AlkauthaarTv
Nearby media companies
Katsina
Katsina
Goruba Road G. R. A Katsina, Katsina
Dandagoro, Katsina
Katsina
Katsina KANTINSAUKI
Makera, Funtua
Scholarship Board, Katsina
Barka da zuwa Shafin Facebook na (Alkauthar_Tv).
Kasance da wannan kafa dan ilmantarwa, faɗakarwa, da wa'azantarwa, da ma labarai sahihai na halin da duniya take ciki.
Labarin cikin hotuna; Yadda ’yan’uwa musulmi Almajiran Sayyida Ibraheem Zakzaky (H) na Zariya s**a gabatar da Sallar Idil Fitr a Fudiyya Babban Dodo Zariya.
📷📷 Almujtaba Abubakar
Daga Karbala ƙasar Iraq (Haramin Imam Hussain (A.S), za a ga yadda aka gudanar da Sallar Idil Fitr a cikin hotuna.
Yau Laraba 1 ga Shawwal 1445 dai-dai da 10/04/2024, yayi dai-dai da ranar Sallah a ƙasar ta Iraq.
Daga ina kuke gabatar da taku Sallar Idin?
AlkauthaarTv
Muna taya ɗaukacin masu bibiyarmu barka da Sallah, Fatan Allah Ya maimaita mana ya karɓi Ibadunmu.
Ku cigaba da kasancewa da AlkauthaarTv
Eid Mubarak.
YANZU-YANZU:
Daga Ƙasar Iraq an sanar da cewa gobe laraba shi ne 1 ga watan shawwal kuma ranar Idil Fitr. Sanarwar ta fito ne daga Ofishin Sayyid Sistany da ke Najaf.
Allah Ya karɓi ibadu ya maimaita mana na baɗin baɗaɗa.
AlkauthaarTv
SANARWA:
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وال محمد وعجل فرجهم
Ba mu sami labarin ganin jinjirin watan Shawwal ba a duk inda muka tambaya a faɗin Nijeriya a yau Litinin. Don haka za mu cika Ramadan kwana talatin. Jibi Laraba za ta zama 1 ga watan Shawwal 1445, watau ranar Sallah Ƙarama, in sha Allah.
Muna roƙon Allah Ta'ala ya amshi ibadodinmu ya kuma nuna mana na shekaru masu zuwa cikin ƙoshin lafiya da yalwar arziki.
تقبل الله منا ومنكم صالح الأعمال🙏
29/Ramadan/1445
08/04/2024
DAGA KADUNA:
Yanda aka gudanar da Janaizar Shahid Mustapha Adam Daya daga cikin marasa Lafiya da Yansanda s**a harba a ranar juma'a 5/4/2024 a yayin da Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky s**a fito Muzaharan Nuna Goyan Baya ga Alummar kasar Palestine a kaduna izuwa yanzu mutum shida ne dai dai Adadin wayanda Rundunar yansanda s**a kashe a ranar Juma'ar.
Angudanar da janaizar ne a kofar Fudiyyah dake hayin rigasa kaduna wakilin Yan uwa na kaduna Sheikh Aliyu Tirmizi kaduna ne ya jagoranta janaizar.
Ga wasu daga Cikin Hotunan da muka dauko muku a wajan.
KD PRESS
8/4/2024
LABARI CIKIN HOTUNA:
-
Wasu daga cikin hafizan kur'ani na Fudiyya Tahfiz Katsina, wadanda ke karatu A Iraq.
-
Malam Musa Alkazim.
Malam muhammad Sani
Malam Aliyu Sani
-
Sun gabatar da hardar karatun Ƙur'ani wanda dalibai mahardata suke yi cikin ramadana domin sauke alkur'ani. A muƙamul Imam Mahdi (AF) ALLAH YA KARA HAZAKA.
AlkauthaarTv
Ko shi ne kowwa ke karantawa kuwa?
AN KARANTA QUR’ANIN ’YAN SHI’A A IRAQI Wannan wani ɓangare ne na karatun Qur’ani na watan Ramadhan da ya gudana a Maqam Imam Mahdi (A.F) a ƙasar Karbala Iraq, tare da ’yan’uwa Hafiza daga Najeriya...
