Darul Hikma
Muyi karatu mu sami ilimi muyi rayuwa mai tsafta kuma mu tsira a gaban allah swt بلغوا عني ولواية
Manzon Allah s.a.w yace kwadaitar a hadisi cewa ku nemi Daren lailatul qadri a goman karshe na watan Ramadana
Wanda a wannan dare ne ubangiji yake rubuta abun da zai wakana a shekarar gaba daya kuma a wannan Daren ne dai kuma Allah s.w.t yake ce mana Daren tafi darare dubu alheri
Akwai wani tambihi da nake son mana na wani kuskure da muke yawan afkawa a duk shekara a kan wannan dare ..
Kuskuren kuwa shine kawai sai mu Kame daga aikata nau'uka na ibadu sai lakacin tahajjaud kadai muke qoqarin ribata alhali Daren gaba daya ake so mu raya da ibadoji
Sai kaji saurayi ko budurwa na cewa Aih zamu hadu a tahajjaud tsammanin su kawai aure ko soyaiyar wani ake roqa a Daren ko kuma mu shagaltu da roqon duniya zallah mu manta da batun lahira
Tabbas addu'a ibada ce Amma so samu mu dage aiyuka na ibadu k**ar karatun qur'ani nafilfili tasbihi da shauran ibadu da s**a tabbata a sunnar ma'aiki sallallahu alaihi wa sallam in yaso in Ka qarisa ibadar kayi tawasuli da ibadar don ubangiji ya karbi taka addu'ar
Amma mu sani ba zallan addu'a bane kawai
Wani sahabi manzon Allah yace masa Ina roqon kusan ci da Kai a aljanna sai manzan Allah yace masa ka taimake ni a karan kanka da yawan sujuda
Da dare anfi son yawan raka'o'i a sallah
Nana Aisha manzon Allah ya koyar da ita Kalmar da zata na fadi in har ta hadu da Daren yace mata tana fadin اللهم انك عفو تحب العفو فاعف عني
Masu yi a masallaci in an idar da sallah ba shike Nan ba In an koma gida a ci-gaba da tasbihi da s**a ba tabbata daga bakin fiyayyen hallita .
Kamar Istigfari hailala hauqala salatin annabi D.s.s
Domin Daren na karewa ne in alfijir ya keto k**ar yanda Allah subhanahu wa ta'ala yace
سلم هي حتى مطلع الفجر
Aminci ne a cikinta har ketowar alfijir
Allah mana muwafaqa
Darul Hikima
Yace "Wallahi malam ni naga aya. Kullum sai na rabawa mutane kudi 'yan dubu dubu. Kawai bayarwa nake yi. Kuma wallahi haka kullum nake samun kudi nima.
Kawai sai wani abokina lakcara yace min gaskiya yana bani shawara na daina kyautar nan haka. Ai kuwa da na bi shawarar sa na daina bawa kowa komai. Abin mamaki, ina dainawa wallahi nima sai da na yi wata guda cur ban samu ko kwabo ba.
Sai daga baya na yi tunani na dawo da kyautar da nake yi, nan da nan sai gashi samu na ya dawo."
Muhammad mahmud
FITA TA ASHIRIN DA DAYA (21)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 41. A ina karagar iblis take?
Daga jabir dan abdullahi yace; manzon Allah(S.A.W)yace: al’arshin iblis na kan ruwa,
yana tura rundunoninsa su fitini mutane, wanda yafi daraja a gunsa shine wanda yafi
ditinan bayin Allah. Musnad 3/97
Q 42. Su wanene jakadun shaidan?
Sahidan na da manyan jakadu guda biyar, kowani da aikin da ya daura masa, gasu k**ar
haka:
-subr: shine mai zuwa wa bawa yayin da musiba ta sameshi, ya riya masa kuka da
rashin hakuri.
-Al a’awar: shine mai kawata wa bawa zina.
-Masud: shine mai riya karya.
-Dasim: shine mai hada mutum fada da iyalansa.
Zalanbur: shine mai kafa tuta a kasuwa. Ya rinka sac in riba da rantsuwan karya
da algishshu da sauransu (Akamul murjan #148)
-Abu: shine mai hana mutum rufe baki yayin hamma (adabul mufrad 397)
-Alwalhanu : shine mai hana mutum cika alwala ( jamius sagir 4780)
Q 43. Wasu abubuwa shaidan yake sawa?
