Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria, Religious Center, NO 5A Shagari Quaters Old Kano Road Sabon Gari Kudan, Kaduna.

An bude wanna shafi ne domin isar da sakon Musulunci, tare da wayar da kan al'umma bisa koyarwar Annabin Rahma (saww) da iyalan gidansa tsarkaka da sahabbansa managarta.

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 07/05/2024

Ga masu bukatar Kai yaransu makarantar Kwana (Boarding School) Ɓangaren Junior Secondary School.
Al-Akram Islamic Academy Kudan tayi maku tanaji mai kyau don inganta karatun ƴaƴanku tare da basu cikakkiyar tarbiyar addini da zamantakewa.
Muna da shaidar Hukumar Ilimi (Ministry of Education) Wato Muna da Rijista da Hukumar Ilimi yaronka yana kammalawa zamu bashi takardar shaida wanda zaije makarantar gaba da ita domin dora karatunshi.
Kira kai tsaye: 07020507070
Whatsapp: 08032439792

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 06/05/2024

ZAMAN MUHADARA

Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (S) Kudan tacigaba da gudanar da zaman Muhadara, wanda take gudanarwa duk darasin ƙarshe na ranar Lahadi. Wanda a wannan satin Ɗalibai Guda biyu s**a gabatar da Muhadara. Wadda ta fara gudanar da Muhadara Zainab Aliyu, Sai Dalibi Kamilu Abdullahi.

Daliba Zainab Aliyu ta gudanar da Karatun Muhadara akan Ɗalibun'imi, yadda ya k**ata ɗalibi ya kasance wajan neman Ilimi, da yin aiki da shi. Ɗalibi Kamilu Abdullahi, ya gudanar da karatun Muhadara akan Hadisan da suke magana akan iyalan gidan Manzon Rahama ( S ) tare da yadda Hadisan suke magana akansu da irin kimarsu da Darajar da suke da ita.

Wanda ya jagoranci wannan zaman Muhadara Malam Auwal Akil Dabai shi ne ya jagoranci zaman Muhadara na wannan satin.

Wannan darasin ana gudanar da shi ne domin faɗakarwa akan inganta tarbiyyah Ɗalibai ta hanyar bayanin akan ayoyi da hadisai dake magana a bangaren kyawawan ɗabi'u.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
06/May/2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 05/05/2024

KUTUBUL ARBA'A
An gudanar da zaman muhadara a Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (S) Kudan wanda Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan yayi bayani akan Littafan da Shi'a suke dogara dasu... wanda ake kira da KUTUBUL ARBA'A k**ar yadda SUNNAH suke da KUTUBUL SITTA tare dayin takaitaccen bayani akan waɗannan Littafai.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
05 May 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 04/05/2024

DARASIN AKLAQ

Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (S) Kudan tacigaba da gudanar da zaman Aklaƙ wanda take gudanarwa duk darasin ƙarshe na ranar Juma'a.

Wannan darasin ana gudanar da shi ne domin faɗakarwa akan inganta tarbiyyah Ɗalibai ta hanyar bayanin akan ayoyi da hadisai dake magana a bangaren kyawawan ɗabi'u.

Shugaban Makarantar Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan shine ya jagoranci zaman a wannan satin.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
03 May 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 30/04/2024

ZAMA NA MUSAMMAN
A ranar Lahadi 28 April 2024 ne Makarantar Ma'ahad dake Kudan ta gudanar da zama na musamman domin nazarin hanyoyin da za'a bi domin bunƙasa cigaban makarantar da Ɗalibai.
Ɗaliban makarantar sun bayar da shawarwari domin ganin an bunƙasa cigaban makarantar tare da amfanar da al'ummar da kuma yunkurin samar da ilimi mai inganci.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
30 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 27/04/2024

DARASIN AKLAQ

Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (S) Kudan tacigaba da gudanar da zaman Aklaƙ wanda take gudanarwa duk darasin ƙarshe na ranar Juma'a.

Wannan darasin ana gudanar da shi ne domin faɗakarwa akan inganta tarbiyyah Ɗalibai ta hanyar bayanin akan ayoyi da hadisai dake magana a bangaren kyawawan ɗabi'u.