Ku garzaya Channel ɗinmu na Youtube Ku kalli Yadda Muzaharar Quds ta bana 1445/2024 ta gudana a birnin Karbala, Iraq.👇🏾
MUZAHARAR QUDS DAGA KARBALA Wannan ita ce muzaharar tare da ’yan’uwa musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) da ke zaune a Karbala ƙasar Iraq.Ta gudana ne a ranar Juma’a 5/4/2024....
Labari cikin Hotuna:
Yadda ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaqub Al-zakzaky (H) da ke zaune a ƙasar Iraq, birnin Karbala s**a shiga sahun al’ummar musulmi na faɗin duniya wajan nuna goyon baya ga al’ummar Falasɗinu.
Wannan muzahara ta gudana ne a jiya juma’a da dare bayan Iftar.
Shaikh Mahdi Sanda wanda shi ne ya rufe muzaharar da taƙaitaccen jawabi kan maƙasudin Muzaharar, inda daga ƙarshe kuma ya gabatar da addu’o’in Allah ya gaggauta rusa haramtacciyar ƙasar Isra*l da uwar gidanta Amerika.
Ga wasu hotunan da wakilinmu ya ɗauko mana.
AlkauthaarTv
06/04/2024
Harkar Musulunci Ta Gudanar Da Muzaharar Quds A Nijeriya
Daga Cibiyar Wallafa
'Yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) sun gudanar da Muzaharar Quds a yau Juma'a 26 ga Ramadan 1445 (5/4/2024) a manyan garuruwan Nijeriya kimanin 30, ciki har da babban birnin Tarayya, Abuja.
Muzaharorin wadanda aka yi su don bayyana goyon baya ga Al'ummar Falastinawa, da kuma yin Allah wadai da haramtacciyar ƙasar Izra'ila da ke kashe su ba dare ba rana tsawon fiye da shekaru 70, a dukkan garuruwan ya samu halartan dubun dubatan al'umma.
Muzaharar ya kunshi dukkan bangarorin al'ummar Musulmi, Shi'a da Sunnah, a wasu garuruwan kuma, k**ar a Katsina, an gudanar da Muzaharar ne tare da wasu daga mabiya addinin Kirista, inda s**a bayyana cewa al'amarin Falastinawa ya shafi mutuntaka ne ba addini kawai ba, kuma in ma addini ne, Yahudawan Sahayina suna kashe har da Kiristoci ne a Gazza.
An gudanar da Muzaharar a birane da dama, inda aka yi ta da safe a garuruwan Katsina, Bauchi, Kaduna, Potiskum, Zariya da wasu garuruwan masu yawa, sannan kuma bayan sallar Juma'a, aka gudanar a Abuja, Kano, Jos, da wasu biranen, sannan aka yi kashi na biyu kuma a garin Zaria.
A dukkan garuruwan da aka gudanar da Muzaharorin, an yi an kammala lafiya, in banda a Jihar Kaduna, inda gamayyan jami'an tsaron Nijeriya s**a bude wa masu Muzaharar wuta a Kaduna da Zaria, sun jikkata mutane kimanin 30, tare da kashe mutum 4 a Kaduna, 1 a Zariya.
Ga hotunan yadda Muzaharar ta gudana a Abuja.
— Cibiyar Wallafa
26/9/1445 (5/4/2024)
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya Isa Birnin Masshad a safiyar yau Lahadi 15/10/2023.
Daruruwan al'umma sun taru domin tarbansa, inda s**a rika raira taken gwagwarmaya da jinjina ga Jagoran.
Masshad, nan ne garin da Haramin Imam Ali Bin Musar Ridha (AS) yake, Limami na 8 a jerin Imaman shiriya, kuma halifofin Manzon Allah (S).
Ana sa ran bayan haka, su Jagora su wuce asibiti, domin yin jinyar da ta fitar da su daga kasarsu InshaAllah.
AN CANZA ALAMOMIN JUYAYI ZUWA NA MURNA.
Sashen kula da kwalliya (Decoration) na Haramin Imam Ali (A.S) da ke Najaf da na Imam Hussain (A.S) da ke Karbala a birnin Iraqi sun canza alamomin da ke nuna juyayin waƙi’ar Ashura da 40 na Imam Hussain (A.S) da kuma na wafatin Manzon Allah (S) da aka kammala kwanan nan, inda aka sauya su da na murnar shigowar watan Haihuwar Fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S).
