Ælhãjï karami emir

Ælhãjï karami emir

You may also like

Urine
Urine
revo4879
revo4879

ماشاءاللہ......ماشاءاللہ.......

06/12/2023

Ya faru!!! ❗

A Maiduguri an ce kuskure❓
A Nasarawa an ce kuskure❓
A Benue shima kuskure❓
A Katsina an ce kuskure❓
A kaduna shima an ce kuskure❓

Yo shi wannan kuskuren akan yan Arewa kadai zai dinga faruwa ne?

Yan media na Arewa saiku kyale batun Kunu kuzo mu hada murya waje daya mu nemawa yan uwanmu haqqinsu.

Allah ya jiqan wanda s**a rasu ya bamu ikon tadda su da alkhairi.

28/11/2023

Allah Ka azurta mu yadda iyayenmu ba za su nemi wani abu su rasa ba.

Photos from Ælhãjï karami emir's post 24/11/2023

CIKAKKEN BAYANI KAN WASIKAR SHEIK JA'AFAR

Daga, Zainab Ja'afar Mahamud" Allahu Akbar...!

Wata Wasika Mai Kwanan Watan 3\2\2002 da Marigayi Sheikh Ja'afar ya rubutawa, yarsa Zainab ja'afar Mahmud, a lokacin da yake karatu a sudan. Ga abunda ita zainab ta rubuta a shafin ta ku karanta.

Shekaru 19 kenan da watanni mahaifina ya rubuto min wasikar nan daga qasar Sudan, lokacin yana karatun shi na masters degree a can.
Yau babu zato babu tsammani na ci karo da ita cikin wasu tsofaffin littafaina, ina karantawa sai na ke jin ina ma ina da damar da zan sake samun irin wannan wasika daga gareshi yanzu amma inaa!! Sai nake jin kamar yanzu ne ya rubuto min ita saboda gamammun sakonnin da ke cikinta da zansu amfane ni tsawon rayuwata.

Ina karantawa cike da tunanin irin yadda rayuwata ta kasance da shi a wancan lokutan, na yi rayuwa mai cike da kulawa, gata, tarbiyyantarwa, bada kariya, ilimantarwa, uwa uba kuma kauna ta musamman daga gareshi wadda ba zan taba mantawa da ita ba har na koma ga Allah😭😭

Ga Wasikar Malam \

Assalamu alaikum wa rahmatullah

Dafatan kina lafiya, yaya karatu? Ina fatan komai yana tafiya Kamar yadda ake fata,

Ina farin cikin sanar da ke cewa na isa Sudan cikin aminci da koshin lafiya, Amma kuma zan sake komawa Saudiyyah a karo na biyu domin yin aikin hajji,

Ina yi miki Wasiyya da TSORON ALLAH, a sarari ko a boye, ina kuma yi miki Wasiyya da yawaita TULAWAR AL'QUR'NI. Tare da kiyaye SALLOLIN FARILLAH, a kan lokaci, da kuma HIMMA wajen neman ILIMI da kuma HARDAR AL'QUR'NI

Haka nan kuma ina yi miji nasiha da BIYAYYA ga MAHAIFIYARKI da hakurin mu'amala da kannenki

Insha allahu zan dawo gida bayan aikin hajji

Na barki lafiya

Mahaifinki
Ja'afar Mahamud Adam
Khartoum Sudan.

Lallai rashin mahaifi babban gibi ne da babu mai iya cike wa mutum shi har abada!!!

Ubangiji Allah Ka ji kan mahaifanmu da s**a rasu Ka sanya Aljanna ce makomarsu,

wadanda suke raye kuma ka kara musu lafiya da imani da tsawon kwana mai amfani amin..pls follow thi page

22/11/2023

Pls my friends kusani cikin addu o inku Ina fama da rashin lafiya allah uban giji ya bani lpy

22/11/2023

Everyone

17/11/2023

BA'A YANKE TSAMMANI DAGA RAHAMAR ALLAH.

√√ Matukar Bawa Zaiyi Tuban Da Babu Kome Tabbas Allah Mai Gafara Ne Da Rahama Ga Bayin Sa.

√√ Allah Ta'ala Yasa Mu Wanye Lafiya.

^^ Mentor Malamina Professor Isa Ali Pantami, CON. Allah Ya Dawo Mana Dashi Lafiya.

