Anwarul faidha muhammadiyya

Wannan page an budashine saboda bunkasa ayyukan darikar tijjaniya da faidha ibrahimiyya

22/06/2023

Sayyadi Abul fathi Athani
Allah yaqara lfy danisan kwana 🙏

22/06/2023

Sufi k**ar kasa yake,
Ana jefa kowace irin ƙazanta a kanta,
Amma babu abin da ke fitowa daga gare ta,
Sai kowane irin alheri."

27/11/2022

Wanda ya bar sallah
a cikin jama'ah ya afka cikin bid'ah

Wanda ya bar sallah cikin jama'ah
Allah zai tafiyar da albarka a gareshi da dukiyar shi

Shiyasa sallah a cikin jama'ah

Daya ne daga Cikin manyan sharudan darika

Domin an Ginata ne
akan Sunnar manzo (s a w)

04/11/2022

Annabi (s a w) yace
Ka guji abunda Allah ya Hana
Sai Allah ya So ka,

Ka guji abunda yake a hannun mutane
Sai mutane su So ka,

Matukar muka guji abunda Allah ya Hana mukayi iya Ƙoƙarin mu wajen aikata abunda ya umarce mu zai so mu zamu zama abun alkfahari har a wajen mala'iku

Haka Kuma kowane mutum matukar zamu yawaita tambayar sa Wani abu son mu da shi Zai ragu

Idan muka guji abunda yake a hannun mutane Babu hanyar da Wani zai raina mu dan Yanada abunda Bamu da shi domin ba mu da wata bukata a gare shi

Shiyasa sayyiduna Rasulullahi
Yace yawan dukiya ba shine wadata ba wadata itace wadatar zuciya
Idan aka samu wannan an samu kowane irin arziki Kuma Babu yadda zamu zama abun rainawa a inadanun wasu

Ya Allah Ka Bamu wadatar zuciya
Alfarmar Annabin Rahama
Sallallahu Alaihi Wasallam

01/11/2022

BAYAN MUTUWA
Mutum Baya da wani gida da yake zaka a cikin sa

Sai dai Wanda ya gina shi kafin mutuwar sa

Idan ya gina shi da alkhairi zaiji dadin mazaunin sa (tun a kabari)

Idan ya gina shi da sharri abunda ya gina Yayi muni

Ya Allah Ka Bamu Ikon Gina na mu da alkhairi Alfarmar Annabin Rahama.

30/10/2022

MASALLACIN KUSA DA JAHANNAMAH
Masallacin da ake cutar da musulmai
Masallacin da ake kafurta musulmai
Masallacin da ake raba kan musulmai
Masallacin da ake ba wanda ya yaƙi Allah da Manzon sa kariya
Irin wannan masallacin Yana Gabar wutar jahannamah
Mu kiyayi Irin wannan masallacin

da Yawa a yau akwai masallacin da babban hatsari ne sallah a ciki Saboda Allah ya tsine ma wannan masallacin

Muyi nazari Mafi Yawa masallacin da za'a samu Irin wannan ba masallacin da ya Dade bane kawai an samu wasu masu wawan tunani suna kafurta musulmai suna cutar da musulmai suna Raba kan musulmai

Masallatan da iyayen mu da kakan-nin mu s**a gina s**a bar Mamu Babu zagin wani b***e kafirta Wani su s**a fi cancanta muyi Ibadah a cikin su

YA ALLAH KA NISANTA MU DAGA IRIN WANNAN MASALLACIN ALFARMAR ANNABIN RAHAMA

Ga Ayar mauludi kuma ga 50k ga duk wanda ya kawo muna Ayar musabaka acikin Alqur'ani 30/10/2022

https://youtu.be/hY3SaY1-wJ8
👆👆👆
Ina Yan izala/salafawa ? Ga Ayar mauludi in kun isa ku kawo muna Ayar musabaƙa indai har ku Ahlus Sunnah ne na gaske ba tatattun yan bidi'a ba.

Kuyi share zuwa wasu groups idan sun Isa su Kawo.

