Arewa Daily Reporters

Domin kawo maku labarun Nigeria a lokacin da suke wakana dakare martabar arewa da Nigeria baki daya

19/02/2024

Tsohon Shugaban Kasa Ya Yi Magana Ya Bayyana Abin da Ya Ke Tsoron Zai Faru Gameda Tsadar Rayuwa

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan mawuyacin halin kunci da ‘yan kasar ke ciki na tsadar rayuwa Tsohon shugaban kasar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki Janar din ya bayyana haka ne a ranar Juma’a 16 ga watan Faburairu a shafinsa na X kan irin halin kunci da ake ciki

Tsohon shugaban Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida ya yi magana kan halin da ake ciki a kasar. Ibrahim Badamasi ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin gaggawa kan halin da ‘yan Najeriya ke ciki na mawuyacin hali.

Mene tsohon shugaban ke cewa ga Tinubu?

Tsohon shugaban ya ce ba ya goyon bayan juyin mulki a kasar amma kuma dole Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta taimaki ‘yan kasar. Ya ce idan har gwamnatin ba ta dauki matakin kawo dauki ga ‘yan kasar ba komai na iya faruwa. Ya kuma bukaci Shugaba Tinubu ya dauki tsauraran matakai da za su dakile matsalar kafin komai ya rikice a kasar. A cewarsa: “Ba na goyon bayan karbar mulki daga hannun farar hula, amma ina rokon Gwamnatin Tarayya ta kawo dauki ga ‘yan Najeriya.

19/02/2024

Idan Kunfi Karfin Doka Bakufi Karfin Ta Allah Ba, Yanzu-Yanzu Saurari Wani Bayanin Sheikh Daurawa...

Photos from Arewa Daily Reporters's post 19/02/2024

Ana Ci Gaba Da Nasara Kan 'Yan Ta'adda a Sakkwato

Yan ta'addan jihar sokoto na Cigaba da Shiga Hannun jami'an Tsaron jihar sokoto:

Cikin daren jiya jumu'a a tashi safiyar yau Asabar, jami'an tsaro sun damke wadannan Yan Bindiga a hanyar Bodinga zuwa Tambuwal dake nan jiharmu ta sokoto kan hanyarsu ta zuwa wurin ta'addancin.

Daya daga cikinsu ma yana fama da ciwon hannu ne Amman duk da hakan bai hanashi fita Aika aikar ta'addanci ba.

Photos from Arewa Daily Reporters's post 19/02/2024

DA ƊUMI ƊUMI: Gwamnatin Najeriya Tayo Odan Kayan Abinci A Jiragen Ruwa Zuwa Nijeriya

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta NPA, ta samar da manya manyan jiragen ruwa guda Talatin da biyar, 35 sun nufo Najeriya dauke da tataccen man fetir da kayayyakin abinci da dama, Kuma jiragen zasu fara sauka a tashoshin jiragen ruwa guda biyu dake jihar Legas, da s**a hada da tashar Apapa da tashar tsibirin Tin Can.

Kuma jiragen guda 35 din zasu fara isowa Najeriya NPA, tace cikin ababan da suke dauke da shi guda goma sha hudu daga cikinsu na dauke da tataccen man fetir ne, inda sauran guda ashirin da daya ke makare da danyen kifi, acca, kayan karafa, siga, manja, taki, man gas da sundukai da dama.

Hukumar NPA, tace akwai wasu jirage guda goma sha daya da s**a riga s**a iso tashoshin jiragen ruwan Najeriya, wanda suke jira a saukesu, dauke da kayan taki, mai, da dai sauransu.

Wanne irin fata zakuyi?

17/02/2024

MATAWALLE YA GARGAƊI MASU YIN MUNANAN KALAMAN ƁATANCI GA GWAMNATI

Minista a ma’aikatar tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle MON, ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji yin kalaman batanci ga gwamnati, inda ya ce irin wadannan kalamai sam ba su dace ba.

Ministan ya yi wannan kiran ne sak**akon wasu kalamai na rashin dattaku da ke fitowa daga bakunan wasu al’ummar kasar.

Ya ce "Irin wadannan maganganun na tada hankali ne da firgici kuma hakan na iya ta'azzara tashe-tashen hankula tare da zaman dar-dar a cikin al'umma.”