Shugaban Makarantar Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan shine ya jagoranci zaman a wannan satin.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
27 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 22/04/2024

ZIYARAR TA'AZIYA GA MAHAIFIN MALAMIN MAKARANTAR MA'AHADUR RASULIL-AKRAM ( S ) KUDAN

A jiya 21/4/2024 dai-dai 11/Shawwal/ 1445h, Allah Ta'ala yayiwa mahaifin Malam Abubakar Ƙasim, ɗaya daga cikin Malaman Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (saww) Kudan rasuwa ajiya Lahadi.

Shugaban Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram Kudan Shaikh Isma'il Yusha'u Kudan tare da Shugaban ɓangaren Hauzah na Makarantar Malam Auwal Aƙilu Dabai da wani ɓangaren na Ɗaliban makarantar sunje Ta'aziya da jaje da rashin Mahaifin Malam Abubakar Ƙasim.

Daga bisani anyi ta'aziya tare da addu'o'i, Allah Ta'ala ya kai ladan dukkan wata addu'a da aka gudanar ga Ruhin Marhum Malam Kasim..

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
22 April 2024

22/04/2024

Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (saww) Kudan tana miƙa ta'aziyyarta ga ɗaya daga cikin Malaman Makarantar Malam Abubakar Ƙasim bisa rasuwar mahaifinsa jiya 21 April 2024 bayan magariba.
Muna roƙon Allah ya jiƙanshi yayi masa gafara ya karɓi uzurinsa sannan ya sadashi da ceton Annabi da iyalanshi.
Allah ya bama iyalanshi haƙurin jure wannan rashin.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
22 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 22/04/2024

Zasu daga cikin hotunan zama na Masamman wanda Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan yayi da Ɗaliban makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (saww) Kudan.
An gudanar da zaman ne akan sabbin tsare-tsare domin inganta karatun dalibai tare kuma da bayani akan abubuwan da s**a shafi ɓangarorin uku na Makarantar.
Wannan makaranta tana da bangare uku: 1. Ɓangaren Hauza 2. Ɓangaren Tahfiz 3. Ɓangaren Boko (Nursery, Primary da kuma Secondary).

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
22 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 21/04/2024

TARON WALIMAR AURE

A ranar Asabar 20 April ne aka gudanar da taron walimar Auren Ɗaliban Ma'ahadur Rasul Al-Akram Kudan A'isha Abdulkadir Kudan.
An gabatar da walimar ne a Husainiyyar Rasul Al-Akram Kudan, Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan Shugaban Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram Kudan shine ya gabatar da Jawabi tare da nasiha ga ma'auratan.

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 21/04/2024

MALAMAI A BAKIN AIKI
Jajartun Malaman Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram Kudan a yayin da suke koyar da Ɗaliban makarantar a satin farko na zangon karatu na farko.
Muna rokon Allah yasa an dawo a sa'a kuma Allah ya bada Nasara ya karawa malamai da dalibai hazaka.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
21 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 21/04/2024

ZANGON KARATU NA FARKO
Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram Kudan ta dawo daga hutun karshen shekara inda taci gaba da karatu a zangon farko na sabuwar shekarar karatu.
An dawo hutun ne a ranar Alhamis 9 Shawwal 1445h, 18 April 2024.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
21 April 2024

18/04/2024

Fifth Agenda

18/04/2024

Fourth Agenda

18/04/2024

Third Agenda

18/04/2024

Second Agenda

18/04/2024

First Agenda

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 18/04/2024

AL-AKRAM ISLAMIC ACADEMY KUDAN
Our effort is to provide your child with five things before they graduate from us.
It's like this: 👇

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 18/04/2024

AL-AKRAM ISLAMIC ACADEMY KUDAN
Ƙoƙarinmu shine mu samarwa yaranku abubuwa guda biyar kafin su kammala karatunsu a wajenmu.
Gasu k**ar haka: 👇

15/04/2024

MA'AHADUR RASUL AL-KARAM ( SALLALLAHU ALAIHI WA ALIHI ) KUDAN
Address: NO 5A Shagari Quaters Sabon Gari Kadan, Kudan LGA, Kaduna State
Tel: 09128282624, 08032439792, E-mail: [email protected]
KOMAWA MAKARANTA
ZANGON KARATU NA FARKO A SHEKARA TA HUDU
Muna sanar da kafatanin Ɗaliban wannan makaranta ɓangaren Hauza Ilmiyyah masu kwana (Boarding) da masu jeka ka dawo (Day) da ɓangaren Tahfizul Kur’anil Karim da Secondry ɓangaren masu kwana (Boarding) cewa za'a koma karatu ne ranar Alhamis 09 Shawwal 1445H daidai da 18/04/2024M.
Wajibi ne ga kowane Ɗalibi ya dawo makaranta a wannan rana, saɓama hakan zai iya kawai ga dakatar da Ɗalibi.