Kudanna SUBSCRIBE Kuyi share zuwa wasu groups domin samun karatuttuka idan mun dora
👇👇👇
https://youtube.com/channel/UCCQzLJDv348SU1fHflSaAOA

Ga Ayar mauludi kuma ga 50k ga duk wanda ya kawo muna Ayar musabaka acikin Alqur'ani Kuyi share zuwa wasu groups idan zasu iya suzo

29/10/2022

WALIYYI
Waliyyi shine wanda Idan an ganshi
Za'ayi zikirin Allah
(Za'a ambaci Allah)
INJI ANNABI
Sallallahu Alaihi Wasallam

Wani basalafe Dan izala ya tsere daga hannun sheikh Abul fathi sani Attijjaniy 28/10/2022

https://youtu.be/DF7DtzsrZRQ
👆👆👆
Tofah yau ake yinta wani basalafe Dan izala ya fada hannun Abul fathi sani Attijjaniy

Kuyi share zuwa wasu groups kuji ya akayi ya tsere 😂😂😂😂
👇👇👇
https://youtu.be/DF7DtzsrZRQ

Wani basalafe Dan izala ya tsere daga hannun sheikh Abul fathi sani Attijjaniy Idan masara taji wuta 🔥🔥🔥 ita ke fadi

26/10/2022

sayyiduna Rasulullahi
sallallahu alaihi wasallam
yace abun mamaki ga al'amarin mumini Domin mumini al'amarinsa duka Alkhairi ne a gareshi
Idan sauki ya same shi sai ya gode ma Allah sai ya zama Alkhairi a gareshi
Idan tsanani ya same shi sai Yayi hakuri sai ya zama Alkhairi a gareshi Babu Wanda ya samu wannan sai mumini
ya Allah Ka Bamu Ikon gode Maka a lokacin da Wani Alkhairi ya same mu
ya Allah Ka Bamu Ikon hakuri a lokacin da sabanin alkhairi ya same mu
ya Allah Ka Bamu Ikon daukar kaddarar da ka kaddara ta a kan mu
alfarmar sayyiduna Rasulullahi
sallallahu alaihi wasallam

24/10/2022

KYAWUN FUSKAR ANNABI (ﷺ)!.

Kyawun "fuskarsa"!, da walwalinta, da sheƙinta, yafi "ƙallin takobi haske"! wane wata, bare tauraro, ba'a iya haɗa fuska da shi, saboda tsantsar kwarjininsa SalLalLahu AlaiHi WasalLAm.

Da zarar yayi murmushi "haƙoransa" zai fitar da wani haske k**ar walƙiya ta tsakanin wushiryarsa, saboda kyawun fuskarsa Har cikin ƙur'ani saida Allah Ya ambaceta.

قَدْ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِي السَّمَاءِ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَاهَا فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ

Lalle ne, Muna ganin jujjũyãwar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yardã da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallãcin harami.

Al-Baqara:144

ALLAH YASA MUYI MAFARKI DA WANNAN KYAKKYAWAR FUSKAR.

Taruhin hijarar Manzon Allah s.a.w daga Makka zuwa madina saboda cutawar mutanensa 23/10/2022

https://youtu.be/RnK-Hx-fVjA
👆👆👆
Tarihin hijirar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama daga Makka zuwa Madina domin cutawar mutanen sa.

Idan kana Kaunar Annabi Sallallahu alaihi Wasallama kayi share zuwa wasu groups biyar Allah ya cika maka burinka na Alkhairi don shugaba s.a.w

Kudanna SUBSCRIBE masoya Annabi s.a.w
👇👇👇
https://youtu.be/RnK-Hx-fVjA

Taruhin hijarar Manzon Allah s.a.w daga Makka zuwa madina saboda cutawar mutanensa kudanna SUBSCRIBE Kuyi share zuwa wasu groups

Kada su yaudare ku da sunan Ahlus Sunnah mu Yan dariqa mune Ahlus Sunnah na gaske 22/10/2022

https://youtu.be/oRg_oL22Qck
👆👆👆
Kada su yaudare ku da sunan Ahlus Sunnah mu Yan dariqa mune Ahlus Sunnah na gaskiya wallahi

Bayani gamsasshe gameda salafawa Masu karyar Sunnah

Kuyi share zuwa wasu groups kuji su waye Ahlus Sunnah na gaskiya
👇👇👇
https://youtu.be/oRg_oL22Qck

Kada su yaudare ku da sunan Ahlus Sunnah mu Yan dariqa mune Ahlus Sunnah na gaske kudanna SUBSCRIBE Kuyi share zuwa wasu groups

Raddi zuwaga jahili Dr. Rabi'u Rijiyar lemu akan littafin Prof. maqari 21/10/2022

https://youtu.be/WWYt3XnB5yA
👆👆👆
Raddi zuwaga jahilin Malamin izala Dr. Rabi'u Rijiyar lemu akan littafin maulana Prof. Ibrahim maqari