Shaidan yakan sa mutum abubuwa k**ar haka:
-Munana mafarkai
-Hamma da kasala yayin ibada
Yawan hattishawa yayin ibada
-Gyangyadi lokasin ibada.
-
Darul Hikma
FITA TA ASHIRIN (20)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 39. Tarkon shaidan guda nawane?
Manya-manya cikin tarkon shaidan guda shida ne:
-Shirka da kafirci
-Aiki da bidi’a
-Aiki da manya laifuka
Aikata kananun laifuka.
-Shagaltuwa da ayyukan da basu da laifi ko zunubi.
-Shagaltuwa da ayyuka masu karamin lada, a bar masu babban lada.
Q 40. Wasu abubuwa shaidan yake anfani dasu ajen yakan mumini?
Duk wani abinda ka sani na sabon Allah ,shaidan yana anfani dashi wajen yakan mumini.
Kuma duk mai sabon Allah ,shaidan yaka samu dama akansa na ya cutar dashi. Amma duk
mai bin Allah ,shaidan yakan ji tsoron sa, k**ar yadda yake jin tsoron sayyidina umar, har
ma baya iya hada hanya da shi.
Darul Hikma
FITA TA SHA TARA (19)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 37. Suwaye aka samu Aljanu sun yi kuka a mutuwarsu?
-Abdullahi dan jud’an
Abu ubaida
-Umar dan khaddab
-Usman dan affan
-Ali dan abi dalib
-Husaini dan ali
-Umar dan abdulaziz
-Harunar Rashid
-Waki’u da jarrah
Q 38. Menene waswasi?
Waswasi shine abinda yake darsuwa zuciyar bawa. Ida daga ubangijine ana kiransa
ilhama, don na nuni ne zuwa ga alkhairi, k**ar; sadaqa, azumi, sallah da sauransu.
Idan kuma daga shaidan ne ana kiransa was-wasi, don na nuni ne zuwa ga sharri,
k**ar; sata, karya, hasada da sauransu.
Shaidan na shiga zuciyar bawa yasa masa wasu kulle-kulle, yaro ne ko babba. Kuma duk
abinda ya kulla ko da bai fada ba , mutane za su iya sani.
Darul Hikma
FITA TA SHA TAKWAS (18)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 34. Menene hukunci magani ma wanda Aljanu s**a shafa?
Wajibi ne a ceto ran wanda Aljanu s**a shafa, amma ta hanyan addu’o’I da karatun
qur’ani, amma haramun ne ayi haka ta hanyan tsafi.
Q 35. Wasu irin cututtuka Aljanu suke iya sabauta wad an adam?
Aljanu suna iya sabauta wa ‘yan adam cututtuka k**ar haka:
-Annoba
-Jinin siwo ga mata
-Bakin launi a fuska.
Da sauran cututtukan da bokaye s**a umarce su, ko su a karan kasu s**a yi nufin
utar da wani.
Q 36. Shin ya halatta a tambayi Aljani wani abu?
Shibli yana ganin za a iya tambayan Aljani abinda ya wuce da abinda ake ciki, amma ba
za a tambaye shi abinda zai zo ba.
Kuma ya zama da sharadin ba biyansa za a yiba
Darul Hikma
FITA TA SHA BAKWAI (17)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 32. Shin Aljanu suna iya zama a cikin jikin wanda s**a shafa?
Sashin malamai cikin mu’utazila suna ganin Aljani baya iya shiga jikin mutum.
Wasu malamai kuma suna ganin Aljanu suna iya zama a jikin wanda s**a shafa, duba da
dalilai k**ar haka:
-Wata mata ta kawo danta wa Annabi(S.A.W)tace hauka na damunsa, sai Annabi
yayi addu’a ya shafi kirjinsa sai yayi aman wani bakin abu.
A hadisin abi dauda Annabi yace, fita abokin gaban Allah, nine manzon Allah
(S.A.W).
-Fadin manzon Allah(S.A.W)shaidan yana gudana a jikin daya daga cikinku k**ar
yadda jini yake gudana jikinsa.