Hukumar Makaranta
6 Shauwal 1445h / 15 April 2024

08/04/2024

3- WACCE AKA SADU DA ITA BA TA DA CIKI DA YARINYA DA TSOHUWA:-

5. Idan aka saki macen da aka sadu da ita, kuma ba ta kasance yarinya ba, ba kuma tohuwa ba, ba kuma mai ciki ba, idan ta kasance ‘Mutakimatul Haid’ (wacce jini ke zuwa mata duk wata sau ɗaya), to iddarta ita ce jini sau biyu, amma idan wacce tana cikin shekarun haila ne, sai dai cewa ita ba ta haila, to iddarta ita ce wata uku.
6. Idan lokacin aure ya ƙare, a aure munƙadi’i, ko ya kyautar mata da sauran muddar, kuma ya sadu da ita, to iddarta idan ta kasance ‘mustakimatui haid’ ce, to jini biyu ne. Amma idan ta kasance a shekarun haila ne, sai dai ita ba ta yin haila din, to iddarta kwana arba’in da biyar (45) ne.
7. Idan mijin wacce aka sadu da ita ya rasu, to iddarta wata huɗu da kwana goma ne.
8. Idda ba ta sauka a kan wacce aka sadu da ita a yayin da aka sake ta ko lokacin da auren ya ƙare, ko aka kyautar matar da sauran lokacin,ko da kuwa ya kasance mijin ba ya tare da ita ne, kuma bai sadu da ita ba na tsawon lokaci.
9. Idan ya kasance mace tana ganin haila, sai dai a wasu lokuta ne masu tazara, idan ya kasance tazarar sama da wata uku ne a tsakanin haila biyu, to iddarta idan aka sake ta wata uku ne. Amma idan tazarar lokacin wata uku ne, ko ƙasa da wata uku, to iddarta tsarki uku ne. Amma wacce aka yi mutu’a da ita, iddarta yin haila ne. Idan ya kasance tana haila ko da kuwa tazara tsakanin haila biyu ya kai sama da wata uku.
10. Ba wajibi ba ne mazinaciya ta yi idda ga wanda ya yi zina da ita. Eh, to idan ta yi aure sai aka sake ta, ko mijin ya rasu, to wajibi ne ta yi idda.Bai halasta ba ta yi wani auren, ko wani ya aureta a lokacin da take cikin idda, ko da kuwa ita ba ta lizimci kiyaye hukuncin ba.
11. Idan mace ta ƙulla alaƙa da wani namiji, alaƙar da ba ingantacciya ba a addini (misalin alaƙar ƙawance da abu mai k**a da wannan), idan wannan alaƙar bisa imaninta da kuma a addininta hukuncin zina ne, to ba wajibi ba ne idda a kanta bayan rabuwarta da namijin, kuma ya halasta a aure ta a lokacin. Amma idan hakan ya kasance aure ne ko da kuwa bisa iyakar abinda ta yi imani da shi ne, to wajibi ne a kanta tayi idda bayan rabuwarta da namijin. Iddar ta wadatar bisa yadda take a addininta ta ɓangarenadadi da yadda ake yin iddar.
12. Idda tana farawa ne ga matar da aka saki daga tsarkin da mijinta bai sadu da ita ba a cikinsa. Sannan ta ga haila, sai ta yi tsarki. Sanna ta ƙara ganin wata haila din, ta ƙara yin tsarki. Sai ya kasance ta k**ala tsarki uku kenan wanda a tsakaninsu akwai haila sau biyu.
13. Idda tana farawa ne ga macen da aka aure ta auren mutu’a da ganin jini (haila) bayan ƙarewar mudda, ko kyautar da sauran lokacin gare ta, sai ta yi tsarki daga wannan hailar. Sai ta ƙara ganin haila a karo na biyu, sai ta ƙara yin tsarki. Sai ya kasance ta yi haila biyu cikakku ke nan, tare da tsarki ɗaya a tsakaninsu. Da a ce lokaci zai ƙare ko a kyautar mata da sauran lokacin a yayin da take haila, ba za a ƙirga da wannan hailar ba. Kai, dole ne ma ta jira yin tsarkinta sannan ta ƙara yin wata hailar,sai ya kasance wannan ita ce ta farko, sai ya zamo tana buƙatar yin haila ta biyu bayan wannan ta farkon.
14. Babu bambanci tsakanin ƙarancin lokaci ko tsawonsa tsakanin hailoli guda biyu ko tsarki.Zai iya yiwuwa ta sanya hailar a mafi kusan na lokaci ta hanyar yin amfani da magani, idan ta so yin hakan. Wannan fa tare da kiyaye ƙa’idar ƙarancin kwankin haila kwana uku (3) da kumaƘarancin tsarki kwana (10).
15. Idan aka saki matar da aka sadu da ita, kuma ba yarinya ba, ba kuma tsohuwa ba, ba kuma wacce ba a sadu da ita ba, sai mijinta ya rasu, idan ya kasance iddar da take ta kome ce, to iddar sakin ta ɓaci, sai ta koma ta yi iddar wafati. Idan kuma iddar ba ta kome ba ce,ma’ana ba’ina ce, sai ta ƙarasa iddarta ta saki.Babu iddar wafati a kanta.