★ Magajin Malam
★ Pantamin Kano

››› Ãlhaji karami særk

17/11/2023

Mafi Yawan Jinkiri Yakan Zama Alkhairi.
Ya Allah Kasa Duk Abinda Yayi Jinkiri a garemu Ya Zama Alkhairi.

16/11/2023

Ya Allah!
Saboda ƙaunar da kake yiwa Ma'aiki Sallallahu alaihi wa Sallama ka yi mana arziki duniya da lahira.

01/11/2023

Yah Allah ka tsaremu daga aikata abinda zaisa muji kunya 🙏

01/11/2023

ILLOLIN ZINA

1 zina nasa talauci

2 zina nasa duhun fuska

3 zina nasa hana kwanciyar kabari

4 zina mutun ya mutu babu imani

5 zina na bada ta kaitachiyar rayuwa

6 zina nasa ka rayu babu amfani cikin rayuwar

7 zina nasa allah yay fushi da mutum

8 zina nasa zuriyan ka ta lalace

9 zina nasa mala'iku su tsine ma

10 zina nasa asa mutum cikin wuta jahannama matukar bai tuba ba

Allah tsaremu daga aikata zina AMEEN

01/11/2023

Ga hanyan warware matsalolin duniya da lahira

27/10/2023

Allah ya Jikan Sheikh Abubakar Giro Argungu ya Haskaka kabarin shi.
Da rayuwar shi takai yau da Muna tare dashi a Katsina. Amma jiya sai dai Muryan danshi mukaji.

Allah ya Sakamar da gidan Aljannah.

27/10/2023

"Malam in ka yi taimako ba don Allah ba, bayan kudinka ya tafi a banza, masifa zata biyo baya kuma Allah zai yi fishi da kai. Duk abinda za ka yi ka yi don Allah, kar ka yadda shaidan ya yi wasa da aikinka".

Sheikh Ahmad Tijjani Yusif Guruntum (Hafizahullah)

Ælhãjï Kãrãmï Særkï



Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Fans

27/10/2023

“DUK RAYUWAR DA BABU ADDINI, MATACCIYAR RAYUWA CE.”

Ælhãjï karami særk

Photos from Ælhãjï karami emir's post 24/10/2023

Asslamu alaikum

Dun Allah kayi bincike a wannan film din a fadakar da mutane irin bannawa musulunci suna ake so ayi gameda wannan film din.

The New film TheBlackbook coming in 22/09/2023 at Netflix.

Wannan film me suna theblackbook za'asakeshi ne awannan wata.

A tsammanina wannan film an shiryashi ne domin muzanta addinin musulunci SBD, abun dubawa kuwa shine meyasa za'abawa matan kafiria bindigogi tattare da hijabi🤔 bayan duniya ta shaida cewa musulmine kawai suke sanya hijabi? Muyi tinani.

Nayi wannan post ne kawae SBD mu musulmi mu tashi tsaye kamar kada kin amincewar mu yayi tasiri akan na wakar da yayi sanye da jallabiyya suna rawa a masallaci dun Allah mu fadakar kamin ace an haska wannan film din a adakatar dashi.

Ina me janhankali tattare tunasar da fada muku cewa dukkan mu hakkine akan mu mu kare wannan addin islama daga dukkan cin mutunci da muzantawa da kafiran duniya suke shiryawa musulunci.

Kuji tsoran Allah Ku fitow kuyi magana. Meyasa sai sun siffanta da addinin musulunci zasuyi ta'addanci. Musulmi mu duniyyah ta shaida masu saka hijab ne

We against

ÆÆlhãjï karami særkkÆlhãjï karami særksÆlhãjï karami særk🆕

23/10/2023

Ba Wata Halitta Da Bayajin Maganar Ta.

MUHAMMADUR RASOOLULLAHI ﷺ♥️

23/10/2023

Yadda Kwankwaso ya zama gatan mahaddata Alqur’ani. Allah ya zama gatansa. Allah ya kara shiga lamarinsa.