Dr. Matawalle ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR yana da manufa nai kyau don haka yana aiki ba dare ba rana wajen ganin Najeriya ta gyaru ta zama kasa mai kyau.

Ministan ya kuma yi karin haske kan wasu manufofi da gwamnatin Tinubu ta bullo da su zuwa yanzu don sake fasalin tattalin arzikinmu da kuma tabbatar da tsaron rayuka da samar da walwala ga al’umma.

A cewarsa, Shugaban kasa ya dauki tsaron ‘yan kasa da matukar mahimmanci inda ya baiwa sojojin Najeriya kayan aiki yadda ya k**ata yayin da aka kuma dora wa Hafsoshin sojin kasar hakkin inganta fannin tsaron kasar

Da yake magana kan tattalin arzikin kasa, Matawalle ya ce shugaban kasa yana da kyakkyawar fahimta kan alakar rashin tsaro da talauci don haka ne gwamnati ke kara tallafawa masu kananan sana’o’i wanda kuma kari ga shirin tallafawa magidanta miliyan 15 masu karamin karfi.

Ministan ya kara da cewa: “ba da jimawa ba, shugaban kasar ya amince da kafa wani kwamiti wanda ya hada da gwamnonin jihohi da wakilan tarayya da za su binciko yiwuwar kafa ‘yan sandan Jihohi da za su taimaka wajen dakile laifukan bata gari.

Sai dai Ministan ya jaddada muhimmancin hadin kai, inda ya bayyana cewa abin da ya shafi dan Najeriya daya ya shafi al’ummar kasar baki daya.

“Ya zama wajibi mu ‘yan Najeriya mu rungumi zaman lafiya da fahimtar juna da magance bambance-bambancen da ke tsakaninmu, kuma ta hanyar hadin kai ne kawai za mu iya shawo kan kalubalen da al’ummarmu ke fuskanta,” inji shi.

Bugu da kari, Ministan ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu GCFR yana iya bakin kokarinsa wajen magance matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.

Dakta Matawalle ya kara da tabbatar wa al’umma cewa shugaban kasar da mukarrabansa suna bakin kokarinsu wajen ganin sun rage wa al’ummar Najeriya radadin da suke fuskanta inda ya gargadi masu son raba kan al’umma da su guji yin kalamai marasa inganci da za su tada hankalin al’umma.

Don haka, Dokta Matawalle ya bukaci dukkanin ‘yan kasa da su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya, hakuri da hadin kai da kuma sanin kalaman da za su furta, yayin da ake fatan samar da ci gaba mai dorewa a Najeriya.

Henshaw Ogubike, FCAi, fsca, fcpe, mnipr
(Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a)

17/02/2024

A yanzu mutum zai iya tuƙa mota da dare daga Kaduna har Kano ba tare da shakkar komai ba. An kakkaɓe mafi yawan gaggan 'yan bindigar da s**a addabi jama'a a yankunan, Cewar Nuhu Ribadu

Me zaku ce?

17/02/2024
16/02/2024

Kungiyar masu manyan motocin da ke jigilar fetur a Najeriya (NARTO) ta ce daga Litinin mai zuwa za ta dakatar da aikinta saboda zargin rashin cin riba a aikin da mambobinta ke yi.

Photos from Arewa Daily Reporters's post 16/02/2024

LABARI: Shahararren mawakin siyasar nan Dauda Adamu Abdullahi Kahutu Rarara ya gwangwaje Ma'aikaciyar sa Aisha Humaira Da Kyautar Dalleliyar mota.

Masu karatu mai zaku ce?

16/02/2024

BA NI DA BURIN DA YA WUCE NA SAMAR DA HAƊIN KAI DA ZAMAN LAFIYA A NAGERIYA GABA DAYA - BOLA TINUBU

- A Matsayina Ná Musulmí Da Na Yí Rantsuwa Da Alƙur'ani Maì Gírma Lokacìn Karɓar Mulkí Ya Zama Wajibi Ná Yi Shugbanci Na Adalci Ga Ko Wanne Sashe Na Kasar Nan, Céwar Bóla Tínubu

Shugaban ya bayyana cewa daga cikin manyan burukan da ya ke da su har ya nemi shugabancin Nageriya sun haɗa har da batun samar da haɗin kai da kuma zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar.

