Gimbiya TV

Jaridar Gimbiya jarida ce mai tsage gaskiya komai ɗacinta ga al'umma da kuma kawo ingantattun labari

21/11/2023

A ranar Lahadi ne, ofishin kakakin Majalisar wakila na tarayyar Najeriya Honourable Dr. Tajudeen Abbas(Dan iyan zazzau), karkashin kulawar Mai bashi shawara na musamman kan Harkakokin Matasa Hon. lamir Umar s**a gudanar da taron Wayar da kan daliban makarantun sakandare a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, game da illar ta'ammuli da miyagun kwayoyi.

Photos from Gimbiya TV's post 20/11/2023

Leonel Messi ya saka jesinan shi guda shida da ya buga gasar ƙwallon duniya a kasuwa domin siyar da su.

Messi ya ce idan aka siyar da jesunan zai miƙa kuɗin ga asibitin kula da yara na Barcelona, inda aka yi jinyar shi lokacin da yake da matsala.

Photos from Gimbiya TV's post 19/11/2023

Kotun Ɗaukaka ƙarar zaɓe ta kori gwamnan Filato mai ci Caleb Mutfwang na Jam'iyyar PDP tare da umartar INEC ta miƙa shaidar lashe zaɓe ga Nentawe Yildwada na Jam'iyyar APC

18/11/2023

VIDEO: Haɗakar Ƙungiyar Musulmi Ƴan Jam'iyyar PDP a Filato Sun Yi Kira ga Kotun Ɗaukaka Ƙarar zaɓe da ta yi Adalci Wajen Tabbatar da Caleb Mutfwang a Matsayin halastaccen Gwamnan Filato a Hukuncin Yau.

17/11/2023

Cikakken Jawabin Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf akan Hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙarar zaɓe na yau

16/11/2023

WATÁ SABÚWA: mutane na cigaba da ragargazar dakataccen ɗan film ɗinnan da hukumar tace fina-finai a Kano ta dakatar mai suna Malam Ali na kwana Casa'in.

Me zakù cè?

Photos from Gimbiya TV's post 12/11/2023

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa Jeddah domin k**a hanya zuwa Makkah domin gabatar da Ummara.

12/11/2023

JIRA YA ƘARE...

FATAKE SEASON 2

Zai fara zo maku daga ranar 12th November 2023 In Shaa Allah a tashar GASKIA TV PLUS.

*Lokacin nunawa*
Duk ranar Lahadi 8pm Ghana, 9pm Nigeria

*Lokutan Maimaitawa*

-Lahadi 11:30pm Ghana, 12:30am Nigeria

- Litinin 7am Ghana, 8am Nigeria

-Talata 7pm Ghana, 8pm Nigeria

- Laraba 5pm Ghana, 6pm Nigeria

- Asabar 12:30pm Ghana, 1:30pm Nigeria

Producer - Umar Uk

Director - YaseenAuwal

KBeautiful Actres with and also known as in movie📽📺??







'sBest

Photos from Gimbiya TV's post 12/11/2023

SAMANJA MAZAN FAMA AN KOMA GA ALLAH

Allah yayi rasuwa wa Alhaji Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja. Ya rasu a daren jiya yana da shekaru 81 bayan jinya da yayi fama da ita.

Tuni an yi mishi jana'iza da safiyar yau a gidansa dake hanyar Aduwa Costain Quarters, Kaduna.

Allah jikansa da rahama ya sa Aljannah ce makomarsa da mu baki daya.

10/11/2023

Shirin FATAKE SEASON 2

Zai fara zo maku daga ranar 12th November 2023 In Shaa Allah a tashar GASKIA TV PLUS.

*Lokacin nunawa*
Duk ranar Lahadi 8pm Ghana, 9pm Nigeria

*Lokutan Maimaitawa*

-Lahadi 11:30pm Ghana, 12:30am Nigeria

- Litinin 7am Ghana, 8am Nigeria

-Talata 7pm Ghana, 8pm Nigeria

- Laraba 5pm Ghana, 6pm Nigeria

- Asabar 12:30pm Ghana, 1:30pm Nigeria

Producer - Umar Uk

Director - YaseenAuwal

KBeautiful Actres with and also known as in movie📽📺👈







'sBest

Photos from Gimbiya TV's post 08/11/2023

Muna tallata muku Frames na siyarwa masu kyau da inganci.