ALHAMDU LILLAH

Kuna iya tuntubar marubucin ta wannan lambar a whatsapp wa.me/2348032439792 domin tambaya ko karin bayani

Telegram: https://t.me/fiqhunshia

Whatsapp: https://chat.whatsapp.com/E39sAnECkqaBLRha6eCDiu

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria

www.rasulilakramfoundation.org

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 07/04/2024

ZAMAN KARATUN ALƘUR'ANI MAI GIRMA
Domin neman albarkar dake cikin watan Ramadan da kuma ɗebe kewa da karatun Al-ƙurani mai Girma Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (saww) dake Kudan ta shirya zama na musamman domin Tilawar Al-ƙur'ani mai Girma.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
28 Ramadan 1445H
07 April 2024

06/04/2024

wani bangare na rufe ka
25 Ramadan 1445H daidai da 04 April 2024.

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 06/04/2024

YADDA AKA GUDANAR DA KARATUN ALƘUR'ANI MAI GIRMA A HUSAINIYYAR RASULIL AKRAM (SAWW) KUDAN
Domin neman albarkar dake cikin watan Ramadan da kuma ɗebe kewa da karatun Al-ƙurani mai Girma Makarantar Ma'ahadur Rasul Al-Akram (saww) dake Kudan ta shirya zama na musamman domin Tilawar Al-ƙur'ani mai Girma.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
27 Ramadan 1445H
06 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 06/04/2024

SHAN RUWA (BUƊE BAKI)
A karo na uku a ranar Shahadar Imam Ali (Karramallahu Wajahahu) Husainiyyar Rasulil Akram dake NO5A Shagari Quarters, Old Kano Road, Sabon Gari Kudan, ta gabatar da bude baki ga kimanin mutane 300 a shirinta na ciyar da mutane 1,500 a kowane watan Ramadan kuma a kowace Shekara.
Wannan ya faru ne bayan tsarinta na kullum wanda ake raba ƙullin Dabino da ƙullin Suga (Sukari) ga duk wanda ya sami halartar wajen Karatu wanda Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan ke jagoranta a Husainiyyar kuma a kowace rana kimanin mutane 150 ne ke halartar wajen Karatun.
Bayan haka akwai Ɗalibai dake zaune a Makaranta waɗanda basu tafi hutu gida ba su 22 wanda Husainiyyar ke gabatar masu da abincin bude baki da abincin da zasuyi Sahur a tsawon watan na Ramadan baki ɗaya.
Duba anan 👇
https://t.me/ifdaarsaeemfishahrillah

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
27 Ramadan 1445H
06 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 06/04/2024

AN RUFE KARATUN LITTAFIN ZADUL ƘULUB FI SHAHRILLAH.
A ranar Alhamis 25 ga watan Ramadan 1445H daidai da 04 April 2024 ne Sheikh Isma'il Yusha'u Kudan ya rufe karatun da yake gabatarwa a Husainiyyar Rasulil Akram dake NO5A Shagari Quarters, Old Kano Road, Sabon Gari Kudan.
An rufe karatun ne bayan kwashe kwanaki 25 ana gabatar da shi a kowace rana da misalin karfe 4:00 zuwa 6:30 na yammacin kowace rana.
A lokacin rufe karatun Sheikh ya gabatar da tafsirin aya ta 183 zuwa aya ta 185 a cikin Suratul Baƙara sannan daga bisani yayi addu'o'i ga mahalarta da mamata da malamai da sauran al'umma baki daya tare da fatan Allah ya nuna mana na shekara mai zuwa cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki da ƙarin ilimi.