Daga bakin Sheikh Abulfathi sani Attijjaniy 👉👉👉 kuyi share zuwa wasu groups domin kuji irin jahilcin da ya tafka

Kudanna SUBSCRIBE domin samun sakonninmu idan mun dora
👇👇👇
https://youtu.be/WWYt3XnB5yA

Raddi zuwaga jahili Dr. Rabi'u Rijiyar lemu akan littafin Prof. maqari Jahilin banza Dakiki waishi Dr. Amma komai bai saniba

08/10/2022

ANNABIN MU DABAN YAKE DA KOWA
sunan mahaifin sa
ABDULLAHI
(Bawan Allah a halaye abun Koyi)
sunan mahaifiyar sa
AMINATU
(amintacciya a halaye itama abar Koyi ce)
sunan wadda ta anshi haihuwarsa
SHIFA'U
(Waraka)
wadda ta shayar da shi
HALIMATU ASSA'ADIYYA
(Mai hakuri yar kabila Mai sa'a)

Sallallahu alaihi wasallam 🥰

01/10/2022

ANNABI MUHAMMAD ﷺ۔۔۔۔

Watarana wani almajiri yaje gidan manzon ALLAH ﷺ bara, gashi kuma bawani abu da zaa bashi, sai annabi yace. "Da nana Aisha tabashi mayafinsa۔۔۔

Aka baiwa almajiri ya tafi, sai yaje kasuwa yana cewa wazai sayi mayafin da manzon ALLAH ﷺ yabani ۔۔۔ Nan take mutane s**a taru don sayen mayafin, kowa yanaso asayar masa۔۔۔

To acikin mutanen akwai wani makaho sai ya umurci bawansa kuma jagoransa da yaje gida ya dauko kudi domin sayen wannan mayafi kuma yace konawa almajirin ya bukata to ya bashi sannan yace inhar ya sayo mayafin zai yantashi۔۔۔

Bayan bawan ya cika umurni ya kawo masa wannan mayafi, shikuma ya yantashi ۔۔۔ Nan take makahon ya daga mayafin sama yana cewa. "Ya ubangiji albarkacin wannan mayafin da kuma me mayafin manzonka ﷺ ka bude min idona ۔۔۔

Rufe bakinsa keda wuya sai idanuwansa s**a bude, yana ganin komai bai gushe ba makahon yazo wajen ma'aiki ﷺ yace "Ya Rasulullah da ni makaho ne amma nayi tawassuli da mayafinka idona ya bude, yanzu ga mayafinka na dawo maka dashi ۔۔۔

Sai Annabi ﷺ yayi murmushi har hakoransa s**a bayyana ۔۔۔ Ya ALLAH ka rayamu da son Annabi ﷺ kuma ka kashemu cikin soyuwa gareshi ۔۔۔

"Ni me rubutu ina neman dacewar ALLAH da Ni da Ku abisa yardarshi da amincewarshi tareda mu baki daya"
~

27/09/2022

HAPPY MAULID
kar a ɓata lokaci wajen masu shirme
Domin su sunyi k**a da wadanda Allah yake cewa

إِنْ هُمْ إِلَّا كَٱلْأَنْعَٰمِ ۖ بَلْ هُمْ أَضَلُّ سَبِيلً

saboda haka masoyan Annabi (s a w)
ayita tunanin Annabi muje wajen da aka taru Saboda Bada tarihin sayyiduna Rasulullahi
zukatan mu su samu natsuwa
muyi Kuka akan Wani abun muyi farin ciki akan Wani abun
Idan wasu sun aibata mu ko sun zage mu sai mu tuna da fadin Allah (s w t)

وَعِبَادُ الرَّحْمَنِ الَّذِينَ يَمْشُونَ عَلَى الْأَرْضِ هَوْنًا وَإِذَا خَاطَبَهُمُ الْجَاهِلُونَ قَالُوا سَلَامًا

babu wata Jayayya da zamu tsaya da wasu
Tunanin Annabi ne a gaban mu
sallallahu alaihi wasallam.

20/09/2022

ABI HANYAR DA MAGABATA S**A BI A ZAUNA LAFIYA
Dukkan abunda yake da madogara a shara'ah ba bid'ah bane
Koda magabata Basuyi aiki da shi ba
Domin Barin su ga aiki da shi Zai Iya zama Saboda Wani uzuri da ya tsayu a garesu a wannan lokacin.

