Gaskiya Daily Post

Gaskiya Daily Post jarida ce da zata dinga kawo muku labarai cikin harshen Hausa.

04/05/2023

ZINARIYAR CE DA GASKE, SHI YASA AL'UMMA S**A RUNGUMI HIDIMARTA DA ZUCIYA DAYA

Daga Iro Manu Rimi (Sarkin Yakin Zinariyar Gwagwaren Katsina)

Yada ayyukan alkhairan Zinariyar Gwagware bamu fara shi don mu daina ba. Ko da kuwa ace hanya zata rufe kanta, hakan ba zai sa mu nannade hannunmu mu koma gefe ba. Ba abin da zai hana mu sa katafila mu sake barke wata sabuwar hanyar domin ci gaba da yada ayyukan alkhairin Zinariyar Gwagwaren Katsina Haj. Fatima Dikko Radda ba.

Ba don komai ba, sai don ta haka ne kadai zamu iya haskakawa tare da jan hankulan saurar al'umma, musamman matan shugabanninmu na sauran jihohinmu, da su yi koyi da irin kyawawan halaye da dabi'un Haj. Fatima Dikko Radda domin gani sun taimakawa al'ummarsu, tare kokarin ganin sun kawo musu ci gaban da ya dace.

Ma'am ko shakka babu ta ciri tuta, domin kyakkyawan tunaninta na a taimaki al'umma shi yake kara haskakata akan kowa, wannan yake nufin Jihar Katsina sai dai muce Alhamdulillahi, domin munyi dace da First Lady din da idanu bai tava ganin irin ta ba a Jihar Katsina, cikin wannan karnin.

Allah ya ci gaba da yi muku jagora, da taimako a cikin manufofinku ke da mai gidanki zababben Gwamnan Jihar Katsina mai jiran Rantsuwa Dr. Dikko Umar Radda na alkhairai ga Jihar.

18/09/2022

Yan kasar burtaniya da Amurka sun nemi zama yan Nigeria inda a yau shugaban kasa Muhammad Buhari ya cika musu burin su

A yanzu sun zama cikakkun yan kasa k**ar kowane dan Nigeria

Ku bayyana mana ra'ayoyinku

10/09/2022

Gwamnatin tarayya ta bada umarnin yin kasa-kasa da tutocin Nigeria da hukumomin Nigeria a kasashen waje a ranakun Lahadi 11-09-2022 da ranar Litinin 12-09-2022, don nuna alhinin mutuwar sarauniyar England ELIZABETH ta biyu

Umarnin na zuwa ne cikin sanarwa da ministan gida Ra'uf Aregbesola ya sanya wa hannu aka kumawa manema labarau

10/09/2022

Ambaliya: Ana fargabar sama da gonaki dari ambaliyar ruwa ta shafe a garin Tiga dake Kano

Sai dai hukumar Hadeja da Jama'are ta musanta cewa Dam din ya b***e

Photos from Gaskiya Daily Post's post 08/09/2022

Jarumar Kannywood Wadda Ta Yi Fama Da Cutar Typoid Da Maleriya, Maryam Yahaya Ta Fitar Da Zafafan Hotuna

Wane Fata Za Ku Yi Mata?

08/09/2022

Fitaccen lauya a Kano Abba Hikima Fagge ya ce gwamnatin Kano nayi masa barazana akan ya daina s**arta. Me za ku ce?

08/09/2022

Sakon Gaskiya, Daga Gaskiya Daily Post

08/09/2022

'Yan Fashi Sun Fasa Bankuna Tare Da Yin Awon Gaba Da Makudan Kuɗaɗe A Jihar Kogi

08/09/2022

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa wani sabon kwamiti domin nazartar bukatun Kungiyar Malaman Jami’o’in kasar ta ASUU wadda ke ci gaba da yajin aikin sai-baba-ta-gani.