Q 33. Shin maganganu da ayyukan wanda Aljanu s**a shafa nasa ne ko na Aljanun ne?
Imam ahmad yana ganin magan-ganunsa daga Aljanin ne, wasu malaman suna ganin
aikinsa ma daga Aljanine. Saboda haka:
In yayi saki bata yiba, haka in ya saya ko ya sayar ko yayi kyauta.
-In yayi kisan kai baza’a kasha shi ba amma zai biya diyya.
-In ya lalata dikiyar wani zai biya.
-In bai yi sallah ba ko azumi baya da laifi amma zai biya.
Darul Hikma
FITA TA SHA SHIDA (16)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 31. Me ake nufi da shafan Aljanu?
Aljanu s**an iya cutar da mutum ta hanyar shafansa, k**ar yadda dan uwansa mutum
ma zai iya. Aljanu s**an shafi mutum saboda dalilai k**ar haka:
Ramako: idan mutum ya cutar da Aljani da ganganko a rashin sani, s**an iya
ramawa, kuma galibi s**an rama ne da sama da abinda aka musu.
-Jahilci: galibin Aljanu suna da jahilci, saboda haka suna iya cutar da mutum koda
bai musu komai ba.
Mugunta da hassada: galibin Aljannu suna jin haushin mutane, saboda mutane ne
s**a maye gurbinsu a duniya, s**a Aljanu s**a koma duwatsu da ruwaye, s**a
kuma cigaba da cin taroso da kasha.
-Wasa: k**ar yadda wani cikin mutane zai iya dukanka ko ya mareka matsayin
wasa, haka ma wasu cikin Aljanu za su iya ma.
-Soyayya: wasu daga cikin Aljanu za su iya raban mutum har su cutar da shi da
sunan soyayya.
-Biyayya ga wani: Aljani zai iya cutar da wani saboda umarni da aka masa daga
wajen boka ko wani Aljani na sama da shi.
Darul Hikma
FITA TA SHA BIYAR (15)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 29. Me yasa shaidanu suke halarta in anyi kulumboto?
Shaidanu cikin Aljanu suna jin dadi in anyi shirka, an keta alfarman musulunci. Saboda
haka suke bawa bokaye wasu kalmomi na zagin Allah don su rinka fada, ko kuma su
ambaci sunansu yayin bukata, a maimakon sunan Allah. Wannan yasa suke bada
kulumboto (Ahkamul murjan #85)
Q 30. Shin Aljanu suna sakawa in an musu kyakkyawa ko mummuna?
An samu ruwayoyi da yawa da uke nuna cewa Aljanu suna sakayya da kyakyyawa yayin
da aka faranta musu, kuma suna sakayya da mummuna yayin da aka bakanta musu.
Darul Hikma
Masu ganin cewa mata su zauna a gida cewa Hakan gidadanci ne ko tauye wa mata haqqi ne sai ku nuna mana su wadanda kuke koyi dasu din shin sun yarda mace ta jagorance su ne ko qaqa
mace fa ta zauna a gidan miji nan ne filin gwagwarmayar ta nan ne jihadin ta nan aljannar ta take
Mu musulmai ne kuma addinin mu nada tsari ba kara zube muke rayuwa ba muna da kundi wanda shi yake mana nuni ko hani akan me zamu yi ko me zamu bari
Allah swt yace a cikin alqur'ani suratul ahzab aya ta 34 " وقرن في بيوتكن ولا تبرجن تبرج الجاهلية الأولى واقمن الصلاة وءاتين الزكاة واطعن الله ورسوله انما يرد الله ليذهب عنكم الرجس..... cewa ku zauna a gidaddajin ku ,kada kuna fita irin fita na jahilan farko ,Kuma ku .tsai da Sallah ku bada zakkah Kuma kubi Allah da manzon sa ,Allah na nufin ya tafi da datti "zunubai "Kuma ya tsarkake ku tsarkakewa ,
Wannan ayar ababen da take magana akai shine fitan mata ranbatsau suna fita da ado da sanya turare..