(INJI IMAMU SHAFI'I RA)

18/09/2022

KYAWAWAN HALAYE
murmushi da sakin fuska
yayin haduwa da mutane
Suna daga Cikin halayen Annabawa
Yin haka Yana tafiyar da girman Kai
Yana jawo Soyayya a tsakanin Al'ummah.

14/09/2022

SOCIAL MEDIA
WAYA (PHONE)
waɗanan wayoyin da Allah ya kawo mamu
da social media,
sai munyi hattara Allah Yana sane da duk abunda mukeyi da waya
Allah ya kawo Mamu social media ne,

لِيَعْلَمَ اللّهُ مَن يَخَافُهُ بِالْغَيْبِ

Domin Allah yasan Wanda yake tsoron sa
a ɓoye,
Wanda ya ƙetare Iyaka Yayi abunda yake so
da waya Allah zaiyi masa azaba,
Allah ya kiyaye mu,
Allah ya Bamu Ikon aikata Alkhairi.

12/09/2022

KUNYA
Sayyiduna Rasulullahi
Sallallahu alaihi wasallam yace
kunya abuce Mai kyau
amma Tafi kyau ga mata
Idan Babu kunya Babu cikakken Imani.

11/09/2022

TUBA 🤲
SAYYIDUNA RASULULLAHI 💝
Sallallahu alaihi wasallam yace
Tuba abune Mai kyau
amma Tafi kyau ga matasa
Yan Uwa matasa
Mu zama masu tuba
zuwa ga Allah (SWT)

10/09/2022

MUJI TSORON ALLAH
a Kullum abunda Malamai suke fada Mamu Kenan
"MU ZAMA MASU TSORON ALLAH"
Idan muka samu wannan Mun samu komai
Mun samu dukkan Wani Alkhairi
Allah zai kiyaye mu Daga dukkan sharrin zuciya da Mai bata shawara
kowane aikin Mai kyau Yana samuwa ne ta hanyar Tsoron Allah
MUJI TSORON ALLAH

08/09/2022

ADDININ MUSULUMCI
ADDINI NE MAFI SAUKI
mune muke tsanantawa a ciki
kowa Yayi abunda ya Fahimta
ba tare da ya Bata na Wani ba
a Cikin sahabban
sayyiduna Rasulullahi
Sallallahu alaihi wasallam
akwai Wanda Idan Yana tafiya Baya bi ta cikin mutane sai ya koma nesa da mutane
haka Kuma akwai Wanda
Baya Saida komai a kasuwa amma Yana zuwa kasuwa Saboda Idan ya hadu da mutane Yayi masu sallama Yana son haduwa da mutane
amma wannan baisa wani daga Cikin su
yace ma Wani baiyi Dai-dai ba,
duk abunda muka ga Wani yanayi Yanada Dalilin da yasa yakeyi Kuma ba dole bane sai Ka yarda ko na yarda,
KOWA YAYI ABUNDA YA FAHIMTA
SAI AZAUNA LAFIYA.

04/09/2022

MATA
ZAKA GA WASU MATA
suna sanya wasu Irin kaya masu bayyana suffar jikin su, suna tafiya suna wata rangwada suna Jan hankalin mutane sun bar abunda Allah yace
sayyiduna Rasulullahi
sallallahu alaihi wasallam yace
da Yawa ma'abociyar tufafi a duniya,
zata tashi tsirara a lahira Saboda tana bayyana surar jikin ta,
Mai yin haka ba zata ji kamshin Aljannah ba
b***e ta shiga
Idan muka kiyaye,
sai Allah ya kiyaye mu,

02/09/2022

ZUWA GA MATA

عَنْ عَلْقَمَةَ بْنِ أَبِي عَلْقَمَةَ عَنْ أُمِّهِ أَنَّهَا قَالَتْ دَخَلَتْ حَفْصَةُ بِنْتُ عَبْدِ الرَّحْمَنِ عَلَى عَائِشَةَ زَوْجِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَعَلَى حَفْصَةَ خِمَارٌ رَقِيقٌ فَشَقَّتْهُ عَائِشَةُ وَكَسَتْهَا خِمَارًا كَثِيفًا.

wata rana sayyada hafsatu Bnt Abdurrahman bn Abubakar saddiq (rta)
taje wajen mamar ta sayyada Aisha,
sayyada hafsatu ta Saka mayafi Wanda Wanda Baya da kauri,
wanda bai rufe jikin ta duka ba,
Kamar yadda ana son mayafi ya rufe jikin mace ko'ina Mai tsawo Mai fadi Mai kauri,
Ba Mai shara-shara ba,
sai sayyada Aisha ta yaga shi Saboda bai kai yadda ake so ba,
ta bata Wani mayafi Mai kauri wanda ya suturta ta yadda ya k**ata
Duba da yadda Al'ummar wannan zamanin suke
sai Allah ya kawo Mamu hikimar hijab wanda zai rufe mace ko'ina,
Ba wayewa bane ki Saka mayafi Wanda zai bayyana surar jikin ki,
sayyiduna Rasulullahi
sallallahu alaihi wasallam yace
mai bayyana tsiraicin ta ko kamshin Aljannah ba zata ji ba.