Photos from Gaskiya Daily Post's post 07/09/2022

Yanz-yanzu.Hukumar kula da kafafen sadarwa NBC ta dakatar da gidajen rediyo da talabijin sanya wakar GWANJA mai taken WARRR

Photos from Gaskiya Daily Post's post 07/09/2022

ABIN A YABA: Sarauniyar Gusau, Hajiya Dr Lubna Muhammad Ta Gina Katafaren Masallaci Tare Da Kawata Shi

Photos from Gaskiya Daily Post's post 07/09/2022

An gurfanar da Shahararrun mawakan Arewa hip-hop 442, Safara’u, Gwanja, da wasu mashahuran TikTok a gaban kotun shari’a a Kano.

Photos from Gaskiya Daily Post's post 07/09/2022

Ina Masu Sha'awar Aikin Wucin Gadi Da Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa (INEC)

Ga dama ta samu ana Iya jarabawa Allah ya bada Sa'a Amin.

Za'a buɗe link ɗin daga Ranar Laraba 14th/Sep/2022 zuwa wata Laraba 14th/Dec/2022.

Photos from Gaskiya Daily Post's post 07/09/2022

Gidajen Da S**a Haura Shekaru Sama Da 700 A Duniya

Waɗannan gidaje masu ban sha'awa na Kogo da aka sassaƙa daga dutse a Kandovan, cikin ƙasar Iran ya na jan hakalin masu yawon buɗe Idanu.

Wajen ya na a arewa maso gabashin Iran a wajen dutsen Sahand, gidaje masu k**a da tuddai, an sassaƙa su ne daga dutsen mai aman wuta, wanda ke nufin cewa galibin kayayyakin da aka buƙata don gina su sun ri ga sun kasance a wurin.

Akwai ƙofofi da tagogi na zamani da aka gauraye tare da ƙarin daɗaɗɗen kyan gani da aka sassaƙa.

Daga Taskar Nasaba

06/09/2022

Abin Al'ajabi

"Tollund Man" wani mutum ne mai shekaru 2,400 da haihuwa da kuma sadaukarwa ga ɗan adam da aka kashe daga zamanin Iron Age, wanda aka samu a Bjældskovdal dake Denmark. An kiyaye jikinsa sosai ta yadda ko bayan shekaru 2,400 bai rube ba. Masana kimiyya suna iya ɗaukar sawun yatsansu sun kuma tantance abin da ya ci na ƙarshe a lokacin rayuwarsa..

06/09/2022

Gaskiya ana fama da rashi a kasar nan.

Wasu shekaru da s**a gabata, idan almajiri yai bara, yara yan kasa da shekara uku ba abin da s**a iya sai, "yaka dan malam". Ko da kuwa ba ace su kira shi ba.

Sai dai kaji almajiri ya shigo yace gani.

Amma abin mamaki a wannan lokacin abinda yara s**a gwanance a yanzu idan almajiri yai bara shi ne, "Yi hakuri".

Abin har ya fara zama jikin yan kananun yara.

Allah ka kawo mana dauki da rangwamin wannan rashi da ake fama dashi.

Daga Iro Manu Rimi

Photos from Gaskiya Daily Post's post 06/09/2022

"Janaza Mafi Girma a Tarihin Ƙasar Pakistan"

Wata mata a kasar Pakistan tayi batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam, aka kulleta a kurkuku kafin yanke mata hukunci, sai Gwamnan jihar Punjab wanda yake samun goyon bayan Amurka yai ta ƙoƙarin kubutar da matar ta hanyar canja hukuncin da ƙasar ta tanada ga duk wanda ya munana ladabi ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.

Matakin da Minister ya dauka bai yiwa mai tsaron lafiyarsa dadi ba, sai ya dauki bindigarsa ya harbi Gwamnan jihar Punjab harbi sama da 20 ya kashe shi har lahira.

Hukumomin ƙasar s**a k**a mai tsaron lafiyar Minister mai suna "Muttaz Qadri" aka yanke masa hukuncin kisa, bayan aiwatar da kisan aka miƙa gawar Muttaz ga danginsa.