Bayan wanke haramin tare da sa turare da furanni, maziyarta sun cigaba da ziyara.
Karbala Media Hausa
19/09/2023
CIKIN HOTUNA: Yadda Aka Yi Jana'izar Marigayi Ayatullahil Uzma Sayyid Muhammad Mahdiyul Khurasany wadda ta gudana a yau cikin haramin Imam Ali (A.S) da ke a birnin Najaful Ashraf, Iraq.
Bayanai na nuna za a bizne Sayyid Muhammad a yanzu a cikin Haramin na Imam Ali (A.S).
Dubunnan al’umma daga ciki da wajan waƙasar gami da manya-manyan malamai ne su ka halarci jana’izar tasa.
Allah ya jiƙansa da rahama.
Karbala Media Hausa
18Sept2023
Daga Shafin Shaikh Yakub Yahya Katsina
SHAIKH MUSAL QASUYUNI NASIRU KABARA, YA JAGORANCI ZIYARA GIDAN ƘADIRIYYA NA DUNIYA A BAGHDAD.
A cigaba da ziyarorin da tawagar maziyarta Arba’een na Imam Hussain (A.S) ke yi, a jiya Asabar 01 ga Rabi’u'l Auwal 1445, dai-dai da 16/09/2023 sun ziyarci gidan Ƙadiriyya na duniya da ke birnin Baghdad a ƙasar Iraqi.
Ziyarar wadda ta gudana a ƙarƙashin jagorancin Shaikh Musal Qasuyuni Nasiru Kabara, (daga gidan ƙadiriyya na Najeriya) inda ya samu rakiyar wani ba’adi na ’yan’uwa daga ɓangaren Ɗariƙar Tijjaniyya, da kuma wasu ɓangare na Mazhabar Ahlulbaiti (A.S) (duk daga Najeriya).
Bayan samun tarba ta musamman daga shugaban Ƙadiriyya na duniya, Shaikh Al-Alusy, an gabatar zikirori dai baitoci ga shugaba Annabi Muhammad (S) k**ar yadda Ƙadirawa su ka saba, tare da shafa larba (Bandiri, Mandiri). An tattauna kan yadda da za a ƙara karfin haɗin kan al’ummar musulmi baki ɗaya musamman ɓangarorin uku. Sheikh Adamu Tsoho Ahmad Jos da Shaikh Yakub Yahya Katsina na daga cikin almajiran Sayyid Zakzaky (H) waɗanda su ka yi rakiyar zuwa gidan na Ƙadiriyya.
Ga wasu Hotunan yadda ziyarar ta gudana.
17Sept2023
RAHOTON GAUGAWA...
Mutum miliyan huɗu da dubu dari takwas da saba'in da huɗu , da ɗari huɗu da hamsin (4,874,450) ne s**a halarci taron tunawa da shahadar Manzon Allah (saww) a bana , taron da ya gudana yau a birnin Najaf mai alfarma dake ƙasar Iraqi .
Hukumar gudanarwa ta haramin Imam Ali (a.s) ce ta sanar da haka yanzu .
✍️Al-Abdul Faneey Al-kanaweey
ANA CIGABA DA JUYAYIN WAFATIN MANZON ALLAH (S) A IRAQ.
Daga Iraq, birnin Najaful Ashraf (Harmin Amirul Mumineen A.S), yadda al’umma ke cigaba da tururuwa domin ziyara tare da jajanta wa Imam Ali (A.S) dangane da Wafatin Yayansa kuma Sirikinsa Manzon Rahama (S).
Kamar yadda ya zo a tarihi dai a irin wannan rana ta 28 ga watan safar a shekara ta 10 (ko ta 11 a wata ruwayar), Manzon Allah (A.S) ya amsa kiran Allah (S.W.T) ,ya koma zuwa ga rahama Ubangijinsa.
Dukkanin faɗin duniya musamman a haramomin Ahlulbaiti (A.S) a yau cike su ke da al’ummar inda su ke gabatar da ziyarori na ta’aziyya bisa ga wannan babban rashin da duniyar musulunci ba za ta taɓa mantawa da ita ba.