Ko wanda yake buƙatar a yi masa, za a yi masa duk irin wanda yake so.

Ga lambar da za a kira ko a tuntuɓa ta whatsapp 08092258331

07/11/2023

Tattaunawa da shugaban ALGON na bangaren jam'iyyar APC a jihar Filato, Miskoom Alex Naatuam, game da rikita-rikitar shugabancin kananan hukumomi tsakaninsu da gwamnatin PDP mai ci a jihar.

03/11/2023

Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun yi cikakken bayani game da ƙwace kujerun su da kotu take yi a jahar Filato tare da tabbatar da cewa za su shiga zaɓen da kotu ta bada umarnin sake wa

03/11/2023

Kwamandan Hukumar Hisbah, Malam Aminu Daurawa Zai Gana Da Ƴan Tiktok Na Jihar Kano

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Nijeriya kuma shugaban hukumar Hisba ta jihar Kano Sheikh Imam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa na gayyatar ƴan Tiktok zuwa hukumar Hisbah da ke kan titin Sharaɗa Kano.

Ana gayyatar ƴan Tiktok din ne domin zama na musamman da Sheikh Daurawa zai yi da su a ranar litinin da misalin ƙarfe huɗu na yamma.

Wannan gayyata ba za ta rasa alaƙa da ƙoƙarin da hukumar ke yi ba na daƙile ayyukan ɓarna da baɗala a jihar Kano ba, wanda manhajar Tiktok manhaja ce da jama'a ke ƙorafin tana lalata tarbiyya.

Daga Imam Aliyu Indabawa

03/11/2023

Rundunar sojin Najeriya da hukumar DSS sun yi nasarar dakile wani harin Boko Haram a Kano.

Photos from Gimbiya TV's post 02/11/2023

Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Ya Dawo Gida, Bayan Kammala Wata Ziyara A Birnin London

Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar Ya Kai Ziyara Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari Bayan Ya Dawo Gida Daura Daga Wata Ziyara Da Ya Kai Ƙasar Burtaniya.

02/11/2023

Dr. Zakir Naik Ya Ba Falasɗinawa Kyautar Miliyan 380

Ya shaida haka ne yau a wajen taron karatun da ake gabatarwa a Sokoto inda ya ce

"Wasu 'yan siyasa guda biyar sun ɓata min suna, kuma na shigar dasu 'kara a kotu. Mun sasanta da huɗu daga cikin su, amma na biyar ɗin kam na ki amincewa mu sasanta. Bayan tsawon lokaci ana Shari'a, yau da safe, 2 ga watan November, an yanke hukunci. Alkali ya umarce shi ya biya ni kuɗi akan ɓata min suna da yayi, kuɗin idan an canza su zuwa kudin Nigeria, suna dai dai da Naira miliyan ɗari uku da tamanin da uku! Ku shaida na sadaukar da kudin ga Falasɗinawa. Ba na buƙatan ko sisi a ciki!"

Bawan Allah, Allah ya biya ka, ya karba maka aiyukan ka, ya 'kara daukaka fiye da yadda Makiya suke zaton ka kai.

01/11/2023

Gadi nake yi domin ciyar da iyalina, a gadin ma an sallame ni saboda na tsufa - Cewar Tsohon Direban Buhari na gidan Soja

31/10/2023

Gadi nake yi domin ciyar da iyalina, a gadin ma an sallame ni saboda na tsufa - Cewar Tsohon Direban Buhari na gidan Soja

Sajan Ali Mai Anguwa wanda ake yiwa laƙabi da Ɗan Borno ya shaidawa Zinariya haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi a gidansa da ke Bauchi.

"Na tuƙa tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari tsahon shekaru 5 lokacin da yake gidan soja. Bayan shi na tuƙa TY Ɗanjuma, Domkat Bali, Garba Duba da sauran manyan sojoji"

Sajan Ali Mai Anguwa ya shaidawa Zinariya irin halin ƙuncin da ya shiga biyo bayan kammala aikin gidan soja inda ya ce har gadin "stadium" ya fara domin samun na cefane inda daga baya aka sallame shi saboda tsufa.