"Mun sani cewa matsalolin rashin tsaro na da alaƙa da matsalolin rashin aikin yi da ƙarancin ilimi a tsakanin matasa, ina mai ba wa ƴan Nageriya tabbacin cewa su kara hakuri zamu yi nasara, zan wadata matasa da ƴan ƙasa da wadataccen aikin yi, kowa zai samu abin yi domin a gujewa tarzoma da ƙin juna, za mu samar da tsaro da zaman lafiya".

Na tabbata zan dawo da Najeriya cikin hayya cinta, cèwar Shùgaban Kasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

Tinubu ya ce yana da hanyar da za ta sake ɗaukaka Najeriya da kuma kawo ci gaba ga kowa da kowa, ya ƙara da cewa “Zan iya tafiyar da hanya zuwa wadata, na san hanyar ilimi domin na yi imani da shi, na san hanyar da za a magance matsalar rashin tsaro a kasar."

Sai dai ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ba shi damar yin aiki ta hanyar hakuri da taya shi addu’ar fatan yin nasara.

Ya ce, “Za mu yi aiki tare ne domin ba za mu koma lokacin da wasu ke sace kudin kasar ba, ba za mu bari a yi mulkin k**a karya ba.”

16/02/2024

Mun Tura Takarda Zuwa Ofishin TikTok Dake Ƙasar Singafo, Cewar Kwamandann Hisbah Na Jihar Kano Sheikh Aminu Daurawa

Fitaccen malamin addini a Najeriya, kuma kwamandan Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa sun fara shirye-shiryen yadda zasu kawo ƙarshen masu yaɗa munanan abubuwa a kafar sadarwa ta TikTok.

Daurawa ya bayyana haka ne a cikin wata hira da yayi da DW Hausa.

Menene ra'ayinku?

16/02/2024

An cire tallafin Man Fetur.
An cire tallafin Gas.
An cire tallafin kudi na farashin Dala.
An cire tallafin Noma.
An cire tallafin manyan makarantu.
An cire tallafin tattalin arziki.
An cire tallafin shigo da motoci da sauran manyan kayyaki.
An cire tallafin zuwa aikin Hajji.
An cire tallafin zuwa Umrah.
Yanzu za'a cire tallafin wutar lantarki.

Wane tallafi ya rage?

Daga Comr Abba Sani Pantami

16/02/2024

Hukumar Hisbah tak**a Ramlat princess wacce ta yi bidiyon da ta tallata kanta take cewa duk namijin da zai aure ta sai ya auro mata macen da za su dinga lalata da ita📌

Hizbah aikin Allah

16/02/2024

Ango Da Abokansa A Wajen Ɗaurin Aure
Shin A Ganinku A Wacce Jiha Ne?

16/02/2024

An samu raguwar masu amfani da iskar gas a Najeriya, saboda tsadar rayuwa inji ƴan kasuwa

Photos from Arewa Daily Reporters's post 15/02/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Matashi ya fara tattaki zuwa Abuja don karrama shugaban Sojoji

Rahotanni sun nuna cewa wani matashi mai suna Sulaiman ya fara tattaki daga gombe zuwa abuja a wannan Laraba.

Matashin yace zai je Abuja ne dan bada lambar ga shugaban rundunar sojojin Najeriya Janar Chiristoper Musa lambar yabo.

Sulaiman yace Janar Musa ya cancanci lambar yabon saboda namijin kokarin da yake na tabbatar da tsaro a fadin Najeriya.

23/11/2023

Harin Isra'ila a Gaza ya saba hankali,

-Inji Azali Assoumani shugaban AU
Duniya

– Shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU Azali Assoumani ya bayyana cewar matakin da Isra’ila ta dauka a matsayin martani bayan harin da kungiyar Hamas ta kai mata abu ne da ba za’a lamunta da shi ba, ganin irin illar da ya yi wa rayukan jama’a da kuma yankin baki daya.

Yayin da yake tsokaci wajen taron shugabannin Afirka da G20 a Jamus, Azali yace matakin na Isra’ila wanda ya yiwa fararen hula matukar illa, ka iya haifar da karin masu tsatsauran ra’ayi.