Allah Ya ƙara wa Annabi daraja da ɗaukaka 🤲
Karbala Media Hausa
Thu,Sept,2023
Yanzu haka daga Karbala adadin Maziyartan Imam Hussain (A.S) na bana 1445/2023 ya kai Miliyan 22 da ɗoriya, inda ya fi na bara da miliyan 1.
SHAIKH YAKUB YAHYA KATSINA A SAHUN TATTAKIN 40 DAGA NAJAF ZUWA KARBALA.
A jiya Talata 19/02/1445 (05/09/2023) Shaikh Yakub Yahya ya samu shiga sahun Tattakin Arba’een wanda ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) su ka gabatar daga Najaf Zuwa Karbala (Haramin Imam Hussain A.S).
Kafin shiga sahun dai ya gaggaisa da ’yan’uwa daban-daban da kuma wasu ba’adin ɗalibai da ke karatu a Iraq ɗin.
Miliyoyin al’umma ne daga sassan ƙasasshen duniya su ka halarcin wannan Tattaki, domin jajantawa ga Manzon Allah (S) da iyalan gidansa na cika kwanaki 40 da kisan gillar da aka yiwa Imam Hussain (A.S) da sahabbansa baki ɗaya.
Ga wasu hotunan Tattakin.
#وفاءللحسين
Wakilin ’Yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Katsina, Shaikh Yakub Yahya Katsina tare da wakilin ’yan’uwa na Jos, Sheikh Adamu Ahmad Tsoho Jos, a yayin ziyararsu a Haramin Imam Hussain a yau Litinin.
Taqabbalallah 🤲
Karbala Media Hausa
Cikin Hotuna: Wani Ɓangaren ma'akatan lafiya na Harkar Musulunci Ƙarƙashin jagoranci Sayyid Zakzaky (H) da ake kira da (ISMA).
Su na a bakin aiki dan kula da lafiyar ma su yin Tattakin 40 daga Najaf zuwa Karbala.
Karbala Media Hausa
TAWAGAR TATTAKI DAGA NAJAF ZUWA KARBALA TA ISA MAUKIBIN JQGORA (H).
A cigaba da Tattakin 40 na Imam Hussain (A.S) daga Najaf zuwa Karbala wanda ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Yaqub Al-Zakzaky (H), a yau kwana na 4 wuni na 5, sun isa a maukibin jagoran harkar musulunci a Nigeria Sayyid Zakzaky (H) a bisa hanyar ta su.
Kamar yadda kowace ƙasa da kuma ɓangarori al’ummar musulmi ke da mawakib da su ke rarraba wa al’umma abubuwan amfani, k**a daga abinci da kayan masrufi da sauransu, ita ma Harkar Musulunci a Najeria ta samar da nata Maukibin da ke Amudi na 1117, domin yin hidima ga maziyarta Imam Hussain (A.S).
Bayan isar tawagar ’yan Najeria ma su Tattaki sun tsaya a gaban maukibin na Jagora (H), inda aka rarraba ma su abubuwan sha, sannan daga bisani aka gabatar da addu’a ta musamman ga jagora (H). Prof. Abdullahi Ɗanladi ne ya gabatar da taƙaitaccen jawabi bayan kammala addu’ar, zuwa wani lokaci sannan tawagar ta yi bankwana ta yi gaba dan cigaba da Tattakin.
Bayan matsawa gaba, an yada zangon rana domin yin salloli da cin abinci tare da hutawa wanda bayan hakan Tattakin zai cigaba.
Karbala Media Hausa
أدبوا أولادكم على ثلاث خصال: حب نبيكم، وحب أهل بيته، وقراءة القرآن.
ABUN GWANIN BURGEWA..
Yadda wata karamar yarinya ta ke raba wa masoya Imam Husaini (A.S) biscuit, a sahun Tattaki yawm Arba'een da ya gudana a yau Lahadi yankin malumfashi, katsina (Nigeria).
(Allah Ka kara sa soyayyar Ahlulbaiti a cikin zukatan ’ya’yammu da dukkan iyalimmu).