"Kwanakin baya lokacin da Buhari ya zo Bauchi mu yi ido biyu da shi lokacin da zai shiga mota ya kira suna na muka gaisa kuma ya ce zai turo da mota a ɗauke ni a kai ni gidansa domin mu gana, amma hakan ya ci tura. Har Daura na je aka hana ni shiga gidansa.

Yanzu dai Mallam Ali Ɗan Borno yana zama ne a cikin garin Bauchi a Anguwar Rafin Makaranta.

Za mu wallafa muku cikakkiyar hirar mu da shi nan da wani lokaci.

Photos from Gimbiya TV's post 30/10/2023

Masallacin Harami da na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallama ne gurare mafi tsafta da aka fi kula da su a duniya.

Photos from Gimbiya TV's post 29/10/2023

Yadda Musulman ƙasar Palasɗinu dake zirin Gaza ke yiwa iyalansu ta’aziyyar rashin ‘yan uwansu da s**a mutu sak**akon hare-haren da sojojin kasar Isra’ila s**a kai wa zirin Gaza.

Photos from Gimbiya TV's post 26/10/2023

MARTANI GA ƳAN SOCIAL MEDIA: Duk Arewa Babu Wanda Ya Kai Rarara Damuda Da Matsalar Tsaron Da Yankin Ke Fama Da Shi

Ya k**ata ƴan social media ɗin da s**a juya wa mawaƙi Rarara su sani cewa duk yankin Arewa babu wanda ya kai Mawaƙi Rarara damuwa da matsalar tsaro da yankin ke fama da shi.

Kuma babu irin ƙoƙarin da ba ya yi wajen ganin an daƙile wannan matsala. Rarara ya bayar da gudummawa daga baiwarsa wanda har waƙoƙi ya rera na ankarar da shugabanni kan su tashi tsaye su kawar da rashin tsaro, daga cikin waƙoƙin akwai 'Jahata jahata ce' wacce ya rera kan rashin tsaron da jiharsa Katsina ke fama da shi, don haka ba wanda zai nuna masa damuwa da matsalar rashin tsaro domin jiharsa na fama da wannan matsala.

Masu zanga-zanga ba su fahimci irin ƙoƙarin da gwamnati ke yi ba ne, a lokacin da su ke zanga-zangar gwamnati ta ceto mutane sama da ɗari biyar kuma ta ƙarfafa tsaro a hanyar Kaduna zuwa Abuja inda matsalar rashin tsaron ta fi tsananta, mafi yawan mutane ba su san da haka ba, amma shi ya san da haka kan me zai fito ya yi zanga-zanga?

Daga Masoyin Rarara

26/10/2023

TUNA BAYA: Lokacin ana ɗasawa tsakanin Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso da Mataimakinsa Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Shin meye fatan ku game da waɗannan mashahuran ƴan siyasan?

Photos from Gimbiya TV's post 26/10/2023

DA DUMI DUMIN SA ....!!!

Kotun koli taki karban sabon korafin Atiku Abubakar. Na zargin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da takardar shaidar karatu na bogi a jami'ar Chicago.

Kotun Koli tace Atiku Abubakar ya makara da korafin nasa.

25/10/2023

Innalillahi wa inna ilaihil Raji'un.

Anyi rashin daya daga cikin
Dattawa Arewa Alhaji Adamu Fika.

Marigayi Alh Adamu Fika ya rasu ne a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba cikin jirgi sama a kan hanyar dawo wa Najeriya Daga kasar Ingila.

Wazirin Fika, Adamu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 90 Aduniya

Adamu Fika Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Nijeriya ne

Danburan Fika, Alhaji Idris Adama Kukuri shi ya tabbatar wa Daily Trust labarin mutuwar a wata ganawa ta wayar tarho.

Ubangiji Allah ya jikan sa da rahama yasa Aljanna ce makomar sa.

