Allah ya Kara Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasalam Daraja Ameen

By Humaira Yahaya

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Jigawa?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Thanks for being a top engager and making it on to my weekly engagement list! ๐ŸŽ‰ Umar Abba, Babaiyali Adamu, Usman Muhamm...

Category

Telephone

Address

Tsangaya
Jigawa
08039480482
Other Public Figures in Jigawa (show all)
Muhammad Abba Muhammad Abba
Kwaimawa
Jigawa, 2081

Umar farouq layoyo grm Umar farouq layoyo grm
Auyakawa Street
Jigawa

Peaceful and truth

E-Islamic da'awah E-Islamic da'awah
Jigawa, LAWAL

Islamic progress electronically

Umar alvaseerky Umar alvaseerky
Baseerka
Jigawa, 07063618312

MUSULMI INA MAFITA

Sautin sunnah Sautin sunnah
Dutse Gida Dubu
Jigawa

Wannan group din anbude shine domin fadakarwa .nishadantarwa .

Manufar Halittar Mu Manufar Halittar Mu
25A Tukur Housing Estate
Jigawa

Political Organization for the success of Bola Ahmed Tinubu presidential Ambition.

Garzali G Ya'u Garzali G Ya'u
Kofar Kudu
Jigawa

Personal page

SB Graphics SB Graphics
Bulangu
Jigawa

Comrade Nura Aminu Comrade Nura Aminu
Jigawa
Jigawa

Nura Aminu Jigawa state Gwaram L.G Digijin town Youth_Scientist_Researcher

Rabi'u Ibrahim Rabi'u Ibrahim
Magama Jahun Gidan Kurna Jigawa
Jigawa, MAGAMA24

Rabi'u ibrahim

Abdulrahman Lawan Abdulrahman Lawan
Mama Street Sabon Gari Kiyawa
Jigawa

We are always try to be honest pple