Hoto: Muhammad Lawal.
Karbala Media Hausa
اشرب الماء وزكر عطش الحسين عليه السلام
Ku sha ruwa ku tuna ƙishirwar da Imam Hussain (A.S) Ya sha.
Karbala Media Hausa
Ziyarar wasu ’yan’uwa ma su Tattakin Arba'in a ƙasar Iraqi a makwancin Salmanul Farisi da Huzaifatul Yamani, da kuma rijiyar da Imam Ali (A.S) ya tona.
Sannan sun ziyarci katangar Kisra wadda a lokacin da aka haifi Annabi (S) ta tsage, cikin ma su ziyarar akwai wakilin Yan’uwa na garin Gombe Sheikh Muhammad Abbari da sauran wasu ba'adin yan’uwa da su ka halarci Tattakin 40 na bana daga Najeriya.
Allah Ya karɓi sa’ayi.
Karbala Media Hausa
Kaitsaye: DAGA HANYAR TATTAKI, NAJAF ZUWA KARBALA.
Bayan kammala salloli da cin abinci tare da hutawa har zuwa ƙarfe 4 na yamma, tawagar ta ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) da ke Tattakin 40 daga Najaf zuwa Karbala, ya ci gaba cikin tsari da nizami k**ar yadda aka fara tun daga yammacin ranar Alhamis da ta gabata zuwa yammacin yau Lahadi.
Bayan matsawa daga Amudin na 875, wakilin ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na Jos, Shaikh Adamu Ahmad Tsoho Jos ya jona tare da ’yan’uwa da cigaba da Tattakin duk da yanayin na jikin Shaihin Malamin.
Yanzu haka dai Tattakin na cigaba da tafiya inda ’yan’uwa ɗauke da tutoci maza da mata su ke tafe cikin juyayi da jimami gami da alhini na cikar kwana 40 da kisan Abu Abdullahil Hussain (A.S) a filin Karbala.
Ga wasu hotunan da mu ka ɗauko ma ku a dai-dai wannan lokaci. Kar ku manta ku kasance tare da:
Karbala Media Hausa
HANYAR ZUWA KARBALA RANA TA 3, WUNI NA 4.
’Yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Zakzaky (H) na cigaba da gudanar da Tattakin 40 zuwa Karbala daga Najaf inda yau Lahadi ana rana ta 3, wuni na 4 da fara wannan Tattaki.
Da safiyar yau ɗin bayan shafe awanni aƙalla 5 ana tafiya an isa zangon rana inda za a yi sallolin Azahar da La’asar tare da cin abinci a tsakanin Amudi na (875 da 876).
Tun kafin zuwa masaukin na rana, sai da aka tsaya aka yi Tablig k**ar jiya a cikin harshen farsi wanda Shaikh Dr. Shu’abu Ya gabatar a gaban maukibin wasu Iraniyawa.
Ga wasu hotunan Tattakin na yau da mu ka ɗauko ma ku.
Karbala Media Hausa
“ZAI ZAƁI YA CI JARABAWA NE? KO KUMA A’A ZAI BARI YA FAƊI JARABAWA NE?” ___Shaikh Yaƙub Yahaya Katsina.
_Bin Yaqoub Katsina✍🏽
“Alhamdulillahi wannan garin baku jahilci abinda ya faru a Zariya ba ku jahilci Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da kiransa ba. Shekara da shekaru kuna ƙarƙashin wannan da’awa da wannan kira.
Kunga dai abinda ya faru da shi (Sayyid Zakzaky) da almajiransa, to hanƙoronsa shi ne cewa al’ummar Musulmi da suke zaune k**ar kara zube to su dawo su bi koyarwar Manzon Allah (S).
Kun ga abinda ya sameshi, Allah kaɗai Ya san (adadin) harsashin da ya ratsa jikin Malam (H). Allah kaɗai Ya san (yawan) harsashin da ya ratsa jikin iyalinsa, sannan kuma ’ya’yansa guda 4 ris Maza baki ɗaya aka kashesu gaban idonsa, yayin da almajiransa sama da 1000 aka kashe kuma aka yi masu ramin bai ɗaya aka rufesu wasu ma da rai, Maza da Mata da Yara har masu ciki. Saboda mene? Saboda Ya ce a dawo bisa turbar Manzon Allah kuma shi ne kawai warwarar matsaloli, ba wata warwarar matsaloli illa addini (addinin nan shi ne warwar matsalolimu) ko wace matsala maganinta na cikin addinin nan.