Photos from Gimbiya TV's post 24/10/2023

CIKIYA CIKIYA CIKIYA

Ana cikiyar wannan bawan Allahn mai suna Mustapha Rabilu ɗan makarantar Hayatul Islam dake garin Jos.

Ya bar gida jiya Litinin da safe sanye da kayan makarantar Hayatu. Kawo yanzu ba'san samu labarin inda yake ba.

Idan Allah yasa an samu inda yake za a iya kiran ɗan uwansa a wannan lambar wayar:

08032058880.
08038814413
08032311419

A taimaka a yi share.
Mun gode.

24/10/2023

Ku Taimaka Ku Ceto Rayuwar Wannan Baiwar Allahr Ana Neman Miliyan Biyu Domin Yi Mata Aiki

Sunanta Amina Sunusi tana zaune a unguwar Fagoji Dutse jihar Jigawa, tun tana wata huɗu a duniya take fama da ciwon kunkumi tsawon shekaru 21 ke nan tana fama da wannan ciwo, a yanzu ta samu karaya a kunkumin nata, za a yi mata aiki a asibitin kwararru na Rasheed Shekoni Specialist wanda likitoci s**a ce za a biya miliyan biyu.

Domin ƙarin bayani ko ziyarar gani da ido mara lafiyar na unguwar Fagoji Dutse, za a iya kiran wannan lambar domin ƙarin bayani 08086118760

Masu niyyar taimakawa da abin da Allah ya h**e musu kuma za su iya turawa ta wannan asusun da ke ƙasa.

Account number:0045619679
Name: Sunusi Balarabe
Bank Name: GT Bank.

Allah ya bada ikon taimakawa.

Photos from Gimbiya TV's post 22/10/2023

Allah ya azurta Hajiya Rahama MK wacce aka fi sani da Hajiya Rabi Bawa Kwana Casa'in samun aihuwa a yau.

A yau kuma aka tabbatar da ita a matsayin zaɓaɓɓiyar gwamnan Alfawa a shirin Kwana Casa'in na Arewa 24

Mansur Isah ce ta sanar da aihuwar a shafin ta na Instagram

Shin za mu iya cewa Hajiya Rabi'u has arrived Kenan?

Photos from Gimbiya TV's post 22/10/2023

SASHIN TALLACE-TALLE

Manyan shaddodi manya masu kyau da inganci. Muna Kantin Kwari Gidan Alaramma. Masu siya da gaske za su iya yi mana WhatsApp ko kira a 08035996090 Za mu tura muku kaya a ko ina ku ke.

20/10/2023

FATAKE SEASON 2

Zai fara zo maku daga ranar 12th November 2023 In Shaa Allah a tashar GASKIA TV PLUS.

*Lokacin nunawa*
Duk ranar Lahadi 8pm Ghana, 9pm Nigeria

*Lokutan Maimaitawa*

-Lahadi 11:30pm Ghana, 12:30am Nigeria

- Litinin 7am Ghana, 8am Nigeria

-Talata 7pm Ghana, 8pm Nigeria

- Laraba 5pm Ghana, 6pm Nigeria

- Asabar 12:30pm Ghana, 1:30pm Nigeria

Producer - Umar Uk

Director - YaseenAuwal

KBeautiful Actres with and also known as in movie📽📺👈







'sBest

Photos from Gimbiya TV's post 20/10/2023

Bayan Engr. Abba Kabir Yusuf shin wanne gwamna ne kuke gani zai iya wannan yunƙurin a Najeriya?

Photos from Gimbiya TV's post 19/10/2023

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya baiwa sakataren zartarwa na hukumar raya babban birnin tarayya (FCDA), Engr Shehu Ahmed Hadi, wa'adin sa'o'i 24 da ya bayyana matsayin gwamnati dangane da rushe wani bangare na masallacin Babban birnin Tarayya Abuja kasar.

Wasu sassan filin masallacin na kasa ya shiga cikin tsarin da zasu bi wajan Kara fada da Hanyoyin a birnin Tarayya Abuja. lamarin da ya sa mahukuntan hukumar ke neman a biya su diyya ta fuskar sauran filayen.

Kamar yarda Jarida Daily trust ta rawaito.