Raddi Zuwaga Dr. Ahmad Al-Azhari akan hana mutane wuridi 01/09/2022

Raddi Zuwaga Dr. Ahmad Al-Azhari akan hana mutane wuridi Kudanna SUBSCRIBE Kuyi share a groups dinku na WhatsApp da Facebook da telegram

30/08/2022

Annabin mu Saboda Soyayyar da yakeyi Mamu Yana Raba Mamu Aljannah Kamar ruwa,
matukar muka kiyaye mu'amular mu
da Al'ummah ba cuta ba cutarwa,
Zaiyi Alfahari da mu,

عَنْ أُمِّ حَبِيبَةَ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
مَنْ صَلَّى قَبْلَ الظُّهْرِ أَرْبَعًا وَبَعْدَهَا أَرْبَعًا حَرَّمَهُ اللَّهُ عَلَى النَّارِ

sayyiduna Rasulullahi
sallallahu alaihi wasallam yace :
Wanda yayi sallah raka'a hudu kafin Azahar
Kuma Yayi hudu bayan Azahar,
Allah ya haramta masa shiga Wuta,
musulumci akwai Dadi.

29/08/2022

Mu taimaki Yan Uwan mu
da abunda Allah ya h**e Mamu,
Idan Allah ya bamu lafiya ko ba komai,
Mun samu jarin da zamu taimaki Yan Uwa musulmai,
da yiyuwar a asibiti Mafi kusa da Kai akwai marasa lafiya musamman mata wadanda Suke bukatar Jini ba'a samu ba,
sai muje a auna Idan Yayi mu taimaki Yan Uwa musulmai da shi,
wannan Babban Jihadi ne,
Idan Allah ya Basu lafiya zasu cigaba da yi Mamu Addu'a ta Alkhairi,
na tsawon lokaci,
Saboda Jin Dadin abunda mukayi masu,
Ashe ko ba kudi Idan akwai lafiya zamu Iya Taimako,
Allah ya taimaki Mai taimakon
Al'ummar Annabin Rahama (s a w)

28/08/2022

TA YAYA ZAMU TAIMAKI
YAN UWA MUSULMAI
A HALIN DA MUKA TSINCI KANMU
Mafi Yawa Daga Cikin mu Muna mantawa da yadda Yan uwan mu suke rayuwa,
a lokacin da akace an sace (kidnapped) Wani Wanda muka sani Muna hada kudi masu yawa domin ganin an anso shi,
Wani ma Baya da komai
ko sana'a Baya da Ita,
amma Muna hada kudi mu anso shi
Idan har zamu Iya hada kudi domin anso dan Uwan mu to lalle zamu Iya hada kudi domin nema masa sana'a,
mafi yawan masu bara akan tituna yan uwan mu ne musulmai
maganin cutukan mu Yana cikin mu,
amma Mun bar maganin
Mun koma Wani waje,

Allah ya Bamu Ikon Taimakon Al'ummah.

28/08/2022

'Ranar Hausa',
'Ranar Independence',
'Ranar Mata',
'Ranar Kanjamau',
'Ranar Yara Ta Duniya',
'Ranar Ma'aikata',
'Ranar Wanke Hannu'

Da Sauransu....

Duk Wannan HALAL Ne.. Kuma Babu Laifi Yinsu Kuma musulmai ne sukeyi Amma Wai Ranar ANNABIN RAHAMA(S.A.W) Ita Ce "BIDI'AH....

SUBHANALLAH 😢

Kaico!!!

Wai Wanda Ya Girmama Wadancan Ranakun "Mai Kishin 'Kasa" Ne.
Ko Kuma wasu s**e tunawa da wadannan ranakun ba Addini bane,
To Ina ruwanka da abunda ba Addini ba tunda ba Addini bane Ka barshi mana,

Amma Wanda Ya Girmama; RANAR HAIHUWAR ANNABI(S.A.W) Shi Ne "'DAN BIDI'AH"..