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
27 Ramadan 1445H
06 April 2024

Photos from Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria's post 04/04/2024

KARATUN LITTAFIN ZADUL ƘULUB FIY SHAHRILLAH

Rana ta ashirin da hudu ( 24 ):

Tare da Shaikh Isma'il Yusha'u Kudan.

A wannan rana ta 24 ga watan Ramadan, 1445(H) dai-dai da 03/04/2024, an shiga rana ta 24 a cigaba da gabatar da karatun Littafi mai suna 'Zadul Qulub Fiy Shahrillah' wanda Shaikh Isma'il Yusha'u Kudan ke gabatarwa a kowace rana a cikin watan Ramadan, daga karfe 4 na yamma zuwa karfe 6 na yamma. Inda ake gabatar da karatun a makarantar Ma'ahad Rasulul-Akram(S) dake Kudan.
Sheikh yayi bayani ne akan I'itikafi da muhimmacinsa.

FALALOLIN KARANTA AL-QUR’ANI TARE DA TADABBURI DA CIKINSA

A cikin karatun yau, Shaikh Isma'il Yusha'u ya sake janyo hankalin yan uwane dangane da muhimmantar da karanta Alƙur'ani mai tsarki musamman a wannan watan domin samun rabauta da falalolin dake tattare da karatunsa.

A cikin karatun nasa, Ya kawo Ayoyi da suke nuna falaloli na karanta shi Alƙur'anin, sannan ya karanto wasu daga cikin hadisan Manzon Rahama(S) da suke kwadaitar da al'umma dangane da muhimmantar da Alƙur'ani.

Karatune wanda ke koyar da al'umma kyawawan ɗabi'u, tare da nuna musu hanyar samun kusanci ga Allah Ta'ala ta hanyar tsarkake zuciya, da yadda mutum zai riskar da ibadarsa musamman azumi cikin aminci zuwa ga Allah Ta'ala.

Akan raba kayan buɗe baki ga mahalarta taron a kowace rana bayan kammala karatun, k**ar Dabino da s**ari (suger).

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria
03/04/2024. 24/1445h

04/04/2024

SALLAR DARE NA ASHIRIN DA SHIDA:
SALLAH RAKA'A 8, KOWACE RAKA'A FATIHA 1, QULHUWA 100. ALLAH ZAI BUDAWA MUTUM KOFOFIN SAMUN ALKAIRI TA INDA BA YA ZATO.

04/04/2024

IDDA DA KOME

Wajibi ne yin idda ga matar da aka saki k**ar yadda zaizo a bayyane:

1- YARINYA DA TSOHUWA DA WACCE BA A SADU DA ITA BA

1. Ba wajibi ba ne ga yarinyar da aka saki da tsohuwa (wacce ba ta haila) da wacce ba a sadu da ita ba (bayan aure), da za a sake ta ya halasta gare ta ta sake auren wani a lokacin.
2. Wajibi ne iddar wafati ga yarinya da tsohuwa da wacce ba a sadu da ita ba. Bai halasta gare su ba auren wani har sai bayan wucewar wata huɗu da kwana 10 daga lokacin da mijin ya rasu. Babu bambanci a cikin hakan auren ya kasance na munkaɗa’i ne, ko kuma aure da’imi.

2- MACE MAI CIKI.