18/10/2023

Fitacciyar Jaruma ce a masana'antar Shirya Fina-Finai ta Kannywood, Shin kun gane ta?

18/10/2023

Anyi kira ga Gwamnati data kara yawan asibitoci dama daukar ma'aikatan da zasu dinga bada kulawa ga mata masu juna biyu a yayin awo da kuma haihuwa, domin rage yawan mace mace ga masu juna biyu a kasar.

Wani babban likitan Mata dake aiki da Asibitin kwararru na jahar Filato, Dr Golit Williams Nengak ne yayi wannan kira a yayin zantawa da wakilimu yayin bikin ranar tunawa da mata masu ciki da mace macen jarirai ta duniya ta wannan shekara.

Ana bikin ita wannan rana ce a duk 15 ga watan Oktobar kowacce shekara.

17/10/2023

VIDEO: A'isha Sulaiman ƴar ƙabilar Ibo da ta karɓa addinin Musulunci ta samu kyautar kujerar Hajji, kyaututtuka, kuɗi da aiki da gwamnatin tarayya

Photos from Gimbiya TV's post 16/10/2023

Gwamnatin Tarayya ta ce a shirye ta ke ta fara biyan basus**an da wadanda ke shirin N-Power ke bin ta Masu kula da shirin na N-Power ne s**a sanar da hakan yayin taro da wasu masu amfana da shirin a taron a Abuja .

An kirkiri shirin na N-Power a ranar 8 ga watan Yunin 2016, karkashin gwamnatin jam'iyyar APC, domin magnce matsalar karancin ayyukan yi da kuma inganta walla da cigaba .

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba, ta ce za ta fara biyan bashin alawus dinsu na watanni 9 a Nuwamban 2023.

Manajan shirin N-Power na kasa, Akindele Egbuwalo ne ya bayyana hakan a cewar The Nation.

Photos from Gimbiya TV's post 16/10/2023

Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi Na Buƙatar Taimakon Gaggawa, Cewar Imam Aliyu Indabawa

Ina kira ga iyalan Malam Idris, ƴan uwansa da almajiransa da su yi gaggawar ɗaukar Malam zuwa asibiti domin nema masa lafiya. Zancen gaskiya Malam na buƙatar ganin likitan ƙwaƙwalwa ba wai maganar cin fuska ba.

Duk me lafiyayyen hankali ya san abubuwan da Malam ya ke yi sun wuce neman suna sun ci karo da ƴantaccen hankali, musamman ma maganar da ya yi kan Falasɗinawa, da idona na kalli bidiyon yanzu haka ina da shi a wayata.

Sannan Malam kullum ba shi da aiki sai zagi da cin mutuncin mutane masu mutunci. Yadda ya ke gani duk Nijeriya babu malamin kirki sai shi kaɗai, shi ya sa ya ke cin zarafin malamai a mumbarinsa son ransa. Duk wata fitina da za ta janyo a yi ta cece-ku-ce Malam Idris sai ya taso da ita.

Ka duba ƙoƙarin da su Bala Lau da Sheikh Abdulwahab Abdallah s**a masa don ganin an fito da shi daga Kurkuku, amma mutumin nan yana fitowa sai ya hau kansu ya ce Allah ya isa tsakaninsa da su.

Ina mamakin masu zama a gabansa yana wannan hauragiya da kuma masu ba shi kariya, ko da ya ke an ce mutum ne mai arziki kuma yana kyautata wa almajiransa shi ya sa su ke binsa ido rufe.

Allah shiryi Dr. Idris ya ba shi lafiya.

Photos from Gimbiya TV's post 15/10/2023

A'isha Sulaiman Ta Samu Aiki da Gwamnatin Tarayya Tare da Tallafin Kuɗaɗe Masu Nauyi Domin Fara Sana'a

Biyo bayan videon da Zinariya ta yaɗa wa duniya na A'isha Sulaiman ƴar ƙabilar Ibo da ta karɓa addinin Musulunci, Musulmi a faɗin duniya sun kaɗu tare da tabbatar mata da cewa tana da gata inda s**a tallafa mata da taro da sisi domin ganin sun cika mata burin ta na samun aiki ko jari domin fara sana'a.