Photos from Ælhãjï karami emir's post 22/10/2023

*COMPLETE WA'AZIN KASA NA JIYA DA KUNGIYAR IZALA TA GUDANAR A KATSINA🔊*

________________________________________________

Wannan Sune Complete Wa'azuzzukan Dare Da malamai S**a Gabatar A Wa'azin Kasa da Kungiyar JIBWIS ta Ƙasa Ta Gudanar A Garin Katsina Jiya Asabar 06/04/1445 - 21/10/2023 https://t.ly/xL5qi

001 Sheikh Safiyyu Alkasim Saulawa
https://t.ly/BSg3f

002 Ustaz Hussaini Abubakar Gero
https://t.ly/bmT1Z

003 Malam Muhammad Kuludu
https://t.ly/HGp4u

004 Sheikh Abdullahi Buba Jalingo
https://t.ly/h0sKP

005 Sheikh Nasir Yusuf Kidir
https://t.ly/w_lPr

006 Malam Abdulkadir Isah Yola
https://t.ly/lzFnj

007 Sheikh Imam Ladan Bunza
https://t.ly/w_lPr

008 Dr Abdullkadir Saleh kazaure
https://t.ly/S07ZK

009 Sheikh Gambo Kyari MaiDuguri
https://t.ly/dlOXh

010 Sheikh Barr Ibrahim Sabi'u Jibia
https://t.ly/saMjA

011 Sheikh Dr Kabiru Haruna Gombe
https://t.ly/vpCSs

012 Sheikh Imam Abdullahi Bala lau
https://t.ly/xGhsj

Zaka Iya Download Din Duka Wa'azin Ta Telegram Channel Din Mu. https://t.me/jsmkubau

Follow Our page:
https://www.facebook.com/jsmkubau

Join Our WhatsApp Group.
https://chat.whatsapp.com/GbtKlrqTxn51zNrBmyFVzQ

Join Our Telegram Channel.
https://t.me/jsmkubau

AAbubakar Nuhu Yahya KosoJibwis Social Media Kubau LG Kaduna State
07 Rabi'ul Akhir 1445
22 October 2023

21/10/2023

Ku yawaita Sadaka da Istigifari Suna Yaye Bakin Ciki Da Damuwa.

~Inji Rasulillah ﷺ pls follow dis page

16/10/2023

Ƴar uwata! Ki sani duk wanda yake ƙaunarki da gaske ba zai yi yunƙurin taba jikinki ba b***e aikata barna.

Ƴar uwa! Mafi girman kuskuren da zaki yi a rayuwa shi ne ki bar saurayinki ya mayar da gangar jikinki wajen wasansa da kuma jin daɗinsa.

Ƴar uwa! Ki sani, tabbas kin ci amanar Iyayenki da kika bar wani ya lalata tarbiyar da s**a yi miki.

Ƴar uwa! Da wana idon zaki kalli wanda yazo yana ƙaunarki da gaske har ya aureki bayan duk kin bar wani a baya ya gama lalata miki jikinki..!?

Kin san wani abu, mafi yawan matan da s**a bar saurayi ya yi wasa da jikinsu sun fi kowa wahala a lokacin da aka bar su, sun fi kowa yawan damuwa da kuma shiga baƙin ciki.

Lokacin d kika bar saurayi y gama biyan buƙatarsa; ina mai tabbatar miki ji yake a jikinsa takalamin ƙafarsa ya fiki darajar.

Ƴar uwata! Ki kiyaye kan ki da mutuncinki sai ƙima da kuma darajarki ta ƙaru.

Macen da tafi kowacce jan hankalin namiji ita ce wacce ta kame kanta kuma ta kiyaye mutuncinta.

Ƴar uwa! Kin taba ganin wanda ya ce, Fasiƙa yake son aure...!? Amma kowa mai mutunci yake nema!
Imam Hafiz

16/10/2023

!

Ki kiyayi shan abin kara kiɓa domin yana kokarin zamo wa abin zargi a yau, ke da kika kasance nutsassiya, kiyi hakuri ko kina sha ki daina ki godewa ALLAH a matsayin da ya yi ki, in ba haka ba za ki ja wa kanki babban matsala musamman ta fuskar mutunci da kuma auruwa

Akwai yanmata da ba nutsassu ba s**anje su sha magani ko sanya abin hana ɗaukar ciki robar hannu, to wai yana sanya wasu jiki, shine sai yarinya tayi jiki ayi ta mamakin me ya sanya ta jiki, ko ayi ta cewa magani tasha ashe ashe ...... Abinda yake gaskiyar magana biye biyen maza take wanda daman duk mace yarinya BUDURWA da take bin maza yanayin ta na sauyawa sosai to ga kuma in tayi planning yazo planning din tana daga cikin wa'enda yake sanyawa jiki.