Wanda hakan ka bayu ga yada barna a ban kasa
Sai Allah yake kuma umartan matan mu da cewa to fa su tsai da sallah da bada zakkah kuma subi Allah da manzon sa s.a.w wanda wannan shine hanyar tsira gare su ba wancan mummunanr hanya ba ta .wadanda s**a gabaci matan mu wadanda basa da addini kuma ba ilimi a tare dasu
Allah yake cewa a suratun Nur " ولايبد ين زينتهن الا ما ظهر منها "
Kada su baiyana adon su sai abun daya baiyana daga ciki (fuska,tafukan hannuye ) shima hakan in an aminta da fitina
Wannan shine matsaya tabbatatta a musulunci wanda du mai nemar hanyar tsira ta lizimci umarnin Allah wanda kuma yake da mata ko ya a karkashin sa to aiki ya same shi wajen tabbatar da umarnin Allah iya qarshen karfin sa
Darul Hikma
FITA TA SHA HUDU
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 27. Shin Aljanu suna tsoron mutane.
Lallai Aljanu suna tsoron mutane. Imam mujahid yace; Aljanu suna tsoron mutane k**ar
yadda mutane suke tsoron su, don haka in sun bijiro wa mutum kar ya gudu.
Q 28. Shin qur’ani na tasiri wajen Koran Aljanu?
Alqur’ani na qona shaidanun Aljanu ya kore su koma ya kashe su, amma muminai cikin
Aljanu har truruwa sukeyi domin sauraron alqur’ani. (Ahkamul murjan #84)
Darul Hikma
FITA TA SHA UKU (13)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 25. Shin Aljanu suna iya saw a mutane hikima da waqoqi a bakinsu?
An samu ruwayoyi da yawa da suke nuna hakan, kuma hankali baya kore hakan, k**ar
yadda s**a fadi wadu jumloli kuma aka sanya su a al’qur’ani. (Akamul murjan #72)
Q 26. Shin Aljanu suna iya koya wa mutum likitanci?
Ibn abid dunya ya kawo riwayoyi da yawa cikin littafinsa na “alhawatif” wanda suke
nuna cewa Aljanu suna sanar da mutane magun-guna. Daya daga cikin riwayoyin nada
kyakkyawar salsala. Don haka ya halatta Aljanusu sanar da mutum magunguna amma
da sharruda k**ar haka:
Ya zama maganin yardajje ne a shar’ance, k**ar ganye, fure, saiwa, sassake da
sauransu.
-Ko kuma ya zama ayoyi ne da tabbatatun hadisai daga Annabi(S.A.W)
-Ya zama ba a biyansu kan abinda suke yin a taimako, domin galibin abinda suke
nema kafirci ne.
-Ya zama maganin bai kunshi fadan wasu kalmomin da ba’a san ma’anasu ba, ko
yanka ko sadaka ko wasu abubuwan da suke k**a da sihiri.
Darul Hikma
FITA TA SHA BIYU (12)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 23. Mene hukuncin matan da Aljanus**a sace mijinta ?
A zamanin sayyidina umar Aljanusun sace wani mutumi da matarsa ta fada masa sai
yace ta jira na shekaru hudu, bayan shekaru hudu yasa tayi aure.
Q 24. Shin Aljanusuna iya karban ilimi daga mutane?
An samu ruwayoyi daga malamai da yawa,k**ar su abubakaril qurashiy suna cewa;
Aljanus**an halarci majilisan ilimi na mutane, harma suyi tambayoyi. Sannan suna iya
fito wa mutum da wata sura su masa wa’azi.
Darul Hikma
FITA TA SHA DAYA (11)
TAMBAYOYI ARBA'IN (40) DA AMSOSHINSU AKAN ALJANU
Q 21. Shin mata-maza ‘ya’yan Aljanune?
Abdullahi dan abbas yace; mata-maza ‘ya’yan Aljanune. ana samunsune in mutum ya
kwanta da matarsa tana haila (Akamul murjan #66)
Q 22. Shin Aljanusuna iya sace mutum?
Lallai Aljanusuna iya sace mutum, kuma an samu hakan da yawa a baya, tun daga
zamanin sahhabbai.
Darul Hikma
FITA TA GOMA (10)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 19. Menene hukuncin auren Aljani ko Aljana?