Mutanen Pakistan sun fito jana'izar wannan gwarzo wanda ya fansar da ransa ga masoyin mu Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Sallam, wadannan sune kadan daga cikin hotunan jana'izar fiye da mutum miliyan 5 s**a halarci jana'izar wanda ya hada da sojoji da 'yan sandan kasar.

Tabbas abinda Muttaz Qadri yayi shi ake kira so! Allah ya jaddada masa rahama, Allah ya kara kusantamu Annabi Muhammadu SAW. Amiin

Daga: Sadi Ahmad Yalo.

Photos from Gaskiya Daily Post's post 06/09/2022

Subhanallah! subhanallah!! subhanallah!!!

Daga shafin Rabe fadar bege zango...

A Taimaki Makauniyar da Bata da Da Bata da Jika! Dan jagora ma Bata dashi.

Ace Dan Adam Yake Rayuwa a cikin wannan Dakin abin yakai a tausaya mata.

A haka Take Kwanciya a wannan Dakin.

Duk da yake Ansha Rushe Rushen Gine Gine a wannan Damunar ta Bana to Amma dole Zakaga wani yafi wani abin Tausayawa.

Wannan Baiwar Allah Mai suna Umma Makauniya tana Rayuwa a wannan Dakin da zai iya danne ta basai Ana ruwa ba, Allah Tsare.

Tana zaune ne a kofar Kudu Zango kusa da gidan Marigayi Alh. Abba Kurunbacha shine muke nema mata Gudun Mawa ko second din kwano ne da katako da bulo na kasa ko abinda za'a siya a gyara mata dakin nata.

Don karin bayani 09026931990
07037592127

Ko a saka abinda Allah ya H**e a wannan Account Number din 2167002356 UBA Habibu Muntari

06/09/2022

Sakonmu na wannan rana ta talata.

Da kuruciya ake neman abin da tsufa zai rayu da shi.

Follow our Page for more update.

Photos from Gaskiya Daily Post's post 06/09/2022

MUSULUNCI A KASAR IBO: Kyawawan Hotunan 'Yan Matan Inyamurai

Ina da mai zuwa neman aure?

05/09/2022

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Batun Kara Kudin Harajin Kiran Waya

05/09/2022

Karfin hali sata a gidan yan' bindiga: M@su garkuwa sun k**a barawo dake yi masu sace-s@ce a gidajensu

Daga Taskar Labari

Wasu gungun yan bindig@ a kauyen Kilili na jihar Katsina sun k**a wani matashi da s**a ce baraw0 ne dake zuwa gidajen su yana yi masu barna yana sace karafuna da sauran kayayyaki a gidajensu,

A wani bidiyo da Taskar Labarai ta kalla an ga yadda yan bindgar s**a daure matashin mai suna Halliru wanda ya ce shi dan kauyen Ranka ne, sannan s**a gabatar dashi ga yan jarida kafin daga bisani s**a mika shi ga hukumar soji domin a d@uki mataki akansa.

Alh Usman Kachalla Rugga shine shugaban yan bndigar wanda ya shaidawa dan Jarida Usman Saleh Jino cewa dama sun dade suna neman k**a masu zuwa suna yi masu sace-s@ce a gidajensu sai gashi yau Allah ya basu sa'a sun k**a baraw0n,

Ya ce sunyi niyyar k@she shi to amma s**a yanke shawarar gayyatar yan jarida cikin dajin domin nunawa Gwamnati irin kokarin da suke yi wajen k**a ba@tagari, "kuma yanzu zamu baku shi a kaishi wajen hukuma su hukunta shi"

Photos from Gaskiya Daily Post's post 05/09/2022

Ambaliyar Ruwan Sama Ya Malale Garin Jimun Dake Karamar Hukumar Darazo A Jihar Bauchi