Shugaban yace duk da yake basu amince da kazamin harin da Hamas ta kai wa Isra’ila ba, irin martanin da kasar ta mayar ba abu ne da zasu amince da shi ba, domin y asaba ka’ida.

Azali yace ta yaya zaka kwatanta makomar yaron da a idansa aka kashe mahaifi da mahaifiyarsa yana kallo, inda ya kara da cewar wannan ne ke sanya ake samun masu tsatsauran ra’ayi.

Shugaban kungiyar ta AU na daga cikin shugabannin kasashen Afirka sama da 10 da yanzu haka ke halartar taron zuba jari tare da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da shugaban Faransa Emmanuel Macron da kuma shugabar gudanarwar kungiyar Turai, Ursula von der Leyen a birnin Berlin.

23/11/2023

Najeriya ta ce za ta kwace lasisin kamfanonin rarraba wutar lantarki

Gwamnatin Najeriya ta yi barazanar kwace lasisin kamfanonin tattarawa da raba wutar lantarki daga hannun ‘yan kasuwa masu zaman kansu, sak**akon abin da ta kira rashin tabuka komai da s**a yi cikin shekaru goma da mayar da wasu sassan kamfanonin hannunsu.

Gwamnatin ta kuma gindaya wasu sabbin sharudda da za a cimma kafin sabunta musu lasisin.

23/11/2023

DA ƊUMI-ƊUMI: Kamfanin sadarwa MTN ya fara raba kyautar Data 30GB da katin kira kyauta don faranta ran masu ta'ammali da layin su gaba ɗaya.”

23/11/2023

Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Ce Gawuna Ne Ya Yi Nasara, Abba Aka Ci Tara

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta yi magana kan rudani da ake yi dangane da fitowar wani kundin shari'ar zaben Kano da wasu ke cewa ya nuna Abba Kabir na NNPP ne ya yi nasara.

Umar Bangari, babban magatakardar kotun ya ce kuskuren rubutu aka samu kuma za a gyara a bangarorin biyu.

Photos from Arewa Daily Reporters's post 15/11/2023

Shugaban gwamnatin Nijar ya yi hannu da hannu da Bola Tinubu shugaban ECOWAS da Alassane Ouattara shugaban UEMOA a karon farko tun bayan da s**a kakaba wa Nijar jerin takunkumai.

Da kai ne, ko ke ce, me za ki/ka fara cewa da su?

15/11/2023

Fargabar tarwatsa hadin kan al'umma ta tilasta wa gwamnatin Nepal haramta amfani da TikTok a fadin kasar.

Shin ko irin wannan matakin ya dace a wasu sassan Najeriya?

15/11/2023

Nijar ta kasa biyan kudaden ruwa na bacin da ta ciwo na dala miliyan 304 a cikin watanni ukun da s**a gabata.

15/11/2023

Ra'ayin Matsa

Hukumomi a wasu sassan Najeriya sun lashi takobin cigaba da yaki da ayyukan badala a yankuna da dama na kasar ciki har da jihar Kano, inda a baya-bayan nan hukumar Hisbah ta kaddamar da samame a wasu yankunan Kano da ta zargi ana aikata ba daidai ba.

Hukumar ta gana da taurarun TikTok da 'yan Kannywood a baya-bayan nan, wanda hakan ya zo daidai da wasu karin matakai da ake dauka a jihohi irinsu Borno na magance ayyukan batanci.

Shin me ke tasirin wadannan ayyukan da hukumomi s**a kaddamar ga rayuwar al'umma musamman ma matasa?

Ta yaya ya k**ata hukumomin su fitowa lamarin yaki da gurbatar tarbiya a tsakanin matasa?

Photos from Arewa Daily Reporters's post 15/11/2023

Wata mata mai suna Jisel da ke auren maza biyu a kasar Congo ta ce tana jin dadin rayuwa da su, sai dai ta ce da kowane zai samu gidansa a daban da za ta fi jin dadin rayuwa maimakon su uku a gida guda.

Me za ku ce kan irin wannan aure?

Photos from Arewa Daily Reporters's post 14/11/2023

INNÂ LILLAHÎ WA'INNÂ ILAIHÎ RAJI’ÙN.