Sashin malamai suna ganin zai yiwu mutum ya auri Aljana ko mace ta auri Aljani, sannan
har su iya haihuwa, don ana ruwaitowa cewa daya daga cikin iyayen balkisu Aljanne.
Sai dai mafi yawan tabi’ai sauna ganin makaruhi ne, a’amash da imamu malik suna ganin
ba laifi (Akamul murjan #59 –64)
Q 20. Shin Aljani na iya jima’I da mace?
Malamai sun tabbatar da cewa Aljani na iya zuwa ya sadu da mace kuma har taji dadi
k**ar yadda na miji yake iya zuwa ya sadu da ita. Sai dai akwai maganganu biyu akan
cewa wanka ya wajaba akanta ko bai wajaba ba. To amma In tayi inzali ya wajaba
(Akamul murjan #60)
Darul Hikma
FITA TA TARA (9)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 17. Shin Aljani na yanke sallan mai sallah in yabi ta gabansa?
A hadisin abi zarri yace Annabi(S.A.W)yace: bakin kare yana yanke sallan mai Sallah
idan baya da sitra, saboda shaidani ne. (tirmiziy 338)
Q 18. Shin ya halatta mutum ya kashe Aljani?
Bai halatta mutum ya kasha Aljani ba sai dai da wani dalili mai karfi, k**ar jin tsoron
cutarwansa.
A hadisin abi sa’id yace Annabi(S.A.W)yace: “ a madina akwai wasu Aljanu da s**a
musulunta, in kuka ga wasu dabbobi (macizai da sauransu) ku musu Magana na kwana
uku, in kuka sake ganinsu to ku kashesu. (muslim 141, abu dauda 5256)
An ruwaito daga nana aisha cewa ta kashe wani maciji a dakinta, daga baya ya bayyana
mata cewa musulmin Aljani ne, sai tabiya dirhami 12,000 a matsayin diyya. A wasu
ruwayoyin kuma ta ‘yanta bayi hudu.
Darul Hikma
FITA TA TAKWAS (8)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 15. Shin an daura wa Aljanu ibada?
An daura wa Aljanu ibada, duk da ba manzanni a cikinsu amma an daura musu biyya wa
manzannin cikin mutane gwargwadon ikonsu da yanayin jikinsu. Don haka cikinsu akwai
muminai da kafirai. Muminai zasu shiga Aljannah, kafirai kuma su tafi wuta.
Q 16. Shin za a iya bin Aljani sallah?
Abul biqa’I al’akbariy yana ganin za a iya bin Aljanis sallah, saboda shima mukallafi ne.
kuma shar’ar Annabi Muhammad (S.A.W)yake bi. (Akamul murjan #54)
Darul Hikma
FITA TA BAKWAI (7)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 13. Da wani hannu shaidan yake ci da sha?
Shaidan yana ci ko sha ne da hannun hagu, a hadisin abdullahi dan umar Annabi(S.A.W)
yace: “kar dayanku yaci da hagu, kar ya sha da hagu, domin shaidan yana ci yana sha da
ita. Muslim 106.
Q 14. Shin Aljanu suna aure?
Lallai Aljanu suna aure, shibliy ya kawo cewa, Aljanu suna aure suna jima’I da matansu,
kuma suna haihuwa. (Akamul murjan #33)
Darul Hikma
FITA TA SHIDA(6)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q 11. Yaya mutum zai yi yafi karfin shaidaninsa?
Mutum zai iya fin karfin shaidaninsa ne ta hanyan lura da abubuwa k**ar haka:
-Addu’a, Annabi(S.A.W)ya kasance idan zai yi barci ya kance: “ ya Allah da
sunan ka na kwanta, ina neman tsari daga sharrin shaidanina. (Abu Dauda 5054)
-Yin bisimillah yayin ayyuka.
-Yin addu’a yayin shiga bayan gida da wuraren najasa.
-Yawaita ayyukan alkhairi.
-Zama cikin tsarki.
Q 12. Shin Aljanu suna ci ko sha?
Lallai Aljanu suna ci kuma suna sha. Abu ya’ala yace: Aljanu suna ci kuma suna sha kuma
suna aure k**ar yadda muke yi. A hadisi Annabi(S.A.W)yace; duk kashin da aka ambaci
Allah yayin cin sa to zaku same shi a nama (wato Aljanu) muslim 150.