3. Idan aka saki mace mai ciki, to iddarta shi ne haife abin da ke cikinta. Haka nan idan lokacin ya ƙare a auren munkaɗi’i, ko ya kyautar mata da sauran lokacin, kuma ya kasance tana da ciki, to ita ma iddarta shi ne haife abin da ke cikinta.
4. Idan mijin mai ciki ya rasu, duk ɗaya ne mijin ya kasance na auren da’imi ne, ko na munkaɗi’i, to wajibi ne idda a kanta, wanda ita ce mafi nisan lokaci biyu daga iddar wafati. Misali da a ce zai kasance cikin ya kai wata huɗu, sai mijinta ya rasu, to iddarta shi ne haife abin da ke cikinta, saboda zai rage saura wata biyar ta haihu. Idan kuma da a ce cikin ya kai wata shida ne, sai mijin nata ya rasu, to iddarta iddar wafati ce.

3- WACCE AKA SADU DA ITA BA TA DA CIKI DA YARINYA DA TSOHUWA........zaizo insha Allah

Kuna iya tuntubar marubucin ta wannan lambar a whatsapp wa.me/2348032439792 domin tambaya ko karin bayani

Telegram: https://t.me/fiqhunshia

Whatsapp: https://chat.whatsapp.com/E39sAnECkqaBLRha6eCDiu

Ma'ahadur Rasul Al-Akram - Nigeria

www.rasulilakramfoundation.org

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

wani bangare na rufe ka25 Ramadan 1445H daidai da 04 April 2024.
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha tara:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskawa ...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha takwas:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskaw...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha shida:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskawa...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha shida:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskawa...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha shida:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskawa...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha biyar:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskawa...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha huɗu:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan, Wanda ake haskawa ...
KARATUN LITATTAFIN ZADUL KULUB FIY SHAHRILLAHRana ta sha uku:  tare da Shaikh Isma'il Yusha'u kudan23/3/2024 =13\1445h
KAI TSAYE: karo na biyu  taron Mauludin Sayyida Zahra (  A.S ) daga makaranta Ma'ahad Rasulil-Akram kudan wanda yake Gud...
KAI TSAYE: taron Mauludin Sayyida Zahra (  A.S ) daga makaranta Ma'ahad Rasulil-Akram kudan wanda yake Gudana yanzu haka...

Telephone

Address


NO 5A Shagari Quaters Old Kano Road Sabon Gari Kudan
Kaduna
812104 ©KUDANLGAPOSTALCODE-ZIPCODE SOURCE:HTTPS://WWW.ZIPCODE.COM.NG/2019/02/KU
Other Religious Centers in Kaduna (show all)
New Covenant Church SABO New Covenant Church SABO
Nassarawa Street, Off, Gwari/Kasupda Road By Tranformer, Sabon Tasha
Kaduna, 800246

This is the official page for New Covenant Church Sabo, Kaduna. It has been commissioned to

Khadijat  Alhassan Khadijat Alhassan
Constitution Road
Kaduna

Do Shop in My Store at hadigitalstore.com

Worthy Lamb MCN G/gora Kaduna Worthy Lamb MCN G/gora Kaduna
Lamigyi Gonin Gora Kaduna
Kaduna

THE LAMB IS WORTHY TO RECEIVE ALL THE GLORY AND HONOUR. A VISIT WILL CONVINCE YOU

TLGRM TLGRM
Destiny Rentals Behind Catholic Church, Ugwan Bijeh Goningora
Kaduna, 800

Tower of Liberation Global Revival Ministry. Is. 61:1-3, 2nd Corinth 5:18-20 a.k.a Reconciliation and Restoration Ministeries..Non Denominational

City Of Zion Global City Of Zion Global
Kaduna

Official account of City of Zion (CZI Global) Upon Mount Zion there shall be Deliverance✨

Rccg Salvation Centre, Kaduna Province 1 Hq. Rccg Salvation Centre, Kaduna Province 1 Hq.
Patric Yakowa Express Way, Karji
Kaduna

Jesus Christ the same yesterday today and forever.

Rccg Achiever's Level Kaduna Rccg Achiever's Level Kaduna
104, GWARI Road, BY NAFDAC, NARAYI HIGH COST
Kaduna

People of Great Minds, Achieving God's Purpose

Philemon Enoch Philemon Enoch
No4 Opposite Alheri Baptist Church, Gabi Jema'a
Kaduna

Pacesetter Discipleship Pacesetter Discipleship
Ungwan Gimbiya
Kaduna

Pacesetter discipleship is a program designed to bring God's chosen ones (Matt 22:14) into the desired goal of His Son Jesus (Rom 8:29) through the enlightenment of who they are in...