Wani Ɗan Arewa Ya Rasú A Yańkin Kudu, Amma Káfin Rasuwarsá Ya Ce Shi Ɗan Jihar Borno Nē

Jama'a ku taya mu binciken ƴan uwan wannan bawan Allah. Allah ya yi masa rasúwa a jihar Inugu ranar Juma'a, amma kafin ya rasú ya shaida mana cewa shi ɗan Maiduguri ne daga ƙaramar hukumar Shani a gundumar Bargu.

A taimaka a taya mu yaɗawa ko Allah zaisa a dace.

Allah ya jikansa Allah kuma ya sa a sami ƴan uwansa.

Photos from Arewa Daily Reporters's post 14/11/2023

Wani masoyin Buhari yayima wanda ya maka Rarara a kotu kyautar motar miliyan 20

A rahoton na cewa; wani masoyin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yayi kyautar motar miliyan 20 ga Alhaji. Sani Ahmad Zangina, wanda ya maka Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara a kotu, “inda yake zargin mawaƙin da cin zarafin tsohon shugaban kasar.”

An yi kyautar mota ga wanda ya maka Rarara a kotu a yau lahadi ne wato Alhaji. Sani Ahmad Zangina, ya sanar da sabuwar motar da wani masoyin tsohon Shugaban kasar Nijeriya ɗin Muhammadu Buhari ya bashi bisa baiyana irin farin cikinsa da yaji na yadda ya shigar da mawaƙin Kotu na zargin cin mutuncin Muhammadu Buhari da Rarara yayi a wani taron manema labarai.

A gobe litinin ne akesa ran fara sauraren ƙarar da ya shigar da mawaƙin siyasar Dauda Kahutu Rarara a gaban kotu.”

Photos from Arewa Daily Reporters's post 14/11/2023

An samar da Wani Takalmi Mai Suffar Ɓera Ku Hanzarta Kasuwa Domin Ku Mallaki Naku...

14/11/2023

Hukumar Husbah a jihar Kano ta gayyaci ‘yan Kannywood wata ganawa a yau, bayan ta yi irin wannan da taurarin Tik Tok a makon jiya.

Kutse ko saita al’amurra? Me kuke fatan ganin hukumar ta yi wa masana’antar Kannywood ?

14/11/2023

Muna aiki tukuru wajen sauya matsayar Najeriya - Bola Ahmed Tinubu

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Idan Kunfi Karfin Doka Bakufi Karfin Ta Allah Ba, Yanzu-Yanzu Saurari Wani Bayanin Sheikh Daurawa...
#IsahAliPantami #skillrether #arewachallenge #arewaweddings #sautusunnah #duniyartech#arewadailyreporters

Address

Yahaya Madaki Way
Katsina
811922
Other Media/News Companies in Katsina (show all)
Jaridar Gizo-Gizo Jaridar Gizo-Gizo
Shahura
Katsina

Domin samun Labarai tare da ruhotanni akan al'amuran da s**a shafi tsaro a Nijeriya tare da makwabta

DMCV Online News DMCV Online News
Lay Out
Katsina

This page is meant for local and international news

Hausa da Al'adu Hausa da Al'adu
No 140 Mani House, Yahaya Madaki Way Kofar Ƙaura New Lay-out Katsina
Katsina

Hausa da Al'adu is a platform that is being operated by CONTENT AND CLIPS Media Services Limited, a

Kukan Kurciya Daily Post. Kukan Kurciya Daily Post.
Katsina

Success through labour

Katsina Digest Katsina Digest
Katsina

Katsina Digest is a news outlet that serves as a Gateway To The Home Of Hospitality in Nigeria 🇳🇬

Gaskiya Daily Post Gaskiya Daily Post
Katsina

Gaskiya Daily Post jarida ce da zata dinga kawo muku labarai cikin harshen Hausa.

Smart∆ngle Smart∆ngle
Katsina

Yakara a yau news Yakara a yau news
Katsina

Slm yan uwa da abokan arziki na garin yankara da kewaye anbude wannan pag ne domin tattauna matsalolin da s**ashapi yankara da kewaye dakuma bada shawara akan yadda za a magance ma...

Popular News Hausa Popular News Hausa
Katsina

we are giving consultancy services on media activities and other matters arise

Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai
Kofar Kaura Katsina
Katsina

Tatauna muhamman bayanai na hon musa gafai

Bindawa News Bindawa News
Katsina

We are in bindawa