In ka dubi tarihi abinda zaka gani kenan yanzu dai gashi tarihin da muke gani na Malam da almajiransa, halin da suke ciki. Ga kuma abinda muka ji na lokacin Shehu Usmanu Ɗan Fodiye (R.A) da daular Hausa ko daular Gobir a wancan lokacin, da irin abinda s**a faru. Ga abinda ya faru da Imamu Khomaini (Q.S) a Iran da irin yadda aka kwashe da Shah, har al’amura s**a shashace. Duka waɗanlnan al’amura yana nuna maka cewa; Duk wanda zai ce a dawo wa turbar addini to fa akwai matsala, to kuma in ba a dawo ba to akwai fa waɗancan gidajen (Aljanna da Wuta) kuma. Wanda ya dawo, ga wannan gidan, wanda bai dawo ba? ga wancan gidan. Saboda haka kaga ya zama gwaji, wace irin jarabawa zai ci? Zai zaɓi ya ci jarabawa ne? Ko kuma a’a zai bari ya faɗi jarabawa ne?
Wannan shi ne fafutikar da ake ta yi yanzu aga cewa an falkar da al’ummar Musulmi ta koma kan tsari na Musulunci da koyarwa irin ta Musulunci k**ar yadda Manzon Allah (S) ya koyar da ita. Wannan kuma ba zai yiwu ba sai mun samu wahada mun dunƙulu wuri ɗaya sannan kuma dole mu samu mai irshadi wanda zai gaya mana dai-dai da ba dai-dai ba k**ar yanzu misali Alhamdulillah al’ummar ’yan’uwa almajiran Malam (H) suna da murshidi shi ne Malam, shi ne jagora, shi ne ke bada irshadi kuma gashi muna rayuwa cikin al’umma...To muna fatan ya zama wannan ce hanyar da kowwa zai taka ya bi dan shima ya samu tsira wannan ma shi ne dalilin kawo wannan taro a nan da kuma yin tabligi a dai-dai wannan lokaci a nan kuma hasken ya shiga gidan kowwa, yaje kunnen kowwa”.
{A wani ɓangare na jawabinsa na (Tablig) a garin Rimin Guza, 23/12/2021. Kuma shi ne karo na biyu da Malam ya yi jawabi a garin bayan shekaru 10 da s**a wuce}
24Dec.2021.
12 Ga WATAN 12, RANAR DA GWAMNATIN BUHARI TA YI TA’ADDANCI A ZARIYA.
Lallai lamari yayi girma, zukata sun raunana, hawayen sun kwaranya, farin ciki ya tafi, kai ya kulle, yayin da walwala da duk wani jin daɗi ya shude😭😭
Shin ta ina zan fara? Ta jinanen da s**a kwarara? Ko ta wadanda aka kona? Ko wadanda aka binne a ramin bai daya? Shin ta rushe gine-gine masu himmanci da wajan Ibada (Massalaci) zan soma ko kuwa yara da Mata masu juna biyu da aka karkashe zan yi magana?. Ko Halin da jagorana ya shiga tare da Iyalinsa? Ko kuwa zan yi magana ne akan ’yan’uwana Maza da Mata da aka tsare gidan yari, tsawon shekaru bisa zalinci?.😭😭
Kai na rasa ta ina zan fara😭😭 domin ranar 12 ga Disamba shekarar 2015 rana ce da har in koma ga mahaliccina ba zan taɓa mantawa da ita ba. Ranar ne wani abu ya faru da ba a taɓa samun irinsa ya faru a tarihin wannan zamanin namu ba.
Sojojin Najeriya karkashin umarnin shugaban kasa bisa jogorancin shugaban Sojoji s**a afka wa ’yan kasa da rana tsaka a Zariya s**a kashe dubunnai, tare da kone su. Sannan s**a ci zarafin Malamin addinin Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da Matarsa Malama Zeenatu tare da kashe masu ’ya’ya a gabansu da rushe muhallan da suke gudanar da ibadodinsu har da Makabarta da Masallaci.