Photos from Gaskiya Daily Post's post 05/09/2022

Rundunar Ƴan Sandan Jihar Katsina Ta Yi Nasarar Cafke Wani Dilan Tabar Wiwi Abdulrazak Ajibade, Mai Shekara 58, Ɗan Asalin Karamar Hukumar Ofa A Jihar Kwarai Da Kullin Tabar Wiwi 185

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

05/09/2022

An yanke wa ƴan madigo biyu hukuncin kisa a Iran

BBC Hausa

Photos from Gaskiya Daily Post's post 05/09/2022

DA ƊUMI ƊUMI: Za'a Rubuta Sunan Ganduje A Cikin Kundin Sunayen Mutanen Da S**a Ba Wa Musulunci Gagarumar Gudunmawa A Na 21 A Cikin Kundin Tarihin Musulunci

Ƙasar Saudiyya ta duƙufa wajen tsara biki na musamman domin karrama mai girma gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a dalilin namijin ƙoƙarinsa wajen musuluntar da maguzawa sama da mutum dubu goma batare da zubar da jini ba.

A cewar mahukuntar ƙasar, abin da gwamna Gandujen ya yi wata babbar gudunmawa ce ga addinin musulunci wacce babu wani ɗan siyasa da ya taɓa ba da irinta a Afrika ta yamma gaba ɗaya a wannan ƙarni na 21 tayadda hakan ke nuni da yadda gwamnan ya cancanci yabo.

Ƙasar ta Saudiyya ta kuma ƙara da cewa a dalilin wannan ƙoƙari da gwamna Ganduje ya yi, za ta rubuta sunansa a cikin kundin tarihinta wanda ta samar domin rubuta sunayen mutanen da ke ba wa musulunci gudunmawa mai girma a Nahiyar .

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ƙasar ta Saudiyya ta ke yabawa gwamna Ganduje a kan ƙoƙarinsa na hidimtawa addinin musulunci ba, ko da a baya ta taɓa karrama shi da lambar yabo mai ɗauke da ƙyallen ɗakin 'aba.

Sai dai a wannan karon a na tunanin salon karramawar zai sha bamban da duk wanda aka taɓa yi masa a baya girma domin kuwa gagarumin biki ne na musamman wanda ake za ra halartar manyan shugabanni na duniya.

Wane fata zaku yi masa?

Photos from Gaskiya Daily Post's post 30/08/2022

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Sayo Motocin Yaki Masu Sulke Domin Cigaba Da Yakar 'Yan Bindiga

Photos from Gaskiya Daily Post's post 30/08/2022

Innalillahi wa inna'ilaihi rajiun
Ana fargabar wani ginin bene ya danne wasu mutane a kasuwar wayoyin hannu ta Beirut dake Kano

25/08/2022

Yadda aka kammala raba rukuni na gasar Zakarun Turai 2022/23

RUKUNI [A]:-

Ajax
Liverpool
Napoli
Rangers

RUKUNI [B]:-

FC Porto
Atletico Madrid
Leverkusen
Club Brugge

RUKUNI [C]:-

Bayern Munich
Barcelona
Inter Milan
Plzer

RUKUNI [D]:-

Frankfurt
Tottenham
Sporting CP
Marseille

RUKUNI [E]:-

AC Milan
Chelsea
Salzburg
Dinamo Zagreb

RUKUNI [F]:-

Real Madrid
RB Leipzing
Shakhtar Donetsk
Celtic

RUKUNI [G]:-

Manchester City
Sevilla
Dortmund
Copenhagen

RUKUNI [H]:-

PSG
Juventus
Benfica
M. Haifa

[Fagen Wasanni]

Photos from Gaskiya Daily Post's post 20/08/2022

An Yi Jana'izar miji da matan da aka tsinci gawarsu a cikin gida a Katsina

Daga:- Shaheed Ammar Al'ameen

Al'ummar unguwar Rahamawa dake cikin garin katsina sun kwana da mummunan al'amari na mutuwar miji da mata a cikin gidansu.