Babban jan hankali ga yanmata masu irin wannan halin su ji tsoron ALLAH suna tuna mutuwa, yanzu har zamani ya kai yarinya ta zamo har da planning, ? Wannan musiba ce.

Abu na biyu yanmata wa'enda su ba aikata aikin banza suke ba ku ji tsoron ALLAH ku rufawa kanku asiri, in ba ki sha kada ki sha, in kina sha kidaina don yana da illa sosai ga lafiya, sa'annan kuma yanzu magana ta canja salo ke watakila ba ki daga cikin yanmata masu Ɗabi'ar yawon banza, maganin kiɓa kika sha azo ana zargin ki, ana bata miki suna.

Daga karshe ina jan hankali ga iyaye, yayyu, da yan uwa musulmi mu ji tsoron ALLAH muna kulawa da amanar ya'yan mu da kannai, da yan'uwa musulmi.

Maza kuma aji tsoron ALLAH, a daina shigar da ya'yan mutane harkar banza don wata sanadin lalacewarta daga yaudara ce, ku kuma mata adaina kwaɗayi da ɗaukar wa kai Rayuwa ta karya, a kame kai a fuskanci abinda zai amfanar da rayuwa a cire kwaɗayi da buri ayi aure, sai na canja waya ko sanya sutura da sauran kwaɗayi shi ke hallakar da mata, babu nutsuwa ko kwanciyar hankali da tunani mai kyau ga duk wanda ya auka irin Mummunar Ɗabi'ar nan

DUBA_COOMENT_NA_FARKO_DOMIN_SAURAN_BAYANI..👇👇

12/10/2023

Faman Ada'ahu Dakhalal Jannah ☑️🌴🍏🍍
Waman Asani Dakhalan nari 🔥💥

Duk Wanda yabi Manzon ALLAH S A W ♥️♥️ zai shiga Aljannah

Duk Wanda yasaba Masa zai shiga Wuta 🔥

ALLAH kabamu ikon yiwa Annabi'Da'a 🙏

12/10/2023

Tsakani Biro Da Bindiga Wane Yafi Cutar Da 'Yan Najeriya.......?

Photos from Ælhãjï karami emir's post 11/10/2023

الْحَمْدُ لله الذي بنعمته تتم الصالحات!!!
ALLAH GWANIN HIKIMA!!!

Mu Al'ummar Obajana Alhamdulillah, Allah ya zaba mana jagorori na Kwarai:
-Ga Dattako
-Ga Iya Jagoranci
-Ga Sanin Ya Kamata
-Ga Son Jama'a
-Ga Son Alkhairi Ga Jama'a
-Ga Hikima Wajan Hada Kan Jama'a
-Ga Hangen Nesa
-Ga Tunani Mai Kyau

MIKIYOYI MASU HANGEN NESA!
Hikima Allah sai ya hada LATTIJON ARZIQI DA KUMA MATASHIN MALAMI. Don su yi masa aiki.

Chiarman: Mallam Muhammad Haruna Zaria
Secretary: Imam Yusuf Umar Abu U'naisa
- Sun Samar Da Masallaci
-Sun Samar Da Makarantar Islamia
-Sun Samar Da Makarantar Boko
Yanzu kuma ga clinic sun fara project din ta.

Muna taya ku addu'a Lattijon Arziki Da Matashin Malami Allah ya taimakeku ya cika maku gurin ku na ganin wannan clinic din ta samu ga al'umma. Ãmeen Yaa Hayyu Yaa Qayyuum.

✍️Abu JA.AFAR

10/10/2023

Last 2 weeks Malam Ahmad Tijjani yayi magana akan Maulidi, bayan karatun akwai wasu ƴan ɗariƙa da s**ayi ta haushi da sunan Raddi, Sai waɗannan Munafukan da suke neman kuɗi da rikicin Malamai a blogs da YouTube channel nasu, s**ayi ta Turumun Raddin da akayi wai na Turawa Malam yaga irin abinda ƴan ɗariƙa suke faɗa a kansa!

A raina nace waɗannan basu san waye malam ba, shi malam ai ko gidan Radio baya musu program, saboda gidan Radio su zasu tsara maka abinda suke so ka faɗa, shi kuma ba haka yake ba! Domin ko gayyatar sa wa'azi zakuyi, sai dai shi yasa lokacin da zai zo amma ba wai ku kuce ga ranar da kuke so ya zo ba.