KAI JAMA'A!!!
Wanne Irin duhun Kaine wannan,
Bayan Annabi yace Imanin dayan mu ba zai Cika ba sai munfi son sa fiye da kowa fiye da komai

Kai da kake kin maulidi tambaya gare ka ?

Tsakanin Ka da Allah Nawa Ka Taba kashewa Saboda Annabi
Kamar yadda sahabbai sukeyi su bayar da dukiyar su Saboda tsananin Soyayyar Manzon Allah saw

Idan matar ka ta haihu baka kashe kudi ba Ka kashe 100k Saboda murnar samun jariri ko jaririya kana farin ciki akan samun karuwa

Nawa Ka Taba kashewa Saboda farin cikin Kasancewar Ka masoyin Annabi

To Annabi Yafi wannan jaririn da ka kashe ma kudi,
Idan har ba zaka Iya kashe dukiyar Ka Saboda Annabi ba to bai k**ata ka zargi wadanda Suke kashewa ba,
Domin sun fika son sa shiyasa har suke Iya kashe dukiyar su Saboda shi,

Albishirinku Masoya! Yau Saura Kwanaki 41 Cif MAULUDIN FIYAYYEN HALITTA(S.A.W)....❣️❣️❣️

ALLAH Ya Kara Tsare Mana Imaninmu, Ya 'Kara Mana 'Kaunar SHUGABA(S.A.W), Ya Horewa Kowannenmu Abin Hidima🙏❣️🙏
Alfarmar Annabin Rahama 🥰

27/08/2022

matasa a yau !!!
a wannan lokacin ne muke da Damar gyara gaban mu,
Muna ganin wasu sun Tsufa,
Ana Bada labarin su lokacin da suna matasa
Wani ya more ma samartakar sa
ta hanyar Ƙoƙarin aikata abunda Allah Yayi Umarni, da kiyaye abunda ya Hana,
Wani Kuma Yayi amfani da samartakar sa wajen biye ma rudanin duniya
abokan banza son wakokin banza,
sai kaji labarin Wani ya burge Ka Wani Kuma ya baka haushi,
IDAN MUKA BIYE MA SON ZUCIYA
HAKA ZA'A RIKA BADA LABARIN MU,
WATA RANA
DA ABUNDA MUKAYI A DUNIYA
IDAN MUN KYAUTATA ZA'AYI MAMU ADDU'A IDAN MUN BATA KUMA ZA'A BATA MAMU
ALLAH YA SAWAKA.

27/08/2022

ALFAHARI BA NA MUSULMI BANE
wai kana Ganin Ka zama Wani abu ko kasan wani abu kanayi ma mutane alfahari da shi,
zai zama Masifa a wata rana Mai zuwa,

وَاللَّهُ أَخْرَجَكُم مِّن بُطُونِ أُمَّهَاتِكُمْ لَا تَعْلَمُونَ شَيْئًا وَجَعَلَ لَكُمُ السَّمْعَ وَالْأَبْصَارَ وَالْأَفْئِدَةَ ۙ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Allah ne ya fitar da mu Daga Cikin uwayen mu a lokacin Bamu San komai ba duk Wani Ilimi ko wata dukiya ko Wani abu da mutum zaiyi tak**a da shi a lokacin Babu Daga Baya ne aka samu munzo duniya Bamu da komai Kuma Bamu San komai ba
Allah ya Saka mamu kunnuwa Domin mu Ji magana ba Dan munfi Wadanda Basu Jin magana ba ( kurame) ya Saka Mamu Idanuwa ba Dan munfi Wadanda Basu da Idanu ba (makafi) sannan ya Bamu Kwakwalwa da tunani da hankali wanda da shi ne zamu San Allah
mu Bauta masa,
sai mu nuna godiya ga Allah ta hanyar guje ma Abubuwan da ya Hana,
da Ƙoƙarin aikata Abubuwan da Yayi Umarni,
duk Ilimin Ka kar Ka manta ba da shi kazo ba haka duk Kudin Ka haka duk matsayin ka,
kafin Kai an samu Wadanda s**a Fi Ka,
Allah ya kyautata Karshen mu.