Ajiya Juma'a ne 19/08/2020 mutanen Unguwar Rahamawa s**a kwana a mutuwar miji da mata. Mijin mai Suna Murtalad (Over) da Matar tasa Shamsiyya an tsinci gawarsu ne a cikin gida dukkansu a mace al'amarin da ya gigita jama'a unguwar.

An shaidin cewa dukkan su sunje ziyara a ranar Juma'ar wanda Shi murtala shine yakai Lamamin masallaci kuma ya dawo dashi daga bisani kuma ya wuce gidansa wanda bayan dawowar nasu ne daga Masallaci s**a shiga gida wanda sai dai gawar tasu aka fiddo

Kaninsa mai suna Abdullahi wanda shine yaje gidan marigayin ya fada mana cewa " Bqyan na dawo gida bayan magrib sai ake cemin ai anje gidannmurtala an buga bai bude ba dan haka naje nida kanina ko ta katangane mu haura mushiga, da mukaje sai dora kanina yahau ya shiga ya bude mana gidan ina shiga na dudduba a daki naga babu kowa sai na dawo nan dakin dake cikin zaure shima nagansa a kulle na leka ta aga sai naga kafarsa ina shiga na dagansu shida matar duk a kwance na daga kafarsa naga motsi.

" Sai na dawo gida nike fada masu abinda ke faruwa shine aka ce muje a kaisu Asibiti muka samu mashin mukahau aka dora mijin ita matar aka samu mashin aka dorata mukatafi sai muka samu mai mota ya dauke me ya kaimu asibitin koda mukaje likita yake shaida mana cewa ai dukkan su sun rasu"
Da muke tambayarsa ko akwai wani abu da suke tunanin shi yayi sanadin mutuwarsu sai yace mana " Gaskiya munfi tunanin hayakin Genaretor ne saboda a dakin da suke na zaure ne kuma anan Injin din yake "
Anyi jana'idarsu k**ar yadda addini musulunci ya tana da kuma Dubbin Al'ummah ne s**ayi rakiyar su zuwa makwancinsu

Allah ya jikansu ya gafarta masu mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Katsina
Other Media/News Companies in Katsina (show all)
Jaridar Gizo-Gizo Jaridar Gizo-Gizo
Shahura
Katsina

Domin samun Labarai tare da ruhotanni akan al'amuran da s**a shafi tsaro a Nijeriya tare da makwabta

DMCV Online News DMCV Online News
Lay Out
Katsina

This page is meant for local and international news

Hausa da Al'adu Hausa da Al'adu
No 140 Mani House, Yahaya Madaki Way Kofar Ƙaura New Lay-out Katsina
Katsina

Hausa da Al'adu is a platform that is being operated by CONTENT AND CLIPS Media Services Limited, a

Kukan Kurciya Daily Post. Kukan Kurciya Daily Post.
Katsina

Success through labour

Katsina Digest Katsina Digest
Katsina

Katsina Digest is a news outlet that serves as a Gateway To The Home Of Hospitality in Nigeria 🇳🇬

Arewa Daily Reporters Arewa Daily Reporters
Yahaya Madaki Way
Katsina, 811922

Domin kawo maku labarun Nigeria a lokacin da suke wakana dakare martabar arewa da Nigeria baki daya

Smart∆ngle Smart∆ngle
Katsina

Yakara a yau news Yakara a yau news
Katsina

Slm yan uwa da abokan arziki na garin yankara da kewaye anbude wannan pag ne domin tattauna matsalolin da s**ashapi yankara da kewaye dakuma bada shawara akan yadda za a magance ma...

Popular News Hausa Popular News Hausa
Katsina

we are giving consultancy services on media activities and other matters arise

Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai Sarkin Yakin Hon. Musa Yusuf Gafai
Kofar Kaura Katsina
Katsina

Tatauna muhamman bayanai na hon musa gafai

Bindawa News Bindawa News
Katsina

We are in bindawa