Shi yasa zaku ga ko irin hiran nan da ake yi da malamai a BBC Hausa baku taɓa ganinsa ba, saboda shi bazaka tsara masa abunda zai faɗa ba, sai abinda ya tabbatar da idonsa.

Su iya burinsu su haɗa malamai faɗa ayi ta Raddi a daina karantar da Al'umma, a gefe guda kuma suyita samun kuɗi su barku da fama da sayan data.

Ælhãjï karami særk

Photos from Ælhãjï karami emir's post 10/10/2023

WAI WANE IRIN HADDA KABIRU GOMBE YAYIWA QUR'ANI NEH

Computer mai kwakwalwa kenan,idan kana sauraran tafseer din mallam anan zaka gane cewa mallam yayiwak qur'ani hadda ba tawasaba,
kai mallam takai ta kawo yana fassara aya da aya a cikin qur'ani ,
Kai nidai a iya sanina bansan wani malami da yake hakaba a fadin nageria,
A gaskiya mallam yayi irin wata hadda ne wanda ba kowa neh zai iya sai dan baiwa .
Ya Allah ka karawa mallam lafiya da nisan kwana ..

BY IBN SALËËS

TABBAS MALAN YANADA HADDA BA WASA 😁😁😁 KOMAI HARDAR ARAMMA ZAKAGA MALAN YA RIKITASHI CIKIN ALQUR'ANI

Photos from Ælhãjï karami emir's post 08/10/2023

State metting kenan yake gudana a garin lokoja kogi state.

Wanda State Director (F.A.G JIBWIS) Ilyasu Suleiman shi da kansa yake shugabanta, muna rokon Allah ya bashi sa'a wajan gabatar da shugabancin sa...kuma Allah ya sa a tashe taro lafiya, kuma Allah ya sa a tattauna abinda zai ci da addinin musulunci gaba. Ãmeen Yaa Hayyu Yaa Qayyuum.

✍️alhaji karami sark

05/10/2023

Idan zaki roqi miji nagari to kiroqa da Abokai Nagari Domin sune yan majalisar zartarwa!

03/10/2023

Kyakyawar😘 Magana🗣️ Mabudi🗝️ ce Takan bude🛅 zukatan💞 Masu Alheri,😊 Ta Rufe🤫 Bakunan Masharranta.🧐🤢🙄

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

Everyone @followers

Category

Telephone

Website

Address

Bauchi
Other Writers in Bauchi (show all)
Hon.maheeru.Maiwada wundi for senator b/south Hon.maheeru.Maiwada wundi for senator b/south
Rishi
Bauchi

To remain in peace and unity /justice and kindness is our hope. Mahiru remain our boss. Our ambitio

Vocation time Vocation time
Misau
Bauchi

Shafin masoyan arewa

Tongyai Groups clothes product Tongyai Groups clothes product
Dutsan Tanshi Bauchi
Bauchi, KHAMISKAKUM

Legendry😎😎

Yusuf Abubakar muhammad Yusuf Abubakar muhammad
Yakubu Wanka
Bauchi

business man

Abdull Media Abdull Media
Tilden Fulani
Bauchi

Too funny �

Usman Isah Abubakar Usman Isah Abubakar
Shop No 33 Gsm Village Wunti Market Opp Swarming Full
Bauchi

If you want to be strong learn to enjoy being Alone

NORTH concern ME. NORTH concern ME.
Bauchi

maintaining Justice and equity

Muryar Sayyid Zakzaky H Muryar Sayyid Zakzaky H
Bauchi

Instagram 👇👇 @Murayar_Sayyid_Zakzaky_H

Sarah Tawus Sarah Tawus
Bauchi

God's girl ||StoryWriter|| Volunteer|| JournalistInTraining||

The Best Home for the Tijjaniyya's The Best Home for the Tijjaniyya's
Yelwan Makaranta, BauYelwan Makaranta, AauchiYelwan Makaranta, AaYelwan Makaranta, Yelwan Makaranta Of Nigeria
Bauchi

Sufi path

Amir Khalil Amir Khalil
Bauchi

You can shut my lips but never my pen�

Darul Hikma Darul Hikma
Bauchi

Muyi karatu mu sami ilimi muyi rayuwa mai tsafta kuma mu tsira a gaban allah swt بلغوا عني ولواية