Sake videon ke da wuya, wani babban mutum mai riƙe da madafan iko a Najeriya ya tuntuɓi Zinariya inda aka tabbatar mishi da gaskiyar lamarin. Nan take ya wa A'isha Sulaiman albishir da samun aiki da gwamnati tarayya. A cikin kwanaki uku, A'isha Sulaiman ta karɓa takaddar k**a aiki da wata babbar ma'aikatar ilimi a ƙarƙashin wata jam'iar gwamnatin
tarayya a jahar ta.
Ga A'isha nan riƙe da shedar k**a aiki tare da wakilan Zinariya.

Bayan haka, A'isha Sulaiman ta samu tallafin kuɗi fiye da yadda ake tsammani domin fara kasuwanci.

Har wa yau, wata baiwar Allah wacce bata so a ambaci sunan ta ba ta canja wa A'isha Sulaiman kayan ɗaki baki ɗaya tare da yi mata tayel da fentin ɗaki kai ka ce amarya ce. Ta siya mata sabbin kujeru, injin wanki, firiji, gado, katifa, tukwane da duk wani abu da ka san ana wa amarya.

A'isha har wa yau ta samu kyaututtuka daga wajen mutane a jahar Bauchi da faɗin Najeriya da ƙasashen ƙetare. Har da muke wannan rubutun tana ci gaba da samun tallafi.

A irin bayanan da muke da su a hanu, ba abun mamaki bane ku ga A'isha Sulaiman a ɗakin Allah a Hajjin bana idan abu ya tabbata.

Ko ma dai ya ta kaya, za ku ji kuma zaku gani.

Muna godiya matuƙa ga dukkan waɗanda s**a taimaka da taro da sisi. Allah saka muku da alheri. Kuma Allah faranta muku k**ar yadda kuka farantawa A'isha Sulaiman.

Uwa uba, muna godiya ga mabiya Zinariya da s**a dinga sharing videon A'isha Sulaiman har ya kai ga inda ake so. Allah sakawa kowa da alheri.

Mun gode.

Hukumar Zinariya

14/10/2023

Al'ummar Fulani Da Mwaghavul na karamar hukumar Mangu a jihar Filato sun bayyana sun sharudar da za a kiyayesu kafin dawowar zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Al'ummomin biyu waɗanda s**a fara rikici da juna cikin watanni kadan da s**a gabata, wanda hakan ya janyo asarar rayuka da kuma dukiyoyi da dama tare kuma da raba dubbannin mutane da gidajensu.

Da yake magana yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a karamar hukumar ta Mangu Ranar Talata, wanda babban basaraken al'ummar kasar Mangu, Mishkhakam Mwaghavul, Da John Hirse ya shirya, Shugaban kungiyar Matasan kabilar Mwaghavul, S. D Dankaka, yace kafin zaman lafiya ya dawo, sai an kai musu hare-hare da kuma lalata musu amfanin gona da kuma tura shanu cikin gonaki domin yin barna.


A nashi jawabin, Saidu S. Jauro, Shugaban matasan kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen Mangu, shima yace idan ana bukatar zaman lafiya a yankin, sai an daina tsarewa da kuma kashe kabilar Fulani akan titin mota.

Ya kuma zargi rundunar tsaron jihar Filato ta Operation Rainbow da jagorantar kai musu hare-hare domin sace musu shanu.

Daga karshe ya bayar da shawarar hada kwamitin zaman lafiya da zai hada da al'ummar Fulani da Mwaghavul domin lalubo hanyoyin dawowa da zaman lafiya a yankin.

Da farko a jawabinsa, babban basaraken al'ummar Mangu, Da John Hirse, yayi kira ga bangarorin waɗanda basa ga maciji da su yafe wa juna kuma su baiwa zaman lafiya dama domin dawowar ci gaba a yankin.

A jawabinsa, Shugaban rundunar wanzar da zaman lafiya ta Operation Safe Haven, Manjo Janar A E Abubakar ya bukaci dukkannin masu ruwa da tsaki da su kiyaya ababen dake janyo rikici a yankin, kana kuma ya bukaci bangarorin biyu masu husumar dasu yafe wa juna kuma su cire dukkan wani gaba da sukeyi da juna a zukatar su.