25/08/2022

TSORON ALLAH BA'A CANZA
MURYA YAKE BA KO CANZA TAFIYA
Kayi tafiya yadda kake kar ka canza tafiyar ka
a matsayin wai kai mai Taƙawa, kar ka canza magana wai dan kana mai Taƙawa,
Wannan ba tsoron Allah bane Girman kai ne,
Wanda yake hallakar da mutum,

عمر بن سليمان بن أبي خثمة، عن أبيه قال: قالت الشفاء ابنة عبدالله: ورأيت فتيانا يقصدون في المشي يتكلون رويدا فقالت: ما هذا ؟ فقالوا: نساك، فقالت: كان عمر إذا تكلم أسمع وإذا مشى أسرع وإذا ضرب أوجع وهو الناس حقا،

Sayyada Shifa'u Bint Abdullahi tace taga wasu samari suna taƙaitawa a cikin tafiya suna tafiya k**ar ba tafiya sukeyi ba daƙyar suke tafiya kuma suna magana kaɗan-kaɗan suna canza murya Daga yadda take,
Sai tace wannan kuma menene?
Sai akace mata su masu bauta ne
masu tsoron Allah
Sai tace sayyidina Umar ya kasance Idan yayi magana kowa sai yaji Idan yayi tafiya yana sauri ba k**ar yadda sukeyi ba Idan yayi duka yana jiyar da ciwo shine yafi mutane gaskiya amma bayyi Kamar yadda sukeyi ba,

Kamar yadda zaka samu a wannan zamanin akwai Irin wadancan wadan suke da'awar tsoron Allah a magana da canza tafiya haka zaka samu suna yi suna Ganin wannan a matsayin Yaqawa Basu San girman Kai bane
Lalle wannan hadari ne babba Ka Rika canza muryar Ka wai Kai malami Mai tsoron Allah kana Magana Kamar zakayi amai kana tafiya Kamar ba tafiya kakeyi ba wannan ba tsoron Allah bane
Saboda haka matasa a kiyaye
Makircin shedan yanada Yawa
Kar Ka yarda Ka dauki kanka Wani tsoron Allah da har zaka Rika canza tafiya ko magana kana Hausa amma Kamar kana Larabci

Allah ya Kiyaye mu.

22/08/2022

Allah ya Bamu Ikon Gyarawa
a lokacin da muka zama Mafi Yawa Daga Labaran da muke sanya masoyan mu dariya ko farin ciki karya ce kawai muke kirkira
dan mu burgesu,
a wannan lokacin ne muke Kara Fadawa
cikin fushin Ubangiji (S W T)

وَيْلٌ لِلَّذِي يُحَدِّثُ بِالْحَدِيثِ لِيُضْحِكَ بِهِ الْقَوْمَ
فَيَكْذِبُ وَيْلٌ لَهُ وَيْلٌ لَهُ

Ma'aiki (s a w) yace
azaba ta tabbata ga Wanda yake bayar da Labari Dan Yaba mutane dariya da shi,
sai Ya kirkiri karya a cikin labarin,
annabi yace
Azaba ta tabbata gare shi !!!
Azaba ta tabbata gare shi !!!.
Ko sau Daya Ma'aiki yayi magana akan haka abun tsoro ne b***e sai da ya maimaita
Sau Uku Saboda munin yin haka.

21/08/2022

Mafi yawan waɗanda suke Shugabanci a nigeria 70%
musulmai ne,
Mafi yawan waɗanda ake kashewa a Nigeria 98% Musulmai ne,
me ya kawo wannan
Musulman ne s**a Raina kansu s**a fifita Al'amarin duniya akan na lahira sai aka Raina su duk Wani abu marar Kyau sai kaga ana jingina shi ga musulmai Kuma sai kaga anyi shiru
ana kashe mu Kamar kaji amma Babu wani mataki da ake dauka
Matukar Bamu gyara ba zamu ga gyara ba,

20/08/2022

KAR MU RAINA AIKIN ALKHAIRI KODA RAKA'A BIYU CE A CIKIN DARE
Ma'adan Ibn Abi dalhata yace naje wajen Sauban sai nace masa Ka bani labarin Wani aiki Wanda Idan nayi Allah zai shigar da ni Aljannah da shi Sai sauban Yayi shiru sai ma'adan ya sake tambayar sa har Sau uku Yana tambayar sa sannan sai sauban yace na tambayi manzon Allah ( s a w) akan haka sai Manzon Allah (s a w) yace man
Ina horon Ka da yawaita sujjada Saboda Allah (yawaita Sallah)
Annabi yace masa Domin ba zakayi wata sujjada ba sai Allah ya daukaka darajar Ka da Ita Kuma sai Allah ya kankare Maka Zunubai
sai Ma'adan yace sannan na gamu da
Abi daddarda'i na Tambaye shi akan wannan Shima ya gaya man abunda
sauban ya gaya Mani
Allah ya Taimake mu 🙏