A hadisin abi huraira Annabi(S.A.W)yace na roki Allah duk wani ka sha ko taroson da
Aljanu s**a wuce su samu abinci akai.
Darul Hikma
FITA TA BIYAR (5)
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q9. Menene yake Koran Aljanu daga waje?
Yawan ambaton Allah a waje. Muslim da abu dauda sun rawaici hadisi daga anas yace:
“idan dayan ku ya shiga gida ya ambaci Allah a wajen abinci da wajen bacci, shaidan zaice
wa ‘yan uwansa; baku da abinci, baku da makwanci………. (muslim 103 abu dauda 2765
ibn majah 3887)
Q10. Shin da gaskene kowane dan adam an hada shi da shaidani?
Da gaskene kowani dan adam an hadashi da shaidani. A hadisin abdullahi dan mas’ud
yace: “ babu wani a cikinku face an hada shi da abokin zama cikin Aljanu, da daya cikin
mala’iku” (muslim 69)
Darul Hikma
FITA TA HUDU (4)
TAMBAYOYI ARBA'IN AKAN ALJANU
Q7. Shin Aljanu suna rikida?
Abu ya’ala yace: Aljanu basu iya canza halittarsu gaba daya, sai dai Allah ya basu wasu
kalmomi da wasu ayyukan da idan s**ayi za su bayyana da wata sura, k**ar kare, kule,
maciji da sauransu.
Kuma rikidan yafi samuwa daga matsafa daga cikinsu, k**ar yadda sayyidina umar ya
fada, kuma yace in an gansu ayi kiran saAllah. (Akamul murjan #25)
Amma Aljannu basu yawan rikida, saboda in sun bayyana da sifar wata dabba, duk
abinda ya samu wannan dabban su ya samu.
Q8. Ina ne mazaunin Aljanu?
A hadisin bilal Annabi(S.A.W)yace musulmai cikin Aljanu da mushrikai sun yi husuma,
sai nabar musulmai a birane, mushrikai kuma a duwatsu da tekuna. Dala’ilun nubuwwa
542. Shibliy yace; ana samun Aljanu a wuraren najasa da bayan gida da bola da
sauransu. (Akamul murjan #28)
Darul Hikma
FITA TA UKU (3)
TAMBAYOYI ARBA'IN (40) AKAN ALJANU
Q5. Me yasa ba’a ganin Aljanu?
Abdullahi dan abbas yace: lokacin da Allah ya halicci baban Aljanu, sai yace masa ka roki
wani abu, sai yace; ina rokon mu rinka gani amma mu kar a ganmu, kuma mu rinka iya
buya a cikin kasa, kuma wanda ya tsufa a cikinmu ya iya dawowa saurayi. (Akamul
murjan #15)
Q6. Nau’o’in Aljanu guda nawa ne? Suhaili yace" Aljanu nau’I uku ne, k**ar yadda yazo a hadisi; wasu suna kan suran
macizai, wasu kuma suna kan suran karnuka, wasu kuma iskokai ne, suna da fiffiken da
suke tashi da shi (Akamul murjan #21)
Darul Hikma
FITA TA DAYA
TAMBAYOYI ARBA'IN (40) DA AMSOSHINSU AKAN ALJANU
Q3.Meye bambanci tsakani Aljanu da ruhanai da iskokai da ‘yan gwai-gwai?
Ibn abdilbarri(Rahimahullah)yace: idan masana larabci s**ace Aljani, suna nufin asalin
Aljani wanda bai siffantu da wata sifa kyakkyawa ko mummuna ba. Masu bijiro wa yara
kuma (ko a siffan yara) su ake kira iskokai ko ‘yan gwai-gwai. Masu cutarwa kuma sune
shaidanu, wanda s**a gawurta kuma sune ifritai
Q4. Menene tarihin halittan Aljanu?