Yau shekaru 6 bayan tsare Shaikh Zakzaky na tsawon shekarun, ba a hukunta masu laifin ba kuma an hana shi fita kasar waje dan neman lafiyarsa duk da kotu ta wanke shi da cewa; bai da wani laifi hasali ma shi aka zalinta.
To mun kai kara ga Allah, ba mu manta ba kuma ba zamu yafe ba.
_Bin Yaqoub Katsina✍🏾
12/12/2021
IMAMU KHOMAINI (Q.S) DA MALAM ZAKZAKY (H) ALAMA NE NA SADAUKARWA...Shaikh Yaƙub Yahaya Katsina
...“Shin kana jin labarin gwarzantaka da sadaukarwa irin ta Manzon Allah (S)? to ka kalli waɗannan bayin Allah ɗin su s**a aikata a aikace. Imamu Khomaini (Q.S) ya zama dodon arna da yahudu, ya kafa daular Musulunci ƙaƙƙarfa wadda ta gagari turawan yamma, tare da ƙarfinsu da makircinsu da munafuncinsu da ƙulle ƙullensu amma ya gagaresu, ya kafa daular da sai ta dangana da Imamu Mahdi (S.A).
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ɗosano mana hasken gidan Annabi (Ahlulbaiti) ya kawo mana a nan, ya ɗora mu a kan gwagwarmaya ta addinin Musulunci domin dawo da al’umma zuwa ga koyarwar Annabi ta haƙiƙa.
To amma abin takaici da muke samu shine; mutane an sa masu ƙiyayya da gidan Annabi (S). Suna ƙiyayya da gidan Annabi ba tare da sun sani ba, wannan kuwa yana da hatsari. Ba yadda za a yi ka ce kana tare da gidan Annabi amma baka tare da ’ya’yansa. Ba yadda za a yi ka ce kana son Annabi amma kana ƙin masoya gidansa, wannan ba zai yiwu ba, tiƙa da warwara ne.
Idan duk zaka kashe abinda ka mallaka wajan hidimar Mauludi, amma idan kaga masoya gidan Annabi ka ƙyamacesu to baka yi komai ba fa, ba yadda za a yi kace kana son Uwa amma baka son ’ya’yanta (ba zai yiwu kace kana son Annabi ba amma baka son ’ya’yan Annabi).
To yanzu da an ga hoton waɗannan bayin Allah ɗin, shi ke nan waɗanda ke ɗauke da hoton yanzu sunansu ’yan kaza ƙarara zaka ji ana cewa (’Yan Shi'a ne)... ai taron 'yan Shi'a ne, mi ke nuna taron ’yan shi'a ne? Hotunan waɗannan jaruman bayin Allah ɗin. Ko yana ganin ƙima da mutuncin abin, da an ce taron ’yan shi’a ne sai abin ya zube masa.
Ya Ilahi! To minene laifin Soyayya da gidan Annabi? Idan mutum na son 'ya’yan Annabi mi ye laifinsa? A fito mana da laifin ko a Hadisi ko a ayar Al-ƙur'ani inda aka ce ga laifin soyayya ga iyalan Annabi (S)”...
{An ciro a wani ɓangaren jawabinsa na rufe Muzaharar Mauludin Annabi (S) a garin ’Yan Albasa a ranar Asabar 20/11/2021}.
_Bin Yaqoub Katsina✍🏾
17,R/Sani.1443(22/11/2021).
Click here to claim your Sponsored Listing.
Videos (show all)
Category
Telephone
Address
Karbala'
56001
BabeKibla
Karbala', 56001
Contact For Azadari , Matam Dari & Majalis Events . Contact For Any kind Of Information � Whatsapp 03040974860 You Can Also Visit Our Youtube Channel By Searching ( Azadari Kach...
Karbala'
We aims to mirror the reality of the peaceful Islamic religion to the entire world.
Karbala
Karbala'
Hadafin zauran shine Yada Anbaton Ahlulbait (As)
Karbala'
صفحة اخبارية تهتم بالشأن السياسي العام والخدمي و تنقل المعلومة بأعلى درجات المصداقية والمهنية