A nashi bangaren, babban bako a wajen taron, Alhaji Haruna Sambo Muhammad, Sarkin karamar hukumar Wase, ya bukaci matasan bangarorin biyu da suyi koyi da kyakkyawan zamantakewa da iyayensu s**ayi a baya wanda ya kawo dumbin cigaba a yanzu.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Videos (show all)

A ranar Lahadi ne, ofishin kakakin Majalisar wakila na tarayyar Najeriya Honourable Dr. Tajudeen Abbas(Dan iyan zazzau),...
VIDEO: Haɗakar Ƙungiyar Musulmi Ƴan Jam'iyyar PDP a Filato Sun Yi Kira ga Kotun Ɗaukaka Ƙarar zaɓe da ta yi Adalci Wajen...
Cikakken Jawabin Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf akan Hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙarar zaɓe na yau
Tattaunawa da shugaban ALGON na bangaren jam'iyyar APC a jihar Filato, Miskoom Alex Naatuam, game da rikita-rikitar shug...
Jiga-jigan jam'iyyar PDP sun yi cikakken bayani game da ƙwace kujerun su da kotu take yi a jahar Filato tare da tabbatar...
Gadi nake yi domin ciyar da iyalina, a gadin ma an sallame ni saboda na tsufa - Cewar Tsohon Direban Buhari na gidan Soj...
Shirin FATAKE SEASON 2Zai fara zo maku daga ranar 12th November 2023 In Shaa Allah a tashar GASKIA TV PLUS.*Lokacin nuna...
Al'ummar Fulani Da Mwaghavul na karamar hukumar Mangu a jihar Filato sun bayyana sun sharudar da za a kiyayesu kafin daw...
Hajiya Layla Ali Othman ta fashe da kuka yayin da ake saka ta a lalle.
SHAFI MU LERA: Ku kalli yadda masu satar mazaƙutar maza suke lalube maza su kwashe musu abubuwan su.
Na tsinci kaina a mawuyacin hali bayan karɓar Musulunci amma har yanzu ban yi nadamar sauya addini ba Cewar Aisha Suleim...
A ranar Asabar ne Gidauniya Mai Akwala charity Foundation karkashin Shugabancin da daukar nauyin Hon. Abubakar Kabiru Ga...

Telephone

Website

Address


Abuja
Kano
Other Broadcasting & media production in Kano (show all)
KBC News KBC News
First Office No. 115 Dorayi Kano
Kano

Wellcome to🎙️Kano Broadcasting Corporation📡 @Kbcnewsdaily. This is media broadcaster online news📰

Moh’Waves Concepts by Moh Usman Moh’Waves Concepts by Moh Usman
Kano

Media •Audio Content• Voice Over• Unplugged: The Moh Usman Podcast• www.google.com/podcasts?feed=aHR0

Jalla TV Jalla TV
171 Mission Road Bompai Kano
Kano

Connect with practical solutions on Economy, Education, Energy and a touch of Entertainments.

Ibrahim Suleiman Tsamiya Babba Ibrahim Suleiman Tsamiya Babba
Tsamiya Babba, Gezawa
Kano, TSAMIYABABBA

Nigerian journalist Media consultant Sports Analysis Reporter Newscaster Programme presenter

DNN RADIO DNN RADIO
26 ADEBOLA Street
Kano, 0001

An audio newsroom by DNN & MEDIA FOUNDATION for news coverage and analysis | from [email protected] | 0809-1477-345 | DNNRadio.com

FIBAN KANO STATE FIBAN KANO STATE
Abba Road Sabon Gari Kano
Kano

The only people that voiced out for the voiceless once. We are Radio Presenters and Reporters.

Mai Shadda Reposted Mai Shadda Reposted
Kano

Barka Da Zuwa Dandalinmu Na Yada Alkairan Abubakar Bashir Maishadda

AZ Hausa AZ Hausa
Kano

Khairiyyah TV Khairiyyah TV
State Road, Tarauni
Kano

Albayan Islamic TV kafa ce a YouTube da yake yada karaturan malaman addinin musulunchi na Nigeria