Ubangiji ya halicci Aljanu daga tartsatsin wuta, sunan babansu (Sumiya) sun zauna a kan
kasa shekaru dubu biyu suna bauta wa Allah, daga baya s**a kashe jagoransu mai suna
yusuf, s**a cigaba da sabo da zubar da jinni. Sai Allah ya turo musu ma;a’ikun sama ta
daya karkashin jagorancin iblis da mayaka dubu hudu, s**a korasu tekuna da duwatsu.
(Akamul murjan #15)
Darul Hikma
FITA TA DAYA
TAMBAYOYI ARBA’IN
(40) DA AMSOSHINSU
AKAN ALJANU
Q1. Shin da gaske akwai Aljanu?
Da gaske akwai Aljanu, Ibn Taimyya (Rahimahullah)yace:babu wani cikin tawagan
musulmai da yake karyata samuwan Aljanu, sai dai wasu tsiraru cikin kadariyya da wasu
dayawa cikin falasifa da zindikai. Har ma yahudawa da nasara sun yarda da samuwan
Aljanu. (Akamul murjan #12)
Q2. Me yasa ake kiran Aljani da sunan Aljani?
Ibn Duraid(Rahimahullah)yace: ana kiransu Aljanune saboda ba’a ganinsu, shi yasa ma
a jahiliyya suke hada mala’iku da Aljanua matsayin abu daya. Shiyasa ma ake kiran
jaririn da ke ciki da “Aljanin” saboda ba’a ganinsa. Kuma ake kiran garkuwa da “junnah”
saboda na suturce jiki. (Akamul murjan #13)
Darul Hikma
Rufewa
Muna wani lokaci da sihiri yayi yawa atsakanin al’umma
talakawa da masu kudi ‘yan siyasa da‘yan kasuwa,
masarauta da fadawa, ‘yan mata da samari ………..
Yana da kyau mu gane cewa Allah shi yake bada komai,
sihiri bayabada komai duk abinda ba’a sameshi ta hanyar
Allahba to bazai yi albarkaba.
Kuma Mugane cewa, galibin bokayenmu a yau basu iya ba.
‘yan danfara ne kawai. Zasu iya ma aiki, kuma yakoma
kanka.Mata da yawa sunyi sihiri wa mijinsu ya tsani kowa saisu,
a karshe suma ya tsnesu kuma ya sake su!.
Ya jama’a mu koma zuwa ga Allahda ya samar damu daga
babu, ya azurta mu a mahaifan iyayenmu. Mu saki komai
wa ubangijinmu, mai tausayi ne, mai karaban tubane.
Iya abinda Allah ya nufe mu da rubutuwa kenan. Ina fatan
Allah ya shiryar da duk wanda ya karanta ko ya saurari
wannan littafin.
Darul hikma
FITA TA ASHIRIN DA HUDU (24)
Tsoratarwa daga sihiri.
Saboda mummunan illan da sihiri yake da shi a cikin al’umma,
addinin musulunci yayi gargadi akansa a hadisai k**ar haka:
-Sihiri na daga cikin laifuka masu halakarwa:daga Abu
Huraira, ManzonAllah(S A W) :yace ku nisanci abubuwa
bakawai masu halakarwa. S**a ce wadanne ne;yace :
shirka da sihiri.
-Daga Imrana Dan Husaini, Annabi (S A W) Yace : baya
tare da duk wanda yayi canfi ko aka masa, ko yai duba ko aka masa, ko yayi tsafi ko aka masa. Bazzar ne ya
ruwaito
-Daga Jabir dan Abdullah, manzon Allah(saw) yace: duk
wanda yaje wajen dan duba ya gaskatashi a
maganarsa, to ya kafirce daga abinda aka saukar wa
Annabi Muhammadu (S A W) in kuma bai gasktashi ba,
baza’a karbi sallansa ba na kwana arba’in.
-Daga Abidarda’i, manzon Allah(S A W) yace: ba zai samu
darajoji madaukaka ba; wanda yayi bokanci ko duba,
ko ya fasa tafiya saboda canfi.
-Daga Abi Musa, Manzon Allah(S A W): mai shan giya da
mai imani da sihiri da mai yanke zumunci bazasu shiga
Aljanna ba.
Darul Hikma
FITA TA ASHIRIN DA UKU (23)
Fa’ida
Ga mutumin da ake tunanin za a iya sace shi, yaro ko babba. A
samu kaucin kuka, a nika, a sa a ruwa ludayi daya, sai mutumin ya
rinka sha. Ko mutanen gida gabadaya.