IMAM TV ✍️

19/08/2022

Sayyidina Abdullahi bn Abbas (rta)
yaga manzon Allah (saw) a mafarki lokacin da ya Farka sai ya tuna hadisin da Annabi yace Wanda ya ganshi a mafarki da sannu zai ganshi a farke sai yaje wajen uwar muminai Maimunatu
sai ta dauko masa madubin Ma'aiki sai ya Duba madubin sai yaga surar annabi a ciki baiga kansa ba,
Kamar yadda a bayansa an samu salihan Bayin Allah sunga Annabin Rahama a mafarki sannan sun ganshi a farke (Ido da Ido)
Allah ya bamu Albarkacin su.

FAT'HUL BARI KITABU ATTA'ABIR BABI NA GOMA (10) HADISI NA FARKO.

18/08/2022

YA LABARIN ZAMAN MUQABALA ?

Kamar yanda wasu suketa turo saqonninsu suna tambaya cewa wai ko an dage muqabala ?.

Amsa : Wannan labarin da kukeji cewa an dage muqabala ba gaskiya bane. Inma kunji ance an dage daga wajensu ne.

Insha Allahu zuwa gobe za'ayi duk da yake mu insha Allahu ko yau s**a shirya bismillah ba Wani abu bane sai azo ayi kawai domin banbance tsakanin gaskiya da karya.

Want your place of worship to be the top-listed Place Of Worship in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Telephone

Address


Kano
Kano
Other Religious Organizations in Kano (show all)
RCCG KOG YOUTH Fellowship RCCG KOG YOUTH Fellowship
77, Onitsha Road By Ibo Road Sabo Gari
Kano

Jesus the reigning King

Most Holy Trinity Adoration Ministry, Umunze Most Holy Trinity Adoration Ministry, Umunze
32A MINDANAO Avenue
Kano, 2770

God bless you as follow Eucharistic Adoration @ Most Holy Trinity Adoration Ministry Umunze every Tuesday afternoon and Friday night.

Remnant Christian Network - Kano Remnant Christian Network - Kano
First Baptist Church Multipurpose Hall, France Road, Sabon Gari
Kano

We are a Ministry striving for the rebirth of Apostolic Christianity, together, heralding the revival of Christ Jesus.

Salvation Dunamis HolyGhost Church International. Salvation Dunamis HolyGhost Church International.
No 39 Emir Road
Kano

Home Of Signs And Wonders

Masjid Al-imamin Nawawy Masjid Al-imamin Nawawy
Jido Layout, Behind Danladi Na Sidi Housing Estate
Kano

Jido layout, opposite Danladi Nasidi Housing estate

The Apostolic Church SanyaOlu The Apostolic Church SanyaOlu
34 Sanyaolu Street, Sabongari
Kano, 700231

Welcome to The Apostolic Church Sanyaolu Assembly. God bless you as you fellowship with us

Sheikh Abubakar Muhammad Tudun-Wada Sheikh Abubakar Muhammad Tudun-Wada
Kano

Ku Ziyarci Shafukan 'Dan Autan Media' Domin Sauke Karatun Malam Kai Tsaye, Facebook, YouTube, TikTok. Allah Ta'ala Yasa Mu Wanye Lafiya Duniya Da Lahira.

Youth for Christ, CEFN Church Youth for Christ, CEFN Church
55 Abeokuta Road, Sabongari
Kano

Youth for Christ CEFN is the Youth arm of CEFN zonal headquarter church, Kano Nigeria.

Shallom city prayer network. Shallom city prayer network.
After Methodist Church A*o Road KABAYI Mararaba
Kano

mainly for prayers on healings and deliverance.

Jesus Testimony Tabernacle Jesus Testimony Tabernacle
51 New Road By Abedie Sabongari Kano
Kano

JESUS TESTIMONY TABERNACLE IS AN INTERNATIONAL MINISTRY THAT GOD HAS BEEN TREMENDOUSLY TOUCH THE! LIFE OF PEOPLE THROUGH HIS SERVANT PROPHET S.A. ADEOJO. TUESDAY 8::30am THURSDAY 5...

Methodist Church Nigeria - Diocese of Kano Methodist Church Nigeria - Diocese of Kano
1/3 Gold Coast Road, Sabon Gari
Kano

To consistently win more souis for Christ, Develop spiritually fulfilled members and Remain very act