Fadakarwa
Idan ciwo yaki karewa, kuma an gwada ba mayu bane, amma
ana zaton matsalan rayuwa ne kawai, to asamu:
Gabaruwa, habba, hulba, magarya, zagargade. A hada a dafa,
mara lafiyan yayi wanka da shi, kuma ya sha.
Darul Hikma
FITA TA ASHIRIN DA BIYU (22)
2.A samu saiwan dusha, a sa a ruwa ya kwana.
-Sai a dauki Sai a hada arinka hayaki dashi. dushan a cikin gidan koyin kazan.
-Sai a daura a gaushi, ruwan yayi zafi.
-Sai a zuba garin tuwo acikin ruwa a tuka
-Sai abawa mara lafiyan yaci.
3.A samu Albasa, Ruwa,Da Gishiri dan kadan. Asa a Kwarya
ko kwano.
-Sai mara lafiyan yasa hannun sa a cikin ruwan
-Wani a gefe ya rinka karanta ayatul kursiyyu
-In yanayin mara lafiyan yacanja ta hanyan bari, ko yayi
kokarin cire hannun sa a ruwan, to mayu ne. sai a rike shi,
a cigaba da karatun.
-Bayan an gama, sai ya cire hannun sa, a bashi Albasar
yaci kadan, sannan ya sha ruwan ma kadan.
-Sai ya dauki sauran ruwan yayi wanka dashi a waje mai
tsarki. A yi haka na kwana bakwai ko fiye.
4.A samu Saiwan Tunfafiya, Ciyawar Makasa, Ciyawarda ta
tiro a kan gidansama. Turaren da a ke kira “kanfani”,
turaren Wardi da Jan Miski.Sai a hada arinka hayaki dashi.
Darul Hikma
FITA TA ASHIRIN DA DAYA (21)
Alamar cutar maita.
Mutumin da ake zaton cutarsa maita ce, ko mayu ne s**a
k**a shi, za a masa gwaji don a tabbatar. Yanda ake gwajin
shine:
A samu:
-Jan al’garib (‘ya’yan lamsur)
-Ganyen tsamiya
-Tafarnuwa.
Sai a nika su su zama gari, sai a jika a ruwa. Mara lafiyan yasa
hanunsa a ciki ya wanke, in mayune s**a k**ashi, to hanun zai
rinka yauki k**ar ansa karkashi. In kuma ba mayu bane, to
bazai yi yauki ba.
Idan ta tabbata mayu sun k**a mutum, to ga magun-guna da
za’a iya masa:
1.A samu:
-Saiwan tunfafiya-Koyin kazar gida
Sai a hada a dafa, a bare koyin a bashi yaci. Bawon koyin kuma
da sauran saiwan a nika yazama gari, sai a rinka barbadawa a
kunu ko abinci mara lafiyan ya rinka ci.
Darul Hikma
FITA TA ASHIRIN (20)
Maita da mayu(cultism)
Maita wata hanyace da Dan’adam yake bi don cimma wata
bukatarsa ta hanyan zubardajini. Aljannu da shaidanu su suke
bada sharadin zubar da jinin.
Mayun s**an fara da razanin wanda za su kashe a mafarki,
sannan su sa masa rashin lafiya sannan su cigaba da razaninsa
a bacci da farke.
Mayu s**an shiga maita saboda:
Son samun Mulki, Kudi, Sarauta, Daukaka, Sanuwa, Farin Jini,
Tsawon Rai Da sauransu.Wasu mayun kuma zallan mugunta ce take sasu maita, ba da
daya daga cikin dalilan da muka ambata ba.
Darul Hikma
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Rishi
Bauchi
To remain in peace and unity /justice and kindness is our hope. Mahiru remain our boss. Our ambitio
Shop No 33 Gsm Village Wunti Market Opp Swarming Full
Bauchi
If you want to be strong learn to enjoy being Alone
Yelwan Makaranta, BauYelwan Makaranta, AauchiYelwan Makaranta, AaYelwan Makaranta, Yelwan Makaranta Of Nigeria
Bauchi
Sufi path